Showing 75001 words to 78000 words out of 101986 words

Chapter 26 - KAUNAR MU COMPLETE HAUSA NOVEL

MAMUGEE   

27 Sep 2024

15649

ya kalle ta sannan yayi wani murmushin dole kafin ya amsa ta..
"Can u cook"?sai ya kalle ta na wasu seconds sannan ya amsa mata da
"Uhmm"bata gamsu ba sai ta kuma tmbyr sa
"I don't understand uhmm"!!kallon ta yayi sai ya bar abinda yake yi ya tako har dab da ita ya ja ya tsaya kamar gunki..

Tsoron sa ta fara ji yana shigar ta sai ta ɗago kan ta ta kuma kallon sa da kyau nan take ya mata ƙwarjini sai ta kasa cigaba da kallon sa dole ta sunkuyar da kai ƙasa..

Tana ta wasi wasi a zuciyar ta sai ta ji numfashin mutum kusa da fuskar ta,ɗagowar da zata yi kuwa ta gan sa kamar zai shige fuskar ta.. .

Kallon ƙwayar idanun sa tayi a tsorace sai ya sakar mata da wani lafiyayyen murmushi da ya ratsa ta sannan ya riƙo kafaɗun ta a sanyi ya ce

"Eh...,na iya girki,are u satisfied"?saurin gyaɗa mai kai tayi tana kawar da fuskar ta gefe..

Murmushi yayi yana riƙo hannun ta cikin nashi haɗe da da jan ta zuwa kan kujerar kitchen ɗin yana mata tayin abincin.. .

Bata mai yanga ko jan aji ba ta amsa tayin nasa ta hanyar farawa da tea ɗin da ya haɗa masu sannan ta ɗau spoons ta fara cin abincin wanda frayed plantain ne da aka yi sa da ƙwai kamar balls aka yi scrambling aka soye sa..

Matuƙa ta ji daɗin wannan breakfast ɗin dan har cinyewa tayi bata sani ba sai da ta saka spoon ɗin ta ji babu komai sannan ta ɗago ta kalle sa shi da kwata kwata bai fi spoons huɗu da yayi ba yana da kallon yadda take cin nata.. .

Turo mata plate ɗin sa yayi ya mata alamar ta ci da ido sai kuwa ta ja gaban ta ta fara ci tana murmushi..

Tagumi yayi yana kallon ta tana bashi dariya sai dai ba girman sa bane yin dariya anyhow ba sai kawai ya murmusa yana cigaba da kallon ta har ta gama sannan ta dube sa ta tmby sa..

"Kai fah?me zaka ci"?ɗage kafaɗu yayi yana mata alamar bai sani ba,ɗan buɗe baki tayi da mamaki ta ce
"Da fatar ba ni na hana ka cin naka ba"?girgiza mata kai yayi ya ce
"Kin ƙoshi"?kallon sa tayi da murmushi shimfiɗe a fuskar ta ta amsa mai da eh..
Tashi yayi yana riƙo hannun ta suka bar kitchen ɗin zuwa bedroom ɗin su sai ya bar ta a nan ya shige toilet yana mai ce mata yana zuwa..

Zama tayi a wurin har ya fito da bathrobe a jikin sa ya nufi wardrobe ya nemo kayan sa as usual kaftan da hula..
Tana kallon sa yana dressing har ya gama wani sabon ƙaunar sa na fizgar ta a ran ta da hankalin ta..

Ƙamshin turaren sa ne ya ankarar da ita ya zo kusa da ita sai ta ƙare mai kallo sama sama sannan ta sunkuyar da kai ƙasa tana jin ƙamshin nasa na shigar ta..

"Zan ɗan fita i have a meeting to attaind misalin 4 zan dawo InshaAllah and don't bother to stress ur self akwai lunch ɗin ki a warmer ɗin nan a kitchen and about dinner,i will make a takeaway for us ok"!!gyaɗa mai kai kawai tayi tana yaba manly attitude ɗin sa,bata yi zaton hakan ba daga gare sa,tunanin ta na ta bashi ba zai wani bata muhimmanci ba amma yanzu ta ƙaryata tunanin nata dan ta ga zahiri...

Juyawa yayi zai tafi sai ya ga bata biyo sa ba sai ya ja ya tsaya yana kallon ta,bata san dalilin sa na tsayuwar ba sai dai ta ƙura mai ido har ya ce wani abin

"Babu rakiya"!?a ɗan kunyace ta tashi ta biyo bayan sa ta raka sa har bakin motar sa tana ɗan takawan a sannu dan tana jin zafin na bijiro mata..

Bayan tafiyar sa ta dawo ciki ta kwanta a parlor saman kujera,tuni kewar sa ya fara mamaye ta da sabon feelings ɗin da take ji game da shi..

A haka nan ta ɓannata ranar cikin kewa da begen sa har sai da ya dawo sannan ta ji daɗin gidan..

Tun wannan rana kusanci mai ƙarfi ya shiga tsakanin Marshall da matar sa kuma ƙanwar sa Mufida,babu dai wata abin da ta sake shiga tsakanin su na dangane da rayuwar aure irin ta ma'aurata,hasalima kula ta musamman da ban mamaki yake ta bata a ganin sa shi ta fi buƙata a yanzu fiye da komai...

****
Kimanin sati ɗaya kenan da faruwar wannan ɗin haka sati ɗaya cif kenan da fara special care da Marshall ke ba Mufida abin sai wanda ya gani,Ita kan ta da ta zauna tayi doguwar nazari da tunanin kulawar sa gare ta sai ta rasa irin mizanin da zata saka sa akai sai dai a ƙarshe,ta danganta shi da so ne mai ƙarfi burin ta bai wuce kar ya bar ta tayi ta iyo cikin son nasa ba tare da shi ya biyo ta sun yi tare ba dan da son maso wani da ake mai inkiya da ƙoshin wahala gwara son bayyane ko rashin saka kai a soyayyar wanda bai san kana mai so ba..

Tana zaune tana danna remote tana nemar tasha ɗaya da zata kalla duk bata sami wanda hankalin ta ke so ba,sai ta ja ƙaramar tsaki gashi tun rana da ya fita bai dawo ba.. .

Kwanciyar ta tayi a kan kujerar ta lumshe idanun ta har bacci ya fara zuwar mata..

Cikim baccin da bai fi 15 minutes da ɗaukar ta ba ta ji an manna mata kiss a kumatu sai ta buɗe idon ta a sannu har ta gama buɗe su tayi tozali da nasa..
Da sauri ta tashi zaune tana gyara zama haɗe da yi mai barka da dawowa sai ya zauna next to her yana tmbyr ta ya zaman kaɗaici..

Buɗar bakin ta cikin shagwaɓa kawai sai ta ce mai
"I missed u"!murmushi ya mata ya kuma maida hankalin sa gare ta ya ce
"Really?did u missed me"?gyaɗa mai kai tayi kawai da niyyar zata bar wajen sai ta ji ya janyo ta ya rungume ƙam ƙam yana faɗa mata cikin kunne
"I missed u more"!a ran ta ta maimaita "!!sai dai tayi shiru bata ce komai ba..

Sun jima a haka kafin daga bisani ya raba jiki da ita yana kallon ta cikin ido babu ɗar ya ce da ita
"I want to spoil u tonight"ya kanne mata ido ɗaya abin sai ya mata wani iri ta kalle sa da ayar tmby sai ya gyaɗa mata kai kawai ya ɗago ta suka wuce zuwa bedroom ɗin su,ko me yake faɗa mata,sai dai murmushi da take ta yi tana ƙasa da kan ta abin mamaki abin sha'awa...

_bayan wasu awowi_

Kwance suke kan ta a saman ƙirjin sa babu kaya a jikin sa sai blanket da rufe su su biyun,wasa yake yi da hannun sa a jikin ta daga sumar kan ta mai daɗin taɓawa zuwa gadon bayan ta..

Daga ita har shi babu mai mgn sai shi ne ma mai sauke ajiyar zuciya idanun sa na kallon sama.. ..

"Was it painful"?tmbyr da ya mata kenan ta ƙyale sa tana mai ƙara shige masa jiki,all her life bata san wannan mijin nata zai zame mata abin farinciki da jin daɗi ba dan tun impression ɗin fari da ta bashi akan tsoho ne sai ta ji bata marmarin ganin sa amma yanzu kam ta tabbatar shi ne mahaɗin sinadarin rayuwar ta babu yadda za a yi ta cigaba da rayuwa a doron ƙasar nan ba tare da shi ba

A fannin Marshall ma kusan hakan ne,ɓoyayyen soyayyar matar nasa ne ke ratsa sa sai dai yana fargabar bayyana mata kar ya rasa ta dan bai gama yarda da tana son sa ba maybe shi kaɗai ke hidima da soyayyar nata ita bata yi..
Addu'ar sa Allah ya sa kar ya zama one sided love dan in hakan ya faru,tabbas zai yi wa zuciyar sa hukuncin yi mai abinda ya mai na barin sa ya kamu da soyayyar wacce bata san yana yi ba..
Jin numfashin ta ya ƙaru sai ya leƙo fuskar ta nan ya ga bacci take yi mai nauyi sai ya murnusa ya manna mata good nyt kiss a lips ɗin ta da goshin ta sannan ya ƙara manna ta da jikin sa ya rumtse nasa idanun ko bacci zai yi nasarar ɗaukar sa..
#Mamuh[8/6, 10:58 PM] Miss Xoxo: *30*

bayan sati biyu da kasancewar su anan yau fifi kwance take a jikinshi tana karanta mai wani English novel hankalin ta kwance sai data kawo kan tsakiyan labarin sannan ya dakatar da ita ta hanyar cemata, "we are going back home tomorrow" ajiye book din tayi a gefenta sannan ta kalle sa a nitse tace "ok Allah yakaimu lafia"ba yabo ba fallasa yace ameen saidai bataji dadin hakan ba ko kadan sabida tafara sabawa da sabuwar kwanciyar hankali da kalar soyayyar dayake nuna mata anan din duk dama tasan sababin sa tausayi ne,shikuwa saheeb yana kula da mood dinta daya canza sai yakai hannunshi kan tummy dinta yace,meye ne?yunwa?Tayi murmushi ta mike xaune a kunyace ta girgixa kanta...

" kodai kar mu tafi naga kin kara kyau komi yakara cikowa"nan yafi dadi ko...sai yakare maganar da irin tsigan wasan nan Murmushi medan sauti tasaki dan ita abun daria yabata dan tasan ina maganan nasa ya dosa Hmm 3weeks kawai ya isa tadau cikine abunda tafada kenan acikin zuciyar ta?tanata murmushi haka kawai taji burin samun hakan ya mamaye ta Tunanin hakan ta mugun sawa aranta

Kamar yadda yace xasu tafi goben baiyuba wani sati guda suka kara inda babu abunda ke ninkuwa a tsakanin su sai sassanyar so da shakuwa

Kullum in tana jikinsa sai yayi ta tsokanan ta da cewa..."seriously bakiga yanda kika canza ba, inaga idan munkoma gida zamuje hospital a duba munke" dage eyebrows dinta takeyi tace, "ok" bata iya cewa komai

Kwance take sannan tamike tace bari taje tafara shirya kaya tun yanzu shima mikewan yayi yabi bayanta yace su shirya kayan atare

Bedroom dinta suka shiga suka fara shirya komi a inda yadace bayan sungama hada kayan nata sai suka wuce nashi closet din shima suka shirya komi inda ya dace da la'asar bayan yadawo daga masallaci suka shiga kitchen tare suka hada dinner saidai tun a kitchen Fifi tafara jin wani irin sauyi acikin jikinta dakyar ta iya bari suka gama aikin batare da ta nuna masa alaman komi ba...

suna gamawa tayi saurin wucewa room dinta tashiga bathroom zatayi wanka nanfa tafara jin tashin zuciya jim kadan ta soma kwarara Amai mai yawa mai gajiyarwa Sosai gaban ta ya fadi...

Nan take taji wani irin bakon yanayi ya dulmuye xuciyarta
tsoro da fargaba wanda bata san dasu ba taji yana dirar mata take gabobin jikin ta yayi sanyi sosai ba abunda take tunawa sai ranan mutuwar ta,tsuguno tayi agaban toilet tana haki,wasu silent tears ne ke ziriya daga cikin idanun ta marasa ma'ana marasa dalili..

Takanji kamar Wani bangaren xuciyarta ya amince da sabuwar zabin da Allah ya mata na samun wata nitsatsiyar rayuwa da saheeb amma takan gujewa rudin zuciya musamman akan soyayya dan ta riga tasan iya madakatan rayuwar ta ba wani boyayyar abu bane,mutuwa ne.

Ta dade anan cikin rudanin haka,batare da sanin me zatayi ba.

Jin shirun ta yyi yawa Marshall ya biyo bayanta da sauri yashigo bathroom din ganin yanayin ta kawai yafara jera mata sannu,uhmm kawai take iya cewa harya gama tayata wanke mata jiki yacire mata atamfar dake sanye ajikinta ya daura mata wani white towel ya daukota kamar wata baby yafito da ita yadireta akan gado,a daren ranan ba karamin wahala tayiba sabida aman da take tayi ya tsanan ta wani bin sace jikin ta takeyi tayi abun ta ta dawo..

Washe gari Koda tayi sallan asuba saita koma ta kwanta sabida baccin da batayi a daren jiya ba,har cikn ranshi ya damu sai Bai tashe taba sai wuraren 10am shima yatada tane sabida su isa gida dawuri da kanshi yayi mata komi yayi feeding nata da kyar tea kadai ta iyasha
Ciwon kai da bacci ya gama kashe mata jiki

saida yasaka Duk trolley dinsu a mota sannan yadawo ya daukota a owner seat ya ajiyeta hade dayin kissing dinta sannan yamaida door din yarufe yakoma yarufe ko ina nagidan sannan yabawa gate man keys din yashiga driver seat yatada motar sukabar compound din gidan

5pm yamusu a gida suna shiga cikin compound din gidan taji gabanta yawani fadi saidai takosa sosai taga twinnie dinta sabida she have missed her so much fiye da tunanin me tunani , a bakin apartment dinsu yafaka motar da kanshi yafito yabude mata door din motar tafito sai yace mata tashiga zaishugo yanzu uhm kawai tace sannan takai hannunta kan handle din door din tabude tashiga babban falon saheeb bakinta dauke da yar karamar sallama.


A Zaune ta tadda wata mata a daya daga cikin kujerun falon sanye take da wa'insu hadaddun riga da skirt na Atamfa English Aura wax wani irin qamshin turaren Arabians na tasowa daga cikin ahankali Yana gauraya palon.

ganin kyakkyawar dirarriyar mace a zaune cikin palon saida yafadar ma Fifi da gaba duk dama bata san ta ba,dan karamar ajiyar zuciya ta sake saita dake takarasa shiga cikin falon tanajin wani rawar jikin sanyi na shigarta da tsantsar tsoro da wani tauri nason danne mata zuciya ta kakalo murmushi harta karasa inda Muhibba din take zaune tana pressing phone dinta, "asslm alaikm Ina yini" shine abunda Fifi tace a taqaice tana sake kallonta cikin tsananin sarewa da faduwar gabanta dake tsananta,

Kallonta ta sake dagowa muhibba tayi cikeda da qare Mata kallo tana qoqarin danne abinda ke taso Mata gameda fifin sbd Babu tantama wannan itace mufeeda wadda ta auri Marshall dinta Wanda ya kasance nata ita kadai....itadai Fifi murmushi tayi dan she don't really care
Wucewa room dinta tayi Muhibba tabi bayanta da harara mai zafi.
#Mamuh
[8/6, 10:58 PM] Miss Xoxo: *29*

5am ta farka da face dinshi tafara tozali sosai ta wani kafeshi da ido tana karewa face dinshi kallo soyayyar shi na huda duk wani gabobin jikinta har batasan sanda tasaki wani murmushi ba hade dakai hannunta tashafa gefen face din nashi, abunda bata saniba tun farkon tashin ta shima yatashi sai jin hannun shi tayi akan nata hannun sai tayi saurin zaro manyan idanunta hade da sauke su akan face dinshi dayake aika mata da wani rikitaccen murmushi me ma'anoni da dama saurin rintsa idanunta  tayi tana boye face dinta a jikin pillow,
a hankali yakai hannun shi kan lips dinta yana shafawa lips dinta yana daya daga cikin abunda yafi birgeshi da ita Duk dashi komi nata birgeshi yakeyi, cikin yar karamar voice dinta tace, "it's already late lokacin sallah yayi" lips din nata kawai yatsirawa ido sabida yanda take motsa bakin kamar ba daganan maganar tafito ba,
"I know" shine abunda yafada hade da daukan ta cak yakaita bathroom a tare sukayi wanka suka tsaftace jikin su still da zasu fito daga bathroom din daukar ta yayi yafito da ita yadireta akan gado, sannan yace mata
"pray nima zanje na shirya nayi nawa sallan" nodding kanta kawai tayi tana wasa da fingers dinta harya fice daga dakin saita tsinci kanta da sakin wani murmushi tabbas yanzu kam tagama yarda da soyayyar Marshall yagama kama Duk wani sashi na jikinta a hankali tamike daga kan gadon takarasa gaban wardrobe tasanya hannunta guda biyu tabude inda long abayas dinta suke tacuro wata purple color me manyan design a gaba tasaka hade da daukan hijab sannan takarasa ta dauki prayer mat tashinfida ta tada sallah,

Bayan 30min Marshall yashugo dakin zaune ya tadda ita akan prayer mat tana azkar kallon ta kawai yakeyi yanajin wani shauki akanta he loves her so much saida yakusan 5min a tsaye sannan yakarasa shiga cikin dakin yamaida door din yarufe karasawa yayi inda take hade da samun waje a bakin gado yazauna yana kallonta atare suka shafa addu'an sannan ta dago takalle shi  suka sakarwa juna murmushi cikin yar karamar voice dinta tace

"Good morning" saida yakai hannun shi yakama mata nata hannun sannan ya amsa da, "Morning mon amour, how's ur night?" sosai taji dadin sunan daya kirata dashi shafa tafin hannunta daya keyi shiya hanata amsawa dawuri dan haka saida ta dauki lokaci sannan ta amsa da

"Alhamdulillah dafatan kaima katashi lafia" takare maganar da dan dagowa tana kallon shi ta wutsiyar ido,

bata ankara ba saijin mutum tayi ya sunkuceta yayi kan gado da ita saida yakwantar da ita sannan yacire mata hijab din dake sanye a jikinta ya ajiyeshi a gefe guda sannan yacire mata long abaya din a cewarshi abayan zata takura ta itadai idon ta yana rufe har shima yacire nashi jallabiyan ya ajiye agefe sannan ya janyota zuwa jikinshi hade da rufe suda blanket, yafara wasa da long hair dinta dayasha gyara harshen shi yakai cikin kunnanta yana latsawa a haka wani baccin yakara daukan ta,

8am suka farka a tare suka shiga bathroom sukayi wanka half gown tasaka mara hannu milk color saita zubo da gashin kanta har gadon bayanta sosai tayi kyau Duk dako powder bata shafa a face din nataba sai kalolin perfumes data feshe jikinta dashi tana gamawa tawuce kitchen cikin 30min tagama hada musu abun breakfast,

Arabian meal tahada musu Wraps, sandwiches and manakeesh tana son kalolin abincin larabawa sosai shiyasa ta iya dukkan nau'o'in abincin su, anan dinning table na kitchen din ta jera komi tana juyawa zata fita daga kitchen din Marshall nashugowa sanye yakeda kananun kaya black jeans da white T-shirt yayi kyau sosai har batasan ta kafeshi da idanu ba saida yakaraso

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login