Showing 21001 words to 24000 words out of 110331 words

Chapter 8 - MAWAHIB COMPLT HAUSA NOVEL

13 Sep 2024

19682

tunanin me kake?"


Ashraf ya kalleshi yace"Ina tunanin abubuwan dasuka same mune dagani har kai cikin kwana biyun nan,kaiga qaddarar data sameka,nikuma Momy batason aure na da Mawahib,shekaran jiya fa anyi tashin hankali a gidan nan, inata kiran wayarka bata shiga,qarshe ma Daddy har marin Momy yayi"

Cikin sauri Captain Aryan yace"mari kuma? tome ta masa?"

Cikin sanyin jiki Ashraf yace"hakane,kayi haquri kayafemin nasa Daddy ya mari momy,amma yanzu dasauqi rashin lafiyarka yasa wancen rikicin ya kwanta,amma gaskiya Ina cikin damuwa,yanzu Momy bazata barni in auri yarinyar danake soba kenan?,wai ashe ba uncle Isah ne ya haifi Mawahib ba,Ina tunanin akwai abinda yafaru a gidannan wanda bamu saniba lokacin da muka fita karatu, kuma babu wanda yasanar damu, idan ba uncle Isah ne ya haifetaba waye mahaifinta to? yaushe Anty Mamy ta haifeta awani wajan kuma duk bamu sani ba?,amma ni koma waye ya haife ta inason ta ahaka"

Captain Aryan yayi shiru bayan yagama Jin labarin da Ashraf yabashi,to Mawahib ma dasuke gida daya Momy tatashi hankalin ta tace baza'a aure taba,inaga shi da ko yarinyar ma baisaniba?πŸ€”

Cikin damuwa yasaki ajiyar zuciya sannan yace"naka mai sauqi ne Ash..."(πŸ˜‚)

Ashraf dabai fahimci me Captain yake nufi ba cikin sigar tambaya yace"kamarya?"

Kafin Captain Aryan yayi magana Mamy tashigo dakin bakinta daukeda sallama, suna ganinta suka saki murmushi, Ashraf yace"Anty Mamy kece?"

Mamy tayi murmushi tace"nice nazo dakin tuzurai, nasan basuda dan abun ta6awa shine na kawo musu"

Captain Aryan yayi wani d'an qaramin murmushi mai aji, cikin sauri ya gyara zamansa ta hanyar had'e qafafunsa,sannan yad'auki fillo yad'ora akan cinyarsa saboda kar Anty Mamy taga abubuwan dasuke 6oye(πŸ™ˆπŸ™ŠπŸ˜²)

Ashraf daya lura da abinda yayi, cikin sauri ya kawar da kansa gefe yana murmushi,gashi ko riga babu a jikinsa, bazai iyu yasaka riga ba saboda audigar da'aka saka masa a wajan harbinsa.

Mamy kuwa batamasan wainar dasuke toyawaba tanemi waje agefen gadon ta zauna tareda bude plate din hannunta mai daukeda sweet potato banana bites, tace"kuzo kuci"

Babu musu Ashraf ya matso ya zauna agefen hannunta na hagu, shikuma Captain Aryan yana gefen hannunta na dama,sai suka sakata a tsakiyar su kamar wata yayar su, Ashraf yasaka hannu yafara ci yana lumshe idonsa, Mamy ta kalli Captain Aryan wanda fuskarsa take cikeda damuwa sannan ta d'auko daya tanufi bakinsa dashi, babu musu yabude mata bakin tasaka masa sannan yafara ci, Ashraf ya kalleta ya Sosa qeyarsa alamun kunya shime suruka, sannan yace"Anty Mamy nifa"

Mamy ta girgiza kanta sannan tadauki daya shima tasaka masa a bakinsa sannan tace" Captain dazu Alhaji yafadamin abinda yake faruwa,kayi haquri ka kwantar da hankalinka,komai mai wucewa ne, watarana sai labari, sannan ya kamata idan kagama warwarewa koda a Abuja ne kasamu qwararren likita,nasan sunada likitoci masu kyau, inde suka doraka akan magani, abun zai zama tarihi "

Ahankali yace"to Anty Ma-my zanje"

Daga haka yayi shiru baisake cewa komai ba.

Wayar Mamy ta dauki qara alamun kira yashigo,zuciyarta daya ta kalli wayar nan take taga sunan sa yafuto 6aro-6aro a fuskar wayar, mamaki ya kamata, cikin zuciyar ta ta maimaita sunan wanda yake kiran, MA'ARUF?,tome Ma'aruf zai fada mata? har abada bata fatan wani Abu yasake shiga tsakani ta dashi, batare da tunanin komai ba tayi rejecting Kiran (πŸ™†πŸ»β€β™€οΈ)

Saida takai wajan qarfe goma tana sake lallashin Captain Aryan, sannan tayi musu sallama ta futo daga dakin.


Haly JASHERU venture's,munada kayayyaki masu kyau da inganchi ba algus da ha'inci, kayanmu daga Ethiopian ne, prdct dinmu muna Ethiopian magic hair oil, anti dandruff shampoo serum, bdy cream, hand cream, magungunan chuttuka da na mata masu inganchi da qara lfy ajikin dan
adam ga number kmr hk 07046665338 ko 07061664264 munada distributor ako Ina afadin kasarnan da ketare muna koya harkokin kasuwnchinmu ga masu bukata akan 5000 kacal

sannan munada tsuntsaye na kasashen waje tattabaru game bukata ko koya akwai riba kwarai aharkar mebuqata yasiya koya koya seyanemeni a number na kamar haka 07046665338 ko 07061664264, ku antayo ayi tafiyar daku,yar'uwa kikoyi sana'ah akan wannan farashi me sauqi kema ki kafa kankiπŸ’ƒπŸΌ


******

Washegari da yamma Mawahib da Nabiha suna Hanyar dawowa daga islamiya Nabiha tace"Mawahib yau qawar ki Jiddah bata zoba"

Mawahib tace"eh wallahi nima nayi mamaki amma bari muqarasa gida saina kirata inji ko lafiya?"

Nabiha tace"Mawahib kinji abinda yasamu Yaya Captain ko? wai likita yace bazai Iya haihuwa ba,saboda harbin da aka masa"

Mawahib tace"naji wallahi,inaji lokacin da Abba yake fad'awa Mamy, ai gara hakan, dama menene amfanin haihuwar Yaya Captain? shiyasani,garama ya zauna hakan saboda may be idan ya haihun ma yaran suyi irin halinsa,saboda haka canta matse masa, ni abinda yake damuna ma ya'isheni"

Cikin sauri Nabiha tace"meyake damunki?"

Mawahib tace"Nabiha tunda abun nan yafaru nasan cewa niba yar gidanan bace wallahi bana baccin kirki,sai yanzu ne nasan dalilin dayasa Momy kilishi bata qauna ta,sannan na cewa Mamy na tabarni na koma wajan mahaifi na inde yana raye, tace karna kuskura nasake yimata maganar sa,gaba daya narasa yanda zanyi, gashi inajin gabana yana yawan faduwa kusan kwana hudu kenan, haka kawai sai gabana yadinga faduwa"

Nabiha tace"innalillah...,toki dinga Addu'ah,amma maganar tafiya kima dainata Mawahib, kema kinsan idan kika tafi nima bazanji dadi ba"


******

Alhaji khaleed mahaifin Nabiha, yadubi sauran yan'uwansa yace"koda ace likita bai bamu shawarar muyiwa Aryan aure ba, dole ne dukansu ayi musu aure,saboda gudun kada wata matsalar tasake faruwa,inda ace tun farko sunyi aure da wuri,da yanzu daga shi Ashraf din har Aryan din babu wanda baida d'ansa na kansa,to amma mun zuba musu ido, munbar yara suna zaune babu aure"

Alqali yace"wannna hakane,nima nayi wannan tunanin,kuma munyi magana da mahaifiyar su,nariga nafada mata auren Mawahib da Ashraf babu fashi,to itama takawo wata magana cewa shi Aryan din tasamo masa yarinya,yar wajan qaninta wato Asalamiyya,saboda haka yanzu gaba dayansu su hudun za'a hada ayi auren su,itama Nabiha akirata aji idan akwai wanda takeso"

Alhaji Isah yace"wannan shawarar tayi Yaya, Allah yabasu zaman lafiya"

Alqali yace"Amin Amin, yanzu kiramin ita Mawahib din"
Yajuya ya Kalli Alhaji khaleed yace"kaima Khaleed kiramin Nabiha"

Babu 6ata lokaci Alhaji Isah yadauki wayarsa yakira Mamy,tana dauka yace"turomin yarinyar nan bakin get yanzu yanzu"

Mamy tanajin haka tasan cewa akwai abinda yake faruwa, kuma bazai wuce maganar Mawahib din da Ashraf ba,to amma bata tabbatar ba,dole zata masa biyaiya ta tura Mawahib din dan taji ko menene dalilin kiran.

Mawahib tana zuwa taga Nabiha agaban iyayen nata a zaune,cikin ranta take fadin to lafiya?
Ta qarasa itama ta zauna tareda sallama.

Alqali ya dubeta yace"Mawahib munyi magana da iyayenki gasunan a zaune,muna so muhada aurenki da Ashraf,to amma muna so muji ta bakinki,kina sonsa kokuwa?"

Gaban Mawahib ya yanke yafadi,tayi tunanin tunda akayi tashin hankalin nan da Hajiya kilishi ai magana ta wuce,harga Allah batason Yaya Ashraf,koda wasa batason tashin hankali gara ta nesanta kanta da Momy kilishi, to amma yaya zatayi? tayaya zata kalli idon mutanan dasuka riqeta tsakani da Allah tun tana yarinya suka ciyar da'ita suka tufatar da'ita, suka shayar da'ita tace musu batason d'ansu?

jin tayi shiru yasa Alhaji Isah yace"kinyi shiru Mawahib koda matsala?"

Cikin sanyin jiki tace"Babu matsala Abba Ina sonshi"

Alqali yayi murmushi yace"to Alhamdulillah,Allah yayi miki Albarka,tashi kije"

Ahankali ta amsa sannan tatashi tabar wajan.

Alqali ya kalli Nabiha tace"Nabiha kefa? akwai wanda kike tare dashi ne yanzu?"

Nabiha tayi shiru tana tunani,mutumin datake qauna tun tana 'yar qanqanuwarta hankalinsa da zuciyarsa suna wajan Mawahib,kuma itada Mawahib kamar abu dayane,dole zatayi haquri dashi ta auri wani koda kuwa hakan zai cutar da zuciyar ta.
Ahankali tadago ta aalli Alqali sannan tace"A a Daddy babu"

Alqali yace"kin tabbata?"

Cikin sanyin jiki tace"eh Daddy"

Yace"to shikkenan,zamuyi magana daga baya, tashi kije"

Cikin nutsuwa tatashi tatafi tanajin zuciyar ta tana karyewa kamar ta fashe da kuka,daqyar ta'iya qarasa wa part dinsu, tana zuwa tun daga falo taji zuciyar ta tana mata zafi,lokaci daya tasaki wani irin kuka maicin rai tafada jikin Mama Sadiya tana fadin"Mama wallahi Ina sonshi"

Mama Sadiya ta dinga binta da kallon mamaki tace"ke kalau kike kuwa? wani abun su Alhajin suka fada miki?"

Cikin kuka tace"wai Mawahib zasu bawa Yaya Ashraf,Mama wallahi Ina son Yaya Ashraf...."

Mama Sadiya tadago Nabiha daga jikinta cikin sauri tace"Nabiha kanki daya kuwa? kirasa wanda zaki so sai d'an Yaya kilishi? kirufamin asiri banason tashin hankali,ko ba'a kan idonki komai yafaru ba shekaran jiya jiyan nan?"

Cikin kuka Nabiha tatashi tashige d'akinta, Mama Sadiya tabita da kallo tana tafa hannu tana sallallami.


******
Haly JASHERU venture's,munada kayayyaki masu kyau da inganchi ba algus da ha'inci, kayanmu daga Ethiopian ne, prdct dinmu muna Ethiopian magic hair oil, anti dandruff shampoo serum, bdy cream, hand cream, magungunan chuttuka da na mata masu inganchi da qara lfy ajikin dan
adam ga number kmr hk 07046665338 ko 07061664264 munada distributor ako Ina afadin kasarnan da ketare muna koya harkokin kasuwnchinmu ga masu bukata akan 5000 kacal

sannan munada tsuntsaye na kasashen waje tattabaru game bukata ko koya akwai riba kwarai aharkar mebuqata yasiya koya koya seyanemeni a number na kamar haka 07046665338 ko 07061664264, ku antayo ayi tafiyar daku,yar'uwa kikoyi sana'ah akan wannan farashi me sauqi kema ki kafa kankiπŸ’ƒπŸΌ


******
Cikin damuwa tasake goge hawayen idonta tace"Mamy dan Allah kibarni natafi....,ni bazan Iya auren Yaya Ashraf ba,Momy kilishi kasheni zatayi, kibarni natafi wajan mahaifi na Mamy"

Mamy da ranta yayi baqiqqirin tace"kinsan bakya so dan me zaki amince musu? babu inda zan barki kije,ko Ina halin hauka bazan bari kikoma wajan mahaifin kiba,bare kuma inada hankali,ki daina 6ata lokacin ki kina kuka itama mahaifiyar tasa bazata bari ayi auren ba,konima nan har abada bazan yarda ki auri yaron Yaya kilishi ba, gara kitafi maiduguri kiyi zaman ki acan, kokuma Alhaji yasakeni mutafi gaba daya, amma nima bana goyon bayan wannan auren "

Mawahib tanajin abinda Mamy tafada taji hankalin ta yadan kwanta,ko banza tasan baza ayi auren ba tunda gashi tasamu goyon bayan Mamy, hakan ne yasa hankalin ta yadan kwanta hartaje daki ta kwanta


******

Washegari da safe suna zaune a dining ng suna break fast su hudu,Alqali da Hajiya kilishi, da Ashraf da Aryan,Hajiya kilishi ta kalli Aryan taga banda ruwan black tea babu abinda yakesha, cikin damuwa tace"Aryan bakasan cin abinci,kacire damuwar nan aranka kadauki qaddara komai fa mai wucewa ne"

Cikin sanyin jiki yace"to Momy"

Alqali ya ajiye cup din hannunsa ya kalli yaran nasa yace"mungama magana da iyayenku,zuwa jibi za'a saka muku ranar aurenku,Ashraf Mawahib, kaikuma Aryan za'a hada auren ka da Asalamiyya 'yar gidan kawunku Tafida"

Cikin sauri Aryan dayake shan tea yaqware,lokaci daya yariqe qirjinsa yafara tari.
Cikin sauri Hajiya kilishi tatashi tafara bubbuga bayansa tana masa sannu.
Alqali yasan ma'anar tarin da Aryan yakeyi,yana nufin bayason auren, kuma bazai lamunci jin wata magana ba,dolen dole yayi aure kodan neman lafiyarsa.

Yana gama wannan tunanin yatashi yabar wajan.

Yana ganin tashin Alqali ya kalli Hajiya kilishi yace"Momy nifa banason auren nan..."

Cikin sigar lallashi tace"yanzu Aryan menene laifin Asalamiyya?"

Cikin tsananin damuwa ya lumshe idonsa yabude,su Momy bazasu gane ba,tayaya ne zai fada musu cewa shifa yana aure batare da sun sake qaqaba masa wani auren ba?
Cikin damuwa yatashi daga dining d'in yafuto daga part din gaba daya.

A compound din gidan yatsaya yarasa Ina zai nufa? wa zai fadawa halin da yake ciki yabashi shawara? gaba daya kansa yadauki zafi jiyake lallausar sumar kansa tana tiriri,bayan yagama yankewa kansa shawara kai tsaye yanufi part din Mamy.

Yana zuwa falon yaga babu kowa sai qarar TV datake yi,zama yayi acikin daya daga cikin kujerun falon yayi tagumi hannu bibbiyu tareda zubawa tv ido,amma azahiri ba kallon yakeba,ya lula ne cikin duniyar tunani, saida yagama tunani yaga bashida mafita sannan yasaki ajiyar zuciya, yajuya gefensa anan yaga wata yar madedeciyar brezia akan kujera, ya qarewa breziar kallo ya yatsina fuska,yasan aikin Mawahib ne,ya kalli qoqon breziyar yana tunanin yanzu boobs dintane yake cika duk wannan qoqon? bazai iyuba, saide in cuko take,duka duka nawama take dazata saka wannan? dama duk ciko ne,za'a bawa dan'uwan sa fake,shikuma Ashraf duk ya rangauce jiyake abubuwan ne (πŸ˜²πŸ™Š)


Adede lokacin Mamy tafuto daga dakinta taga Captain yana kallon brezia,mamaki ya kamata meyake damunsa ya zauna shi kadai anan yana tunani?

Cikin sauri taqaraso wajansa ta zauna tace"Captain meyake faruwa ka zauna anan kana tunani?"

Shiru yayi yakasa bata amsa,harta fitar darai ba zaiyi magana ba, sai can kuma yace"Babu komai"

Mamy tayi shiru tana tantama aranta tabbas akwai damuwa,akwai abinda yake damun Captain, tajuya ta kalli breziyar Mawahib data sameshi yana kallo, ta qwala mata kira....

Tana daga cikin dakinta ta amsa tafuto da sauri,tana sanye cikin riga da wando,sai hula mai girma data saka akanta, kwata-kwata baka ganin baiwar dogon gashin kanta, wandon na jeans ne sai kuma rigar yar qarama mai launin ja,hips dinta yacika wandon taf... sai rawa sukeyi, cikin sauri Captain yadauke idonsa daga kanta.

Mawahib tana qarasowa falon ganin Captain a zaune tayi tunanin Ashraf ne,shiyasa tad'an saki ranta tayi murmushi har dimple dinta suna futowa tace"laa Ya Ashraf yaushe kashigo?"

Binta yayi da kallo cikin ransa yace"dama tana murmushi?"(πŸ€”)

Kafin yayi magana Mamy tace"banason shashanci Mawahib,dauke wannan abar daga anan...yayun nakima har gobe kin kasa ganesu"

taqarasa maganar tana yi mata nuni da breziyar ta dake gefen Captain,sai a lokacin Mawahib tashiga taitayinta,tanajin furucin Mamy tasan cewa toba Yaya Ashraf bane, Yaya Captain ne,nan take tashiga hankalin ta,tasa hannu ta dauki breziyar ta sum-sum takoma cikin dakinta.

Mamy ta kalli Captain tace"muje daki?"

Babu musu ya daga mata kai,tatashi tayi gaba shikuma yabiyo bayanta har cikin d'akinta, suna zuwa ta zauna abakin gadonta shima ya zauna, ta kalleshi dakyau, cikin sigar lallashi tace"meyake faruwa? wani abunne yasake ya faruwa kuma?"

Bude bakinsa yayi zaiyi mata magana amma saiya kasa,saboda raunin da zuciyarsa tayi,ahankali yadora kansa akan kafadarta,babu wata-wata yasaki wani irin kuka (πŸ˜³πŸ™ŠπŸ™†πŸ»β€β™€οΈ)

Gaban Mamy yayanke yafadi, ta tabbatar akwai babbar matsala, Captain da kuka? yaushe rabon dataga yana kuka? zata Iya cewa tun suna yara

Ajiyar zuciya ta sauke tadora hannunta akan lallausar sumar kansa tafara shafawa, sannan tamaida hannunta kan gadon bayansa tafara bubbugawa alamun lallashi, batace dashi uffan ba, saida tabarshi yayi kukan, yaji sauqin rad'ad'in dayake damunsa, sannan tad'agoshi daga kafad'arta tace"fad'amin meyake faruwa?"


"Anty Ma-my....su Daddy ne sukace zasu saka mana rana jibi,nikuma banason auren"

Mamy ta lumshe Idonta tabude, sannan tace"yanzu Captain banda shagwa6a kawai saboda bakason aure saika fara kuka?meyasa bakason auren?,ko akwai yarinyar dakake so?"

Cikin sauri ya girgiza kansa sannan yace"ni babu yarinyar danakeso Anty Ma-my"

Mamy tace"to meyasa?"

Duk da gabansa yana faduwa hakan bai hanashi baiyana mata gaskiya ba,may be zai samu shawarar dayake nema a wajanta,kai tsaye yadago kansa ya kalle ta sannan yace" SABODA INADA AURE"

Cikin sauri Mamy tace"What...?"








(Ina ganin ikon Allah ni AminaπŸ˜‚
kowanne irin matsayi abokiyar shawara zata koma bayan Aryan yagano itace sirikar tasa? πŸ€”




Mawahib littafin kudi ne,duk me buqata naira 500 ne kacal ta wannan account din
0164549488
Amina muhammad
GTbank

Kokuma katin MTN ta wannan number 08033300034

Taredashedar biya ta wannan number 08033300034
idona nahana bacci nacinye lokaci na narubutashi,bazanja Allah ya'isa ba,amma muddin kika karanta baki biyani haqqina ba nabarki keda mahaliccinki faqadπŸ‘ŒπŸ»





Amnah El Yaqoub ✍🏻
[7/9, 9:20 AM] AMINA KABIR CAPS: *Page 19&20*


Mawahib littafin kudi ne,duk me buqata naira 500 ne kacal ta wannan account din
0164549488
Amina muhammad
GTbank

Kokuma katin MTN ta wannan number 08033300034

idona nahana bacci nacinye lokaci na narubutashi,bazanja Allah ya'isa ba,amma muddin kika karanta baki biyani haqqina ba nabarki keda mahaliccinki faqadπŸ‘ŒπŸ»



Captain Aryan yayi shiru yana kallonta ganin yanda ta tsorata takuma d'auki zafi akan maganar,to inaga Momy kilishi Kuma?

Cikin tashin hankali Mamy taci gaba da fad'in"innalillahi...to garin Yaya hakan tafaru? meyasa kayi hakan Captain?"

Ahankali Captain yafara yimata bayani tiryan-tiryan yanda abubuwa suka faru harya gama sannan yace"ni bansan Yaya zanyi da Momy ba"

Mamy tayi firfita da hannunta alamun garin yafara yimata zafi tace"Hasbunallahu wani'imal wakeel, toshi mahaukacin inane zaiyi ma aure babu sanin iyayenka?"

Captain Aryan yayi shiru yakasa bata amsa

ganin yayi shiru hakan yasa ta fahimci bashida amsar dazai bata, tasaki ajiyar zuciya tace"wannan ba maganar daza'a yi shiru bane,maganar aure aita wuce wasa,zanje In samu Yaya kilishi Infada mata komai"

Cikin sauri Captain yace"a a Anty Ma-my,kada kisake yin wani laifin a wajanta, zan fad'a mata"


"to Ashraf yasani ne?"

"A a ban fad'a masa ba"
tace"toka sameshi kafad'a masa,kuje kusamu Daddynku da Yaya kilishin kufad'a musu komai "

Cikin gamsuwa ya girgiza mata kansa alamun amsawa, sannan yatashi yafuto daga dakin itama tabiyo bayansa gaba daya jikinta yayi sanyi,qwaqwalwar ta tatsaya cak tarasa gane tunanin me zatayi....


******

Abba yana zaune afalo yana ganin labarai,ya kalli Mamy yace"kiramin Ruqayya"

Mamy tatashi tashiga d'akin Mawahib a lokacin tana zaune akan sallaya tana karatun qur'ani, Mamy ta kalleta tace"kizo"

Saida takai qarshan ayar datake karantawa sannan tarufe qur'anin tafuto, tana zuwa ta zauna cikin ladabi tace"Abba gani"

Alhaji Isah Yadauki remote yarage qaran tv sannan yace"gobe muke shirin saka ranar ku keda Ashraf,Ina fatan de babu wata matsala ko?"

Kafin Mawahib tayi magana Mamy tace" Alhaji matsala ta nawa kuma? nifa dakun bar wannan maganar tazauna tajira Nabil din har zuwa lokacin dazai shirya"

Abba ya gyara zamansa sosai Yajuya yana kallon Mamy yace"saboda me? shi jinin nawa ne bakya so 'yarki ta aura kinfi son taje ta auri d'an d'an'uwanki?"

"bahaka bane Alhaji"

Cikin zafi Abba yace"to menene Maryam?tunda munkira yarinya jiya kuma ta amsa mana da bakinta tanaso to meyasa zaki dauko wata maganar kuma?"

Mamy tace"Alhaji, kaida kanka kasan cewa uwar yaron nan bata qaunar hadin nan,tunda Mawahib take cikin gidannan banta6a ganin Yaya kilishi tayi mata kallon arziqi ba,tayaya ne inaji Ina gani zan bari adauki yata qwalli daya akaita wajan Yaya kilishi bayan nasan cewa idan akwai wadda Yaya kilishi ta tsana a duniya to baiwuce nida Mawahib ba?"

Abba yace"Okay to yanzu hukuncin da muka zartar nida Yaya Alqali shi zaki warware kenan saboda kina taqama Ruqayya 'yarki ce?"

Mawahib tanajin haka idonta yaciko da qwalla,bata ta6a ganin Mamy da Abba suna sa'insa ba,sai gashi akanta hakan tana faruwa,ahankali tatashi tabar wajan takoma dakinta tana share hawaye

Mamy ta kalli Abba tace"Amma wanne irin hukunci ne wannan?,bayan kunsan abinda yake faruwa saboda me zaku hada aurensu? nide Alhaji bana maraba da wannan auren,idan kuma kuka dage sai kunyi tozan tattara kayana nabar muku gidanku"
Tana fadin haka ta miqe zatabar wajan.

Abba yace"to aikuwa dagake har Yaya kilishi,baku Isa kuhanamu abinda mukai niyya ba,idan kuma zaku fara toga wajan nan"


******


Da daddare suna d'akinsu,Ashraf sai waya yake da abokansa na wajan aiki yana fada musu very soon zai zama ango

Captain yana zaune agefen gado yana kallonsa, saida yabari yagama yin wayar sannan yayi ajiyar zuciya yace"Ashraf"

Ashraf dayake tsaye

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login