Showing 75001 words to 78000 words out of 110331 words
din tafita, Nabiha ta zauna agefen gadon tace"Mawahib?,sannu Mawahib,gaskiya kinyi kokari,bakya tsoron kisamu matsala?"
Murmushi tayi tace"Nabiha likita yace zuciyarta zata samu matsala idan ba'a saka mata ba,kuma irin jini nane,dan Allah nabata ai,badan halin datake nunamin ba"
Nabiha tace"eto hakane, aikuwa yanzu wallahi saitaji kunya,ai tanaji likitan yace kece kika bata jinin,zamuga ya zatayi idan ta warke "
Mawahib tayi murmushi tace"Allah ya shiryeki Nabiha,Nabiha wai tayaya kike gane Yaya Ashraf idan suka hadu da Yaya Aryan? ni yanzu dasuka hadu duk saina kasa gane menene banbancin su, har yanzu bana ganesu,saide idan Naga fuskar mutum daya adaure to shine zan gane"
Nabiha tayi dariya tace"idan zamu futo wani turaren daban nake fesa masa ba irin Wanda suke amfani dashi shida Yaya Captain ba,to zoben hannunsu iri daya,kuma a'irin dan yatsa daya,sannan su saka kaya iri daya, hula daya, agogo daya,turare daya,waya iri daya, tayaya zan ganesu idan suka hadu? Yanzu kuwa tunda gida daya nake dashi wallahi sauya masa turare nake, Kuma baya cewa komai,"
Mawahib ta gyara kwanciyarta tace" to idan qamshin turaren ya sheqe fa?"
Tace"to daga nan kuma saina barwa Allah sauran"(π)
Mawahib tayi dariya adede lokacin suka dawo dakin, Captain ya zauna kusada ita yabude mata maltina sannan yatashe ta zaune, yajanyota jikinsa kad'an, sannan yafara bata,saida tasha kusan rabin gongoni sannan ta kawar da kanta tace"ya'isa"
Cikin sigar rada yace"kin tabbata?"
Kanta ta daga masa.
Ashraf dayake tsaye agefensu yace"sannu Mawahib,Allah yasaka miki da Alkhairi"
Murmushi tayi batace komai ba.
Ashraf ya Kalli Captain yace"muje wajan Momy tunda ga Nabiha suna tare"
Cikin gamsuwa yadaga kansa,sannan ya sunkuya yasakar mata kiss akumatunta,yariqe fuskarta da hannunsa biyu, yayi qasa da muryarsa yace"karki sake irin haka,because idan kika samu matsala Nima matsalar ki tashafeni"
Qasa tayi da idonta batare da tace komai ba, ahankali yasaki fuskarta sannan suka fice daga dakin.
Nabiha tasaki wata nauyaiyar ajiyar zuciya tace"irin wannan soyaiya haka Mawahib?"
Cikin mamaki Mawahib tace"soyaiya kuma?"
Nabiha tace"emanah, gashinan duk kin rikita Yaya Captain ko kunya ta baiji ba yake miki kiss"
Mawahib ta girgiza kanta tayi shiru,tana tunani,har yanzu bazatace ga sahihin abinda take ji akan Yaya Captain ba,tasan cewa de bata tsanar sa.
Nabiha tadawo kusa da ita ta zauna sannan tafara bata fruit din dasukazo dashi.
Kusan awarsu biyu itada Nabiha adakin, doctor yazo ya tambaye ta ko akwai abinda takeji tace masa babu damuwa, bayan yafita suma suka futo daga dakin,ta kalli Nabiha tace"rakani muje nadauko kayan Momy dana shanya dazu"
Nabiha tace"muje dama nagaji da zaman"
kayan sukaje ta dauko ta ninke su, sannan suka juyo,zasu koma dakin Hajiya kilishi sukaga wata mata ankawo ta tana murqususu cikin naquda,jikin Nabiha yayi sanyi tace"nashiga uku Mawahib wannan haihuwa zatayi"
Mawahib tace"tabdi lalle abun na gaske ne,kingafa daqyar take tafiya baiwar Allah,wannan wahala ahaka matar abokin Yaya Captain take cewa zan haifi yanbiyu? bazan iyaba"
Nabiha tace"aikuwa tunda mijinki yanbiyu ne ko baki haifa yanzu ba, agaba saikin haifa"
Murmushi Mawahib tayi tace"kema haka ai"
Daga nan suka shiga daki,kamar dazun har yanzu duka mazan gidan nasu suna cikin dakin,harda Mamy da mama Sadiya,Ashraf da Aryan suna gefen Hajiya kilishi.
Duk yanda Hajiya kilishi ta addabi duka 'yan gidan Alqali da tashin hankali,hakan baisa sun gujeta ba,tun safe gaba dayansu suna cikin dakin sun sakata agaba kamar idan suka matsa zata koma halin jinyar.
Suna ganin Mawahib sukayi mata sannu ta amsa,Alqali ya kalleta cikin kulawa yace"bakyajin komai de ko?"
Cikin ladabi tace"banajin komai Daddy"
Kafin yasake magana ta kalli Hajiya kilishi dake zaune akan gadon tanashan Yagourt,amma takasa dago kanta ta kalli kowa, cikin ladabi ta qarasa tabawa Mama Sadiya kayan Hajiya kilishi,sannan ta zauna kusada Mamy tadaga kanta tasake kallon Hajiya kilishi sannan tace"sannu da jiki Momy"
Cikin sanyin jiki Hajiya kilishi tace"Sannu Mawahib,Allah yayi miki Albarka"(π³ππ»ββοΈπ²)
Cikin sauri mutanan dakin suka juya suna kallon Hajiya kilishi,babu wanda furucin Hajiya kilishi bai bawa mamaki ba,Captain Aryan yaji wani irin dadi aransa,Ashraf kuwa murmushi yayi.
Mamakin su bai gama yankewa ba sukaji Hajiya kilishi tana cewa Mamy "Maryam nagode,Allah yasaka da Alkhairi"
Mamy tayi murmushi tace"babu komai Yaya,Allah yabaki lafiya"
Sun dade adakin sannan sukai shirin tafiya,Captain Aryan yadauki wayarsa yaturo wa Mawahib saqo,wayarta tana hannunta taga shigowar saqo,dubawa tayi taga yaturo mata "idan zasu tafi karki bisu kijirani"
wani irin taqaici taji aranta, saboda taso tabi Mamy su tafi gida, kamar tafashe da kuka ta jefa wayar acikin jaka ko replay batayi masaba.
Bayan su Mamy sun tafi itada Nabiha ne suke dan zance qasa qasa suna kallon wayar Nabiha, idan Nabiha zata mata gulma saita rubuta mata ta wayar ita kuma saita karanta.
Basu bar asbitin ba sai dare,Nabiha tabi Ashraf, shikuma Captain Aryan yadauki Mawahib suka yiwa mama Sadiya da kilishi sallama suka tafi.
Yana driving yana juyowa yana kallonta,ita kuwa luf tayi acikin kujera saboda tagaji sosai,abakin titi ya Parker motar yatsaya, sannan ya juyo ya kalleta,yaruqo hannunta yace"meyake faruwa?"
Cikin yanayin gajiya tace"inajin gajiya ajikina ne kawai"
Cikin kulawa yace"kinajin jiri ne?"
Girgiza kanta tayi tadan lumshe idonta tace"kawai gajiya nakeji"
Fuskarsa cikeda damuwa yarage sautin muryarsa yace"meyasa kika bada Jininki?"
Cikin sanyin murya tace"tana buqatar jinin itama,ka manta kaima ka temaki mahaifina?"
Idonsa ya lumshe sannan yabude yafara kallonta, yarasa wanne matsayi zai bata acikin zuciyarsa, abinda yasani shine tariga tazama komai nasa,baisan menene acikin Zuciyarta game dashi ba,baisan meyasa tabawa Momynsa jini ba, soyaiyar datake masa ne kokuma tsabar tausayi ne?
Hannunta yasake riqewa sannan ya kalli cikin idonta yace"MAWAHIB...."
Wannan ne Karon farko da taji ya kira Sunan Mawahib a bakinsa bayan Ruqayya, cikin gajiya ta sake lumshe idonta, sannan ta kalleshi da idonta me yanayin bacci, tace"um.."
Lokaci daya idonsa ya kada yayi jajir kamar zaiyi kuka sannan yace"meyasa bakya sona? mekikeso nayi miki kisoni?"
Idonta ta lumshe cikin damuwa, sannan ta bude tace"Yaya Captain inajin bacci kuma nagaji"
Cikin sauri yagyada kansa, sannan yace"I'm sorry,bari muje gida,zakiyi baccin yanzu kinji?"
Kanta ta daga masa, sannan yasaki hannunta yaja motar suka bar wajan, kafin su qarasa gida saida yatsaya yasai mata kaji gasassu,sannan yasake tsayawa awani store yabude boot din motar aka saka masa katan katan din maltina ta gwangwani, sannan yakoma motar yaja suka tafi gida.
Da taimakon maigadi aka shigar mata da kayan daya siyo mata part din Mamy,Mamy tana zaune sai ganinsu tayi ita dashi,gakuma megadi yana shigowa da kaya.
Mawahib zubewa tayi a kujera, shikuma ya tsugunna tareda sunkuyar da kansa qasa cikin girmamawa yace"Anty Ma-my barka da hutawa"
"yawwa Captain,ita kuma wannan menene yake damunta?" ta qarasa maganar tana kallon Mawahib.
Kallon Mawahib din yayi yace"tace tanajin gajiya ne,kuma tanajin bacci "
Mamy ta bude idon Mawahib ta kalla sannan tace"jinin data bayar ne,kuma batasha maltina dayawa ba,kamata yayi tasha sosai, tashi kije fridge akwai sauran maltina me sanyi saikisha kuje ki kwanta zuwa safe zakiji ki normal"
Kansa ya sosa kadan sannan yace"Anty Ma-my, tayi baccin tare dake"
Mamy tace"to shikkenan rakata dakinta,bari na kawo mata Maltinar"
Bai tashi ba saida yaga Mamy tanufi fridge dinta tabasu baya,kawai yasaka hannu ya dauketa cak, yanufi dakinta da'ita,kwantar da'ita yayi akan gadon sannan yashafa kanta,yace"sannu"
Daga masa kanta tayi,Mamy taturo dakin tashigo takawo mata maltina, sannan ta fice tabarsu,yana ganin fitar ta yatashi yadawo gadon yadauke ta ya d'orata akan cinyarsa, sannan ya kwantar da kanta akan qirjinsa yabude maltina yafara bata, saida ta shanye daya, sannan yasake bude wata, taqara sha kad'an, sannan tafara girgiza kanta tace"naqoshi"
Cikin sigar rada yace"dan qara wannan dan kadan"
Sake sha tayi,ta kawar da kanta,yasake bata maltinar cikin lallashi yace"sha wannan to dagashi shikkenan"
Kukan shagwaba tasakar masa,ya lumshe idonsa yabude,sannan cikin dabara yasake bata tasha, ya ajiye sauran tareda kwantar da kanta a qirjinsa, yana shafa kanta,sun dad'e ahaka har bacci ya dauketa me nauyi, saida ya tabbatar tayi bacci sannan ya kwantar da'ita, ya sunkuya yadora bakinsa akan lips dinta,yayi kissing dinta, sannan ya futo daga dakin.
Yana futowa yaga falon babu kowa,cikin sauri yafice yanufi dakinsa yayi wanka sannan ya rungume fillo a qirjinsa ya lumshe idonsa yana tunanin ta har bacci ya dauke shi.
Washegari takama Monday,tun asuba Captain yake faman kiran wayarta yanajin yanayin jikin nata, ta kuma tabbatar masa ta warke ras.
Saida gari ya waye sannan yashiga part din,tare sukai breakfast shida ita da Mamy da Abba,tanajin yanda yake ta6o mata qafarta da tasa qafar ta qasan table din dasuke zaune, amma saita maze bata nuna komai ba, saide tadan kalleshi kad'an sannan ta kawar da kanta.
Abba yatashi zai tafi aiki, Mamy ma tayi shirin tafiya asbiti tadauki abincin su Hajiya kilishi, Abba zai fara kaita asbitin takai musu abincin, sannan ya rakata wajan nata aikin sannan shima yawuce nasa.
Su kadai suka bari afalon,hakan ba qaramin dadi yayiwa Captain ba,domin kuwa suna tafiya yasaka ta a jikinsa, ahaka suka wuni,banda shagwa6ata babu abinda yakeyi,bai tafi asbiti ba sai yamma dede lokacin da Mamy ta dawo kenan, bai yarda yabarta ita kadai a gidan ba,acan asbitin ya tarar da Ashraf,basu dawo gida ba sai dare kamar kullum.
haka rayuwar gidan Alqali ta kasance har tsawon sati daya,tsawon wannan lokacin Mama Sadiya ce me zama da'ita,Mamy kuma kullum zata kai musu abinci sannan tawuce aiki,zuwa wannan lokacin jikinta ya warware sosai,saide rama irinta rashin lafiya kafin jikinta yagama komawa daidai.
Azaman Aryan da Mawahib kuwa babu abinda ya sauya,bai ta6a tunanin neman haqqinsa awajan taba,koda yaushe kokarin ganin ya kyautata mata yake,kuma bai ta6a jin haushinta dan taqi baiyana masa menene acikin zuciyar taba.
yau aka sallamo Hajiya kilishi,mutane sai sintirin zuwa gidan suke ana yimata yajiki,gaba daya sanadin wannan rashin lafiya yasa Hajiya kilishi ta sauya kamar wanda aka sauya ta,tazama shiru shiru kamar ba'ita ba,cikin ranta kuwa tsantsar nadama ce take damunta,dama ance baka gane masoyinka sai kana halin jinya,tunda Maryam tazo da yarinyar nan cikin gidan Alqali shedan yake kitsa mata abubuwa marasa kyau cikin ranta, bayan babu abinda yarinyar ta tsare mata,ubangiji ya nuna mata Ishara akan danta Aryan mafi soyuwa aranta,Allah yahada aurensa da Mawahib, duk da haka bata saduda ba,ajiyar zuciya ta sauke bayan tagama tunani ta Kalli Ashraf da Aryan dasuka sakata agaba Ashraf yana zaune aqasan kujera yana game awayarsa Aryan kuma yana zaune agefenta akan kujera yayi shiru.
Kallonsa tayi tace"Baba na kamar kanada damuwa, meyake faruwa?"
kallonta yayi yana shakkar yimata maganar abinda yake ransa, cikin sanyin jiki yace"Momy dama inaso zanyima yarinyar nan lefe ne"
Cikin sauri tace"Mawahib?"
Kansa ya sosa yace"eh Momy"
Tace"kuyi musu mana,nima akwai wasu kayan awajena,idan kun gama sai ahadasu gaba daya"
Ashraf yadaga kansa ya kallesu yace"Momy to guda nawa zamu siyo?"
Hajiya kilishi tace"toku bawa Maryam kudin saita hado muku komai mana"π€
Ashraf yace"shikkenan ma, yafi sauqi"
Captain Aryan ya6ata fuskarsa cikin shagwa6a yace"Momy...gaskiya nide gara kihada min da Kanki"
Hajiya kilishi tayi murmushi tace"ina ganin ikon Allah ni kilishi,au bazaka bawa surukar ka tahada muku gaba daya ba? yanzu Baba na inani Ina shiga kasuwa? ita Maryam din de itace yar zamani duk zata sako muku abinda yadace, amma tunda baka so toka bawa Sadiya saita hadoma"
Cikin sauri yace"eh zan bata"
Murmushi tayi tajashi jikinta tana shafa kansa.
Adede lokacin Alqali yashigo falon, yana ganinsu yayi murmushi yakalli Hajiya kilishi yace"Kilishi maman biyu,kede kawai burinki kisa yaranki a gabanki kina lailayasu kamar jarirai"
Ashraf yayi murmushi yace"Daddy Aryan takewa haka,shine yaro"
Cikin sauri Captain Aryan yadago kansa daga kafadar Hajiya kilishi yace"waye yaron? Momy kidena bari yana cemin yaro"
Hajiya kilishi tace"yazan masa ne Aryan? kutashi muje kurakani part din Maryam"
Alqali yayi murmushi yace"lafiya deko?"
Cikin sanyin jiki tace"ai harda kai zamuje Alhaji,zan sake bawa Mawahib haquri,tunda gashi an sallamoni nadawo gida"
Gaba dayansu su ukun kallonta sukai cikeda jin dadi,Ashraf yayi wulli da wayar hannunsa yace"muje Momy"
Cikin jin dadi suka nufi part din Mamy gaba dayansu.
Haly JASHERU venture's,munada kayayyaki masu kyau da inganchi ba algus da ha'inci, kayanmu daga Ethiopian ne, prdct dinmu muna Ethiopian magic hair oil, anti dandruff shampoo serum, bdy cream, hand cream, magungunan chuttuka da na mata masu inganchi da qara lfy ajikin dan
adam ga number kmr hk 07046665338 ko 07061664264 munada distributor ako Ina afadin kasarnan da ketare muna koya harkokin kasuwnchinmu ga masu bukata akan 5000 kacal
sannan munada tsuntsaye na kasashen waje tattabaru game bukata ko koya akwai riba kwarai aharkar mebuqata yasiya koya koya seyanemeni a number na kamar haka 07046665338 ko 07061664264, ku antayo ayi tafiyar daku,yar'uwa kikoyi sana'ah akan wannan farashi me sauqi kema ki kafa kankiππΌ
******
Mamy ta kalli Mawahib tace"tunda Yaya kilishi ta warke nasan kun kusa tafiya ko?"
Mawahib da hankalinta yake kan waya tace"wallahi bansani ba Mamy,banyi maganar dashi ba"
Mamy tace"to kafin kusa ranar tafiya saiki fara zuwa wajan gyaran jiki,nayi magana da Hajiya Balaraba,saiki fada masa zaki fara zuwa gobe,kona kwana biyu ne a miki kafin kutafi "
Tace"to Mamy zan fada masa"
"magungunan dasuke wajanki wanda na aiko miki sun qare ko?"
Mawahib ta kalleta,sai yanzu nema da Mamy tayi mata maganar magani sannan ta tuna da maganin da Matar Captain Habib tabata,yana cikin Jakarta,ta kalli Mamy tace"duka na shanye,turare ne bai qareba,yana can"
Mamy tace"to turaren babu qamshi ne? ko bayaso kina amfani dashi?"
Murmushi tayi tace"Yaya Captain din? besan ma Ina amfani dashi ba"
Mamy ta jinjina kanta daga haka bata qara magana ba,saide tunanin ta yagama bata Mawahib da Captain babu abinda yata6a hadasu, idan kuwa sunyi mu'amular aure toda kanta zata nemi maganin saboda yanada kyau sosai,idan taga Aryan din yana rawar jiki akanta lokacin da zata nemi wani ma babu wanda yasani.
Adede lokacin su Hajiya kilishi suka shigo falon,cikin farinciki Mamy ta kallesu tana tashi tsaye tace"sannunku da zuwa,Yaya meyasa kika taso keda bakyajin dadi aida kinmin waya nata so"
Hajiya kilishi tace"A a jiki ai yayi kyau Maryam,babu komai wallahi"
Mamy ta kalli Mawahib tace"kawo musu ruwa"
Sannan ta kalli Alqali cikin ladabi tace"Yaya Bissmillah"
Zama yayi a kujerar, sukam su Ashraf tuni sun zauna,Mawahib takawo musu ruwan takoma zata dauko lemo Hajiya kilishi tace"Mawahib dawo ki zauna,Maryam kibarta ta dinga hutawa mana"
Cikin sauri Mawahib ta kalli hajiya kilishi sannan ta nemi waje ta zauna, Mamy ta sunkuyar da kanta qasa tanata mamakin Hajiya kilishi.
Hajiya kilishi tajuya ta kalli Mawahib tace"Mawahib wajanki nazo, zuwa nayi nasake yimiki godia akan taimakon dakika min a asbiti,haqiqa naga aya,kuma na dauki darasi,inaso ki yafemin duk abubuwan dasuka faru abaya, Sharrin shaidan ne,kiyi haquri kiyafemin kodan mijinki Aryan"
gaba dayansu sai jikinsu yayi sanyi,Alqali yayi shiru yana sake godewa Allah acikin ransa, ashe yana raye zaiga irin wannan ranar, kafin yagama tunanin sa yaji Mawahib tace"babu komai Momy, nayafe miki"
Hajiya kilishi tace"Allahu Akbar,haqiqa ni kilishi Naga ikon Allah,rayuwa kenan,Allah ya miki Albarka Mawahib"
Ahankali Mawahib tace"Amin"
Hajiya kilishi tajuya takalli Mamy tace"Maryam kiyi haquri,daga yau namiki alqawari insha Allahu bazaki sakejin wani tashin hankali awajena ba, abubuwan dasuka faruwa Dan Allah na roqeki ki manta dasu, ki daukeni amatsayin yayarki daga yau"
Cikin farinciki Mamy tace"wallahi babu komai Yaya, yawuce, Allah yayafe mana baki daya"
Cikin farinciki Hajiya kilishi tace"nagode Maryam"
tajuya tasake kallon Mawahib da kanta yake qasa tace"Mawahib...? Allah yabaku Zaman lafiya "
Cikin jin kunya Mawahib tatashi tawuce dakinta, Captain Aryan yayi murmushi yabita da kallo.
Sun dan jima afalon,har Abba yadawo ya gansu,shima yazauna sukaci gaba da firarsu gwanin sha'awa, sannan Alqali ya rufe musu taro da Addu'ah suka tafi nasu part din.
Da daddare suna zaune a dining itada Mamy bayan sungama cin dinner,tadauki wayarta tatura masa saqo "Yaya Captain inaso gobe zanje wajan gyaran jiki"
Alokacin da saqon yashigo wayarsa yana wajan Mama Sadiya yana fada mata irin kayan lefen dayake so a hadowa Mawahib,saqon nata yaduba yagani yayi murmushi, sannan yayi mata replay yace"send me your account number"
tura masa tayi sannan ta ajiye wayar,Mamy tafuto daga dakinta tabata magani a cup tace"ungo shanye kiban cup din"
Ganin yanda Mamy ta tsareta yasa babu musu ta shanye maganin sannan tabata cup din.
Alert ne yashigo na dubu dari cikin wayarta, mamaki ya kamata, ta nunawa Mamy alert din tace"Mamy nafada masa shine yaturo min wannan kudin"
Mamy tace"har dubu dari? lalle Captain gyaran jiki yakeso dakyau"
Mawahib taturo bakinta gaba tatashi tawuce dakinta cikeda shagwa6a, Mamy tayi murmushi takira Hajiya Balaraba tafada mata bayan gyaran jikin ayi mata hadin magunguna masu kyau hadin amare ta zaunar da'ita tasha komai agabanta, yanzu zatayi mata alert.
Hajiya Balaraba tanajin zancen alert tasan Mamy ba wasa,cikin tabbaci tace"karki damu Hajiya Maryam,ai tunda kin kawo ta wajena kingama komai,inde nayi mata gyaran jikin nan ko mijin ta kasa ganeta zaiyi,sannan zanyi mata hadin nafi qarfin reni,ina tabbatar miki daqyar mijinta zai iya kallon wata yarinyar amatsayin mace,saina sata ta gigitashi banida sasssauci ta wannan fannin"
Mamy tayi murmushi tace"to shikkenan saita zo,zakiji alert yanzu yanzun nan"
Daga nan sukai sallama Mamy tawuce daki,tana jiran zuwan Abba Ashraf yakirata awaya yake fada mata maganar lefensa, suka tattauna abinda zasu tattauna sannan sukai sallama
Kamar yanda Mamy ta tsara washegari tun sassafe Mawahib tabar gidan,tatafi gidan Hajiya Balaraba,bata dawo ba sai yamma lis,tun aranar yau din Mamy tafara ganin canji,farar fatar Mawahib din taqara yin fresh,kasancewar tana dadewa bata dawo da wuri ba, hakan yasa tana zuwa gida take kwanciyar ta tayi bacci,Mamy tana lura da shige da ficenta kokadan taqi bata damar da zata hadu da Captain,tafi son agama yimata gyaran jikinta tsaf,sannan ta tattara ta sukoma Abuja.
kwananta biyar tana zuwa kuma yaune qarshe,tana dawowa tawuce part dinsu cikin kasala saboda kwana biyu wannan magungunan da ake bata yasa take yawan jin feeling ajikinta.
Acikin kwana biyar dinnan su Mamy suka gama hada komai na lefe, apart dinsu Nabiha suke ajiye komai wajan Mama Sadiya.
******
Hajiya kilishi ta Kalli akwatunan dasuke gabanta guda ashirin,tace"wanne ne na Mawahib?"
Captain Aryan ya sosa kansa yace"wannan ne guda takwas,na Ashraf kuma guda shabiyu"
Cikin sauri ta kalleshi tace"guda takwas ai yayi kad'an,guda shabiyu zaka mata,kaikuma Ashraf kasake tura mata wani kudin asiyo da kayan baby,Babanah kaikuma kafitar da kudi akaro mata wasu akwatunan guda hudu, sai aqara musu da kayan wajena"
Cikin tsananin mamaki Captain Aryan ya kalleta,yayi tunanin zatayi fada shiyasa lokacin da mama Sadiya tace asiyo shabiyu yace a a saboda kar Momy tayi fada asiyo guda takwas, amma abun mamakin gashi itada kanta take cewa yayi kad'an, lalle Momy ta sauya.
Sumar kansa ya shafa yace"to Momy"
Kafin tasake magana wayarsa tayi qara,ganin Captain Habib ne mekiran yasa yadauka cikin sauri, bayan sun gaisa Captain Habib yace"yaushe zaka shigo ne? akwai damuwa fa"
Captain Aryan yace"meyake faruwa? Ina tunanin mafa hutu zan dauka gaskiya"
Captain Habib yace"saboda kayi amarci dakyau kenan"
Saida yasaci kallon Momy kilishi yaga hankalinta baya kansa sannan yace"eh wallahi"
Captain Habib yayi murmushi yace"hakan yanada kyau,amma yanzu de ya kamata shirya kataho anyi mana rashi wallahi,dazu muka samu labari ankashe Captain Shu'aibu awajan yaqin