Showing 24001 words to 27000 words out of 101986 words
y zame mana alheri
wuf Mufida ta miƙe tsaye tana kallon Ammy baki buɗe...
Ammy duk ta gama azawa ki wani abu ne
Dariya ne ya cunkushe a zuciyar fifi sai dai bata son yin sa a gaban Ammy kar Ammy ta ji wani iri,haka ta rinƙa tarar dariyar dan kar ya fito,a ƙarshe dai ɗagawa Ammy hannu tayi alamar zata je ta dawo...
Bin ta da kallo Ammy tayi tana mamakin reaction ɗin fifi dan ta ɗauka zata ga tayi negative reaction ne sai ta ga akasin haka...
Mufida na fita daga ɗakin Ammy bata tsaya ko ina ba sai ɗakin Hamida wacce ke kwance ƙasa tana baccin wahala..
Da zuwar ta bata tsaya tunanin bacci ƴar uwar nata ke yi ba kawai ta hau tapping nata a baya tana kiran sunan ta..
"Hamee...,Hamee na ki tashi...common wake up i have a gist for u,dan Allah ki tashi".jijjiga ta fifi ta rinƙa yi tana assasa mata akan lallai lallai sai ta farka daga baccin dan kawai ta labarta mata abin da Ammy ta sanar da ita..
Daga cikin baccin da bai jima da ɗaukar ta ba Hamida ta ji muryar fifi sai ta buɗe idanun ta a hankali ta zuba su a kan fuskar fifi dake ta dariya kamar wacce ta ga abin dariyar..
Fifi na ganin ta farka sai ta riƙo hannun ta tana mai cigaba da yin dariya tana magana..
"Hamee wai kin san wani babban albishir da su Ammy zasu maki kuwa?tayi maganar tana kuma ƙara ƙarfin dariyar ta...
Bin ta da kallo Hamida tayi dan in dai wannan ne special package ɗin,toh ta san da zaman shi...
Tace "Hamee me?na yi tunanin zaki matsu dan son sanin wannan zancen?girgiza mata kai Hamida tayi tana kawar da fuskar ta gefe..
Kai tsaye fifi ta hau bata labarin komai sannan ta ɗora da sunan wanda za a haɗa su auren..
"Hamee wallahi na fi dacen miji kin san fah wai har mata gare sa kuma ta ƙi yarda ta haihu over years,though Ammy bata sanar da ni gabaɗaya labarin sa ba amma daga wannan ɗin ma na gane cewa Ammy ta matsu ta sami grandchildren you see in aka haɗa ni da yaya.....Khalid ke kuma aka haɗa ki da...."!!!wani dariyar ne ya tasowa fifi ta rinƙa yin sa har Hamida ta ji kamar ta ɗauke ta da marin da ubangijin ta kaɗai ya san halin da zuciyar ta ke ciki game da wannan lamarin,ba fah ita aka roƙa aka nemi yardar ta da izinin ta ba kai tsaye aka nuna mata iko,amma ita fifi da yake ƴar so ce ƴar gida ce bayan Hajja ta yanke hukunci har sake tuntuɓar ta Ammy tayi dan jin ra'ayin ta wai kar a mata dole..
these people are unbelievable ta furta aranta .ta ja tsaki,ba ma su suke sanar da ita ba? Mufida ce yar aikan su akan maganar dan kawai bata da daraja da ƙima...
Duk wannan dariyar d fifi take bai dame ta ba dan dana ta ji shirun sua ɗazu,so wannan ba abu ne da zai ɗaga mata hankali ba duba da irin rayuwar da ta taso a ciki na kaɗaici da rashin samun kulawar kowa a kan ta..
Murmushi mai ciwo Hamida ta yi tana kallon Mufida dake ta ƙunshe dariyar ta,sai ta girgiza kai kawai dan wani lokaci in ta gwada nauyin ƙiyayyar da take yiwa Mufidar sai ta ga ya rinjayi ƙaunar da take mata hakan ya sa take ta ƙoƙarin ganin shaiɗan bai kai ta ƙarshe ba ta yadda in ta tashi barakar ta abin ba zai yi muni ba
sai dai daga dukkan alamu yazama dole ne tayi introducing Mufida zuwa ga other side na halayen ta dan ta san ba komai mutum ke yi ya tafi haka nan kawai ba...
Tae wai za a aura min
"Yaya Muhammad Saheeb ko"?sai fifi ta gwalalo idanun ta waje tana tunanin a ina Hamida ta san wannan labarin..
"Kina mamaki ne dan na san da shi ɗin dama za a haɗa ni, kuma kin san me fifi?hakan bai dame ni ba a hakan ma,ina son shi"!!
baki buɗe fifi ta rinƙa kallon Hamida jin cewa wai tana son shi a hakan ita da baya cikin jerin tsarin mazajen da take burin aura sai kuma yanzu wai har ita ce mai cewa ya mata a hakan..
Lallai Hamida ta sauya amma meyasa Kika ce kina son shi a hakan Hameeda"?
Gyaɗa mata kai Hamida tayi tana kallon ƙwayar idanun ta dan duk inda jarumta yake Hamida ta nemo sa ta ara ta yafawa kan ta bata so fifi ta ga gazawar ta har tayi taking advantage ɗin gazawar nata ayau dan ji take kamar hakrin ta ya riga ya kare..
Tashi fifi tayi tana yar dariyar rashin fahimta tana girgizawa Hamida kai cikin tsokana tana faɗin.
"Ni Mufida,yanzu Hamida duk irin burin nan da kika ɗaura akan samin namiji ƙerarre mai muscle duk sun tafi abanza kenan?tsohon nan mai mata zaki aura kuma wai kina son sa a hakan?unbelievable"!!
sai dariya dama on normal basis ya aka iya da dariyar tsokanar fifi bare yanzu da ta sami dalili...
Tsanar ta ne kawai ke ruruwa a zuciyar Hamida,ji take kamar ta kawo ƙarshen wannan masifar yau yau ta hanyar shakure ta,Mufida kowa Mufida kowa Mufida,daurewa tayi ta danne ɓacin ran ta ta cigaba da ɗora murmushin yake har Mufida ta gama tsokanar ta da zata yi ta ɗora da yabon nata husband to be ɗin wato Khalid...
Ƙala Hamida bata ce da fifi ba har ta gama ta dawo ta rungume ta tana masu fatar alkhairi su duka sannan ta tafi dan ta matsu ta san ko ta sami ƙarbuwa a zuciyar Khalid ɗin..
Bayan fitar ta ne Hamida ta kira Dr Fatima Yonas cikin kuka tayi narrating mata abin da ake ciki,babu abin da ya wuce shawarwari da sauƙaƙa zuciya da Dr Fatima Yonas ta ba Hamida ƙarshe ta mata fatan alhari da alƙawarin inshaAllah ko da bata sami damar halartar bikin ba Ameed zai zo..
Zama Hamida tayi tana ta saƙe saƙen ta ita kaɗai da zuciyar ta,hawayen dai na kan zubowa amma zuciyar ta bai karaya ba tana nan tana jiran ji ko za a same ta a sanar da ita wannan shawarar ta musamman ko kuma daga wanda fifi ta sanar da ita shikenan...
****
Bayan an kammala dinner har an bar wurin cin abincin sai Hajja ta kira attention ɗin Mufida ta aike ta da ta kirawo Hamida dan tana da magana ta muhimmin ga dukkan su...
Tashi fifi tayi ta nufi ɗakin Hamida ta sanar da ita saƙon Hajja,biyo ta tayi suka dawo tare
A gaban Hajja duk suka zauna Mufida ta fi kasancewa kusa da ita,nasiha sosai Hajja ta masu sannan ta ɗora da sanarwar da ta sa aka yi a cikin family game da batun auren,kuma jadadda masu tayi akan a tsarin su kwata kwata ba su son bikin ya wuce wata guda,dalilin barin sa ya kai har wata gudan kuma shine dan su ƙara fahimtar junan su ne da abokan da zasu yi rayuwa da su..
Duk kan su a ƙasa Hamida dai ta san ba dan ita aka yi wannan tsarin ba sai dan fifi dan ita kam an gama cutar ta mijin da ake shirin haɗa ta da shi batun wai su fahimci juna kuma duk wannan bai taso ba dan shi kan sa ba a ƙasar yake ba bai da lokacin kan sa bare nata toh ta yaya zata wani fahimce sa,again her life is about to get ruined so bata jin daɗin komai a duniyar ma...
"Hamida ina ra'ayin ki akan wannan tsarin da muka maku ke da ƴar uwar ki"ta ji muryar Hajja a kan ta sai ta kalli Hajjan da murmushin dole ta ce
"Komai kuka tsara yayi Hajja"daga haka ta tashi ta bar wurin duk da ta haɗu da Ammy a hanyar ta na komawa ɗakin ta hakan bai sa ta tsaya ta ma Ammyn magana ba...
"Kin ga irin halin ƴar uwar taki da ya sa muka ga sun dace da Saheeb kenan,kullum mutum na zaman kaɗaici"?..murmushi fifi tayi tana tunano irin kallon da Khalid ke aiko mata ɗazu da suke cin abinci...
Kwanciya kawai tayi jikin Hajja tana ta murmushi wanda ita ta san me ke saka ta murmushin...
****
Kwanaki na ja fahimtar juna na ƙara ninkuwa a tsakanin fifi da Khalid haka mizanin ƙiyayyar fifi a zuciyar Hamida babu abin da ya ragu sai ƙaruwa sabida son kan da aka dade ana nuna mata yau ya fito mata karara duk wani shiri na musamman da ake yiwa fifi ita bata sami wannan rahamar ba,haka duk hankalin su ya koma kan fifi ba Hajja ba ba Ammyn ba,wannan ya janyowa Mufida baƙar tsana a zuciyar Hamida wanda da wuya wannan tsana da ƙiyayyar ta gogu a zuciyar Hamida..
A zahirance Hamida na nuna amincewar ta da auren amma a baɗini kuwa ubangiji shikadai yasan me ta kulla zata aiwatar ta dai ɗauke kan ta daga dukkan abin da zai ɗaga mata hankali har ɗaurin auren da ta san ita kaɗai zata yi zaman aure babu wani miji sabida da shi da babu abu daya ne wurin ta...sede hakan bazata taba bari ya afku ba
#Mamuh*_Mamuhgee_*
*12*
Rai bace cikin ɗan ɗagin murya da ala dai ba cikin dadin rai take maganganun ba dan har kasa zama wuri ɗaya tayi,ta juya nan ta juya can kafin daga bisani ta yi wata magana cikin tsawa mai nuni da oder take bayarwa..
"Nan da kwanaki goma sha biyu nake son ganin ka a ƙasar nan,ni na haife ka ba Muhibbah ba dan haka a matsayi na na mahaifiya a gare ka tun kafin rai na ya sosu da kai Saheeb,ka dawo gida ka halarci ɗaurin auren ka dan ita kan ta yarinyar dole aka mata ba dan zuciyar ta na so ba sai dan ita ɗin mai biyayya ce,for the very last time kar ka yarda in kuma yin magana da kai akan wannan issue ɗin am i clear"?shiru ne ya ratsa tamfatsetsen ɗakin nata kafin daga bisani tayi magana...
"Sai ka zo Allah ya kare min kai ya dawo mana da kai lafiya take care"!!tana kaiwa nan ta sauke ajiyar zuciya haɗe da sauke wayar daga kunnen ta..
Juyowa tayi ta kalli Hajja dake ta sauraron ta tun farawar wayar naya har yanzu da ta dire wayar daga kunnen ta..
"Wai zai zo ɗin"?Hajja ta tambaya da sanyin gwiwa sai Ammy ta ce
"Eh Hajja,zai zo idan bikin ya rage saura kwana biyu inshaAllah".gyaɗa kai Hajja tayi tana magana
"Allah ya kawo mana shi lafiya".da amin Ammy ta amsa daga haka suka cigaba da tsare tsaren bikin dama ba wata bidi'a za a yi sosai ba abin da fifi ta zaɓa are just three,na fari bridal shower na biyu family get together ne sai walimah,kuma in aka yi la'akari kusan duk taron cikin gida ne..
Tsarin ta sak tsarin turawar da ta taso a ƙasar su bata son yawan hayaniya in ba ita ta so ba toh kuma sun gama tsarin su akan duk yadda za a yi bayan bikin ita da angon ta zasu gudu zuwa honeymoon a can zasu yi abin da ran su ke so..
"Yanzu ki aika a kirawo ita Hamidar dan a mata ɗan taƙacciyar bayani akan rayuwar mijin nata dan ina ga takwara ta har yanzu kamar bata sanar da ita ba kamar dai yadda kema baki ƙarasa mata bayanin ba,kin ga ai haƙƙin ta ne ta san da wanda zata yi rayuwar zaman aure da shi dan in takwara ta ce na san bani da ɗar akan hakan sun saba da junan su"!!.gyaɗa kai Ammy tayi tana sauke ajiyar zuciya..
Wayar ta ta ɗaga ta kira layin Hamida,bugu uku Hamida ta ɗaga sai bata tsaya jiran komai ba ta ce da ita ta same ta a ɗakin ta.
Sauke wayar tayi daga kunnen ta tana yi wa Hajja bayanin ai tana zuwa..
Kafin ta zo ɗin ne suka cigaba d tattauna lamarim bikin dan sun saka an yi iv na soft copy an yaɗa ma ƴan uwa da abokan arziƙi sbd a zamanin yanzu wannan ɗin shine dai ya fi saurin kaiwa wurare fiye da hard copy..
Suna cikin hirar sallamar Hamida ya ankarar da su,shigowa ɗakin tayi bayan an mata iso ta nemi wuri ɗan nesa da Ammy ta zauna sai Hajja ta ƙure ta da kallo ganin kamar tayi rama fiye da da da suka zo,bata kawo komai a ran ta ba illa rashin sakin jikin Hamidar da take kallon ta da shi but ta san in har aka yi auren nan toh komai zai zo ƙarshe ko ba komai miskilanci da ɗauke kan ta zai sauka..
Gaida su tayi tana yin ƙasa da kai haɗe da cewa ammy
"Ga ni Ammy"..sai da ta gama kallon ta ta ga kamar ita bata gyaran jikin sai ta tambaye ta surprisingly..
"Hamida ina gyaran jikin da na sa ana maku ke da Mufida"?wani irin abu ne ya tasowa Hamida ya tsaya mata a ƙirji sai take tambayar kan ta a zuciyar ta..
"Wai mutanin nan...,are they for real?ni Ammy ke tambaya ina gyaran jikin da ta sa a mana?wai ma tukun yaushe aka yi hakan?ina fifi ce kaɗsi centre of concern ɗin su?ita kaɗai ake yiwa gyaran ita kuma da yake bare ce a gare su bata cancanci wannan kulawar ba,"girgiza kai kawai tayi ta ce da Ammy..
"Ammy fifi kaɗai ake ta yiwa ni ban ma sani ba sai jiya da na gan ta a wun cin abinci"!!kallon mamaki Ammy ta bi ta da shi tana jimamin hali irin na Hamida mutum so quite and ignorant haka,..
"Amma ai kin san dole tunda baku haɗuwa akwai abin da ake mata kuma ya kamat a matsayin ki na babba ke ce kika cancanci fara zuwa duba lafiyar ta,toh in wata matsalar ce ke damin ta shikenan kin ɗauke kan ki bski damu da ita ba"?kallon fuskar Ammy Hamida tayi tana mamakin son kai irin na Ammy..
Yanzu ita da fifi har wani fidda babba za a tsaya yi alhalin duk tare suka faɗo duniyar sai bambancin mintuna biyar da ke tsakanin su amma Ammy kawai tsabar bata son a ga laifin ɗiyar so fifi sai ta juya ignorance ɗin su akan ta akan duk dai laifin ita ce ba su ba ba Mufidar ba..
Ƙala bata ce da su ba har Ammy ta gama yin faɗar ta Hajja ta ɗora da nata sannan suka hau yi mata bayanin abin da ya sa aka kirawo ta wanda Hajja ce ta jagoranci bayanin..
"Ba komai ne ummul aba'isin ɗin kiran ki nan ba Hamida sama da yi mski bayani na musamman akan wannan mijin naki da zaki aura,kin ga dai yabawa da hankalin ki da tunanin ki da muka yi shi yasa muka ma ɗan uwan ki kwaɗaiyin auren ki,baki san shi ba bai san ki ba amma haɗin ku zai zamo alkhairi ga kowa,shi dai ba mai son magana bane kuma bai da matsala bare damuwa,kasancewar sa mai ɗauke kai ga abubuwa ya sa auren sa na fari da matar sa Muhibbah ya zamo kamar cutarwa,kwata kwata bata da lokacin sa bata zama yana south africa tana Los Angeles mafi yawan lokutan su sukan yi sa ne ta waya,basu cika haɗuwa ba sai shekara shekara,kusan shekarun su goma da aure kenan amma tun bayan shekarar su ta farko da suka yi sa cikin zaman lafiya basu ƙara samin zaman lafiya ba,dan ni abin da zan iya kiran zaman nasu da shi kenan,ta yi gaban kan ta ta tafi wata dunuyar tana kula da businesses ɗin late mahaifin sa"..kaiwa nan Hajja ta ja ta tsaya..
Kan Hamida na ƙasa zuciyar ta na mata zafi da raɗaɗi dan wata sabuwar ƙiyayya ce ke samin gurbi da mazauni a zuciyar ta game da auren nan da ita kan ta ƴar uwar nata,tsabar son kai wai har shekarar su goma da aure ita wancan matar nasa bata da lokacin sa tana business ɗin ta sai ita ce mai zaman gida marar aikin yin da zata na kula da tsoho kamar shi,ai ko da bata san shi ba a ido ta san in ba a yi wasa ba ya haife ta because a shekarun da Hajja ta kirawo mata akan shekarun sa da aure ita a lokacin ina take?sannan kwata kwata tana ten years as at then toh shi ɗin a shekaru nawa yayi auren?..
Muryar Hajja ta ji a kunnen ta tana ƙarasa mata labarin.
"Shi ɗin Brigade ne na sojoji,kuma dalilin da ya sa ya bar mahaifar sa zuwa ƙasar south africa shine,akwai wata shekarar da ta gabata kusan shekaru ashirin da suka wuce an sami wata tarzomar da ta tayar da ƙura a tsakankanin ƙasar nan Nigeria da Cotonou,duk sojojin da ake kaiwa wannan boarder ɗin sai dai su yi iya yin su ba tare da sun yi nasara ba,wasu su dawo da rai wasu a dawo da gawarwakin su wasu kuma ba ma za a gan su ba,toh a wannan shekarar ne aka umarci head division ɗin wannan yankin da ya saka hannu wun bada gudunmawar sa kuma a haɗa da na ƙasar chad dan ganin ko za a sami nasara dan in har aka bar tarzomar ta cigaba toh zata iso nan ƙasar gabaɗaya ta addabi ƙasar,a lokacin yayan ku Saheeb bai jima da fara aikin sa ba sai wannan buƙata ta taso,da zuciya ɗaya ya amshi umarnin da aka basa daga sama ya nemi addu'ar mu suka nufi wannan yankin Cotonou ɗin wanda suka shafe kusan watanni shida suna jeji sai a na bakwan ne suka fito da babbar nasara mafi yawan yabo ya sauka akan yayan ku Saheeb,wannan jarumta nasa ya sa ya ɗaukaka har ya sami cigaba sosai fiye