Showing 24001 words to 27000 words out of 110331 words

Chapter 9 - MAWAHIB COMPLT HAUSA NOVEL

13 Sep 2024

19678

yana danna waya yadago yace"ya'akayi?"

Cikin damuwa Captain yace"magana zamuyi"

Mamaki yakama Ashraf,yadawo kusada Aryan ya zauna sannan yace"meyake faruwa? Ko wani abune yakema ciwo?"

Captain ya girgiza kansa yace"Ash...inada damuwa,narasa yanda zanyi inyi magana dasu Momy,but nayi maganar da Mamy, tace insameka muyi magana dakai sannan muje mufad'awa su Momy komai"

Ashraf yace"meyake faruwa? fadamin "

Cikin damuwa yace"Ash nifa anbani mace..."

cikin rashin damuwa Ashraf ysce"nasani ai,koba Asalamiyya ba?"

Captain yasaki dan qaramin tsaki sannan ya lumshe idonsa yabude yace"inama maganar serious kana min zancen wata Asalamiyya ni banma san yarinyar nan ba,Ina nufin inada aure Ash"

Cikin sauri Ashraf ya kalleshi yace"kana hayyacinka kuwa?"

Captain Aryan ya kalli Ashraf cikin damuwa yace"da gaske nake,anbani mace"

Cikin sauri Ashraf yace"to Aryan kode kafara shan wani abu ne bansani ba? tayaya zakace min kanada aure in yarda? yaushe kayi aure? kuma a'ina?"

Cikin sanyin jiki Captain Aryan yace"niba ni nayi ba,qaqaba min akayi,har yanzu bansan yaya yarinyar take ba,shi kansa wanda yamin auren bansan ko waye shiba"

Ashraf yace"mekake san cewa?"

Captain Aryan ya kwashe komai tun daga farko har qarshe ya fadawa Ashraf, sannan yaci gaba da cewa"bawai damuwar haihuwa ce tasa nake tunani ba Ash,wannan maganar auren ne,bansan ta'ina zan fara yiwa su Daddy maganar ba,nikuma gaskiya banda ra'ayin yin mata biyu,shiyasa nashiga damuwa,idan nayi shiru hakan yana nufin zasu sake daura min aure da Asalamiyya,bayan itama waccen yarinyar bansan yaya take ba,kaini yanda banason kowacce yarinya ma inde nasake had'uwa da mahaifinta banason damuwa gaskiya zan sakar masa 'yarsa...."(๐Ÿ™†๐Ÿปโ€โ™€๏ธ)

Lokaci daya gumi ya wanke fuskar Ashraf,cikin sauri yasaka hannunsa ya goge sannan ya doka tagumi hannu bibbiyu(๐Ÿ™‰)
Yayi shiru yakasa magana.

Captain Aryan yaci gaba fa fadin "kuma ni gaskiya bazan Iya tunkaran Momy da wannan maganar ba,kuma banason su sake liqa min wata yarinyar, gaba daya narasa yanda zanyi da raina,Ash... inaji araina dama banzo gida ba,kwata kwata wannan zuwan nawa bashida dadi,komai ya lalace min, kamar a film nake ganin komai yana faruwa akaina"
Ya qarasa maganar sannan shima yayi tagumi hannu bibbiyu kamar yanda Ashraf yayi.

Har zuwa lokacin Ashraf yayi shiru yakasa magana,shi kansa daba shine hakan tafaru dashi ba,gabansa faduwa yake, toshi kuma Aryan din yaya yakeji kenan?

Cikin rashin qwarin gwiwa Ashraf yace"tunani na yatsaya cak,bansan ma yaya zamuyi ba, amma abinda yafi kawai mu fadawa Daddy gobe,shidin yad'anfi Momy sauqi "

Captain Aryan yadaga kansa alamun amsawa sannan yasamu yacire tagumin da yayi yajuya ya kwanta tareda rufe idonsa badan yanajin baccin ba.


******


Washegari da safe daga Aryan har Ashraf babu wanda yaje part din Hajiya kilishi yin break fast, gaba dayansu suna zaune a dakinsu kowa yayi shiru, shi Captain yana zaune agefen gado yayi tagumi, shikuma Ashraf yana tsaye daga gefen window hannunsa harde a qirjinsa shima yayi shiru, Hajiya kilishi dataji shiru basuzo cin abinci ba saita hado musu komai tabiyosu dashi dakinsu,kai tsaye taturo qofar dakin tashigo, saita gansu kowa gabansa, kuma duk sunyi shiru, cikin mamaki tace"kukuma lafiya kuka zauna ad'aki ku kad'ai bakuzo kunci abinci ba?"

Ashraf ne yayi kokarin bata amsa yace"bamajin yunwa Momy"

Cikin mamaki ta kalleshi sannan tasake kallon Aryan, tace"ina ganin ikon Allah ni kilishi tome aka muku?"(๐Ÿ˜‚)

Yanzun ma Ashraf ne yabata amsa yace"babu komai..."

tata6e bakinta tace"cikinku..."

Tajuya ta kalli Aryan tace"kasha maganin kane?"

batare daya kalleta ba, yabata amsa a taqaice yace"nasha"

Kilishi tasaki ajiyar zuciya tace"wai saboda batun Asalamiyya ne kake ta wani d'aure fuska? to babana kadad'e baka d'aure fuska ba,dan aure babu fashi"

tajuya ta kalli Ashraf dayake tsaye har lokacin, tace"kada Allah yasa kuci abincin, kanku kuka yiwa "

tajuya ta fice daga dakin.

Tana fita Captain ya kalli Ashraf cikin shagwa6a yace"kanaji abinda Momy take fada ko?"

Ashraf yace"rabu da'ita, zamu fadawa Daddy ai"

shiru suka sake yi,kusan awa daya babu wanda ya kula abincin data kawo musu, kamar wasa Ashraf dayake tsaye jikin window yaga wani abokin Alqali yashigo gidan hannunsa daukeda goro,cikin mamaki yabude bakinsa zaiyi magana saiya ga Alqali yashigo shida wani maqocinsu da Alhaji khaleed mahaifin Nabiha, dakuma Alhaji Isah mijin Mamy, sai fara'ah sukeyi dukansu sunsha manyan kaya kamar yaune ranar d'aurin auren.

Cikin sauri yajuya ya kalli Aryan yace"Aryan sunzo,wallahi gasu Daddy can sun wuce part din Momy da goro,Ina tunanin fa ranar nan zasu saka, taso muje muyi musu bayani"

Cikin sauri Captain Aryan yatashi kamar wanda aka tsikare shi,Ashraf ya dauko masa riga da wando na qananun kaya yasaka, shikuwa Ashraf d'in jallabiya ce a jikinsa yau hankali ba'a kwance yakeba babu wanda yayi tunani saka kaya iri daya a cikinsu.(๐Ÿ˜‚)

Suna zuwa falon suka tararda iyayen nasu sun zazzauna sunata sake gaishe-gaishe,suma suka nemi waje suka zauna,Alqali yabisu da kallon mamaki, saide kafin yayi magana suka sake Jin wata sallamar, yan'uwan Hajiya kilishi ne sukazo wato dangin Asalamiyya,nan aka sake sabuwar gaisuwa,sannan kowa yayi shiru Ana jiran Alqali ya zartar da komai.

Alqali ya kalli yaran nasa yace"Ashraf meyake faruwa ne naganku anan?"

Daya daga cikin yan'uwan Hajiya kilishi yayi murmushi yace"Alhaji arabu dasu mana, suma ai zasu ga yanda akeyi ko?"

Alhaji khaleed ya kalli wanda yayi magana yace"zumudi ne da rashin haquri kawai irin nasu,mezai kawosu wajan saka ranar aurensu Alhaji Sammani?"

wanda aka kira da Alhaji sammani yayi murmushi yace"to Alhaji khaleed aida an qyale su,Asalamiyya ai 'yar gida ce....danma batason zumunci ne aida zaku dinga ganinta a gidan koda yaushe,shima angon aida bazaiyi d'okinta har hakaba...."(๐Ÿ˜‚๐Ÿ™Š)

Captain Aryan da yaji wannan furucin lokaci daya ransa yayi baqiqqirin,idan za'a kasheshi baimasan Yaya Asalamiyya takeba bare ace wai yana d'okinta,gaba daya maganganun nasu ma sai suka sake 6ata masa rai, cikin dakiya irin tasu ta sojoji yadago kansa ya Kalli Ashraf yace"Kafada musu"(๐Ÿ˜‚)

Shima Ashraf ya kalli Captain yace"A a,kaika fada musu"


Alhaji Isah yayi murmushi yace" yanbiyu meyake faruwa ne? kuyi magana mana"

Adede lokacin Hajiya kilishi takawo wa baqi ruwa da lemuka, anan taga ansaka Aryan da Ashraf agaba ana cewa suyi magana, cikin mamaki taja ta tsaya tanaso taga menene yake faruwa,dama tunda tagansu a dakinsu sunyi shiru tasan akwai abinda suke qullawa.

Ashraf da Aryan kuwa suna ganin Hajiya kilishi ta tsaya gaba dayansu sai suka sunkuyar da kansu, sunma kasa dago ido bare su kalli iyayen nasu.

Hajiya kilishi data gama tabbatar wa akwai abinda yaran suke 6oyewa, ta kalli su Alqali sannan ta kalli su Ashraf tace"ina ganin ikon Allah ni kilishi,toko kunzama kurame ne ana magana kunyi shiru?"

Alqali yazuba musu ido yana kallonsu,duk da bayason had'in auren Aryan da Asalamiyya fatansa daya kada Aryan ya kunyatashi agaban wad'annan mutane yace bayason Asalamiyya saboda tun ranar daya fada musu zai musu aure yake ganin take takensa.

Alhaji Isah yayi gyaran murya cikin sigar lallashi yace"Ashraf kaine babba fad'amin meyake faruwa? karka 6oye mana komai menene yake faruwa?"

Ashraf yadago kansa ya kalli Alqali sannan yayi qasa da kansa, yasosa qeyarsa yace"Uncle dama...dama Aryan ne yace kar asa ranar nan dashi, saboda shi yanada mata, kuma....."

Tun kafin Ashraf yagama magana gaba d'aya mutanan falon suka hada baki sukace "la'ila ha illallahu,Muhammadu rasulillahi"

Hajiya kilishi datake tsaye cikin sauri tazo tafara jijjiga kafadar Captain, cikin tsananin mamaki tace"Aryan...?"
Sannan tafara tafa hannayen ta tana sallallami.

Alhaji Isah yacire hular kansa yafara firfita da'ita, Alqali kuwa duk esin da yakeji afalon hakan bai hana yatashi tsaye yacire babbar rigarsa ba.


Alhaji khaleed ne yagoge gumin goshinsa ya kalli Captain da kansa yake qasa har lokacin yace" Aryan,meyasa kayi haka? yanzu muna iyayenka bamu Isa muyi ma aure ba saide kaje kayi auren sirri? menene ribar hakan? mu muna gida kullum muna fatan ace kasamu mace kayi aure ashe kai kayi auren ka mukake rainawa wayo?"

Cikin sanyin jiki Captain yace"Uncle wallahi bahaka bane,yanda kuke tunani bahaka abun yake ba,abinda yafaru shine tun ranar dana samu harbi mutumin daya kaini asbiti likita yayi masa bayanin rashin lafiya ta,shine shikuma yayanke hukunci yace ya d'auramin aure da yarsa tunda shine sanadin samun matsala ta.... "

Hajiya kilishi tanajin magana daga bakin mai ita tad'ora hannunta aka tasaki kuka, cikin ihun kuka tace"nikam nashiga uku na,ni kilishi Ina ganin ikon Allah,wanne marar mutuncin ne yayi maka aure babu saninmu Aryan?"

Alhaji sammani wakilin Asalamiyya ya kalli Hajiya kilishi yace"Kilishi kiyi shiru kidena wannan koke koken,ai shi bawa babu inda ya'isa yawuce qaddarar sa "

Yajuya ya kalli Captain Aryan yace"kai Aryan,yanzu Ina mutumin daya yi ma auren yake? kasan inda zamuje mu sameshi?"

Captain ya girgiza kansa alamun a a

Alhaji Isa mijin Mamy yace"wanne irin shirme ne wannan? bai nuna maka yarinyar ba kawai ya daurama aure yatafi?"

Captain Aryan ya kalleshi yace"ni har yanzu banga yarinyar ba,yabani katinsa de yace duk lokacin danake buqatar matata in kirashi..."


Alhaji Isa yace"to Alhamdulillah, yanzu Ina katin yake?"

Captain Aryan yatashi yafice daga falon, dukansu suka bishi da kallo, kai tsaye dakinsu yaje, cikin bed side drower dinsu yabude yadauko katin yazuba masa ido kamar yana ganin wani Abu ajikin katin, sannan yafuto daga dakin yakoma falo,har zuwa lokacin Hajiya kilishi tana zaune agefe tana goge hawaye, mazan falon kuwa kowa yayi shiru, kowa da abunda yake saqawa aransa

Haly JASHERU venture's,munada kayayyaki masu kyau da inganchi ba algus da ha'inci, kayanmu daga Ethiopian ne, prdct dinmu muna Ethiopian magic hair oil, anti dandruff shampoo serum, bdy cream, hand cream, magungunan chuttuka da na mata masu inganchi da qara lfy ajikin dan
adam ga number kmr hk 07046665338 ko 07061664264 munada distributor ako Ina afadin kasarnan da ketare muna koya harkokin kasuwnchinmu ga masu bukata akan 5000 kacal

sannan munada tsuntsaye na kasashen waje tattabaru game bukata ko koya akwai riba kwarai aharkar mebuqata yasiya koya koya seyanemeni a number na kamar haka 07046665338 ko 07061664264, ku antayo ayi tafiyar daku,yar'uwa kikoyi sana'ah akan wannan farashi me sauqi kema ki kafa kanki๐Ÿ’ƒ๐Ÿผ

***

Suna nan zaune har Captain yadawo.
Alhaji Isah ya dubi Aryan yace"bani katin "

Babu musu Captain Aryan yabashi katin, sannan ya zauna kusada Ashraf.

Alhaji Isa yadauko wayarsa yakira number Alhaji Ma'aruf, sannan yasaka wayar a amsa kuwwa yanda duka mutanan falon zasu ji abinda yake faruwa, wayar da farko qin shiga tayi, saida yasake kira a karo na biyu sannan tashiga, bugu uku kuwa yadauka tareda sallama, Alhaji Isah yace"muna magana dame wayar ne?"

Daga dayan 6angaren Alhaji Ma'aruf yace"eh nine,me wayar ne, dawa nake magana?"

Abba yace"kana magana ne da Alhaji Isah, daya daga cikin iyayen CAPTAIN ARYAN"

Alhaji Ma'aruf yanajin haka yatashi zaune tareda fadin "Alhamdulillah, Allah nagode maka,tun ranar da muka rabu da wannan yaron nake tunanin halin da yake ciki,kuma ni banyi azanci na kar6i number saba..."

Alhaji Isah yace"yanzu de ba wannan ba bawan Allah,muna nan zamu sakawa Aryan ranar aure sai yake fada mana wata magana, yace kayi masa aure,munyi mamaki tayaya zaka yiwa yaro aure batare da sanin mu iyayensa ba"

Alhaji Ma'aruf yace"wannna maganar bata waya bace Alhaji,tun ranar danabar Captain Aryan a asbiti nake zaune nake jiran ranar dazai kirani inzo har gida in roqi iyayensa gafara suyi haquri akan hukuncin dana yanke"

Alhaji Isah yace"ta tabbata de kayi masa auren kenan,yanzu Ina yarinyar take? ka tabbatar shi Aryan din yanason yarinyar ne kokuma kawai hadin aure ka'iya?"

Alhaji Ma'aruf yanajin wannan furucin jikinsa yayi sanyi, ya tabbatar kuma tabbas iyayen Aryan ransu ya6aci akan hakan,cikin sanyin jiki Alhaji Ma'aruf yace"to nide Ina mai sake baku haquri akan kuskure na, maganar yana sonta ko baya sonta kuma duk basu taso ba, nide daukan yarinyata nayi na bashi kyauta,kuma duk da bansan halin danku ba inada yaqinin zai riqemin yata tsakani da Allah"

Alqali dayake zaune dukansu sunajin yanda take kayawa tsakanin Alhaji Ma'aruf mahaifin Mawahib,dakuma Alhaji Isah wani mahaifin nata(๐Ÿ˜‚)
Alqali ya daga murya yace"isah kace dashi yazo shida yartasa munasan ganinsa"

Alhaji Isah yace"to idan babu damuwa kazo munasan ganinka tareda 'yartaka"

Daga dayan bangaren Alhaji Ma'aruf ya kalli Agogon dake daure a farar fatar hannunsa yace"yanzu karfe goma da rabi na safe,zanyi kokari nabiyo flight din dazai taso yanzu sainazo,kuna wanne gari?"

Abba yace"muna cikin garin kano"

Cikin mamaki Alhaji Ma'aruf yace"a a, ikon Allah, to ai itama yarinyar tana kano,kaga shikkenan takwana gidan sauqi,idan nazo saimu qarasa daku muje inbaku yarinya"

Cikin damuwa Abba yace"Okay yarinyar bata tare dakai kenan,tanada auren kabata iznin tafiya wani garin"

Jikin Alhaji Ma'aruf yayi sanyi,meyasa wanna mutumin yake gwa6a masa magana ne kamar akwai wani abu aqasa?๐Ÿค”
Yayi murmushin qarfin hali yace"gani nan zuwa"

Batare daya jira amsar Alhaji Isa ba yakashe wayar,kai tsaye wajan Abokinsa Alhaji Bala ya nufa,yafada masa abinda yake faruwa,daga nan suka wuce Airport domin tahowa kano, tun ahanyarsa ta tafiya Airport yake kiran Mamy,amma koda wasa bata dauki wayar ba, haka ya dinga kiranta har zuwa lokacin da jirgin su zai tashi sannan ya haqura da kiran.


******


"sister Maryam kina gani tun dazu ana kiranki amma kinqi dauka, kiyi haquri ki dauka mana ko marasa lafiya ne suke kira"

Mamy tayi ajiyar zuciya tace"Sister Bilkisa ba kowa bane yake kira Ma'aruf ne,me Ma'aruf zai fadamin? banason Jin muryarsa ko a mafarki"

Sister Bilkisa tayi murmushi tace"Sister Maryam nasanki da haquri amma bansan meyasa har yanzu kikaqi yafewa Ma'aruf ba,shekara nawa? yakamata ace komai yawuce, ki dauki wayarsa kiji dalilin kiran"

Cikin damuwa Mamy tace"bazaki ganeba,damuwar danake ciki ma ta'isheni basai nahada data Ma'aruf ba,mazajenmu sunacan agida suna kokarin saka ranar Mawahib dina da yaron Yaya kilishi,kwata kwata banason wannan hadin,bansan Yaya zanyi inhana faruwar hakan ba,amma muddin suka saka ranar nan to nima zan saka mana rana nida Mawahib saide su nememu surasa a gidan, maiduguri zamu tafi"

Sister Bilkisa tayi murmushi tace"kitafi kibar gidan aurenki saboda wata kilishi? haba Maryam karki bada matan maiduguri mana, kishiya bata koreki daga gidan miji ba sai wata can facala ce zata koreki? babu inda zakije zama daram a gidan Isah,ita de yarinya yanzu ne zaki samo mata hanyar guduwa, amma fa idan kinso"

Cikin mamaki Mamy tace"kamarya? mekike nufi?"

Sister Bilkisa tayi murmushi tace"kidauki wayar Ma'aruf kiji menene yake tafe dashi, daga nan kiji Ina yake da zama yanzu? dazaran yafada miki to ki hadawa Mawahib kayanta takoma wajan ubanta,hakan ai zaifi"

Mamy tayi shiruuu tana nazari akan maganar abokiyar aikin ta, sai can tace "kumafa hakane, ni kwata kwata ma bankawo wannan tunanin arainaba,saide Ina fatan ace zuwa yanzu Ma'aruf ya sauya halaiyarsa"

Tana gama wannan maganar ta kirashi,adede lokacin Alhaji Ma'aruf da Alhaji Bala saukarsu kenan a Airport din malam Aminu suna kokarin tare taxi,yana ganin kiran nata yayi sauri yadauka, cikin damuwa yace"Haba Maryam, me yayi zafi haka? amma ko babu yarinya a tsakanin mu ai zanci darajar kasancewata musulmi ki dauki wayata kiji abinda yake tafe dani ko? kinsan halin dana shiga saboda haka? Inda nasan gidan da kike aure wallahi da tuni kin ganni "

Cikin damuwa Mamy ta lumshe idonta sannan ta bude tace"Ma'aruf inajin ka meyafaru?"

Kai tsaye yace mata"ina Ruqayya? Inason ganinta"

Cikin mamaki tace"au dama kadamu da'ita ne?"

Alhaji Ma'aruf ya runtse idonsa, yace" Maryam, yanzu ba lokacin tone tone bane,inaso naga Ruqayya "

Mamy yace"Ina wajan aiki,Mawahib tana gida"

Alhaji Ma'aruf yacika da mamakin Mamy, har abada halinta mai kyau bazai canza ba,gashi de sunan mahaifiyar sa yarinyar taci, amma shi kai tsaye yake kiranta da sunan,amma gashi Maryam har wani suna daban tasaka mata,hakan yana nufin har yanzu tana ganin darajar mahaifiyar sa,tunda gashi ta kasa kiran sunan kai tsaye, yayi ajiyar zuciya yace"toki yi mata magana tahada kayanta gani nan zuwa"

Cikin mamaki Mamy tace"bangane ba"

Yace"idan mun hadu zanyi miki bayani,tahada kayan de zanzo har gida In dauketa"
Yana fadin haka yakashe wayar.

Sister Bilkisa tace"meyake faruwa kuma?"

Mamy tafada mata duk yanda sukai dashi, sister Bilkisa cikin mamaki tace"kode yaji labari ne za'a aurar masa da yarinya?"

Mamy yace"Ina zansani sister Bilkisa?amma bana tunanin haka gaskiya"

Sis Bilkisa tace"to ai zama bai ganki ba, ki kama hanya kije gidan, idan kunhadu dashi duk wacce za'a yi sai ayi"

Cikin sauri Mamy tace"to shikkenan"
Daga nan ta dauko jakarta, tacire dan qaramin hijab dinta na ma'aikatan asbiti, tasaka wani babban hijab me tsawo shima fari, sannan tanufo gida.



Haly JASHERU venture's,munada kayayyaki masu kyau da inganchi ba algus da ha'inci, kayanmu daga Ethiopian ne, prdct dinmu muna Ethiopian magic hair oil, anti dandruff shampoo serum, bdy cream, hand cream, magungunan chuttuka da na mata masu inganchi da qara lfy ajikin dan
adam ga number kmr hk 07046665338 ko 07061664264 munada distributor ako Ina afadin kasarnan da ketare muna koya harkokin kasuwnchinmu ga masu bukata akan 5000 kacal

sannan munada tsuntsaye na kasashen waje tattabaru game bukata ko koya akwai riba kwarai aharkar mebuqata yasiya koya koya seyanemeni a number na kamar haka 07046665338 ko 07061664264, ku antayo ayi tafiyar daku,yar'uwa kikoyi sana'ah akan wannan farashi me sauqi kema ki kafa kanki๐Ÿ’ƒ๐Ÿผ


******


Direban taxi yana zuwa inda aka yi masa kwatance ta waya yayi parking sannan yajuya ya kalli su Alhaji Ma'aruf yace
"Alhaji munzo"

Alhaji Ma'aruf yace"Okay nan suka kwatanta ma?"

Dan taxi yace"eh nan ne gidan Alqali"

Alhaji Bala yayi masa godia sannan yadauki kudi meyawa yabashi, bayan yatafi suka qarasa wajan Musa megadi Alhaji Ma'aruf yace"kashiga gidannan kace musu sunada baqi a waje"

Musa megadi yashiga ya'isar da saqon,nan take Alhaji khaleed mahaifin Nabiha yamiqe yabiyo Bayan Musa, yana zuwa ya gansu su biyu atsaye abakin get,yana ganin Alhaji Ma'aruf yaga kamar Mawahib atare dashi, Alhaji khaleed yamiqa musu hannu yace"baqin namu ne? sannunku da zuwa,ku qaraso mana,ku qaraso daga ciki..."

Alhaji Ma'aruf yace"to mungode"
Daga nan suka shigo cikin gidan, kai tsaye suka wuce part din Hajiya kilishi, har zuwa lokacin gaba dayansu suna nan a zaune,Hajiya kilishi kuwa takafa ta tsare tana so taga waye yayi mata katsalandan acikin rayuwar d'anta,Captain Aryan yana ganin Alhaji Ma'aruf yasaki wata irin ajiyar zuciya,Alhaji Ma'aruf kuwa cikin fara'ah yafara bawa duka mazan falon hannu suna gaisa wa, sannan ya zauna yamaida kallonsa ga Alqali ganin shine babba a cikinsu, yace"Alhaji kuyi haquri nasaku kuna jirana,ni Sunana Alhaji Ma'aruf,dan asalin jigar Kebbi,kuma nine wanda na aurawa 'yata Captain Aryan bisa shaidu da wakilai kamar yanda addini ya tsara,amma nayi hakanne badon komai ba saidon ganin nine silar dayasa yaron nan yashiga matsala,kuma inada tabbacin yata batazata ta6a yimasa gori akan batun haihuwa ba,amma...ina roqon ku da kuyi haquri kuyafemin, haqiqa nasan nayi kuskure,sannan yarinya ta na bashi ita halak malak, saide in shine yaga bata yi masa ba to zai Iya sauwake mata,amma amatsayina namai laifi Ina qara baku haquri amatsayin ku na iyayensa,idan har baku haqura ba to duk hukuncin dazaku min kuyimin inde zaku huce akan abinda na muku"

Alqali yayi shiru yanajin dogon bayanin da Alhaji Ma'aruf yayi,gaba daya sai jikinsa yayi sanyi,ada yayi niyyar yashiga qara tareda duk wanda yayiwa dansa aure ba tareda saninsa ba,amma bayan yaji bayanan mutumin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login