Showing 51001 words to 54000 words out of 110331 words
tafi dakinsa, meyake yi anan?
agogon hannunsa ya kalla karfe shida harta wuce saide ace bakwai saura,yatuna baije masallaci sallar asubaba yau,dayayi wata irin zabura yatashi zaune yafara jada baya, hakan yasa itama cikin sauri tafarka,tana ganinshi itama saitayi baya da sauri tana gyara hargitsatstsan gashinta.
Kanta yana qasa takasa kallonsa,shima kasa kallonta yayi,cikin sauri yafara saukowa daga gadon yana dana sanin zuwansa dakin gaba daya,batare daya kalleta ba yace"sannu"
Cikin sauri ta kalleshi,kode yafara jin tausayin tane?
Shi kansa saida yafada yake mamakin kansa,meyasa yake girmamata, meyasa yake tausayinta shi kansa baisani ba,kafin tagama tunanin taji yace"yajikin"
Cikin sanyi jiki tace"dasauqi"
Duk wannan maganar dasuke babu wanda ya Kalli dan'uwansa,cikin sauri yabar gaban gadon zai fice daga dakin,saida yaje bakin qofa sannan ya kalleta yace"karki dafa komai"
Bata Iya magana ba saboda gaba daya mamakin sa yagama daure mata kai, sai kanta kawai data daga masa alamun amsawa.
Yana ficewa daga dakin tasaki wata irin ajiyar zuciya menene ya sauya shi haka?
dukkan tambayoyinta babu me bata amsa,hakan yasa tasauko daga gadon takashe esin dakin sannan tagyara shi tsaf, ta wuce toilet ta kunna ruwan zafi domin wanka.
bayan tagama wankan shiryawa tayi cikin doguwar riga ta material,bata shafa komai a fuskarta ba,falon tafuto ta zauna tana dan daddanna waya kadan kadan, ba tajin ciwon komai yanzu,saide jikinta babu qarfi sosai, David ne yayi nocking tatashi tabude,babbar Leda yabata yace oga Aryan ne yace akawo mata, ta amsa tareda juyowa, zama tayi tabude ledar taga abinci ne kusan kala biyu sai Kuma snacks shima daban, cikin mamaki tabude daya taci dan kadan, sannan takoma sama ta dauki maganin ta tasha.
Falo ta dawo ta kwanta a kujera tana tunanin jiya da daddare, itade tasan tabbas ciwo da rashin qwarin jiki yasa ta jingina a jikinsa, amma batun kwanciyar su tare batasan Yaya akai hakan tafaru ba, lumshe idonta tayi tanajin har lokacin kamar qamshin jikinsa yana nan ajikinta.
Baidawo gidan ba sai dare,a lokacin tana dakinta a zaune tayi shirin kwanciya tana Sanye cikin riga da wando amma masu kauri,snack ne agabanta tanaci kad'an kad'an kamar bataso.
Kai tsaye dakinta yawuce,tana ganin shigowar sa ta kalleshi sannan ta janye idonta tace"sannu da zuwa"
Yana tsaye daga bakin qofar dakin yace"yajikin"
Kanta aqasa tace"dasauqi"
Daga nan bai sake yimata magana ba ya juya yafice daga dakin,dakinsa yashiga yayi wanka,sannan yasanya farar jallabiya,yadawo dakin nata,tsayawa yayi yana waya da Ashraf, Ashraf din yana fada masa yasake musu sabin wayoyi zai turo masa tasa yagani,zama yayi dab da'ita saide bai had'a jikinsa da nata ba, a lokacin tagama cin samosa kenan,yana wayar yana kallonta tagefen idonsa.
tun shigowar sa dakin jikinta yayi sanyi taji batada wani sauran kuzari,ahankali tasaka hannunta ta dauki maganin ta ta6allo zatasha,cikin sauri yayi sallama da Ashraf, ya ajiye wayar a tsakanin su, sannan ya kalleta cikin kulawa yace"sannu"
kanta ta daga masa sannan tasaka maganin a bakinta ta runtse idonta tasha tafara maida numfashi kad'an kad'an adede lokacin wayarsa dake gefensu ta dauki haske kasancewar yasakata a silent,ganin sunan Asalamiyya a fuskar wayar tana kiransa sai hakan yatuna mata da shawarar Nabiha datake cewa muddin Asalamiyya tashigo gidan Yaya Aryan to haqiqa tata taqare,batasan Yaya zatayi tashawo kan Yaya Aryan zuwa gareta ba,saboda bata sonshi,kana kokarin shawo kan Wanda kakesone zuwa gareka ba Wanda bakaso ba,ahankali tafara yamutsa fuska ganin tunanin yana Neman saka mata ciwon kai, Captain Aryan daya dauki wayarsa zai amsa ganin yanda take yatsina fuska Sai hankalinsa yadawo kanta,ya ajiye wayar ya kalleta da kulawa, cikin rad'a yace"lafiya? ko jikin ne?"
Batace masa komai ba amma ta daga masa kanta alamun haka ne,Sannan ta tagyara fillo zata kwanta
Cikin damuwa ya sunkunyo daidai kunnanta yace"komu koma asbiti?"
Sanin datayi babu abinda takeji cikin sauri ta girgiza masa kanta ma'ana basai sunkoma asbitin ba,hannunsa yadaga zai ta6ata, saikuma yayi sauri yafasa ya janye hannunsa tareda dunqule hannun,wayar ce tasake yin haske akaro na biyu, Mawahib tana ganin kiran ta jinjina kanta tana mamakin wasu matan, zaka kira mutum bai dauka ba, kuma kira da daddare awajan me mata, amma bazasu fasa kiran ba,ta6e bakinta tayi sannan muskuta ta gyara zatayi kwanciyar ta, ahankali tace"wash..."
Bata qarasa rufe bakinta ba taji Captain yaruqota gaba daya arikice yafara cewa"Akira miki Anty Ma-my ne kinason waya da'ita?"
nanma batace masa komai ba Sai girgiza kanta datayi,ganin yariqeta a jikinsa hakan yasa cikin dabara tafara qoqarin raba jikinta da nasa.
Captain Aryan kuwa yayi tunanin ciwon ne yadawo shiyasa take yatsina fuska,hakan yasa bai damu da kasancewar ta a jikinsa ba, yasan sha'anin rashin lafiya ne,da kalau take kokadan bazai aikata hakan ba,yanajin yanda takeson zare jikinta daga nashi, amma bai bata damar hakan ba,sake rungume ta yayi kamar yana tsoron wani zai ganshi,sai gashi ba'a dauki wani lokaci metsawo ba bacci ya dauketa,Captain ya kalleta yaga tayi bacci, ahankali yafara qoqarin kwantar da'ita akan gadon saboda bayaso yasake yarda abinda yafaru jiya yauma yasake faruwa.π
Cikin dabara yafara qoqarin zareta ajikinsa,tanajin haka tabude idonta,Shima yana ganin haka yafara bubbuga bayanta alamun takoma taci gaba da baccinta,baccin takoma kamar wata Baby, saida takai kusan minti talatin tana bacci, baccinta yayi nisa sosai sannan tajuya tasake gyara kwanciyar ta tahanyar sake riqeshi,Captain Aryan Yasaki wani irin numfashi saboda yanda yaji tasake shigewa jikinsa, ahankali ya matse qafafunsa saboda kartaga halin dayake ciki gashi da jallabiya kuma azo aji kunya girma yafadi,numfashi yake saukewa da sauri da sauri yana kuma jin azaba taciki,π
yayinda fuskarsa tacika da gumi sosai,Kuma yakasa raba jikinsa da nata,ahaka yayi kwanan zaune, Mawahib kuwa tayi baccinta cikin kwanciyar hankali.
******
tunda suka tashi yau yaji jikin nata babu sauqi,dalilin wannan qananun zazza6in datake ne yasa ko wajan aiki bai tafi ba wanna satin, kuma taqi yarda suje asbiti,ganin yau jikin nata yayi zafi sosai yasa cikin tsantsar soyaiya da kulawa yasake gyara mata kanta dake kwance a qirjinsa yace"sweet nace muje asbiti kinqi,gashi tun dazu kina kuka,kitashi muje muga likita"
Hawaye ne ya zubo mata, cikin kuka tace"dan Allah ya Ashraf kakaini gida Naga mamana karna mutu tunda mukai aure fa banjeba"
Runtse idonsa yayi yabude sannan cikin damuwa yace"banason jin wannan maganar,karki sake cemin zaki mutu kibarni kinji ko?"
Cikin sauri ta daga masa kanta
Yasaka hannu ya share mata hawayen idonta sannan yace"shirya muje gidan,amma dazaran kin ganta,asbiti zamu wuce kin amince?"
Cikin sauri ta amsa masa amma cikin ranta tariga ta yanke babu inda zata dawo saita warke,kusan sati uku Kenan kullum cikin qananun zazza6i take, ga tashin zuciya,uwa uba Yaya Ashraf baya daga mata qafa,idan tashiga hannunsa baya yimata ta sauqi,tana fama da zazza6i amma idan yafara abu daya bayason bari, yacika fitina dayawa har bataso weekend yazo yadawo gida(ππ»ββοΈ)
Tsaf ta shirya yariqe hannunta suka futo zuwa cikin motarsa, suna tafiya ahanya tana kallon yanda yake driving cikin kulawa tana sake godewa ubangiji daya mallaka mata abinda take Qauna a Duniya,kai tsaye gida suka wuce,a lokacin qarfe tara da kwata nasafe,Mamy tafuto cikin shirin tafiya aiki tayi tsaf cikin uniform dinta saita gansu sun shigo,ganin yanda Nabiha take tafiya tana hada hanya hakan yasa taja tatsaya turus tace"Ashraf lafiya? meyake damunta?"
Momy kilishi data futo daga kitchen itama ta tsaya tana kallonsu,Ashraf ya Sosa kansa sannan yace"Anty Mamy ba tajin dadi ne, zamuje asbiti Sai tace mufara zuwa taga mama tukunna,amma tunda gaki ma shikkenan Sai muje asbitin gaba daya"
Mama Sadiya tafuto daga part dinta,cikin sauri Ashraf ya sunkuyar da kansa qasa yace"Ina kwana?"
Cikin fara'ah tace"lafiya kalau Ashraf,kune a gidan yau?"
Ashraf bai bata amsa ba ya qarasa yagaida Hajiya kilishi.
Mamy taja Nabiha jikinta cikin farinciki tace"Amarya...meyake damunki ne?"
Nabiha ta rungume Mamy,wani irin hawaye yazubo mata, adede kunnan Anty Mamy tafara mata magana qasa-qasa, "Mamy karki bari yatafi dani Dan Allah,zazza6i nakeji sosai Allah zai kasheni,bashida tausayi Yaya Ashraf mugu ne...."(π³)
Gaban Mamy yayanke yafadi,tuni ta gano inda matsalar take,lokaci daya jikinta yayi sanyi,to Ashraf ma Nabiha tana masa kuka,Mawahib datake hannun Soja, awanne hali take ciki kenan?π€
ganin mama Sadiya tana wajan karta fahimci komai hakan yasa cikin lallashi tafara bubbuga bayanta tana cewa"ya'isa to, kukan ya'isa,zakiji sauqi insha Allah"
Hajiya kilishi ta kalle su tace"ina ganin ikon Allah ni kilishi....,kukan metake to? ko kukan jin dadi ne kukan ganin uwa?"
Mamy tayi murmushi cikin sauri tace"A a Yaya,ba tajin dadi ne zazza6i ne yake damunta,amma yanzu ma zasu wuce asbiti saisu ga likita"
Mama Sadiya tace"Subhanallah,to amma Maryam bagaki ba? kiduba ta kawai saita zauna tahuta inyaso saiya siyo mata magungunan ko a chemist ne"
Mamy tace"to shikkenan,"
Ta Kalli Nabiha tace"meyake damunki?"
Nabiha taja hancinta alamun tasha kuka,cikin murya qasa qasa tace"Mamy zazza6i nakeji,kuma komai naci sainayi amai,kuma nasha magani zazza6in yaqi tafiya"
Cikin farinciki Mamy tasake kallonta tace"masha Allah,to Ina zuwa"
Tasaketa tashige part dinta, ta dauko wata roba dawani dan qaramin tsinke (pt strip)
Sannan tabata robar tace"jekiyo fitsari anan kikawo min"
Hajiya kilishi tanajin abinda Mamy tace saitaja ta tsaya tana so ta tabbatar da abinda idonta yake gani,meyake shirin faruwa kenan?
Nabiha taje dakinta nada tayi abinda Mamy tasa ta,Sannan tadawo,Mamy tayi gwaje gwajenta ta dudduba idon Nabiha, sannan ta Kalli Ashraf da Mama Sadiya tace"Alhamdulillah,ciki ne da'ita,Nabiha tasamu ciki,zanje asbiti da sauran fitsarinta sai aduba agani wata nawane"
Cikin sauri Ashraf ya sunkuyar da kansa qasa gabansa yana faduwa,ga Mama Sadiya awajan, shida yayi alqawari bazai ta6a mata yaba yanzu gashi ciki ya bayyana,wata irin kunya ta rufeshi yaji dama baizo gidan ba,yarasa tayaya zai tashi yafice yabar gidan.
Cikin sauri Hajiya kilishi tajuya ta Kalli Ashraf da kansa yake qasa tace" yanzu kai Ashraf kaida kanuna min bakason aure shine daga ganin 'yar mutane saboda tsohuwar jaraba harka lalla6a ka d'kirka mata ciki?"(πππ»ββοΈ)
Ashraf yayi shiru yakasa cewa komai Kuma yakasa dago kansa,gashi Aryan baya Nan bare yatare masa, haka yakasa dago kansa sai qeyarsa dayake sosawa cikin kunya.
Cikin farinciki Mamy ta Kalli Hajiya kilishi tace" Yaya wannan ai abun farinciki ne"
Cikeda masifa Hajiya kilishi tace"kyace haka kam,gara da Allah yasa Aryan baya haihuwa,shima nasan da yanzu ancika masa gida da 'ya'yan wasu anfake dacewa abin farinciki ne"(ππ»ββοΈ)
Maganar tata tadaki Mamy sosai,taso tayi haquri kamar yanda tasaba, to amma bazai iyu tayiwa 'yarta qwaya daya jal mummunan Fata irin wannan tayi shiru ba, ahankali tayi wani irin murmushi mai ciwo tace"Yaya kenan,Aryan ai Addu'ar ki yake buqata,kiyi masa Addu'ah Allah yabashi lafiya,shima ya haifi dansa na kansa koba ta hanyar 'yataba, idan Kuma ta hanyarta yasamu haihuwar babu yanda zamuyi da hukuncin Allah, dama yariga ya tsara akwai haihuwa a tsakanin su"
Cikin sauri Hajiya kilishi tace"Kinga dakata Maryam,karki yiwa dana Aryan fatan hada zuri'ah dake,saide yarki taje can wani kwararon tasamo cikin,amma bata hanyar dana Aryan ba"
Cikin sauri Ashraf ya kalleta yace"Haba Momy...,meyayi zafi ne har haka?"
Hajiya kilishi ta Kalle shi tace" kaida Allah rufe min baki, shashasha,meka sani dahar zaka tsomo mana baki, da Aryan ya haihu da wannan yarinyar gara in mutu inbar duniya,dana bazai ta6a hada iri da wannan mayyar ba, saide in shegu za'a liqa masa"
Ashraf ya sunkuyar da kansa qasa hawaye ya sulalo daga idonsa, Nabiha kuwa kuka take sosai takama Mama Sadiya ta riqe gani take duk itace silar wannan tashin hankalin, data sani batasa Yaya Ashraf yakawo taba,da wannan tashin hankalin gara tabi mijin ta su koma gidansu inma kasheta zaiyi ya kasheta, yanzu gashi tajawa baiwar Allah Mawahib zagi nacin mutunci.
Mamy ta kalli Hajiya kilishi,cikin 6acin rai tace"Mawahib bazata haifi shegeba,dan halak zata haifa kuma tareda Captain Aryan,meta tsare miki? yarinyar nan batason auren nan,nima banaso,amma haka nayi haquri itama na tilastata tayi haquri saboda nariga na yarda da hukuncin Allah, ba zanyi jayaiya da qaddarar da Allah yariga yahad'a ba, shiyasa nayi haquri nabarsu, Yaya tunda nake acikin gidannan ban ta6a qin yaranki ba,Ina daukar su ne kamar Mawahib,amma yanda kike nunawa yata qiyaiya nima bazanso ace ta auri danki ba,banda ubangiji yahada aurenta da Aryan wallahi tallahi gara ace Mawahib ta auri mahaukaci data hada zuria dake"
Cikin masifa Hajiya kilishi tace"haka kikace?"
Mamy tace"haka nace Yaya"
Hajiya kilishi tace"yau zan nuna miki raino ba haihuwa bace,zan kira Aryan yazo yasaki yar taki saki uku akan idonki,inyaso kije kibata mahaukaci"
Cikin 6acin rai Mamy tahade hannunta waje daya tace"Allah yabaki sa'a yaya"(ππ»)
Daga Nan tajuya tashige part dinta cikin qunan rai.
Hajiya kilishi tabude wayarta tafara qoqarin kiran wayar Captain Aryan.
Ashraf kuwa cikin kuka yafice yabar gidan Kai tsaye yaje yasamu mazan gidan dasuke waje,yafada musu komai, sannan yafara qoqarin kiran wayar Aryan....
Haly JASHERU venture's,munada kayayyaki masu kyau da inganchi ba algus da ha'inci, kayanmu daga Ethiopian ne, prdct dinmu muna Ethiopian magic hair oil, anti dandruff shampoo serum, bdy cream, hand cream, magungunan chuttuka da na mata masu inganchi da qara lfy ajikin dan
adam ga number kmr hk 07046665338 ko 07061664264 munada distributor ako Ina afadin kasarnan da ketare muna koya harkokin kasuwnchinmu ga masu bukata akan 5000 kacal
sannan munada tsuntsaye na kasashen waje tattabaru game bukata ko koya akwai riba kwarai aharkar mebuqata yasiya koya koya seyanemeni a number na kamar haka 07046665338 ko 07061664264, ku antayo ayi tafiyar daku,yar'uwa kikoyi sana'ah akan wannan farashi me sauqi kema ki kafa kankiππΌ
******
Yana wajan aiki bayan yagama waya da Momy saiga kiran Ashraf,yana dauka cikin sauri Ashraf yace"Momy zata kiraka, karka dauka,kayi sauri kakashe wayarka karta kira tasameka"
Captain Aryan yace"aina dauka,munyi magana da'ita tace tana son ganina nida Mawahib yanzu yanzu,Ashraf tunda akai auren nanfa Momy bata daukan wayata,tayaya yau zanga kiranta inki dauka? meyasa zakace karna dauka akwai abinda yake faruwa ne?"
Ashraf ya dafe kansa tareda fadin"ya Salam,meyasa zaka dauka?"
Alqali dayake gefe yanajin abinda yake faruwa yace"kace masa sutaho din,zanyi maganin matsalar"
Ashraf yace"shikkenan,kutaho inji Daddy"
Captain Aryan yayi shiru yana tunani bayan sungama wayar,meyake faruwa a gidan?
haka kawai rana tsaka ace sutaho gida meyafaru?
Ajiyar zuciya yasaki sannan yadauki excuse yataho gida, yana zuwa gida afalo ya zauna ya lumshe idonsa,baisan meyasa ba haka nan yakejin bayason tafiya gidan,yafison suyi zamansu su kadai anan ba tareda sunyi nesa da juna ba(π)
Mawahib tafuto daga kitchen ta ganshi a zaune,mamaki ya kamata yau shine yadawo da wuri?
Kitchen din takoma tahado masa fruit da ruwa takawo masa tace"sannu da zuwa"
Cikin sauri yabude idonsa ya kalleta,tana Sanye cikin doguwar riga bubu ta leshi,ruwa kawai yadauka yasha dan kadan sannan yace"ki shirya zamuje gida"
Cikin murna Mawahib tace"gida?, wayyo Allah, to bari in shirya"
Bata jira amsar saba tahaye sama da gudu cikin murna,yabita da kallo yana mamakin murnar ta,kenan so take sutafi gida ta barshi? π’π
Meyasa shi bayason tafiya gidan?π€
yana nan zaune tafuto hannunta daukeda qaramar jaka hand back,bai damu da cire uniform din jikinsa ba yatashi suka fice daga gidan jikinsa a sanyaye.
Kusan awarsu daya a airport sannan suka tashi, acikin jirgi yana kallon window yana satar kallonta yaga sai walwala take,tunda tazo gidan sa, bai ta6a ganinta tana walwala ba, hakan yana nufin atakure take dashi Kenan, lokaci daya ,jikinsa yasake sanyi.
Suna sauka yakira direban gidan yaje airport din yadauko su,direba sai satar kallonsu yake ganin yanda sukai mutuqar kyau da dacewa da juna,suna zuwa gida sukaci karo da Mamy da Alhaji Isah a compound din gidan kan Mamy aqasa Abba kuma yana mata magana da alama fada yake mata, cikin murna Mawahib tayi wani irin gudu ta rungume Mamy, Captain Aryan yayi sauri ya sunkuyar da kansa qasa cikin ladabi yabawa Alhaji Isah hannu suka gaisa,Alhaji Isah yace"Captain kun qaraso Kenan,kana aiki antasoka ko?"
Captain yayi murmushi yace"babu damuwa uncle"
Yajuya ya Kalli Mamy yace"Anty Ma-my"
Mamy tasaki fuskarta babu yabo babu fallasa tace"sannunku da zuwa Aryan,ku qaraso ciki "
Tafadi haka tana musu nuni da qofar Hajiya kilishi,gaban Mawahib yafadi,daga nan jikinta yayi sanyi saboda tasan zuwa part din Momy kilishi ba Alkhairi bane"π
Cikin takunsa na sojoji Kuma ingarman namiji maiji da kansa, yayi sauri yawuce gaba zuwa part din mahaifiyar tasa,yana shiga yaga iyayen nasu gaba dayansu,Nabiha ce kawai bata nan amma kowa Yana falon,zama yayi yagaida kowa,suma su Mamy suka shigo Mawahib tana jikin Mamy ta riqeta kamar za'a qwace ta,Alqali yayi ajiyar zuciya sannan yace"Kilishi kece dalilin Zaman mu anan,Ashraf yafada mana cewa zakisa Aryan yasaki matarsa saki uku menene dalili?"
Cikin sauri Mawahib tadago kanta ta Kalli Captain Aryan,adede lokacin shima yadago kansa idonsu ya sarqe dana juna,cikin kamewa ya janye idonsa,ahankali itama tayi qasa da kanta bazatace ga yanayin datake ciki ba, itade tasan cewa batason sa,saide azaman dasuke gudanarwa na yanzu bazatace yanayi mata abinda bataso ba, daidai gwargwado yana bakin kokarin sa, soyaiyar sa cede bataji aranta har yanzu,cikin sanyin jiki ta sunkuyar da kanta qasa, tasan cewa tabbas wani abu yafaru.
Hajiya kilishi tace"Alhaji kasan de bana qaunar auren nan,kawai fin qarfina akayi,saboda haka idan de nice na haifi Aryan, inaso abani damata ta mahaifiyar sa d'ana yamin abinda nakeso"
Tajuya ta Kalli Captain Aryan da kansa yake qasa har lokacin yana tsugunne ko zama baiyi afalon ba, sannan taci gaba cewa"gashinan a zaune tun auren Ashraf na bashi umarnin yasaki yarinyar nan,idan yasan bai sake ta ba,to karya kuskura yasake kirana,amma saboda ban Isa dashi ba, shine yadaina kirana kwata-kwata yaza6i yazauna da wannan tijararriyar yarinyar akan yabi umarnina,kuma muddin Ina raye bazan ta6a daukan wayarsa ba saiya cikamin umarnina,gashinan a zaune, itama yarinyar gata nan a zaune yasaketa,uwarta taje ta aura mata mahaukaci..."
Mamy kanta yana qasa,tunda sukazo falon batadago kanta ta Kalli kowa ba,tana jira ne kawai Alqali yayanke hukuncin wannan aure,wani irin hawaye mezafi yazubo daga idon Mawahib, tasaka hannu ta share,ta tabbatar akwai abinda yafaru agidan yau,ta tabbatar anciwa Mamyn ta mutunci yau,meyasa Hajiya kilishi bata sonta? a gaban kowa da kowa taza6i taci mata mutunci saboda qiyaiya.
idon Ashraf yayi jajir qiris yarage yafara hawaye.
Wayar Captain Aryan tafara qara alamun Kira yana shigowa, yasaka hannu yayi rejecting kiran.
A'irin wannan lokacin bashida qwarin gwiwar daukan waya.
Kansa yana qasa bai dago ya kalli iyayen nasaba,saide yarasa dalilin dayasa yakejin mummunan faduwar gaba atare dashi.
Alqali yayi ajiyar zuciya yace"to kilishi ki kwantar da hankalinki,insha Allah yau wannan matsalar taku zatazo qarshe,dama can abinda yasa mukayi tunanin hada Ashraf da Mawahib aure, saboda wannan sa6anin dakuke samu ne keda Maryam, munyi tunanin idan danki, ya auri yarinyar Maryam,rikicin naku zaizo qarshe,kika nuna baza'a yi wannan aure ba, Kuma daga qarshe Allah da ikonsa Sai ubangiji yayi ikonsa akan Aryan,mukayi haquri bamu bashi umarnin yasaketa mu aurawa Ashraf itaba saboda Allah yariga yayi ikonsa,Sai muka kar6i tsarin Allah da hannu bibbiyu mukayi haquri muka bisu da Addu'ah,amma tunda har yanzu kin nuna bakyason auren,amatsayin ki na uwa,dole zamu