Showing 72001 words to 75000 words out of 110331 words
tana mamakin meyasa Yaya Ashraf yake kira a'irin wannan lokacin?
Saboda taga shine me kiran.
Dauka yayi sannan yazauna abakin gadon yace"Ash..."
Cikin damuwa Ashraf yace"tun qarfe uku nake kiranka fa,ina kasa wayarka ne? Momy batada lafiya cikin dare Daddy yamin waya muka tafi asbiti,yanzu haka muna asbitin,jikina yayi sanyi da rashin lafiyar ta Aryan..."
Cikin sauri yatashi tsaye yace"what innalillahi...,meyake damunta to? meyasameta? kode saboda nine?"
Ashraf yace"tun ranar dakukazo gida tace kasaki Mawahib,yan'uwanta sukazo har gida suka lallashe ta, tun daga ranar tadaina kula kowa,daga nan kuma sai zazza6i kad'an kad'an,nafi tunanin tasaka abun aranta ne,dazu tana aman jini har mukazo asbitin"
Dafe kansa yayi da hannunsa sannan yace"Ash inada laifi awajan Momy,nasan cewa bazata yafemin ba saboda banbi umarnin taba,bansan Yaya zanyi ba"
Ashraf yace"Aryan,kadena wannan tunanin,Momy zata so aurenku,kuma insha Allahu watarana zatayi alfahri da aurenku"
Cikin damuwa yace"Allah yasa,zamu taho yanzu"
Wayar ya ajiye ya Kalli Mawahib da jikinta yayi sanyi,saboda duk taji abinda yafaru a wayar,lokaci daya, kuma karon farko da taji tausayinsa ya kamata, cikin sanyin jiki yace"Allah yabata lafiya"
Kansa ya gyada yace"Amin,kiyi sallah zan dawo daga masallaci saimu tafi"
Ta amsa masa sannan tafuto daga dakin nasa tawuce nata dakin, wanka tayi sannan tatada sallah, tana idarwa tatashi ta shirya cikin doguwar riga ta abaya,ta dauki abinda zata buqata tasaka ajaka sannan tafuto falo,shima yana idar da sallar gida yataho,sai waya yakira ya fadawa Captain Habib komai, yana zuwa ya shirya suka futo, lokacin har gari yafara Haske, magana yayi da David sannan yadawo suka wuce airport.
Haly JASHERU venture's,munada kayayyaki masu kyau da inganchi ba algus da ha'inci, kayanmu daga Ethiopian ne, prdct dinmu muna Ethiopian magic hair oil, anti dandruff shampoo serum, bdy cream, hand cream, magungunan chuttuka da na mata masu inganchi da qara lfy ajikin dan
adam ga number kmr hk 07046665338 ko 07061664264 munada distributor ako Ina afadin kasarnan da ketare muna koya harkokin kasuwnchinmu ga masu bukata akan 5000 kacal
sannan munada tsuntsaye na kasashen waje tattabaru game bukata ko koya akwai riba kwarai aharkar mebuqata yasiya koya koya seyanemeni a number na kamar haka 07046665338 ko 07061664264, ku antayo ayi tafiyar daku,yar'uwa kikoyi sana'ah akan wannan farashi me sauqi kema ki kafa kanki๐๐ผ
Qarfe tara daidai a Airport ta musu,kasancewar sun dade kafin jirgin yatashi, Ashraf ne yaje Airport din daukosu,tundaga nesa yahango su yaga sun qara wani fresh kamar daga wata qasar suka dawo,suna qarasowa wajansa Aryan ya rungume shi, sannan suka shiga mota,duka su biyun suna gaba, Mawahib tana baya,saida suka fara tafiya sannan ta gaida Ashraf, ya amsa mata cikin sakin fuska.
Gida suka fara zuwa,suka ajiye Mawahib, sannan suka wuce asbitin, Mamy tana kitchen itada Mama Sadiya kasancewar weekend ne sai ganin Mawahib sukayi,cikin murna taje ta rungume Mamy.
Mama Sadiya tace"mutanan Abuja,kun qaraso kenan?"
Cikin farinciki tace"mama munzo wallahi, Ina Nabiha?"
"Nabiha tana gidanta,itace ma take fadamin Ashraf yakira Aryan din ai yasanar dashi, shine nace to yau Kuna hanya"
"hakane tun asuba muka futo daga gida fa,yame jikin?"
Mama Sadiya tace"jiki da sauqi za'a ce,yanzu zan koma asbitin ma"
Zata sake magana Mamy tace"sannunku da zuwa"
tace"sannu Mamy, Mamy yunwa nakeji"
"ga abinci nan dauki kije kici"
Mama Sadiya tayi murmushi tana sake qarewa Mawahib din kallo taji tana maganar yunwa kode sun samu qaruwa ne,to amma data tuna da matsalar Captain saita daina tunanin"
abincin ta dauka sannan ta Kalli Mamy tace"Mamy ina na Yaya Captain?"
Mamy ta kalleta cikin mamaki,kode tafara sonsa ne?
Kafin tabata amsa Mama Sadiya tace"kizo ki zuba masa mana Mawahib,saiki kai masa dakinsa"
Ta amsa mata sannan tafuto daga kitchen din,Mamy ta Kalli mama Sadiya tace"Maman Nabiha Kinga zamani?"
Mama Sadiya tace"ai Mawahib da sauqi,ni Nabiha kallon cikin idona takeyi take cewa ita tana son mijin ta"
Mamy tayi murmushi ta girgiza kanta sannan ta dauko wani flask din tazuba wa Aryan din,kasancewar yau itace da girki tasan cewa basai an sake yimasa wani girkin daban ba, girki ne na zamani wanda zai birge wanda yaci.
Tana shirin futowa daga part din Mamy saiga Mamy din tashigo, abincin ta bata tace"gashi saiki ajiye masa"
Kar6a tayi tajuya ciki,itama tazubo abincin ta zauna kusada Mamy tanaci, kana ganinta kasan cikin farinciki take,tana gama cin abincin suka dasa sabuwar fira,har yamma su Captain Aryan basu dawo gidaba,Mamy tana lura da Mawahib taga koda wasa bata kira mijin nata tayi masa maganar yazo yaci abinci ba,Bata kirashi tayi masa tambaya Yaya jikin mahaifiyarsa ba, bata kirashi taji Yaya lafiyar saba, daga nan tasan cewa har yanzu ba lalle Mawahib tana sonsa ba,inda tana sonsa ko awa daya ba zatayi ba dole ko acikin magana ne saita sako maganar sa, amma koda wasa banda tambayar abinci, babu abinda tayi wanda ya danganci Aryan,daga nan tasan cewa akwai sauran rina a kaba.
Sai qarfe goma shadaya nadare suka dawo gida tareda Alqali,kai tsaye Alqali part dinsu yawuce, shikuma Captain Aryan da Ashraf suka shigo part din Mamy, alokacin suna zaune itada Mamy, cikin farinciki Mamy tace"sannunku da zuwa"
Captain Aryan ya Sosa kansa yace"Anty Ma-my,barka da dare"
"Yawwa Captain,yame jikin?"
Ashraf yace"jiki da sauqi Mamy,mun taho de tasamu bacci"
Mamy tace"Allah yabata lafiya,aida safe munje nida Alhaji,to dazan dawo gida sai muka taho da maman Nabiha saboda tatafi musu da abinci, ku zauna bari akawo muku abinci, kun wuni bakuci komai ba"
Ashraf yace"eh wallahi,Allah yasa ba Mawahib ce tayi jagwalgwalo ba,girkinki kawai zamuci Anty Mamy"
Mawahib ta Kalli Yaya Ashraf cikin shagwaba taturo bakinta gaba tace"Mamy wai nice nake jagwalgwalo?"
Mamy tayi murmushi tace"Kinga tashi ki basu abinci dan Allah"
Tashi tayi tanufi dining,Captain Aryan yana jinsu baice komai ba sai dan qaramin murmushi da yayi,yarasa meyasa yakejin nauyin Mamy yanzu.
Abincin ta ajiye musu, sannan tazuba musu,ta kalli Captain tace"Yame jikin?"
wani irin kallo yayi mata yace"Alhamdulillah"
Daga haka bata sake cewa komai ba,tatashi tawuce dakinta,Captain yabita dawani irin kallo,Ashraf yana ganin haka yayi sauri yata6o shi,cikin sauri ya sunkuyar da kansa, saide Mamy tana kallonsa ta gefen idonta,yanzu kam tagama tabbatar wa Mawahib bata bawa Captain kulawa,bataga wata soyayyar captain mashahuriya acikin idon Mawahib ba.
Sun dade a part din suna firarsu da Mamy sannan sukai mata sallama suka tafi,directly wajan Alqali sukaje alokacin shima yana cin abinci, sallama suka masa, sannan Ashraf yaraka Captain dakinsu, shikuma yayi masa sallama yatafi gida.
Kwanciya yayi adakin shiru shi kadai,tunani rashin lafiyar Hajiya kilishi yake,tunda sukaje asbitin oxygen ne a hancinta ko magana basu samu damar yida itaba.
Idan har sakin Mawahib shine zaisa Momy ta warke Yaya zaiyi kenan?
tunani ne yayi masa yawa,kuma Ashraf yatafi bare suyi magana akan matsalar,juyi yasake yi yashafa gefen sa yau bata nan,tsaki yasaki yatashi ya zauna yana tunanin tayaya zai Iya bacci shi kadai batare da'ita ba?
Tayaya zai Iya bacci bayan tariga tasaba tana shige wa jikinsa laushin fatarta yanasa yayi dogon bacci cikin nutsuwa?
Agogon dakin ya kalla yaga shabiyu nadare,amma kokadan bayajin alamun bacci a'idonsa,wayarsa yadauka yadoka mata kira,alokacin tana bacci tayi daidai tana shan esi tana Sanye cikin doguwar rigar bacci irin kayanta nada wanda take amfani dashi kafin ayi musu aure, wayarta ce take vibration cikin bacci ta laluba ta dauka takara a kunnanta batare data kalli me kiran ba,shiru yayi tsawon lokaci baice komai ba, itama batace komai ba,yanajin yanda numfashinta yake sauka tacikin wayar.
Wani irin numfashi ya sauke yace"kinyi bacci?"
tanajin muryar sa tabude idonta,cikin muryar bacci tace"um"
"zaki Iya baccin ne?"
Juyi tayi, tasake riqe wayar tace masa"um"
Cikin kulawa yace"Okay,gud night"
Batace masa komai ba yakashe wayar,bayan ya ajiye wayar shiru yayi tsawon lokaci,yasake daukan wayar yakirata.
Saida wayar takusa katsewa sannan ta dauka,cikin wata irin murya yace"are sure zaki Iya bacci batare dani ba...?"
Cikin shagwa6a irinta masu bacci tace"yaya Captain bacci nakefa"
Cikin lallashi yace"no kitashi kitaho..."
Wani irin kukan shagwa6a tafara zuba masa,ya lumshe idonsa sannan yakashe wayar batare da yayi magana ba,tashi yayi yasaka jallabiya kai tsaye yanufi part din Mamy(๐๐ปโโ๏ธ)
Yana tura qofar falon yaji shi abude,cikin sauri yanufi dakinta,yakama handle din dakin yabude yashiga,wutar dakin ya kunna yaganta tana baccinta cikin kwanciyar hankali,doguwar riga ce ajikinta amma mai kauri,zama yayi agefen kanta yafara shafa fuskarta,sannan yayi kasa da kansa yadora fuskarsa akan nashanunta yafara yawo da fuskarsa akansu yana shafasu da fuskar, cikin rada yace"kitashi mutafi"
Wani irin zabura tayi jin fuskarsa tana yawo akan na shanunta,cikin sauri yariqe fuskarta, murmushi yasaki yace"muje dakinmu?"
Cikin sauri tace"yaya Captain su Mamy fa..., agida muke fa"
Cikin sauri yadora hannunsa a kan bakinsa, ya kalleta da idanunsa dasuka fara qanqancewa yace"shiiiiit"
Sannan yasaka hannu yadauketa cak,suka futo daga dakin.
Adede lokacin Abba da Mamy sun futo daga dakin Mamy din zasu koma dakin Abba su kwanta kamar yanda suka saba,Abba ne yafara ganinsu, cikin sauri yaja hannun Mamy sukai baya,basu yarda su Captain sun gansu ba, saida sukaga fitarsu sannan Abba ya Kalli Mamy yace"meyasa baki tura ta wajan mijin taba?"
Mamy tace"Alhaji ai danaga abun da kunya,duka muna gida daya?"
Murmushi yayi yace"a a,kibar yaro yaji dumin matarsa,adena barin ta tana kwana anan,inde baso kike yadawo nan suna kwana tare ba"
Mamy tace"amma Alhaji fisabilillah kunsan da irin wannan lokacin amma tun farko baza'a tura yaran nan wani gidan ba? "
Cikin tsokana yace" a a gara kusa damu danki gane da kyau yarki jarumi ta aura,yarona babu daga qafa"(๐)
Wata irin hararar soyaiya tayi masa, sannan tawuce dakin nasa shima yabi bayanta.
Suna zuwa daki yadireta agadon yace"yi baccin anan"
Kwanciya tayi agadon tana turo bakinta gaba cikeda shagwa6a,jallabiyar jikinsa yacire,yarage dagashi sai gajeren wando sannan yakashe wutar dakin, yahau gadon yajata ya rungume ta yana sakin wata irin ajiyar zuciya,lokaci kankani bacci yadauke su gaba dayansu.
Kiran sallar farko akan kunnan Mawahib akayi,cikin nutsuwa tafara zare jikinta daga nashi,yana jinta yabude idonsa yace"Ina zakije?"
Rigar jikinta data dan tattare ta gyara sannan tace"tafiya zanyi,ni tsoron Mamy nakeyi, karta tashi taga bana Nan"
Murmushi yasaki yace"muje nakaiki to"
Yafadi hakan yana qoqarin tashi,cikin sauri tace"A a,zanje dakaina"
Murmushi yayi yace"kishirya qarfe takwas zamuje asbiti"
Cikin sanyin jiki tace"to"
Sannan tafuto daga dakin cikin sauri takoma part din Mamy,tana zuwa tashige dakinta tareda rufowa.
itace takai masa breakfast dinsa daki lokacin yana wanka, sannan itama taje taci, Mamy ta shirya mata wanda zata tafi dashi asbitin takaiwa Maman Nabiha,kamar yanda yafad'a qarfe takwas suka yiwa Mamy sallama suka shiga Mota suka tafi,suna zuwa asbitin shine yariqe kwandon abincin suka qarasa ciki,itace take binsa abaya jikinta yayi sanyi saboda batasan Yaya wannan zuwan nata asbitin zai qare ba,suna shiga dakin taganta a kwance likita yana yi mata gwaje-gwaje,Mama Sadiya tana gefe a zaune,agefe guda ta raku6e kana ganinta kasan akwai wani abu aqasa, likitan yadubi Captain Aryan yace"jikin nata yana sake warwarewa,hawan jini ne yake damunta saikuma ciwon zuciya dayake son kamata,munyi magana da Alhaji ta waya shima na sanar dashi komai,amma insha Allah zamuyi Iya kokarin mu akan hakan,akwai buqatar aqara mata jini, zamu duba jinin nata sai mu duba idan muna dashi sai azo asaka mata"
Captain Aryan yabashi hannu suka sake gaisawa, sannan likitan yafita, gadon ya qarasa ya sunkuya daidai kanta yariqe hannunta yace"Sannu Momy,Allah yabaki lafiya"
Ahankali ta lumshe idonta sannan ta bude alamun amsawa,Mawahib dake gefe adan tsorace tace"Momy Allah yaqara afwa"
Hajiya kilishi tayi shiru bata amsa mataba,saide kallonta datake yi, mama Sadiya datake gefe ta girgiza kanta,me hali de baya fasa halinsa,Ina laifin wanda yatako yazo inda kake domin ya duba jikinka?
ta kalli Mawahib tace"Mawahib qaraso ciki mana"
Ahankali taqaraso dakin, taja kwandon da Captain ya ajiye ta turawa Mama Sadiya gabanta tace"ga abincin ku inji Mamy,tace tana mata yajiki"
Mama Sadiya tace"jiki da sauqi, tun cikin dare tafarka saide bakin shiru babu magana saide tana amsawa da idonta,har zan kira su Ashraf ma saina fasa tunda dare ne, saina fadawa likitocin"
Cikin sanyin jiki Mawahib tace"Allah yabata lafiya"
Mama Sadiya da Captain suka hada baki suka amsa tare.
Mama Sadiya tazuba abincin sannan ta matsa tadago Hajiya kilishi tafara bata abincin,ko spoon uku bataci ba, tafara kwara amai wanda yake tahowa harda jini acikin aman, gaba dayansu tsorata sukai da Amman nata ganin yanda take zubar da jini dayawa,lokaci daya kuma aman nata ya tsaya cak, tafara maida numfashi,dukansu kanta sukayi suna mata sannu.
Mama Sadiya tafara qoqarin cire mata kayan, Mawahib ta matso suka cire mata,duka kayan ya6aci da jini,cikin rashin qyanqyami Mawahib tacire dankwalin abayarta ta daura shi akanta,sannan ta dauki kayan tanufi cikin toilet din dakin tace"bari na wanke mata kayan"
Mama Sadiya tace"to sannu Mawahib,Allah yayi miki Albarka"
Tafadi hakan tana sakawa Hajiya kilishi wani kayan.
Tsaf Mawahib ta wanke kayan, sannan ta dauko wata mopper tazo tagyara wajan, tabude Jakarta ta dauko turare ta fesa awajan, Hajiya kilishi babu abinda take sai kallonta.
Captain Aryan kuwa dayake gefe banda ido babu abinda ya zuba mata, wacce irin yarinya ce ita?
Meyasa har yanzu taqi ta amshi tayin soyaiyar sa?
Mezai mata arayuwa taji dadi kodan wannan kulawar data ba mahaifiyar sa?
Menene acikin ranta har tsawon wannan lokacin data kasa kar6ar tayi soyaiyar sa?
Yana wannan tunanin yaga tafita da kayan zataje ta shanya su.
Bayan fitar ta Ashraf da Nabiha da Alqali da Mamy da Abba da Alhaji khaleed,sukazo asbitin saboda duka sunji labarin ta farka.
tasha wahala kafin tasamu inda ta baza kayan saboda batasan kan asbitin ba.
Bayan tagama shanya kayan tadawo dakin, tana shigowa taga duka Yan gidan sunzo, gaida su tayi takoma kusada Nabiha ta tsaya,likita ne yasake duba ta sannan ya kalli Alqali yace"Alhaji munrasa irin jininta wallahi,bamu dashi yanzu,saide mufara gwada naku idan yayi daidai sai asaka mata,idan baiyi ba sai mu tura asiyo da wuri saboda idan yawuce awa biyu ba'a saka mata ba maganar gaskiya zuciyarta zata samu matsala"
Cikin sauri Captain Aryan yace"wanne irin jini ne da'ita? zamu bata nida Ashraf"
Likita yace"O negative ne da'ita"
Alqali yace"ba irin nasu bane,da Ashraf dani da Aryan duka irin jini nane dasu,saide a gwada na khaleed da Isah"
Likita yace"babu damuwa zamu Iya tafiya"
Lab sukaje aka dauki jininsu,sannan suka dawo dakin suka zauna kowa sai sannu yake mata.
Mamy tayi shiru tana tantama aranta kode tafada musu irin jinin Mawahib ne?
to amma Hajiya kilishin zata so hakan ne?
Ba lalle ne taso asaka mata jinin Mawahib ba,saboda tsanar data mata, danhaka tayi shiru ta bari adauki nasu Abban Nabihan sai asaka mata.
Mawahib kuwa tunda taji anfadi irin jinin Hajiya kilishi gabanta yafara faduwa saboda tasan cewa irin jininta ne,tadaga kanta tana kallon mutanan dakin,ta kalli Hajiya kilishi taga idonta yayi wani irin yallow,gashi ta qara fari dama Kuma gata fara tas,ahankali tafice daga dakin,duka Yan dakin sunga fitar ta saide kowa yayi tunanin wani uzurin ne yafiyar da'ita,Captain Aryan yabi bayanta da kallo yana tunanin inane zataje Kuma?
Tana futowa daga dakin tafara dube dube ko zata ga likitan,tafiya takeyi da baya saitaji tayi karo da mutum, tana juyawa taga likitan ne,cikin sauri tace"doctor jinin nasu yayi?"
Cikin damuwa yace"wallahi ansamu matsala,baiyi ba, kinsan irin jinin nata ne akwai wahalar samu gaskiya, gashi kuma matar nan tana cikin had'arin gaske"
.
Cikin rashin damuwa tace"doctor irin jinina gareta,kad'auka kasaka mata"
Cikin sauri likitan yasake kallonta yace"are sure babu damuwa su Alhajin sun sani?"
Tace"babu damuwa doctor"
Lab din suka juya,yadauki jinin nata yagwada danya sake tabbatar wa, yajira results yafuto yagani zata Iya bata, wani dakin daban sukaje ta kwanta a gadon wata nurse tana tsaye agefensu,likitan yasaka wani qaton sirinji suka fara daukan jinin,tsawon lokaci yadauka yana tsaye saida yagama daukar jinin sannan yabarta da nurse din yatafi dakin da ahalin Alqali suke.
Yana zuwa mamaki ya kamasu ganinsa da jini a hannu,Alhaji khaleed yace"doctor muna jira kazo da result din gwajin jininmu domin mugani zamu Iya bata kokuwa, amma kuma yaya muka ganka da jinin? ko kunsamu ne awani wajan?"
Likita yayi sauri yajonawa Hajiya kilishi jinin,ya daidaita gudun shigar jinin sannan ya kalli Alhaji khaleed yace"kamarya? tacemin Alhajin yana sane taje wajena,dama ba kune kuka turo taba?"
Gaba daya mutanan dakin sai suka zubawa likita ido suna kallonsa.
Cikin sauri Alhaji khaleed yace"muka turo wa?"
Cikin mamaki likita yace"yarinyar dana gani dazu anan me doguwar riga abaya ai itace tasameni yanzu tace adauki nata jinin asaka mata saboda irin jininsu daya"
Mamy tanajin haka tasan cewa Mawahib ce,Hajiya kilishi datake kwance tana magana da ido wannan lokacin bayan tagama jin abinda likita yafada lokaci daya ta qame takasa motsa idon natama.
Cikin sauri Captain Aryan yatashi tsaye gaba daya idonsa yarufe ya manta iyayen nasa suna cikin dakin,ya kalli likitan tace"yanzu tana Ina? tana wanne hali?"
(Ina masu sirika me halin Hajiya kilishi?
Shin zaku Iya sadaukar war da Mawahib tayi kokuma Allah yabata lafiya? ๐ค๐ค)
Mawahib littafin kudi ne,duk me buqata naira 500 ne kacal ta wannan account din
0164549488
Amina muhammad
GTbank
Kokuma katin MTN ta wannan number 08033300034
idona nahana bacci nacinye lokaci na narubutashi,bazanja Allah ya'isa ba,amma muddin kika karanta baki biyani haqqina ba nabarki keda mahaliccinki
Amnah El Yaqoubโ๐ป[7/14, 1:55 PM] AMINA KABIR CAPS: MAWAHIB
*Page 19&20*
Mawahib littafin kudi ne,duk me buqata naira 500 ne kacal ta wannan account din
0164549488
Amina muhammad
GTbank
Kokuma katin MTN ta wannan number 08033300034
idona nahana bacci nacinye lokaci na narubutashi,bazanja Allah ya'isa ba,amma muddin kika karanta baki biyani haqqina ba nabarki keda mahaliccinki faqad๐๐ป
Doctor yace"tana next roo...."
Kafin ya qarasa cewa room,Captain yafice daga dakin,ganin Captain Aryan yatafi hakan yasa Mamy ko kuskuren fita daga dakin batayi ba.
Alqali yace"bamu saniba doctor, aida nima bazan bari ba saboda kada yarinyar tashiga matsala"
Likita yace"idan ba'a saka mata akan lokaci ba itama marar lafiyar zata Iya shiga matsala Alhaji,kuma naduba naga tanada isasshen jini, shiyasa nadauka"
Mamy takalli Alqali yace"Yaya ai babu damuwa,Mawahib ma ai daya suke dasu Ashraf..."
Hajiya kilishi tanajin furucin Mamy wata irin kunya ta kamata,yau itace a kwance a wannan halin amma yayanta na cikinta basuda ikon taimaka mata sai gashi Mawahib din datake qi itace yau tabata jini,itace ta tsaftace mata jikinta lokacin da tayi amai harda jini,ahankali ta lumshe idonta wani irin hawaye ya silalo daga idonta, babu wanda ya lura da hakan.
******
Yana zuwa dakin yaganta a kwance a gadon,tariqe hannunta da aka dauki jinin ta danne wajan da audiga,mayafin abayar yafadi akan gadon,dogon gashinta ya baiyana,cikin sauri ya qaraso gadon yafara tatta6a jikinta baima lura da nurse din datake tsaye ba,yariqe fuskarta da hannayen sa cikin damuwa yace"meyasa kikai haka?, bakyajin magana ko? idan kikai rashin lafiya fa? Yanzu inane yake miki ciwo?"
Kallonsa tayi ganin yanda ya rikice yake jero mata tambaya tace"Yaya Captain banajin komai"
Ashraf ne da Nabiha suka shigo dakin,nurse din ta kalli Aryan tace"yalla6ai asamo mata fruit da maltina saitasha kafin tatashi,zai qara mata kuzari"
Captain Aryan yadago ya kalleta, sannan yashafa fuskar Mawahib ya miqe tsaye,ya Kalli Ashraf,batare da yayi masa magana ba suka juya suka bar dakin, itama nurse