Showing 18001 words to 21000 words out of 110331 words
a zaune.
Saida gari yawaye sannan likita yazo inda suke,hannunsa daukeda file,ganin Alhaji Ma'aruf yana kuka tunda sukazo,kuma yahana kansa sukuni,sannan gashi fari tas kamar yanda Captain Aryan yake,shiyasa yayi tunanin ko shine mahaifinsa, kai tsaye yace "Alhaji kaine mahaifin marar lafiyar?"
Cikin sauri Alhaji Ma'aruf yace"eh nine,likita babu matsala deko?bai mutu ba yana nan da ransa ko?"
Likitan yabude file din hannunsa ya kallesu gaba daya yace"menene sunan marar lafiyar?"
Daya daga cikin Sojojin nan take yace"Captain Aryan I. Alqali"
Likita yayi rubuce rubuce a file din sannan ya kalli Alhaji Ma'aruf yace"kazo ka sameni a office"
Cikin sauri yabi bayansa zuwa office din,suma sojojin suka doru abayansu,Likitan da baisan menene a tsakanin suba ya juyo ya kalli Sojojin yace"babu damuwa,zamuyi magana ne dashi kawai"
Jin hakan yasa suka dakata daga bakin qofar.
Suna zama a kujera likita ya kalli Alhaji Ma'aruf yace"Alhaji yaronka yasamu harbi a haqarqarinsa,ma'ana qasan qirjinsa daga gefe, amma bullet din bai shiga canciki sosai ba, Alhamdulillah yanzu ma zamu Iya sallamar sa idan ya farfado daga dogon suman dayake, saide akwai matsala guda daya,Alhaji kayi haquri yaronka yasamu matsala bazai Iya haihuwa ba,saboda bullet din baishiga cikin qashin haqarqarin ba amma yagogi qashin wajan , shikuma wannan qashin da bullet din ya goga, maniyin namiji yana fara samuwa ne daga cikin jinin dayake yawo daga tsakanin qashin haqarqari zuwa qashin baya,zaiji sha'awa normal kamar yanda yasaba, but idan yayi aure yanzu, bazai samu maniyi mai lafiya kuma me kaurin dazai bawa matarsa ciki ba,saboda bullet din yariga ya gogi qashin wajan, amma zamu dorashi akan magani,sannan kuma ya kiyaye cin abinci barkatai,saide megina jiki,yakiyaye cin maiqo,saboda cin abu mai maiqo zaisa yasake samun qarancin maniyin, (low sperm count),amma idan yafara shan maganin da zamu dorashi akai,lokaci zuwa lokaci yana gwada mu'amular aure da matarsa insha Allah sperm dinsa zai dawo Normal,harma yasamu ciki...."
Cikin sauri Alhaji Ma'aruf yafashe da kuka yace"likita karka qarasa, karka qarasa likita shikkenan nacuci yaron nan...."
haka yataso yafuto daga office din kamar mahaukaci kamar wanda baya hayyacinsa ya nufi kofa zai fice daga Asbitin,Alhaji bala yabi bayansa cikin sauri yana tambayar "Alhaji Ma'aruf Ina zakaje? Meyasamu yaron?"
Alhaji Ma'aruf bai kula shi ba saida yafuto harabar asbitin kuka yaci qarfinsa yazube a farfajiyar asbitin yana kuka,nan da nan mutane suka taru a kansa ana bashi haquri, dayawa daga cikin mutanan sunyi tunanin mutuwa aka masa,Alhaji bala dayayi tunanin Captain Aryan yarasu ya tsugunna yace"Haba Alhaji Ma'aruf shi mamaci ai addu'ah yake buqata,ba kuka zaka masaba, addu'ar mu yake buqata yanzu haka"(π³)
Alhaji Ma'aruf yace"kabarni inyi kuka Alhaji Bala,banta6a jin na tsani kaina nayi tir da halina ba tun bayan barin Maryam cikin rayuwa taba sai yau"
Alhaji bala ya runtse idonsa sannan yabude yadafa kafadar Alhaji Ma'aruf sannan yayi qasa da murya yace"akwai mutane anan,kayi haquri ka tashi dan Allah"
Alhaji Ma'aruf ganin mutane suna masa kallon wanda aka yiwa mutuwa hakan yasa cikin sauri yatashi tsaye kamar wanda aka tsikare shi yafice daga harabar asbitin yana doka sauri kamar wani mahaukaci,tuni yagama yanke hukunci acikin ransa.
shima Alhaji Bala cikin sauri yad'oru abayansa suka fice daga asbitin.
******
ahankali yafara bude idonsa harya gama budeshi gaba daya,yaqarewa dakin dayake kwance kallo,ya kalli kayan jikinsa,sai a lokacin yatuna da abunda yafaru,ahankali yasake lumshe idonsa sannan yabude,babu wani alamun Jin ciwo yatashi zaune kamar ba aiki ne a jikinsa ba,sojojin dasuke tsaye daga waje suna hangoshi ta glass din dakin cikin sauri daya daga cikinsu yakira likita, likitan yana zuwa tare suka shiga dashi,likita yana ganin Captain a zaune nan da nan da yashiga taitayinsa saboda yasan cewa asbitin nasu ya kar6i baqin fuska masu ban tsoro, ahankali yafara dudduba shi, sannan yahada allura yayi masa a hannunsa, ya kalleshi yace"yaya kakejin wajan ciwon?"
Cikin miskilanci yace" banajin komai doctor,zaka Iya sallama ta yanzu?"
Cikin sauri yace"za'a baku sallamar insha Allah,amma akwai magungunan da zakasha yanzu,tukunna"
Baice dashi komai ba sai d'aga kansa da yayi kawai alamun yaji.
Likitan yabawa daya daga cikin Sojojin kati sannan yace"muna buqatar wannan magungunan"
Daga nan yafuto daga dakin.
Captain Aryan ya dudduba gefensa baiga wayarsa ba yadago ya kalli sojojin dasuke tsaye yace"whare is my phone?"
Cikin sauri daya daga cikinsu yasara masa sannan yabashi wayar cikin ladabi yace"mun rufe wayar ne oga,saboda kada hankalin yangida yatashi"
Cikin 6acin rai yace"kamarya kada hankalinsu yatashi?,idan mutuwa nayi ma haka zaku kashe waya bazaku Kira gida kufada musu halinda nake ciki ba?"
Kasa bashi amsa sukai saboda babu girma yana fada suna fada, cikin sauri ya kunna wayarsa,yafara neman wayar Ashraf
******
Ashraf yana zaune cikin damuwa, Alqali ya kalleshi yace"Ina tunanin nima akwai abinda yake faruwa,tun jiya Ina kira gaba daya nakasa samunsa"
Alhaji khaleed yace"yaya Ina ganin fa gara ka barshi yaje wajan aikin nasu yagano koba lafiya ba"
Adede lokacin kiran wayar Captain yashigo cikin wayar Ashraf, cikin sauri Ashraf dayake zaune yatashi tsaye yana fadin"gashinan yana kira Daddy"
Yadauki wayar tareda sakata a amsa kuwwa,cikin muryar sa maicikeda aji murya can qasa yace"Ash..."
Cikin sauri Ashraf yace"Aryan Ina kakai wayarka tun jiya da yamma Ina neman ka?"
Lumshe idonsa yayi,a hankali yace"ka kwantar da hankalin ka,munsamu tsautsayi ne a hanya harma nasamu harbi...."
Alhaji khaleed da Alhaji Isah tareda Alqali sunajin haka suka saki wani irin Salati
Cikin sauri Ashraf yace"harbi? innalillahi garin Yaya? saida nacema karka tafi,yanzu kana Ina? Yaya Harbin naka da sauqi?"
Gaba daya ya rikice,kwata kwata baya cikin nutsuwarsa sai tambaya yake jerowa Aryan din
Captain Aryan yayi murmushin qarfin hali yace"Ash..."
Kafin yaci gaba da magana Alqali ya kar6i wayar yace"kuna wanne asbiti....?"
******
Alhaji Ma'aruf da abokinsa Alhaji Bala suka turo kofar dakin suka shigo gaba dayansu su biyun duk jikinsu yayi sanyi kalau, adede lokacin Captain Aryan yagama waya da yan gida ya ajiye wayar agefensa,Captain ya zuba musu ido yana kallon su musanman Alhaji Ma'aruf wanda har zuwa wannan lokacin rigar jikinsa tana nan da sauran jini ajikinta,sai yanzu Captain yaqare masa kallo yaganshi fari tas idan ba hausa yayi bama zaka dauka ba bahaushe bane,Alhaji Ma'aruf ya kalleshi, tun kallon farko daya masa yasan cewa wannan acikin sojojin ma akwai tsare gida, zama yayi agefen gadon yace"yajikin naka?"
Ataqaice yace"Alhamdulillah"
Daga nan sukai shiru gaba dayansu,Alhaji Ma'aruf yarasa ta'ina zai fara,gaba daya yaron yayi masa kwarjini, daqyar yasamu qwarin gwiwar kallon sojojin yace musu "Dan Allah kuyi haquri kud'an bamu waje inaso zanyi magana dashi"
Sunajin abinda Alhaji Ma'aruf yafada amma ko kadan basu motsa daga inda suke ba,saida Captain Aryan ya kallesu sannan suka fice daga dakin.
Alhaji Ma'aruf ya kalli abokinsa Alhaji Bala yace"Alhaji bala zauna mana"
Alhaji Bala dayake tsorace da ganin sojojin yaqaraso ya zauna akan kujerar dakin.
Alhaji Ma'aruf ya kalli Captain Aryan yace"Captain Aryan ko?"
Fuskar Captain Aryan babu wasa Ataqaice yace "yes"
Alhaji Ma'aruf yayi ajiyar zuciya yasake kallon Captain Aryan cikin tausayawa yace"Aryan kayi haquri nayi maka babban laifi,bansanka ba, kaima baka sanni ba, amma ka za6i ka sadaukar da rayuwarka saboda ni,da nasan cewa abinda zai faru dakai kenan bayan tare harbin nan dakayi,da wallahi gara ni in mutu, akan wanna masifar tasameka"
Captain Aryan yayi shiru yanajin Alhaji Ma'aruf yana masa bayani,yarasa menene dalilin yin wannan dogon bayanin,aikinsa shine ya kula da yan qasarsa,bai dauki wannan abun da yayi abakin komai ba.
Alhaji Ma'aruf ya goge zufar daya fara sannan yaci gaba da fadin"likita yace sakamakon wannan harbin daya sameka, ba lalle sperm dinka ya iya samarda haihuwa ba,amma zai doraka akan magani idan kafara shan maganin insha Allah watarana za'a dace"
Cikin sauri Captain Aryan ya Kalli Alhaji Ma'aruf,cikin ransa yafara furta Kalmar nan ta"innalillahi wa'inna ilaihirraji'un...."
Ya lumshe idonsa yaci gaba da maimaita kalmar acikin ransa,Alhaji Ma'aruf yasake kallonsa sannan yaci gaba da fadin"Ina roqon alfarmarka kadubi girman Allah da darajar sa, kayafemin,nasan cewa nine sanadi,ta dalilina hakan tafaru dakai,sakamakon hakane yasa yanzu-yanzu naje masallaci nida Aminina Alhaji Bala,NA 'DAURA MAKA AURE DA 'YATA RUQAYYA" (π³ππ»ββοΈππ±)
Captain Aryan da idonsa yake lumshe yana maimaita Kalmar innalillah aransa,cikin sauri yabude idonsa ya zabura daga inda yake zaune,gabansa banda dukan uku uku babu abunda yake,wacce irin masifa ce ta sameshi haka? daga taimako?
Alhaji Ma'aruf ya kalleshi,cikin sanyin jiki yaci gaba da fadin"nasan yanda kakeji aranka,kuma nasan nime laifi ne awajanka,nasan cewa duk matar daka aura taji labarin cewa ga lalurar data sameka,zaiyi wahala ta zauna dakai,idanma ta zauna dakai to watarana zata gorantama akan hakan
wannan dalilin ne yasa nabaka 'yata tacikina, nasan cewa 'yata bazata ta6a goran tamaba har abada,saboda nasan cewa mahaifiyar ta batayi mata irin wannan tarbiyar ba,idan babu damuwa inaso ka had'ani da iyayenka zanyi musu bayanin komai"
Captain Aryan ya runtse idonsa cikeda damuwa,sannan yabude su,idanun sunyi jajir,gabansa banda faduwa babu abinda yake,kansa ya dauki ciwo kamar zai rabe gida biyu, cikin tashin hankali ya kalli Alhaji Ma'aruf yace"please ko zaka bani space?"
Ganin yanda yake cikin damuwa komai zai Iya faruwa hakan yasa babu musu Alhaji Ma'aruf yatashi,yasaka hannu cikin aljihunsa yad'auko wani d'an qaramin kati ya ajiye agefen Captain Aryan sannan yace"wannan shine katina,duk lokacin da hankalinka ya kwanta,kaji kana buqatar matarka,kakirani,zankawo ma matarka..."
Masha Allah...Mawahib de Allah yayi ta Auri miji nagari π
Yaya batun saka ranar Ashraf da Mawahib? π€
Shin Nabil zai haqura? π€
menene zai faru idan Captain Aryan yasan cewa wannan qwailar itace matarsa?π€
Mamy tace kobayan ranta bazata bari Mawahib ta auri 'ya'yan Hajiya kilishi ba,mezai faru idan labari yazo wajanta? π€
Alqali yace inde yana raye Ashraf saiya auri Mawahib,shin kuna ganin Captain Aryan zai saketa ne?π€
Da alama yanzu ne Hajiya kilishi zataga ikon Allah π
Alhaji Ma'aruf rashin sani yasa ya qulla qullalliya a gidan Alqali ππ
Yanzu labarin yafara,karki bari ayi bake ki, kibiya kudin ki, ki antayo paid group din Mawahib atafi dakeπππ
Alhamdulillah....anan nakawo qarshan free page's dina, duk meson cigaban littafin MAWAHIB, yabiya naira 500 kacalππ»
Yanzu kwamacalar tafara,akwai rikici agaba kala kala duk a gidan Alqali, koda kudinka saida rabonka ππΌππΌππΌππΌππΌππΌ
Insha Allah zaku dinga Samun posting biyu arana,wani lokacin kuma posting daya, kamar de yanda mukai daku a SHAHAAB, sai kunzo ππ»
Zaki turo 500 ta wannan account din ππ»
0164549488
Amina muhammad
GTbank
Kokuma katin MTN ta wannan number 08033300034
Tareda shedar biya ta wannan number 08033300034
Amnah El Yaqoubβπ»[7/9, 9:20 AM] AMINA KABIR CAPS: *Page 78*
Mawahib littafin kudi ne,duk me buqata naira 500 ne kacal ta wannan account din
0164549488
Amina muhammad
GTbank
Kokuma katin MTN ta wannan number 08033300034
idona nahana bacci nacinye lokaci na narubutashi,bazanja Allah ya'isa ba,amma muddin kika karanta baki biyani haqqina ba nabarki keda mahaliccinki faqadππ»
Bayan sunfuto daga dakin kai tsaye wajan payment sukaje Alhaji Ma'aruf yabiya kudin komai harda na magunguna ta hanyar atm dinsa, sannan suka futo daga asbitin,Alhaji Bala ya dubi abokinsa yace"Alhaji Ma'aruf kana ganin abinda ka zartar kuwa babu matsala? idan mahaifiyar yarinyar tayi mata aure fa? sannan idan yarinyar tana soyaiya dawani kuma kai karaba wannan soyaiyar ai kamar da cutarwa aciki"
Alhaji Ma'aruf yace"ni ina ganin wannan ba matsala bane,koda RUQAYYA tana soyayya dawani dole zatayi haquri tabarshi ta rungumi wannan sojan,saboda shi d'a na halak dole zaiso mutumin daya taimaki mahaifin sa,zan kira MARYAM Infada mata abinda na yanke"
Alhaji Bala yace"to shikkenan Alhaji Ma'aruf,Allah ya shige mana gaba"
******
Kasancewar jirgi suka biyo hakan yasa cikin sauri suka qaraso asbitin,gaba daya mazan gidan ne suka taho cikinsu harda Hajiya kilishi datake kuka wiwi,Mamy ce kawai bata taho ba itada Mama Sadiya,amma dukansu sun taho.
Suna shiga asbitin d'aid'aikun mutane suketa kallonsu,ganin yanda Hajiya kilishi take kuka har lokacin babu tantama zakayi tunanin mutuwa aka musu.
Sojojin dasuke tareda Captain suna ganin zuwansu Alqali suka musu iso zuwa dakin da Captain din yake, suna shiga Hajiya kilishi ta rungumesu shida Ashraf din gaba dayansu tana kuka, gaba daya saita bawa mazan gidan tausayi.
Alqali yayi gyaran murya yace"Kilishi kukan ya'isa haka,tunda yana raye to Alhamdulillah,Allah zakiyi wa godia"
Yajuya ya kalli Sojojin yace"muje wajan likitan"
Cikin sauri suka juya suka rakasu har office din likitan,da Alqali da Alhaji khaleed da Alhaji Isah,su ukun dukansu suka shiga office din likitan,Bayan sun gaisa Alqali ya kalleshi yace"likita,mune iyayen yaron nan da aka kawo muku wanda yasamu harbi"
Cikin girmamawa likita yace"Sojannan?"
Alhaji Isah yace" qwarai shi,ya ake ciki ne dangane da jinyar tasa? shikkenan babu damuwa zamu Iya tafiya dashi yanzu sai acigaba da kula dashi a asbitin mu nacan?,kokuma zamu sake barinsa ne yasake warwarewa?"
Cikin mamaki Likita yace"ikon Allah,wai dama wancen mutumin ba shine mahaifinsa ba?"
Alhaji khaleed yace"wanne mutumi?"
Mamaki cikeda fuskar likita yace"mutumin daya kawo shi,nayi tunanin shine mahaifinsa shiyasa ma nayi masa bayanin komai"
Alqali yace"kai likita,mune iyayen Captain Aryan,kayi mana bayanin meyake faruwa"
Likita yayi ajiyar zuciya yace"wato abunda yake faruwa shine....."
Nan take yasake yimusu bayani kamar yanda yayiwa Alhaji Ma'aruf.
Lokaci daya gumi ya rufe Alqali,Alhaji Isah mijin Mamy yacire hular kansa yafara firfita da'ita,Alhaji khaleed ne ya dinga maimaita salatin Annabi a fili, sannan yasamu qwarin gwiwar yiwa likitan magana yace"yanzu likita menene abunyi? zamu Iya fitar dashi qasar waje ne a nema masa lafiya kokuwa akwai wani abu wanda zaku iyayi basai anfitar dashi ba?"
Likita yace"Alhaji no need ace anfitar dashi wata qasa saboda duk maganin dazai buqata munada shi anan qasar,sannan zamu dorashi akan magani idan yafara shan maganin lokaci zuwa lokaci yana mu'amular aure da matarsa to zai gani idan Sperm dinsa yazama normal kamar yanda yake abaya,idan har yadawo normal to zai Iya samun ciki da matarsa,idan kuma yaga yanayin Sperm din bai sauya ba,to dole zaici gaba dashan maganin sa"
Alhaji khaleed yace"likita Captain Aryan bashida aure,tayaya zamu gane ya warke idan yafara shan maganin sa yanzu?"
kai tsaye likita yace"saikuyi masa auren,kuma Ina baku tabbacin inde yafara shan maganin akan qa'ida kamar yanda nafada muku,to insha Allah bazai dauki dogon lokaci ba zai warke"
Alhaji khaleed yasaka gefen babbar rigarsa ya goge gumin fuskarsa, sannan yace"mungode likita,yanzu zamu Iya tafiya dashi ne?"
Likita yace"Why not?"
Daga nan sukai masa godia suka futo daga cikin office din jikinsu a sanyaye.
Daga waje Sojojin suka tsaya,su Alqali suka qarasa cikin dakin, Captain Aryan yana ganin yanayin jikinsu yasan cewa sunji komai, Alqali yanemi waje ya zauna, Alhaji khaleed da Alhaji Isah suna tsaye,Hajiya kilishi data kama yaranta ta riqe duka su biyun kamar za'a qwace mata su, cikin sanyin jiki ta kalli Alqali tace"Alhaji.....yana ganku jiki a sanyaye? lafiya?"
Alqali yayi ajiyar zuciya yace"akwai matsala kilishi,yaron nan yasamu matsala......"
nan take yabata labarin komai kamar yanda likita yafada musu.
Tun kafin yagama yimata bayani take hawaye harya gama,amma bai fada mata yanda sukai da likitan akan shawarar daya basu ta batun auren Aryan dinba,ajiyar zuciya ta sauke sannan ta share hawayen idonta tace"hasbunallahu wani'imal wakeel,Ina ganin ikon Allah ni kilishi,wacce irin masifa ce wannan Alhaji?"
Alhaji Isah yasaki ajiyar zuciya yace"Yaya kilishi kiyi haquri,kowanne bawa baya Iya kaucewa qaddarar sa,Ina ganin kutashi muyi shirin tafiya kawai"
Adede lokacin shima doctor yashigo dakin, shida Ashraf sune suka fara qoqarin kamashi,cikin muryarsa kamar bayaso yace"zan'iya Doctor"
Dakansa yatashi kamar ba ciwo ne a jikinsa ba,suka futo yabawa Sojojin sa umarnin suwuce Abuja kawai,zai taho daga baya, cikin girmamawa suka sara masa, sannan suka wuce, sukuma gaba dayansu suka nufi Airport suka dauki hanyar dawowa gida
Tun kafin su koma gida labari ya Isa unguwar kowa yaji abinda yafaru,suna sauka kuwa sukaga mutane sun tattaru abakin get din gidan gaba dayansu ire-iren wanda yake yiwa Alkhairi ne idan yazo, sosai mutanan sukai musu jaje tareda addu'ar Allah yakiyaye gaba,sun dade a bakin get din, sannan suka samu nasarar shiga gida.
Agidan ma kai tsaye suka wuce part din Hajiya kilishi, Mama Sadiya da Mamy da Nabiha nan take sukaje sukai masa sannu,amma Mawahib bataje ba,suma su Mamyn dasukaje Hajiya kilishi ko d'ago ido batayi ba bare ta kalli inda Mamy take.
Tun safe dasuka zo Captain Aryan yayi shiru baya cewa um bare um um, saide in anyi masa Addu'ah Allah yakiyaye gaba yace Amin, daga haka babu qari, iyayen nasa sun lura yana cikin damuwa,sai suka dauki hakan amatsayin maganar rashin haihuwar sane take damunsa,abunda basu saniba shine maganar haihuwar kokad'an bata damunsa tunda ba cewa akai gaba daya har abada bazai sake haihuwa ba, yanasa ran shima zuwa gaba idan Allah ya qaddara zai iya haihuwa shima,maganar auren nan ce kawai take damunsa, yarasa wazai fad'awa yaji dad'i ko zai samu shawarar data dace.
tun saukar su Hajiya kilishi bata zauna ba,dakanta tadafa musu abinci shida Ashraf takuma hanasu fita ko nan da can,sai yamma Ashraf yaje dakinsu yayi wanka sannan yadawo falon wajan Aryan.
Ya zauna ya kalli Captain Aryan dayayi shiru kana ganinsa kasan yana cikin damuwa, yace"muje daki kayi wanka?"
Kafin yayi magana Hajiya kilishi tace"bari inhada masa ruwan wankan a toilet dina saiya shiga yayi"
tafadi hakan tana shigewa cikin dakinta,Ashraf yabi bayanta da kallo tareda murmushi yajuyo ya kalli Captain Aryan yace"d'an autan Momy"
Captain Aryan baice komai ba Sai idonsa daya lumshe kawai
Batafi minti biyar ba tadawo tace"Ashraf rakashi yayi wankan"
Sai a lokacin ya bude lumsassun idonsa yace"zan'iya Momy"
Daga nan yatashi ya shige dakin nata,yana shiga yawuce toilet yacire rigar jikinsa zai fara wankan.
Hajiya kilishi ta dubi Ashraf dake zaune agefenta tace"dauko masa kayansa Ashraf"
Kafin Ashraf yatashi sai qara suka jiyo daga toilet din Hajiya kilishi
Cikin sauri Hajiya kilishi ta nufi dakinta tana fadin"Aryan lafiya?meyasa meka?"
Yana daga cikin toilet d'in cikin shagwa6a yace" Momy zafi ruwan...."
Ashraf yasaki d'an qaramin tsaki yafice daga dakin,yayi tunanin ma faduwa yayi shiyasa yashigo d'akin aguje(π)
Hajiya kilishi ta dafe kanta da hannunta(π€¦π»ββοΈ)
tace"Aryan anya hardakai akai training din aikin nan naku kuwa?"
Yanajin abinda tace yayi shiru, badan yaso ba haka ya runtse idonsa yashiga ruwan,cikin ransa yana jinjina zafi irinna ruwan.
Da daddare suna d'akinsu shida Ashraf,Captain Aryan yana zaune akan gado dagashi sai gajeren wando,wandon yanada laushi sosai hakan yasa mutum zai Iya ganin shacin komai(π)
Baqin gashin dayake faffad'an qirjinsa ya kwanta luf asaman farar fatarsa,Ashraf kuwa yana sanye cikin kayan bacci wata doguwar riga mai kyau.
Yazo bakin gadon ya zauna kusada Captain Aryan sannan yace"wai damuwar ce har yanzu? banajin dad'in yanda kake yawan tunanin nan Aryan,idan de magana ce akan haihuwa bagani ba, sai indinga haifo mana yaran"
Captain Aryan yayi shiru yana tunani,kwata-kwata ba wannan ne damuwar saba, tunanin aurensa yake baisan yaya zai fadawa su Momy ba.
Ashraf yaga yayi magana amma kamar ma Captain Aryan din baya tareda shi,ahankali yasaki ajiyar zuciya sannan yaja fillo ya kwanta agefen Aryan din,Captain Aryan kuwa yanata tunani saida yadawo daga duniyar tunanin nasa sannan ya kalli Ashraf yace"yanaga kaima kayi shiru?