Showing 27001 words to 30000 words out of 110331 words
sai yaji bazai Iya masa komai ba,yasaki ajiyar zuciya yace"to Alhaji Ma'aruf munji bayanin ka, kuma mungode, adade nayi tunanin ko duk abinda na mallaka zai qare to sai inda qarfina yaqare akan mutumin da yayi min auren d'ana, to amma bayan naji bayananka saina gamsu da maganganunka,haka ubangiji ya tsara masa,Allah yasa hakane yafi Alkhairi, yanzu Ina yarinyar take?"
Alhaji Ma'aruf yadauko wayarsa daga aljihu yace"bari nakira inji inane address din gidan sai muje daku a dauko yarinyar"(ππ»ββοΈ)
Cikin sauri yadokawa Mamy Kira,bugu biyu Mamy data dawo daga wajan aiki tadauka, Alhaji Ma'aruf yace"gani akano, inane address din gidan"
Mamy tace"akawoka gidan Alqali,duk wanda ka fadawa yasan gidan"
Cikin tsananin mamaki Alhaji Ma'aruf yace"a a, gidan Alqali kuma? to ai Ina cikin gidan"
Yajuya ya kalli mutanan falon daduk suka zubo masa ido suna kallonsa yace"yanzu dan taxi yace mana nanne gidan Alqali, koba nan ne gidan ba?"
Ya qarasa magana yana kallon yan falon
Gaba dayansu sukace" Nanne"
Alqali ya kalli Alhaji Ma'aruf yace"kafada musu suzo cikin gidan Alqali yanzu yanzu part din matar Alqali"
Alhaji Ma'aruf yacewa Mamy "to Ina cikin gidan Alqalin,gani ga mutanan gidan kuzo keda ita, Ina jiranku" yana fadin haka yakashe wayar
Mamaki yakama Mamy, kamarya suzo gidan Alqali? to Ma'aruf yariga yazo gidan kenan kome? waye yafada masa a gidan take?
Tadaga kanta ta kalli Mawahib datake tsaye a gaban tv tana qoqarin kashe kayan kallo, tana sanye cikin doguwar riga abaya mai kyau, tace"ke zomuje part din yaya kilishi"
Cikin sauri Mawahib tace"Mamy lafiya?, inaso ne inje gidansu Jiddah munyi waya tacemin zasu tashi sunkoma gombe dazama gaba daya"
Mamy tace"muje nace"
Babu musu tabiyo bayan Mamy suka tafi part din Hajiya kilishi,tun abakin qofar sukaga takalma dayawa hakan ya tabbatar wa Mamy mazan gidan suna ciki kenan, da sallama Mamy tashigo falon,Mawahib ma tashigo, gaba d'aya sai kallo yakoma kansu,cikin sauri Hajiya kilishi tatashi tsaye tace"Rainin hankali....idan an'isa in nutse anan,ni za'a rainawa hankali?"
Cikin tsawa Alqali yace"Kilishi meyake damunki ne?"
yajuya ya kalli Mamy dabai san dalilin zuwansu ba yace"maryam meyake faruwa?"
Kafin Mamy tabawa Alqali amsa Alhaji Ma'aruf yace"Alhaji ai itace wadda nayi waya da'ita yanzu,itace mahaifiyar 'yata Ruqayya wadda na aurawa d'anku Captain Aryan...."
Cikin sauri Ashraf yatashi tsaye yace"What....?"
Gaban Captain Aryan yayi wata irin muguwar fad'uwa,ya runtse idonsa afili ya furta "innalillahi wa Inna ilaihirraji'un,Hasbunallahu wa ni'imal wakeel...,ko ba'a fada masa wacece Ruqayya ba yasan Mawahib suke nufi tunda itace yarinyar Anty Ma-my"
Mamy tanajin furucin Alhaji Ma'aruf,saita tuna lokacin da Captain Aryan yake fada mata wani mutum yamasa aure da 'yarsa,ta tabbata de dolen dole sai yarta ta auri jinin Yaya kilishi, cikin tsananin damuwa tadafe kanta da hannunta (π€¦π»ββοΈ)
Mawahib data gama rikicewa tana ganin abu kamar a film,cikin ranta tana fatan ace bade da'ita Ruqayyan sukeba, cikin rawar murya tace"Mamy meyake faruwa?"
Alhaji Ma'aruf ya kalleta, tsananin kamar datake dashi shine yasake tabbatar masa da cewa tabbas itace Ruqayyansa yace"Ruqayya nayi miki aure,na aura miki Captain Aryan nasan insha Allahu....."
Kafin yagama magana Mawahib takoma bayan Mamy da sauri ta rirriqeta,lokaci daya hawaye ya wanke mata fuska,jikinta yadauki rawa tafara girgiza kanta alamun rashin yarda
Hajiya kilishi ta kalli Mamy wadda har yanzu hannunta yana goshinta takasa dago kanta, cikin masifa tace"Maryam kinji dadi....wato dana nuna miki baza'a bawa Ashraf Mawahib ba saida kika koma kikai kutun-kutun kika liqawa Aryan ita, to billahillazi bazai iyu ba"
Tana fadin haka tanufi Captain Aryan wanda kansa yake sunkuye yanaji kamar a mafarki wannan abubuwan suke faruwa, tana zuwa takama hannunsa tatashe shi tsaye ta nuna masa Mawahib tace"gatanan saketa yanzu yanzun nan, maza yimata saki uku"(π³ππ»ββοΈ)
Alqali dayake zaune yana ganin ikon Allah yayi murmushi ya kalli Captain yace"kai Aryan....dauki matarka kubar gidannan"
Mawahib tanajin wannan furucin tasaki ihun kuka ta qanqame Mamy tana cewa"Mamy zan mutu,wallahi banason sa,bagarama Yaya Ashraf dinba..."
Hajiya kilishi ma tanajin furucin Alqali tayi maza tazo bakin qofar tatare tace"Babu inda zasuje saiya saki wannan yarinyar"
Alqali yatashi tsaye yanufi qofar,Alhaji khaleed da Alhaji Isa ma suka Isa qofar, Alqali yasa hannu ya matsar da kilishi gefe,yakamo hannun Mawahib yasaka acikin tafin hannun Aryan,sannan ya kalli Aryan d'in yace" d'auki matarka ka koma bakin aikinka"
(Kai wata dramar Sai a gidan Alqali,yau Hajiya kilishi tana ganin ikon Allah tsagwaron saππ)
mutara zuwa gobeππ»
Mawahib littafin kudi ne,duk me buqata naira 500 ne kacal ta wannan account din
0164549488
Amina muhammad
GTbank
Kokuma katin MTN ta wannan number 08033300034
idona nahana bacci nacinye lokaci na narubutashi,bazanja Allah ya'isa ba,amma muddin kika karanta baki biyani haqqina ba nabarki keda mahaliccinki faqadππ»
Amnah El Yaqoub βπ»
[7/9, 9:20 AM] AMINA KABIR CAPS: Mawahib littafin kudi ne,duk me buqata naira 500 ne kacal ta wannan account din
0164549488
Amina muhammad
GTbank
Kokuma katin MTN ta wannan number 08033300034
idona nahana bacci nacinye lokaci na narubutashi,bazanja Allah ya'isa ba,amma muddin kika karanta baki biyani haqqina ba nabarki keda mahaliccinki faqadππ»
Tsawar daya matane yasa tajuya cikin dakin da gudu tana sakin wani irin kuka mai ciwo.
Jakar kayanta data futo dasu daqyar,gaba d'ayansu guda ukun yadagasu da hannusa guda daya,ya watsa mata su cikin dakin sannan ya rufe kofar yajuya cikin dakinsa cikin damuwa,yana zuwa Yafada kan gadon sa tareda hargitsa sumar kansa yana Runtse idonsa, lokaci daya yaji wani ciwon kai yana neman kamashi, bayason damuwa kokadan.
Cikin kuka tajanyo wayarta takira Mamy amma takasa cewa komai banda kuka babu abinda take, daga dayan 6angaren Mamy tayi shiru tanajin yanda Mawahib take kuka,adede lokacin tana kitchen, tasaka hannu takashe gas din sannan tabar kitchen din takoma dakinta ta zauna, bata hanata kukaba saida tabarta tayi kukan sosai, sannan tace"ya'isah haka"
Sai a lokacin Mawahib takejan zuciya alamun taci kuka ta qoshi,Mamy ta dafe goshinta alamun damuwa, ta tabbatar akwai abinda yake faruwa a gidan yaran, cikin sigar lallashi tace"meyake faruwa?"
Saida tarage kukanta sannan tace"Mamy ni gida zan tafi,Yaya Captain zai kasheni,mugune...."
Mamy tanajin wannan furucin gabanta yafadi,tayi tunanin ko takurawa yarinyar yake ta 6angaren auratayya,to amma kuma tana shakku akan hakan,cikin rashin sani tace"mekike nufi? meya miki?"
Cikin muryar kuka tace"yana takuramin,ni banason yana shiga harkata,ni kawai kowa yayi rayuwar sa,amma saiya dinga cin zalina yana sakani Ina faduwa,ni Mamy nagaji bazan iyaba"
Mamy tasaki ajiyar zuciya,tayi tunanin matsalar ta wuce haka, ashe Iya haka ta tsaya,duk da tana cikin dakinta saida ta rage murya sannan tace"Mawahib, keda Captain gaba dayanku nasan halinku ciki dabai, babu wanda zai kawomin qaran dan'uwan sa acikin ku bangane waye marar gaskiya ba,kinyi masa laifi ne?"
Cikin muryar kuka tace"Mamy ni banyi masa koma ba,Ina goge kitchen ban shiga sabgar saba yazo yaje far min da goran ruwa,Ina shara yasamin qafa nafadi,menayi masa dazai dinga cutata"
Mamy tayi murmushi marar sauti,gaba daya cikin bayanan na Mawahib tagama gane cewa da niyya Captain din yayi mata haka,soyake ta kula shi amma Kuma taqi kula shi ta nuna masa itama miskilar kanta ce,tasan cewa tun yana yaro bayason raini,Ashraf ma daya bashi Yan awanni kokadan bayason yaji Ashraf yana cewa ya girmeshi yanzu saisu fara musu har aje Ana tambayar kilishi waye Babba,gaba daya su biyun daga Mawahib din har Captain din kowa Yana buqatar ajashi ajiki a lallasheshi,shide dama tun yana yaro tasan cewa bai iya lallashi ba bare tasaran zai lallashi Mawahib,Shima kansa lallashin yakeso.
Cikin nutsuwa tace"Mawahib mekika dauki aure ne?"
Saida taturo dan qaramin bakinta gaba sannan tace"to Mamy dole ne saiya shiga harkata? kowa yayi rayuwar sa"
Mamy tace"karna sakeji kin fadi haka, kina qarqashin ikonsa ne yanzu,Sai abinda yace dake, duk cikin bayanin ki banji inda kikace kin gaishe shi ya mareki ba,banji inda kikace haka kawai kina zaune yazo ya rufeki da duka ba,Mawahib tayaya zakiga yayanki bazaki gaida shi ba? Kuna rayuwa gida daya kubiyu dole zaki gaishe shi,dole zaki tambayeshi koda abinda yake damunsa, idan kinzo gidama Abbanki a ranar zai maidake"
"to Mamy dole ne hakan? ni banason shi, banason auren nan,dole ne sai nayi masa magana?"(ππ»ββοΈ)
Kai tsaye Mamy tace"dole ne,kishiga hankalinki Mawahib banason shirme,kina tunanin zai zauna ya dinga lalla6aki ne kamar Abbanki? Kece zaki masa biyaiya kimasa abinda yakeso saboda aljannarki kike nema,daga yau, gaisuwa kullum safe da yamma,girki kullum Kuma ba Kala dayaba,shara kullum mopping kullum, kinji abinda nace? Karna sakejin wata matsala makamanciyar wannan kuma"
Qit....takashe wayarta, Mawahib ta Kalli wayar da idonta,itace zata tambayi Yaya Captain meyake damunsa? tayaya? mutumin da inde ta zauna kusa dashi jikinta yadinga karkarwa Kenan ta'ina taga qwarin gwiwar yimasa magana?.
******
Washegari da sassafe yadawo daga motsa jiki, yana Sanye cikin Riga wacce take hade da hula, sai dogon wando qafarsa tana Sanye cikin farin kambos,yana shigowa gida dadan sauran gudunsa adede lokacin Nabiha tagama share musu compound din gidan gaba daya,kallo daya yayi mata yadauke kansa, Nabiha dabata lura dashi ba,kamar daga sama taji yace"kikai min abinci anjima"
Bai saurari abinda zata fada ba yawuce ciki,cikin sauri tabi bayansa da kallo tasaki wani irin murmushi sannan ta wuce part dinsu.
Darana takai masa abincin kamar yanda ya buqata, tajuya zata futo yace"zonan"
Babu musu tadawo ta zauna aqasansa, shikuma yana zaune akan gadon su, ya kalleta batareda da damuwa ba yace"Nabiha nasan bakyason auren nan,dole ce za'a miki,toki kwantar da hankalin ki Nima banaso,bazan 6oye miki ba, idan nasamu yarinyar danake so zan aureta,kema nabaki dama daga Nan zuwa lokacin da za'a liqa wannan aure,idan Kinga wani Wanda kikeso, toki sanar dani namiki alqawarin dakaina zanje nasamu su Daddy Nafada musu a dakatar da maganar auren nan,idan Kuma yanzu ma kinada Wanda kikeso toki sanar dani,Sai afasa wannan hade-haden"(ππ»ββοΈ)
Nabiha tayi shiru tafara tunani cikin sanyin jiki,itade tasan cewa tun tashinta ba kula wasu samari takeba,asalima yanda gidansu yake da tsaro da wahala kaga saurayi yazo yana Neman su,abinda tasani shine tatashi da soyaiyar Yaya Ashraf acikin ranta, komai yayi birgeta yake,saide shi hankalinsa yana kan Mawahib,yanzu idan ta nuna masa batada saurayi kamar zai dinga yimata kallon wacce aka liqa masa yadinga hantarar ta,cikin dabara tace"inada saurayi amma bai shirya aure yanzu ba,makaranta yakeyi"
Cikin farinciki Ashraf yace"Alhamdulillah,tokinga ta kwana gidan sauqi,idan Naga yarinyar danake so,zan aureta,kema duk lokacin daya gama makarantar kifadamin, zan sauwaqe miki kije kuyi aurenku"
Mamaki yakama Nabiha,yanzu harya yarda da wannan qaryar data shirya masa? tayaya zata yarda yarabu da'ita bayan ya aureta?
Cikin ladabi tace"to Yaya Ashraf nagode"
Cikin sauri Shima yace"ki godewa Allah, zaki Iya tafiya"
Babu musu tayi masa sallama tafuto daga dakin.
******
tsawon sati biyu Kenan Mawahib bata sake saka Captain a'idon ta ba, Bata futowa sai taji baya gidan,zata futo ta dauki lemo ko madara da biscuit takoma dakinta, Shima Koda wasa bai nemetaba,yauda daddare daqyar tagama cin biscuit din,saboda ya'isheta, Kuma Mamy tace ta dinga yiwa Yaya Captain girki, ita Kuma qyashin yimasa girkin take,amma dole gobe zatabi umarnin Mamy tayi,kodan cikinta ma, wannan cin biscuit din babu inda zai kaita,shiyasa tayi sauri tayi wanka sannan tasaka kayan bacci ta kwanta saboda tana son tashi da wuri tayi gyaran gida tayi girki.
Acan dakin Captain kuwa bayan yagama abinda zaiyi Shima yayi shirin bacci, wayarsa tayi qara yana dubawa yaga Ashraf ne, cikin sauri yadauki wayar, Ashraf yace"yanaga kadauki wayar da sauri haka? Aryan anya kuwa? Kode baka zama da matarka ne kullum Ina kiranka saikayi caraf kadauka kod'an irin Ina zuwa zan kiraka dinnan babu?"
Cikin taqaici Captain Aryan yace"dan Allah kadena min maganar yarinyar Nan Ashraf,ni gaba daya na manta da'ita ma,tunda nabata abinci shikkenan na sallameta"(π²)
Ashraf yayi murmushi yace"kayi haquri mana,koba dan itaba, kodan Anty Mamy"
Captain Aryan yace"yanzu haka zanyi ta zama da'ita Kenan? Banson ganinta wallahi"(ππ»ββοΈ)
Ashraf yace"to ya zakayi? Nima wallahi banason ganin Nabihan nan,but ni matsala ta tawuce, nace Koda bayan bikinne zan sauwaqe mata ta auri Wanda takeso"
Cikin sauri Aryan yace"yes hakan yayi,Nima zanyi tunanin Yaya zanyi da yarinyar nan"
Ashraf yace"kaikam Mawahib aita zame ma dole,zaka saki yarinyar Anty Mamy ne Kuma kadawo gidannan kaje wajanta? aikai auren zobe aka muku,nine de bazan dauki wannan auren nasu ba"(π²)
Captain Aryan yace"alaqa ta da Anty Ma-my daban,wannan yarinyar Kuma banda alaqa da'ita, saboda ita har yanzu Momy bata daukan kirana"
Cikin sauri Ashraf yace"what...? Amma Meyasa baka fadamin ba?"
"bansan tadama hankali ne,nabari ne idan nazo bikinka Sai muyi magana da'ita"
Ashraf yace"to shikkenan Nima zan bata haquri kafin lokacin insha Allah,wajan aiki zan tafi gobe da sassafe Nima, but kafin nawuce zanje nakai mana dinkunan mu insha Allah"
Captain Aryan yace"nima kwanciya zanyi, zanfita aiki da wuri gobe,sauqi nama kwana biyu Bata damuna da wannan kukan nata.
Ashraf yayi murmushi sannan yace"Bye"
Haly JASHERU venture's,munada kayayyaki masu kyau da inganchi ba algus da ha'inci, kayanmu daga Ethiopian ne, prdct dinmu muna Ethiopian magic hair oil, anti dandruff shampoo serum, bdy cream, hand cream, magungunan chuttuka da na mata masu inganchi da qara lfy ajikin dan
adam ga number kmr hk 07046665338 ko 07061664264 munada distributor ako Ina afadin kasarnan da ketare muna koya harkokin kasuwnchinmu ga masu bukata akan 5000 kacal
sannan munada tsuntsaye na kasashen waje tattabaru game bukata ko koya akwai riba kwarai aharkar mebuqata yasiya koya koya seyanemeni a number na kamar haka 07046665338 ko 07061664264, ku antayo ayi tafiyar daku,yar'uwa kikoyi sana'ah akan wannan farashi me sauqi kema ki kafa kankiππΌ
Sassafe tatashi ko dogon hijabin datayi sallah dashi bata cire ba,tafuto Kai tsaye tawuce kitchen tashareshi tayi mopping, sannan tafara shirya abincin breakfast, ta dauki dankalin turawa tahada Chip salad,da pancake, sai tea Wanda tasaka kayan qamshi aciki sosai,tayi sauri tagyara wajan dining table din ta gogeshi, sannan ta dauko abincin ta jerasu akai, takoma kitchen tasake gyara shi, gashi de bawani girkin kirki tayi ba amma duk qamshi yacika gidan.
tadawo falo ta share tafara mopping.
Adede lokacin Yafuto daga dakinsa yayi masifar kyau cikin uniform dinsu na sojoji,kamar kullum yar qaramar bindiga tana soke a aljihun wandon sa nabaya,tun kafin yasako qafarsa kan Stairs yaji wani qamshin girki yadaki hancinsa,Mawahib kwata kwata bataji futowar sa,tasaka mopper akan stairs din zata fara gogewa taji alamun takun mutum,bata tsammaci ganinsa ba hakan yasa tanajin takun ta zabura cikin tsoro,hakan yasa santsi ya dauketa zata zube a wajan,kamar wasa tajita acikin jikinsa, shi kansa baisan menene ya fusgeshi ba harya tareta daga faduwar da zatayi,Mawahib kuwa cikin tsoro taqi bude idonta, kawai jira take yasaketa tafadi a wajan kamar yanda yayi abaya.
Batare da tunanin komai ba Captain yatsaida ta, saida yaga ta tsaya da qafafunta sannan yasake ta, yazo ya ra6a ta gefenta zai fice daga falon,fuska babu alamun wasa yace"kikula"
Abinda yace da'ita Kenan yakama handle din qofar falon zai fice,Mawahib dabata gama dawowa daidai ba daga tsananin mamakinsa, ganin zai fita cikin sauri tace"ina kwana?"
Baice da'ita uffan ba yabude qofar falon,tasake bin bayansa da kallo tace"break fast..."
Kai tsaye yace"no"
Daga haka ko waiwayen ta baiyi ba yafice cikin sauri,Sai dirin motarsa taji alamun yafice daga gidan.
Tasaki ajiyar zuciya tayi sauri ta qarasa aikin datake, sannan ta hau Sama tayi wanka,ganin baya gidan yasa tasaka wata yar 6ingilar Riga marar hannu,gaba daya tsawon rigar Iya gwiwar ta tatsaya, tawuce ta bararraje a dinning tafara yin break fast dinta cikin kwanciyar hankali tanaci tana danna waya,tunda tazo gidan yaune Karon farko data ta6a girki,kullum batada aiki saicin lemo da biscuit,shiyasa taci abincin sosai,tatashi takoma sama tasako zumbulelen hijabi akan rigar jikinta, hijabin dogo ne har qasa,ta dauki sauran abincin data rage takaiwa megadinsu maisuna David,bayan tagaidashi ta bashi abincin,cikin girmamawa ya kar6a,saitayi mamakin yanda yake bata girma kamar wata matar wani, harta tafi David yana binta da kallo yana sake jinjina wa oga Aryan akan yanda ya murji amarcinsa hankalinsa kwance(π²)
tunda sukazo gidan shida Madam kullum suna ciki saiyau yata6a ganin tafuto,ya tabbatar wannan yarinyar yanda ta keda kyannan Sai yanda tayi da oga Aryan.
Zuwansa wajan aiki da awa uku,suka shirya fita ganin wani daji zasuga yanayinsa kafin atura rundunar sojoji zuwa dajin.
Futowa sukai susu ukun suna tafiya zuwa ma'adanar Helicopter dinsu, ga wasu sojoji a bayansu kowa fuskarsa a daure kamar Wanda aka musu albishir da mutuwa.
Tun kafin su qarasa wajan helicopter din mai launin army green driver ya tadashi, babu wata-wata suka shige ciki duka su ukun.
Tunda suka shiga idon Captain Aryan yana waje,yana ganin yanayin yanda hanyar take,basu yi tafiya mai nisaba suka qaraso dajin mai cikeda duhuwa dakuma bishiyoyi.
Jirginsu bai sauka ba,kawai a'iya wajan yake zagaye.
Major Abdullahi ya Kalli Captain Aryan yace"Captain wannan ne dajin damuke tunanin yana cikeda yan bindiga"
Cikin zafin nama Captain Aryan yace"Okay sir..."
Colonel Abdul wahab yadora da fadin"dole Sai kunyi taka tsantsan dashi,kamar yanda labari yazo mana suma labari zaije musu zamu kawo musu hari"
Cikin biyaiya Captain Aryan yace"angama Sir"
Daga Nan suka Bawa driver umarnin Yajuya dasu.
Bayan sunkoma kai tsaye office dinsa yawuce yadauki takardar taswirar dajin yana sake qarewa wajan kallo ta yanda shida rukuninsa zasu cinmusu kafin yan bindigar su ankara.
Tsawon sati uku Captain Aryan yadauka yana sake horar da rukunun sojojinsa dayake aiki dasu, saboda dajin dazasu fuskanta, har zuwa wannan lokacin Mawahib kullum saita tashi da safe tagyara gidan tayi masa girki amma ko saudaya bai ta6aci ba,tun tanayi dashi hartazo ta daina tadinga dafa wa itada David Maigadi.
zaiji qamshi yacika gidan amma acewarsa bazaici jagwalgwalon taba.
Adede lokacin bikin Ashraf yazo,bai tafi da wuri ba kasancewar kullum yana bawa Yara horo, Sai ranar daurin auren yaje, tunda yaje kwata-kwata basu zaunaba shida Ashraf din,duk da bawani farinciki sukeda auren ba, hakan bai hanasu yin kyauba,farar shadda suka saka tareda babbar riga,komai iri daya sukasa, tundaga kan takalmi har hula da Agogo da links din dayake hannun rigar, babu Wanda yake gane waye angon a cikinsu,acikin masallacin suka zauna da sauran abokan su yan unguwa,har limamin unguwar yadaura auren Ashraf da Nabiha Akan sadaki naira dubu dari lakadan ba ajalanba.
Basu samu shiga gidaba Sai can dare wajan qarfe goma da rabi zuwa lokacin mutanan gida baqi sunyi sauqi Sai Wanda baza'a rasaba,kai tsaye part din Mamy suka shiga,tana zaune tana kallo afalo taci kwalliya cikin leshi Riga da zani Sai walwali take kamar ba dare ba,falon nata tsaf Sai tashin qamshi yake,ita kadaice takeyin kallon, Sai baqi Yan kwana datayi yan'uwan mama Sadiya, suma Kuma suna dining tazuba musu abinci sunaci, tana ganin shigowar su Ashraf da Aryan ,cikin fara'ah tace"A a angwaye"
Ashraf yayi murmushi, atare suka hada baki suka gaisheta,Captain kuwa fuskarsa babu murmushi,daga gaisawar nan yayi qasa da kansa(π)
Ashraf yace"Anty Mamy yunwa mukeji"
Mamy tayi murmushi tace"to bari insama muku wani abu sai akai muku daki,ahado muku da coffee ne?"
Ashraf yasake bata amsa yace"eh ahado"
Ta miqe tsaye zata wuce kitchen ta Kalli Captain Aryan da