Showing 78001 words to 81000 words out of 101986 words
gabda ita sannan tayi saurin sunkwi da kanta tana sakin murmushi me cike da ma'anoni dayawa ita kanta ta shaida Marshall hadaddan namiji ne ita kanta tasan tayi sa'an samun gwarzon namiji kamar Marshall tana kuma jin shauki sosai a kansa,
Hannun sa yakai kan face dinta yashafa hade dacewa
"You look so cute Mon amour I like ur dress" saida takara murmusawa akaro na biyu sannan tace, "I like urs to" sannan tayi saurin karasawa taja kujera tace, "Seat" baiyi mutsu ba yakarasa ya zauna saidai Duk abunda takeyi idanun shi yana kanta harta kammala serving dinshi ta ajiye mai komi a gaban shi sannan tasaka nata taja kujera ta zauna,
saida yakalli Breakfast din sannan yakalleta sai yasakar mata murmushin gefen baki sannan yace, "so you know how to cook Arabian meals?" saida takai cinnamon tea bakinta tadan kurba sannan tayi nodding kanta tace, "Arabian Meal yana daya daga cikin favorite dina I will cook Arabian meal for dinner if you like it" tayi maganar da dage mai gira saidai kanta a duke yake,
"yeah I like it bakisan ina son abincin larabawa ba" hira sukeyi har suka kammala cin abincin a tare suka wanke dishes din suka maida komi inda yake sannan ta goge kan dinning din, yana rike da hannunta suka fito daga kitchen din a three seater suka zauna sai tayi pillow da cinyar shi suka fara taba hira kadan kadan anan yake kara sanin halinta itama tuni tagama fahimtar halinsa sabida anan zaman da sukayi ta fahimci yanada dadin zama sosai kuma baida matsala,
A cikin yan kwanakin wani shakuwa ne me karfi yakara shiga tsakanin su dan tuni Fifi tazubar da Duk wani abu tafara nunawa mijinta tsantsar soyayya shima anashi bangaren hakane dan har mantawa sukeyi da akwai wa'insu mutane a duniya bayan su sabida zallan soyayyar dasuke nunawa junan su.
#Mamuh[8/12, 12:04 PM] Nadady: *31*
Turo kofar tayi a gajiye tana maida numfashi Bata jima ba ta nemi waje a gefen gadon ta xauna a kasale,fuskar matan ne yaki fice mata arai wani irin yanayi ta tsinci kanta a ciki Wanda batayi tsammani ba.
A Sashen su ammy saheeb ya jima by 8pm kusan kowa ya fito za'ayi dinner Allah Allah Fifi take ta samu damar ganawa da su ammy gashi har cikin ranta take matukar jin muradin ganin hamidarta.
Ayanzu ji take kamar Zuciyar ta yayi sanyi,wani sashi daga abubuwan da suke yawan damun ta game da tarayyar su da hamida ba laifi sun ragu mata,bathrum ta shiga tayi wanka kasalan data ke yawanji shi ya sa ta sanya doguwar Riga pure red material and masa design da wild rose hipup belt wanda ya Dan sake ta yau batayi wani kwaliya sosai ba
Babban sashen gidan ta nufa inda Tasamu duk an zazzauna a dinning wani sanyi ne ya mamaye Zuciyar ta ayayin da take kallon su kusan kowa fuskan sa dauke da murmushi musamman hamida da Khalid Wanda Babu wani Abu daya rage ayanayin su na nuna tsananin so da shakuwa dake wanzuwaa a zukatansu.
Purple atampa ta sa Mai kyau Wanda ya dau kalar fatan kusaan kala daya da tsadadiyyar yadin vice chair man Wanda ya amshe jikin Khalid ya masa kyau sosai Shima.
Agefe da shi ammy ne da hajja wani
murmushi me sanyi ne ya kufce mata ji tayi kamar taje ta rungume su Dan bakaramin zazzafan kewarsu takeji aranta ba,a hankli ta maida kallon ta kan saheeb Wanda kallo daya ya isa yasa kasan bai Saba zaman cikin su hakanan ba dago kanta ke da wuya caraf Suka hade idanu da muhibba agefen sa irin kallon datayi mata yasa tayi saurin dauke kai gyaran murya tayi sannan ta karaso ciki a yanayin fara'a da basarwa.
" Salam alaikum"
Tace da muryan ta na da can Wanda shi kowa ya fi Sanin ta dashi, hamida ce ta soma juyo ta kalle ta cikin dakakkiyar murmushin da ya kufce mata baxata
Ammy ce ta soma mikewa sannan Hajja tabi bayan ta wani rungumar ta sukayi atare ayayin da suke gaisawa
Fifi Fifi tuni waje ya kaure da sabuwar surrutayya.
Saheeb ne kawai baice uffan ba"fifi kuwa har ta xauna Bata wani samu cikakkiyar nutsuwa aranta ba Dan rasa gane inda zata ajiye tunanin tatayi,wani bangare yanaga hamida wani Yana ga mijin ta saheeb da matar sa dataa Sha uban kwalliya tana serving kowa a nutse wacce Babu alaman kasawa ko yaranta a fuskan ta.
Normally wajen ya dau shiru kowa ya nitsu ya maida hanklinsa akan dishes dinsa ana hira sama sama,Banda hamida data fiye bada hanklin ta a kan Khalid kadai Dan in ba shi yayi magana ba Sam Bata cewa komai.
Ganin Fifi Ras fiye da yanayin yadda suka bar gidan yasa su ammy shagala,waccan yanayin zazzafan so da nuna tsananin kaunar da kulawa da suka Saba mata shiya ke fallasa kansa a duk sanda sukayi magana awajen
Babu tantama tun zamar su anan hajja take ta mata tambayoyi da wasan gata irin na tsoffi sakalci da kauna duk da ma Fifi tana basarwa Amma hamida ko ajikin ta,gani take inda sabo to ta Saba muhibba ce Abun ya mata banbarakwai sabida ji kawai tayi Abakin hamidar Amma Bata tabbatar ba Sai yau dataga cewa kusan hanklin kowa akan dinning din akan Fifi yake
Hirarrkin ma It's all about her, duk abubuwan da fifin tayi sabo sanda basa Nan seda sukaso suji duk dama ita fifin tana hankalce da furucin ta na rashin son bayyana wani Abu daxai sake kawo wani tsabanin fahimta tsakanin ta da yar uwantan.
hakan yasa taki Jan magana kwata kwata baifi Tace eh aa ba ko ma tayi dariya ba.
Duk da hakan ba shi ya Hana hamida Sanin cewa fahimtar juna ya samo mafaka tsakanin su da saheeb ba Allah Allah take Subar wajen ta samu ganawa da muhibba Dan tun xuwarta gidan suke kulla maganan a tsakanin su batare da kowa yasani ba
Tun ranar da su ammy suka sanar da muhibba cewa tana da kishiya Hamida ta gane cewa muhibbar mace ce me tsananin kishi musamman reaction din ta nuna lokacin da akace mata tare sukaje hutu
Kwanan muhibba biyu agidan Amma Babu Wanda ya gane kanta face hamida da tasanya mata idanu tana karantar abubuwan dake wanzuwaa a zuciarta na fushi da tsananin kishi hade da boyayyen damuwa.
A da can ko gaishe da su ammy Bata son fitowa tayi,tanan ne hamidaa ta shige ta da sigar nuna cewa tana tausaya mata duk dama muhibbar Bata amshe ta lokacin guda ba Sanin cewa ita taawainiyar kishiyaartan ne
Amma daga bisani hamidar ce ta wayar Mata da kai,ta cusa mata wani rufaffiyar ra'ayi me shiga har Zuciya a dunkule...
Duba da cewa Auren rufin asiri akayi ma Fifi da saheeb yasa su ammy basu bude ma muhibba komai da komai ba Sabanin nuna mata da akayi cewa Auren dangi kawai aka musu wanda aka barshi a matsayin Qaddara ne ya hada.
Hamida kuwa fede Mata biri tayi har wutsiya tayi cikin salon yaudara sanda ta cimma wani boyayyen manufarta.
Ta fara ne da nuna Ma muhibba yadda kowa
Da komai yake komawa na Fifi,ta hanyar Bata labarin yadda kowa agidan yake daukakata ake Fifita ta ake son ta fiye da komai.
Tace dama wannan ciwon shine makamin ta wajen kwace komai na jin dadi a ryuwar wani nikaina danake yar uwanta Saida 'ta kwace min nawa rayuwar,na wajen iyayen mu kakanin mu kawayen mu ke har mijina ma Saida taso ta juya masa kwakwalwa,arayuwa Fifi tafison kowa da komai ya zame nata ne ita daya
..koda akayi Auren ai mijinki bai kwatanta cin amananki ba Ina lura ya kama kansa duk dama yasan lankaya masa ita akayi,amma yarinyar Nan waini take so tayi amfani Dani Dan cimma manufarta akan saheeb sabida na nuna musu cewa na gano mugun halayyarta na son Kanta da son Zuciyarta,inkina so kiga munafukar mace inkika hadu da Fifi kinsamu kankat.. duk yadda naso ace su ammy sun gane menake nufi Amma sun ki, gani suke kamar karya nakeyi bansan meye asali a Zuciyar Fifi ba,ba gashi Nan a bayyane ba?kawai tasan nafi Karfin ne shiyasa take nuna kamar tayi nadama but ni nasan da ciwon Nan nata take harin gamawa da mijin ki Shima.
Ko ke baki gane bane? in har dagaske akaina take cikin wancan damuwar da Zama zatayi Dani Dan In Yafeta bawai tace mijin ki xata bi wani waje ba,to wayasan Me taje ta aikata Masa ko wani irin karya ta shimfida Masa Dan ta shiga rayuwar sa ta janye ra'ayin sa makanta ita daya.
Kedai kiyi hankli da ita ni kadai nasan halayyar fifi daga ta cimma burin ta akan saheeb to babu me sake kallon ki ko jinki,sannan a gidan nan for 23yrs ana nunamin cewa fifi bata lefi bata kuskure kuma duk abunda take so nata ne, ina guje miki shiga kunci da damuwa irin nawa,compare to me aike tamkar bare ce in har anmin to kowa ma za a masa,dan haka bana cire tsammnin cewa duk wata mace me tsananin kishin mijin ta kamar ki zata iya rayuwa a tarkon fifi.
"Nice tawainiyatta kuma nice nafi kowa sanin komai akanta ln kina son kanki da lpy sai ki bani hadin kai wajen kwaco yancin mu da farincikin mu,nikam na kwace miji na a tarkon ta saura ke,in bazakiyi wani abu ba wannn ya rage miki.
.
Wayannan munanan maganganun Muhibba take juyawa aranta ayayin da dukanin hanklin ta gaba daya ya koma ga kan su fifi da ammy da shikansa saheeb daya tsoma baki a hirar su ta yanxun dake hirar ya shafi lapiyar fifin ne
Banda boyayyen kallon kallon da sukeyi a sace Wani shiru muhibba tayi tana kan fahimtar gaskiyar maganganun hamida data sha gaya mata akan fifi, ta dade cikin wannan yanayi
can tayi boyayyar ajiyar xuciya ta tabe baki a hankali bata ce uffan ba.
Fannin fifi kuwa tun Daga yanayin bayanan saheeb da tambayoyin da ake mata tana amSawa Khaleed ne ya soma fahimtar cewa ciki ne ya shige fifi.
Bayan sun koma sitting room duka akan za'ayi musu nasiha Cikin salo sanda khaleed yasa kowa ya fahimci hakan su ammy da hajja ina Kasaka da murna,alkwarin so da kulawa babu wanda basu bayyyana shi ba fifin dai batace uffan ba ayayin da saheeb ya sulale ya bar wajen dan dama shikam ya gane abun tun jiyan datake ta laulayi.
Yana barin wajen muhibba tabi bayansa
Ita kuwa fifi a Duk murnan da akeyi hanklin ta nakan yar uwanta ne,sakamakon wani bangaren zuciyatta yana alfahari da cikin wani kuma yana kinsa da jimamin kada yar uwan ta ta sake alakanta hakan da samun fifikon da zai sake haddasa wani kiyayya da damuwa aran yar uwan tan.
Tana cikin wannan tunanin hamidar ta mike bayabo ba fallasa tayi musu sallama,a gurguje fifin ta mike tabi bayanta tanata kirar sunan ta gasunan daf da daf amma hamida ta sakai bata juyo ba bare ta amsa hakama ta rufe kofarta agaban idanun ta batare da ta ce mata uffan ba.
A sanyaye fifi take kallon kofar wani karayar xuciya da gabobin jiki su suka lullube ta sai tayi shiru bata dawo hayyacin ta ba sanda taji gyaran muryan khaleed ta bayan ta
Yace yadai Mufida baki shigaa ciki bane?
Matsawa baya kadan tayi cikin boye damuwarta tace
"ah'a yanxu na fito..im just abt to leave.
Ajiyan zuciya ya sauke
yace "ohh to shikenan..
kwayar idanun su suka hada atare tayi saurin kawar da nata gefe kureta da idanun sa yayi yanata kallon ta bakinshi da zuciyar sa cike da ababen cewa
"gudnite.. ta furta slowly batare da ta jira amsar sa ba ta bar wajen da sauri bayan ta yabi da kallo yana me lumshe ido can ya sauke ajiyan xuciya ya shiga room din su.
Kwance ya tarar da hamidar idanun ta a lumshe tayi shiru dan haka ya shirya da sauri shima ya biyota kan gadon.
Wani wawan runguma da zafafan smooches ya bata wanda yasa tuni suka dulmuye juna cikin shaukin so da raya daren su cikin kyakwar shakuwa
Can Bayan sun kimtsa ne yake tambayarta ko dagaske sun gana da fifin,eh kawai tace masa batare da nuna masa komai ba.
Yasan matsayin fifi a zuciyar hamida dan haka yaso yaji ko maganan cikin ma ya dame ta amma haka fir taki ta bayyana masa komai.
Fifi kuwa tana barin wajen su ammy suka rike ta da sabuwar hira da tarairaya dan samu tayi har hajja ta kira daddyn su tana kai masa gulman
Sosai tayi farinciki dan acewarta murnan ta kashi biu ne,musamman in ta tuno da yadda akayi auren,da tunanin cewa yau ko fifi ta mutu abunda ke cikinta zai zame musu sassaucin jin zafin rashinta a duniya da zasu zo suyi
itama fifi karban wayar tayi tafi awa suna hira me dadi da shi su hajjan na tayasu musamman da kowa ya san cewa by now saheeb yana tare da muhibba ne so Anan site dinsu ta kwana.
****
Bangaren saheeb
Suna shiga dakin muhibba ta hade rai ta kau da fuska tayi zaman ta a bakin gado batare da tace masa uffan ba,kallon ta yakeyi direct dan gaba daya alamomin fushi da zafin kishi sun bayyana a fuskan ta amma dake halayyar sane kamewa da shan qamshi sai yaki yace mata uffan
shima,wani zaman kurame akayi a dakin shiru ne ya ratsa tsakanin su ko minti biyar basuyi cikin hakan ba ta mike fuuu ta wuce bathrum tana me buga kofar da dan karfi kayan jikinta ta sauya zuwa towel ayayin da kuka me tsuma da cin rai ya kufce mata kan gwiwarta ta sauka tana zubda hawayenta sosai tana kuka tafi awa guda a hakan
saheeb dake zaman jiran fitowar tan Tun baijin sautin kukan har ya tsinkayo Da kamar bazai je ba can dai ya daure ya kai kansa bakin door din bayabo babu fallasa ya kira sunan ta amma ko sau daya bata kulasa ba
Sunfi mintuna talatin ahakan har abun ya dame sa sosai dan dolen sa ya Soma halayyar maza na rarrashi wanda sam bai saba ba.
Wai meke damunki haka ne?
"Can u please come out lets talk?
Wai miye hakane muhibba,i hate wen u act childish...open the door
Tanajinsa tayi shiru abun ta Da can kamar zata amsa sai kuma ta tuno da cewa ranta a matukar bace yake a yanzu,tana bukatar nitsuwa da samun kyakkyawar ganawa da hamida kafin ta san matakin da zata dauka me gaba daya.
Jin har yanxu bata kula sa ba yasa ya harxuka tsaki yaja ya bar mata dakin ya nufi nasa yayi kwanciyar sa se can ta fito ta kimtsa ta hau gadon ta ta kwanta abunta
Juyi take acikin ranta cikin tunani me xurfi babu wani abunda take s akawa face yadda zata bullo masa da Shi da matar sa ta hanyar da zata fi iya cimma burin ta cikin sauki.
#Mamuh
[8/12, 12:08 PM] Nadady: *32*
Washe gari da safe koda ya dawo duba muhibba ya samu kofarta a kulle Tsaki yayi Bai sake dawowa Nan ba direct ya nufi sashen su ammy ya gaida su tare da duba lapyar Fifi wacce take Nan lafiya lau Dan bakaramin kulawa da ita yau akayi ba tsaban zumudi har sun shirya lokacin da zasu je asibitin Dan Khalid yace zai duba ta acan.
Suna ta shirmen su Dan haka Bai wani jima anan ba ya fice da sojojin sa daganan basu sake jin duriyar sa ba itama fifin anan tayi zaman ta saidai duk Abunda ake Mata na nuna tsaninin kula da gata Bai wani dame ta ba Ayanzu ba.
By 4pm suka dawo daga asibitin bayan Dan karamin yawon bude Ido da sukaje dukan su su ukun ita da ammy da hajja, khaleed yana asibitin sa ita Kuma hamida tana gida tare da muhibba Babu Abunda sukeyi yau Sai kulle kullen su na Sanin Abunda zasuyi akan fifi
Kuma duk tarayyar sun Nan Babu Wanda ya sani sabida hamida takan nuna ma kowa cewa ita Sam Babu ruwan ta da rayuwar kowa face na mijinta ta khalid Dan haka wani bin ma ko cikanki Bata cewa muhibba a fili.
Itaman muhibbar dake ba sarar su bane ko a shekaru Sai rashin kula junan sun Bai Ba kowa mamaki ba Amma a zahiri kusan hamida ce me asalin dorata akan gayyar kishi dake tsokalarta a xuciyarta
Tsaf suka kammala hade haden su ayayin da kowacce ta koma site dinta tana abubuwan daya dame ta.
fannin fifi kuwa a fili ne kawai take yawan murmusawa Amma aranta wani uban kadaici takeji me nauyi She really feel alone,har cikin zuciyarta take jin kewar rayuwarta na da can Wanda Babu fargaba ko kiyayya rayuwar da Bai nisantar da ita da soyayyar yar uwanta ba
Bayan ta idar da ishai Wanka tayi a site din hajja ta sauya shiga xuwa simple white Milano gown marar nauyi ta sakaya hular sakanta shima white wani boyayyr damuwa rashin jin saheeb tun safe shiyake cike mata kirji Yana damun ta har kwakwalwa tanajin zafin Abun Yana shiganta a hankali
Numbar San ta dada dialing daga bisani ta jefar da wayar tabi lapiyar gado tana me lumshe idanun ta sosai Jin kamar baxata iya dauriyar ba ta bude Tex messg ta soma rubuta mashi Sako'
Hy can u please come home Ina son ganin ka,Sai ta goge ta rubuta Salam,kana lafiya pls wen r u coming back? ta rubuta messages yafi sau goma tana gogewa
gaba daya sai ta rasa me xata ce Wani baccin baxata ne yayi awon gaba da ita da wayar a hannun ta hajja ce ta rabata da wayar Bayan ta Gama karance sakon ta na karshen da ta rubutu Bata goge ba murmushi tayi sannan ta gyara mata kwanciyarta.
Wajajen karfe 10 saura saheeb ya dawo sashen sa ya nufa straight ya kimtsa kansa cikin kananan kaya sannan ya taho ya same hajjan dake yau ita daya ya samu tana zaune ta toshe da medicated glass da qur'ani a hannun ta tana dubawa.
A ladabce ya rusuna ya gaida ta ta amsa Masa cikin faraa,duk daama tasan baxai wuce aiki ne ya Sha kansa ba Amma sanda tamai tambayar hakan..
Ce mata yayi muhimmin meeting ne ya ritsashi yau da ogogin sa ko lokacin kansa Bai samu ba
Tace Allah ya bada sa'a yace amen zai mike yay waje ta sanar da shi cewa Fifin tana Neman ganin sa Amma tana bacci ayanzu