Showing 105001 words to 108000 words out of 110331 words

Chapter 36 - MAWAHIB COMPLT HAUSA NOVEL

13 Sep 2024

19700

da Nabiha adakin,Ashraf yasake qarewa yaran kallo yace"Momy wannan ne babba,saboda haka shine Ashraf"

Cikin sauri Captain Aryan yace"inji waye? saboda Kaine babba kuma yanzu ma saika za6i babban kace shine Ashraf?, to bazai iyu ba, suma suna girma haka babban zai iyo halin ka ya dinga cewa shine gaba da Aryan, saboda haka na sauya, yanzu Aryan ne babba, Ashraf qarami"

Hajiya kilishi tace"Dan Allah sai yaushe zaku girma kudena musu akan waye babba waye qarami? Akan yayan naku ma saikun gwada halinku?, to duk ku barsu, uwarsu saita za6a da kanta waye zai zama babba waye qarami"(πŸ˜‚)

Wannan furucin natane yasa sukai shiru tunda tabarwa uwar yaran wuqa da nama a hannunta.


tunda akai haihuwar duk wasu masu zuwa barka anan falon Hajiya kilishi suke ganin yaran, Mawahib kuma tana cikin dakin tana hutawa, saide in yunwa suke ji sai Nabiha takawo mata su susha.


Kwanan ta uku da haihuwa Alhaji Ma'aruf yazo yaga yaran, bai hadu da Mamy ba alokacin tana wajan aiki,duk wata kulawa data dace Hajiya kilishi tana bawa Mawahib,koda yaushe tana sakata tana zama acikin ruwan dumi saboda dinkin da'aka mata, tsakanin ta da yara saide in suna jin yunwa kawai, da rana haka zasu wuni suna bacci, da daddare kuma su hana Mawahib da Hajiya kilishi bacci da kukan su.

Ana gobe suna suna zaune da Hajiya kilishi da Mamy da Mama Sadiya dukansu adakin Hajiya kilishin,Mawahib taci kwalliyar ta cikin riga da siket na leshi tayi kyau sosai duk da dare ne,ruwan tea takesha Abba yashigo dakin yadauki yaran Wanda idonsu yake qur akan hasken dakin, cikin kulawa Abba yace"suna tayaku fira kenan"

Hajiya kilishi tace"wadannan? lumbu lumbu kenan, Ana jimawa zasu fara kuka kamar wanda ake zigasu, daya yana fara kuka Shima dayan zai farka yafara har tausayi uwar tasu take bani,haka zan yi juyi inganta daram a zaune tana faman jijjigasu, to sai in dauki daya in tayata Nima, amma bama bacci wallahi, nikuma lokacin danayi goyon su Ashraf bahaka nayi ba, kalau muke bacci"

Abba yace"toku dinga hanasu baccin da rana mana Yaya"

Hajiya kilishi tace"ana musu wanka ma idonsu a rufe yake, saide in wankan yayi wanka shine zasu farka,amma wannan kukan nasu yayi yawa, kamar hadin baki Yara kudinga ihun kuka cikin dare"

Kafin Abba yabata amsa megadinsu yadoko sallama yafara ajiye wasu hadaddun akwatuna agabansu, mamaki ya kama su, kafin suyi magana Ashraf da Aryan ma sun shigo da wasu, wasa wasa saida suka ajiye akwatuna guda goma, na yara shida, kowa uku uku, na Mawahib kuma guda hudu.

Abba ya kallesu yace"wannan kayan menene?"

Ashraf yace" kayan Baby's ne dana mejego"

Cikin sauri Abba yace"ba Maryam tasiyo wa yaran wasu kayan ba?, meza suyi da kayan har haka?"

Captain Aryan da kansa yake qasa yace"Uncle ai basuda yawa"

Abba yayi murmushi ya girgiza kansa sannan yafice daga dakin.

Hajiya kilishi ta kalli Mama Sadiya tace"Sadiya bude mana kayan mugani"

Kayan Mama Sadiya tafara budewa suna ganin hadaddun kayan baby's Kala Kala masu masifar kyau, Captain Aryan ya kalli Mawahib yanaso su ke6e amma babu dama, alama yayi mata akan ta duba wayarta, sannan suka fice daga dakin shida Ashraf.

Ahankali ta dauki wayarta taduba taga yayi mata alert din kudi ko zatayi wasu buqatun dashi na suna.

Saqo tafara tura masa tana masa fada akan yawan kudin dayake kashe musu, nan take ya tabbatar dashi da abunda ya mallaka duka mallakinta ne tayi yanda takeso dasu, haka suka dinga musayar saqo sai murmushi take saki ita kadai.

Washegari akayi taron suna,yara sukaci sunan Ashraf da Aryan, kamar yanda mahaifiyar su ta za6a itama, saide babban tace a sakawa sunan Ashraf,a ko'ina babba babba ne, haka tatoshe kunnanta bayan kallon harara data samu daga wajan Yaya Captain bayan yaji hukuncin data yanke.

Alhaji Ma'aruf yazo suna,shida matarsa murjanatu, Mamy taja murjanatu ajiki kamar qawarta, ganin yanda murjanatun take kulawa da Mawahib adan Zaman dasuka yi na wunin ranar,Mawahib tasha wanka yanda ya kamata, gida yacika dam da baqi, wasu dangin kilishi, wasu dangin Mama Sadiya, wasu kuma dangin su Alqali, wasu kuma dangin Mamy ne Yan maiduguri, idan kaga jama'ar da gidan Alqali ya dauka zaka rantse aure akeyi ba bikin sunaba.

Captain Aryan yayi kokari sosai kuma ya kashe kudi kamar banza wajan ganin an wadata kowa da abinci da sha, yayinda Mamy ta dauki nauyin duk wasu abubuwan daza'a rabawa mutane na kyauta.

Hajiya kilishi kuwa kasa zama tayi, anjima ki ganta acan, anjima kisake ganinta acan tana kula da baqi.

Yayinda Mama Sadiya da Murjanatu matar Alhaji Ma'aruf dawata mata daga maiduguri suke kula da yaran, duk baccinsu kuwa yau ba suyi baccin ranaba saboda hayaniya dakuma yanda ake yawan daukar su.

Murjanatu da Alhaji Ma'aruf basu tafi ba, saida suka kwana, dasafe da Murjanatu akai aikin gyaran gidan da komai, sukai suyar naman suna, suka gyara kitchen sannan da yamma sukai shirin tafiya itada Alhaji Ma'aruf, kafin su tafi saida Alhaji Ma'aruf yasake neman yafiyar Mamy ta kuma tabbatar masa komai yawuce, sannan suka tafi kebbi.


Saida Captain Aryan yayi sati daya bayan suna, sannan ya shirya yatafi Abuja, Mawahib kuma sukaci gaba da wanka 6angare daya kuma yana tareda matarsa da baby's dinsa ta vedio call, kullum saiya gansu yakejin dadi.


Haly JASHERU venture's,munada kayayyaki masu kyau da inganchi ba algus da ha'inci, kayanmu daga Ethiopian ne, prdct dinmu muna Ethiopian magic hair oil, anti dandruff shampoo serum, bdy cream, hand cream, magungunan chuttuka da na mata masu inganchi da qara lfy ajikin dan
adam ga number kmr hk 07046665338 ko 07061664264 munada distributor ako Ina afadin kasarnan da ketare muna koya harkokin kasuwnchinmu ga masu bukata akan 5000 kacal

sannan munada tsuntsaye na kasashen waje tattabaru game bukata ko koya akwai riba kwarai aharkar mebuqata yasiya koya koya seyanemeni a number na kamar haka 07046665338 ko 07061664264, ku antayo ayi tafiyar daku,yar'uwa kikoyi sana'ah akan wannan farashi me sauqi kema ki kafa kankiπŸ’ƒπŸΌ

A wannan zaman wankan da Mawahib tayi,tasamu kulawa sosai,6angaren Mamy bata wasa da'ita wajan bata magunguna masu kyau na mata, amma Koda wasa bata ta6a bata maganin a gaban Hajiya kilishi ba, saide idan sun ke6e zata sata agaba saita sha duk wani magani na mata da tasan cewa zaiyi wa Mawahib din amfani,Mama Sadiya ma ba'a barta abayaba, ganin yanda Mamy ta zage dantse ta kula mata da Nabiha lokacin haihuwar ta ba tareda ko sisinta ba, hakan yasa itama tazauna da kanta tayi mata hadin kaza da nonon raqumi tasata agaba tacinye kazar tas, cikin sati uku kuwa saiga Mawahib tasake cika tayi wani fresh kasancewar ko cikin rana ba shiga takeba, hips dinta suka sake girma haka breast dinta ma, tana kula da yaran ta sosai bata gajiya da kukan su, haka dan dolenta tamaida tsarin baccinta yadawo irin nasu, da rana suyi bacci da daddare kuma ido biyu.


Captain Aryan koda wasa baiyi kuskuren zuwa gidaba, saboda shi kansa yasan anbawa Mawahib tsaro yanda ya kamata, bai Isa ya tunkare taba.


saide duk lokacin dasuke vedio call tana ganin irin ramewar da yayi.

Hakan yasa suna zubarda wanka ya taho gida,afalon Hajiya kilishi ya sauka Mawahib tatashi tagabatar masa da abinci kala kala wanda tashiga kitchen da kanta tayi masa, duk inda tajuya kuwa idonsa yana yawo ajikinta kwata kwata ya manta da zaman Hajiya kilishi afalon, idan Mawahib tana wajan ita yake kallo, idan tabar wajan hankalinsa saiya dawo kan yaransa, yanda yake ganinsu a vedio call saiya ga sunfi haka warware wa, yadaga kansa ya kallo Hajiya kilishi yace"Momy yaran nan me ake basu ne naga sun qara girma haka?"

Hajiya kilishi tace"babu abinda ake basu Babana,nonon uwar ne me kyau,kullum basuda aiki sai shan nono, shiyasa aikuwa gatanan duk sun tsotseta sai rama take"

Cikin sauri Captain Aryan ya kalli Mawahib yaganta 6ul6ul masha Allah komai yacuko yayi girma, Yaya Momy takeso tazama kuma bayan haka?
yaga alama jarabar shan nonon da yaransa sukeyi shine yasa Momy zata huce akan sa, kuma nono yanzu tafara bayarwa dan shima gashi yadawo yazama cikon na uku(πŸ™Š)


Murmushi yayi a fili daga nan baice komai ba, Mawahib ta tsugunna tafara zuba masa abincin sannan ta dauke yaran daga cinyarsa shi kuma yafara cin abincin, Hajiya kilishi tazuba masa ido tana kallonsa cikin tausaya wa, yanda taga ya rame ta tabbatar ba qaramin qoqari yayi ba, musanman yanda taga yakama abincin da gaske yanaci, hakan yasa tagama yanke shawarar bashi matarsa yau su tafi dakinsa saboda da alama yana qirga kwanakin wankan Mawahib din duba da yanda bai qara mata ko kwana daya ba yadawo, ga wannan kallo dayake binta dashi, tajuya ta kalli Mawahib taga wayarta a hannunta tana dannawa, itade bataga iyayen nata su Sadiya da Maryam sun dan bata wani abu tasha ba, gashi shi Captain yariga yadawo, hakan yasa ta miqe tashiga kitchen din falon ta, tabude fridge dinta tana tunanin irin hadin dazata bawa Mawahib din domin tayiwa danta gata kasancewar ya rame dayawa tasan cewa yayi kokari, kankana ta yanka tahada da dabino, da cocumber , da ayaba, da kwakwa, tazuba peak ta ruwa gongoni daya, sannna tayi Blanding dinsa tajuye tasaka mata a fridge, tadawo falon ta zauna.

Captain Aryan yana gama cin abinci yafice daga falon saboda idan yaci gaba da zama za'a Iya Samun matsala, kuma ga Momy akusa.

Hajiya kilishi tana ganin yafita ta kalli Mawahib tace"kije fridge kidauko dan fruit nahada miki ki shanye shi duka"

Mawahib ta kalleta da sauri,tasan batasan su Mamy da Mama Sadiya sun bata wannan abubuwan ba, har zataqi zuwa tasha saita ga kuma Hajiya kilishin zata Iya tambayarta dalili, hakan yasa babu musu tawuce taje ta dauka ta shanye tana mamakin irin qaunar dasuke wa Yaya Captain.


Har qarfe goma nadare Captain bai shigo ba,Mawahib tana shirin kwanciya Hajiya kilishi tace"A a dauke su kutafi,mijinki yadawo Ina zaki kwanta anan,dauke su kuje shima yau yadana rashin baccin"

Mawahib tayi murmushi ta dauki yaranta suka tafi dakin Yaya Captain, kwantar dasu tayi, tafara qoqarin kwanciya sai gashi yashigo dakin.

Cikin sauri yaqaraso yasaka ta a jikinsa, yafara kissing dinta ahaukace,dagashi har ita wata irin ajiyar zuciya suke saukewa, bai bari tacire kayantaba yasaka hannunsa yayagasu.


yanda ya birkice mata ne yasa ta garara yimasa magana, saida tafiya tayi nisa sannan tace"Baby munyi dakai fa bazan sake haihuwa ba"

Cikin sauri yace"amma ai bamuyi dake ba zamuyi wannan abun ba..."

Zata sake magana yahade bakinsu waje daya,sannan ya dauketa cak suka qarasa gadon, yanda yaji ta tsaf yanda yakeso hakan yasa daya fara surutansa tarufe masa baki, cikin ikon Allah bata barshi yayi musu tonon sililin daya sababa, saide abunda ya daurewa Mawahib kai ganin yaronsu ko guda daya babu wanda yafara alamun kuka, bayan komai yalafa sukai wanka yasaka ta a jikinsa ita kuma tasaka yaran agabanta tana masa mita itade karya yi mata wani cikin, shikuma gaba daya ya lalace awajan lalla6a ta, baccinsu sukai me dadi amma wani qarin mamakin Yara kamar sunsan ubansu yazo sun barshi yayi baccinsa yayinda suma sukai baccin.

Da asuba bayan yadawo daga masallaci ya dauketa suka koma zasuci gaba da bacci kamar yanda suka saba, sai alokacin yara sukace basu san zance ba, Mawahib ta dauki daya tana lallashi, shima Captain yadauki daya, har gari yafara Haske suna kuka, Captain Aryan ya kalleta yace"wai haka suke wannan kukan?"

Cikin sanyin jiki tace"haka suke,bama bacci da daddare nida Momy,yau dinma nayi mamaki da basu hanamu bacci ba"

Cikin damuwa yace"inaga daga min qafa sukai"

Dariya taso kama Mawahib saita fuske, hannunta yakamo yace"zauna kidan basu ko kadanne saimu kwanta wallahi bacci nakeji, kuma ni bazan Iya bacci Ina ganinki ba tareda naji ki ajikinaba"

Babu musu tazauna, tafara bawa Ashraf nonon, cikin sauri yakama yafara sha.

Captain Aryan yasaka hannunsa yaciro dayan tayi tunanin Aryan dinta zai bawa nonon saitaga yadora bakinsa yanasha ahankali, cikin jin dadi ta lumshe idonta tana sake riqe kansa.

Aryan dayake hannun Captain Aryan yasaki wani irin kuka, cikin shaqaqqiyar murya Mawahib tace"Baby ka barshi yasha"

bakinsa yadauke ahankali, sannan yasaka hannunsa yacire dayan datake bawa Ashraf, ya ajiye Ashraf din akan gado sannan yace "kibashi wannan mana"

Yafadi hakan yana maida kansa yaci gaba da sha shima, Mawahib ta kalleshi ta girgiza kanta, taga alama nema yake dagashi har yaransa so suke su qarar da'ita.

Ganin yaran sunyi shiru hakan yasa suka kwanta, saide bacci yana fara dadi suka sake sakin sabon kuka, cikin damuwa Captain yace"waiba sunsha nonon bane? me suke so kuma?"

Mawahib tace"to ai baka barsu sunsha sun qoshi ba, kahanasu"

Cikin damuwa yace"duk wannan dadewar dasukai sunasha be ishesuba sai d'an wanda nasha ne zaisa sukama kuka,? nasu ne ko nawane? hado musu kayansu daga yanzu sun koma wajan Momy da kwana"(πŸ™ŠπŸ™†πŸ»β€β™€οΈπŸ˜‚)


Babu musu tatashi ta dauki dan kayansu da tazo musu dashi, ta dauki Aryan yadauki Ashraf suka futo,itace agaba tana zuwa qofar daki taci karo dawata qatuwar kunama, cikin sauri tayi baya yace"Yaya Captain kunama"
Cikin rashin damuwa yace"ki dauketa mana"

Kallonsa tayi tace"haka kawai saika ce wanda nayi gamo zansa hannu na in dauki kunama?"

Kansa yashafa, sai yanzu yatuna ashefa ba Ashraf bane,ya kalli yanbiyunsa, sannan yazo yawuce tagabanta ya dauke kunamar, Mawahib ta matso da sauri takama hannunsa tace"ina kunamar? bata cijekaba?"

Baice mata komai ba yace"muje"

Kanta ta daga masa suka futo daga dakin,
alokacin gari harya gama wayewa safiya tayi, Hajiya kilishi tafuto zata shiga kitchen da flaks din tea a hannunta sai ganinsu tayi da yara a hannu, ga jakar pampers dinsu da sauran kayan buqata a hannun Captain, cikin mamaki ta tsaya tace"lafiya naganku sassafe? meyafaru?"

Kafin su bata amsa Mamy tafuto daga kitchen din da alama itace take qoqarin hada break fast, itama taja ta tsaya, babu kunya Captain Aryan ya kalli hajiya kilishi yace" Momy dama sun dawo wajanki ne,mun bakisu"(πŸ˜‚πŸ™†πŸ»β€β™€οΈ)

Mamy tanajin haka ta kwashe da dariya, cikin sauri Captain da Mawahib suka juya, ganin Mamy yasa yayi saurin sunkuyar da kansa yana sosa qeyarsa.

Mamy ta qaraso wajansu takalli Hajiya kilishi tace"Yaya yanaga kin bude baki kina kallonsu, ko bakyason kyautar da'aka miki?"

Hajiya kilishi tace" Ina ganin ikon Allah ni kilishi, yanzu kai Aryan shine kasakota agaba kukazo kukawo min yara wato ni karna yi bacci ko?"

Mamy tayi murmushi ta kalli Captain da Mawahib tace"kafin kuyi aure kuyi bacci, bayan kunyi aure ma kuyi bacci, waye yace muku yanzu lokacin bacci ne? ai wanda kukai abaya kunyi Iya rabonku,banda shirme wannan qananun yaran ne za'a rabasu da uwarsu ace sun koma wani waje? toku bani tunda bakwa so"
Tafadi hakan tana meqa musu hannu, Captain da Mawahib suka hada ido,cikin sauri suka juya Sum sum suka koma dakinsu da yaransu.




Mawahib littafin kudi ne,duk me buqata naira 500 ne kacal ta wannan account din
0164549488
Amina muhammad
GTbank

Kokuma katin MTN ta wannan number 08033300034

Idan kika karanta baki biyani haqqina ba nabarki keda mahaliccinki






Amnah El Yaqoub✍🏻
[7/22, 11:25 AM] AMINA KABIR CAPS: MAWAHIB



Mawahib littafin kudi ne,duk me buqata naira 500 ne kacal ta wannan account din
0164549488
Amina muhammad
GTbank

Kokuma katin MTN ta wannan number 08033300034

Idan kika karanta baki biyani haqqina ba nabarki keda mahaliccinki




Suna komawa daki Captain yayi tagumi hannu bibbiyu yana kallon yanda Mawahib ta goya Ashraf, Aryan kuma tana jijjigashi, wani irin tausayin tane ya kamashi, lalle in hakane Momy tayi qoqari, ahankali yatashi ya kar6i Aryan yafara jijjigashi yana zagaye dakin dashi.

Cikin kulawa tace"Yaya Captain kakawo shi saika kwanta kahuta"

Shiru yayi bai tanka mataba, tasake kallonsa tace"please"

Kallonta yayi yace"kidena fadamin sunan nan mana Honey"

Murmushi tayi tace"to Baby, Baby na kawo shi ka kwanta kahuta"

Sunkuyawa yayi yadora Aryan abayansa sannan yafara jijjigashi yace"da'inada damar dazan dauke ciwon naquda dana dauke miki Honey,meyasa rainon yaranmu zan barki kiyi ke kadai?"

Murmushi tayi cikin ranta tana jin yanda soyaiyar mijinta takesake nunkuwa acikin Zuciyarta, haka suka dinga lallashin yaran har sukai nasarar sakasu bacci sannan suka kwanta gaba dayansu sukai baccin.

Kwanan Captain Aryan uku agida sannan sukai shirin komawa Abuja,Hajiya kilishi tahada wa Mawahib kayan tsaraba sosai musanman abubuwan girki,Mamy tasake yimata nasiha akan kula da mijinta, bayan sun futo zasu wuce Mamy tayi mata sallama saboda gobe zata wuce maiduguri wajan bikin Nabil.
Ashraf da Nabiha ne suka rakasu Airport, saida jirgin su yatashi sannan suka dawo gida.


Da daddare suka sauka agida, gaba dayansu dakin Mawahib suka wuce suka gabatar da sallah sannan Mawahib tacire kayan jikinta tafara gyaran gidan, ganin yaran basa kuka hakan yasa shima Captain yazage sukai aikin tare, sai wajan qarfe tara suka gama aikin komai, kayan Yara ma suka adanasu inda yadace,batayi girki ba sai fita yayi yanemo musu abinci, sunacin abincin yaran suna gefen su kwance akan kujera, bayan sungama cin abincin tagyara wajan sannan tadawo falon, tun kafin ta zauna Captain Aryan yabata hannunsa, babu musu tasaka hannunta cikin nasa, yajata jikinsa tazauna akan cinyarsa, yayinda tadora kanta akan qirjinsa tayi luf.

Sunkuyawa yayi, yayi kissing dogon gashinta, sannan yasaka hannunsa ya sarqe musu hannun cikin na juna yace"Honey kode muyiwa Mamy magana asamo mana wadda zata dinga tayaki raino?"

Cikin sauri tadago kanta ta kalleshi tace"me raino kuma? haka kawai daga zuwa rainon yara takoma rainon mijina?"

Cikin sauri Captain Aryan yayi dariya yace"waye yace miki akwai wacce zataci gaba da raino na bayan ke?,Momy da Mamy sungama nasu, har abada kece zakici gaba da raino na nida yarana,Ina tausayin aikin dakike ne,kinashan wahala Honey..."

Kanta ta girgiza takama fuskarsa ta riqe tace"zanci gaba da kula daku har abada,bana fatan wata daban tashigo cikin rayuwar mu harta zama silar Samun sa6anina da mijina, Allah n daya bani su yasan zan kula dasune shiyasa,karka manta ubangiji baya jarabtar bawa da abinda bazai iyaba"

Kansa ya daga mata alamun gamsuwa da maganar tata,ahankali takoma cikin jikinsa ta kwantar da kanta akan qirjinsa, hannunsa yasaka yafara shafa dogon gashinta, yadaga kansa ya kalli yaransu da Mawahib tasaka musu kan fida a bakinsu sai tsotsa suke, dukansu idonsu biyu.

Mawahib tace"Baby da tuni nasa Mamy tamin allurar planning fa"

Cikin sauri ya kalleta yace"saboda me? meyasa?"

Dagowa tayi ta kalleshi tace"saboda munyi dakai mundena haihuwa"

Idonsa ya lumshe sannan yabude yace"yanzu de tayi miki kokuma bata miki ba?"

Kai tsaye tace"batamin ba"

Wata irin ajiyar zuciya ya sauke sannan ya rungume ta yace"bazamu yi planning ba, insha Allah zanyi bakin qoqari na Inga nayi abinda yadace baki samu ciki yanzu ba"

Ajiyar zuciya tasauke tasake shige wa jikinsa, ahankali yafara shafa jikinta yana shaqar qamshin jikinta, cikin wata irin murya yace"Honey yarannan basa kuka yanzu,please inyi?"

Babu musu tadaga masa kanta, anan falon suka fara sha'anin su gaba dayansu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login