Showing 6001 words to 9000 words out of 101986 words
biyo bayan tane tace
Hamida Waye ne?
Tun kafin hamidar ta amsa idanun ta suka sauka akan tarin boxes dake gaban ta awajen
"cike da mamaki ta durkusa gabansu tace waw nawaye?waya kawo miki.. masha Allah..
Nan Hamida tai saurin cewa Bafa mani aka kawo ba
Mai bada sakone yazo shima bai gaya min komai ba sai dai in mun bude hala xamu gani
Nan fifi ta taimaka suka tarkato dukan su suka dauko box daya daya a hannun su suka shigo har gaban mahaifin su da shi saidai baice uffan ba har suka shiga budewa
Atare suka kai hannun kan wani dan madaidaicin katin da aka manno sakon tare da shi wanda sunsan dole anan ne zasu ga sunan wanda yayi sakon da wanda aka aiko ma
hamida ce tayi nasaran fara dora hannu ta akai dan haka ita ta dauki katin cikin warware makullin sa ta bude shi tsaf ta shiga karancewa
Sako ne me cike da nuna tsantsar so gata da kuma kauna wanda yayi mummunan fallasa girman irin kewar ta da za'ayi...
tsaban kalaman da aka rubuto sun tsaru cikin nitsatsiyar harshe mafi sanyayawa a cikin sassanyar yanayi hamida ta tsince kanta nan take ta shiga maimata kalaman ma zuciarta wanda yayi musabbin janyowa idanun ta cikowa da ruwan hawaye
Danne duk wani abun da takeji tayi ta karance har karshe,ina ma ace ko sau daya zata same irin wannan damar arayuwan ta
Waye zai so ta ya fifita itama ya turo mata wayannan kalmoni masu ma'ana wanda zai sa zuciyarta tayi saurin amincewa da cewa ita ma mutum ce wanda ta cancanci nuna kulawa da kauna
Duk yadda dadin kalaman suka karbu suka kuma sanyaya zuciyar ta suka ratsa ta hakan bai sauya mata jin komai ba dan kuwa babu sunan ta a jiki sunan yar uwan ta mufida ne Kenan sakonnin na mufida ne saidai bata ga sunan wanda ya aiko ba
Jiki a sanyaye ta mika mata batare da ta nuna yanayin data tsinci kanta na kishi da jin haushi akan fuskan ta ba.
Nan fifi ta amshe sakon tana kan tambayarta nawaye?wani shiru ne kawai ya ratsa wajen har fifin ta kammala karantawa dakanta ta dago idanuwan ta da zimman yin nazarin wanda zai iya aiko mata kyautar
charaf sai idanun ta suka sauka akan wani abu,shima a killace yake shikadai ana shi gidan a gurguje fifi ta dauko shi ta budeShi
Wani abun wuyar danyen dutsen safaya(saphiere)ne kalar sa ya shiga ja sosai yana faman sheki kamar asalin duwatsun diamond
Design din bana engine ko bugun kamfani ba bane asalin hannun kwarancewa ne ya tsara zaman zanen aka dedeta siffar duwatsun ta inda zaiyi matukar kyau wanda ko kallo daya bazai ishesa ba
Wannnan shine abun wuyar data gani a wani jaridar london times tace tana matukar sha'awar sa kuma tasan wa dady kawai ta nuna sukayi hirar kenan shi ya mata wannan sakon?tunda in ba shi ba babu wanda ta taba gaya ma wannan zancen
Daga yanayin yadda yay tsaye yana kokrin saka fuskn tausayi ta fahimci cewa tabbas shi din ne da wani irin gudu ta taho ta fada jikin sa ta saki wani irin kukan murna da tsananin kaunar sa
Tace. "Dukkan wayannan nawa ne? Nagode dady na Suna tayi dai hamida batace musu uffan ba
Wani shiru tayi agefe tana kallon su cikin tuno da Allah me kyautar kunci,..
Agaban ta mahaifin su ya tallafo fuskn fifin yana gaya mata maganganu masu dadin ji,yana me tabbatr mata cewa zai iya sallame dukan arzikin sa da komi nashi a duniya domin jin dadin ta da samun kwanciyar hankalin ta,kayan data sa ajikin ta kalar ja ne dan haka ta warware abun wuyar kamar zata kwama sai ta kuma ta fasa ta dawo tana kallon yar uwanta hamida dake kwakwulo murmushi da kyar
Da faffadan nurmushi fifi ta karaso wajen ta tana me damka mata abun wuyar tace hamida sakamin"ba musu hamida ta karbe,fifi tana ta surutun ta cikin bata labarin abunda ya wakana alokacin da sukayi hirar da daddy.
"Wani irin kishi da damuwa shi yake cin zuciar hamida amma ahakan ta daure ta shiga dannewa da tattausan lafazi tana amsata cikin sautin murmushin ta me fallasa tsananin kuna da ciwo
Warware abun wuyar tayi ta zago da shi a wuyar fifi tana malkaya mata last hook din abun wuyar,yadda ya xauna a wuyar fifin yay matukar kyau ya dada sawa takeji har can cikin ranta dama ace itace ta mallake sa..
Dauke kai tayi cikin sauke maganganun zuci a cikin dukkan tarin kyautattukan nan yanzu babu nata ko daya aciki?
Ta gama fahimtar cewa Bawai ana mata hakan dan ba'a son ta bane mancewa da ita akeyi agabanin farincikin yar uwan ta
Yaya zataji aranta me takeji duk babu wanda ya taba yin la'akari da hakan.
Zama sukayi dukan su suna cin abinci suna hirar ban kwana still wani shiru hamida tayi tana tura abincin bakin ta kadan kadan sakamakon rashin dadin sa datakeji abakin ta
Bayan sun gama sun fito zasu wuce nan ma su dr fatima yonas da yayan ta duka biyun suka tada nasu wasar inda gaba daya suka fi bada muhimmanci da kulawar su akan mufida,har hawaye sukayi ma juna alkwarin zasu na kirar ta sunyi shi yafi abun a kirga
10am na safiya suka isa aiport babban jirgin zirga zirga na kasan shiya kawo su nigeria aqashe garin ranan asabar karfe 2 na rana..
Kusan dukkan mutanen familyn sune suka zo tarban su,yayar baban su ammy khalid harma da kakar su hajja...
To Hamidar ce ta soma isowa garesu domin ta bar mufida acan baya tana famar tattara nata kayan.
Kallo daya ta musu ta gane su inda ta taho,nan suka tarbe ta da murna da fara'a ayayin da dukkan hankalin ta ita kuma ya koma kan kyakyawar hadadden namijin dake tare da su wanda take kyaun tsammanin cewa shine KHALID MAKARFI wato yaron ammy na biyu
zuciyarta ne ya shiga tsananin bugu ayayin da suka kalle juna suna masu sakar ma juna murmushi me sanyi
Su ammy da hajja kuwa sai tambayar ina fifi take?da alaman ita kawai suka fi so su gani so tsaban nuna zakuwar su da rawan jikin su ko hamidar ma bata iya samun damar nitsuwa ta amsa su dakyau ba
Haka kawai hamida taji khalid ya mugun dauke mata hankalin ta domin kuwa babu marabar sa da irin namijin data ke muradi a zuciar ta wanda takejin duk duniya da shi kawai zata ita rayuwar ta
Daga yanayin yadda suke satar kallon juna hajja tayi murmushi sbd Shi khalid dama yafi yayansa SAHEEB MAKARFI sakewa dason mu'amala da mutane Kuma gidan kaf yafisu rashin qyamar mutane yafisu fara'a da tausayi Dan komai na uwarsa ammy ya dauko
Sama sama suka gaisa da shi sai ya dan kawo Hannun sa zai karbe Troleyn hannun ta yana mikowa kamar daga sama yaji an wani tunkude sa a mugun razane ya dago kansa ya juyo inda yayi gamo da wata kyakyawar surar data dauke mai numfashi atake ta kuma tafiyar da shi sumewar tsaye yayi yana me tsura mata brown eyes dinsa cikin yanayin da ba sai ka tambaya ba
Hakika yasan yau yaci karo da muradin zuciyar sa
#Mamuh_*KNM*_
https://www.youtube.com/channel/UCMylPCg0TCgTWAmy6HHvcEQ
PLEASE SUBSCRIBE
*5*
Idanun sa kyar a kan wannan kyakyawar surar da ya zamo mai abu mafi haske tun tashin sa daga safe zuwa wannan lokaci..
Fifi kuwa Hankalin ta ba a kan sa yake ba sai kan yar'uwar ta mafi soyuwa a gare ta wacce ita kuma hamida gaba daya nata hankalin a kan na Khalid yake sakamakon taimakon da ya kawo mata wanda ita a zuciyar ta ji tayi kamar shima ya fahimci wani sirrin dake zuciyar ta ne da bai jima da darsuwa ba..
Da fara'ar ta cikin maido hankalin ta ga Hamida ta shiga daga mata hannu tana mata nuni alamar ta zo ta taimaka mata trolley din ta ya budu har kayan ta suna shiri zubewa ga kuma sauran tarkacen ta da take kan kwasowa daga jirgin..
Khalid dake daf da rike trolley din Hamida a hannun sa idanun sa gaba daya yakoma wannan kyakyawar surar rasa abin cewa yayi,yana iya fadawa zuciyar sa cewa tunda yake tunda yake mu'ammala da yan mata masu ji da kyawun fuska da kyawun dirir halitta bai taba dirar da idanun sa kan mace mai irin wannan surar ba,ba wai hasken ta ne ya rude sa ba a'a,tsantsar kyawun ta ne ya ja hankalin sa a haduwar idanun su na farko..
Hamida dake tsaye tana kallon ikon Allah ganin ita ce aka zo taimakawa da daukarwa kayan ta amma kuma an tsaya ana karema yar'uwar ta Mufida kallo,kallon da ko makaho ne ya san ba kallon da kowa kewa kowa bane,cikin wannan kallon akwai abubuwan fassarawa da dama sai dai in mutum bai da lura da la'akari akan abubuwa..
Ganin Hamida tayi tsaye ta kasa responding mata kuma har yanzu babu wanda yayi la'akari da zuwan ta sakamakon shigowar baya da ta yi kuma ba wani magana tayi ba bare muryar ta ya ankarar da su cewa ta iso,shi kadai Khalid din ya san da zuwan ta acikin su sai hamida dake tsaye..
Maida dubar ta tayi ga Khalid din dan ganin wa ta buge a rashin sani nan take idanun ta ya sauka a kan kamanni jini da suke danyi da daddyn su..
Wani irin kallon karshe ta mai a kyau,idanun ta ko kiftawa basu yi ba ta ware su kyar a kan kyakyawar fuskar sa mai cike da abin kallo dan kuwa wannan kallo nasa da tayi babu abin da ya fado mata fiye da mijin dake cikin mafarkin ta..
Ba taba ganin khalid tayi ba sai yanzu amma da ganin haduwar sa ta ji wani bakon abu ya ziyarci zuciyar ta wanda bata san menene shi ba amma ta san akwai wani abu da yake rubutacce da zai faru a tsakanin su nan kusa ko anjima..
Magana ne ya fito masa ba tare da ya san ya fito ba hakan ya faru ne sakamakon wani abu da ya rinƙa tsikarar sa wanda bai san menene ba..
"Mu...fffida"!?ya kira sunan da sigar tambaya dan ya tabbatar ko ita din ce sai tayi mamakin yadda ya san sunan ta dan ita ba sanin sa tayi ba sai dai kiran sunan nata da yayi ya nuna mata ya san ta din ne..
Tun kafin ta amsa mai Ammy ta juyo gabadaya tana mai son tabbatarwa kan ta da gaske mai sunan da aka kira din ce ba gizo kunnuwar ta ke mata ba,a yayin da ta juyo din a wannan lokacin Hajja ta juyo itama..
Fuskantar juna da suka yi ne ya tabbatar mata da wadannan sune mutanin da take hira da su a waya kuma take kirgawa a matsayin nata na jinin ta,tana iya cewa bayan soyayyar mahaifin ta da na yar'uwar ta da take da shi a zuciyar ta,toh tabbas soyayyar wadannan mutanin ne ya biyo baya dan bata taso da sanin su ba amma muryoyin su ya saka mata kaunar su a zuciyar ta..
Wani irin runguma Ammy ta ma Mufida wacce ke tsaye tana kallon yar uwar ta dake ganin wani sabuwar shafi da babin tsaka mai wuya dake shirin tunkarar ta a nan Nigeria din..
Hajja ce ta matso kusa da su Ammy cikin farinciki da nuna tsantsar jin dadin ganin jikar ta mafi kusanci da zuciyar ta kuma takwarar ta wacce tausayin ta ne ya rikide ya dawo so da kauna a zuciyar ta..
"Mufida tah matso in gan ki in rike ki in rungume ki ko zan sami natsuwar zuciya,tun safe nake zullumin zuwar ku hankali na bai kwanta ba sai da na ji jirgin ku ya iso a yanzu kuma nake kara samin sukuni da na gan ki da idanuwa na,ban yi tsammani ba amma Allah ya ara min tsawon rai rabo na da ke tun kina jinjirar ki sai yanzu"..
Ihu zata fasa ko barin wurin zata yi ta koma cikin jirgin ya maida ta germany,rasa abin yi tayi,yanzu har a nan din ma babu wanda zai nuna ya san da ita bare ya nuna mata damuwar sa a kan ta bare a kai ga ana ririta ta ana tambayar ta nata lafiyar da rayuwar,a yanzu din ma still fifi ce ba ita ba?..
Take wani irin mugun tsana da kiyayya ya taso mata wanda a kan yar uwar ta duk wadannan abubuwan suka ta'allaka,ita shikenan haka tata rayuwar zata cigaba da tafiya..
Bata ida tunanin zucin ba ta ji su suna fadin Mufida zo mu tafi mun san kin kwaso gajiya ga yunwa...
Tun da Hamida take bata taba sanin tana da wani mummunar fanni a zuciyar ta mai karfi da yake kamar ya rinjayi daya kyakyawar fannin zuciyar ta ba sai yanzu dan kasa rike hawayen ta tayi sai da suka fito kuma ta kasa goge su sai juyawa da tayi ta basu baya tana mai warware nadin mayafin da tayi a kan ta dan ya taimaka wurin boye halin da ta shiga...
Yanzu Tsakani da Allah duk cikin su babu wanda zai tuna da wata wai Hamida? duk hankalin su na a kan Mufida kamar ita kadai ce mutum daya cikin zuri'ar su...
Kasa natsuwa Khalid yayi dan ba karamin dauke mai hankali fifi tayi ba musamman ganin irin shigar ta da yadda ta rinka exchanging tambayoyin da ake mata hakan ya bashi tabbacin ita din kamar shi ne
wato mace ce mai son rayuwa da faram faram bata da dagon kai da daukaka kan ta fiye da wasu halittun...
Tun a nan airport din Khalid ya sallamarwa kan sa ya sami abokiyar tafiya dan da alama ba iya son life kadai take da shi ba wanda shima yake da shi ba,hatta wasu dabi'un ta yana ganin zai zo iri daya da nasa dan haka ya dada saukar da kan sa fiye da yadda ya saba yi a cikin family din su...
Baki daya sun juya da zumar shigewa mota dan su kai gida fifi ta huta,shaf sun manta da Hamida har aka gama kwashe kayan fifi aka saka cikin booth itama zata shige ciki amma ganin kamar babu mutum daya cikin su sai ta tsaya ta hau dube dube
A nan cikin motar kuwa Ammy ce ke kiran sunan fifi akan ta shigo su tafi amma hankalin ta na ga yar uwar ta da ta hango ta chan tsaye..
Karasawa tayi gare ta ta dafo kafadar ta cikin farin ciki game da yi mata magana cikin yanayin jin dadin da take ciki..
"Hamee kin ga yadda su Ammy da Hajja ke murnar ganin mu kuwa,zo mu tafi gida dan duk mu suke jira "murmushin yake Hamida tayi sakamakon gama sauraron zantukar yar uwantan na wai su Ammy da Hajja na murnar ganin su
bayan baro baro ita kadai suka nuna a matsayin nasu yayin da ita aka ware ta kamar ba tare suka zo duniyar da ita mafi soyuwar nasu ba...
Kamar ba zata juyo ba sai daga baya ta juyo da murmushin da ya fi kuka ciwo zuciyar ta kuwa shake yake da kiyayyar yar uwar nata da take ma kallon katanga ce ma farincikin ta dan bayan ta karbe zuciyar daddyn su da na Ammy da Hajja har wanda take ganin Allah ya kawo mata shi shima fifi ta dauko hanyar kwace mata shi
Shin wai ita laifin me tayi ne da babu masu son ta da damuwa da ita ne?
menene aibun ta da bata samin kulawar kowa sai yar uwar ta kadai ke samu,shin ita a haka zata yi ta rayuwa komai nata fifi na samin sa ba tare da ta nema ba?..
Hankalin ta kamar baya jikin ta haka ta rinka bin bayan fifi har suka zo wurin motar wanda sai a sannan Ammy ta tuno da Hamidar amadadin ta ji wani iri ko damuwa batayi ba sai ta ce..
"Wai dama Hamida baki shigo cikin motar bane kika tsaya a waje kamar ba jinin ki kika hadu da su ba?..wannan tambayar ta Ammy ta kara tabbatarwa Hamida shikenan wani bakin cikin zata kuma fadawa ciki bayan wanda ta baro a germany...
Gyada kai kawai Hamida ta iya yi ta shige cikin motar ta zauna a kujerar baya yayin da fifi ta shiga na gaba,da so samu ne daga Ammy har Hajja so suka yi fifi ce a nan inda Hamida take amma ganin kamar ita ce ke muradin zama nan kusa Khalid sai suka bar ta dan kar su saka ta yawar magana...
Wani abin bakin cikin da ya sa Hamida jin zaman motar ya gundire ta taji ta matsu su zo gidan ta kebe ko zata sami sanyin zuciya shine,ita ce a tare da su a bayan seat din motar amma kaf hankalin su na a kan fifin ne
kowa sai son nuna mata so da kauna yake yi ta hanyar tambayar ta akan karatun ta,akan raywarta akan lpyarta a nan kusa da fifi kuma Khalid ne yake ta sakar mata murmushi yana nuna mata kulawar sa shima ta hanyar tambayar ta "if she will be comfortable da zaman nigeria din...
A haka har suka iso babbar gidan dake dauke da different parts ginin duplex mai ban sha'awa saboda tsarin da aka yi ma gidan kadai abin a zo a gani ne,wannan gini ya sa fifi kasa boye kyawun da gidan ya mata ta fitar da shi ta hanyar furta
"Wow,nice house"nan take kuma aka maida hankali hade da ba maganar nata muhimmanci..
Sai nan nan ake ta yi da ita har suka shiga daga cikin gidan inda nan ma wata duniyar ce abin kallo,mai aiki aka kirawo akan ta zo ta kwaso kayan fifi dake booth dan a kai mata wata killatacciyar dakin da aka gyare sa musamman saboda ita nan kusa da na Ammy da site din hajja..
Ana shigo da kayan ne Hamida dake tsaya a matsayin batacciya tayi ta kallon su har suka gama shigewa da kayayyakin fifi ciki
Khalid ne ya fito dan gyara parking din motar sa sai a sannan ya ankara da Hamida...
Yace."Ohh no"da dan sauri ya karaso gare ta yana