Showing 57001 words to 60000 words out of 110331 words
musu hannu yake.
Suna daukan hanya batare daya kalleta ba yace"cire glass dinnan"
Cikin sauri tasaka hannunta tacire, tabude Jakarta tasaka shi aciki, babu wanda yasake magana a cikinsu, har sukaje wajan wankin kai, wanda ita de batasan inane ba, shine ya kaita da kansa, suna tsaya tabude zata fita,taji yace"qarshan number Anty Ma-my"
Cikin sauri ta juyo ta kalleshi saitaga atm dinsa yake bata,tana so tace masa akwai kudi a Jakarta to amma tana shakka ganin yanda yahade fuskarsa, babu musu ta kar6a sannan tace"thanks"
"idan kingama kikirani"
Kallonsa tayi sannan tace"to"
tafuto tarufe masa motar, sannan tashige wajan, tana jujjuya atm din nasa a hannunta tana tunani ,qarshan number Mamy ne pin dinsa? wacce irin shaquwa cene a tsakanin sa da Mamy?
Saida yaga shigewarta sannan yaja motar yana fatan ace Karta sake maida wannan glass din idonta saboda ba qaramin kyau yamata ba.
Ta dade awajan sosai kasancewar gashin nata yanada yawa,kuma saida aka mata harda fulawa ta baqin lalle a hannunta, sannan tabasu atm din suka cire kudin su,ana gama wanke mata lallen takira wayar Mamy bayan sun gaisa zuciyarta daya tace"Mamy dan turomin number Yaya Captain,naje wajan wankin kai yace idan nagama nakira shi"
Mamy tayi shiruuuu tana tunani,mata ce take tambaya aturo mata number mijin ta wai yaran nan anya Zaman nan nasu kuwa babu gyara? kina zaune da miji wata da watanni amma bakida number sa wacce irin rayuwa ce wannan?ajiyar zuciya tayi, cikin ranta tace akwai matsala, da sauran gyara,a fili saitace "to bari inturo miki,kingama ne yanzun?"
Tace"eh nagama,inaso na koma da wuri saboda baquwarki da kikace zatazo Kuma Kinga har azahar tayi"
Mamy tace"to shikkenan Allah Yakiyaye hanya"
takashe waya tatura mata number Captain,sannan takira qawarta Hajiya Saudat,bayan sun gaisa Hajiya Saudat tace"yanzu nake shirin kiranki dama, ki turomin address din gidan zanfita yanzu"
Mamy tayi ajiyar zuciya tace"Sister Saudat akwai matsala,Zaman yarinyar nan taki akwai gyara, idan kinje inaso kisha cikinta sosai tafada miki duk abinda yake faruwa Sai kiyi settling komai,Ina aiko mata maganin mata tana tambaya ta maganin menene, sannan yanzu haka da'ita nagama magana tana tambaya ta number mijin..."
Sister Saudat tace"haba sister Maryam,to tayaya zakibarta haka bazaki kirani da wuri ba Kuma yarinya tana zaune a'irin wannan garin, gari garin 'yan boko Kuma mijin ta me yawan fita salon yaje yagano wata a waje?"
Cikin damuwa Mamy tace"Saudat bazaki gane ba, naci buri sosai akan auren Mawahib,nabaki labarin yanda auren ya kasance de,a yanda na tsara maiduguri naso turata duk su koya mata komai ayi mata gyaran jiki kamar ma wata biyu,to komai yazo a baibai, Ma'aruf ya ruguza min komai"
Sister Saudat tace"to shikkenan, yanzu de ki kwantar da hankalinki,zanje gidan ai, duk yanda ake ciki zakijini"
Daga nan sukai sallama tareda kashe wayar.
******
Wani soja ne yazo ya dauketa ya maida ta gida, tana zuwa tacire hijabin jikinta tafara qoqarin girkawa baquwar tata abinci,bata gama ba Sai yamma, saboda tahada harda girkin Captain tayi komai gaba daya,tayi wanka ta zauna afalon kenan, David yashigo yasanar da'ita tanada baquwa,ta bashi umarnin yashigo da'ita,saida yakawo ta har falo sannan Yajuya, Mawahib tatareda cikin farinciki,sister Saudat ta rungumeta tana kallon tsarin gidan nasu cikin ranta tana yabon kyan gidan, zama sukai a kujera Mawahib ta gabatar mata da abincin da tayi mata tareda lemuka da ruwan sha,ta kunna musu kallo sunayi, sister Saudat tadage tana kallon duk da ba ma'abociyar kallon bace,amma dan Mawahib din tasake da'ita yasa tasaka kallon agaba sunayi suna fira kad'an kad'an har yamma,saida taga Mawahib din tasaki jiki da'ita sannan tace"karatu yafara nisa Kuma gashi Captain yagudo dake Abuja"
Cikin murmushi tace"A a baiyi nisa ba,ai yanzu ne zamu shiga level 200"
Sister Saudat ta jinjina kanta sannan tace"hakane fa,to amma ai zai barki Kici gaba da karatun ko?"
Tace"bansani ba wallahi,ban ta6a yimasa maganar ba"
kafin sister Saudat tayi magana Captain yashigo falon,gaba dayansu qofar suka kalla,Mawahib tana ganinsa tayi qasa da kanta, tace"sannu da zuwa"
bai amsa mataba ya tsugunna cikin ladabi yacewa sister Saudat"sannu da zuwa,barka da yamma"
Cikin farinciki tace"yawwa sannu da zuwa,ya aiki?"
Kansa a qasa yace"Alhmdulillah"
Daga nan yatashi yawuce sama,Sis Saudat ta bishi da kallo cikin ranta tana fadin lalle 'yar tasu tayi dacen miji irin wanda kowacce mace take burin samu.
Mawahib tadago kanta taci gaba da kallo ko inda Captain yake bata kalla ba, cikin mamaki sister Saudat tace"bazakibi mijin naki bane?"
Zaro idonta tayi sannan tace" la'ila...aibana zuwa"
Sis Saudat ta jinjina kanta sannan tace"Meyasa?"
Mawahib tace"ai agida ma bayaso muna zuwa dakinsu,nikuma tsoro nakeji"
Cikin shan ciki Sister Saudat tace"eh Kuma hakane,dole Kiji tsoro,babu dadi ka takura wa mutum,amma idan yanason wani abu fa yakuke?"
Mawahib tace"ai girki ne kawai,idan nayi masa na ajiye masa shikkenan,zaizo yaci,girkin ma da bayaci, shine Mamy tace inci gaba dayi masa"
Sister Saudat ta zubawa Mawahib ido tanajin komai, tace"amma duk dadin girkin ki bayaci? yanzu yanaci sosai ko?"
Tace"yanaci yanzu,idan yaci zai fita wajan aiki"
Sis Saudat tace"to idan yadawo yana sake fita ne? kokuma zama kukeyi agida?"
Tace"wataran yana fita,amma ba sosai ba,nide dakina nake tafiya inyi bacci shikuma yana aiki a falo"
Sis Saudat ta Zaro ido tace"bacci?"
Mawahib tace"eh,saboda nagaji,kullum sainayi gyaran gida da girki"
Sis Saudat ta kalleta ayanda tadanji zancen nata ta fahimci abubuwa dayawa,cikin sigar dabara tace"to yanzu kitashi kije dakinsa kiji koda abinda yake buqata, Kinga yadawo daga wajan aiki,Kuma Ina zaune afalon,bazai Iya futowa yazo yazauna ba, kije kiyi masa sannu da zuwa idan akwai abinda yakeso sai kizo kikai masa"
Mawahib tace"to"
Sannan tatafi sama cikin ranta tana mamakin wannan baquwa,Kuma daga zance saita turata dakin Yaya Captain?
to taje ta masa me?
Sis Saudat tabi bayan Mawahib da kallo ta girgiza kanta,da alama girman qashi ne da'ita kawai,amma batada wayo,tuni matan bariki zasu Iya qwace mata mijin...
tana zuwa bakin qofar dakin takama handle din dakin ahankali tatura tashiga a karo na biyu tunda tazo gidan,wani irin sanyin esi da daddadan qamshi ya daki hancinta,adede lokacin ya futo daga toilet yasaka hannunsa biyu yana gyara sumar kansa,murdaddan jikinsa ya baiyana sai sheqi fatarsa take,tana ganinsa tayi sauri tajuya baya tareda runtse idonta tana jiran taji saukar duka kamar yanda yata6a cewa zai daketa lokacin dataje dakinsu.
Kallonta yayi,yana mamakin zuwanta dakin, ahankali yatako yazo dab da'ita,kamar zai rungumota tabaya,yadan karkatar da kansa dede kunnanta cikin rada yace"lafiya?"
Cikin sauri ta girgiza masa kanta,jitake zaiyi mata masifa saitaji sa6anin haka,saima magana daya mata cikin rad'a.
ganin batason hada ido dashi ne yasa yajuya yazauna abakin gadon sannan yace"bani mai"
rikicewa tayi,cikin sauri tajuya wajan mirror ta dauko masa wani mai batasani ba shi yake shafawa koba shi bane, ta qarasa wajansa kanta aqasa taqi kallonsa tace"gashi"
Kallon fuskarta yayi yaga idonta a runtse,da alama a rikice take,wani dan qaramin murmushi yayi cikin jin dadi yasake cewa "bani kayana"
Cikin sauri tasake juyawa tabude Wadrob din tarasa wanne kaya zata bashi?
ganin yamma ce Kuma tasan yafi saka kayan shan is'ka saita dauko masa qananun kaya,ta bashi, yana kar6a tayi sauri zata fice daga dakin taji yace"zonan"
gabanta ne yafadi,mekuma zata masa?
Ahankali tajuya taqarasa wajansa ta tsaya kanta aqasa tana wasa da hannunta, kamar wasa taji ya fuzgota saigata d'are d'are akan cinyarsa,idonta ta runtse hannunta na hagu ta dorashi akan qirjinsa da fatar jikinsa tayi sanyi sosai, kallonta yayi yaga idonta a runtse,dan qaramin bakinta Sai motsi yake amma takasa magana,meyasa ne wasu lokutan take tsorace dashi? ya kamata ace yafara qoqarin cire mata wannan tsoron nasa, hannunta dayake kan qirjinsa ya kalla ahankali yasaka hannunsa ya janye hannun nata,sannan zubawa fulawar hannunta ido yafara murza hannun, wani iri Mawahib tafara ji ajikinta, wani irin yanayi wanda tunda take bata ta6a Jin irin wannan yanayin ba,amma idonta a runtse yake har lokacin,daina murza mata hannun yayi,cikin sigar rad'a yace"yaushe aka miki wannan abun?"
Sarai tasan da zanen lallan hannunta yake,batareda tabude idon ba tace"awajan wanke kai"
Cikin wata irin murya qasa qasa kamar meyin rad'a yace"shine baki nunamin ba? i luv it..."
Yafadi haka sannan yakai hannun saman lips dinsa,ya lumshe idonsa yasakar mata wani irin kiss
Cikin sauri tabude idonta ta kalleshi,a lokacin shima yabude idonsa suka zubawa juna ido tsawon yan sakwanni,cikin ranta take mamaki dama yana lura da wannan abun?
cikin sauri tafara motsa wa zata bar jikinsa, bai hanata ba yabarta tatashi,saide tana zuwa bakin qofar dakin tun kafin tabude taji yace"wait.."
Cak taja ta tsaya awajan,amma koda wasa batayi kuskuren juyowa ta kalleshi ba, tashi yayi yasaka kayansa, yafesa turare sannan yatako yazo wajanta,kudi yabata me yawa yace"kibata tasha mai"
Kanta ta gyada masa sannan tace"to Allah yasaka da Alkhairi"
Yaji dadin addu'ar data masa,baice da'ita komai ba, yakamo hannunta suka futo, saida sukazo falon qasa sannan yasaki hannunta yafice daga gidan gaba daya
Sister Saudat taga yanda yaruqo hannun Mawahib din amma saita maze ta nuna bata gansu ba har Mawahib kusa da'ita tazauna, tana zama taji tana wani qamshin turaren daban,tayi murmushi cikin jin dadi da alama akwai abinda yafaru,taji dadin hakan sosai,Mawahib tabata kudin tace"gashi yace kisha mai"
Sister Saudat takalli wannan uban kudi cikin ranta tafara tunani irin wannan kudi haka ai dole nema ta hurewa yarinyar nan kunne Shima yaga canji(π)
Cikin farinciki tadauki kudin sannan tace" kice nasa d'an namu wahala,to kice masa nagode sosai"
Tamatso kusada Mawahib din sosai takama hannunta duka biyun tace"toki saurareni dakyau kina Jina?"
Mawahib tadaga kanta dasauri tana kallon cikin idonta,hannunta na dama yanakan na hagu tana shafa inda Captain yasakar mata kiss dazu,har yanzu tanajin abun acikin jikinta.
Sister Saudat tace"akwai kayan dana taho miki dasu suna cikin mota, su zaki dinga sakawa karki sake shiga irin wannan tajikinki,wannan kayan kine tunna gida karki sake sakasu,kuma kidaina kwana adakin ki ke kadai,kidinga tafiya dakin mijinki Kuna kwana tare,abinci kidinga sakashi agaba yanaci yana kallonki kokuma ki zauna kuci tare,banaso nasake ji kince idan kikaje dakinsa wai bayaso ko agida, gida daban Mawahib,can gidanku ne gaba daya, nan Kuma gidanki ne kekadai Sai abinda kika tsara sannan zaiyi,sannan magungunan da mahaifiyar ki tabaki kici gaba da amfani dashi kullum kinji abinda nace?"
Cikin sanyin jiki tadaga kanta, sister Saudat tace" yawwa,muje ki rakani ni tafiya zanyi"
Tashi sukai tarakata har wajan motar ta,tabude motar ta janyo mata wata uwar jaka tabata sannan sukai sallama tatafi,Mawahib ta janyo jakar tajuyo cikin gida jikinta a sanyaye tana tunanin maganar sister Saudat, kai tsaye dakinta ta wuce da jakar tazauna akan gado tabude duk tafitar da kayan ciki,wasu irin shedanun kayan shan is'ka ne dana bacci abun babu dadin gani inji ustaz.
kayan ta d'ad'd'aga tagama kare musu kallo, tasan cewa tun agida Mamy tana siyo mata qananun kaya tana amfani dasu amma wannan kayan na daban ne,tayaya zata Iya saka su taje dakinsa?
anya bazai yimata fadaba?
(sister Saudat Captain yana godiaπ)
Haly JASHERU venture's,munada kayayyaki masu kyau da inganchi ba algus da ha'inci, kayanmu daga Ethiopian ne, prdct dinmu muna Ethiopian magic hair oil, anti dandruff shampoo serum, bdy cream, hand cream, magungunan chuttuka da na mata masu inganchi da qara lfy ajikin dan
adam ga number kmr hk 07046665338 ko 07061664264 munada distributor ako Ina afadin kasarnan da ketare muna koya harkokin kasuwnchinmu ga masu bukata akan 5000 kacal
sannan munada tsuntsaye na kasashen waje tattabaru game bukata ko koya akwai riba kwarai aharkar mebuqata yasiya koya koya seyanemeni a number na kamar haka 07046665338 ko 07061664264, ku antayo ayi tafiyar daku,yar'uwa kikoyi sana'ah akan wannan farashi me sauqi kema ki kafa kankiππΌ
******
Kasancewar yasan akwai baquwa a gidan hakan yasa bai dawo ba sai dare,saide harya dawo gidan yana mamaki aransa menene yakawo ta dakinsa dazu?
wani tunani yayi Kode wannan baquwar ce taturo ta?
Idan kuwa hakane zuwan ta yamasa dadi zai so ace Koda yaushe tana kawo musu ziyara(π)
Murmushi yasaki yashafa sumar kansa a lokacin daya rufe motarsa Yafuto, wayarsa ta dauki qara,yana dubawa yaga abokin aikinsa ne, Kuma abokinsa, suna mutunci sosai dashi, ya karanci halaiyar Captain Aryan hakan yasa suke mutunci sosai, yana dauka Bayan sun gaisa abokin nasa yace"Captain nayi shiru nazuba ma ido naga har yanzu bakada niyyar kawo mana Amarya mugaisa, to yanzu madam dina tamin magana da kanta,tace akawo mata qawarta su gaisa kada suhadu awani wajan Kuma ayi abun kunya"
Captain Aryan dayake cikin walwala yace"karka Captain Habib tunda gobe babu aiki insha Allah zamuzo"
Cikin farinciki Captain Habib yace"amma da munji dadi sosai,Allah yakaimu goben, zan fadawa Madam"
Batareda yace komai ba yakashe wayar.
Yana shiga falon yaga bata nan, da alama tana dakinta, Kai tsaye dakin nata yanufa adede lokacin tagama maida kayan da sister Saudat takawo mata ta adanasu,tana gwada kiran wayar qawarta Jidda,Sai gashi yashigo, tana ganinsa kiss din dazu yafado mata arai, cikin sauri ta sunkuyar da kanta qasa tace"sannu da zuwa"
Kallonta yayi batareda ya amsa ba yabata ledar hannunsa, cikin ladabi ta amsa sannan tace"nagode"
Kallonta yayi yanaso su kasance tare amma yarasa yanda zaiyi yafada mata hakan, kuma shiba ma'abocin surutu bane bare yajata da zance,haka dan dolensa ya haqura,harzai fice saiya sake dawowa yace"kishirya gobe zamuje unguwa"
Batare data Kalli qwayar idonsa ba tace"to Allah yakaimu"
Idonsa ya lumshe sannan ya futo daga dakin badan ransa yaso ba.
Yana fita daga dakin tasaki ihun murna tafada kan gadonta,dama tagaji da wannan zaman,cikin murna tasake sakkowa tabude ledar daya kawo mata,kayan gyaran gashi ne masu tsada,mamaki ya kamata,wai meyake damun Yaya Captain ne?
Murmushi tasaki sannan tasake duba kayan tanata jujjuyasu, sannan ta dauke ta ajiyesu a'inda ya dace.
harta kwanta ta tuna da maganar sister Saudat datace karta sake kwanciya ita kadai,tasaki ajiyar zuciya ta Kalli kayan jikinta,idan taje yace me yakawo ta, me zata cemasa?
girgiza kanta tayi,tawuce inda ta 6oye tsimin ta da Mamy tabawa Yaya Captain yakawo mata, tadaga gorar gaba daya ta shanye shi tas π
Sannan takoma gadonta ta kwanta.
Kasancewar yawon takeso hakan yasa sassafe tatashi tagyara gidan kamar kullum sannan tashiga kitchen tafara kokarin hada musu breakfast,potatoes crush take hadawa,tana soya naman dazata hada aciki yashigo kitchen din,dagashi sai gajeren wando da singlet,itama rigar baccin tace ajikinta bata cireba,doguwar rigace har qasa, saide Kuma jikin rigar yanada santsi sosai, ko Yaya ta motsa Sai jikinta ya nuna,tanajin shigowar sa tajuya ta kalleshi, cikin sauri ta janye idonta tace"ina kwana"
Kallonta yayi yadage girarsa daya batare daya amsa ba,yatsaya daga bakin qofar kitchen din yanajin wani irin farinciki yana lullu6eshi,amma fuskarsa bata nuna hakan ba, tana nan adaure kamar kullum,cikin sigar rada kamar bayaso wani yaji abinda yakeson fada yace"bani ruwa"
Cikin sauri tasaki spoon din hannunta tabude fridge din zata dauko masa ruwan, mamaki ya kamashi, saurin metake haka kamar Wanda zatayi laifi idan taqara seconds bata bashi ruwan ba?
Meyasa har yanzu takasa sakewa dashi ne?
Yaya zaiyi da'ita?
bai gama tunanin ba tanufoshi da sauri zata bashi ruwan garin sauri tatake gaban doguwar rigar ta tatafi luuu zata fadi,ko qafarsa bai motsa daga inda yake ba cikin sauri yasaka hannunsa yataro ta, madedetan na shanunta dabata saka musu bra ba suka sauka cikin tafin hannun Captain(ππ»ββοΈ)
yanda yayi niyar riqe jikinta dakyau dan karta fadi, haka yakaiwa nashanunta wani irin ruqo.
Lokaci daya numfashin Mawahib yake neman tsayawa cak, tazaro idonta waje.(π³)
Captain Aryan kuwa laushin nashanunta da santsin rigar jikinta yasa yaji ilahirin jikinsa ya kar6i wani irin kyakykywan saqo Wanda yasa ya lumshe idonsa nan take, Kuma yakasa sakin abinda ya riqe din(π)
zuciyarsa ce take zigashi akan ko sau dayane ya matsa ko kadan ne yaji abinda akeji, saide kafin yagama yanke shawara Mawahib data ji shiru yaqi sakinta, cikin sauri tafara qoqarin raba jikinta da hannunsa,cikin sauri shima yasake ta,yakai dubansa ga gorar ruwan data fadi,anan idonsa ya sauka akan gaban gajeren wandonsa yaga halin dayake ciki, cikin sauri yajuya yafice daga kitchen din batare dayasha ruwan ba,yana zuwa dakin sa yazube kan gado yayi kwanciyar rub da ciki ko hakan zai rissinar da halin dayake ciki,yajima ahaka, sannan yatashi ya shige toilet din dakin.
Mawahib kuwa aikin take amma gaba daya jikinta karkarwa yake,ta Kalli rigar jikinta tanajin kamar ta yageta ta zubar saboda taqaici,da tasaka yar qarama daduk haka bata faru ba,takai hannunta tashafa breast dinta guda daya Wanda Captain yariqe,tunda take babu Wanda yata6a kuskuren Kai hannunsa wannan wajan,amma yau a Karon banza Yaya Captain ya kama matashi,wani irin taqaici da haushin kanta ya kamata,haka tayi abincin a gurguje ko yayi dadi ko Kar yayi haka de tagama tareda tea, takai musu dining sannan ta wuce dakinta domin watsa ruwa.
Bayan tayi wanka ta shirya cikin leshi mai launin purple dinkin riga da zani,tazauna ta tsara kwalliya sosai tayi kyau, tunda tazo gidan bata ta6a zama tayiwa kanta zanen kwalliya sosai kamar yau ba,ta kalli dan qaramin agogon hannunta irinna mata taga qarfe goma shadaya da kwata,da niyya taqi sauka qasa da wuri saboda batasan ganin Yaya Captain,ta lura yanacin galaba akanta sosai akan abubuwa dayawa,yaganta tsirara haihuwar Mamy,yanzu kuma abun yawuce gani da ido yakoma ta6awa, to tun kafin abun nasa yakoma matsawa gara tafara ja baya dashi,saida takai shadaya da rabi sannan tafuto hannunta riqeda mayafinta dakuma jaka da wayarta,a hankali take sakkowa daga stairs din kamar batasan taka qasa,a lokacin yana zaune yana cin abincin data hada musu,tun tana sakkowa yazuba mata ido yana qarewa shigar jikinta kallo,meyasa kowacce shiga take mata kyau ne?
waye yakoya mata gayu haka?
Wata zuciyar tace dashi Anty Mamy, kwalliyar idonta ya kalla cikin ransa yace"Beauty"
Zama tayi a kujera tana duba agogon hannunta,kallonta yayi yace"zonan"
Kasa kallon idonsa tayi,ahankali tatafi kanta aqasa taqaraso wajansa ta tsaya tana murza hannunta,kallon hannun nata yayi Wanda yaji baqin lalle, yaso ya maze saide Kuma bazai Iya hana zuciyarsa abinda takeson ta6awa ba,dan haka yakai hannunsa kan nata hannun ya janyo ta dab dashi sannan yace"zauna Kici abinci"
Saitaji wani iri banbarakwai,tayaya zai sata cin abinci agabansa bayan kowa abincinsa yake ci?
bata gama tunanin ba yaja mata kujera fuskarsa a tsare yace"seat..."
Babu musu ta zauna,yana ganin zamanta yatashi da kansa yazuba mata komai sannan yatura gabanta,yazuba mata ido yana kallonta.
Jikin Mawahib yayi sanyi tarasa gane meza tayi?
Tunda take dashi basu ta6a Zaman cin abinci tare ba,asalima tun agida ma basu saba hakan ba,dago idonta tayi ta kalleshi,Yajuya manyan idonsa yayi mata nuni da abincin,babu yanda ta Iya tasa fork tafara cin potatoes crush din,tanaci ahankali kamar bataso tana juya dan qaramin bakinta,amma koda wasa taqi kallonsa,wayarsa yake dannawa yana turawa Captain Habib saqon cewa gasunan zuwa,zuciyarsa tana azalzalarsa akan yaci gaba da kallonta, saide bayason yawan takura mata da kallon,ya lura har yanzu akwai sauran rashin sakewa a tsakanin su,wanda dole shine zai yi maganin wannan matsalar da kansa.