Showing 15001 words to 18000 words out of 110331 words

Chapter 6 - MAWAHIB COMPLT HAUSA NOVEL

13 Sep 2024

19679

yayi murmushi yace"saboda muma kanmu tsaron ne,muda ya kamata mubawa yan qasa tsaro idan muka fara gudun hanya yaya kenan? dani kadai ne sainabi jirgi Ash,amma yanzu duk wanda yaganmu ahanya zaiso yabiyo bayanmu saboda yasan zai samu tsaro da kariya awajan mu,insha Allah babu damuwa"
Ashraf yasaki ajiyar zuciya yace"to shikkenan,sai munyi waya"
Captain Aryan yagyada kansa sannan yashiga mota sukaja suka tafi.

Suna tafiya ahanya yana tuna irin kunyar da matar nan qawar Mamy tabashi agaban yarinyar nan Mawahib,koda wanne ido zai sake kallonta oho,danma ba sabgarta yake shiga ba bare tasake samun damar rainashi,sai yanzu ne yatuna dukansu matan gidan yabasu kudi amma banda Anty Mamy saboda ya futo cikin kunya ko sallamar kirki ba suyi ba,already yanada account number dinta, cikin sauri ya laluboshi yayi mata transfer, sannan yamaida wayarsa aljihunsa tareda lumshe idonsa,motar shiru babu surutu kasancewar sunsan cewa ogan nasu bayason surutu.


******

Har motocin su Captain Aryan sukai nisa aka dena hangosu Ashraf yana tsaye a wajan yakasa dena kallon hanyar, mamaki yakama Alqali, da alama akwai abinda yake damun Ashraf,qarara ga damuwa nan ta baiyana a fuskarsa,yana kallonsa saida ya dade atsaye a wajan sannan yajuya yashiga gida,shima kansa Alqali sai zaman qofar gidan ya gagareshi, Ashraf din baidade da shiga gidaba shima yad'oru abayansa ya shige, kai tsaye dakinsu Ashraf din yanufa,Ashraf yana ganin mahaifin nasa a dakinsu mamaki ya kamashi,saboda babu abinda yake kawo shi dakin saide in yanason ganinsu yakira su suje, zama yayi abakin gadon cikin fuskarsa ta kamala yadubi Ashraf yace"babu damuwa deko?"

Babu 6oye-6oye Ashraf yace"Daddy banason tafiyar Aryan,kuma nafada masa banaso yatafi shine yarabu dani ya shirya yayi tafiyarsa,nikuma inaji kamar wani abune zai sameshi"

Alqali yayi ajiyar zuciya yace"ka kwantar da hankalin ka,kayi masa addu'ah insha Allahu babu abinda zai faru sai alkhairi,kasaki jikinka kayi walwala kaji ko?"

Sai a lokacin Ashraf yasaki wata irin ajiyar zuciya,Alqali yasake kallon fuskarsa yagade har zuwa lokacin kamar akwai sauran magana, cikin hikima irin tasu ta iyaye yayi murmushi yace"tosaime kuma?"

Cikin kunya Ashraf yafara sosa kunnansa yace"Daddy dama....dama inaso inyima magana Daddy inaso ka nemamin auren Mawahib a wajan Kawu Isah,wallahi Ina sonta Daddy"

Tsananin mamaki yakama Alqali,kowanne irin so Ashraf yake yiwa Mawahib ya tabbatar badan qarami bane,tunda bai tsaya Iya cewa a nema masa auren ba, saida ya dubi tsabar idonsa yasake cewa yana sonta, Alqali yayi murmushi tace"to wannan aiba abun damuwa bane,abun farinciki ne ai wannan,saide kasan mahaifiyar ka batayi da mahaifiyar Mawahib din ko? to saboda kwanciyar hankalin ita yarinyar, yakamata kaje kasamu mahaifiyar ku da maganar idan har ta nuna tana son Mawahib din kaga babu damuwa koda ka aure ta zasu cigaba da zama lafiya a tsakanin su"

Ashraf yace"eh Daddy zanyi mata maganar ,ita naso nafara fadawa ma, to sai nafara yiwa Aryan maganar,dafarko yanuna bayaso, saidaga baya naga yabar maganar, amma nasan Momy zataso abinda nakeso"

Alqali tace"to Alhamdulillah,naji dadin wannan maganar taka,koba komai aurenka da Mawahib din zai Iya kawo shiryawar mahaifiyar ka da mahaifiyar ita Mawahib din,zan samu Alhaji Khaleed da shi Alhaji Isah akan maganar,Allah yayi maka albarka"

Cikin jin dadi Ashraf yace"Amin ya Allah Daddy"

Cikin sigar tsokana Alqali yace"shikkenan hankali ya kwanta?"

Cikin kunya Ashraf yace"eh Daddy"

Alqali yasaka hannu yashafa sumar kansa, sannan yafice daga dakin tareda rufowa.


******

Tafiyar su tayi nisa sosai har zuwa lokacin Captain Aryan idonsa a lumshe suke,kamar an jefo musu wani abu haka wani babban mutum sanye da farar shadda gamida babbar riga sai maiqo shaddar take yafado gaban motarsu Captain,lokaci daya direban su Captain Aryan yataka wani mahaukacin birki wanda yasa Captain din bude idonsa cikin sauri, motar tana tsayawa mutumin yanufo murfin motar tasu yana kokarin budewa yanayi yana waigen bayan sa, lokaci daya suka fara jin qaran harbi, cikin sauri Captain da sauran sojoji suka bude motar suka futo, Captain Aryan yadubi mutumin yana tambayarsa "meyake faruwa?"

Kwata kwata tashin hankali yahana Captain Aryan gane tsananin kamar da wannan mutumin yake da Mawahib,daga idonsa har cikakkiyar girarsa gaba daya basuda banbanci dana Mawahib, fari ne tas kamar ka latsa jikinsa jini yafuto, kafin mutumin yabashi amsa kamar daga sama sukaji taaaassss an iyo musu harbi, cikin tsananin tashin hankali mutumin nan yadubi Captain Aryan yace"ka taimaka min yaro, zasu kasheni, zasu kasheni ka taimaka min mubar wajannan basuda Imani zasu kasheni...."

Captain Aryan yanajin haka ya juya ya kalli sojojin dayake tare dasu, kallo daya yayi musu, suka gane abinda yake nufi nan take suka fitarda bindiga suka fara sakin wuta, lokaci daya wajen ya karade da qaran bindiga, har zuwa wannan lokacin Captain Aryan baiyi harbi ba, yana tsaye yariqe wannan babban mutumin ya 6oyeshi a bayansa

Daya daga cikin wanda suka kawo harin ne yazo daga bayansu Captain zai harbi mutumin,wannan mutumin yana ganin haka nan take ya lumshe idonsa yafara karanta kalmar shahada, saboda yagama tabbatar da cewa harbin da'aka iyo daga bayan nan yariga ya sameshi, yasan cewa yau tasa taqare mutuwar sa tazo,Captain Aryan dayake riqe dashi yajuya da sauri saboda qaran harbi dayaji, yana juyawa adede lokacin har bullet din yazo wajan su,cikin sauri yature wannan mutumin,yana tureshi adede lokacin bullet din yazo kai tsaye harbi yasauka agefen qirjin Captain Aryan, cikin sauri yasaka hannu yadafe wajan,yasaka hannunsa na dama ya dauko 'yar qaramar bindigar datake aljihun wandonsa babu 6ata lokaci shima yarama harbin,nan take kuwa wancen din yafadi qasa babu alamun numfashi atare dashi.

Sauran maharan suna ganin ankashe ogansu,suma suka gudu kowa yayi ta kansa, wannan babban mutumin kuwa yana ganin yanda Captain yatare masa harbi lokaci daya jikinsa yadauki rawa,yadora hannunsa aka kamar ba babba ba yafara kuka wiwi, cikin kuka yake fadin"lahaula wala quwata illa billahi aliyal azim,yaro meyasa kayi haka? meyasa baka bari sun kasheni ba? meyasa zaka sadaukar da rayuwarka saboda ni?"
Duk wannan maganganun dayake Captain Aryan baya jinsa, hannunsa dayasa yatare inda yaji shigar bullet din jikinsa gaba daya hannun ya6aci da jini,yawan jinin daya zubane yasa nan take jini yafara daukar sa, idanunsa suka fara lumshewa, atake jiri ya debeshi yazube a wajan,sauran sojojinsa suna ganin halin da Captain yashiga cikin sauri suka saka shi cikin mota,shima wannan mutumin cikin sauri yafada cikin motar sukaja da mugun gudu sukabar wajan,kai tsaye nasarawa state suka qarasa dashi saboda tafi musu kusa akan Abujan,wani private hospital suka qarasa dashi,motocinsu suna tsayawa wannan babban mutumin yabude motar yafuto sai hawaye yake kamar ba babban mutum ba, farar shaddarsa wacce take maiqo gaba daya ta6aci da jini, ganin yanda babban mutum kamar sa yake kuka wiwi, yasa hankalin ma'aikatan asbitin yadawo kansa, cikin sauri aka kawo musu dauki, aka turo dan qaramin gadon daukan majinyata zuwa gaban motarsu, cikin sauri aka dora Captain Aryan akai, wanda yake kwance babu alamun numfashi atare dashi nurses suna tura gadon zuwa dakin tiyata dasauri amma wannan babban mutumin cikin kuka yake bin gadon yana fadin"likita ka taimakeni,kada yaron nan yamutu ta sanadi na,katemakeni likita"

Yana wannan surutun baisan ma sun qaraso zuwa dakin tiyatar ba,suna zuwa suka dakatar dashi sukuma suka shige ciki da Captain tareda rufo qofar


******


Da yamma Nabiha tana dakin Mawahib suna firar su,Nabiha tace"Mawahib Yaya Ashraf kuwa yafada miki yana sonki?"

Mawahib tace" Dama tunanin kine,ni har yanzu banga alamun hakaba,muna de mutunci kamar baya"

Jikin Nabiha yayi sanyi,ahankali tace"Mawahib Yaya Ashraf yana sonki...."

Cikin sauri Mawahib tace"koda yafadamin ko, bazan ta6a aurensa ba, saboda dan'uwansa yaya Captain baya sona,sannan mahaifiyar su Momy kilishi itama bata sona, to wanne irin zaman aure zanyi dashi?, kidena min wannan maganar Nabiha,Allah yamin tsari da auren 'ya'yanta"

Nabiha tayi murmushi tace"to shikkenan Mawahib yawuce"

Abba da Mamy suna zaune afalo Abba ya Kalleta yace"ina yarinyar nan take ne?"

Mamy tace"Mawahib? tana daki itada Nabiha tun dazu"

Kafin yasake magana saiga Alqali da kansa shida Alhaji khaleed acikin falon nasu, mamaki yakama Abba da Mamy, cikin sauri Alhaji Isah yatashi tsaye yana cewa "Yaya kaida kanka? aida kun kirani nazo"

Alqali yayi murmushi, suka nemi waje suka zauna,cikin ladabi Mamy ta tsugunna ta gaishe su,cikin ranta tana mamakin menene yakawo su Yaya Khaleed da Yaya Alqali har part dinsu yau?

Ahankali tajuya tashiga kitchen domin tahado musu dan abun motsa baki.

******

Ashraf yayi wankansa ya shirya tsaf cikin qananun kaya nashan is'ka kamar yanda yasa ba, wayarsa yadauka yakira Captain Aryan saide wannan karon ma wayar taqi shiga,tun azahar yake kiransa yanason yaji kosun sauka lafiya amma wayar taqi shiga yarasa meyasa?

a fili yace"insha Allah lafiya...."

Sannan yafuto iai tsaye yatafi part dinsu, Hajiya kilishi tana zaune akan kujera tana waya cikin iko kamar yanda tasaba, Ashraf ya zauna agefenta yana sake try number Aryan...

Cikin wayar yaji tana fadin"banason atamfofi tsofaffi fa,masu tsada nakeso ki bayar akawo min guda goma,amma guda bibbiyu kala daya,kayan lefen 'yanbiyu na nake hadawa banason asaka kaya masu araha acikin lefensu".

Ashraf yayi murmushi ya jinjina kansa alamun lalle Momy da gaske take (😂)
Can saiyaji tace"to shikkenan ki gaida Asalamiyya,saita kawomin din"

Yanajin takashe wayar ya Kalleta cikin zaquwa yace "Momy"

Cikin kulawa tace"Na'am Ashraf, yanaganka cikin farinciki ne ko an samomin sirika ne?"

Cikin murna yace" kamar kinsani Momy,ai harna fadawa Daddy ma a nemamin auren ta"

Hajiya kilishi ta gyara zamanta ta kalleshi dakyau, sannan tadaga hannunta sama tace"Alhamdulillah, Allah abun godia,saura Aryan kuma"

Tajuya tasake kallonsa tace"yar gidan waye afadin qasar nan?"

Cikin rashin damuwa yace"Momy Mawahib cefa...."

Hajiya kilishi saitaji kamar bataji bataji abinda yafada daidai ba,cikin son tabbatar wa tasake kallonsa sosai tace"wakace?"

Ashraf yayi murmushi yace"Mawahib din Anty Mamy cefa"

Cikin sauri Hajiya kilishi tamari fuskarta,incase in mafarki take tota farka (😂)
saida tasake marin fuskarta akaro na biyu taga de tabbas ba mafarki takeba babban danta Ashraf shine a zaune agabanta yana fada mata yanason jinin Maryam, cikin son tabbatar wa ta kalleshi tace"Ashraf kaine kake fadamin kanason ka auri 'yar gidan Maryam?"

Cikin sauri ya sunkuyar da kansa qasa,kafin yadago yabata amsa yaqa ta miqe tsaye, cikin sauri yadago kansa yace"Momy Ina zakije?"

Bata saurari abinda zaice mataba tanufi qofar fita daga part din nasu,cikin sauri Ashraf ya riqo hannunta,yace"Momy ki tsaya muyi magana Ina zakije?"

Hajiya kilishi gaba daya idonta ya rufe, burinta kawai taganta a gaban Mamy, ko sauraren Ashraf batayi ba tafizge hannunta tanufi part din Mamy

******



Tunda suka shiga dakin tiyata dashi har yanzu basu futo ba,wannan babban mutumin banda zagaya wajan babu abinda yake, hular kansa tana hannunsa yana firfita da'ita, gumi duk ya jiqa masa jiki, idanunsa yayi jajir har zuwa yanzu hawaye yake,sai zagaya wajan yake yana fadin"innalillahi wa'inna ilaihirraji'un..."

Gashi mutane sun kasa zuwa kusa dashi su bashi haquri saboda sojoji guda hudu dasuke tsaye a wajan kowanne a cikinsu hannunsa yana dauke da bindiga,kana ganin yanda suke zare ido suna zagaya wajan,zakasan cewa ba qaramin mutum suka kawo asbitin ba.

Cikin sauri wannan mutumin yadauki wayarsa yayi kira,daga dayan 6angaren aka daga akace"ALHAJI MA'ARUF.... Ina kashiga ne naje gidan gonarka bansamekaba?"

Cikin kuka wannan babban mutumin wanda aka kira da Alhaji Ma'aruf cikin tashin hankali ya goge hawayen idonsa yace"Alhaji Bala akwai matsala,muna asbiti, yaro zai mutu a dalilina,kazo kasameni yanzu"

Alhaji bala daga nasa 6angaren yace"Yanaji kana kuka? gani nan zuwa, kayi haquri gani nan zuwa yanzu-yanzu, kuna wanne asbiti?".


******

Haly JASHERU venture's,munada kayayyaki masu kyau da inganchi ba algus da ha'inci kayanmu daga Ethiopian ne prdct dinmu muna Ethiopian magic hair oil anti dandruff shampoo serum bdy cream hand cream magungunan chuttuka da na mata masu inganchi da qara lfy ajikin dan
adam ga number kmr hk 07046665338 ko 07061664264 munada distributor ako Ina afadin kasarnan da ketare muna koya harkomin kasuwnchinmu ga masu bukata akan 5000 kacal

sannan munada tsuntsaye na kasashen waje tattabaru game bukata ko koya akwai riba kwarai aharkar mebuqata yasiya koya koya seyanemeni a number na kamar haka 07046665338 ko 07061664264, ku antayo ayi tafiyar daku,yar'uwa kikoyi sana'ah akan wannan farashi me sauqi kema ki kafa kanki💃🏼

******

Abba yadubi yayansa Alqali yace"to yanzu Yaya, Yaya zamuyi da maganar Nabil?"

Alqali yace"Nabil ai tambaya yayi yana so yafara zuwa wajanta zance,ba izni ya nema a bashi dama yakawo kayan neman aure ba,inda ace yakawo wani Abu gida,kokuma iyayensa sunzo sun sameni munyi magana dasu baki da baki, to bazan goyawa Ashraf baya ba,sannan inda ya shirya da tuni iyaye sun shiga cikin maganar"

Alhaji khaleed yace"to Yaya koda ace sunzo munyi magana ma,ai munada damar dazamu hana auren mubawa danmu,saboda gida bai qoshi ba,ai baza'a bawa daji ba, Yaya muna ganin yarinya me hankali da tarbiya, zamu bari wani daga nesa yazo ya dauketa 'ya'yansa dashi kansa su mori wannan tarbiyar tata, bayan mukuma gamu da samari agida har guda biyu ace mun kasa qwato wannan tarbiyar tadawo cikin gidanmu? nima Ina ganin tunda maganar Nabil din batayi nisa ba, abawa Ashraf din kawai..."

Kafin Alhaji khaleed yayi magana Hajiya kilishi ta bankado kofar falon tashigo idonta yarufe da masifa ko ganinsu Alqali dasuke zaune a falon batayi ba, Ashraf ma yabiyo bayanta yana kokarin riqe hannunta musanman shida yaga iyayensa maza a zaune a falon,Hajiya kilishi ta fizge hannunta ta qarasa shigowa cikin falon.

Cikin masifa tadaga murya tafara qwalawa Mamy kira"Maryam! Maryam!! kina Ina?"

Mawahib da Nabiha dasuke zaune adaki suna kalle kallen video a Instagram din Nabiha sunajin wannan kiran da akewa Mamy sukasan cewa yau gidan ba lafiyaba, cikin sauri sukai wulli da waya suka futo,saide suna ganin su Alqali a wajan sai sukai turus suka tsaya abakin kofar dakin Mawahib din.

adede lokacin Mamy takawowa su Alqali wani hadadden cake jikinta duk yayi sanyi tun lokacin data farajin mazan gidan suna tattauna maganar auren Mawahib da Ashraf, wanda a zahiri bazata yarda da wannan auren ba.

Cikin Masifa Hajiya kilishi ta tunkari Mamy tace"Maryam kinji dadi,yau burinki yacika,kinshiga kin fita kin rabani da d'ana,naji dadi kuma na godewa Allah dayasa baki hada da CAPTAIN ba,shima dakin mallakeshi da yanzu 'ya'yana biyu suna fada akan AGOLAR 'YARKI"

Cikin sauri Mawahib ta kalli Hajiya kilishi tana maimaita kalmar 'Agola' acikin ranta....
Ashraf ya sunkuyar da kansa qasa yana tunanin kode Hajiya kilishi bata cikin hayyacin tane shiyasa take kiran Mawahib da Agola? a'iya saninsa Mawahib de Uncle Isah ne ya haifeta.

Mamy tana Jin furucin Hajiya kilishi lokaci daya hawaye ya wanke mata fuska,kokadan takasa daga idonta ta kalli mutanan falon,wani irin kukan baqin ciki ne ya kamata take taci gaba da kuka harda shashsheka.
Nabiha tadinga rarraba ido tana ganin mutanan falon gaba daya jikinta rawa yake tashiga shock sosai saboda basu ta6a ganin tashin hankali irin wannan ba

Alqali dayake zaune ransa idan yayi dubu toya 6aci,baqin cikinsa a gaban qannansa maza matarsa tazo tashigo babu da'a duk da tana ganinsa a zaune a wajan kokadan bashida kwarjinin dazai hana Kilishi ciwa Mamy mutunci kenan? koda tayi niyyar zagin Mamy ai idan ta ganshi a zaune ya kamata ace tayi haquri tabari yabar wajan tukunna, cikin baqin ciki yatashi tsaye baiyi wata-wataba yadauke Hajiya kilishi da mari (🙆🏻‍♀️😳)

Cikin sauri Ashraf yadago kansa ya Kalli iyayen nasa,baqin ciki ya kamashi yau Daddy ne yake marin momy? shi kuwa wanne irin yaro neshi da yayi silar da mahaifinsa zai daga hannu yamari mahaifiyar sa?

Cikin qunci Hajiya kilishi ta kalli qwayar idon Alqali tace"qarya nayi? Ina ubanta? har yau kun ganshi da idonku ne? to billahillazi dana Ashraf bazai ta6a auren SHEGIYA ba"

Cikin sauri Mamy da fuskarta tagama jiqewa da hawaye tace" 'yata ba shegiya bace Yaya...,kiyi haquri nima ko bayan ranki bazan bari 'yata ta auri danki ba"

Mawahib tanajin furucin Mamy ta tabbatar da cewa kenan maganar Hajiya kilishi gaskiya ne, cikin tashin hankali tace"Mamy?"
Bata Iya sake magana ba wani kuka yataso mata, cikin sauri ta shige cikin dakinta tashin hankali yasa har tana bige Nabiha bata sani ba, cikin sauri itama Mamy tabi bayan Mawahib din cikin kuka.

Alhaji khaleed mahaifin Nabiha yatashi tsaye saboda bazai Iya jure ganin fadan yayan nasu shida matarsa ba, cikin sauri yafice daga falon, Nabiha ma da idonta yayi jajir cikin gudu tafice tabar part din.

Alqali ya Kalli Hajiya kilishi yace"kinji dadi? kin tonawa yarinya asiri kinji dadi ko? yanda kike qoqarin ganin kin tozarta wannan yarinyar kisani Allah zai saka mata ta'inda baki ta6a zato ba,saboda bata tsare miki komai ba"

Alhaji Isah yatashi tsaye cikin sanyin jiki yace"yaya kayi haquri,yaya kilishi kema kiyi haquri insha Allah wannan maganar anbarta"

Cikin sauri Ashraf ma da jikinsa yayi sanyi ya kalli mahaifin nasa yace"Daddy kuyi haquri,tunda Momy bataso zan haqura"

Cikin 6acin rai Alqali yace"Aure babu fashi sai anyi shi inde Ina raye,saide in Mawahib ce dakanta tace bataso"
Daga nan yasakai yafice daga falon cikin fishi babbar rigar nan tasa sai tashi sama take.


Cikin 6acin rai Hajiya kilishi tace"haka Nima muddin Ina raye, wallahi dana bazai ta6a auren wannan yarinyar ba"
itama tafice daga falon ko rufo musu qofar batayi ba, Alhaji Isah yaja Ashraf jikinsa ya rarrashe shi, sannan ya bubbuga bayansa alamar lallashi, yajuya yabi bayan Mamy wadda tashiga dakin Mawahib.
Tarar dasu yayi dukansu suna kuka daga Mawahib din har Mamy.
Cikin kuka Mawahib tace"mamy da gaske ni shegiya ce banida mahaifi? Abba ba shine ya haifeni ba?"

Cikin sauri Mamy tarufe mata baki tace"karki sake kiran kanki da wannan sunan,ke yar halak ce kamar 'ya'yanta"

Alhaji Isah yayi gyaran murya yace"Maryam kudena wannan koke koken dan Allah,Mawahib de koda ace batada mahaifi nime tsaya matane a kowanne hali take ciki,barema kunadani, bazan ta6a bari kuyi kukaba, kuyi haquri kudena kuka,ki rarrasheta tayi shiru,"
Yana fadar haka yafuto daga dakin cikin sanyin jiki.

Mawahib ta Kalli Mamy cikin kuka tace"Mamy waye mahaifi na? kibarni natafi wajansa ko Momy kilishi zata daina yimin gori Mamy"

Mamy ta goge hawayen idonta tace"karki sakemin maganar mahaifin ki Mawahib,babu abinda zai kaiki wajansa,zan maye miki gurbin sa ako'ina"

******

Cikin tashin hankali Ashraf yakoma dakinsa, yana zuwa yakama kansa dayake masa barazanar rabewa gida biyu,cikin tashin hankali yafurta"innalillahi wa Inna ilaihirraji'un...."

Cikin sauri yadauki wayarsa yafara kiran Captain Aryan, saide har yanzu wayar kwata kwata bata shiga, cikin baqin ciki yayi wulli da wayar yadafe kansa da hannunsa (🤦🏻‍♂️)


******

Basu futo daga dakin tiyatar ba sai qarfe biyu nadare,kai tsaye dakin hutu aka turashi,aka hana kowa shiga inda yake,Alhaji Ma'aruf yakasa zaune yakasa tsaye,sai leqen Captain yake ta glass din kofar dakin yana kwance andaura masa qarin jini babu riga a jikinsa, ansaka masa audiga da bandeji a'inda harbin ya sameshi, fuskarsa tayi wani irin fayau lokaci guda.

Har aka kira sallar asuba shida sojojin nan idonsu biyu,abokinsa Alhaji Bala shine de yake dan gyangyadi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login