Showing 3001 words to 6000 words out of 110331 words
maciji gobe kunama,idan d'aya yana kuka tad'aukeshi tana lallashinsa shima dayan saiya fara kuka,tarasa yanda zatayi ta lallashe su duka su biyun saboda haka saita ajiye d'aya idan d'ayan yayi shiru saita lallashi d'ayan,to duk ranar datayi hakan abincin gidan baya ciyuwa,haka zata dinga sakawa abinci wuta qarshe saide ayi asarar sa,data gane saitake had'asu duka su biyun take lallashin su,d'aya abaya,daya a hannu, daga lokacin bata sake ganin kunama ba,sai lokacin dasuke rarrafe idan sukai ta'adi tad'an dakasu alamun abinda sukai ba daidai bane,tana barin wajan taga wata baqar kunama,sai wata aminiyarta tabata shawara akar6o musu abincin maqota azuba musu akan murfin tukunya bazata sake ganin komai ba,haka akayi kuwa taje maqota takar6o abinci, tadauko murfin tukunya zata zuba musu Alqali yace karta fara, wannan duk canfi ne na mutane, Allah ne kawai yake kawo kunama amma ba yayansa ba,duk surutun mutane ne.
a hankali rayuwa taci gaba da tafiya 'yanbiyu suka fara tafiya har suna fita kofar gida wasa,ba'a Isa adakesu ba yanzu Hajiya kilishi zata sa6a mayafi koda sanin Alqali ko babu saninsa,zataje har gidan yaron daya dukar mata 'yanbiyu tarama musu, sannan takamo 'ya'yanta sudawo gida, wannan halaiyar kwata kwata Alqali bayajin dadinta.
Amma hajiya kilishi inde akan yaran nan ne, to zaka Iya Jin kanta dakowa, kasancewarta yar sarauta idan aka taba su Ashraf,mantawa take ita yar sarauta ce taje ayi wacce za'a yi,kokadan batason abinda zai ta6a mata lafiyar su,lokacin da aka haifeta, a lokacin a kayiwa mahaifinta sarauta, shiyasa mahaifinta ya Sanya mata suna KILISHI.
tashin datayi a gidan sarauta yasa take wa kowa kallon raini da Kuma nuna Isa da taqama da izza,kana ganin yanda take gudanar da al'amuranta zakasan cewa jinin sarauta yana yawo a jikinta,ahakan ma saboda Alqali a tsaye yake agidansa, shiyasa take rissinawa.
Bayan Alqali Ibrahim Sai qaninsa na biyu Alhaji KHALEED,adede wannan lokacin yayi aure, yaso yazauna agidansa shi kadai amma Alqali yace babu inda zaije, ya zauna a gidan duk suyi zamansu tare babu wanda zaibar cikin gida, Alhaji KHALEED ya auri Mama Sadiya mace mai kawaici da kawar dakai akan komai, kasancewarta mace mai tsoron fitina yasa zamanta da kilishi ya d'ore,bata Isa tayi komai ba saida iznin Kilishi, komai zatayi saita tambayeta,hakan yasa kilishi take qarajinta asama,kanta yana sake kumbura tana jinta eh lalle ita d'innan fa yar sarauta ce.
Alhaji Khaleed baifi wata shida da aure ba, Alhaji ISAH shima yataso da batun nasa auren,wato d'an qaramin su, babu abinda yayi na aure komai Alqali da Alhaji Khaleed ne sukai masa kasancewar sa shine qarami a cikinsu,kuma sunaji dashi tun bayan rasuwar iyayensu,to duk abinda Isah yace yana so suma shi suke so, tun yana yaro suka shagwa6a shi abinda yakeso shi suke masa,alokacin Maryam, wato Mamy tagama degree dinta nafarko fannin Nursing,yar asalin garin maiduguri, ganin wahalar datasha a karatun ta yasa ta fad'awa Alhaji Isah cewa itafa bayan auren nan zatayi aiki, bazata bar karatun ta yatafi ahakaba,tanaso tabawa yan'uwanta mata gudunmawa ta fannin karatun ta,Alhaji Isah yasamu yayunsa su Alqali yafada musu qudurin Maryam, Nan take Alqali yace ai babu komai,aikin nata ai 6angaren lafiya ne,inde har tana son d'an'uwan nasu to babu matsala tazo tayi aikinta.
Wannan mataki da Alqali ya dauka yayi bala'in qonawa kilishi rai, tayaya suna zaune agida,za'a bar yarinya tazo cikinsu tana aikin gwamnati? me suka rasa agidan daza'a zo musu da wani fi'ili na aikin gwamnati? hukuncin Alqali baiyi mata dadi ba, daga nan ne matsalar tafara faruwa tsakanin Mamy da Hajiya Kilishi.
Bayan Maryam, wato Mamy tayi sati buyu a gidan Alqali, a lokacin Alqali ya tarasu duka su ukun yayi musu maganar girki, tunda harkarsuce tacikin gida Yaya suke ganin zasu tsara girkin?
Nan take Mamy tace tunda tana aiki, tana ganin kawai kowa yayi nasa girkin,ba zai iyu ace saita dawo daga wajan aiki sannan zata dafa musu abinci ba, lokaci daya Alqali yace hakan bazai iyu ba, shida qannansa qwaya biyu rak a duniya bazai iyu su raba girki ba,hakan yana nufin kenan dan autan su Alhaji Isah haka zata dinga barinsa da yunwa harsai ta dawo aiki ne zata dinga dafa masa abinci, a lokacin Mamy saita nuna masa cewa inde cikinsu ne daga ita Sai mijin ta Alhaji Isah,bazata bar mijin ta da yunwa ba, amma Alqali yace Bai yarda da wannan batu nataba,dole zasu hade girkin su, sai Mamy tace to tunda ita tana fita aiki, tana neman Alfarmar su Hajiya kilishi da Mama sadiya abar mata Iya weekend su sai suyi sauran ranakun, nan take Hajiya kilishi ta watsawa Mamy harara tace bazai iyu ba, a dinga yi kwana bibbiyu, babu wani weekend daza'a barmata,Alqali baiji dadin furucin kilishi ba, amatsayinta na babba a cikinsu kamata yayi ace taja matan qannan nasa a jikinta, su zama qawayenta kuma qannanta, koba komai matar autan nasu alfarma tanema akan su bar mata weekend din,kuma babu wanda yawuce yanemi alfarma, to har zai dauki mataki saiya fasa ganin harkar suce ta mata, daga haka taron ya tashi.
Ko wata uku ba'a yi ba,Hajiya kilishi taga Mamy bata musu girki akan lokaci, saita dawo daga wajan aikinta sannan ne zata fara shirin dora musu abinci, sauqinsu daya idan aikin yamma takeyi, to shine kafin tatafi take musu girkin,kuma Mamy Bata girkin gargajiya,saboda tana aiki da kudin ta take kashewa tayi girki mai rai da lafiya,wanda duk wanda yaci, saiya so ranar girkin ta yasake zagayo wa, to daga nan ne Kilishi tayiwa Alqali magana yakamata asake zama akan batun girkin nan, Maryam bata musu abinci akan lokaci idan aikin safe ne da'ita saita taso wajan karfe uku na aana sannan za'a fara shirin dora musu abinci,tosu yanzu sun yafe gara ta dinga yi da weekend din kawai,(😂)
Alqali yayi murmushi bai tanka ba,tun farko abinda yahango musu kenan, shiyasa yaso subata weekend din, tunda Alfarma ta nema,sannan itace qarama a cikinsu kuma matar dan autansu, kamata yayi su ja yarinyar a jikinsu musanman ma ita Hajiya kilishi tunda itace babba, amma mugunta ta rufe mata ido, takasa gane hakan tun farko.
Haka Alqali yayi mursisi yaqi saka baki akan maganar girkin.
Mamy tanada masifar haquri,zaiyi wahala kaga 6acin ranta,tana zaune da kowa lafiya a cikinsu Kuma da zuciya daya, tanajin dadin yanda Mama Sadiya take janta ajiki,nan da nan sai suka saba, suka zama kamar qawaye,duk lokacin da Hajiya kilishi ta 6atawa mamy rai, Mama sadiya ce take bata haquri, kuma Mamy bata ta6a fadawa mijinta ba, saide tabar abun aranta.
Tunda tazo gidan ta lura kwata kwata Hajiya kilishi bataso su Ashraf suzo wajanta,koda wasa taga sunyi hanyar part din Mamy toda gudu zataje ta janye su, abun baya yiwa Mamy dadi, tana bala'in qaunar yaran, amma babu damar daukar su saide tadinga leqensu daga nesa.
Hajiya kilishi ganin Alqali yaqi kula maganar ta dangane da girki, hakan yasa wata rana Mamy tana girki Hajiya kilishi taje ta sameta a kitchen din tayi mata tatas,Mamy ko uffan batace mataba, ganin Mamy taqi tanka mata yasa tafara zaginta, tayi mata zagi nacin mutunci,hartana fada mata yar gidan talakawa wadda take aiki saboda talaucin iyayenta, juya....wacce bata haihuwa tunda tazo gidan ko 6ari bata ta6a yiba(😥)
Mamy bata ramaba saide kuka da takeyi duk da hakan tana bata haquri,ashe duk abinda ake Alqali yana ganinsu yazo wucewa,cikin 6acin rai yayiwa kilishi magana cikin tsawa,itama 6acin rai ya rufe mata ido tarama,nan take babu 6ata lokaci Alqali yabawa Hajiya kilishi jan Kati, yayi mata saki daya(🙆🏻♀️)
Sannan agabanta yaje yadauko Ashraf da Aryan yace yabawa Mamy su halak malak(😳)
A wannan lokaci kilishi hauka ne kawai batayi ba,taji tsanar Mamy tasake nunkuwa aranta,tanaji tana gani haka tabar 'yanbiyunta a hannun matar data tsana tafice tabar gidan Alqali.
A lokacin Mamy tajasu ajiki sosai kamar 'ya'yanta,musanman yanda takeson haihuwa amma gashi Allah bai bataba, idan taje asbiti taga mata sun haihu tadinga kula da yaran kenan bata kyamatarsu, hakan ne yaja mata farin jini a wajan aikinta,dama hajiya kilishi ce tayi mata iyaka da 'yanbiyun, amma tana sonsu sosai, Alqali yana danqa mata su kuwa tabude bakin aljihu tadinga yimusu siyaiya, shikuma yaro inde za'a bashi, musanman kayan chocolate to yanzu zaka siyeshi, tun basa sakin jiki da'ita har suka dawo suka saba da'ita,sune suka fara kiranta da MAMY, tun suna yara Mamy ta lura Aryan baya son surutu,yafison ya zauna yanata game da wayarta,koda tajashi da zance irin dan surutun nan na yara saide taga yace mata eh kokuma a a,saide in yanason abu zaice Ma-my inason sweet, kokuma Ma-my ruwa, kai tsaye de yace Mamy,ba zakaji yafadi hakaba, wannan saide Ashraf, amma shide Aryan a rarrabe yake kiran Sunanta.
Tayi amfani da hikima sosai wajan shawo kan yaran,haka kawai tana dawowa daga wajan aiki zata cire uniform dinta tasa qananun kaya tadinga goyasu sunata wasa saide Alqali yajiyo su sunata qyalqyala dariya,da yamma haka zata musu wanka ta shirya su tsaf suyi kyau, sufuta wajan wasan yara takai su suyi wasa son ransu, sannan su dawo gida,harta kai takawo idan zata fita aiki ma dasu take tafiya, kowa yasan su a wajan aikinta,qawayenta na wajan aiki har chocolate suke kawo musu, wasu Kuma kayan wasa suke kawo musu,mutane dayawa suna tunanin ma yaranta ne, saide su din farare ne sosai kuma identical twins kwata kwata baka banbance su,amma ita kam sarai tana ganesu, kai tsaye zata nuna Ashraf tace wannan ne babba, shikuma Aryan rashin surutun sanema yakesa nan da nan aganeshi, amma kuma idan shida Ashraf ne har mamakin yanda yake surutu take,inde dagashi sai dan'uwan ne yanzu zakaji yanata masa magana, daga qarshe a kaure da fad'a, saide fadan nasu baya zuwa ko'ina zakaga sun shirya, Mamy tasan halin kowa a cikinsu, Ashraf gaba daya halin Alqali yad'auko, babu ruwansa, inde yazo waje sai kasan yazo,haka idan tahada musu tea dasafe, gashi de tea din bawani zafin kirki gareshi ba,haka Ashraf zai dauka yasha abunsa, yayinda Aryan yadebo halin Hajiya Kilishi gaba d'aya,tun yana qarami Mamy ta fahimci yanada son girma, baya son raini, gashi de shine qarami amma Ashraf bai Isa yace ya girmeshi ba,kuma kokadan bayason zafi,shide kawai sanyi, idan tahada ruwan dumi zata musu wanka nan da nan zai fara kuka shi bazata masa da ruwan dumi ba saide na sanyi, ita kuma tana tsoron kar ruwan sanyin yayi masa illah, haka zata riqeshi yana kuka yana cewa ruwan da zafi, ahaka suke wankan kullum, idan Ashraf yaga Aryan din yana kukan ruwan zafin saiya saka hannunsa acikin ruwan, ya kalli Aryan din yace kaji ruwanfa babu zafi(😂)
Darana kuwa taci karo dawata baqar kunama a qofar dakinta,cikin tsoro tajuyo aguje,suma suka bita da gudu suna dariya,mamaki ya kamata,tadauko abu zata kashe Ashraf yace shine zai kashe,yasaka hannu ya dauki kunamar shima Aryan yace saiya bashi,shikuma Ashraf yahana,lokaci daya kunama tahada su fada, ganin ana qoqarin fada akan kunama kuma gatanan tana ganinta qiri qiri a hannun Ashraf lokaci daya Mamy ta suma a tsaye, batasan lokacin data saki qaraba,tariga tabayar kunamar zata cutar dasu.
ganin tana kuka yasa suka dawo wajanta suma suna kuka,saida tagama kukan tafara lallashin su anan taga babu kunamar a hannun su babu dalilin ta,haka tayi shiru da bakinta bata tambayesu Ina take ba.
Haka Mamy tadinga kula dasu, yanda take kaffa-kaffa dasu yasa su kayi mugun sabo da Mamy, yanda suke liqe mata saika rantse itace ta haife su,ko dare yayi bazasu kwanta ba saide a jikinta, haka zata tofesu da Addu'ah har suyi bacci, saide cikin dare ta lallaba ta gudu wajan Alhaji Isah,suyi abinda zasuyi (🙈)
kafin ace sun farka sun fahimci bata wajan su zata dawo cikinsu suci gaba da baccin, kuma hakan kokadan baya damun Alhaji Isah saboda qarancin kulawar dayake samu a wajanta, saima dadi da yakeji yanda take riqe 'ya'yan dan'uwansa kamar itace ta haife su.
Sun kwashi watanni a wajan Mamy,yau suyi fad'a tadinga rabiya, gobe azauna kalau ahaka har sukayi mugun sabo da'ita, komai Mamy,bakajin komai a bakin su sai maganar Mamy, ta rainesu yanda ya kamata, raino wanda zaiyi wahala yaro ya manta da uwar rainon sa.
Ganin Alqali yayi mursisi baije bikon Hajiya kilishi ba, hakan yasa tadinga yiwa yan gidansu magana har sukuma suka yiwa Alhaji Khaleed da Alhaji Isah magana, suka basu haquri akan laifin kilishi suka roqesu Alfarmar suyiwa yayansu Alqali magana akan dawowar kilishi dakinta,domin sude bazasu Iya tunkarar sa da maganar ba, domin kuwa Alqali akwai kwarjini,hakan akayi kuwa, Alhaji Isa da Alhaji Khaleed sune suka shige gaba, aka maida auren Hajiya kilishi da Alqali Ibrahim,suka sake bawa yayan nasu haquri akan katsalandan din dasuka masa, badan Alqali yaso ba, haka yayi haquri kilishi ta dawo dakinta, bayan alqawari data dauka masa cewa hakan bazata sake faruwa ba.
Mamy kuwa tayi tunanin ganin hajiya Kilishi tadawo zaisa su Ashraf su koma wajanta, saitaga yara sunyi mursisi sunqi komawa wajan Hajiya kilishi,irin murnar nan ma taganin uwa sude ba suyi ba, saida Alhaji Isah yasata tahada musu kayansu sannan yace tarakasu wajan mahaifiyar su, a lokacin data gama hada musu kayan harda kukanta, a lokacin yarinta tasa basu fahimci kukan me takeba,Ashraf ne yafara matsowa yana goge mata hawayen,amma shikam Aryan da bai Iya lallashi ba shima saiya kwanta a cinyarta yafara kuka (😂)
Haka tarakasu wajan Hajiya kilishi, tayi mata sannu da zuwa ta amsa mata da qyar, itade Mamy ahaka ta futo tabarsu tareda mahaifiyar su.
Tunda Hajiya kilishi tadawo taji suna kiran Maryam da Mamy,babu 6ata lokaci tahanasu fadar sunan, saide suce Anty, sukuma basu saba da Anty ba, da Mamy suka saba, dan dolansu babu yanda suka Iya shine suke kiranta da Anty Mamy,maimakon suce Anty kadai,sai suka hada mata duka biyun suke kiranta da Anty Mamy
Bayan wasu shekaru suna kammala primary school dinsu Mama Sadiya ta haifi yarta mace, aka sanya mata sunan Mahaifiyar su Alqali, suna kiranta da NABIHA, adede lokacin Alqali yafitar dasu qasar waje karatu,saida karatun su yayi nisa sosai sannan Allah yabawa Mamy ciki,ta haifi yarta mace mai tsananin kyau kamar balarabiya,mahaifinta ya sanya mata suna RUQAYYA,Mamy kuma take kiranta da MAWAHIB.
ma'anah (MAI YAWAN KYAUTA).
Mawahib tun tana qaramarta Allah yayi mata diri,tanada jiki mai daukan hankalin samari, tanada sanyin hali kamar Mamy, kwata kwata batada hayaniya,Allah yayi mata baiwar hips kamar ita ta sakawa kanta,saide batada cikar qirji, boobs dinta ba manya bane kuma ba qananu bane, 'yan madedetane hakan ne yasa suke a tsaye qyam....
Mamy da Abbanta sunaji da'ita,sosai Mamy take siyo mata qananun kaya daga nashan is'ka harna bacci, haka zata saka kayan ta tayi uzurinta Iya part dinsu babu wanda yake mata magana, haka 6angaren kayan kwalliya ma ba'a barta abaya ba,idan Mawahib ta dauki kwalliya babu musu zakace mata yarinyar Momy da Daddy ce,saide bahaka bane,kawai Mamyntace ta tsaya mata take shigar ta yanda taga dama, tunda samarin gidan bawani zama suke ba.
Aqasar waje su Ashraf sukai secondary school dinsu,suka dora da jami'ah,bayan sungama jami'ah suka nunawa Alqali cewa suna so suzo gida, yace su dakata suyi masters tukunnah,duk tsawon wannan shekarun Mamy tana nan a ransu, tun basa fahimtar mahaifiyar su Hajiya kilishi bata son Mamy, har suka dawo suka gane,idan suka tambaye ta awaya Ina Mamy nan da nan Hajiya kilishi zatayi kicin kicin darai ta nuna musu batason mu'amularsu da wannan matar.
Haka sukai haquri basuzo gidaba saida suka kammala karatun su kamar yanda Alqali yakeso, sannan suka dawo gida, anan sukaga an sauya tsarin gidan, ansake masa fasali, anyi masa get biyu,gida yakoma gidan zamani ankashe masa dukiya, a wannan lokacin Alqali yayi ritaya,yana zaune agida yana hutawa,duk wani nauyin kula da gidan yakoma kan Alhaji Khaleed mahaifin Nabiha, saikuma Alhaji Isah mijin Mamy, gida de ya sauya, saide halin Yan gidan dabai canja ba(😂),tunda suka dawo Ashraf yaga Nabiha da Mawahib shikkenan yake jansu a jikinsa, musanman Mawahib din Mamy, yana bawa Mawahib kulawa yanda ya kamata, jinta yake aransa kamar me,duk abinda takeso nan da nan zakaga yaje yasiyo mata,amma kwata kwata baya bawa Nabiha wannan damar, tsakanin sa da'ita saide gaisuwa amma fuska asake yake amsawa, shikuwa gogan ko a jikinsa, daga Mawahib din,har Nabihan, gaba dayansu baya shiga sabgarsu, kwata kwata baya son raini, suma su Mawahib da sukasan halinsa koda wasa basa shiga harkar sa.
Bayan sunyi bautar qasa Ashraf yasamu aiki a NNPC dake Rivers state,shikuma Aryan dama burinsa yasamu aikin soja,kuma yasamu, har yakai matakin CAPTAIN,shiyasa su Mawahib suke kiransa da YAYA CAPTAIN, yana aikinsa a Abuja,bai cika zuwa gida sosai ba, Ashraf ya fishi zuwa gida.
Kamarsu daya da Ashraf sak,zaiyi wahala ka banbance su idan suka saka komai iri daya,suna fad'a ajunansu,saide fad'an nasu babu inda yake zuwa nan da nan zasu shirya, idan Ashraf yayi budurwa shima Aryan yana ganinta zaiji yana sonta, daga dawowar su daga qasar waje zuwa yanzu dasuke aiki Ashraf yayi 'yanmata dayawa, amma wai irin ya nunawa dan'uwansa sabuwar budurwar da yayi, sai shima Aryan din yace wallahi sonta yake (😲)
Babu yanda Ashraf zaiyi saide ya haqura da yarinyar tunda bazai iyu su auri mace daya ba, sunyi haka yakai sau biyar,kuma shima Ashraf din dan masifa kamar anyi masa dole muddin yasamu budurwa saiya nunawa Aryan ita,shikuma yana ganinta kai tsaye zai fada masa wallahi Shima yana sonta,haka Ashraf din zaiyi haquri yabar masa yarinyar kokuma su barta duka su biyun,shikuma captain Aryan baya kula yanmata bare ayi tunanin zai samo wata, yana zaune saide in dan'uwan yasamu, yace shifa duk duniya shima wannan yarinya yakeso,haka zasu haqura da yarinyar gaba dayansu.
Ashraf yanason ruwan zafi,halinsa sak irinna Alqali, shiyasa koda yaushe yake ta'ammali da tea,kuma babu ruwansa da zafin tea dinnan haka zaisha abunsa, amma captain Aryan bahaka bane, kokadan baya hada hanya da ruwan zafi, yafison ruwan sanyi, duk sanyin da ake agari bazaiyi wanka da ruwan zafi ba, dana sanyi zaiyi, wannan dabi'arsu ce tun suna Yara.
Har zuwa wannan lokacin Hajiya kilishi bataso su ra6i Mamy,amma har yanzu suna sonta,kuma suna mu'amula da'ita dan dole Hajiya kilishi ta haqura tabarsu.
Fatan Alqali da Hajiya kilishi shine su samu mata suyi aure, Hajiya kilishi ta dauki buri ta dorawa yanbiyunta kawai so take su samo mata yanmata nagani nafada na kece raini suyi aure irin auren 'ya'yan Masu dashi dakuma 'ya'yan masu mulki, amma har yanzu