Showing 36001 words to 39000 words out of 110331 words

Chapter 13 - MAWAHIB COMPLT HAUSA NOVEL

13 Sep 2024

19709

cikin dakewa yace"kindameni da kuka,kitashi kifice daga gidannan kije waje kiyi,kin takuramin zaki hanani bacci, banason hayaniya"

Tanajin maganar sa tadago fuskarta dake cikeda hawaye ta kalleshi, ganin fuskar tasa babu Rahma yasa cikin sauri ta maida kanta qasa tace"ni yunwa nakeji"

Yanajin haka ya girgiza kansa Yafuto yabar mata dakin, yanzu fisabilillah saboda yunwa kawai ta zauna take masa ihu a kansa? Komai kuka towa zata yiwa kuka? Bata barshi da damuwar dayake ciki ba zata qara masa wata damuwar? Shimafa dazai samu kukan nan zaiyi ko zaiji sauqin abinda yakeji aransa (πŸ˜²πŸ™Š)
Yana gama wannan tunanin yadauki key din Mota yafice yabar gidan, bai dauki dogon lokaci ba yadawo gidan hannunsa daukeda takeaway guda daya,Kai tsaye dakinta yawuce yana zuwa yajefa mata ledar, abincin dayake ciki yawatse ajikinta, kadanne yayi saura acikin ledar, bai saurari komai ba ya rufe mata dakin da qarfin gaske,zafin abincin ne yasa Mawahib tatashi da sauri tana karkade jikinta,shinkafa ce jallop Sai wainar qwai da cinyar kaza guda daya,amma duka ta watse agabanta, qofar tabi da kallo taga harya Riga ya rufe, haushi yasa ta dauki sauran nacikin ledar ta wulloshi jikin qofar dakin Shima ya watse anan, tatafi da gudu tafada kan gado tana kuka,ahaka baccin wahala ya dauketa.


Haly JASHERU venture's,munada kayayyaki masu kyau da inganchi ba algus da ha'inci, kayanmu daga Ethiopian ne, prdct dinmu muna Ethiopian magic hair oil, anti dandruff shampoo serum, bdy cream, hand cream, magungunan chuttuka da na mata masu inganchi da qara lfy ajikin dan
adam ga number kmr hk 07046665338 ko 07061664264 munada distributor ako Ina afadin kasarnan da ketare muna koya harkokin kasuwnchinmu ga masu bukata akan 5000 kacal

sannan munada tsuntsaye na kasashen waje tattabaru game bukata ko koya akwai riba kwarai aharkar mebuqata yasiya koya koya seyanemeni a number na kamar haka 07046665338 ko 07061664264, ku antayo ayi tafiyar daku,yar'uwa kikoyi sana'ah akan wannan farashi me sauqi kema ki kafa kankiπŸ’ƒπŸΌ

Washegari tun sassafe yunwa tatashe ta,Bayan tayi sallah tayi karatun qur'ani kamar yanda tasaba, tagyara dakin tsaf yadawo hayyacinsa, sannan tashiga toilet tayi wanka ta shirya cikin Riga da siket na Atamfa sannan tasaka hijab tafuto zuwa falon qasa,Kai tsaye kitchen ta nufa, Bata tsaya qarewa kitchen din kallo ba saboda jiri jiri take ji saboda yunwa,jikinta har wata karkarwa yake,Kai tsaye tabude fridge din data gani aciki,anan taci karo da lemuka da ruwa harda madarar Hollandia, cikin sauri ta dauki kwali biyu tarufe fridge din takoma Sama, tana zuwa tarufe dakin tasaka key sannan takafa Kai a madarar Nan saida ta shanye kwali daya sannan tafara maida numfashi,ahankali tatashi ta kwanta akan gado tana lumshe idonta, Sai yanzu ne tafara jinta tana dawowa hayyacinta.

Wannan lemukan data dauko suta wuni tanasha bata Bude dakin Bama bare tafuto,Washegari ma haka tayi, sauka tayi tasake dauko wasu, anan taci karo da kayan abinci a kitchen din, duk wani nau'in kayan abinci saida ta ganshi, tabude babban fridge din dayake gefe taganshi da nama danye Kala Kala harda kaji saide duk sun daskare alamun kamar sun dade acikin fridge din.

Kwanansu uku babu Wanda yaga wani, kullum dasafe zata futo ta dauki lemo takoma daki, bata yarda suhadu.

Yauda safe tafuto daukar lemo taga kitchen din yana buqatar gyara, da hijabi ajikinta tafara gyara kitchen din, tafara mopping Kenan yashigo kitchen din da dan gudunsa sai hada gumi yake yana Sanye cikin kayan gym singlet da gajeren wando irin singlet din,kai tsaye fridge ya nufa yabude yadauki gorar ruwa guda daya Mai sanyi yafara Sha,gaban Mawahib yafadi,ta gefen ido ta kalleshi taga yanda murdadden jikinsa yake shinning yana hada gumi da alama daga motsa jiki yadawo,ga yanayin garin akwai sanyin safiya amma ahaka yake shan ruwa sanyi ga jikinsa babu suturar arziqi da alama sanyi baya damunsa, ganin zai juyo yasa tayi saurin yin qasa da kanta, saida ya shanye ruwan tas Sannan ya wullar da gorar ruwan anan,zuciyarsa tayi baqiqqirin alamun 6acin rai,ganin Mawahib ko gaisuwa ta gagara yimasa.

Ita kuwa gaba daya a tsorace take dashi,cikin sauri tazo zata dauke robar ruwan daya Jefar a wajan,santsin ruwan dabai gama bushewa ba ya dauketa tatafi luuuu zata fadi, cikin sauri Captain Aryan yayi sauri yaruqota,kallon fuskarta yayi yaga ta Runtse idonta alamun ta tsorata da faduwar da zatayi,zuba mata ido yayi yana kallonta, wata zuciyar tace dashi yarinyar dabata Iya gaisuwa ba ka taimaka wa? Lokaci daya ransa yasake 6aci,Kai tsaye yasake ta tafadi qasa warwas a wajan, hannunta ya hadu da tiles din kitchen din yabugu,lokaci daya tasaki qaran azaba,Captain ya juya yafita, yana jinta amma Koda wasa bai juyo ya kalleta ba bare yaga halin datake ciki.

Cikin sauri tatashi tana yarfe hannu tareda hura iska a'inda taji ta bugun,daga kanta tayi ta Kalli kofar kitchen din acan ta hango Captain yana hayewa Sama,cikin ranta tace"mugu...."

Kai tsaye ta wuce dakinta tafara dudduba cikin kayan ta kasancewar ko agida Bata rasa magani Mamy tana zuwa da wasu gida, anan taga paracetamol, ta6alla tasha sannan ta wuce toilet tahada ruwan dumi tayi wanka dashi, cikin ikon Allah Sai taji ta kalau,taso tafuto tashare falon ta gyarashi, to amma ganin ya Captain yana gidan yanzu shiyasa ta yanke shawarar gara ta kwanta idan taji alamun yafita zuwa yamma saita futo tagyara falon,doguwar Riga tasaka marar nauyi, ta kwanta agado Nan da Nan bacci ya dauketa.

Da yamma wajan karfe uku taji gidan shiru,tasaka hijabin ta madaidaici akan doguwar rigar data saka dazu,tafuto kamar yanda ta tsara zata gyara falon,zuciyarta daya tasauko qasa tana zuwa Sai tayi turus ganinsa afalon yabaje takardu ga Kuma computer agabansa yana dannawa, yana Sanye cikin Riga da wando,rigar milk color, wandon Kuma na jeans ne,Sai yanzu ne ta ganshi ta kayan arziqi tunda tazo gidan, kullum yana cikin kayan shan Isa ko tsoron sanyi ba yayi.

Mazewa tayi ta wuce ta dauko tsintsiya a kitchen batace dashi uffan ba, yanajin saukowar ta, yanajin lokacin data wuce tasake dawowa, Shima baice da'ita uffan ba.

Sharar tafara cikin sauri sauri danta gama takoma daki, saida tagama share ko'ina tas sannan tadawo inda yake zata share, ta sunkuya tafara Sharar,mamaki yasake kama Captain,yaga alamun gaba daya tagama rainashi,yana gaba da'ita amma tafi qarfin ta gaidashi, ya kalleta ta gefen ido,yagama Lura kan yarinyar yana rawa, Kuma bazai dauki raini ba, dole zai sauke mata duk wani Iya shege datake ji dashi.

zuciyar ta daya tazo gab dashi da Sharar ganin yana zaune a wajan yasa ta miqe zata tsallake inda yake zaune,tashin Nan da zatayi tana daga qafarta Captain yasaka qafarsa a wajan da niyya,aikuwa saita harde tafadi a wajan, yana ganin tafadi ya kalleta tareda ta6e baki yaci gaba da typing din dayake a computer.

Mawahib Batasan lokacin data saki wani irin kukan taqaici ba,tatashi tana riqe da goshinta dayake mata zafi tayi wulli da tsintsiyar sannan ta wuce daki da gudu tana kuka.

Sosai take kuka Kuma kuka Mai sauti kamar Wanda akayi mata mutuwa, jakunkunan kayanta guda uku Wanda suke ajiye d'om,suta fara janyowa da qyar gaba dayatafuto dasu gaban dakinta ta jirgesu anan kofar dakinta.(πŸ™†πŸ»β€β™€οΈ)

Jin kukan nata yayi Yawa Hakan yasa yasaka hannuwansa ya rufe kunnuwansa duka biyun,amma yanajin kukan, cikin 6acin rai ya kawar da computer sa gefe yatashi yanufi Saman, yana zuwa tundaga kan matakalar benin nasu ya hango jakar kayanta a adane agefe,bai damu dasuba ya tsallake su yanufi dakin nata, yana kama handle din dakin zai Bude saiya jiyo muryarta cikin ihun kuka tana fadin"Nabiha wallahi gida zan tafi,Kuma Allah saina fadawa Mamy abinda yakemin,banason wannan auren,zuciyata zafi takemin inajin mutuwa zanyi" ta qarasa maganar tana ruskar kuka

Daga daya 6angaren Nabiha tace"Mawahib karki fadawa Mamy,kinsan kan Garin Abuja ne da zakice zaki taho ke kadai? kiyi haquri Dan Allah koma meya miki kibarshi da Allah, Kuma Allah saiya saka miki"

Cikin kuka tace"idan nasake kwana agidan Nan tobana numfashi Nabiha...."(πŸ˜³πŸ™†πŸ»β€β™€οΈ)

Tana fadar haka ta kashe wayar tafuto daga dakin, tana Bude kofar dakin ta ganshi a tsaye a wajan ya harde hannunsa a qirjinsa, fuskarsa a daure yamiqa mata hannunsa yace"bani wayar nakira miki Anty Ma-myn"

Bata kalli inda yakeba ta sunkuya tafara kinkimar jakar kayanta(😳)

Cikin 6acin rai yadaka mata tsawa yace"go back"



Mawahib littafin kudi ne,duk me buqata naira 500 ne kacal ta wannan account din
0164549488
Amina muhammad
GTbank

Kokuma katin MTN ta wannan number 08033300034

idona nahana bacci nacinye lokaci na narubutashi,bazanja Allah ya'isa ba,amma muddin kika karanta baki biyani haqqina ba nabarki keda mahaliccinki faqadπŸ‘ŒπŸ»





Amnah El Yaqoub✍🏻
[7/9, 9:20 AM] AMINA KABIR CAPS: *Page 47*


Mawahib littafin kudi ne,duk me buqata naira 500 ne kacal ta wannan account din
0164549488
Amina muhammad
GTbank

Kokuma katin MTN ta wannan number 08033300034

bazanja Allah ya'isa ba,amma muddin kika karanta baki biyani haqqina ba nabarki keda mahaliccinki faqadπŸ‘ŒπŸ»



Tsawon lokaci ta dauka tana kuka awajan,gaba daya takasa tashi daga wajan gani take tana miqewa zai sake dawowa yaganta tsirara, ta dade awajan saida tagama kuka a yanda take a tsugunne sannan cikin gudu tatashi tarufe dakin daga jiki, sannan ta murzawa dakin key.


jikinta sai karkarwa yake kwata kwata bata samu qwarin gwiwar saka kaya ba,haka tahau kan gado tashige cikin bargo tana kuka.

Adede lokacin Mamy takira wayarta,tana cikin bargon tayi sauri ta dauki wayar,Mamy tanajin yanda tayi sallama tasan cewa kuka tayi,batayi mata tambaya akan yanayin muryarta dataji ba,tace"Captain yakawo miki saqo?"

Cikin muryar kuka tace"Eh Mamy yakawo"

Mamy tayi ajiyar zuciya tace"gumba ce kidinga ci kullum"

Saida tayi ajiyar zuciya alamun tasha kuka sannan tace"to Mamy"

Mamy taba tambayi dalilin kukan ba,tasan mata da miji Sai Allah, suna gama magana tayi sauri takashe wayar.


Da sassafe tatashi zata futo tadora abinci,ta kirma wani uban hijabi ita kanta tasan wannan hijabin yafi qarfinta,tana futowa daga dakin tayi turus ta tsaya ganin Yaya Captain a tsaye a falon Yajuya bayansa yana magana awaya kamar bayaso, ahankali tafara ja da baya dan karya ji takunta harta dawo sama,abinda bata saniba shine tun futowar ta yajita, yaqi juyawa ne saboda bayason suhada ido,gani yake zata dinga yimasa kallon fassara saboda halin daya ganta aciki jiya,Wanda har zuwa wayewar gari yana danasanin shiga dakin nata saboda masifar da hakan taja masa,(πŸ™ˆπŸ™Š)

Tana gabda shiga dakinta taji yana cewa"toya zanyi? duk inda soja yake yasan cewa dole ne ya dinga sadaukar da ransa ayaqi,dole ne zamu fuskanci maqiyan qasa da abokan gaba komu kashe ko a kashe mu,wannan shine mataki na qarshe...."

Lokaci daya jikinta yayi sanyi, Ina zaije yake maganar kisa?
sanin babu mai bata amsa yasa tashige dakinta tare rufowa,dama saboda cikinta zatayi girkin tunda shide idan tayi bayaci,gara ta haqura da girkin da'ace tafita tahada ido da Yaya Captain,hijabin jikinta tacire tayi kwanciyar ta tana duba wayarta.

Bata sake futowa daga dakiba Sai azahar,gidan shiru kamar kullum,saida ta leqa taga babu motarsa guda daya sannan tasaki ajiyar zuciya ta wuce kitchen tahada abinci mai sauqi, tafuto da abincin daga kitchen ta wuce dining,anan taci karo da rafar kudi Yan dubu daya, kimanin dubu dari,da wata takarda aqasan kudin,abincin hannunta ta ajiye, sannan tajanye kudin taduba takardar "BANDA FITA YAWO"

Abinda aka rubuta a takardar kenan,tadauki kudin tadinga juyashi a hannunta tana tambayar kanta mezatai da kudi to? menene ma'anar wannan rubutun? Meyake nufi?

Tunda tazo duniya bata ta6a riqe kudi mai yawan wannan ba,ba'a bata kudin daya wuce dubu ashirin,sai wannan kudin ya tsoratata, ta ajiye shi agefe tareda takardar tafara cin abincinta.

Wayarta dake gefe tafara qara,tana dubawa taga Nabiha ce me Kiran,cikin sauri ta dauka tace"Nabiha"

Nabiha tace"na'am Mawahib ashe Yaya Captain suntafi wani daji kamo yan bindiga"

Mawahib tayi shiru tana tunani,Kenan shine ma'anar barin wannan kudin da wannan takardar.
Cikin rashin damuwa tace"nima yanzu nakeji a wajanki"

Cikin mamaki Nabiha tace"wai kina nufin bai fada miki zai tafi ba?"

Mawahib tace"to menene hadina dashi dazai fadamin zaiyi tafiya? Kinga kowa rayuwar sa yake a gidannan,tsakani na dashi gaisuwa"

Nabiha tayi ajiyar zuciya tace"ta6di, lalle muna ruwa Mawahib,to aike gara ke ko Yaya ne,kina ganin Yaya Captain, nifa tunda aka fara hidimar bikinnan,aka gama, aka kawoni gidannan,wallahi har yau banga idon Yaya Ashraf ba,gida nikadai kamar mayya, Kuma wallahi duk lokacin daya dawo saiya raina kansa"

Cikin sauri Mawahib ta zaro ido(😳)
Tace"mekikace Nabiha?Yaya Ashraf dinne zai raina kansa? ke kuwa Nabiha nawa kike dashi a account dinki?"


Cikin damuwa Nabiha tace"wai me kike nufi ne Mawahib? auren nan namufa babu fashi,kina ganin dan mun nuna bama so Daddy Alqali zaisa su sakemu ne? Idan sun sakemu mun koma gidan mun zauna suma sundawo gidan hakan dadi zaiyi? gara tun wuri muyiwa kanmu fada, muriqe mazajenmu tun kafin wasu matan su qwace mana su"

Cikin damuwa Mawahib tace"anya zan'iya? kinga Yaya Captain ba kamar Yaya Ashraf ba,kuma ni har yanzu banajin sonsa araina ko kadan,nifa banqi muyi shekara da shekaru ahaka ba,yayi harkarsa inyi tawa"

Nabiha tace"Mawahib bakida wayo, kwata kwata yarinta tamiki illa,to kodan Momy kilishi aikya yiwa kanki fada,amma kiyi tunani"

haka Nabiha takashe wayar tabarta cikin tunani,gaba daya sai taji abincin datake ci yafita aranta,kanta yafara ciwo,cikin damuwa tatashi tabar wajan tahau sama.

Dan qaramin falonsu dayake Sama Wanda yaraba dakinta dana Yaya Captain,nan tashiga,tayi tagumi hannu biyu tana tunani tayaya ne zata Iya sauya zamansu da Yaya Captain bayan kokadan bata jinsa aranta? tayaya zatayi hakan bayan tasan cewa shima awajansa itada banza duk daya?

Ajiyar zuciya tayi tafuto balcony din wajan tafara qarewa gidan kallo tana shaqar wata is'ka mai dadi,ta dade awajan sannan takoma falo ta kunna kallo.


Satinsu daya adaji,tunda yatafi hankalin Mawahib a kwance,bata tunawa dashi kokadan bare tayi tunanin halin dayake ciki, rayuwarta take tama manta dashi,tana zaune afalon Sama tana kallo tabude data tahau Facebook anan taci karo da wasu sojoji da bbc ta dora tana bayanin cewa Sojojin Nigeria sunyi nasarar kama Yan bindiga Wanda suka addabi yankin kudancin qasar.

Mawahib tasake karanta labarin,lokaci daya ta tasaki wani irin murmushi,tunda tazo gidan yaune karon farko da tasan tayi murmushi.


******


Tunda akai bikinsu kusan kwana takwas Kenan Sai yau Ashraf yadawo daga Rivers,tunda yashigo gidan yawuce dakinsa, bai nemi inda Nabiha take ba,ita kuwa tanajin zuwansa tayi sauri tashiga kitchen tafara kokarin yimasa hadadden girki,bata gamaba har bayan magrib,ta wuce dakinta tayi wanka ta shirya cikin shadda Riga da siket ta tsara kwalliya tagani tafada, sannan ta wuce dakinsa tafara qwanqwasa wa, cikin mamaki Ashraf yabude qofar,nan take yayi tozali da kwalliyar da Nabiha tazuba,bai nuna mata komai ba Kai tsaye yace"lafiya?"

Cikin sanyi tace" Yaya Ashraf akwai abinci,kafuto kaci abinci"

Lokaci daya ransa yadan 6aci,shi wannan yarinyar zatazo tana yiwa Kiran miji Yafuto yaci abinci? har zai fara masifa, saiya tuna ai itama bason auren take ba, akwai Wanda takeso agefe, saiya fasa Yasaki ajiyar zuciya yace"to"

Bai jira amsarta ba yamaida qofar ya rufe.

Jikin Nabiha yayi sanyi,tajuya fararen idonta tareda sakin ajiyar zuciya,Yaya zatayi da son wannan bawan Allah?
a'ido ma basai an fada mataba tasan cewa Yaya Ashraf baya sonta,ta wacce hanya zatabi ta janyo hankalinsa gareta?

Cikin sanyin jiki tajuya zuwa falon ta zauna awajan abincin tana jiransa, saida yagama yangarsa son ransa sannan yayi wanka, zai saka gajeren wando da yar qaramar riga saiya fasa dayayi tunanin Zaman nasu bamai dorewa bane menene abun sakewa da yarinya har yana saka gajeren wando duk tagama ganeshi ciki da bai sannan su rabu, saiya janyo jallabiyar sa yasaka Yafuto falon.

Hangota yayi a zaune ita kadai tasa abincin agaba ga waya a hannunta tana dannawa, Kai tsaye zuwa yayi ya zauna yafara bude abincin wani daddadan qamshi ya dakeshi, ya juya ya kalleta yace"to yanzu ke Nabiha kya gajiyar da kanki akaina? inake Ina wani girki muda zaman namu bamai dorewa bane?"(πŸ˜²πŸ™†πŸ»β€β™€οΈ)

Nabiha tace"yaya Ashraf ai girki ne,ko agida amatsayina na qanwar ka aiba laifi bane dannayi ma girki"

Ashraf yayi shiru yatafi dogon tunani, Sai can yace"hakane Kuma,amma de duk da hakan, kidena,karki sake takura kanki akaina"

Cikin ladabi tace"to yaya"

Daga Nan tatashi tafara zuba masa abincin


******


Da daddare wajan qarfe takwas ta dinga jiyo murya sama sama ana magana,sai hayaniya ake wasu suna ihu,cikin sauri tabude qofar dakinta tafuto, anan tafijin hayaniyar sosai,har zataje ta bude qofar falon taga menene Sai tsoro ya kamata, saita shiga dakin qaramin falonsu na sama, tafita ta balcony din gidan anan taga sojoji dayawa a compound din wasu a tsaye wasu a zaune,dawani abu agabansu sunaci Batasan menene ba,Yaya Captain yana gefe yana danna wayarsa kamar baya wajan,tun lokacin data fara leqensu yaganta tagefen idonsa,Sai yaqi dagowa yaci gaba da danna wayarsa.
Mawahib takoma gefe tana qare musu kallo batareda sun sani ba.


Daya daga cikin Sojojin ne yaharba bindiga sama,Mawahib datake tsaye tanajin qaran bindiga tayi sauri tarufe kunnuwanta tareda tsugunna wa awajan.


Kai tsaye Captain yadago kansa, ya kalleta yaga bata wajan, yamaida idonsa kan wayarsa a hankali yace"matsoraciya"

da alama bata ta6ajin qaran bomb ba,dagajin wannan qaran harta tsorata.

Mawahib kuwa cikin gudu tabar wajan takoma daki,cikin ranta tace sundawo kenan.

Wayarta ce tafara qara, tana dubawa taga Mamy ce, cikin sauri ta dauka tareda sallama, Mamy tace"sannu Mawahib, yakukaji da jama'ah Kuma?"

Cikin rashin fahimta tace"jama'ah wanne iri kenan Mamy?"

Mamy tace"mijinki yadawo daga cikin dokar daji kina tambaya ta wacce jama'ah? Mutanan arziqi mana Masu zuwa muku murna"

Cikin halin ko'inkula tace"inajin sunzo sunyi masa,ni har yanzu ban hadu dashi ba"

Cikin tsananin mamaki Mamy tace"dawaye baki hadu ba? Kanki daya kuwa?"

Lokaci daya idonta yakawo ruwa,yanda taji Mamy tana maganar tasan cewa babu wasa a fuskarta, kan kace kwabo har hawaye sun fara zubowa a fuskarta cikin hawaye tace"Mamy ni wallahi banason shi..."

Cikin 6acin rai Mamy tace"banason sakarci Mawahib,cemiki akai shi yana sonki ne? da bakina da nashi yafadamin bayason kowacce yarinya, da komai ya bayyana gaskiya tafuto fili shine mijinki kinji yayiwa iyayensa tijara ne bayason auren? Meyasa ke bazaki kwantar da hankalin ki kizauna adakin mijinki kiyi shiru ba? saikin nunawa duniya da Yaya kilishi cewa bamu baki tarbiya ba kamar yanda take fada?"

Zuwa wannan lokacin Mawahib kuka take harda shashsheka, cikin kuka tace"Mamy konayi masa girki bayaci,baison magana dani..."

Cikin damuwa Mamy tace"toya zakiyi tunda ubanki ya janyo miki? Idan bakiyi haquri kin zauna ba so kike yasakeki kidawo muzauna Yaya kilishi taji dadin goranta miki? Shikkenan,Kici gaba tunda haka kikaga yafi miki"
tafadi haka tareda kashe wayar.

Kifa kanta tayi akan gado tafara ruskar kuka kamar marar lafiya,tasaka hannunta biyu tarufe fuskarta dashi tana kuka, cikin kuka take tunani gani ga Yaya Captain agida daya, idan kasheni zaiyi saide ya kasheni babu wanda ya damu daba Shiri nake dashi ba, itama Mamy tadawo tana bin bayansa,meyasa takeso ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login