Showing 96001 words to 99000 words out of 101986 words

Chapter 33 - KAUNAR MU COMPLETE HAUSA NOVEL

MAMUGEE   

27 Sep 2024

15655

haifa..ki ɗauka,ki kula da shi..ki kula da shi yadda in ina raye zaki kula da ni...ki bashi duk soyayya da ƙaunar da ba zan ba shi ba...pls promise me...promise me that u will fulfil my request"!!da sauri ta gyaɗa mata kai sai tayi murmushin da yafi kuka ciwo sannan ta ce da Hamida

"Kuma kar ki manta da alƙawarin mu na daddyn mu kin ji?kar ki manta ko bayan na mutu ki tsaya ki cika mana alƙawarin mu ok"?kuka kawai Hamida ta fashe da shi tana daɗa rungume Fifi..

Sai da kukan yayi tsanani sannan aka zo aka fitar da Hamida tana fizgewa tana faɗin a bar ta ta gana da ƴar uwar ta but ina,haka aka fitar da ita tana kuka..

Bayan misalin awa biyu,Khalid ya dawo nan asibitin da fifi take ya sanar da su ya kira Saheeb ya faɗa mai an yi admitting Muhibba a asibiti kuma dama yanzu ya dawo so zai tafi can wurin Muhibba..

Ammy ce tayi saurin tmbyr sa ko ya faɗa mai har fifi sai ya ce a'a sai ta ce mai a bar shi kar a faɗa mai tunda su suna nan zasu iya tsaya ma fifi shi kuma ya tsaya da Muhibba kar su yi son kai...

****

After lyk 5 hours da zuwan su fifi asibiti an ɗan tsumayi haihuwan but babu wani cigaba sai kawai Khalid yayi signing ya ce su shirya ta a shiga da ita theater a mata aiki kawai dan situation ɗin fifi na deteriorating ga matsalar cardiac disorder ɗin ta ga na babyn dake jikin ta dake shiga distres..

Wata sabuwa ce ta taso dan ana ta ceton ran ta su Ammy na can na kuka a waje da Hajja,ga Khalid dake cikin firgici but haka fifi ta ƙi yarda a shigar da ita ɗakin theater ta ce sai mijin ta ya zo sun gana sannan ta yarda a shigar da ita..
Duk yadda suka yi haka ta ƙi yarda dole aka fara nemar layin Saheeb wanda sai ringing yake ta yi ba a ɗaga ba..

Hankula ne ya kuma tashi dan fifi bata yarda a shigar da ita ba ana ta addu'a a waje ita kuma sai nanata sunan _"Gentle"_ take ta yi wato Saheeb sai daga baya ma ma'aiakatn suka gane waye gentle ɗin nan aka zafafa kiran Saheeb but bai ɗaga ba,ga fifi na jin jiki ga Hamida na kuka a jikin Khalid...
#Mamuh
[8/24, 8:12 AM] +234 808 540 5215: *39*

On the other side kuma,bayan Khalid ya kira Saheeb ya sanar da shi abinda ake ciki sai ya tura mai adireshin asibitin da take..
Already dama suna gab da landing dama tafiya yayi kusan 6 days ago toh a yau zasu dawo shi ya sa yana dawowa ya nufi asibitin ba tare da ya sauya kayan jikin sa ba...

A lkcn da ya ƙaraso asibitin har Khalid ya tafi,so he appears so shattered kamar marar lfy,haka ya nemi ɗakin da take aka nuna mai sannan ya tafi hnkl tashe..

Yana shiga ya hango ta kwance kamar marar rai,nan hnkl sa ya daɗa tashi ya kasa natsuwa sai da ya ƙarasa gare ta ya durƙusa ƙasa..
Fuskar ta dake lulluɓe kusan duka cikin abin bada numfashi(oxygen)ya kalla ya kawo hannun sa ya fara shafa fuskar nata har ta ɗan motsa ta buɗe idanun nata da ƙyar cikin wahala..

Ganin shine sai ta ƙara buɗe idanun ta da kyau dan ta gan shi shima ya gan ta,hannun ta na rawa ta ɗora saman nasa..
Da sauri ya maida idanun sa kan hannun nata ya kalla sannan ya kalli fuskar ta da ya sauya yayi fari kamar wacce bata da isasshiyar jini a jiki..

Wani tausayin ta ne ya kama shi mai tsanani sai ya ɗan kawar da fuskar sa dan zuciyar sa ya karye for the very first tym Saheeb ya tsinci kan sa da zubda hawaye akan rashin ƙwarin gwiwar ciwon matar sa...

Murya a disashe can ciki yana rawa ta fara mgn tana jan numfashi da ƙyar tana ajiyar zuciya..
"Miji na...ka zo ashe...ban san..ban..ban san zaka zo nan kusa ba..na daɗe ina ta jiran ka ina ta ce masu su kira min kai amma...babu wanda ya gwada kiran ka...but a yanzu da na gan ka na ji daɗi"!da ƙyar ta kai ayar zancen sannan ta ja numfashi da ƙarfi kafin daga bisani ta dakata...

Kallon ta yake yi cikin halin tsantsar tausayin ta ya matso kusa da ita suna kallon juna..
Shafa fuskar ta yayi yana manna mata kisses a kumatun ta hawaye na zubo mai ya kasa mgn sai hawaye dake ta fito mai...

Hannu na rawa ta kawo ta shafa fuskar sa tana goge mai hawayen da ke fito mai tana girgiza mai kai alamar ya daina kuka sai dai shima girgiza mata kan yake yi akan ba zai daina kukan ba..

"Miji na ka yi shiru ka saurare ni..tun ɗazu nake jiran ka ka zo,i hv been fighting with this feelings dan ka zo mu gana,ganawa na ƙarshe"!!saurin rufe mata baki yayi da hannun sa yana girgiza mata kai but ta ɗan fizge ta cigaba da mgnr ta..

"Saheeb am dying...i am dying...it is certain..su kan su likitocin sun gani sun faɗa min..but ina ta daurewa dan ka zo in gan ka ganin ƙarshe kafin in mutu...na riga na gama ganin all signs of death Saheeb kuma na san at any moment...zan tafi in bar ka ba dan ina so ba sai dan ya zama dole...Saheeb bana son ka dakatar da ni daga mgnr da zan yi,i know it will hurt u but ka yafe min dan in sami rahamar ubangiji"..

Ɗan numfasa tayi kuma tana jan iska da ƙyar kamar zata tafi sai tayi yunƙuri ta cigaba da mgnr dan nauyin da take ji a ƙirjin ta ya wuce misali..

"Miji na...na zauna da kai sama da shekaru goma,baka taɓa min abinda zan ce ka zalunce ni ba..baka taɓa min abinda bana so ba,ka yi ƙoƙarin ka wurin ganin ka sauke haƙƙin ka a matsayin ka na miji na,and am proud of u for that..komai ka min a rayuwa sai dai ka san me"??ta tmby tana ɗage giran ta biyu sai ya girgiza mata kai yana kuma damƙe hannun ta cikin nasa yana zubda hawaye..

"Nayi blackmailing naka for long,..duk wasu abubuwan da na faɗa maka akan rashin lfy ta were all lies,i was sick but not to that extent,a lkcn da na tafi ganin likita..ya faɗa min cewa uterus ɗi na was weak but ba har haka ba kamar yadda na faɗa maka ba...i did what i did kawai dan in sami attention ɗin ka ne,ni na saka likita ya rubuta min abinda ya rubuta a file ɗi na sannan na ce ya bani file ɗin in kawo maka ka gani...the result was perfect na sami attention ɗin ka sai dai da yake Mufida bata da haƙƙi na..maganin da na rinƙa sha a matsayin antidepressant ashe yana min illa a jiki ban sani ba...ban daina shan maganim ba duk dan in sami attention ɗin ka,miji na...ka yafe min ka gafarta min...na san na ɗau haƙƙin ka kai da Mufida sbd selfishness ɗi na ashe ina nawa ne Allah ya tanadi min nawa hukuncin nayi tunanin hikima ta ta janyo ka gare ni ashe mutuwa ta na janyo,am deeply sorry Saheeb ka yafe min dan in sami Peaceful death,dan am dying very soon..."!!

A halin nan da yake ciki na ganin matar sa zata tafi ta bar sa bai ɗaukaka mgnr nata da ta gama yi ba sai girgiza mata kai yake ta yi yana ce mata a'a ta daina mgnr zata mutu..
Da yake ita ta san abinda take ji sai ta ƙyale sa har ta ɗan kuma gathering wani ƙarfin ta kuma nemar yafiyar sa...

Sai ga Saheeb na sharɓar kuka kamar ƙaramin yaro,daɗa damƙe hannun sa tayi ta ce
"Saheeb ka ce ka yafe min dan kar in mutu da haƙƙin ka a tare da ni,pls"!!yana kuka yana rungume ta daga kwancen da take bakin sa na rawa ya ce
"Muhibba na yafe maki..baki min komai ba,haka Allah ya ƙaddara zaman mu zata kasance,ni baki min komai ba kuma na yafe maki"!!murmushi tayi mai tafe da ciwon rasa rai sai ta ce mai
"Nagode miji na..na ji daɗi da ka yafe min..na san zan mutu a matsayin yardarjiyar mace da mijin ta ya yarda da ita..ka min alfarma ɗaya Saheeb"..da sauri ya ce
"Menene alfarmar da kike nema in maki Muhibba"?ɗan tsagaitawa tayi sannan ta ce

"Ko bayan na mutu ka cigaba da so na kamar yadda kake so na a yayin da nake doron ƙasa ina rayuwa,ka so ni fiye da yadda ka so ni while am still alive..promise to always pray for me yayin da na bar ka bana tare da kai..i know am still being selfish but son da nake maka ya kawo haka..promise me that Ƙaunarmu ba zata yanke ba ko bayan bana raye a duniya"!!yana kuka yana kissing hannayen ta ya ce mata

"Na maki alƙawari Muhibba,zan maki addu'a a ko da yaushe..ko a sallah na ko a bacci na"!!murmushi ta mai ta ce mai..
"Ka nema min yafiyar Mufida..ka ce ta yafe min pls"gyaɗa mata kai yayi sai ta lumshe idanun ta hawaye na zubo mata..
A halin gajiya da yanayin da take ciki ta ruƙo sa gagam jikin ta na rawa ta ce
"Zo kusa da ni ka kwanta while am dying,i want u next to me while i will fade away ka ji"!!ran maza ya motsu Saheeb duk ya rikice ya ruɗe ya rasa abin yi haka ya zo kusa da ita ya kwantar da kan sa a ƙirjin ta tana shafa kan sa yana kuka a zuciyar sa kuma yana jin raɗaɗi yana mata addu'a haka tun Muhibba na da nunfashi a hnkl ya fara tafiya har ya tsaya cak..

Yana jin ta sauke ajiyar zuciya mai ƙarfi da furta kalmar "sallalahu alaihi wasallam" alamar a zuciyar ta ta fara shahadar sai ta ƙarasa a bayyane..

Ɗago da kan sa yayi ya dube ta yayi zurum kamar statue sai daga baya ya miƙe tsaye ya shafa fuskar ta sannan ya manna mata last kiss a goshin ta ya fito waje...
Ko da suka ga yanayin sa su likitocin,sun san ta tafi ne sai aka shiga ciki kawai aka fara gyara ta...

Yana manne da jikin bango ya fiddo wayar sa sai ya ga kira ya shigo dama wayar a silent yake..
Khalid ke kiran sai ya ɗaga ya kara a kunne ba tare da ya ce komai ba..

Kusan minti ɗaya wayar na kunnen sa kafin ya sauke ya fito jiki a sanyaye ya shiga motar da ya kawo sa dama driver ne..
Gaya mai inda zai kai sa kawai yayi sai driver ya ja motar suka kama hanya...

****
Motar nasu na tsayawa ya fito da ɗan sauri cikin hanzari ya ƙarasa ciki yana tafe kamar zai haɗa da gudu....

Cikin sauri ya ƙarasa ciki inda da zuwan sa ya fara hango su Ammy hnkl tashe..
Ƙarasawa gare su yayi ya tmby inda fifi take nan hnkl tashe Ammy ta ce mai tana ciki tana tmbyr sa ya jikin Muhibba sai dai bai iya amsa mata ba ya wuce ciki inda fifi ke kwance ana shirya ta zuwa kayan theater..

Tana ganin sa ta miƙo mai hannun ta da sauri ya ƙarasa gare ta,abin is heart touching dan ba abu mai sauƙi bane a ce mutum ya rasa matar sa ɗaya ba cikin biyu sannan ɗayan da ta rage ma tana ƙoƙarin barin sa ba...

Durƙusawa Saheeb yayi a gaban ta yana kuka kamar dai yadda yayi ɗazu a wurin Muhibba bcos ita kan ta a nan ɗin,kalmar mutuwa take ta nanata mai sai da ya rufe mata baki sannan ta ɗan tsagaita..

Yana kukan ya rinƙa faɗa mata yadda yake son ta yake kuma ƙaunar ta,alfarmar da ya rinƙa nema daga gare ta shine kar ta tafi ta bar shi,in ta tafi ina zai fuskanta ya ji daɗi..

Yana kukan tana kukan suka rungume juna ta rinƙa nanata mai kar ya manta da ita ya saka ta a zuciyar sa duk da ta san irin son da take mai shi baya mata irin sa amma ya mata alfarma ɗaya,ko bayan bata raye,kar ya manta da ita a zuciyar sa da rayuwar sa...

Da karayar zuci ya ce mata ta daina kiran mutuwa dan in har ta tafi shima bin ta zai yi..
"Na san ni mai laifi ne a gare ki Khadija amma ki sani tun farkon ganin da na maki..na tsinci kai na da son ki,so mai tsanani da ƙarfi haɗe da shiga zuciya farat ɗaya,ko da na rinƙa ƙyale ki ina barin ki a dai dai lkcn da kike buƙata na kusa da ke..ba yin kai na bane,Muhibba ce ke ciwo mai tsanani ban san ya zan yi,in na bar ta na dawo gare ki zata ga na so kai na da yawa tunda ke tawa ce ƴar uwa ta ce,wannan dalili ya sa nake ta kasancewa kusa da ita but duk da haka,hakan bai sa na bata rayuwa ba dan ina ji ina gani ta tafi ta bar ni,ta bar mu mu duka,ta bar mana duniyar,a yanzu da na san halin da kike ciki khadijah..bana so in rasa wata matar kuma..bana so in rasa ki..pls don't do this to me..i will never forgive myself in na zuba ido na kalle ki kika bar duniyar nan khadijah..ki taimake ni ki yi fighting wannan battle ɗin ba dan ni ba ba dan kowa ba sai dan babyn mu da Ƙaunarmu..ki dawo gare ni kar ki rabu da ni,i love u so very much my wife"!!ya ida yana kuka...

Itama kukan take yi sai aka zo aka fara tapping nasa akan ya fita dan har Hamida ta kuma dawowa tana kuka tana son ta shiga ciki amma aka hana ta..
Da ƙyar aka ɓamɓare hannun Saheeb daga na fifi suna kallon juna aka yi wheeling nata zuwa theater room inda suna shiga aka rufe ƙofa take wuta ya kawo mai kala..

Hankula duk a tashe,Hamida ta manne a jikin Hajja tana kuka kamar me,Khalid dake ta namijin ƙoƙari ma a yanzu ya kasa dan abin ya girmi tunanin sa dole ya zauna wuri ɗaya...
Ammy na ta addu'a a zuciyar ta da fatar Allah ya sa a yi aikin lfy,yayin da ta kalle Saheeb ta tmby sa ya jikin Muhibba..

Nan ya faɗa masu cewar ta bar su,salati Ammy ta fara yi Hajja ma haka,tashin hnkl da ba a saka masa rana...
Ana fama da ciwo ga karaya,sabon kuka ne ya kaure a asibitin shi kam daurewa yayi ta yi idanun sa duk sun yi ja jazir..

****
_2 hours later_

Wutar ɗakin theater ya mutu sai hnkl su ya koma ga ɗakin suka yi zurum zurum suna jiran jin sakamako..

Fargaba da zullumi duk ya addabi zukatan su musamman Hamida da ta matso gab da ƙofar ɗakin..
Bayan lyk 5 minutes Dr ya fito hannun sa riƙe da baby duk ya jigata,yana fitowa ya dubi fuskar su su duka,tausayin su ne ya kama sa ya rasa ta ina zai fara gaya masu sakamakon da suke jira,haka ya daure yayi na maza ya miƙo babyn yana faɗin..

"It's a boy"!!daga haka yayi shiru,Hamida ce ta karɓi babyn hannun ta na rawa sannan ta maida idanun ta ga Dr inda ya share zufan fuskar sa ya sauke wata nannauyar ajiyar zuciya sannan cikin tsoron ganin reaction ɗin su ya ce
"Am sorry"!!bai ƙara furta wata kalmar ba Hamida ta fara ganin duhu ko kafin a yi wani yunƙuri har ta fara tanga tanga zata faɗi..

Ammy dake kusa da ita ne ta riƙo ta wacce gwiwar ta ya gama sanyi,ta fashe da kuka tana salati..
Saheeb couldn't say or do anything but zamewa ƙasa da ya yi ya haɗe kai da hannayen sa biyu..

Khalid kuwa shi ya karɓi babyn dan tuni Hamida ta sume,already Hajja ta tsinke da lamarin a zuci take nata kukan but tana salati a hnkl a bayyane..
#Mamuh*40*


  "She is in temporal comma,zata ɗau lkc kafin ta farfaɗo gabaɗaya so sai kun yi haƙuri da yanayin da ta shiga da kuma halin da zata cigaba da kasancewa a ciki for a while"!!..

  Wani irin sanyi ne ya ratsa zuciyar Ammy da Hajja har ma da Khalid dake riƙe da baby a hannun sa..
Shi kuwa gogan da tun ɗazu yake durƙushe bai ɗago ba bare ya ce ƙala yana dai sauraron yadda su Ammy da sauran ke hamdala amma bai iya ɗagowa ba har sai da ya ɗau lkc sannan ya miƙe tsaye ya taka a hnkl har inda likitan ke tsaye ya tsaya a gaban sa ƙeƙam a gaban likitan yayi folding hannayen sa a ƙirjin sa sannan ya ce da likitan
"Sake maimaita abinda ka ce"shi kuwa likita tunanin sa overwhelming sakamakon nasa ya saka Saheeb har yake son maimaicin amsar da ya faɗa mai..

Gyara position yayi ya maimaita ma Saheeb sakamakon surgery ɗin,kamar ƙiftawar ido Saheeb ya shaƙo sa ya haɗa sa da bango yana shaƙe masa wuya.

A tsorace Khalid ya hau kiran sa yayi da Hajja ke mai faɗar wani irin rashin hnkl ne wannan.
Bai saurari kowa ba dan zuciya ta ɗibe sa sai gurnani

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login