Showing 51001 words to 54000 words out of 101986 words

Chapter 18 - KAUNAR MU COMPLETE HAUSA NOVEL

MAMUGEE   

27 Sep 2024

15645

garden tana kallon Saheeb kuma da zarar lokacin tashin sa yayi sai ta bar wurin dan kar ya gane ta kuma daidai da rana ɗaya bai taɓa sanin da zuwan ta ba sai dai yayi abinda ya kai sa ya gama ya wuce..
  In ma fannin abinci ne in ta gama bata saka mai a food warmer sai dai ta bar mai haka nan duk inda ya kai ya kawo da yunwar sa in ya dawo daga aiki haka zai yi reheating abincin ya ci kamar bai da mata,sam sam zaman su ba wani daɗi,kyautatawa sai wanda ta ga damar yi take mai,lokacin sa ma bata da shi sai ta ji dan kan ta ta saurare sa,haƙƙin sa kam ya manta rabon ta da ta ba shi sai dai da ya matso ta ta ɓata fuska ta ce she is not in the mood..
Duk wannan abinda ke gudana babu wanda ya san da shi daga ita sai shi ba ƙaramin gasa mai aya a hannu Hamida ke yi ba kuma bai da ikon yin magana dan yana tunanin wa zai tunkara da wannan batu a wurin sa kamar abin kunya ne a ce shi da matar sa amma bai isa ya ji daɗi ba..

Batun zamantakewar ta da su Ammy kuwa babu abinda ya sauya dan nesanta kan ta da su take yi ba kaɗan ba har ta kai ta kawo in Hajja ta zo sashen ita Hamidar ta manta bata rufe ƙofa ba da ta ga Hajjan sai tayi saurin tashi ta wuce da zarar ta gaishe ta abin na damin Hajja har da Ammy ba kaɗan ba dan da zuciya ɗaya suke son jawo Hamida jikin su amma ita gani take kamar yi suke yi na ganin ido shi yasa ta ƙi sakin jikin ta da su..

****

Yau monday yau ne fifi ta yi nasarar kammala jarabawar ta na first semester kuma da farinciki ta dawo gidan dan papern ya mata daɗi bata yi zaton zai zo mata da sauƙi haka ba.
Ranar Hajja ta shawarce ta ko zata tafi ta kaiwa ƴar uwar ta ziyara ƙila ta yarda da ita su tsaya su yi magana tunda su dai bata tsayawa su yi wata doguwar magana bata zuwa sashen su su kuma in suka tafi sai ta tashi ta bar su..

Fifi dai bata gamsu da shawarar kakar nata ba dan ita kaɗai ta san irin zafin da ta ji a lokacin da Hamida ta ture ta daga jikin ta haɗe da bata wani dirty look ranar ta ji ba daɗi bata san ƙiyayyar da ƴar uwar nata ke mata ya kai haka ba sai ranar shi ya sa ta yanke hukuncin bata kuma zuwa wurin ta sai dai ta cigaba da yi mata addu'ar saukowa dan ba iya nan ta tsaya ba hatta da silent intimidations ɗin da ta ke yi mata a baya ta cigaba da yi har yanzu bata daina ba kawai dai bata sanar da su Hajja ne dan kar abin ya kuma taɓarɓarewa Hamida ta kuma tsanar ta...

A daren ranar ta fito parlor bayan kowa ya kwanta bacci ta zauna ta saka system ɗin ta a gaba tana duba wani abu gudun kar ta tayar da Ammy ya sa ta dawo parlor dan ta sake ta yi abin ta da kyau..
Kimanin mintuna talatin tana ta abinda take yi sai ta tashi tana rufe system ɗin alamar ta gama ta cire shi daga chargi tana naɗewa ta saka footwear ɗin ta tana miƙa tana salati..

Juyowar nan da zata yi sai ta ga mutum a hanyar water dispenser yana ɗiba ruwa dan sha..
Saurin gyara rigar baccin jikin ta tayi duk da riga da wando ne kuma bai bayyana tsiraicin ta ba amma sai ta ji faɗuwar gaba ya riske ta..

Wanene wannan ɗin da ya tsallake kitchen ya ratsa har main parlor ya zo shan ruwa,sai da ya juyo shima ya lura da ita dan akwai tazara tsakanin ta da shi kasancewar parlorn babba ne..
Shaƙewa ya so yi da ruwan dan yayi zaton ghost ne bai taɓa jin tsoro irin wannan ya riske shi farat ɗaya ba..
Sai da ya ƙare mata kallo ya tabbatar mutum ce kuma itama kamar a tsorace take sai shi ya riga ta magana.

"Am sorry"daga faɗin haka ya juya ya fice abin sa ita kuma ta haura a guje dan ganin fuskar mutumin ranar nan da ta yi wanda Ammy ta ce wai shine yaya Saheeb ɗin da suke jin labarin shi...

Da tunanin shi ta kwanta tana ƙoƙonta anya shine ko dai wani Saheeb ɗin ne dan wannan bai yi kamar shine Saheeb ɗin da suke tsammanin gani ba..
Gari na wayewa ta nufi sashen Hajja da yanzu ta idar da sallah tana azkar ta zauna jiran ta har ta ɗan taƙaita suka gaisa bata yi nauyin baki ba ta tambayi Hajja ko waye wannan da ya zo ɗin,Hajja ta tambaye ta dan neman ƙarin bayani nan ta mata kwatancen sa sai Hajja tayi murmushi ta bayyana mata ai shine yayan nasu almost same amsa da Ammy ta bata ne Hajja ta bata sai ta kuma tambayar Hajja wai shin shekarun sa nawa..
A nan sai da Hajja ta dara ta ce ba tsakanin ta da mijin ta bane wannan,haka fifi tayi tayi Hajja ta faɗa mata amma Hajja ta ƙi ƙarshe ma kora ta tayi dan kawo mata zancen wai ya ce matar sa zata dawo daga jibi zuwa juma'a sai fifin ta kama jiki dan Muhibbah ƴar gayu ce kuma ta girme mata ba kaɗan ba..

Wannan zancen Hajjan ne ya kori fifi ta miqe ta nufi qofar fita da sauri ta bude tareda ficewa gaba daya daidai shikuma ya budo qofar zai shigo qirjinta ya sauka a kirjinsa sosai Wanda ya haddasa musu Shirin faduwa sbd baisan da itama hakama itama
Sukayi baya ya dafe bango da hannunsa daya yayinda dayar hannun ya riqeta sbd yanda tsoro da firgici yasa ta qanqamesa tana rufe idanuwanta.

Ahankali ya dago ya kalli fuskarta akaro na farko dayaji razanar zuciya Bayan kallon wata 'ya mace,
Itama ahankali ta bude idanuwanta ta sauke Masa zuciyarta na tsananta harba Wanda haryanaji a qirjinsa datake Kai.

Hajja ce ta Dan daga murya tace"

Meyake faruwane agurin wai naji shiru???

Saurin sakinsa tayi shikuma ya fuske tareda dauke Kai ya fada dakin da sallamarsa data sake fadar da gaban fifin ta waiwayo ta kalli bayansa tana Jin wani zazzabi nason kamata
ta koma ta kwanta a gadon Ammy tana ta tunani da ƙiyasta ya matar nasa zata kasance dan in har shi yayi appearing a haka ba a tsohon da tayi tsammani ba ya matar nasa zata kasance ga shi Hajja ta ce ƴar gayu ce...

Ba ƙaramin halin tunani da jimami fifi ta shiga ba sakamakon waɗannan abubuwan al'ajabi da take gani a gidan right now tunanin Hamida da yanda komwi ke Naman lalacewa a tsakaninsu Yana damunta saikuma na wannan ɗin da wai shine mijin ta da na matar sa da wai zata zo abin na ta mata yawo har bacci dai ya ɗauke ta,tsabar ta saka abin a ran ta sai ta rinƙa ƙananan mafarke mafarke kala kala a baccin nata game da matar yaya Saheeb ɗin ƙarshe da ciwon kai ta tashi ta rinƙa tsaki tana jin haushin ɗorawa kan ta damuwar wasu,da haka ta bar gadon babu Ammy a ɗakin ta wuce dan yin wanka a lokacin har 11am yayi...

Kamar ko yaushe tayi wankanta na yamma tana Shirin zuwa gurin hameda ammy takirawota kicin fuskarta Babu alamar Wasa ta nuna Mata qaramin tray da aka jera combo juice nasu fruits marasa zaqi tace'
Dauka kikai sashen mijinki Yana jira Kuma idan kinkai ki jira yagama ki kawomin kayan.

Kallon ammyn tayi tasake kallon kayan kafin takuma kallon ammyn taga Babu Wasa ko sauqi a fuskanta saitaji jikinta yayi sanyi har zata dauka saita fasa tace"

Bari nadauko mayafina....

Kije ahaka jira yakeyi and karnaga qafarki anan sai ya gama infact ki zauna acan zakuyi mgnar inda kikeson zama.

Rau Rau tayi da ido zatai mgn ammyn ta wuceta tana sake tsuke fuska sbd taga idan Bata tashi tsayeba akan Fifi idan muhibba tazo da matsala.

Part din ta nufa tayi knocking ahankali Kai tsaye yace"

Com in Yana amsa waya.

Murda qofar tayi ta tura ta shigo wani sanyin AC da qamshi suka daketa ta qarasa shigowa tareda tura qofar tana kallon qasa sbd bazata iya kallonsa ba.

Shima dagowa yayi yayi Mata kallo daya ya maida kansa kan kallon laptop Yana cigaba da wayarsa.

Ajiye Masa tray din tayi hannuwanta na Dan rawa ahankali ta furta"

Ina wuni cikin siriryar muryanta data Kuma sashi dagowa ya kalleta da idanuwansa dasuke wasu blue blue.

Kamar bazai amsaba yace"

Lfy klau sit.

Zama tayi adarere tana kallon yanayin tsarin palon a takure ga zuciyarta dake wani irin tsallen rashin sukuni.

Yana gama wayar ya ajiye ya rufe laptop dinsa bai dagoba ya zuba combo din a cup ya dago ya Dan kalli gefenta ya hango zallar yarintarta da kuruciyarta sai kawai ya dauke Kai Babu abinda ya fado Masa sai ranarda aka haifesu Amma shine su ammy basuyi wani dogon tunanin nisan shekarunsu ba aka ɗaura Masa aure da ita alhalin zai Isa haihuwarta insha Allah.

Kamar bazaiyi mgn ba cikin wani irin class yace"

Kije.

Ahankali ta dago ta Dan kalli gefen fuskarsa dake kwance fresh da qananun gashinda suka mugun kwanta cikin siriryar muryar basarwa tace'

Ammy tace nadawo da kayan.

Shiru yayi kamar baiji ba kafin yace"

Ok ki dauka na gama.

Tashi tayi cikin mamakinsa da Dan Jin haushinsa na yanda yake wani basarwa ta dauki kayan ta fice batareda tace Masa komaiba.
#Mamuh*21*

Dawowa sashen su tayi tana jin mamakin sa har ta shiga kitchen bata ankara ba sai da ta ji kamar ta buge abu sannan ta dawo hayyacin ta ta kalli abinda ta buge..
  Ɗan tsaki ta ja tana dire tray ɗin saman babbar fridge ɗin kitchen ɗin tana mai zama saman wani stool mai juyawa amma bata bari ya juya da ita ba sai ta zauna still ta dogara hannun ta da saman kitchen table dake nan kamar round dinning table,sannan ta tallafe kumatun ta da hannuwan ta biyu ta yi shiru tana kallon direction ɗaya..

"Ni kam wannan wani irin mutum ne shi?daga haɗuwa da shi har yana nuna min jin kai yana wani basarwa hala bai san Ammy ce ta tursasa ni kai mai abin shan ba ƙila shi ya sa ya min wannan jan ajin,toh amma ai nima kyau ne da ni ko?ina da kyau mana toh da me yake taƙama"?wata zuciyar ta amsa mata da ai shi soldier ne ko kin manta..

  Jan iska tayi sannan tayi breathing out tana girgiza kai sai ta kuma faɗawa wata duniyar tunanin daga bisani ta kalli agogon dake manne a kitchen ɗin ta ga 6:40pm magrib na gabatowa sai ta sauko daga kan kujerar ta nufi hanyar upstairs dan kaiwa Ammy sakamakon aiken ta da ta yi..

Wani abin al'ajabi da ya faru shine tana haurowa ta yi kicibis da fuskar sa sai ta ga kamar tsananin damuwar sa da ta saka a ran ta ne game da shi ya sa ya zo yake mata gizo.
  Har zata wuce sai ta kuma kallon sa ta ga yayi blinking idanun sa haka ya tabbatar mata da shine a zahiri ba mafarki ba..

Saurin wuce sa tayi tana jin faɗuwar gaba matsananci da bata san dalilin sa ba,bin ta da kallo yayi har ta gushewa ganin sa ya girgiza kai yana mamakin ɗabi'ar ta kamar ta ga dodo har da gudu,shi kam su Ammy sun haɗa shi da aiki wannan yarinya a matsayin matar sa abin na bashi mamaki har yau,dan shi har yanzu da ya kalle ta tunowa yake yi still da lokacin da aka haife ta ita da ƴar uwar ta Hamida aka bashi su ɗai ɗaya ya riƙe su,wai an wayi gari ɗaya cikin yaran ne kuma aka aura mai at his age ya san ko a haihuwar kaji ya haife ta ya kuma haifi wacce zata girme mata..

Ƙarasa saukowa yayi yana ta nazari a zuciyar sa game da irin rayuwar da zai yi tare da fifi a ƙarƙashin inuwa ɗaya a matsayin mata da miji..

Da gudu ta shigowa Ammy ɗaki har sai da Ammyn ta ji tsoro ta kalle ta da mamaki ta ce
"Me ye kuma haka baby,ko kin manta kina da aure ne yanzu da kike guje guje haka"?kallon Ammy tayi sai kuma ta ji bata jin sanar da ita abinda Saheeb ya mata kawai sai ta yi murmushi ta ce
  "Am sorry Ammy i was eager to see you"!!kallon zargi Ammy ta bi ta da shi har sai da ta ji ta tsargu sai ta shashantar da zancen ta hanyar jan hannun Ammy ta kai ta saman sallayar da take shirin hawa dan bada farali..

  Kallon ta kawai Ammy ke ta yi har ta je ta kwanta bisa gadon Ammy ta ba Ammy baya sai Ammy ta girgiza kai kawai bata mata magana ba ta tayar da iƙamar ta dama fifi na fashin sallah sai tayi kwanciyar ta kawai...

_2 hours later_

  A dinning table yau Ammy ta ji a yi dinner sai ta sa aka kawo duka abincin nan har wanda za a kaiwa Saheeb ta ce a bar shi a kawo nan shima zai yi joining ɗin su..
  Fifi dai na jin Ammy amma da so samu ne da ta roƙi alfarmar kar a bar ta a nan a bata dama ta wuce da nata sama ta ci a can dan ta san ko presence ɗin sa kaɗai ya isa ya hana ta sakewa bare ta ci abincin har ta ƙoshi..

A gaban ta Ammy ta kira sa a waya ta ce mai ya zo su haɗu a dinning ta girka mai favourite ɗin sa,sai ko ba a jima ba yayi sallama ya shigo direct ya nufi sashen da dinning ɗin yake nan ma ya kuma doka sallamar sai da fifi ta ji sallamar a kan ta dan ba normal voice da mutani ke amfani da shi wurin yin magana shi yayi amfani da shi ba..
  A matsayin sa na babba kuma elder person yayi sallamar,yana ƙarasowa dan gaida su Ammy kafin ya zauna fifi ta rinƙa kallon sa ƙasa ƙasa..
  Har ya zauna bata sani ba sai muryar Ammy da ta ji tana umartar ta da ta yi serving yayan ta..
 
Duban ta ta maida ga Ammy sai Ammy ta kuma maimaita mata ta tashi tayi serving yayan ta shima Saheeb ɗin sai ya dubi Ammy ya kuma dubi fifi wacce a dai dai lokacin idanun ta ya kai gare sa dan ganin ya zai yi reacting da jin wai ita ce zata yi serving nasa abinci..
  Sai ta ga idanun sa akan ta yana kallom ta abin sa ya bata mamaki tayi tunanin attitude ɗin da ya bata ɗazu zai bata yanzu amma sai ta ga akasin hakan,a zuciyar ta sai ta rinƙa muhawwara da kan ta akan ai ƙila ko halin sa kenan abinda ya maki ɗazu nan gaban mahaifiyar sa ce ba zai yi hakan ba..

Taɓe baki tayi kawai ta tashi a natse dama atamfa ce a jikin ta ɗinkim doguwar riga A-shape dan har yau bata gama zama gwana a ɗaura zani ba dama dama skirt takan ɗan saka sa wasu lokutan but ta fi yin free da doguwar riga..
  Gyara ƙaramin gyalen kan ta tayi ta hau tafiya a hankalin dan table ɗin babba ne kuma yana da faɗi in har so kake kayi serving abinci comfortably toh sai dai ka zagaya dan in ka tsaya a inda kake ba zaka ji daɗi ba..

Takun da take yi shi ya saka sa kai idanun sa gare ta ya rinƙa kallon ta a hankali cikin hikima har ta zo gab da shi ta tsaya,sai kuma ƙamshin ta ya shige sa nan ma still ya kuma aika mata wani irin kallo ita kuwa matsanancin faɗuwar gaban da ta rinƙa samu ne ya sa ta kasa natsuwa ta tambaye sa me zai ci sai kawai ta fara bubbuɗe wadatattun food warmers ɗin ta ɗau babban serving spoon ta fara ɗibar mai abincin tana zubawa..
  Sai da ta zuba mai abinci kusa 4 dishes a plate ɗaya ko wanne da inda take zuba sa da ta gama ta rasa ya zata ce mai ta gama zuba mai sai ta dubi Ammy..
  Abin mamaki sai ta ga idanun Ammy da na Hajja a kan su da har su sun fara cin nasu abincin amma suka dakata suna kallon dramar ta su kamar ba komai suke yi ba..
  Ammy na ganin ta kalle ta sai ta kalli Hajja wacce itama da sauri ta kawar da kan ta daga kallon su ta maida ga abincin gaban ta..
"Hajja kin ƙoshi ko in ƙara maki"!?sai Hajja ta amsa mata da ya isa hakan daga nan suka cigaba da cin abincin su ba tare da sun kuma kallon sashen su fifi ba sai dai sun ƙunshe dariyar su a ciki kar ya fito but ba ƙaramin dariya fifi ta ba su ba duba da yadda ta tsaya kamar soldier a tsaye ta kyaɓe fuska kamar zata yi kuka shi kuma yana kallon ta kamar tana abinda ba daidai ba..

  Tayi tayi Ammy ta ɗago ta kalle ta dan ta taimake ta ta mai mgn amma ko a kuskure Ammy bata ɗago ta dube ta ba haka Hajja kuma ba wai basu san tana buƙatar taimakon bane,sune ankare sai dai suna ganin in suna shiga al'amarin ta har yanzu da mijin nata ke nan toh ba zasu saba ba kuma ba zasu san juna su fahimci juna ba...

  Fifi na nan tsaye kamar an dasa ta Saheeb na zaune yana kallon ta yana girgiza kai dan mamakin saurin girman da ta yi farat ɗaya shi sam bai ma san ana wata drama a wurin ba bare ya ɗauke

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login