Showing 30001 words to 33000 words out of 101986 words

Chapter 11 - KAUNAR MU COMPLETE HAUSA NOVEL

MAMUGEE   

27 Sep 2024

15630

da shi bayan an ƙawata farfajiyar gidan da decorations wanda ya kasance adon royal blue aka yi amfani da shi dan su kan su amaren kalar kayan da suka saka kenan sai sauran ƴan uwa da abokan arziƙi da suka halarci event ɗin,su ma royal blue ɗin suka saka bambancin nasu da na amare shine na amaren an haɗe sa ne da off white head turban da aka masu ɗaurin sa sannan doguwar transparent designed net ɗin da aka ɗora masu saman asalin rigar jikin su ma ya kasance off white,takalman su da purse ɗin su duk off white,makeover aka masu sosai da ya fito da su..

Duk babu wanda zai gan su ya ce bai yaba da su ba,basu da kamanni dai amma da an gan su annga jini,ita Hamida in tayi murmushi gefe ɗaya dimple ɗin ta ya fito ita kuma Mufida in tayi murmushi duk two sides ɗin su bayyana..

A haka cikin kwanciyar hankali suka yi event ɗin su aka yi coverage da hotuna,masu selfie na ta yi ƴaƴan abokan mahaifin su Khalid duk sun taho sannan friends ɗin sa maza da mata sun zo wurin ciki har da close colleagues ɗin sa..

A fannin ammy Da zarar an yi tambayar ina amaryar Khalid sai a hau nuna ta su kuma su yi ta zuzuta kyawun ta dan dama ita ɗin mai kyau ce ko ba ado...

Lafiya ƙalau suka gama event ɗin aka koma cikin gida washegari ma aka yi bridal shower duk da ba su da friends amma close ones sun halarci event ɗin dan a jiya suka sami friends yawanci ƴaƴan abokan daddyn su da na mahaifin su khalid ne suka dawo bridal shower ɗin..

Dama in ka taho da kayan ka toh zaka cire a baka dress of the day da ya kasance mini peach chiffon inner da outer top ɗin sa kasancewar cikin ɗakin Ammy aka yi event ɗin kuma duk mata ne sai abin ya bada armashi nan ma haka aka yi aka gama..

Next day aka yi walimah da ya afku a cikin gidan kuma ya sami albarkar jama'a da dama dan marigayi mahaifin su Khalid ya tara jama'a sbd irin zaman kirkin da yayi da su,haka matayen abokan nasa ma suna mutunci da Ammy sosai Haka shima walimar aka yi aka gama sa lafiya

misalin 6pm daidai ana gama sa daidai Ameed da Meena suna shigowa cikin gidan,wani irin annashuwa fifi ta tsinci kan ta ciki wanda baya misaltuwa dan bata san har da Meena zata zo ba..
Welcoming nasu alka yi zuwa cikin gidan aka gabatar da su.

Duk wannan bidirin babu wanda ya kawo maganan zuwan angon Hamida wato marshall Muhammad Saheeb Maƙarfi,sai sha'anin biki kawai ake ta yi..

Hira sosai suka sha da Meena dan Ameed kam ya bi ayarin ango Khalid suna hira though basu san juna ba amma dalilin fifi sun saba..
*****

_Next morning_

Duk wata shiri irin ta musamman da ya dace a ma amare an zauna an ma su fifi da Hamida misalin ƙarfe goma ne dama ɗaurin auren sai Mufida ta rinƙa hirar ta da ɗaukar selfies tare da Meena da wasu dake ɗakin waɗanda ba zasu wuce sa'oin juna ba,in tayi wanda ya mata kyau sai ta turawa angon ta Khalid amma setaga kamar ma baiya bada hanklinsa sosai,
Hakura tayi daga baya tabarsa atunanin ta hidimar biki ne ya sha masa kai

Suna kan ɗaukar hotunan nasu aka fara shirye shiryen ɗaurin aure inda nan fifi ta bar duk wani abin da take yi ta riƙo hannun Meena ta natsu tana sauraron mallamin dake kan huɗubar sa da nasihohin sa har ya gama..

Sai a lokacin tasake duddubawa tana qoqarin Kiran wayar hameeda data bace Mata tun dazu Bata ganta ba Dama tanason ganinta Dan kebewa tayi Mata tambaya sbd ganin wani irin sauyib data tashi dashi a yau din na tsantsar yalwan farin ciki Dan zata iya cewa ta jima batagan hameeda cikin sakewa da annashuwaba kaman yau din.

Ɗan shiru ne ya biyo baya sai ta kalli Meena da tensed face sai Meena ta gyaɗa mata kai alamar it's all gonna be ok.. Karta damu

Bata gama tunanin ba sai ta ji gyarar murya a microphone sai a sannan ta sami relief ta yiwa Meena murmushi..

Ba a ɗau 3 seconds ba sai ta ji an kira sunan ta nan gaban ta ya faɗi sbd zaƙuwar da tayi ta ji an ce ta mallaki Khalid sai murmushi Meena ta mata
The next name that follows shine _Muhammad Saheeb Maƙarfi_..
Shiru tayi tana jiran jin a kira nata ango amma kuma sai me!?sai jiyo mallamin tayi yana faɗin
_"jama'a ayi hakuri Adakace mu"_..

Wani irin ras gaban mufida ya fadi
takalli meena
Tanason mgn saikuma takasa take ta ji kan ta ya sara kawai ta fara ganin dishi dishi bata ƙarasa jin yadda aka karasa wajen ɗaura auren ba ta koma ta mannu da bangon ɗakin idanun ta widely out tsaban fargaban da bata san mafarin sa ba

nan take hankulan matan ɗakin ya tashi banda mace ɗaya da yanzu ta shigo tana ce da su an dakatar da daurin aure kowa ya nitsu Mufida haka ta zauna shiru kamar statue babu uhm babu uhmuhm

Meena ce ta hau tambayar ya haka?
Wasu tambaya suke yi ko an sami akasi ne daga gun maɗaurin auren ko ya manta sunayen angwayen ne..

Matar nan dai na tsaye sai da surutur tayi yawa sai ta ɗan tsawatar masu ta ce
"Duk ku natsu,ina Hamida take?sai a yanzu aka fara waige waige inda Hamida take,nan hankula ya kuma tashi dan babu ita babu alamar ta..

Wata ce cikin masu duba Hamidar ta ce
"Mama ɗazu fah tana nan ana mata kwaliyya muna selfie tare da ita ina ta shiga"?gyaɗa kai matar tayi tana jinjina lamarin sannan ta ce

"Hamida da Khalid sun gudu,ba su gidan nan,ba su cikin anguwar nan kuma babu trace ɗin su"..

Babu wanda ya lura sai jin ƙarar faɗuwar mutum suka yi nan take aka juyo dan ganin wa ya faɗi,ko da suka juyo Mufida ce kwance a ƙasa kamar marar rai ga kwalliyar ta da ya shimfiɗu a saman fuskar ta ya mata kyau amma daga nesa kamar bata numfashi...
#Mamuh*_Mamuhgee_*

*14*

Rikicewa gidan biki yayi a nan waje maganganu aka rinka yi da masu tir da sigar da Hamida da Khalid suka ɗauka da masu tausayawa Mufida dan shagulgulan da aka yi a kwanakin bikin ya nuna irin ƙaunar da ke tsakanin Mufida da Khalid sai dai kuma yau da wannan abin ya faru,jama'a sun kasa bambance irin wannan lamari..

Kusan rabin ƴan biki sun fara tafiya saboda yadda bikin ya kasance akasin burin da aka dora a bikin amma yau da yake bikin ne sai abubuwa suka sauya.
An bar gidan biki da abubuwan al'ajabi wanda ake ganin ba a taba samin irin hakan a wuraren hausawa ba kamar yadda yake faruwa a wuraren kudu..

A sashen su Ammy kuwa haka Ammy ta rinƙa ji kamar ta saka kuka ba dan komai ba sai dan irin wannan abin maganar da Khalid ya bar mata because ba ta kan Hamida take ba duk laifin a yau ta alaƙanta sa ne da Khalid kuma abin na ran ta..

Hajja kan ta kasa taɓuka komai tayi murna ya koma ciki duk burin bikin takwarar tata kuma jikar ta abin ya wargaje,bambancin fushin ta da Ammy shine ita laifin Hamida take gani while Ammy ta ɗau zafi sosai akan Khalid kuma ta shirya mai..

Daddyn su fifi kuwa rasa abin faɗi yayi dan da a ce yau wata ce hakan ya faru da ita toh ba zai ji ciwo a ran sa kamar yadda yake tsananin jin ɓacin rai ba a yanzu da abin ya shafi rayuwar sa(Mufida kenan)..

Tun ana neman na haƙuri har aka zafafa abin tun safe har dare amma babu wani kyakyawar outcome.
  Ƴan sanda da jami'an tsaro duk sun shigo lamarin amma babu wani sakamako mai daɗi da aka samo..

Hankula duk sun tashi tsoron Ammy bai wuce kar wani abu ya faru da Hamida ba dan ita ce mace da ko da wani abin zai faru ita ce abin a tausayawa..

Matuƙa Ammy ta ɗau zafi hakan ne ma ya sa daddyn su fifi bai nuna nashi ɓacin ran ba gudun kar abin ya fi haka amma ba dan baya jin zafin abin a ran shi ba..

Da ɗai ɗai dama aka bar gidan bikin gidan ya dawo shiru babu hayaniyar kowa kamar ba gidan biki ba abin dai abin ban mamaki da tausayi. 
  Misalin 10pm daddyn su fifi ya sa aka tafi dubo masa ita dan tun faruwar abin ƙulle kan sa yayi a ɗaki yana ba kan sa laifin gazawar sa a uba,yana ganin kamar ya kasa samarwa ɗiyar sa rabin ran sa farincikin ta wanda tunda ta taso tun yarintar ta har kawo yanzu komai take nema sai ya tafi ya samo mata shi..
  Sai dai abin mamaki yadda ya gaza wurin samo mata farinciki mai daweamuwa har ƙarshen rayuwar ta...

Yana zaune a ɗakin sa yana ta tunanin yadda duniyar ta sauya masu su duka a cikin ƙanƙanin lokaci sai aka yi sallama wanda muryar Ammy ne.
Shigowa ɗakin tayi rungume da Mufida a jikin ta da duk ta fita hayyacin ta ta sauya kamanni kamar ba amaryar da few hours ta baza murmushi da annashuwa ba..
 
Kasa hada ido da ita daddyn su yayi sai kawar da kan sa gefe da yayi yana danne zuciyar sa dan kamar hawaye ne ke son ciko mai a idanun sa kuma ya san yana barin hawayen ya zubo toh fah zai kuma karyawa ɗiyar tasa gwiwa..

Suna ƙarasowa cikin ɗakin Ammy ta zaunar da ita sai ta bi Ammy da kallo idanun ta duk ya koɗr dan tun bayan faɗuwar da tayi aka yayyafa mata ruwa ta farka babu abin da ya mata daɗi sama da yin kuka kuma shi ta rinƙa yi har sai da ta ji kamar zuciyar ta na mata nauyi fiye da misali sannan ta ɗan sarara..

Girgiza mata kai Ammy tayi alamar ba tafiya zata yi ba tana nan tare da ita sannan ta saukar da kan ta ƙasa ta zauna shiru. 
  Zama kusa da ita Ammy tayi bata dai taɓa ta ba amma tana tsammanin faɗowar ta jikin ta da zarar hawayen ta sun fara zubowa..

Kusan mintuna goma suna zaune shiru,babu wanda ya tanka ko motsawa,sai chan daga bisani daddyn ya kira sunan ta a hankali.
"Mufida"!!kan ta na ƙasa amma sai da ta ji sunan har cikin zuciyar ta,take taji zuciyar ta ta karaya sabuwar kuka na son kufce mata amma dai ta danne ta amsa mai.
"Na'am daddy"!.shiru ya biyo baya sannan daddyn nasu ya daure ya hau yi mata nasiha akan yanayin rayuwa da yadda Allah ke tsarawa bawan sa rayuwar sa,duk tana sauraron sa tana tanƙwara zuciyar ta dan kar hawayen ta ya fito,amma maganar sa ta ƙarshe sai da ta karya mata zuciya har ta kasa haƙuri ta saki marayan kuka..
  "Kuma ki sani matar mutum ƙabarin sa,dan kin rasa Khalid ba kin rasa miji bane hakan na maki nuni ne da ba alkhairi bane a gare ki kuma wani wanda shine mafi alkhairi a gare ki na nan Allah zai haɗa ku"..
  Kuka sosai take yi bayan sauraron wannan kalamai nasa,bata san ta faɗo mai ba har tana maganganu cikin kukan nata ba sai da Ammy ta zo ta ɗaga ta ta rungume ta ai kuwa ta damƙe Ammy gam gam tana ta kuka yanzu ne ma take asalin kukan daga zuciyar ta sanin ta rasa Khalid kenan har abada dan ko bata san dalilin sa na gudun ta ba ta san tunda tare suka ɓace da Hamida a rana ɗaya toh ba ƙaramin abu bane kuma a ran ta bata jin son da yake mata na da ƙarfi because da yana da shi toh da ba zai ɓace a neme sa a rasa ba a rana mai albarka irin wannan ranar da ita da shi suka ɗau lokaci suna tsara sa ba...

Lura da daddyn su fifi da Ammy tayi kamar kuka zai yi sai ta janye ta suka bar ɗakin dan ita kan ta jarumtar ta ya ƙare ƙiris ya rage ta saki nata kukan dan wannan irin babbar embracement da Khalid ya saka ta ciki bata taɓa fuskantar sa ba..

A ɗakin Ammy haka fifi ta buɗe sabon babin kuka gwanin tausayi dan duk wanda ya kalle ta sai ya tausaya mata..
A haka tana kukan Ammy na rarrashi Hajja na zaune gefe rungume da ita bata sani ba bacci ya sace ta..

The next morning wuraren ƙarfen goma na safe sai ga mai gadin gidan ya shigo a guje kamar ya ga abin ƙi yana haki yana kallon Ammy dake zaune a kujerar dinning ita ɗaya tana tunanin fifi da kusan sau uku tana zabura cikin baccin ta jiya ƙarshe sai da aka kirawo family doctor ya zo ya duba ta cikin daren ya mata abin da ya dace sannan aka sami sukuni..

Kallon sa Ammy tayi ta tambayi lafiya,sai a sannan ya iya buɗe baki ya faɗa mata ai Khalid ne ya dawo yanzu tare da Hamida..
  Rass gaban Ammy ya bayar dan haka ta tashi ta wuce mai gadin ta nufi hanyar ƙofa ta leƙa ta ga su ɗin ne abin su..
  Dawowa ciki tayi da sauri ta nufi sashen Hajja ta faɗa mata abinda ke faruwa itama Hajja cikin tsinkewar zuciya ta tashi ta fito zuwa parlor..
  Daga ɗakin Hajja Ammy ta nufi ɗakin ƙanin ta daddyn su fifi ta ce da shi ya sauko zuwa parlorn ƙasa ga su Khalid nan sun dawo..
  Tashi yayi ya fito tana gaba yana bayan ta suka sauko ƙasan,step ɗin daddy na ƙarshe yayi daidai da shigowar su parlorn..
  Sai bai ƙarasa saukowa ba ya tsaya a nan last step ɗin ya ƙurawa Hamida ido yana nazarin ta yadda ta zamo so selfish..

Ammy kuwa bin su da ido kawai tayi tana jinjina kai dan ko ɗazu sai da aka kawo masu feedback akan fah ba a gan su ba ashe suna hanya...
  Tsayawa suma suka yi a tsakar parlorn ganin all eyes on them sai ya ja hannun Hamida ya maida ta bayan sa shi kuma ya fuskanci iyayen nasu..
  Riƙe hannun ta da yayi a idon Ammy da daddy sai gaban Ammy ya faɗi tsoro ya shige ta firgici ya rinƙa ziyartar ta akai akai..
  Suna tsaye kamar an dasa su Hamida na a bayan sa kan ta ƙasa shi kuma ya buɗi baki direct babu ɓuya ya ce
  "Ku yafe mana"!!wani dum gaban Ammy ya bayar dan bata yi tunanin abu mai kyau bane ya faru a tsakanin su ba..
  Babu wanda ya tanka masu sai Hajja dake zaune ce ta dube su ta ce
"Na me"!?sai ya kuma haɗo jarumta da tattaro qarfin hali da zare tsoro da kunyarsa sbd shine namiji Kuma shugaba sunyi alqawarin shine zaiyi bayani ba wani kwana kwana tunda dai sungama komadai menene. amsa kakar ta su yayi
  "Na gudun da muka yi,ku yafe mana"!!sai Hajja ta ji ran ta na kuma ɓaci a ce a shashancin namiji mace ta saka kan ta ciki..
"Gudun da kuka yi?me ya sa kuka dawo bayan kun zaɓi gudun"?tambayar da Hajja ta masu kenan wanda ya dirar masu ba tare da sun shirya ba sai Khalid ya ce
  "Mun dawo ne dan dalilin gudun namu ya riga ya gabata"!!turus Ammy tayi tana sauraron su yet Hajja ce ta kalle sa ta ce
  "Wani dalili kenan da ya gabata har ya sa kuka waiwayo daga gudun naku"?dama tambayar da yake so ya ji kenan sai ya ce
  "Auren mu,ni da Hamida"!!Ammy was like what??aure?shi da Hamida?wani irin madness ne wannan..
Kasa haɗa ido yayi da Ammyn nasa dan ya san tambayoyi da dama na yawo a zuciyar ta sai kawai ya hau bayani because ya san ko yayi shiru he owe them an explanation..

"Ammy,Hajja,Daddy ku yafe mana ba fushin ku muke so ba a yanzu,albarkar ku zai fiye mana dan in har babu albarkar ku auren nan namu da muka yi ba zai yi tasiri ba"!!dum gaban daddy da Ammy ya bayar jin wai har sun yi aure ba wai zasu yi ba but how??..

"Ni da Hamida mun gudu ne dan samarwa zukatan mu abin da muka daɗe muna muradi kuma shine auren junan mu ba auren mabambantar ra'ayoyin mu ba da aka zaɓar mana"!cutting nasa Ammy tayi a tsawace ta ce
  "Mabambantar ra'ayoyin ku da aka zaɓar maku,Mufidar ce ba ra'ayin ka ba"?shima a hanzarce ya maida mata da amsar
  "Yes Ammy,Mufida was never my choice,Hamida ce zaɓi na kuma ita na so tun asali"!!kan su ne ya ɗaure sai kawai Khalid ya cigaba da maganar sa
  "Eh Ammy,Hamida ce zaɓi na ba Mufida ba"wani tsawa Ammy ta daka mai but sai daddy ya dakatar da ita dan cin ribar zancen dan haka ta haƙura tayi shiru nan fah Khalid ya hau warware masu ai tun kafin su haɗu a ranar da su Hamida suka taho nan Nigeria shi ya riga da ya san ta kuma sun san juna haka suna soyayya toh da suka yi realising cewa su ɗin families ne sai abin ya ƙara ƙarfi dan haɗuwar su a wata experience ne da ita Hamidar ta tafi yi a ƙasar Cyprus sai suka haɗu toh shine suka ƙulla alaƙa wanda daga baya ya girma for almost a year,a ranar da suka haɗu kuma a airport sai basu sami damar bayyana kan su ba a matsayin waɗanda suka san juna ba,abu ɗaya da ya shiga tsakanin alaƙar su ta soyayya shine shigowar fifi rayuwar su,duk yadda fifi ta ɗau alaƙar tasu ba haka bane shi a wurin sa dan ya fi ɗaukaka relationship ɗin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login