Showing 99001 words to 102000 words out of 110331 words
gidan,Shima kayanta kawai yakai mata sama, sannan yarage kayan jikinsa Yafuto suka cigaba da aikin tare,kokadan bai barta tayi wani aikin kirki ba, duk shine yayi ayyukan,saida suka gyara gidan tsaf, sannan yayi wanka ya shirya yafita, itama wankan tayi tashirya ta sauko falon tana kiran wayar Yan gida.
Captain Aryan ne yashigo falon hannunsa daukeda take away dayawa, abinci ne yashigo musu dashi ciki harda tuwo kamar yanda yasan cewa tana so.
Afalon suka baje sukaci su kasha, sannan Captain yajata jikinsa yana shafa cikinta, kallonsa tayi tareda dora hannunta akan nasa hannun tace"Baby baka gajiya da shafa cikin nan ne?"
Kissing din wuyanta yayi yace"to awa nawa bamu gaisa dashi ba? bayan kinmin haramiyar dumin jikinki tun muna Mota?"
Bakinta taturo gaba tace"bayan kaine ka koma wajan Yaya Ashraf karabu dani , saboda na nuna Ina kishin mijina akan Asalamiyya"
Murmushi yayi yace"Honey bazan Iya jinki ajikina hannu na yatsaya haka kawai ba, kuma kinga Ash yana cikin motar, but please kiyi haquri bazan sake ba"
Cikin sauri tabude bakinta tace"Amma ai a jirgi...."
Cikin sauri yadora bakinsa cikin nata yahanata yin mitar datake shirin yi, sai gashi Mawahib tayi dif kamar an dauke wuta, ta manta da batun fada suka fara shagalinsu.
Tunda suka dawo Abuja Captain ya sangarta Mawahib,kokadan baya barin ta tayi aiki me yawa,koda yana wajan aiki yanzu za'a ga yadawo gida duk da lokacin tashin nasu beyi ba,jarabar da cikin yasata ne yasa Captain Aryan shima har wata murjewa yake saboda yanda yake samun ta yanda ya kamata,koda wasa bai ta6a gajiya wa da'ita akan haka ba,ganin yanda yake mata qoqari yasa tadage musu da shan fruit, ko kallo suke saita hado musu fruit adan plate suna kallon sunasha.
Kokadan basuda wata sauran damuwa hankalinsu yana kwance suna gudanar da rayuwar su yanda suke so,kwata kwata Captain bashida lokacin kansa saina Mawahib saboda yanda yake bala'in tausayin ta,ko tafiya yaga tanayi saide yayi shiru yana binta da kallo jikinsa a sanyaye, tausayin dayake mata ne yasa yake hanata aikin komai saide shi yayi, haka yadage mata lokaci zuwa lokaci suna zuwa asbiti tana ganin likita daga nan ayi mata awo su dawo gida har cikinta yasake girma sosai.
Bayan sun shafe wasu watanni a Abuja tafiyar mutanan gidan Alqali zuwa Saudia tatashi,kamar yanda su Captain suka tsara, da Alqali da Alhaji khaleed, Alhaji Isah, da Momy kilishi, da Mama Sadiya, da Mamy, gaba dayansu iyayen nasu sukai shirin tafiya, ya kasance gidan babu kowa,su Mawahib basuje sallama ba,Ashraf da Nabiha ne kawai suka rakasu Airport daga nan suma suka wuce Abuja wajansu Mawahib da niyyar yimusu weekend.
Haly JASHERU venture's,munada kayayyaki masu kyau da inganchi ba algus da ha'inci, kayanmu daga Ethiopian ne, prdct dinmu muna Ethiopian magic hair oil, anti dandruff shampoo serum, bdy cream, hand cream, magungunan chuttuka da na mata masu inganchi da qara lfy ajikin dan
adam ga number kmr hk 07046665338 ko 07061664264 munada distributor ako Ina afadin kasarnan da ketare muna koya harkokin kasuwnchinmu ga masu bukata akan 5000 kacal
sannan munada tsuntsaye na kasashen waje tattabaru game bukata ko koya akwai riba kwarai aharkar mebuqata yasiya koya koya seyanemeni a number na kamar haka 07046665338 ko 07061664264, ku antayo ayi tafiyar daku,yar'uwa kikoyi sana'ah akan wannan farashi me sauqi kema ki kafa kanki💃🏼
Ranar babu wanda yakai Captain Aryan murna shida Mawahib, ita tana murna Nabiha zatazo, shi yana murna Dan'uwansa Ashraf zaizo.
Itace tayi musu girki lafiyaiye da taimakon Captain,suna sauka a Airport Captain yaje ya dauko su ita kuma tana gida.
Kallo ta kunna tanayi kadan kadan har sukazo gidan, tun a compound take jiyo dariyar su Yaya Captain shida Ashraf,ahankali tatashi tanufo qofar falon, tun kafin ta qarasa suka shigo, Ashraf yana ganin Mawahib yaji ta bashi tausayi, saboda cikin nata badan qarami bane, kona Nabiha kafin ta haihu bekai nata girma ba.
Captain yana daukeda Lil Aryan a hannunsa yaronda yake tsananin kama dashi.
Nabiha ta rungume Mawahib tace"sannu Mawahib"
tafadi maganar tana kallon cikin jikinta,cikin murmushi Mawahib ma ta rungume ta tana amsawa.
qarasa wa sukai falon suka zauna sannan suka sake gaishe gaishe, Mawahib ta yunqura zata tashi tace"bari in kawo muku lemo"
Nabiha tayi sauri tace"yi zamanki, zan dinga yin komai har weekend yaqare mutafi"
Babu musu takoma ta zauna, Nabiha ta gabatar musu da komai, sannan suka zauna aqasa kowa yafara cin abinda yakeso sai dariya suke gaba dayansu su hudun kana ganinsu kasan cike sukeda farinciki, yayinda Lil Aryan yake kwance akan kujera yana daddaga qafa irinta jarirai yana kallon p.o.p din falon.
Har yamma suna zaune babu inda sukaje, saida daddare ne sannan sukai wanka suka shirya suka fita zuwa shan ice cream sannan suka zaga gaari, basu dawo da wuri ba sai can dare sannan.
Dayan dakin dayake kusa dana Mawahib nan su Ashraf suka shige suka kwanta cikeda gajiya, sannan Mawahib da Captain ma sukai shirin tafiya, ganin yanda take tafiya daqyar hakan yasa yadauketa gaba dayanta, suka shige dakinsa, yakashe musu wuta suka kwanta.
Ko minti goma ba suyi da kwanciya ba, taji yana shafarta, tasan sarai abun yakeso, duk da itama tana buqatar hakan amma dole zasuyi haquri yau, juyowa tayi ta kalleshi tace"no Baby,banda yau"
Cikin lumshe ido yace"meyasa?"
Idonsa ta kalla sannan tace"saboda su Yaya Ashraf mana,kaida baka komai bakinka arufe tayaya hakan zai iyu?"
Cikin shaqaqqiyar muryarsa yace"Honey ko sau dayane please...,cemiki akai sudin ba zasuyi ba?"
Hannunta tasa takama fuskarsa ta riqe tace" Baby...banason rigimarka,muyi haquri mana kaji?"
Ta qarasa maganar cikin sigar lallashi.
Cikin shagwa6a ya kalleta bece komai ba, Mawahib tayi murmushi ta rungume shi tana shafa sumar kansa alamun lallashi hartaji numfashinsa ya sauya alamun yayi bacci, sannan itama ta samu nutsuwar yin baccin.
Washegari da safe bayan sungama shiryawa kai tsaye kebbi suka tafi bayan saqon gaiyata dasuka samu daga wajan Alhaji Ma'aruf na walimar da abokan sa su Alhaji Bala suka hada masa saboda yayi sabon aure bayan tsawon shekaru daya dauka babu aure.
Dawuri suka sauka hakan yasa aka fara gudanar da walimar suna nan,sai bayan azahar sannan aka tashi daga wajan walima,daga nan Mawahib da Nabiha suka dawo gidan kawun ta, inda yayar Murjanatu amaryar Alhaji Ma'aruf tahada su dukansu Nabihan da Mawahib din ta basu magungunan masu kyau irinna Yan kebbi, sannna tasake yimusu fada sosai akan Zaman haquri da juna, daga qarshe kuma ta qare tana sake wayar musu da kai akan rayuwar aurensu, sosai suka sake daukan darasi a wajanta,Nabiha kuwa har tambaya take mata akan wasu abubuwan daya shige mata duhu, babu kunya matar tayi mata bayani sosai, amma Mawahib bata tambaye ta komai ba kasancewar Sister Saudat dama tagama hure mata kunne akan kula da Captain din.
Sai yamma sukai shirin tafiya bayan ankai Amarya Murjanatu gidan Alhaji Ma'aruf, sannan suka sake sallama da Alhaji Ma'aruf din suka tafi.
Sai gab da magrib suka dawo gida,Ashraf da Aryan kuwa basu shigo gidan ba masallaci suka wuce, bayan sun idar da sallah Nabiha tashiga kitchen tahado musu maganin da Matar kawun Mawahib ta basu, ta kawowa Mawahib nata tana cewa "yanda take ziga maganin nan bari de musha muji inda gaske take"
Mawahib tayi murmushi itama ta shanye magani,daga nan suka gabatar da sallar isha'i, sannan suka zauna afalon.
Sai qarfe tara su Captain suka dawo gidan,Nabiha ta Kalle su tace"ko ahado muku abinci?"
Captain Aryan ya kalli Mawahib yace"no na qoshi,daga nan yawuce sama"
Mawahib tana ganin kallon da yayi mata tasan cewa kiranta yake, Ahankali tatashi tabi bayansa,sai Ashraf da Nabiha ne kawai afalon.
Tana shiga dakin ta ganshi a kwance tace"koka gaji dayawa ne?"
Kallonta yayi yamiqa mata hannu, babu musu taqaraso jikinsa, ajiyar zuciya yasaki yace"nagaji sosai Honey"
Fuskarsa ta shafa tace"sorry, muje kayi wanka"
Babu musu yatashi suka shige toilet, already tayi wanka kafin tayi sallar magrib, amma haka yasata saida tasake yin wani wankan, tun a toilet din takasa gane masa, har suka futo taga duk inda tayi binta yake, Ahankali tajuyo ta kalleshi tace"Baby, yanzun nan fa kagama cewa kagaji,muje kayi bacci mana"
Cikin shagwa6a yadan kalleta yakasa yimata magana,ganin jiya ta hana shi yauma karta sake hana shi ta kwana cikin tsinuwar mala'iku hakan yasa dakanta taja shi zuwa gadon takashe musu wutar dakin sannan ta kalleshi cikin duhu tace"da sharadi..."
Cikin sauri yace" naji koma menene na yarda"
Jin yanda ya rikice mata tun ba'a je ko'inaba, hakan yasa tayi murmushi tace"babu kuka,babu surutu saboda su Yaya Ashraf..."
Kansa yadaga mata alamun ya amince, daga nan salon labari ya sauya.
da farko yayi kokarin ganin yacika mata sharudan data gindaya masa, amma da tafiya tafara nisa yaji tasake sauyawa sakamakon maganin mutanan kebbi, baisan lokacin daya fara sakin qara ba, Mawahib tanajin haka tayi sauri tarufe masa bakinsa,saide tana rufe masa bakin tasake jiyo wani ihun na daban wanda ta tabbatar na Yaya Ashraf ne, ganin tahana mijinta ihu amma tanajin ihun mijin Nabiha, hakan yasa tasaki bakinsa yaci gaba da abinda yakeso ko hakan zaisa tadaina jin na Yaya Ashraf.
Gaba daya sai suka haukata saman da iface iface cikin rashin sanin su kansu sunayin ihun, hakan ya tabbatar musu da cewa lalle maganin da su kasha yanada kyau sosai.
Bai sarara mataba sai can cikin dare kafin su kayi wanka suka kwanta,dasafe baccin gajiya Mawahib take ramawa domin kuwa ba qaramin gajiyar da'ita yayi ba, batasan a halin da Nabiha take ba, baccinta tayi sosai bata tashi ba tun bayan da tayi sallar asuba sai wajan qarfe goma nasafe,wanka tayi sannan ta sauko qasa.
Anan taga Nabiha tana kallo tanacin abinci, Lil Aryan yana kwance agefenta.
Qarasowa tayi ta zauna itama tafara cin abincin Nabiha tace"Harkin tashi?"
"wallahi na tashi yanzu,bansamu bacci bane shiyasa, saida asuba sannan naji wani bacci me dadi yasake daukana"
Nabiha tace"nima ban dade da saukowa ba,qarfe tara na sauko shine nashiga kitchen nayi mana wannan abincin"
Mawahib tace"tosu Yaya Captain me sukaci? banji motsin suba ko sun fita ne?"
Nabiha tace" nakira Sweet yacemin sun fita, duk inda sukaje saisu ci abincin acan,naso in tashi dawuri inyi mana wani abun amma idona yacika da bacci,dama kuma ga gajiyar hanya data wajan walima,kawai sainayi bacci na, dana tashi naga bayanan kawai saina dafa mana Iya ni dake, Shima yaja musu basuyi break fast agidaba tunda shine ya hanani bacci jiya,amma aida zan tashi inyi mana wani abun dawuri"
Cikin sauri Mawahib ta kalleta tana tunani kode tajiyo Yaya Captain itama? Amma bata tambaye ta ba saitace"kema baki kwanta dawuri ba?"
Nabiha tayi murmushi tace"Yaya Ashraf ne ya hanani,amma yanda nagaji naso inyi bacci na"
Mawahib tazuba tea tafara Sha tace"toya za'ai sai haquri,jiya haka mukai da Yaya Captain nahanashi komai nace muyi bacci"
Nabiha tayi murmushi tace"nikam ban hana shi ba,kuma Koda wasa banyi kuskuren rufe masa baki ba, dade ace Aryan dina ya girma ne dole zan dauki mataki akan hakan, amma yanzu Kinga Aida saura,Mawahib a rayuwar Nan banajin akwai abinda nasan cewa zaisa Yaya Ashraf yaji dadi banyi masa Shiba, saboda shi din kamar kyautar Allah ce agareni,tun bansan menene soba nake qaunar sa,alokacin hankalinsa yana Kanki, hakan yasa nayi haquri ban baiyana ba naci gaba da Addu'ah, daga qarshe Kinga na mallakeshi, to mutumin dana tashi da soyaiyar sa, ban ta6a tsammanin zan sameshi ba, kuma sama taka na sameshi, tayaya ne zan hana shi jin dadin sa? ko a gidanmu barin sa nake yayi abinda yaso"
Mawahib ta ajiye cup dinta tagyara zama tace"Nabiha? Wai kina nufin dama duk yawan tambaya ta dakike yaushe Yaya Ashraf zai dawo dama sonsa kike? Amma meyasa baki fadamin ba?"
Kai tsaye Nabiha tace" saboda shi din dan'uwana ne, dole zan tayashi son abinda yake so, ke yakeso alokacin, dani dake kuma duka abu gudane Mawahib, shiyasa nake qoqarin Cusa miki ra'ayinsa"
Mawahib tace"nikam bansan wacce irin soyaiya Yan gidanku suke nunamin ba Nabiha, amma haqiqa kunmin komai, yanzu saboda farincikina saiki sadaukar min danaki farincikin?"
Nabiha tace"to ba gashi naga sakamakon sadaukar war danayi mikin ba?"
Mawahib ta karyi bread tace"kenifa dama nafada miki bana sonsa, bare kuma Yaya Captain da bana saka shi a lissafi, amma gashi Nima cikin hukuncin ubangiji Allah yadora min masifar qaunar Yaya Captain, yanda nakeji araina Nabiha, idan babu Aryan, to babu Mawahib"
Gaba dayansu suka sa dariya, Nabiha takira musu mutanan Saudia ta vedio call suna magana dasu harda Mawahib din, sun dade suna Waya sannan sukai sallama suka kashe
Mutara zuwa gobe🙏🏻
Mawahib littafin kudi ne,duk me buqata naira 500 ne kacal ta wannan account din
0164549488
Amina muhammad
GTbank
Kokuma katin MTN ta wannan number 08033300034
Idan kika karanta baki biyani haqqina ba nabarki keda mahaliccinki
Amnah El Yaqoub✍🏻
[7/20, 10:13 AM] AMINA KABIR CAPS: MAWAHIB
Sis Uzaimat
Mlm murja
Nana Asma'u ab
Sis Asma'u
Rahma delight
Fatima Baban
Fatima iddah
Salma
Ameeeeenah
Sis firdaus(writer)
Mai mahamane kagana
Sis nmera
Sis Ummi ❤️
Maman hunai
Amina Bamu
Mom Asas
Maimunat Muhammad
Umaima
Aisha musa
Mabaruka
Deeja@rh
Bilkisu saulawa
Bintu abyher
Haly jasheru
Nazifa
Fatima Abdullahi
Ummu Maryam
Bilkisu bej
Mrs Adam yar la6e😜
Ruqayya a kawu takwarar Mawahib
Mmn yzeed
Sadiya Bala zakr
Ruqayya maje
HauwaBima
Ummu Irfan
Amina kabir
Hafsat iliyasu
'yar malama me bibiyar shahaab da alama tafi tsoron bindiga akan hukumar efcc.
Bazaku qareba fa,duk wadda batada sunan taba zata gani a next page, Ina Alfahri daku💃🏼
Su Yaya Ashraf basu dawo gidan ba sai bayan azahar, alokacin Nabiha tagama yimusu girki sun sake wanka sun shirya tsaf cikin kyakykywar shiga, Mawahib doguwar riga ce ajikinta ta leshi me fadi, yayinda Nabiha tasaka riga da siket, lil Aryan yana wajan Mawahib tana wasa dashi,zama su Captain sukai a falon suna cigaba da tattauna maganar data shafi aikinsu.
Nabiha ce ta gabatar musu da abinci, yayinda Mawahib tatashi ta zauna tana dan yatsina fuska saboda yanda taji cikinta yana dan mata motsi kadan kadan.
Cikin kulawa Captain ya kalleta yace"babu matsala deko?"
Kallonsa tayi cikin soyaiya tace"babu komai, Ina lafiya"
Tare sukaci abincin gaba dayansu,bayan sun gama sukaci gaba da firarsu kad'an kad'an, saide Captain Aryan wayarsa ce a hannunsa yana turowa Mawahib kalamai tana karantawa, Nabiha sai ganinta tayi tana murmushi ita kadai.
Washegari Monday su Ashraf suka shirya suka tafi, har Airport su Mawahib suka kaisu,bayan sun dawo suka biya shopping sannan suka dawo gida.
Tun daga wajan mota yadauketa, yayinda ta saqalo hannunta ta wuyansa, har falo yakaita ya kwantar da'ita, sannan yakoma yadauko kayan dasuka siyo awajan shopping, dawowa yayi wajanta ya zauna aqasa, yayinda take kwance akan kujera yace"akwai abinda kike buqata kuma?"
Cikin kulawa tadora hannunta akan fuskarsa tace"bana buqatar komai Baby,kai kadai kamaye min gurbin duk wani abu dazan buqata"
Kansa ya gyada mata batare da yayi magana ba, ya shafa cikinta yace"dazu Naga kina runtse ido bakyajin komai yanzu?"
Cikin sauri tace" a a banajin komai"
Zama ya gyara yadora kansa akan kujerar datake zaune yayinda hannunta yake shafa lallausar sumar kansa.
Tsawon sati biyu Kenan kusan kullum Mawahib sai taji cikin yana yawan yimata motsi, ko bacci take haka zata farka, amma ganin abun baiyi mata tsananin ba yasa tayi shiru bata fada masa ba, haka sukaci gaba da kulawa da cikinsu hankali kwance, suna kuma Addu'ah Allah ya sauketa lafiya, har su Mamy suka dawo daga Saudia, basuje musu sannu da zuwa ba saita waya suka musu saboda Mawahib tayi nauyi sosai.
Washegari da safe bayan sungama break fast yana shirin fita aiki yaga tana yatsina fuska, cikin kulawa ya kalleta yace" babu matsala deko?"
Kafin tabashi amsa taji cikinta yayi wata irin juyawa, cikin azaba tafara yarfe hannu tace"cikina"
Arikice yadora hannunsa akan cikin yace"ciwo yake miki? me kike ji?"
idonta ta runtse tace"jinake yana juyawa"
Zaro idonsa yayi yace"juyawa?"
Bai jira amsar taba ya dauketa sai Mota, asbitin datake ganin likita nan yakaita,suna zuwa kuwa likitan sa ya hadasu dawata doctor mace, cikin kulawa ta duba Mawahib sannan tace zata mata scanning, Captain Aryan yana zaune agefen gadon da Mawahib ta kwanta hannunsa yana kanta yana shafa wa gabansa faduwa kawai yake tunda yaji tace ciki yana juyawa.
scanning din aka fara idon Captain da Mawahib yana kan Dr. suna kallonta, juyowa tayi ta kallesu tace"masha Allah, baby's dinku suna cikin qoshin lafiya,bawata matsala bane juyawar datakeji suna motsi ne"
Cikin sauri Mawahib tazaro idonta tareda bude baki, Captain Aryan kuwa zama ya gyara cikin farinciki yace"Dr. naji kamar kince Baby's"
Cikin farinciki ta kallesu tace"emana,yanbiyu ne acikinta ai,haba kukuwa bakuga cikin da girma ba? gashi ku kalla kuga yanda suke motsi"
Cikin sauri suka kai idonsu wajan,Mawahib tazubawa tv ido tana kallon wannan abubuwan duka acikinta suke,? ahankali tashafa cikinta, saide atsora ce take da batun yanbiyun Nan.
Captain Aryan Yasaki murmushi yace"wallahi yanbiyu ne, Alhamdulillah, Allah nagode ma,yanzu Dr. wacce shawara zaki sake bamu akan wannan cikin, banaso baby's dina su samu matsala, kuma Ina tausayin maman su, ko tashi zatayi saita runtse idonta"
Dr. tayi murmushi cikin ranta tace yau nahadu da dan soyaiya, tajuyo ta fuskance su tace"wannna tausayin daka fada kuwa dole zaka rageshi ka dinga tilasta mata kullum ta dinga motsa jiki saboda cikin nata ya girma,hakan zai taimaka mata wajan sauqin naquda,tadena zama haka kawai yanada kyau ta dinga motsa jikinta koda yaushe, sannan ahankali zata daina jin ciwon motsin harta saba daga Nan Har zuwa ranar dazata haihu, idan basa motsin ai akwai damuwa"
Cikin gamsuwa yace"Insha Allah Dr. zamu kiyaye"
Dr. tajuya ta kalli Mawahib tace"Maman twins bakya magana,ko bakya murna da ganin yaranki?"
Cikin sanyin jiki tace"Dr. mata ne?"
Dr. tajuya tasake dubawa sannan tace"maza ne, saide bamusan Yaya Allah zaiyi hukuncinsa ba, amma anan de abinda nagani dukansu maza ne"
Kallon photon yaran tasake yi tace"kuma zan'iya haifar Yara biyu?"
Likita tayi murmushi tace"idan kikai Addu'ah fiyeda biyu ma saiki ga kin haifa, komai yana wajan Allah"
Daga nan sukai shirin tafiya amma har lokacin jikin Mawahib bai rage sanyi ba, suna futowa sukai sallama da dayan likitan daya hadasu da matar data musu scanning sannan suka futo hannunta cikin nasa, adede lokacin aka wuce da wata mata akan gado Ana tura ta da uban ciki da alama naquda take, Mawahib tana ganinta saita fashe da kuka tashafa cikinta.
Captain Aryan yajata ya sakata a Mota sannan ya rufe yaja suka bar asbitin, har sukai nisa a hanya bata daina kukaba,cikin damuwa yataka birki yaja yatsaya sannan ya juyo ya kalleta yace"Honey kode bakya so nane yanzu?"
Cikin kuka ta dago ta kalleshi tace" dole kace bana sonka mana tunda natsaya kamin ciki gashinan kana gani ana mutuwa awajan haihuwa,idan na mutu ba shikkenan kahuta ba"(😂)
Murmushi yasaki yakama hannunta yariqe yana ganin yanda hawaye suke gudu a fuskarta yace"tunda akace yanbiyu zamu haifa naga hankalinki yatashi, waye yace miki ana mutuwa a haihuwa? Momy ta mutu ne? bakiga gashi ta haife mu kuma gashinan har yanzu da ranta ba? duk wanda