Showing 18001 words to 21000 words out of 101986 words
ƙaramar dariya ta kalli Ammy ta ce
"Ammy barka da rana da fatar kuna lafiya"!kallon ta Ammy tayi ta ce
"Lafiya ƙalau Hamida,ya zagayen naku ya kasance ne hope you enjoyed it"?faɗaɗa fara'ar dake saman fuskar ta tayi ta gyaɗa ma Ammyn kai daga haka ta hau buɗe food warmers ɗin dake jere bisa dinning table ɗin ta ɗauko serving spoon da zumar ɗibawa ta zuba a plate amma wani irin magana da Ammy ta mata mai kama da faɗa faɗa ya sa ta dakata ta dago ta sauke idanun ta a fuskar Ammyn wanda ya saka Ammyn jin ba daɗi dan itakanta ta ji ajikin ta kamar ta zafafa abun da yawa sai ta sauke muryar ta ƙasa tana faɗin
"Kiy hkuri Hamida ba fada nake miki ba,kin gane,wannan abincin da nayi na yi sa ne dan in yi surprising ƴar uwar ki dan jiya cikin hirar mu ta sanar da ni cewa tana marmarin cin abinci irin wannan wai jiya ta ci irin sa a outing ɗin su da yayan ku Khalid sai na ga bai dace a ce mutum na da abu a gida amma yana cin na waje ba shi ya sa na shiga da kaina kitchen ɗin na girka mata,yanzu da haka ita muke jira ta dawo sai mu ci abincin dan na kira Khalid kuma ya faɗa min suna hanyar dawowa shi ya sa na sa aka jere su a nan,amma akwai wani variety ɗin a other food warmer kina iya farawa da shi kafin ki dawo!!..
Kallon da Hamida ta bi Ammy da shi ne ya sa Hajja riƙo hannun Ammy ta ƙarƙashin dinning table tana girgiza mata kai alamar bata kyauta ba duk da ita kan ta ba haka ta so ba,ta so a ce wacce aka yiwa abincin ce ta fara gani amma na yadda zasu yi dan ita kan ta Hamidar tasu ce...
Rasa abin yi Ammy tayi sai ta tashi tsaye ta hau bubbuɗe food warmers ɗin da ta ce na fifi ne ta ɗau wani serving spoon ta fara zubawa Hamida a plate,har yanzu kallon ta Hamida ke yi da tsantsar mamaki da alhini..
Ammy na gama zuzzuba mata ta kalle ta tana faɗin
"Bismillah"!girgiza kai Hamida tayi alamar ba zata ci ba,serving spoon ɗin dake riƙe a hannun ta ta saka cikin food warmer ɗaya dake kusa da ita tayi serving kan ta cikin plate ta saka spoon ta janyo cup ta tsiyaya chilled coco smoothie a ciki ta kwashe ta bar dinning musu area ɗin zuwa sama zuwa ɗakin ta...
"Duk bin ta da ido suka yi suna jin wani iri a zuciyar su duk su biyun,har dai suka rinƙa ba kan su laifin abin da Hamida tayi a yanzu na barin su zuwa ɗakin ta...
Sede har yau gani suke kamar adaidai suke game da lamarin su da fifi
Ko sau daya sun kasa nitsuwa su fahimce cewa sune asalin silar jefa hamida a cikin dukan wani hali datake ciki arayuwanta
***
Su fifi kuwa zagaye sai inda ba a ƙirƙiro ta ba amma kusan kaf wuraren buɗe ido sai da Khalid ya kai Mufida suka ba idanun su abinci rough driving kuwa fifi sai da ta saka Khalid raina kan sa dan tun da ya miƙa mata maƙullin motar bayan fitowar su daga wata resort ta riƙe sitiyarin motar,toh bata sarara ba haka ta rinƙa tuƙi tana yi tana jijjiga motar,sai tsoro ne kuma ya shigi khalid dan duk rashin jin sa ta fannin tuƙin ganganci bai taɓa kuskurewa yayi irin wannan tuƙin ba sai gashi mace na yin irin sa...
So yayi ya kai ta wani wuri da ba kasafai ya cika zuwa ba sai dai kiran Ammy ya hana sa dan saka shi dawowa da fifi gida tayi akan ta gama yi mata surprise ɗin da ta daɗe tana mata tun bayan fitar su..
Tunda surprise aka ce sai bai faɗa mata ba ya juya akalar motar zuwa hanyar gida sai ta tambaye sa lafiya sai ya nuna mata ba komai kawai wani emergency ne ya same sa kuma ba yadda ya iya..
Tun a hanya yayi ta bata haƙuri akan gobe zasu cigaba ita kam ƴar son jin daɗin rayuwa ta nunar mai ba komai su koma gidan...
Suna hanya suka tsaya ya siyo mata ice cream vanilla flavour suka dawo gidan tare,duk ta matsu su dawo ta sha ice cream ɗin dan tun jiya take sha'awar ice cream ɗin..
Da shigowar su Ammy ta taso ta riƙo hannun ta tana mata sannu da zuwa haɗe da tambayar ta ya fitar tasu ta kasance har da tambayar da fatar dai Khalid bai yi tuƙin ganganci da ita ba cikin mota..
Haɗa ido suka yi ita da Khalid sai ya hau girgiza kai yana faɗin
"Ba zaki so ki san ya drive ɗin nan ya kasance ba Ammy,ga ta nan tambayeta meya faru?
!kallon ta Ammy tayi da mamaki sai kawai taga ta fashe da dariya har da riƙe ciki tana faɗin
"Ammy Khalid matsoraci ne kawai dannna karɓi tuƙi sai ya ruɗe wai ina tuƙi da too much speed kuma fah baki gani ba Ammy ahankli nake tafiya
"ta ƙarasa tana kuma kallon sa sai ya kaɗa kan sa yana faɗin
"Haka kika ce ko?toh ba zan fita da ke ba gobe sai dai mu fita tare da Hamida
"saurin marairaice fuska tayi tana girgiza kan ta haɗe da langaɓar da shi alamar ban haƙuri sai ya saka mata dariya yana faɗin
"Ammy yakamata abata kyautar ta kar ta ƙulle min ciki da abin dariya"!!jin haka sai fifi ta dubi Ammy tana faɗin
"Ammy surprise"?gyaɗa mata kai Ammy tayi tana jawo hannun ta zuwa kan dinning table ta zaunar da ita sannan ta saka ta rufe idanun ta da sharaɗin kar ta buɗe sai ta ƙirga uku..
Da murna fifi ta jijjiga kai cikin zumuɗin son ganin surprise ɗin,haka aka yi bata buɗe idanun ta ba sai da Ammy ta ƙirga ɗaya zuwa uku sannan ta buɗe idanun ta ta sauke sa kan abinci exactly irin wanda ta ci jiya a yawon buɗe idon su...
Bata san lokacin da ta taso ta rungume Ammy ba tana ta yi mata godiya sai kuma tayi saurin sakin ta ta dawo ta zauna ta fara yunƙurin zuba abincin amma Ammy ta hana ta ta karɓe spoon ɗin ta zuba mata da kan ta har zama tayi akan zata ciyar da ita..
Tana buɗe baki sai tunanin Hamida ya bijiro mata ko ya suka yi da aminiyar nan nata bata sani ba kuma tana son jin karshen zancen dan haka ta maida bakin ta ta rufe tayi wuf ta miƙe Hajja da yanzu take leƙo su dan ganin ko Mufidar ta dawo sai ta gan ta tana sauri sauri zata haura sama..
Kiran sunan ta tayi amma bata juyo ba ta cigaba da tafiya tana ce mata
"Hajja ina zuwa Hamida nake son dubowa yanzu zan dawo"!..
Haɗa ido Hajja tayi da Ammy dake riƙe da spoonful of abincin da ta ɗibo da bawa fifi a baki..
Ajiyar zuciya Khalid yayi yana juyawa da nufin tafiya sashen sa dan kimtsawa kafin ya dawo a yi lunch ɗin dashi shima.
Zama Hajja tayi tana kallon Ammy da alamar tambaya sai dai ta furta..
"Anya Hamida ba damuwa gare ta ba kuwa?kin ga yadda jiya ta rinƙa janye jikin ta daga gare mu sannan yau ɗazu ta sake jikin ta amma ɗazu kuma ta rikice kamar ba ita ba?ina ga ki kirawo min Nuhu in ji asalin abin dake damin yarinyar nan dan ina jin tsoro"
..kallon ta Ammy tayi bata ce komai ba ta ɗauko wayar ta da nufin kira sai wani kiran ya shigo..
Dubawa tayi sai ta ga ƙanin nata ne wato mahaifin su fifi dan haka ta ɗaga kiran ta miƙowa Hajja..
Hajja na sakawa a kunnen ta ta fara magana kamar ran ta a ɗan ɓace sai dai bata yi faɗa mai yawa ba..
Haƙuri ya bata dan shi dama kira yayi dan ya ji ya lafiyar yaran nashi sabida yayi ta kiran layin Mufida amma bata ɗaga ba sai ya kira na Hamida amma itama bata ɗaga ba shi ya sa kawai ya kira na Ammyn..
"Hajja ai duk jikokin ki ne hala bata jin magana ne kin san Hamida ta bambanta da ƴar uwar ta,
Hajja tace ah a Mufida ce ke da matsala itace wacce ya kamata tayi ta zaman shiru amma sai ƴar uwar ta ce ke yin waɗannan ɗabi'un?
Dady yace haka hamida take amma in kuka saba ba zaki ga shiru shirun ta a matsayin matsala ba dan haka halittar ta yake"ajiyar zuciya Hajja ta sauke dan tayi tunanin wani matsalar ne da Hamida ashe kawai tsabar kama kai ne..
**
Fifi ta daɗe tana ta sallama a ƙofar ɗakin Hamida sai dai babu amsa,deciding shiga ɗakin kawai tayi,tura ƙofar ɗakin tayi sai ta ga Hamida kwance kan gadon ta alamar bacci ya jima da ɗaukar ta,gefe guda a ƙasa plate da spoon ne wanda ta ci abinci da shi,tsugunawa tayi ta kwashe plate da cup ɗin sannan ta kalli Hamidar tana murmushi a same time ta ce
"Please Hamee ki yi ki farka i have a lot to tell you,yau...is one of my best days a rayuwa ta kuma na san Allah na jin addu'a ta and zai amsa min because is a positive wish"kallon Hamidar tayi na dan wani lokaci sannan ta juya ta fice...
Haka ta sauko ƙasan ta same su duk suna zaune har da Khalid,nan take ta ji damuwar ta akan ƴar uwar ta Hamida ya ragu dan ta ga fitilar dake haske mata duhun ta wato Khalid ɗin ta..
Zama tayi da annashuwa a fuskar ta ta fara ba ammy haƙurin tashi da tayi ta bar ta da spoon a hannu ɗazu,ƴar lele ce bata laifi bare ɗazu daddyn su fifi ya tuno masu da matsalar fifin sai duk suka ji jikin su yayi sanyi amma ganin ta ta fito cikin fara'a sai suka ga kar su saka ta cikin zargin wani abin..
A walwala aka ci abincin Khalid na ta labarta masu yadda fifi tayi da shi cikin mota ɗazu,duk sai su rinƙa goyon bayan ta suna mai dariya,da haka dai aka yi lunch lafiya aka kammala Hajja ta ja hannun fifi zuwa sashen ta wai tana so su yi hira ta jika da kaka,wannam hikimar duk dan kar su bar fifin cikin kaɗaici da damuwa ne ya sa Hajja bijiro da wannan tsarin dan kam ta...
#Mamuh_*Mamuhgee*_
*10*
Da isar su ɗakin Hajja Fifi ta hau koɗa ɗakin game da zuzuta kyaun d ɗakin yayi dan har wani qamshi yake fitarwa kamar ba na tsohuwa ba komai tsaf tsaf da shi..
Jawo hannun ta Hajja tayi ta zaunar da ita bisa kan silver colour royal bed ɗin ta da ya sha kayan ado na zamani kama daga kab throw pillows da aka zagaye gadon da shi kamar dai yadda ake gyara gado irin ta mutanin da sai dai wannan a zamanance aka gyare sa zanin gadon kan sa abin kallo ne.
Hajja ta gyra zama ta na ta famab murmushi dan ganin halin farin cikin da fifi ke ciki sai ta bar ta tayi ta kalle kallen ta tana yabe yaben ta har ta gama dan kan ta ta dawo ta zauna tana cigaba da yaba ɗakin Hajjan har ta so ba Hajjan dariya..
Riƙo hannuwar ta Hajja tayi tana kallon fuskar ta dake da ragowar murmushin da ya bayyana two sided dimples ɗin ta,hakan ya tuno ma hajja da mahaifiyar su fifin sai tausayin fifin taji ya kama ta sosai duba da irin rayuwar da yarinyar ta taso babu kula ta musamman daga uwa sakamakon bata raye sannan ga jarabtar da ubangiji ya mata na rashin cikakken lafiya,duk waɗannan dalilai ya sake jefa tausayin ta a zuciyar Hajja..
Nan da nan hawaye suka cicciko daga idanun ta amma bata bari fifi ta gama fahimtar dalilin cikowar hawayen ba bare ta tambaye ta,sabida ta gama sawa a abu mafi sauƙi a gare ta shine ta aiwatar da abin dake ran ta ayanzu game da rayuwar fifin dan a ganin ta hakan ne kawai zai fiye mata kwanciyar hankali..
"Hajja ɗakin ki kamar na amarya sabuwa fil,ji kamar ɗaki na ne"!!
kallon mamaki Hajja ta mata sannan ta ce da ita
"Da gaske ɗakin ya maki kina so a ce kina da irin shi ko fiye da shi ko!?da sauri fifi ta gyaɗa mata kai tana dariya..
Hamdala Hajja tayi jin da bakin ta ta ma furta sha'awar ta ga son samin ɗakin kan ta ba tare da ta cigaba da zama a ƙarƙashin su ba amma a ƙarƙashin mijin ta...
"Dama na jima ina son yin wannan magana takwara ta sai dai rashin wanda zan tunkara da maganar ya sa na barwa kai na amma sosai na damu da samun cigaban rayuwar ki a mataki mai inganci da ba zamu sami ɗar ko fargaba ba, amma tunda yanzu kin yi maganar da kan ki ina so ki faɗa min ra'ayin ki kar in maki shigar bazata,kina da wanda ya kwanta maki a rai ne da kike jin ba zai maki riƙon ƙasƙanci da son zuciya ba in an aura maki shi?
Fifi tace haajja aure?laahhh,abin dariya abin mamaki wai fifi da jin kunya sai ta faɗa jikin Hajjan tana ta ɓoye fuskar ta dan ba zata taɓa mantawa ba akwai ranar da suka zauna lokacin a germany suna lissafa irin mazajen da suke son aura ita da Hamida,sai bayan sun gama hirar har Hamidar ta wuce sai ta zauna da zuciyar ta akan in har Allah ya bata aron rai tayi aure ta sami ƙaruwa toh in mace ce sunan Hamida zata saka mata in kuma namiji ne sunan daddyn su zata saka mai har ta samo other name da za a rinƙa kiran baby girl ɗin da shi haka ta samo wanda za a na kiran mai sunan daddyn da shi...
Dariyar manya Hajja tayi dan ta ga amsar tambayar ta ƙarara a fuskar fifi tunma kafin ta amsa,sai ta rungume ta tana taɓa bayan ta game da ce mata
"Amma ni kam takwara ta wanene wannan saurayin ne da yake mana shigar bayan gida ba tare da mun sani ba,fata na dai ba baturen ƙasar can kika samo mana ko?dariyar itama fifin tayi tana cewa Hajjan toh in baturen can ɗin ne ma ba zata so shi ba..
Sai da fifi ta gama juye juyen ta sannan ta rufe idanun ta da tafin hannun ta tana faɗin
"Hajja ai kin san shi dama kike wani kwane kwane "...tana gama faɗin haka ta tashi ta fita daga ɗakin a guje wannan tabbaci ne na alkunya dake jinin matan arewa koda ba anan ta taso ba...
Ganin yadda ta fita da gudu sai Hajja ta fashe da dariya tana girgiza kai dan ko ba a faɗa mata ba ta san hasashen ta ne ya zamo gadkiya kuma da yardar mai duka zata ga tayi iya ƙoƙarin ta dan cika wannan hasashe nata..
Mezai fiye mata dadi ace an Hade mufiida da khalid,ita kuma hamida in Allah ya so ba sai akara ma yayan shi saheeb ba?
Da gudu fifi ta nufi hanyar balcony dan shigewa ɗakin ta dan bata san tana da kunya mai tsanani ba sai yau da Hajja wacce take a matsayin kakace ma a gare ta toh ina ga Ammy ce ta mata wannan maganar,lallai da ta daɗe bata bari Ammyn ta ƙara saka ta a ido ba..
Tana cikin wannan yanayin ta ji kamar ta bangaje mutum sai tayi saurin buɗe idanun ta ai kuwa tayi tozali da Hamida,take ta kuma jin wani kunyar sai ta matsa ta cigaba da tafiyarta..
Hamida da dama ita ta fito nema sai ta tsaya a tsaye tana mamakin dalilin farincikin fifi amma sai ta basar ta ɗage kafaɗun ta ta ƙarasa saukowa ƙasar ta ɗau abin da zata ɗauka ta juya ta hauro saman...
Zata wuce kenan ta ga fitowar Hajja cikin fara'a da ragowar dariyar mamakin fifi,ko bata tambaya ba ta san labarin gizo bai wuce koƙi,fifi ta fito ɗazu da fara'a a fuskar ta tana rufe fuska yanzu kuma Hajja ta fito da nata fara'ar..
Ɗage kafaɗa tayi alamar ba matsalar ta bane,gaida Hajjan kawai tayi irin gaisuwar barka da war haka,bata tsaya jiran amsa ba tayi gaba...
Muryar Hajja ta jiyo tana kiran sunan ta sai ta dakata haɗe da juyowa cikin mamaki ta kalle ta..
Da kan ta Hajjan ta ƙaraso ga Hamida ta riƙo hannun ta na hagu da babu komai ciki tana kallon ta daga bisani ta tambaye ta
"Wai nikam Kin ga min Mufida kuwa? ina ta jiran dawowar ta amma da gaske tafiyar tayi dan kunya ta wai ta ji"
ajiyar zucitayar Hamida tayi a zuciyar ta kuwa sai cewa tayi _"Hajja da abin ban dariya take toh ni ina ruwa na da wata kunyar ta da fifi ta ji har take tambaya ta ko na gane mata ita,ai wannan tsakanin su ne,yanzu dama dalilin da ya sa ta dakatar da ni kenan ashe?ohhhh,,fifi,fifi,fifi ko nauyin ta basu ji kan su tsaye suke nuna mata wariyar soyayya,ko da yake ai komai ya kusa zuwa ƙarshe illar in na kasa cigaba da haƙurin ne amma da zarar na daure toh zan mori haƙurin da na daɗe ina yi"_..
Jin tsyi shiru sai Hajja tayi saurib bijiro da tunan kafin ta dubi Hamida ta ce da ita cikin raha
"Hamida dama maganan aure ne?ko dai ke ma haɗa ku zamu yi ne dan na ga kin fiye son rayuwar kaɗaici nidai wannan salalan ba ajina ba?
Hamida taja tace haajja aure kuma?
Hajja tace eh
Daa wai nace mubawa mufida khalid ke kuma tun da ba wani shkuwa kukayi ba ai sai ahada ku da yayanku ko?kuma wannan haɗin shine zai yi daidai da tsarin rayuwar ki..
Wani kallon durus tayi ma hajja kanta na wani irin juyi,idan da