Showing 102001 words to 105000 words out of 110331 words

Chapter 35 - MAWAHIB COMPLT HAUSA NOVEL

13 Sep 2024

19697

kikaga yamutu kwanan sa ne yaqare Honey"

Wani hawayen ne yasake zubo mata tace"to meyasa zaka min cikin yanbiyu, bayan Nabiha ta fadamin guda daya ma qafar mutum daya lahira daya tana duniya"

Hannunta yasaki yasake matsowa yariqe fuskarta yace"Honey toni tayaya zansan namiki cikin yanbiyu ko dan daya? idan Allah yayi kowacce haihuwa yanbiyu zaki dinga haifomin Yaya zanyi ni?"

Tanajin haka tasake fashewa da kuka, ahankali yasaka harshensa yafara lashe mata hawayen tundaga kumatunta har idonta, sannan yahade bakinsu waje daya, saide har lokacin hawayen take zubarwa, ahankali yadago kansa ya kalleta sannan yazare bakinsa daga nata yace"menene matsalar kuma?"

Cikin kuka tace"ni tsoron haihuwa nake"

Cikin kwantar da hankali yace"zaki haihu lafiya kinji? insha Allah Allah yana tare damu yanda Momy ta haife mu lafiya nida Ash kema haka zaki haifomin sababbin Ashraf da Aryan kinji?"

Ajiyar zuciya ta sauke sannan ta goge hawayen idonta,yasake kallonta yace" shikkenan komai yawuce?"

Dago idonta tayi ta kalli wata bishiyar mangoro agefensu reshen bishiyar duk ya sakko qasa, tace" ni mangoro zansha"

Cikin sauri yace"shikkenan muje Super market kidebi duk yanda ya miki"

Cikin shagwa6a tace"ni wannan danyen nakeso"

Kallon bishiyar yayi yace"Honey danyan mangoro kuma? kinsan zaki nemi danyan mangoro meyasa tun kafin muyi aure bazaki fadamin ba ashuka miki acikin gidanki?"

Cikin shagwa6a tace" to kafin muyi auren baka tsaneni ba"

Cikin sauri yace"kinga, toya Isa,nina manta, basai kinmin wani tone tone ba, bari inciro miki"

Yafice daga Motar tana kallonsa ya dinga ciro mata mangoron sannan yadawo yabata, yashiga yaja motar suka tafi gida.

Suna zuwa gida suka zauna afalo yadauke mangoron yaje ya wanko mata su ganin zata faraci ko wanki babu, dawowa yayi yakawo mata sannan shima ya zauna, anan yaga qafafunta duk sun kumbura, ya miqe qafafunsa yaja qafar tata yadora akan cinyarsa yana matsa mata su, wayarsa yadauka yakira Momy kilishi, bayan sun gaisa yace"Momy munje wajan scanning ance Mawahib yanbiyu ne"

Cikin sauri Hajiya kilishi tadafe qirjinta tace"yan biyu?, har yanzu de Ina ganin ikon Allah ni kilishi,gaba daya de a zabar danasha irinta yarinyar nan take sha, to tunda saura Yan satittika tasauka ko zaka kawo ta gida saita haihu anan?"

Cikin sauri yace" Momy Anty Mamy tataho mana,ba mazajenta za'a haifa ba?"

Hajiya kilishi tayi murmushi tace"to Maryam din gatanan tanajin abinda kafada kuma bazata zo ba"

Cikin sauri yazaro idonsa sannan yakashe wayar.

Hajiya kilishi ta kalli Alqali tace"Mawahib fa takusa sauka Alhaji,shine nake tunanin ko zai kawo ta gida ta haihu anan?"



Alqali yace"naji kince yanbiyu ne ko?"

Tace"eh haka yake fadamin yanzu"

Yace"toki rabu dasu idan tashiga satin haihuwar saisu dawo gida,da Ina tunanin Sadiya taje ta zauna dasu, to amma yanzu tunda yanbiyu ne gara sudawo gida ta haihu agabanku,zasufi Samun kulawa, zan kirashi insha Allah"

Cikin farinciki Hajiya kilishi tawuce part din Mamy zata sanar da'ita.


Captain Aryan bai bar Mawahib agida ita kadai ba ranar baije wajan aiki ba zama yayi tareda ita yana aikin matsa mata qafafu.

Kamar yanda likita tafada Washegari bayan yadawo daga wajan aiki hannunta ya kama suka fita compound din gidan ta dinga yawo, kawai gidan suke zagaya wa bai barta ta zauna ba, aikuwa kafin tagama duk ta hada uban gumi, sannan suka dawo ciki yakamata tana taka stairs dinsu daqyar, dakinta yakaita tayi wanka, tasauko qasa tashiga kitchen tafara kokarin hada musu abinci,zama yayi a falo yana qoqarin waya da Ashraf, sai qaranta yajiyo a kitchen, aguje yashiga kitchen din yaga ta riqe dan yatsan qafar ta tana yarfe hannu.

Hannunta ya janye daga kan yatsan nata yace"meyake faruwa?"

Tace"plate dinnan ne ya fadomin a qafata"

Yakai kallonsa wajan plate din shibega abun kuka anan ba, yadauki plate din a hannunsa yaga idan ya masa kyakykywan ruqo zai Iya karyashi,ya kalli idonta yace"akwai zafi ne?"

Cikin sauri tadaga masa kanta, cikin kulawa ya kamota yace"muje falo ki zauna,yau zanyi mana girkin"

Badan ta yarda ba tazauna shikuma yashiga kitchen din yadauki wayarsa yayi browsing girke girke sannan yafara yimusu, tana zaune afalo sai ganinsa tayi ya ajiye mata plate din abincin agabanta, yace"taste it..."


Murmushi tayi ta dauki spoon taci dan kad'an ta yatsina fuska, saita ga yanayinsa ya sauya jikinsa yayi sanyi, sai tafashe da dariya tace" yayi dadi, dama gwadaka zanyi"

Dariya yasaki yazauna akusa da'ita tareda riqe kafadarta, adede lokacin cikinta yafara motsi, ta dauki hannunsa ta dora akan cikin tace"kaji suna motsi"

Cikin farinciki Shima yasaka hannunsa yanaji, dayan hannun nasa kuma yafara bata abincin.

Haly JASHERU venture's,munada kayayyaki masu kyau da inganchi ba algus da ha'inci, kayanmu daga Ethiopian ne, prdct dinmu muna Ethiopian magic hair oil, anti dandruff shampoo serum, bdy cream, hand cream, magungunan chuttuka da na mata masu inganchi da qara lfy ajikin dan
adam ga number kmr hk 07046665338 ko 07061664264 munada distributor ako Ina afadin kasarnan da ketare muna koya harkokin kasuwnchinmu ga masu bukata akan 5000 kacal

sannan munada tsuntsaye na kasashen waje tattabaru game bukata ko koya akwai riba kwarai aharkar mebuqata yasiya koya koya seyanemeni a number na kamar haka 07046665338 ko 07061664264, ku antayo ayi tafiyar daku,yar'uwa kikoyi sana'ah akan wannan farashi me sauqi kema ki kafa kanki💃🏼


Haka suke gudanar da rayuwar su cikin farinciki,hatta kwanciya saiya kwantar da'ita yayi mata Addu'ah, sannan shima zai kwanta, kullum idan yadawo daga wajan aiki baya zama sai sun fita ta motsa jikinta kamar yanda likita tafada,duk yanda yakaiga son kasancewa da'ita haquri yake,saboda girman cikin, hakan yasa suka rage yin abubuwa saide bayan kwanaki suyi, saide tazarar kwanakin dayake bata baya komai hakan yasa idan suka kasance tare yake kasa controlling kansa harsai yaji yanda yakeso sannan yake rabuwa da'ita.


Kamar yanda Alqali yatsara kwanakin haihuwar ta suna cika, yasa Captain yakawo ta gida, bayan sunzo gida a part din Hajiya kilishi ta sauka, kowa sai sannu yake mata cikinsu harda Nabiha data taho gidan tun safe itama.


anan gida ta wuni tareda Mawahib wadda tunda ta zauna bata motsa ba,Nabiha ce take nuna mata tsarabar su ta Saudia sai murna suke kamar su aka jewa Saudian.

Saida Captain Aryan yayi kwana biyar Mawahib bata haihu ba, hakan yasa yashiga damuwa saida Mamy tasake yimasa bayani cewa dama Ana wuce watannin, sannan hankalinsa ya kwanta harya samu damar komawa wajan aiki.

Bayan yatafi ma saida yayi sati biyu a Abuja kullum yana waya yana tambayar halinda ake ciki, amma saide yaji shiru babu batun haihuwa.

Yau tun asuba tatashi da naquda Mamy taduba tagani tace"dasaura"

Hajiya kilishi tana gefen ta ta riqe hannunta sai sannu take mata, yayinda Mamy tagama shiryawa tsaf domin kar6ar haihuwar jikokinta,tun qarfe shida na safe Captain Aryan yake kiran wayar Mawahib amma no answer, da farko yayi tunanin ko bacci take, saiya haqura, wajan qarfe takwas yasake kira yaji shiru bata dauka ba, alokacin Mawahib batasan inda kanta yake ba, naquda ta sakata agaba gadan gadan.


Captain bai haqura ba yasake kiran wayar Momy kilishi itama yaji bata dauka ba, yakira Mamy ma shiru, yakira Mama Sadiya itama bata dauka ba, tun daga nan jikinsa yabashi ba lafiya ba, kai tsaye ya shirya yanufi Airport ya taho gida.


Baizo gidaba sai qarfe tara da rabi na safe, yaji gidan shiru babu kowa,da alama mazan gidan basa nan, kai tsaye yanufi part din Mamy yaganshi a rufe, cikin sauri yatafi part din Momy kilishi anan yaji maganar matan gidan gaba dayansu a dakin Momy kilishi,yana dosar dakin yaji Mama Sadiya tana cewa"yi nishi Mawahib"

Gabansa yayi wata irin faduwa,yasaka kansa cikin dakin yatsaya abakin qofar dakin yana kallon azabar da Mawahib takesha gaba daya dogon gashin nan nata ya hargitse tajiqe sharkaf da gumi banda kuka babu abinda take, jikinsa ne yayi sanyi kalau yayinda gabansa yake faduwa baisan lokacinda ya jingina da jikin qofar dakin ba.


Mamy datake tsugunne a gaban Mawahib tace"Mawahib kiyi nishi mana,zaki kashe masa yara fa..."

Hajiya kilishi data fashe da kuka tace"ina ganin ikon Allah ni kilishi waiku malaman asbitin nan meyake saku masifa ne? kiyi mata haquri mana da wannan uban cikin zataji koda masifar ki?"

Mama Sadiya ta shafa kanta tace"daure Mawahib, daure Allah yasauke ki lafiya"

Wani irin nishi tayi takama hannun Hajiya kilishi ta riqe kamar zata 6allata saiga kan da yafuto, akan idon Captain yaga yanda Mawahib take haihuwa lokaci daya ya silale yayi qasa ya zauna jagwab, daga nan baisake sanin meyake faruwa ba yasume a zaune (🙆🏻‍♀️)





Jama'ah a taimako da ruwa yau soja ya gaza😂





Mawahib littafin kudi ne,duk me buqata naira 500 ne kacal ta wannan account din
0164549488
Amina muhammad
GTbank

Kokuma katin MTN ta wannan number 08033300034







Amnah El Yaqoub✍🏻
[7/21, 11:44 AM] AMINA KABIR CAPS: MAWAHIB


Godia ta musanman ga:

Ayesha✨🥰
Safeena
Ummu hafsah
Hauwa Umar
Hauwa'u
Bilkisu bej
Saratu Hassan
Nusaiba maga
Hafsat
Zainab jaaf
Asiya Bashir
Mummy A10
Babyj
Ummi Gumi
Mrs Hauwa
Ameenah🥰
Ramatu shehu
Umm
Hafs shareef
Matar mijin
Ummu mujitapha
Zainab
Aisha
Queen
Rashida kham
Maman walid
Murjanatu
Maryam
Teemah Baba
Khadija Muhammad
Hareesa taneem🌹🌹
M@m@n Aish@
Maman samha
Reemah
Shamsiya
A.g Abdullahi
Ummu kulsum

Ina Alfahri daku akoda yaushe ❤️💃🏼



Mama Sadiya da Mamy da Hajiya kilishi ne suka juya jin motsin mutum a bayansu, amma babu wadda tabi takansa sun san cewa tsorata yayi da alama baisan yanda akeyi ba.

Mawahib kuwa bataga shigowar saba, saida ta haifi na farko sannan tafara maida numfashi,Mamy tabawa Mama Sadiya yaron, Mama Sadiya tafara gyara shi, hawaye suka zubo daga idon Mawahib tanajin wata sabuwar qaunar Mamy aranta, bata gama kukanba wani sabon ciwon yataso, wannan karon kam kasa yin shiru tayi kuka take sosai harda ihu, kafin ubangiji yabata damar haihuwar dayan lafiya.

Shikuma Hajiya kilishi ce ta kar6eshi tana hamdala afili idonta fal hawaye, ba komai take tunawa ba sai lokacin data haifi su Ashraf, suma haka taji kamar ta mutu, Mamy kuma tamaida hankali tafara kula da Mawahib, tsawon awanni suka dauka adakin zuwa lokacin harsun gyara yaran tsaf dasu masha Allah farare masu mutuqar kama da juna,Mama Sadiya tayiwa na farkon alama, yanda za'a gane waye babba a cikinsu, Mamy kuwa sai yanzu hankalinta ya kwanta bayan taga tagama gyara yarta tsaf harda dinki tamata, sannan ne Mawahib tafara yin baccin wahala.


Mamy ta kalli Captain Aryan tayi murmushi tace"to sojoji sun fadi sun suma, shi Ashraf inda yagani shikuma Yaya kenan?"

Cikin farinciki Hajiya kilishi tace" rabu da wannan dannaki Maryam Aryan aiba soja bane awajan matarsa"

Mama Sadiya ce ta dauko ruwa ta zuba masa, sai alokacin yazabura yabude idonsa yafara bin dakin da kallo yayinda gumi yahadu da ruwan da aka zuba masa yasa kayan jikinsa suka jiqe, gadon ya kalla yaga Mawahib tana bacci ga yaran nan an shirya su tsaf acikin fararen kaya suma suna bacci.

Ahankali yaji hawaye yana zubowa daga idonsa,yanzu irin wannan wahalar Momy tasha itama kafin ta haife su?
wacce irin kulawa zai bawa matarsa saboda wannan azabar datasha?

Cikin sanyin jiki ya qarasa wajan Momy kilishi yadora kansa a cinyarta yafashe da kuka yace"Momy kiyafemin"

Mama Sadiya ta girgiza kanta cikeda tausayi, yayinda Mamy tafara bashi haquri.

Hajiya kilishi ta shafa kansa tace"Babana bakamin komai,duk abinda yafaru abaya ai yariga yawuce, Allah zaka yiwa godia bisa kyautar da yayi maka"

Cikin sauri yatashi daga kan cinyarta yana goge hawayen idonsa, sannan ya qarasa kan gadon ya kalli yaran masha Allah ba qananu bane,suna baccinsu cikin kwanciyar hankali suna nema su kashe masa mata, bai dauke suba, yakama hannun Mawahib yariqe sannan ya shafa kanta yadora bakinsa akan goshinta yayi kissing dinta, cikin kunnanta yarada mata "Allah yayi miki Albarka Honey"

Yasaka hannunsa yana sake goge hawayen idonsa, Mamy tayi murmushi tatashi tafice,tana fadin "bari inje in bugawa Yan maiduguri waya Infada musu"

Mama Sadiya ma tatashi tafita, Hajiya kilishi kuwa wayarta ta dauka takira Alqali yana dauka tafara fada masa, sannan itama tabar dakin, Captain Aryan yana jiyota daga falo tana buge bugen waya tana fadawa mutane.

Shida kansa yakira Ashraf yafada masa, inda Ashraf din yabashi tabbacin yau zai baro wajan aikinsa yazo yaga yaran shima, Mama Sadiya kuwa itace ta fadawa Nabiha.


Ta dade tana bacci yayinda Captain Aryan yana zaune agefe yana aikin kallonsu itada yaran yanajin wani irin farinciki aransa wai ita da yaran duka nasa ne,kallon yaran yake tundaga kan yatsun qafarsu iri dayane babu banbanci, kamar de shida Ashraf, ahankali yasake jin wani hawayen yana zubo masa, yasaka dan yatsansa ya goge, sannan ya sunkuya yayi kissing dinsu, yasake komawa gefen Mawahib.


Nabiha ce tashigo dakin cikin farinciki tana ganin Mawahib tana bacci saita fara takowa a hankali dan karta tasheta, yaran tafara kalla ta sunkuya ta dinga kissing dinsu cikin farinciki sannan ta gaida Captain Aryan daya kafa yatsare yaqi zuwa ko'ina, sannan tafuto daga dakin.

Nabiha tana fita bayan minti talatin Mawahib ta farka, ahankali tafara bude idonta harta gama bude shi fes a kansa, hannunta yana cikin nasa, cikin kulawa ya sunkuya yayi kissing dinta sannan yace"Sannu Honey,Allah yayi miki Albarka..."

Ajiyar zuciya ta sauke ta kalleshi tace"Yaya Captain..."

Cikin sauri yace"Honey yau ba Baby?"

Bakinta taturo gaba tace"nadena haihuwa"

Hawayen tausayin tane yazubo daga idonsa,ahankali tasaka hannu ta share masa hawayen, cikin hawayen yace"nima bazan bari kisake haihuwa ba, wannan ma sun'isa,wahalar tayi yawa,nayi tunanin mutuwa zakiyi, kingansu nan ban dauke su ba,nabari saikin tashi mu dauki yaranmu da kanmu atare"

Fuskarsa ta shafa tayi murmushi tayunqura tatashi daqyar, yayi sauri yasaka mata fillo a bayanta, sannan yadauko yaran yadora mata su ajikinta gaba dayansu, sannan ya hadasu ya rungume su wani sabon hawayen yana sake zubo masa.

Kallon Yara take tanajin yanda take tsantsar qaunar su acikin ranta, ahankali ta kalleshi tace"wana fara haifa?"

Cikin sauri ya nuna mata nafarkon,ta sunkuya ta sumbaceshi, ta sumbaci dayan ma tace" Allah yayi musu albarka"

Hawayensa ya share yace"Amin"

Dago kanta tayi tasake kallonsa,ganin yana share guntun hawaye hakan yasa ahankali ta dora harshanta akan fuskarsa ta share masa hawayen tas, kamar yanda yake mata, Mamy ce tashigo dakin cikin sauri Captain Aryan yayi baya tareda sosa qeyarsa.

Mamy bata nuna musu komai ba ta qaraso gadon ta zauna tana qoqarin daukar yaran daga cinyar Mawahib tace"wai har yanzu basu tashi daga baccin bane?"

Mawahib tace"basu tashi ba"

Mamy tadan jijjigasu tace"maza kutashi ba bacci kukazo yiba,baccin awa nawa zakuyi, kutashi gasu Yaya khaleed can afalo sunzo suga abokan su"

Hajiya kilishi ce tashigo dakin da tuwon dawa miyar kuka wadda taji Jan nama aciki, sai man shanu da'aka zuba akan tuwon dakuma kunun kanwa, mama Sadiya ma tashigo da farfesun nama duk suka ajiye mata, Hajiya kilishi takalli Mamy tace"wai har yanzu basu tashi bane?"

Mamy tace"gasunan sun kama ido sun rufe sunata bacci ko tsoron ganin mu suke oho"

Hajiya kilishi tace"tashe su"(😂)

Babu musu Mamy tafara tashin su.
Hajiya kilishi ta juya ta kalli Mama Sadiya tace"Sadiya kice su Alhaji su shigo mana,su shigo kawai"

Adede lokacin kuwa Mamy tatashi yaran, nan da nan kuwa suka fara kuka, Captain Aryan ya kallesu cikin jin dadi ya sunkuya yayiwa Mawahib rada yace"kinji kukan su"

Murmushi tayi tanajin dadi aranta.

Adede lokacin Alqali da Abba, da Alhaji khaleed suka shigo dakin,har rige rigen daukan yaran suke saboda farinciki,Alqali ya dinga kallonsu sai suka tuna masa da shekarun baya lokacin da kilishi ta haifa masa yanbiyunsa.
Hajiya kilishi takalli Mawahib tace"sauko kici tuwo saiki basu susha"


Mawahib tace"Momy ni banason tuwo"

Captain yayi sauri ya kalleta yace"yau kuma?"

Mama Sadiya tace"dama ai cikin ne yasa take cin tuwon shiyasa ga yaran nan masha Allah 6ul 6ul dasu kamar ba haihuwar farko ba"

Captain Aryan yayi kasa da kansa yana tunanin maganar Mama Sadiya cikin ransa yana fatan Allah yasa iya cin tuwon tadaina banda daya abun 🙊🙈

Hajiya kilishi tace"tuwo ai dole ne Mawahib,idan kikaci tuwon kika Sha kunun kanwar nan yanzu yanzu ruwan nono zaizo, suma yaran saisu samu abinci"

Badan taso ba tatashi daqyar ta sauko sai taji cikinta sakayau kamar an debe mata komai haka tafara cin tuwon ahankali tana tunanin yanda take masifar son tuwo kafin ta haihu amma yanzu tuwon ne bataso, taci tuwon daidai misali sannan tafara shan kunun kanwa,Alqali yayiwa yaran Addu'ah,yabasu ruwan zam-zam sukasha, sannan ya kalli hajiya kilishi yace"Kilishi yanzu kinsamu sabin angwaye ba Zaman lafiya"

Momy kilishi tace"A a bana wannan auren, ba nayi Sam Alhaji,Ina mazaje anan tunda suka zo suke aikin bacci"

Alhaji khaleed yace"A a Yaya baza'a yi hakaba"

Hajiya kilishi tace"tun yaushe?"

Dukansu dariya sukai, Nabiha tashigo dakin tana sake kunna turaren wuta.

Daga nan su Alqali suka fita, Nabiha ma tasake fita taje takawo mata fruit, sannan ta zauna tana mata sannu.

Saida taci ta qoshi Mamy tahado mata tea me shegen kauri shima tasha, sannan Hajiya kilishi ta kalli Captain Aryan tace"bata su tabasu susha"

Ahankali yadauki guda daya yabata, ta kar6eshi, Hajiya kilishi ta fice, Mamy ma ta dauke sauran kwanunkan da Mawahib tagama cin abinci tace"Nabiha zo muje ki kawo wa Captain abinci"

Nabiha tatashi tabi bayanta, Hajiya kilishi ta kalli Mamy cikin jin dadi yanda take kula da yaranta,Koda bata Raye ta tabbatar Mamy zata kula mata da yaranta, gashi de yazo tundaga Abuja babu wanda yayi tunanin bashi wani abun yaci, ciki harda ita, sai Mamyn ce tayi tunanin bashi.

Captain Aryan yana ganin ficewarsu ya matso da daya yaron a hannunsa ya kalli Wanda yake hannun Mawahib sannan ya kalleta yace"kibashi mana"

Ahankali tazuge zif din rigar ta tafuto da nonon ko brezia babu tafara bashi, Captain Aryan ya kalli breast din yanda suka sake cika yahadiye wani irin Saliva yana kallonsu da birge wa, ahankali ta runtse idonta tace"yanasha da zafi Yaya Captain"

Cikin sauri yace"Honey wai bazaki dena cewa Yaya Captain dinnan ba?"

Kallonsa tayi cikin wata irin hararar soyaiya, cikin shagwa6a tace"to ba Kaine kasa Ina zaman zamana yaranka sukazo suna neman kasheni ba, gashi yanzu suna shamin abu da zafi"

Murmushi yayi cikin jin dadi yace"zaki daina jin zafin Honey,kiyi haquri please muntuba"

Kallonsa tayi tace"Allah da zafi"

Cikin kulawa yace"sorry,basu ahankali to"

Haka ta daure taci gaba da basu duk da zafin datake ji.


Haly JASHERU venture's,munada kayayyaki masu kyau da inganchi ba algus da ha'inci, kayanmu daga Ethiopian ne, prdct dinmu muna Ethiopian magic hair oil, anti dandruff shampoo serum, bdy cream, hand cream, magungunan chuttuka da na mata masu inganchi da qara lfy ajikin dan
adam ga number kmr hk 07046665338 ko 07061664264 munada distributor ako Ina afadin kasarnan da ketare muna koya harkokin kasuwnchinmu ga masu bukata akan 5000 kacal

sannan munada tsuntsaye na kasashen waje tattabaru game bukata ko koya akwai riba kwarai aharkar mebuqata yasiya koya koya seyanemeni a number na kamar haka 07046665338 ko 07061664264, ku antayo ayi tafiyar daku,yar'uwa kikoyi sana'ah akan wannan farashi me sauqi kema ki kafa kanki💃🏼


Sai yamma Ashraf yadawo, kai tsaye suka dauke yaran shida Captain Aryan suka futo falo dasu wajan Hajiya kilishi, Mawahib kuma suka barta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login