Showing 33001 words to 36000 words out of 110331 words
haqura nadena kiranta,har kawo wannan lokacin Ina Nan Ina sana'ah ta tafashi da mamaki nariga nazama shugaba, kwanaki munje gidan wani Alhaji munyi masa fashi ban biya yarana kudin da suke so ba, wannan dalilin ne yasa suka hademin kai suka kawomin hari zasu kasheni, shikuma Captain Aryan yatemake ni, tunda naga dan mutane yana qoqarin rasa ransa akaina, daga ranar nayi tir da halina,naji na tsani kaina saboda Koda nake harkar fashi na niban yarda da kisan kai ba, bayan nabar asbiti naje duk wata dukiyata da nasan cewa ta fashi ce nakaita gidan marayu, gidan da zan'iya tunawa Kuma Natura musu kudin su tareda neman yafiyar su,a yanzu na daina wannan dabi'ar ta sanadin danku,sanadin danku na shiryu nazama nagari, yanzu Iya kudina na halak nake rayuwata dashi,wannan dalilin yasa ban nemi Ruqayya ba, saboda ban Dena fashi ba, idan na nemeta da haramun din zanci gaba da ciyar da'ita, Kuma nasan Maryam batason haka,yanzu da ubangiji ya nufeni da shiryuwa gashi nazo har gida na nemi yata amatsayinta na matar aure"
Dukkannin mutanan falon sukai shiruuuu Bayan sungama jin dalilin mutuwar auren Mamy,wannan ne dalilin dayasa taqi nuna musu mahaifin Mawahib kenan tsawon wannan lokacin.
Alkali yayi ajiyar zuciya yace"ikon Allah,Allah Mai yadda yaso,Allah de ya nufa Kaine zaka haifi Mawahib ba qanina ba, saboda auren ta na farko anan gidan muke da'ita,muna Zaman mu yau dadi gobe babu dadi Har na fitar da Ashraf da Aryan qasar waje karatu, to a wannan lokacin ne suka samu matsala da me dakina kilishi,alokacin Bana Gari munje meeting din Alqalai Abuja,to maganar gaskiya ni kaina shedane Maryam tanada haquri, to ranar ankaita maqura hakan yasa taciwa matata mutunci tarama abinda aka mata, to daga Nan qanina Alhaji Isah yamata saki daya,a ranar tabar gidan Nan tatafi maiduguri,Bayan nadawo nasamu labari nayiwa Isah wankin babban bargo, nasashi agaba mukaje maiduguri, muka basu haquri, sai mahaifanta suka bamu haquri cewa bazata koma ba, haka muka dawo gida duk jikin Isah yayi sanyi,Bayan tsawon watanni bamuji labarin taba,sai daga baya suka sake haduwa da Isah anan yaganta da yarinya, tafada masa tayi aure amma sun rabu da mijin,anan Isah ya nuna yanason tadawo dakinta saboda tsawon wannan lokacin bai sake aure ba,Maryam tace bazata aure shi tabar yarinyar taba, shikuma yayi mata alqawari zai riqe yarinyar kamar yarsa ta cikinsa, Isah ya sameni da maganar Nima na amince, to wannan ne dalilin dawowar ta gidan Alqali Akaro na biyu,gata han har yanzu muna tare"
Alhaji Ma'aruf yace"ikon Allah,dama can Allah ya qaddara saboda samun Ruqayya ne yasa tashigo cikin rayuwata ba"
Yajuya ya Kalli Mamy da kanta yake qasa yace"Maryam kiyi haquri, ki yafemin, sannan akwai kadarorinta dasuke wajena wanda nasiya mata da kudina na halak dakuma Wanda mahaifiya ta tabata kafin tamutu, idan komai ya Lafa zanje Abuja muyi magana da'ita, amma Dan girman Allah ki yafemin ki manta baya"
Mamy batace masa uffan ba, sai Abba ne yayi ajiyar zuciya yace"babu damuwa Alhaji Ma'aruf, Allah yayafe mana baki daya"
Gaba daya falon suka amsa da "Amin"
Daga Nan sukai shirin tafiya, suka sake musabahar rabuwa, gaba dayansu mazan suka futo domin yimusu rakiya, Mamy Kuma ta wuce part dinta, suna zuwa get nafarko adede lokacin direban dayakaisu Mawahib Airport yadawo, Alqali yasashi yasake daukansu Alhaji Ma'aruf suma yakai su Airport din domin tafiyar su jihar Kebbi.
******
Acikin jirgi suna zaune hankalin Captain yanakan window,tunani yake aransa yanzu shine aka hadashi da wannan jaririyar,shikkenan daga taimako taimako yazame masa masifa,?
Yatuna lokacin da suke zancen aurensu shida Ashraf har yana fadawa Ashraf cewa tayaya ne zaiyi aure baiyi komai ba a wannan ranar kamar wani kidahumi?
Shide yasan bazai ta6a neman wannan yarinyar da sunan mu'amular aure ba,ba ajinsa bace,bazai ta6a sunkuyar da kansa awajanta ba har abada bare har hakan yakaisu ga wata mu'amula ta aure,yanzu ta tabbata Kenan shine kidahumin,tunda gashi ga matar tasa amma saide kallo.
Wata zuciyar tace dashi idan hakan tafaru ma aiba haihuwa zakayi ba,saikasha magani sannan ne zaka gwada ko Allah zai baka haihuwar,idan kuwa saboda Mawahib zaisha magani gara ya tabbata babu haihuwa.(ππ»ββοΈ)
kukan datake ne yadawo dashi daga dogon tunanin daya Lula,cikin tsawa yajuyo ya kalleta yace"kokimin shiru kona wanka miki mari...stupid"
Tsit,Mawahib tayi shiru, ita kanta jitayi ta nemi kukan tarasa Sai jikinta dayake karkarwa saboda tsawar daya mata.
Wanda yake zaune agaban kujerarsu yaji tsawar tayi yawa hakan yasa yajuyo ya kallesu, to ganin suna kama hakan ya tabbatar masa da cewa may be qanwar sace,danhaka baice komai ba Yajuya yaci gaba da karatun jaridarsa.
Suna sauka tabiyoshi abaya idanunta harsun fara kumbura saboda kuka,yana hango Sojojin dasuke jiran saukar sa kamar yanda ya musu text Yafada musu yanufi inda suke,suma suna ganinsa suka Sara masa, daya daga cikinsu yayi sauri yabude masa motar,ganinsa tareda mace yasa itama suka bude mata daya gefen tashiga,mamaki ya kamasu ganin ogan nasu tareda mace,Kuma tafiyar tasu kamar babu Shiri,babu jaka babu kwalliya gashi fuskar ogan nasu a daure, basu ga yana fara'ah ba bare a tambayeshi aji ko sunyi suruka ne.
Ahanya ma baice dasu uffan ba,sojan dayake Jan motar ne ya kalli Captain ta madubi yaga fuskarsa a daure yana kallon gefen titi, Yajuya yaga Mawahib itama kanta yana kan window, wannan ne Karon farko da tazo Abuja,amma tashin hankali yahanata kallon garin yanda ya kamata,Sojan ya daure yayi gyaran murya sannan ya Kalli Captain Aryan yace"Oga zamu wuce barrek ne kokuma muwuce gidanka?"
Saida yayi maganar gida sannan Yatuna lokacin dasuke fira da Ashraf yana nuna masa hadaddan gidan daya gina Har yana cewa yaso ace da matarsa zasu fara shiga,meyasa qaddarar sa take zuwa masa ajuye? meyasa yanda ya tsara rayuwar sa Bata zuwa masa daidai? yanzu duk yanda yakeji da sabon gidan Nan nasa hakan yana nufin tareda Mawahib zasu fara shiga Kenan? gashi ya debe komai nasa daga barek yamaida gidansa Dama yanda ya tsara shine yana dawowa yasauka asabon gidansa, cikin taqaici kamar Wanda aka qwato maganar daga bakinsa yace"gida"
Sojan da yayi masa tambayar Wanda harya fidda rai zai samu amsa cikin sauri Yajuya kan motar suka nufi sabon gidan Captain Aryan.
Dayan Sojan dayake zaune a kujerar me Zaman banza shine ya turawa wasu daga cikin Sojojin su text,sannan yamaida wayarsa cikin aljihunsa.
Suna zuwa gidan kuwa Mawahib taga sojoji ta ko'ina,shi kansa Captain Aryan yayi mamakin ganinsu, daga baya saiya gane aikin Sojojin dasuka dauko shi ne, tundaga Compound zaka tabbatar ba qaramin kudi aka kashewa gidan ba,gidane ginan zamani kamar an dauko shi andora a wajan,ginin beni ne sama da qasa,anyi masa farin fenti, daga qasa akayi wata yar qaramar ma'adanar motoci,manya manyan motocinsa guda uku kowacce tana adane aciki, duka windows din gidan brown color ne, daga Saman Benin akwai wani waje kamar balcony ansaka wasu kujeru na hutawa a wajan,motarsu tana tsayawa ya futo, ganin tare yake da mace yasa wani yayi saurin Bude mata motar, gaba dayansu cikin girmamawa suke gaida shi, saikuma abokan aikinsa Wanda matsayin su dayane sune suke dan tattauna wa tareda yimasa addu'ar kiyaye wa gaba, dangane da harbin da'aka masa, dayawa daga cikinsu Sai satar kallon Mawahib suke wadda take tsaye ajikin motar kana ganinta kasan a tsorace take, tunda take Bata ta6a ganinta cikin sojoji haka ba,to sunriga sunsan cewa Captain Aryan shiba ma'abocin kula yanmata bane,mata dayawa suna tatashi amma shi kokadan baya kulasu, Kuma sude basuji labarin yayi aure ba bare suce, Kuma baitaba zuwa da qanwar sa gidan ba,gashi fuska a daure babu damar tambaya(π)
Wani Captain Ilyas ne yayi qasa da muryarsa sannan yace masa"munyi Amarya ne?"
Kai tsaye yace masa"hakane"
Daga haka babu qari, yawuce cikin gida,shikuma Captain ilyas yakoma yafadawa sauran, nan da Nan labari ya watsu Captain Aryan yayi aure.
Yana shiga gidan itama ta doru abayansa,babbar qofa ce tashiga falon,suna shiga taci karo dawani babban madubi abakin qofar,dawani table agabansa ansaka flowers agabansa anyi ado dashi, Sai sauran falon an qawata shi da wasu kujeru Masu launin brown,gawata Uwar plasma agefe, Sai kitchen da dinning table maicin mutum hudu,falon yayi kyau sosai bnda wannan kitchen din babu wani daki aqasa,daga bakin qofar shigowar falon akwai matakalar beni wacce Bata wuce Hawa goma ba,kowanne step guda daya akwai glop din wuta daga fuskarsa ba wajan da zaka taka dinba, daga fuskarsa anan aka jerasu Kuma kowanne akwai Haske Mai daukar hankali a jikinsa, kana gama Hawa daga hannun hagu akwai dakuna guda biyu ajere, Sai dan qaramin falo Wanda aka qawatashi da kujeru Masu kyau, da fridge aciki dakuma kayan kallo amma bekai na falon girma ba, daga falon ne zaka fita zuwa balcony ta yanda zaka dinga ganin gidan gaba dayansa ta Sama, daga bangaren hannun Dama anan dakin oga kwata kwata yake,duka dakunan akwai kayan amfani aciki, kawai kayan sakawa ne babu,gini ne madaidai ci ginin dan Boko mecin mace daya, suna shigowa yahaye sama yabarta a falon qasa,Mawahib tagama qarewa falon kallo yanzu anan Yaya Captain yake rayuwa kamar ba'a Nigeria ba? Shiyasa yakejin kansa kamar shiyafi kowa yadauki girman Kai ya dorawa kansa? Ahankali tasamu daya daga cikin kujerun falon ta raku6e aciki,ta dauki lokaci Mai tsawo anan falon, taga alamun maigidan bazai Mata nuni da makwanci ba, ahankali tatashi tafara hawa matakalar benin hartaje takama handle din dakinsa zata bude Sai taji alamun yana magana awaya, cikin sauri tacire hannunta, takoma dakin dayake hannun hagu, tana turawa yabude, babu tunanin komai kawai tafada ciki tareda rufowa,zama tayi akan gadon tareda tagumi hannu bibbiyu
Haly JASHERU venture's,munada kayayyaki masu kyau da inganchi ba algus da ha'inci, kayanmu daga Ethiopian ne, prdct dinmu muna Ethiopian magic hair oil, anti dandruff shampoo serum, bdy cream, hand cream, magungunan chuttuka da na mata masu inganchi da qara lfy ajikin dan
adam ga number kmr hk 07046665338 ko 07061664264 munada distributor ako Ina afadin kasarnan da ketare muna koya harkokin kasuwnchinmu ga masu bukata akan 5000 kacal
sannan munada tsuntsaye na kasashen waje tattabaru game bukata ko koya akwai riba kwarai aharkar mebuqata yasiya koya koya seyanemeni a number na kamar haka 07046665338 ko 07061664264, ku antayo ayi tafiyar daku,yar'uwa kikoyi sana'ah akan wannan farashi me sauqi kema ki kafa kankiππΌ
******
"Maryam kidena kukan nan haka,farinciki zakiyi Allah yayi auren yarki,Kuma tasamu miji kamili Mai kwarjini Wanda kowacce uwa tagari zatayi fatan ace shine mijin yarta"
Cikin shashshekar kuka Mamy tace"bahaka bane Anty,naci buri sosai Akan auren Mawahib,meyasa Ma'aruf zaimin haka? nasha wahalar yarinya haka kawai yazo yadauketa yabada ita inda banaso? niba haka naso aurenta ya kasance ba,banaso tayi rayuwa irin wacce nayi,nafiso taje tayi aurenta hankalin ta ya kwanta kamar kowacce yarinya"
Daga dayan bangaren Auntyn tace"to Yaya zakiyi da qudurar Allah Maryam? Ki kwantar da hankalin ki kiyi mata Addu'ah Dan Allah, karki biyewa facala kudinga tashin hankali kamar bakusan tauhidi ba,Dan Allah na roqeki kiso auren Nan, Kuma kiyi mata Addu'ah insha Allah watarana Sai kinyi alfahri da auren Mawahib"
Mamy ta share hawayen idonta tace"to shikkenan Aunty, nagode, insha Allah zanyi yanda kikace "
"yawwa Maryam haka nake sonki, Allah yayi miki Albarka"
Bayan sungama wayar mama Sadiya datake gefe tace"ni bansan meyake faruwa ba,saida Alhaji Yamin waya inkai musu abinci sannan naji yace ansaka ranar Ashraf da Nabiha,harga Allah nide banason hadin Nan, banason tashin hankali, tunda Yaya kilishi ta nuna bataso hankali na yaqi kwanciya da hadin"
Mamy da idonta yayi jajir tace"ai yaran nata basuda laifi,sunada kyakykywan hali,Nima ita nafiji,ita din mahaifiyar suce, zata Iya basu kowanne umarni akan matan su"
Mama Sadiya tace"to saide muyi haquri Maryam,ya zakayi da hukuncin Allah? Idan kace lalle lalle baza'a yi ba zaka Iya mutuwa Kuma qarshe ayi auren,yanzu ita data dage Ashraf bazai auri Mawahib ba, ba gashinan abun Yaqare Akan dan lelentaba, aiko da wasa batayi tunanin abun zai juye hakaba,dazu Naga likita yashiga part din nata, saida na tambayi baban Nabiha Sai yake cemin itace zazza6i ya rufeta"(π³πππ»ββοΈ)
Mamy tace"Allah yabata lafiya,dazu Yaya khaleed yacemin na shirya zamuje can Abujan,zakije kine kema?"
Mama Sadiya tace"yafadamin Nima, amma bandani aka shirya tafiyar,inajin muma saidaga baya zamuje, Dan Allah Maryam idan kinje, ki taushi Mawahib sosai,tariqe mijin ta tamasa biyaiya karta Bawa mahaifinta kunya"
Cikin damuwa Mamy tace"to Maman Nabiha insha Allahu"
******
Har dare babu Wanda yasake saka dan'uwan sa a'idonsa,baisan a halin datake ciki ba, yana kwance agadon sa yana waya da Ashraf,yana Sanye cikin rigar wanka fara qal, wadda tsawonta bai wuce Iya gwiwar saba.
Cikin damuwa Ashraf yace"ya hanya"
Captain Aryan yace"lafiya,bayan munzo saida nafita wajan aiki, sannan nadawo, yanzu nede na kwanta"
Ashraf yayi ajiyar zuciya yace"yajikinka? Ciwon dasauqi ko?"
"dasauqi sosai,banajin ciwon komai,but duk da haka zan dan huta na kwana biyu kafin nafara aiki"
Ashraf yace"zaka huta ko zakayi amarci?"
Cikin sauri ya Runtse idonsa Kai tsaye yace"Ash.... zan saki yarinyar nan,bazan Iya zama da'ita ba"
Ashraf yace"kayi dace da mace tagari, meyasa zakace zaka sake ta?saboda me?"
Cikin shagwa6a yace" Ash Banasonta,ni bazan Iya hada Shimfida da'ita ba,neman maganin ma nafasa,wallahi gara in zauna haka,sannan kaima kana sonta,meyasa ni zan zauna da'ita?"
Ashraf ya lumshe idonsa yabude yace"kadena damuwa dani,dama ni nasaba,saina Samo mace saika qwace,yanzu ma gashinan...dama ai kace inde kana Raye ban'isa in aure taba hakane?"
Cikin sauri yace"Ash...,kadena tunamin please,banason maganar yarinyar nan"
Ashraf yayi murmushi yace"nabar ma ita har abada Aryan,tanada kyawawan halaye nasan duk daren dadewa zakasota, Wai Nima Bayan kuntafi Daddy yace zai bani wannan Nabihan nanda sati biyar "
Captain Aryan yatashi zaune yace"wai Dan Allah meyasa su Daddy suke so su dinga janyo mana raini a wajan yaran nanne? Ita wannan yarinyar zata Iya kulawa dakai ne?"
Ashraf yace"takula dawa? Idan nazauna da'ita Kenan,kakira Momy kayi mata sannu, batajin dadi tana zazza6i"
Captain Aryan yace"innalillah, bari inkira ta"
Yana kashe wayar yafara neman layin Hajiya kilishi,saide harya gama yimata 5 missed call kosau daya bata dauka ba, haka ya kwanta cikeda damuwa.
******
Misalin qarfe daya na rana suna zaune a gaban Alhaji khaleed da Alhaji Isah Wanda suka zo gidan bisa jagorancin Captain Aryan,dagashi har Mawahib wadda idonta yake cikeda hawaye ganin Mamy dukansu suna zaune sunajin yanda Alhaji khaleed yake musu fada akan haquri dakuma Zaman lafiya,Mamy Kuma tana daukan jakankunan kayan Mawahib tana Hawa mata dasu Sama,tanajin duk fadan da ake musu, babu buqatar ta zauna tatofa albarkacin bakinta, duk wani Abu dazata fada musu Alhaji Isah da Alhaji khaleed sun fada musu, shiyasa ta maida hankalinta wajan Hawa da kayan Mawahib Sama,duka kayanta Mamy tahado mata shi, daga manyan kaya irinsu atamfofi, Har dogayen rigunan datake yawan amfani dasu, dakuma qananun kayanta nashan is'ka, Sai fici-ficin kayan baccin ta, babu abinda tabar mata agida, tariga ta kar6i qaddara da hannu bibbiyu,zata yiwa yarta fatan Alkhairi da Addu'ar Zaman lafiya itada mijin ta.
Bayan takai mata kayan tadawo falo ta zauna,a lokacin angama yimusu Nasihar,Captain yafita yayo musu takeaway na abinci, sukaci suka qoshi, sannan sukai shirin tafiya,mazan sukai gaba sukabar Mamy da Mawahib abaya ko zasuyi wata maganar,Mawahib tana ganin sun tafi tasake rungume Mamy, cikin rawar murya tace"Mamy Bana sonsa,wallahi tsoron sa nakeji Mamy zai kasheni"
Mamy tasake rungume ta tace"kiyi hakuri Mawahib,ko baki ji fadan da Abban ki yagama yimuku ba yanzu? kiyi shiru kidena kuka babu abinda zai miki kinji?"
Cikin sauri ta goge hawayen idonta sannan tadagawa Mamy kanta alamun amsawa, Mamy tace" idan kin duba kayanki zakiga wani magani aciki, kidinga Sha kullum karki yi wasa dashi,akwai turare zaki ganshi a kwalba kidinga shafawa kullum da daddare idan zaki kwanta"
Saida ta share hawayen idonta sannan tace"to Mamy" yarinta tasa kwata kwata Bata gane menene amfanin abubuwan da Mamy din tace ta dinga amfani dasu ba.
Futowa sukai tarakota har gaban Mota, tana ganin shigar Mamy Mota tajuyo da gudu tana kuka tadawo cikin gidan.
Saida sukaje Airport zasuyi sallama dashi Mamy tace"Captain nasan bakason auren Nan, kayi haquri, Kuma ka dinga haquri da shirman da Mawahib zata dinga yima,yarinya ce Batasan wani abun ba,idan tayi ba daidai ba kayi mata hukuncin daya dace"
Captain Aryan bai Iya cewa Mamy komai ba, Sai kansa daya sunkuyar kawai,shi kansa yana buqatar ace Mamyn ta rungumeshi, ta lallashe shi.(πππ»ββοΈπ)
Amma yanzu gaba dayama Yakasa sakewa da'ita,yakasa kallonta, tazama kamar wata baquwar sa.
tun Bayan tafiyar su Mamy gidan yayi shiru bakajin motsin kowa,tana zaune a dakinta batada aiki Sai tunani, ga wayarta nan agefe amma batada sukunin daukar wayar harta dinga dannawa, haka suka wuni ranar babu Wanda yasake saka kowa a idonsu har dare,Kuma Har lokacin Mawahib bataci komai ba, rabon ta da abinci tun akano,yau kwana daya Kenan, dazu daya siyowa su Mamy Koda wasa bataci ba, saboda ba tajin dandano a bakinta,Shima Captain yana dakinsa, Bayan tafiyar su Mamy ma haka ya dinga Kiran Hajiya kilishi amma Bata dauki wayarsa ba, haka yaja Computer sa ya kunna yana ganin ayyukan office ko hakan zai rage masa tunani,Washegari ma haka suka wuni babu Wanda yaga kowa, gidan tsit bakajin motsin kowa, yauma wuni tayi tana kuka, gaba daya ta kasa sakewa a gidan.
A 6angaren Captain kuwa gaba daya ya manta da Mawahib,rayuwarsa yake kansa tsaye, kasance war baya ganinta yasa shaf ya manta da wata halitta a gidan,damuwa ta masa yawa Kuma babu Wanda zai jashi ajiki bare yaji damuwarsa ya lallasheshi,kana ganinsa zakasan hankalinsa ba'a kwance yakeba saboda rashin daukan wayarsa da Hajiya kilishi taqi yi,bayason ya fadawa Ashraf Sai Shima yashiga damuwar.
Da daddare yayi shirin bacci wajan shadaya da rabi nadare,yana Sanye cikin kayan bacci Riga da wando, rigar yar qarama ce mai gajeren hannu,wandon Kuma dukansa iyakarsa Rabin cinyarsa,farar fatar jikinsa tayi fresh Sai sheqi take, qasa-qasa yakejin kuka yana tashi,mamaki ya kamashi waye a gidan har ake masa kuka da wannan Daren?
Cikin sauri yabude dakinsa Yafuto, yana futowa dayaji daga inda kukan yake tashi saiya tsaya yayi turus tareda dafe kansa da hannunsa, kwata kwata ya manta da yarinyar nan.
Fuskar nan tasa adaure ko alamar annuri babu haka yatura kansa cikin dakin, anan bakin qofar dakin yaci karo da'ita, yatsaya Yazuba mata ido hannayen sa duka biyun suna zube cikin aljihun dan qaramin wandon baccin dake jikinsa,tana zaune ta dora kanta Akan cinyarta tana kuka, abayar jikinta ce tun wacce tazo da'ita gidan Bata sauya wani kayan ba,dakin ya qarewa kallo yaga babu abinda tayi amfani dashi kayanta da Mamy tashigo mata dashi yana Nan inda ta ajiye mata su da alamun Bata Bude kayan ba, saida yagama qare mata kallo sannan yayi ajiyar zuciya