Showing 63001 words to 66000 words out of 110331 words
ne?kacire komai aranka kayi abinda yadace"
Cikin sanyin jiki yace"Okay ,jarababbe sai anjima"
Ashraf ya Kalli wayar da sauri yana murmushi bayan yaji Captain din yakashe wayar,hakan yana nufin yagane da Nabiha yake tare kenan.
Yana kashe wayar yashiga email din wani gidan abinci yana magana dasu,daga dakinta tafuto tayi kwalliya tana sanye cikin doguwar riga ta atamfa fitet gown,daurin dankwalin nata yayi mata kyau sosai,tana qarasowa falon ta ganshi a kwance yana danna waya,qarasowa tayi ahankali tana zuwa kusa dashi qamshin ta yanayi masa sallama, kallon fuskarsa tayi wadda babu fara'ah kamar kullum, sannan ta janye idonta ahankali saboda karsu hada ido,tace"Ya Captain Ina kwana?"
Kallonta yake cikin wani irin shauqi,yana qarewa shigar jikinta kallo a taqaice yace"kin tashi lafiya?"
Mamaki ya kamata,yau Kuma salon gaisuwar tasa kenan,tasaba Koda yaushe saide yace mata lafiya, a taqaice.
Kanta aqasa tace"akwai breakfast"
wayar hannunsa ya ajiye sannan yatashi yace"Okay"
dining suka qarasa,yadora hannunsa akan kujera yana tsaye, itama daga tsayen tafara zuba musu abinda tadafa,kallonta yake cikin zuciyarsa yana yaba irin nutsuwar yarinyar,harta gama zubawa ta ajiye masa agabansa,itama ta ajiye nata agabanta,abincin ya dauka yabar inda yake yadawo kujerar kusa da ita ya zauna har jikinsu yana haduwa dana juna,ta kalleshi ta gefen idonta,sannan ta dauki fork tafara cin arish din dake gabanta ahankali,kad'an kad'an tanajin gabanta yana faduwa amma saita dake,babu wanda yayi magana duka su biyun,saida suka kusa gamawa batare daya kalleta ba yace"ya tsoron jiya?"
Lokaci daya Mawahib ta qware, tafara tari,meyake damun Yaya Captain ne?
tasamu tafara mantawa shikuma yana qoqarin tuno mata da wannan tashin hankalin.
ganin yanda taqware yasa ya danyi murmushi kad'an, saboda ya tabbatar dalilin tambayar ne yasa ta qware, tashi yayi tsaye yadauko gorar ruwa yazuba a cup, sannan yadora hannunsa a bayanta yana shafa wa, yadora mata cup din abakinta, cikin sauri ta shanye ruwan,tafara maida numfashi,gumi ya rufe mata fuska,Captain yana kallonta yana murmushi qasa qasa,yanason ganin wannan tsoron na idonta, birgeshi yakeyi, ahankali yasaka dayan hannunsa yajata jikinsa ba tareda musu ba ta kwantar da kanta luf acikin qirjinsa, wata irin ajiyar zuciya yasauke wadda tabawa Mawahib mamaki sosai, bayanta yake shafawa ahankali,dankwalin kanta yazame yafadi qasa,yabi dogon gashinta da kallo, ahankali yasaka hannunsa yafara tattare mata gashin,Mawahib tanajin yanda yake hade mata gashinta batayi kuskure ko yunkurin hana shiba,wayarsa dake kan dining tafara ringing, atare suka Kai dubansu izuwa wayar, sunan Asalamiyya ne yake yawo akan screen din wayar,kokadan Mawahib bataji komai ba akan kiran,tasan budurwar sace,Kuma batada ikon dazata hana shi mu'amula da'ita saboda yar'uwarsa ce,wani Kishi da akeji kokadan bata jishi ba,saima damar daga wayar data bashi, ta hanyar raba jikinta da nashi,ta sunkuya zata dauki dankwalinta daya fadi qasa.
Captain Aryan ya lumshe idonsa cikin taqaici,yarasa me yarinyar nan take nema awajansa,batada aiki Sai kiran wayarsa Kuma bawani zancen arziqi zata fada masa ba saina tsiya, kullum de maganar itace tanaso taganshi tanaso taganshi to idan taganshi uban me zai mata?(π³)
Yanzu gashi yana cikin nishadinsa tayi masa haramiya(π€¦π»ββοΈ)
bai dauki wayarba harta katse,Mawahib taware dankwalin ta zata yafa akanta cikin sauri yariqe dankwalin yace"no barshi haka,kinfi kyau"
Gabanta ne yayi wata irin faduwa,tafi kyau?
me hakan yake nufi?
bai bata damar cigaba da tunanin ba,yadauki fork din datake cin arish dashi yadauko guda uku,yanufi bakinta dashi,gabanta ya tsananta faduwa,meyake shirin faruwa ne?
me hakan yake nufi? Meyasa yake mata abubuwa kamar wani saurayi da budurwa?
Cikin sigar rada yace mata"please bude bakin..."
Wani irin zirrrr taji ajikinta Sakamakon yanda yayi mata maganar cikin rada hakan ba qaramin tasiri yake acikin gangar jikinta ba,ahankali tabude dan qaramin bakinta yasaka mata arish din guda daya,tafara taunawa ahankali,sannan shima yasaka sauran guda biyun bakinsa,saide idonsa yana kanta,yakasa raba idonsa da dan qaramin bakinta,Mawahib kuwa mutum mutumi tazama awajan,gani take kamar bashi ba,gashi fuskarsa babu walwala bare takawo masa wani wargi.
Ahaka ya dinga basu har suka kammala,cikin sauri tatashi zatakai plate din kitchen,Shima yadauki wasu yabiyo bayanta dashi,ganin kitchen dinma ya biyota hakan yasa cikin sauri tajuya zata fice,yajuyo ya kalleta ganin duk ta rikice,hartaje bakin qofar fita daga kitchen din yace"bakiji ba"
Cak taja ta tsaya awajan,ya harde hannunsa a qirjinsa yace"kishirya da yamma zamu fita"
Kanta kawai ta daga masa sannan tayi wuf tafi ce daga kitchen din tayi sama,murmushi yasaki yabude fridge ya dauki gorar ruwa yakoma falo yabude magungunan sa yafara sha.
tana rufe dakinta ta jingina da bangon qofar gabanta yana faduwa har kana hango yanda na shanunta suke sama da qasa saboda yanda take sauke numfashi, lumshe idonta tayi tana so ta daidai ta kanta, meyake damun sane?
ga budurwarsa agefe shida ya kamata yayi farinciki da kiran ta shine yake neman ya hargitsa mata lissafi,gashin kanta ta hargitsa tana barbaza shi ko zataji is'ka tana shiga cikin gashin nata saboda yanda yadauki zafi.
qarfe hudu na yamma yayi wanka ya shirya cikin qananun kaya riga da wandon jeans, rigar ruwan toka tana hade da hula,yasaka glass wanda yasake qwata kwalliyar tasa, falon yafuto yana zuba uban qamshi,Mawahib kuwa tun safe data shige dakinta taqi futowa falon bare tahadu dashi.
ganin bata falon yasa yafita compound yana waya qasa qasa,saida yagama wayar sannan yaduba number ta,number yazubawa ido yana kallo kamar yana tunanin wani abu,har zai kirata saiya fasa yatura mata text cewa yana jiranta.
tafuto daga wanka kenan tana shafa turare taji alamun shigowar saqo wayarta, "I'm waiting for you"
duk da batayi saving number ba tasan cewa shine zai turo mata saqon,cikin sauri ta qarasa shirin datake tazira abaya ta dauki Jakarta tafuto,tana zuwa compound ta hango shi kusada motarsa yana danna waya, cikin sauri ta qaraso wajansa, yanajin qamshin ta yadago ya kalleta, sannan yabude mata mota da kansa, babu musu tashiga, yazagaya yashiga yatada motar suka fita,suna hanya tana tunanin irin sabin halayen dayake nuna mata a yanzu,duk da batasani ba yana sonta ko baya sonta,saide abinda tasani daga nata 6angaren shine har yanzu batajin sonsa acikin zuciyar ta,saide bata tsaneshi ba,batajin tsanarsa kokadan aranta,wajan shopping sukaje,saida suka tsaya sannan tagane dalilin futowar tasu,kallonta yayi yace"muje"
Babu musu tafuto suka shiga tare,tunda suka shiga tsirarun mutane suke kallonsu,fuskarsa tana hade kamar koda yaushe,itace agaba yana binta abaya yana turo mata kwandon zuba kaya,Sai zagaye suke tarasa mezata dauka,ganin tunda tazo gidan yakawo kayan abinci da kayan maqulashe baisake siyowa ba,tasan may be wannan shine dalilin dayasa yace tashirya sutaho tare saboda taza6i abinda take yawan amfani dashi,kuma miskilanci yahana yayi mata bayani.
kayan shayi tafara dauka tajuya tazuba masa acikin kwandon,wasu yanmata su biyu sunzo wucewa suka kalleshi harda waiwaye,ganin wannan hadaddan gayen ne yariqe mata kwandon yana binta abaya kamar wata sarauniya,saide babu fuskar yimasa magana ganin yanda fuskarsa take ahade danma yasaka glass shiyasa baka gane zahirin yanda fuskar tasa take, sai zagayayyen sajensa daya qara qawata fuskar tasa kamar wani balarabe.
suka zagaya wajan turaruka tadauki wanda takeso,shima ta dauka masa,Sai wajan kayan miya anan tafi 6ata lokaci,sai naman kaza, bata dauki Jan nama ba saboda suna dashi dayawa,fridge din gefe ta kalla sannan tasaci kallon Yaya Captain taga hankalinsa yana kan waya,cikin sauri tazuge glass din fridge din, ta dauko robobin ice cream masu yawa, shima ta zuba, sannan ta kalleshi tace"yaya Captain nagama"
Cikin sauri yace"Okay"
Yatura sukaje yabada atm dinsa suka dauki kudin su,sannan yadauko kayan suka koma mota.
Daga nan wani boutique sukaje,yasake kallonta yace"muje"
Kanta tadaga, tafuto suka shiga ciki, tun kwanaki yaga wata doguwar riga suna tallarta,kuma rigar tamasa kyau,zata dace da irin dirin Mawahib,tunda yanzu sun riga sun futo gara su sayi rigar saisu koma gida gaba daya.
d'aya daga cikin ma'aikatan wajan ya nunawa rigar,cikin sauri tareda girmamawa ya musu iso wajan da rigar take,doguwar riga ce fara mai kama data amare,duka jikin rigar anyi masa ado da qananun stone masu walwali,dogon hannu ne da rigar sai mayafin ta madedeci mai shara-shara,rigar tana jikin mutum mutumi, Mawahib tasaki jiki da baki tana kallon rigar, duk yanda take daukan wankan dogayen riguna sai wannan rigar tatafi da imaninta, batasan mutumin daya rakosu wajan rigar yatafi ba,sai gani tayi yadawo yabawa Captain Aryan rigar acikin kwalinta, Captain ya duba kudin rigar yabashi atm dinsa, mutumin yajuya yabarsu awajan.
Captain Aryan yabata kwalin rigar yace"gashi"
Mamaki ya kamata,cikin tsananin murna ta kalleshi tace"yaya Captain nawane?"
Captain Aryan ya Kalli qwayar idonta yace"yes,kiyi kwalliya dashi"
Cikin sauri ta ajiye kwalin rigar, cikeda tsananin murna ta qarasa jikinsa tayi masa wata irin runguma,cikin farinciki tace"nagode Yaya Captain, Allah yaqara arziqi,thank you so much"
Captain Aryan dabaiyi tunanin wannan rungumar ba saiya qame awajan,dama tana fara'ah har haka?
yanda yakejin tudun nashanunta yana mintsinin qirjinsa hakan yasa ya lumshe idonsa,nan take yafara shiga cikin wani irin yanayi,ahankali kamar yana tsoron ta6ata, yadora hannunsa akan hips dinta yasake rungume ta sannan yagyada mata kansa,kwata kwata yakasa magana, Koda zaiyi maganar ma toba lalle muryarsa tafita ba(ππ)
Mawahib bata lura da yanayin dayake ciki ba kokadan,jin takun dawowar wannan mutumin daya basu rigar hakan yasa tasake shi cikin sauri.
Saide ta riga ta makara , mutumin yariga ya gansu,yayi murmushi yabawa Captain atm dinsa, sannan yajuya yabar wajan,Captain Aryan yadan daidaita kansa sannan cikin shaqaqqiyar murya ya kalleta yace"muje"
Cikin sauri tadaga masa kanta, tadauki rigar ta suka futo daga boutique din,yabude mata motar tashiga, sannan suka dauki hanyar gida.
Haly JASHERU venture's,munada kayayyaki masu kyau da inganchi ba algus da ha'inci, kayanmu daga Ethiopian ne, prdct dinmu muna Ethiopian magic hair oil, anti dandruff shampoo serum, bdy cream, hand cream, magungunan chuttuka da na mata masu inganchi da qara lfy ajikin dan
adam ga number kmr hk 07046665338 ko 07061664264 munada distributor ako Ina afadin kasarnan da ketare muna koya harkokin kasuwnchinmu ga masu bukata akan 5000 kacal
sannan munada tsuntsaye na kasashen waje tattabaru game bukata ko koya akwai riba kwarai aharkar mebuqata yasiya koya koya seyanemeni a number na kamar haka 07046665338 ko 07061664264, ku antayo ayi tafiyar daku,yar'uwa kikoyi sana'ah akan wannan farashi me sauqi kema ki kafa kankiππΌ
A hanya yana lura da'ita sai farinciki takeyi,sa6anin shida yahad'a uban gumi saboda har yanzu yanajin rungumar nan a jikinsa saboda bai ta6a zaton hakan daga gareta ba,suna zuwa gida David yataso da sauri suka dauki kayan shida Captain Aryan,ko tsinke bai bari ta dauka ba.
Kai tsaye kitchen tawuce tashirya duk abinda suka siyo sannan takai nata kayan daki sai wani farinciki takeyi, turarukan data siyo musu ta ajiye nata,sannan tashiga wanka,bayan tafuto adede lokacin ana kiran sallar magrib,saida ta gabatar da sallah sannan tadauki nasa turaren takai masa dakinsa,bata tarar dashi adakin ba tasan yafita masallaci ne,dakin nasa tsaf yake a gyare kamar dakin mace,qasa ta sauko tahada musu fruit salat,tadebi fulawa yar kadan tahada musu meat pie manya guda biyar tasaka isasshen nama aciki,sannan takai falo ta ajiye tadauki fruit salat dinma takawo, tabude fridge tadauko qanqara ta jefa acikin fruit salat din,tana qoqarin barin falon Sai gashi yashigo yana magana a waya qasa qasa,abincin data hada masa ya kalla, yazauna a kujera yagama wayar, sannan ya kalleta fuskarsa kamar koda yaushe yace"dawo kici abinci"
Babu musu tadawo tazauna dama sallar isha'i zataje tayi,saita haqura tazauna suka faracin meat pie din,yadauki remote yana sauya tasha,sosai yakejin dadin zaman nasu,baiqi ace sun qare daren yau ahaka ba.
Guda daya taci taji ta qoshi, tafara shan fruit salat din ahankali tana jiran yagama ta dauke komai tagudu sama,shikuwa yariga yagane so take tagudu tabarshi, hakan yasa yakeci kamar bayaso,ganin suna neman yin awa daya dawani abu hakan yasa yafara goge bakinsa da tissue, tana ganin haka tatashi takai komai kitchen,bata dawo wajan dayake ba tanufi sama zata tafi, yana ganin zata tafi cikin sauri yace"bakiji ba"
juyowa tayi tace"na'am"
"bani magani a dakina"
Cikin ladabi tace"to"
Sannan tawuce dakinsa tafara dube dube,can ta hango wata farar leda, tana dubawa taga magungunan aciki masu yawa, mamaki ya kamata, me Yaya Captain yake da wannan magungunan?
bashida lafiya ne?
Hannu tasa acikin ledar ta dauki guda daya taduba tagani,ta6e bakinta tayi ganin bata fahimci maganin kona menene ba, tafuto tarufe dakin sannan takawo masa,takoma kitchen tadauko masa ruwa takawo masa,bata tashi daga wajan ba tana satar kallonsa saida yasha Kala kalar magani sunkai guda biyar, sannan tadauko ledar tawuce sama.
Har qarfe shadaya da rabi nadare idonta biyu batayi bacci ba,sai yanzu ne abubuwan da Yaya Captain yake mata suke sake dawo mata arai, meyasa yake mata haka?
yaudara ce kokuma yan'uwan taka?
tasan cewa de soyaiya kam babu ita, Yaya Captain bazai ta6a sontaba, to amma meyasa yake qoqarin ganin ya faranta mata a kwanakin nan?
Wayarta dake silent tayi haske alamun shigowar saqo,cikin mamaki ta kallo agogon wayar taga qarfe shabiyu na dare,waye zai mata saqo,?
Number data gani ce tasa gabanta faduwa,a fili ta furta Yaya Captain?
saqon tabude taga yaturo mata "kin kwanta ne?"
Cikin mamaki tace anya lafiya kuwa?
bai ta6a turo mata saqo ba, Kuma a'irin wannan lokacin.
Acan dakin Captain kuwa a zaune yake a gadon yasaka wayarsa a gabansa yana jira ta masa reply,bazai Iya Samun nutsuwar bacci ba sai yaji daga gareta, yanason su dinga fira ta wayar ko yasamu bacci ya daukeshi.
Saqo ne yashigo, cikin sauri ya rarumi wayar zai duba saqon, bai bude ba saida ya kwanta sannan yabude yaga taturo masa "no,but zan kwanta yanzu"
mezaice mata Kuma?
Bawani surutu suke yiba,shibe Iya zance ba, da Ashraf nede saita gaji, to amma shi mezaice yanzu?
Cikin jin haushin rashin surutun sa yayi mata replay da "Ok sweet dream nd take care of yourself...."
Wayar yazubawa ido yana jira ko zata ce masa wani abu, shiru shiru bata turo masa komai ba, haka ya haqura shima yakife wayar tashi sannan ya lumshe idonsa yafara karanta Addu'ah ta bacci.
Washegari sassafe tatashi tayi ayyukan komai ta ajiye masa breakfast takoma sama ta kwanta takoma bacci, saboda tasan yau Monday zai fita aiki da wuri.
Captain kuwa yana dawowa daga wajan motsa jiki kawai wanka yayi,yafuto yaci abinci yazauna afalon yana shan magungunan sa yana kallo kad'an kad'an,yau babu inda zai fita yariga yanemi excuse,har qarfe goma na safe bata futo ba, yayi mamaki sosai,yadade yana falon har wajan goma da rabi, sannan yakashe kallon yadauki fillon kujera guda daya yadora a cikinsa ya rungume shi, sannan ya lumshe idonsa yafara bacci.
Mawahib bata tashi farkawa ba sai wajan qarfe goma shadaya na safe,tayi wata irin miqa sannan tawuce toilet tayi wanka a nutse,tashirya cikin riga da wando tasaka hula akanta,riga da wandon sunada dan fadi tasake acikin kayan sosai,haka yadin kayan yanada santsi amma ba sosai ba,qasa ta sauko domin cin abinci, batayi tunanin yana falon ba,tana zuwa saitayi turus ta tsaya tana kallonsa,tayi sauri taduba wayarta taga de yau Monday,amma yata ganshi a kwance anan?
tajuya gefe taga magungunan sa awajan, ta tuna jiya ma yace tabashi maganin zaisha,Kuma Bayan ta kwanta yamata text yana tambaya ko tayi bacci to Kode bashida lafiya ne?
Ko ciwon ne yasa yaqi fita aiki shida baya wasa akan zuwa wajan aiki?
Kokuma jikin nasa ne yatashi shiyasa yake tambayar ta a text yana nufin idan bata wani abu taje ta taimaka masa?
Shi miskilancinsa yamasa yawa, bazai futo fili yafadi abinda yakeso ba,to amma kuma aiyace mata ta kwanta tayi bacci medadi.
Matsowa tayi kusada kujerar dayake kwance,takai hannunta zataji jikinsa koda zafi,saitayi sauri ta janye hannunta tafasa, ta kalli tulin magungunan dasuke gefe tasan cewa ba kalau ba, matso da fuskarta tayi dab da tashi fuskar ko zataji jikinsa da d'umi.
Captain Aryan yana jinta tun lokacin datazo wajan yafarka saboda qamshin ta daya shaqa, yanajin qamshin turaren yafarka amma bai bude idonsa ba,yanda yaji numfashinta yana sauka a fuskarsa sai hakan yake qoqarin jefashi awani irin yanayi, Mawahib kuwa da taji bataji wata alama ta zafi ba saita dago kanta kad'an, tamaida kallonta kan kyakykywar fuskarsa,zallar kyansa take gani,jan lips dinsa ta kalla tafara tunani, Yaya Captain yanada kyau sosai, amma tarasa meyasa takasa jin sonsa aranta kamar yanda sauran mutane suke sonsa.
Ajiyar zuciya tasauke zata tashi tawuce kitchen,Captain Aryan dayaji zatabar kusa dashi cikin sauri ya fuzgota tafado jikinsa,cikin tsoro tasaki wata yar qaramar qara,cikin sauri yasaka hannunsa ya rufe mata bakinta sannan yazubawa fuskarta ido yana kallonta,itama shi take kallo,fuskarsa da bacci da rashin bacci koda yaushe haka take babu fara'ah, cikin muryarsa tame bacci yace"me kike kallo?"
girgiza kanta tayi sannan ta janye hannunsa daga bakinta tace"dama....dama..damafa nayi tunanin bakada lafiya ne,shin...shine"
saitayi shiru takasa qarasawa,ta sunkuyar da kanta qasa tana kallon yanda tayi male male akan jikinsa kamar tasamu katifa.
Wani irin dan qaramin murmushi yayi,har zaice shine daga tunanin rashin lafiya kika tsaya kina qaremin kallo,? to kuma sai yayi shiru yashareta,idonsa ya lumshe sannan yabude ya kalleta yace"lafiyata kalau,karki yi girki yau,idan kingama abinda kike,qarfe biyu zamu fita"
Cikin sauri ta daga masa kanta, sannan tafara kokarin tashi daga jikinsa,yanda take motsa jikinta anasa hakan yasa yayi saurin lumshe idonsa yanajin wani irin dadi,fatansa daya, Allah yasa idan sun fita ya'iya kallon idonta ya bayyana mata abinda yake cikin ransa ko zai samu ta yafe masa takuma amshi soyaiyar sa.
yanajin tatashi,shima yatashi yayi sama saboda daga haduwar nan tasu tasashi cikin yanayin da bazai Iya tunkaran masallaci batare da wanka ba(π)
kamar yanda yafada qarfe biyu daidai suka fita,yau wankan laffaya tayi,baqar laffaya ce me adon stones,kasancewar ta fara hakan yasa laffayar tayi mata kyau sosai,shikuma yasaka manyan kaya na shadda, saide baisaka babbar riga akai ba,bata ta6a ganinsa da manyan kaya a Abuja ba,kullum saide qananu kamar ba bahaushen mutum ba,amota babu wanda yake magana,Mawahib tana tunanin yau Kuma inane zasuje dahar yaqi zuwa aiki saboda fitar tasu?
shikuma yana tunanin yanda zai fada mata yanda yakejin ta acikin ransa.
wani wajan cin abinci sukaje,wajan yahadu sosai an qawatashi Iya qawatuwa,babu kowa awajan,haka duk kujerun dasuke wajan iya kujera daya ce aka shirya shirya abinci da lemuka akai, hakan ya tabbatar mata wajan yakama gaba daya kenan, Captain Aryan ya Kalli ko'ina yaga tsarin yamasa kamar yanda sukai magana dasu ta Email,wajan zaman suka qarasa yaja mata kujera ta zauna sannan shima yazauna,kallonsa tayi taga yanata walwala,dakansa yatashi yafara zuba mata komai, cikin sauri tace"yaya Captain kabarshi zan zuba dakai...."
Kafin ta qarasa cewa dakaina,yadora hannunsa akan qaramin lips dinta yace"shiiiit"
Babu musu tayi shiru,shine yazuba mata komai yatura mata gabanta, sannan shima yazuba,d'aya daga cikin ma'aikacin wajan yazo cikin ladabi yace"yalla6ai akwai abunda kuke buqata aqaro ne?"
Hannu kawai Captain yadaga masa alamun cewa babu komai, cikin girmamawa yajuya yabasu waje.
Abincin sukaci cikin nutsuwa,har yanzu Mawahib tana tunani aranta meyasa yau suka futo cin