Showing 42001 words to 45000 words out of 110331 words

Chapter 15 - MAWAHIB COMPLT HAUSA NOVEL

13 Sep 2024

19698

tunawa da surar jikinta, harya samu nasara cikin sauri ya shirya cikin qananun kaya riga da wando yayi mutuqar kyau kamar ba gobe.

Wanka yayi da turare sannan Yafuto yana bulbula qamshi zuwa falo, adede lokacin tagama shirya komai na abincin zata koma sama tayi wanka,Koda wasa qin kallonta yayi saboda yana tsoro kar yaje gaban ogansa kuma asamu matsala(πŸ™ˆ)
yagama lura yau tashin hankali takeji shiyasa taqi saka hijabi, shikuma bai shiryawa wannan tashin hankalin ba,yana zaman zamansa nema take qarfi da yaji tasa azo ana abun kunya atsakani,shikuma bayason raini,kokadan hakan bazata ta6a faruwa ba.

ganin zai fice daga falon kamar yana sauri hakan yasa ta kalleshi tace"ga abinci"

Batareda ya kalleta ba fuska a daure yace"no,Ina sauri"

dan qaramin bakinta taturo gaba,Kenan duk wahalar da tayi tatashi a banza,ita kanta Batasan ya akai ba,kamar an qwato maganar daga bakinta saiji tayi tace"bakaci komai bafa.... "

Cak yaja yatsaya yaji yakasa fita,kuma yakasa dawowa.

Tunani yafara tunda yaga ta dage yau, gara yasamu ladanta yaci ko kadanne,may be jiya saboda yanajin yunwa ne shiyasa yaji abincin yayi dadi, juyowa yayi zaije yaci abincin, mamaki ya kama Mawahib, Anya Yaya Captain dinne kuwa? itace zata masa magana Kuma yadawo yayi abinda tace? ganin da gaske abincin zaije yaci,yasa tayi sauri tahaye sama.

Zama yayi a dining din yabude abincin yana gani,bawani abincin kirki tayi ba, daga ita Sai shi kawai tadafa musu Iya cikin mutum biyu.

qamshin da yaji ne yasa yayi Addu'ah Allah yasa yanda yake qamshi Shima girkin yayi dadi duk dade bawani ci zaiyi sosai ba kawai de danya samu ladan tane,abincin yafara ci tundaga spoon din farko yafara jinjina kansa alamun komai yaji.
yaci rabi yana tunanin rufewa saiyaga gara yadan qara kadan de,yasake qarawa ya cinye,dayaga sauran wanda ya rage din bashida yawa kawai saiya cinye (πŸ™†πŸ»β€β™€οΈπŸ™Š)

Saida yagama cinye abincin sannan yatuna babu saura fa gaba daya ya cinye abincin, yazuba wa Empty plate's din gabansa ido yana kallo,da alama de yarinyar nan itace tasamu ladansa,idan tazo taganshi da wanne ido zai kalleta?(πŸ€”)

Cikin sauri yatashi yafice daga falon.

Tana hawa sama taga wayarta tana haske alamun anyi mata missed call,tana dubawa taga Mamy ce,tayi mamakin kiran,saboda tasan cewa da weekend Mamy tana dadewa bata tashi daga bacci ba,kiranta tayi,bayan sun gaisa tace"Mamy Ina kitchen lokacin dakika Kira,sai yanzu Naga kiranki"

Mamaki ya kama Mamy, yau yaushe tana waya da Mawahib amma babu kuka babu alamun damuwa?
Hamdala tayi cikin ranta,tasan cewa addu'ar datake ce Allah ya amsa mata, ajiyar zuciya tasaki tace"kuna lafiya ko?"

Tace"lafiya kalau,jiya Abba yazo shida abokinsa da yamma,sai dare suka tafi"

sarai tasan Ma'aruf take nufi,amma saita nuna mata bata saniba tace"waye Abba?"

Jikin Mawahib yayi sanyi,tace"Abbana,har kudi ma yabani amma nabawa Yaya Captain"

Cikin gwasalewa tace"ashe Abban kine"

Mawahib tayi shiru cikin sanyin jiki batace komai ba, Mamy ma da taji tayi shiru saitabar maganar tace"babu matsala de kinayi masa girkin kina kuma gaidashi ko?"

Cikin sanyin jiki tace"inayi Mamy,yanzu ma nayi masa break fast"

Mamy tace"to yayi kyau,ki daina barin gidan da datti kullum kidinga gyarawa,sannan duk lokacin daya dawo daga wajan aiki kidinga kar6ar abun hannunsa,sannan basai Yanemi wani Abu ba kamar abinci ko ruwa,yana zuwa kidinga bashi dan abunsha mai sanyi"

Cikin sanyin jiki ta amsa mata, aranta tana tunanin menene ma Yaya Captain yake zuwa dashi dazata kar6a banda bindiga?
a fili tace"to Mamy insha Allah"

Mamy tace"shikkenan to sai anjima"

Cikin sauri Mawahib tace"yawwa Mamy wannan abun nawa yakusa qarewa ki qaromin wani,wannan abun da kika bawa Yaya Captain yakawo min, saura qiris yaqare"

Cikin sauri Mamy ta zaro idonta(😳)
Sannan tace"wai menene yakusa qarewa? gumbar daya kawo mikin ce harta qare?"

Dan qaramin bakinta taturo gaba cikin shagwa6a tace"jiya ma shina wuni inasha,naji da dadi ne,dan Allah ki qaromin wata"

Mamaki yakama Mamy,Anya Mawahib kanta daya kuwa?gumbar daya kamata ace ta dade tana amfani da'ita itace take fada mata jiya wuni tayi tanasha Kuma tawaye kalau da'ita bataji labarin tana asbiti ba?
to ai ko'ita kanta idan tasha yar kadan,tanaji ajikinta idan tashiga hannun Alhaji(πŸ™ˆπŸ™Š)

tanaso ta tambayeta datasha din lafiya kalau suka waye itada Captain din kokuma yakira mata likita ne tazo gida ta dubata?
amma Kuma tarasa ta yanda zata mata tambayar kasancewar ta mahaifiya a wajanta.

Cikin shan ciki tace"to za'a kawo miki wata robar, nan gaba saina dinga aiko miki babbar roba,amma de bakyajin tsoron kwana ke kadai ko?"

Cikin sauri Mawahib dabata gane kan tambayar ba tace"tsoron me Mamy?,Ina gama abinda nake zanyi wankana inyi shirin bacci in kulle dakina intayin bacci na"(πŸ€¦πŸ»β€β™€οΈ)

Mamy tayi murmushi,ganin cikin ruwan sanyi taji abinda takeson sani, tace"toki gaida Captain din,sai anjima"

Tana ajiye wayar tafara tunani,wanne irin zama yarannan suke yine?suna zaune gida daya Kuma su biyu amma ace har yanzu shiru? tasan Captain yanada matsalar haihuwa har sai yasha magani to amma ai ba'a ce yanada matsalar jin sha'awa ba,meyasa bazai nemi matarsa ba? dalilin bazai wuce ace saboda baya son yarinyar bane,ajiyar zuciya tasaki, batada ikon dazata sa Captain yaso Mawahib, amma tanada damar dazata yi musu Addu'ah idan har zaman auren nasu akwai Alkhairi, to ubangiji ya sanya musu soyaiyar junansu acikin zukatansu.

Tana ajiye wayar tafasa shiga wankan,kamar yanda Mamy tayi mata magana akan gyaran gidan, duk da bashida datti saida tasake gyara shi, tasaka turaren wuta, tafesa abun qamshi,sannan ta kunna esi afalon,ta wuce dining zataci abinci saide tana zuwa data zauna zataci abinci saitaga wayam babu komai,mamaki ya kamata a fili tace"A a, Ina yakai abincin to?"

Wata zuciyar tace da'ita ya cinye mana(πŸ˜‚)

Qugunta ta riqe da hannu biyu a fili tace"toni meyake so inci? dama yanason abincin amma girman kai yahanashi ci?, idan nace ga abinci, saiyace no..."
tafadi 'no' din tana gwada yanda yake mata magana yana cika yana batsewa

ganin babu Captain babu dalilin sa awajan kawai ihu take bayan hari, hakan yasa takoma kitchen ta dauko biscuit sannan tazo tahada tea Mai kauri tasha dashi,tadebe kwanukan wajan takai kitchen ta wankesu ta adana sannan ta koma dakinta tashiga wanka, a lokacin Kuma qarfe goma shadaya na safe.

ta dade tana wanka,sannan ta wanke kanta wanda rabon dataje wajan wankin kai tun kafin tazo Abuja,tafuto sanyeda farar rigar wanka mai jikin towel,tadaura dan qaramin towel din akanta,Kai tsaye tafuto falonsu na sama tabude d'ayar qofar falon tafuto tafuto balcony,taduba bakin get taga David baya nan da alama yana cikin dakinsa, tayi maza ta warware towel din dake kanta, sannan ta baje dogon gashinta tana sake warware shi dan tasha is'ka

Karkatar da kanta tayi zuwa gefen hannun hagu,gashinta yadawo gefen hagun gaba daya,tasaka towel din tana goge gashin nata,adede lokacin Captain ya danno hancin motarsa cikin gidan,kokadan bataji qara ko alamun shigowar saba,tunda yashigo ya hangota daga inda take,parking ya gyara yafuto daga cikin motar,har zuwa lokacin tana tsaye tana goge gashinta,wayace akare a kunnansa saide bakajin abinda yake fada, yatsaya daga inda yake wayar yana qarewa dogon gashin ta kallo, kamar wasa taji magana qasa qasa, tana dagowa sukai ido biyu dashi, cikin sauri ta janye idonta, ta6ata fuskarta kamar de shi, sannan ta maze taci gaba da abinda take, sannan tajuya tabar wajan.

Magana yake awaya amma tunani yake cikin ransa, meyasa take sauyawa ne?
gashinta yanada tsawo sosai kamar na Anty Ma-my but meyasa bai ta6a lura da hakan ba saiyau?
Ya lura tanada miskilanci sosai,kuma dole zai gyara mata zama bazai lamunci wannan ba.

harya shigo falo wayar tana kunnansa yanayi,adede lokacin itama tafuto daga falon sama,ganin yashigo falon yasa tasake gyara towel din kanta,tadaure shi akanta, sannan tasakko zuwa falon, Shima adede lokacin yazauna afalon cikin daya daga cikin qayatattun kujerun falon, fuskarsa tana nan kamar ko yaushe adaure,bata tsaya yimasa magana ba ta wuce kitchen hankalinta kwance,Captain dayake zaune yana waya yana waya yabita da kallo qasa-qasa, rigar wankan tayi mata kyau,manyan hips dinta ya baje sosai acikin rigar, duka tsawon rigar Iya karta gwiwar ta,saida tashige kitchen din gaba daya sannan ya janye idonsa daga kallonta.

Fridge ta bude ta dauko masa ruwa Mai sanyi kamar yanda Mamy tasata,sannan ta dauko glass cup ta taho wajansa kanta tsaye.

Tana zuwa ta ajiye ruwan agabansa, sannan ta sunkuya ta tabude ruwan tafara zuba masa a cup,sunkuyawar datayi tana zuba masa ruwan hakanne yasa idon Captain yasauka akan madedetan nashanunta,cikin sauri ya runtse idonsa,gabansa yana faduwa,saide daya runtse idon ma wani 6angare na zuciyarsa fizgarsa yafara yi akan yabude idon, ahankali yasake bude idonsa, har lokacin tana sunkuye yasake dora idonsa akansu ko kyafta ido ba yayi,baisaba ganin wannan abu a zahiri haka ba, qare musu kallo yake tsaf, yana tunani aransa dama haka suke,?(πŸ€”)

Kwata-kwata ya manta waya yake(πŸ™†πŸ»β€β™€οΈ)

Ruwan taturo gabansa, sannan ta miqe zata bar wajan, adede lokacin mutumin dayake magana awaya Yace"Captain ina magana kayi shiru kana Jina kuwa?"

Cikin sauri yayi firgigit yadawo hayyacinsa a lokacin Mawahib harta bar wajan, batayi masa sannu da zuwa ba saboda taga yana waya.

Gyaran murya yayi sannan yadauki ruwan cup din ya shanyeshi tas, cikin sarqewar murya yace"Inajin ka, sorry,nasha ruwa ne"

Daga dayan 6angaren mutumin yayi murmushi,tunda yasamu labari Captain Aryan yayi aure tundaga lokacin yayi masa uzuri zuwa nanda wasu watanni(πŸ™ˆ)

Haly JASHERU venture's,munada kayayyaki masu kyau da inganchi ba algus da ha'inci, kayanmu daga Ethiopian ne, prdct dinmu muna Ethiopian magic hair oil, anti dandruff shampoo serum, bdy cream, hand cream, magungunan chuttuka da na mata masu inganchi da qara lfy ajikin dan
adam ga number kmr hk 07046665338 ko 07061664264 munada distributor ako Ina afadin kasarnan da ketare muna koya harkokin kasuwnchinmu ga masu bukata akan 5000 kacal

sannan munada tsuntsaye na kasashen waje tattabaru game bukata ko koya akwai riba kwarai aharkar mebuqata yasiya koya koya seyanemeni a number na kamar haka 07046665338 ko 07061664264, ku antayo ayi tafiyar daku,yar'uwa kikoyi sana'ah akan wannan farashi me sauqi kema ki kafa kankiπŸ’ƒπŸΌ


******


Har qarfe shadaya nadare yana zaune yana aiki a computer, yaso ace yagama aikin tun kafin weekend yawuce,to amma bai zauna ba, shiyasa ya takura kansa yanason yau komin dare ace yagama aikin.

Nabiha tana dakinta,tagama waya da mamanta kenan bayan tagama bata shawarwari akan yanayin zaman nasu, tashi tayi tashiga wanka ta shirya cikin wata yar qaramar rigar bacci doguwa,rigar tayi shara-shara dayawa kana Iya hango komai,Kai tsaye falon tafuto anan taganshi inda ta barshi tun dazu, kitchen ta wuce tahado masa coffee, sannan tazo ta zauna agefensa ta ajiye masa coffee din tace"yaya Ashraf ga coffee"

Cikin sauri yadago kansa ya Kalli coffee din sannan ya kalleta,yana ganin yanayin datake ciki cikin sauri yadauke kansa yamaida kan computer yana cigaba da aikin da dayake.

Bata damu da rashin maganar saba ta zauna dab dashi tana kallon yanda yake danna computer cikin salon qwarewa, har shabiyun dare suna zaune afalon, shi yana aiki ita kuwa harta fara gyangyadi, ta juya ta kalleshi da idanunta mecike dajin bacci, tana lumshe idonta cikin wani irin salo tace"yaya Ashraf bacci....,please muje muyi bacci"

Ashraf ya juya ya kalleta,tasake lumshe idonta cikin jin bacci tace"muje kajiiii"

tafadi maganar tajan Kalmar qarshe,zuba mata ido yayi yana kallonta,kayan dake jikinta Wanda dashi da tsirara duk daya,shine yafara fizgarsa,yaji bazai Iya yimata musu ba,ahankali yadaga mata Kai sannan ya rufe computer yatashi tsaye,itama tashi tayi tareda yin wata irin miqa wadda tasa jikin Ashraf yafara rawa,kallon qirjinta yake yanda taturo su gabansa yaji kamar yadora hannunsa akansu, to amma daya tuna yarjejeniyar su da'ita dakuma message din daya turawa mama Sadiya sai yayi sauri yawuce dakinsa.

Kai tsaye itama tabishi cikin dakinsa,yana shiga yacire rigar jikinsa, yajuya zai ajiye rigar saiya ganta abayansa, mamaki ya kamashi, kanta daya kuwa? meyake damunta yau?.

Ganin yana kallonta fuskarsa adaure nan tagane korarta zaiyi, nan take tafara kukan qarya da kissa,cikin 6acin rai Ashraf ya rufe kunnansa sannan yabude yace"kin dameni,fita"

Ya qarasa maganar yana nuna mata qofa,cikin shagwa6a tamatso dab dashi tace"yaya Ashraf ni wallahi tsoro nakeji,ni anan zanyi bacci na"

Taqare maganar tana hada jikinsa da nata, saiga Ashraf yayi shiru, Yakasa yimata musu,ganin yayi shiru yasa tadora manyan boobs dinta abayansa, ta zagayo da hannayenta tariqe cikinsa sannan tadora kanta abayansa, cikin muryar kissa tace"ni bacci nakeji"

Ashraf yayi shiru yanajin yanda tudun breast dinta yake mintsininsa,nan take yanayinsa yasauya, amma ya gagara yimata komai,numfashinsa yafara fita da sauri da sauri,sai hada gumi yake.

Daqyar ya'iya fuzgo magana daga bakinsa cikin yanayin sha'awa yace"wai lafiya?"

sake rungume shi tayi, tahade jikinsu tayi shiru alamun bacci take,cikin sauri ya fusgota tadawo gabansa,Nabiha tabude idonta dasauri Jin yanda ya fuzgotan kamar ba fusgowar me hankali ba,kafin tayi yunqurin yin wani abu, yadora bakinsa a wuyanta yafara sakar mata wata irin kyakykywar sumbata,hannunsa yakai kan yar qaramar rigar jikinta yayi kasa da'ita, cak ya dauketa yajefata kan gadon sa,sannan yabi ta yafara kissing din ko'ina najikinta,ganin yanda yake abu da qarfi kamar za'a qwaceta yasa hankalinta yatashi, tafara yunqurin tashi, tayi masa hakan ne danta ja hankalinsa yasaki jiki da'ita harsu fara bacci tare, bawai takawo masa kanta yayi wani abu bane, Ashraf kuwa ganin zata tashi yasa yasake riqeta sosai a jikinsa, hannunsa yana yawo a ko'ina najikinta,cikin fargaba tace"yaya Ashraf yarjejeniyar mu,kayi haquri, niba haka nake nufi ba"

Kwata kwata baiji abinda take fadaba, cikin rashin fahimta yace"yarjejeniya,tame?"

hannunta yake qoqarin ja yanason dora mata shi aqasan mararsa,cikin sauri ta fizge hannunta,baidamu da hakan ba yadora bakinsa cikin nata,yayinda hannunsa yake kan manyan nashanunta,babu 6ata lokaci yanemi hanya yashigeta cikin fitar hayyaci,Nabiha tasaki wani irin kuka tafara dukansa abayansa amma Yaya Ashraf idonsa yana lumshe yana zubarda hawayen dadi, kokadan Yakasa magana kawai nishi yake kamar Wanda akayiwa dukan tsiya, bata zaci abun zaizo ahaka ba,cikin aza6a take Kiran sunan sa, amma Ashraf kawai abun gabansa yake,tun tana Kiransa cikin muryar ta datake fita, har muryar ta ta dashe kamar me mura saboda kuka,kukan zuci kawai take tana hawaye, tana tunanin itada sake zuwa dakinsa har abada(πŸ™†πŸ»β€β™€οΈ)

kusan awarsa daya dawani abu,sannan ya qanqameta yana sakin wani irin numfashi,rungume ta yasake yi a jikinsa sosai idonsa a lumshe yana jin kamar yasake maimaitawa (πŸ™†πŸ»β€β™€οΈ)

Cikin muryarta dabata fita tace"Mama nashiga uku na, Yaya Ashraf yakashe ni"

Sunan MAMA dayaji ta ambata shine yadawo dashi cikin hayyacinsa, cikin sauri yasaketa yatashi zaune tareda dafe kansa da hannu bibbiyu,salati yafara maimaitawa aransa yana tambayar kansa meya aikata haka?
Nabiha cefa wadda sukai yarjejeniya a tsakanin su, wadda yayiwa mahaifiyar ta alqawari babu abinda zai faru.


Cikin kuka tace"kamaidani gida,mutuwa zanyi wallahi, kakaini wajan mama,ni kayi haquri zanbar ma gidanka tunda dama baka sona"

Cikin sauri Ashraf ya kalleta yace"to meyasa kikazo dakina bayan kinsan ga yarjejeniyar damukai daku?"(πŸ˜‚)

Nabiha tayi shiru tana goge jajayen idonta da tasha kuka.
Ashraf yasake dafe kansa cikin damuwa,sannan yasake kallonta yace"yanzu dakikazo mukai wannan abun mekikeso na fadawa mahaifiyar ki?"(πŸ˜‚πŸ™Š)


Nabiha tayi shiru takasa magana, domin kuwa radadin datakeji a qasanta ma kadai ya isheta,batasan meyafaru tsakaninsa da maman taba, kuma batada qwarin dazata tambayeshi.

Tashi yayi yadafa ta cikin tausayawa yace"taso muje kiyi wanka"

Cikin kuka tace"ni bazan Iya tashi ba, kawai ka maidani wajan mamanah"

ganin acikin duhu suke, hakan yasa bai damu dasaka komai a jikinsa ba ya dauketa cak, suka shige toilet


******
Haly JASHERU venture's,munada kayayyaki masu kyau da inganchi ba algus da ha'inci, kayanmu daga Ethiopian ne, prdct dinmu muna Ethiopian magic hair oil, anti dandruff shampoo serum, bdy cream, hand cream, magungunan chuttuka da na mata masu inganchi da qara lfy ajikin dan
adam ga number kmr hk 07046665338 ko 07061664264 munada distributor ako Ina afadin kasarnan da ketare muna koya harkokin kasuwnchinmu ga masu bukata akan 5000 kacal

sannan munada tsuntsaye na kasashen waje tattabaru game bukata ko koya akwai riba kwarai aharkar mebuqata yasiya koya koya seyanemeni a number na kamar haka 07046665338 ko 07061664264, ku antayo ayi tafiyar daku,yar'uwa kikoyi sana'ah akan wannan farashi me sauqi kema ki kafa kankiπŸ’ƒπŸΌ

******

Dasafe tagama aikin komai kamar yanda tasaba,tayi masa breakfast tashirya komai yanda yadace, ta wuce sama tayi wanka tashirya cikin gajerar riga,hannun bakin less ne da rigar,daga wuyanta zuwa qasan qirjinta duka da milk din less a kayiwa rigar ado,daga qasan qirjinta Kuma rigar ta bude har zuwa qwiwarta,ganin Yaya Captain ba harkarta yake shigaba, ba kallonta yake ba,kuma bahanata shigar datake so yakeyi ba,datasa hijab datasa qananun kaya duk dayane awajansa, hakan yasa tagyara kanta, ta shafa masa mayuka gashinta yadauki sheqi yana walwali,ta fesa turare tafuto falon ko hula bata saka ba bare mayafi, saitayi kyau kamar kasaceta ka gudu.

Falon tafuto ta zauna akan kujera tayi tagumi hannu bibbiyu,tunda tafara sakkowa daga sama Captain dayake Sanye cikin uniform dinsu yanayin breakfast cikin jin dadi yazuba mata ita yana kallonta,gaba daya saitayi masa kama da yar larabawa,dogon gashinta ya dauki hankalin sa sosai,har tazo ta zauna afalon idonsa yana kanta, cikin sauri yadauke kansa yaci gaba dacin abincin sa.

Tana zama a kujera tayi tagumi hannu bibbiyu,dama haka auren yake? yanzu ita kenan batada aiki sai gyaran gida dayin girki aikin kenan? Idan a gidane Mamy ce zatayi komai saide tataya ta dawani aikin, yanzu kuwa komai itace zatayi babu me taimaka mata da komai,lokaci daya kewar mahaifiyar ta ya kamata,tayi nisa cikin tunani a hankali taji hawaye ya silalo daga idanunta zuwa fuskar ta.

Cikin kwanciyar hankali yagama yin breakfast dinsa,shida kansa yaga abincin yaje yazauna yaci, yau ko tayi batayi masa ba, yazo wucewa yaganta tana hawaye, yanason yaji menene damuwarta amma yarasa tayaya zai fara?
kokadan bayason ganinta da wannan qananun kayan datake sakawa, takura masa suke,sannan bazai Iya hana ta sakawa ba saboda kartaga kamar tana daukan hankalinsa, wucewa yayi ta gabanta yad'auke kansa,bazai yi kuskuran kallonta daga qarshe kallon yazo ya dagula masa lissafi ba,cikin sauri yanufi qofa zai fice, saikuma yaja ya tsaya awajan cak, tunani yafara aransa, yarinyar nanfa amana ce awajansa,duk da cewa ba lalle ne zaman nasu yadore ba,bai kamata ace yaganta tana kuka,Kuma yawuce yabarta ba,itama wani lokacin tana kyautata masa tunda gashi yanzu ma tabashi kulawa ta hanyar yimasa girki,ajiyar zuciya Yasaki, fuskarsa kamar kullum babu fara'ah yajuyo yadawo falon yazo kanta ya tsaya baice da'ita komai ba,Mawahib tadaga kai ta kalleshi, cikin sauri ta goge hawayen idonta,ta6ata ranta itama,kallonta yayi da fuskar nan tasa ta sojoji yace"lafiya?"

Cikin sauri ta girgiza masa kanta, sannan tace"bakomai"

Shiru yayi yazuba hannunsa cikin aljihun wandonsa,sannan yazuba mata manyan idonsa yana kallonta,yafara tunani,bayason damuwa kwata kwata,tazauna tana kuka,ya tambayeta lafiya tace babu komai metakeso yamata? shibe saba lallashi ba, be'iyaba.

kallon qwayar idonta yayi wanda wani sabon hawayen

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login