Showing 84001 words to 87000 words out of 110331 words

Chapter 29 - MAWAHIB COMPLT HAUSA NOVEL

13 Sep 2024

19691

abokin aikinsa awajan yaqin....ina tsoro kar'akashe shi Shima "
tafadi hakan hawaye yana zuba daga idonta .

Mawahib tanajin haka tasake fashewa da kuka tadora kanta akan qwiwoyinta,sai yanzu ne take nadamar abubuwan datake masa abaya,sai yanzu ne take dana sanin meyasa takasa nuna masa soyaiya?

Fita sukai daga dakin Mamy da Mama Sadiya suka ruqo Hajiya kilishi datake ji kamar bazata Iya taka qafafunta ba,compound suka hadu da mazan gidan kowannensu yadawo daga wajan aiki,cikin mamaki Alhaji khaleed yake cewa"meyake faruwa ne?"

Mama Sadiya ta kalleshi "Alhaji yanzu Mawahib take cemana wai yaqi aka tura Captain tsawon wannan lokacin,gashi tunda yatafi Alhaji kana gani bamu ta6a Samun wayarsa ba"

Alhaji Isa dayake tsaye da brief case a hannunsa yace"yaqi? Hasbunallahu wa ni'imal wakeel, amma Captain yayi shiru yakasa fada mana? bari nakira Yaya"

Yadauki wayarsa yakira Alqali,yace"Yaya kana inane?"
Alqali yace"Ina tareda Ashraf zai shirya yaje Abuja"

Alhaji Isah yace"basai yajeba Yaya,kudawo gida akwai matsala"

Alqali yanajin haka suka juyo zuwa gida, afalon Hajiya kilishi suka tararda duka mutanan gidan banda Mawahib.

Ashraf yanemi waje ya zauna, Alqali ya kallesu yace"meyake faruwa? yanaga ana gogewa kilishi gumi?"

Alhaji khaleed tace"yanzu muke samun labari awajansu wai Mawahib tace musu antura Captain wajan yaqi"

Cikin sauri Ashraf yadago kansa ya kalli surukin nasa, Yaya akai Mawahib tasani?
tayi waya dashi ne?
Tayaya akai maganar tafita?

Alqali yanemi waje ya zauna yace"to akwai matsala kenan,to aini yanzu nake shirin tura Ashraf Abuja yaje yagano ko lafiya,toda ace yajema dada wannan mummunan labarin zai dawo kenan"

Alhaji Isah yace"idan munje masallaci anjima sai muyi magana da liman asaka shi cikin Addu'ah"

Mama Sadiya tace"Abban Mawahib nida cewa nayi mezai hana ko sauka ce ayi?"

Ashraf da kansa ke qasa yadago kansa ya kalleta yace"Mama nasa anayi masa sauka duk sati tun lokacin danaga yayi kwana biyar bai kirani ba"

Alqali yace"yafada maka maganar yaqin ne?"

Kansa ya sunkuyar yace"muna tare dashi aka masa waya lalle lalle yatafi Abuja dasafe, akwai abokin aikinsa dayake jagorantar sauran Sojojin ankashe shi,shine sukace kada ya6ata lokaci yaje yamaye gurbin wancen,naso nasanar daku tun ranar daya tafi, to amma yace nayi masa alqawari kada nafada muku saboda kada hankalinku yatashi"

Hajiya kilishi tanajin inda aka tura Aryan wani hawayen yazubo mata, shikkenan shima qila kashe shi zasuyi.

Alqali ya kalli Ashraf yayi shiru,sai yanzu yagane dalilin dayasa jikinsa yayi sanyi lokacin da Aryan din yatafi, ashe su akwai abinda suka 6oye.

Yajuya ya kalli Mamy "waye yafada mata cewa antura shi yaqi?"

Mamy tace"Yaya wallahi bansani ba,ihun ta muka jiyo daga daki muna zuwa saitake fada mana, da alama awaya taji labarin"

Girgiza kansa yayi yace"insha Allahu zamuyi abinda yadace,ubangiji Allah yakare shi aduk inda yake"

Gaba dayansu suka amsa da "Amin"


Tun daga ranar Alqali da sauran qannansa suka yiwa limaman unguwar magana idan aka idar da kamsa salawat ake saka shi acikin kowacce Addu'ah.
Duk gidan kowa idonsa yanakan wayarsa ko zaiga kiran Captain kokuma saqon sa,tun suna zuba idon ganin wayarsa har tsoro yagama wanzuwa a zukatansu, ganin sati na hudu kenan ya shude babu labarin Captain, babu dalilinsa.

Mawahib duk ta rame sai fari kawai,hatta hips dinta saida suka ragu, haka breast dinta,idan tasaka riga da siket wanda abaya kamata yake, yanzu zuruf siket yake wucewa.
Mamy tana lura da'ita amma babu yanda zatayi da'ita kullum cikin haquri take bata,dakuma lallashi.

Idan ta tuna da maganganun daya fada mata adaren dasukai first night dinsu saide taji hawaye yazubo mata.
Acikin sati na biyar ne cikin dare tana bacci tafarka takasa komawa baccin, ahankali tatashi tafuto daga dakin ko tsoro bataji kai tsaye tawuce dakinsu Captain,dakin yana rufe tun ranar da Abba ya dauketa yakai ta part din Hajiya kilishi,tsaf dakin yake a gyare ,rigar jikinta tacire tabude kayansa ta dauki jallabiyarsa tasaka, Sanna ta kwanta akan gadon tareda rungume fillo tanajin kamar Yaya Captain ne,ta dade tana juyi tana tuno irin yanda ya sangartata da daddadar soyayyarsa, ahaka wani bacci me dadi ya dauketa.

Da asuba Mamy taga bata nan, taduba toilet dinta taga bata ciki,cikin sauri tafuto tazo dakinsu Captain anan taga Mawahib tana bacci cikin kwanciyar hankali jikinta Sanye da kayan Captain,murmushi tayi tarufe mata dakin ba tareda ta tashetaba saboda rashin isasshen bacci datake fama dashi.


Tun daga ranar tadena kwana a dakinta tadawo kwana dakinsu Captain,tun mutanan gidan basu ganeba har suka gane,wani lokacin ma da Hajiya kilishi da Mamy da Mama Sadiya idan suna compound din gidan a zaune a kujerun roba haka zatazo ta wuce su tashige dakin tayi kwanciyar ta,Hajiya kilishi saide tayi murmushi,tasan shima rasa kunyar dayana nan haka zai qetare su yashige dakin tunda harya Iya kasa haquri da jarabarsa ya lalla6a ya danne yarinya acikin gidansu.(🙊)


Haly JASHERU venture's,munada kayayyaki masu kyau da inganchi ba algus da ha'inci, kayanmu daga Ethiopian ne, prdct dinmu muna Ethiopian magic hair oil, anti dandruff shampoo serum, bdy cream, hand cream, magungunan chuttuka da na mata masu inganchi da qara lfy ajikin dan
adam ga number kmr hk 07046665338 ko 07061664264 munada distributor ako Ina afadin kasarnan da ketare muna koya harkokin kasuwnchinmu ga masu bukata akan 5000 kacal

sannan munada tsuntsaye na kasashen waje tattabaru game bukata ko koya akwai riba kwarai aharkar mebuqata yasiya koya koya seyanemeni a number na kamar haka 07046665338 ko 07061664264, ku antayo ayi tafiyar daku,yar'uwa kikoyi sana'ah akan wannan farashi me sauqi kema ki kafa kanki💃🏼

******

yauda tatashi da asuba tayi sallah adakin, komawa bacci tayi, bata tashi ba sai qarfe tara na safe,tashiga toilet din dakin tagyara shi,sannan tadawo dakin shima tafara share shi,wata takarda ta sharo aqasa gado ta tsaya da sharar ta duba taga kamar takardar Yaya Captain ce, tadora takardar akan gado, sannan taci gaba da shara saida tagama ta kunna turaren wuta adakin tajuya zata fita,ta hango wannan takardar data bari akan gado, tadawo ta dauketa tabude bedside drower zata sakata aciki,bindiga tagani aciki,ahankali ta tsugunna ta dauki bindigar tafara jujjuyata tana gani, bata ta6a riqe bindiga a hannunta ba sai yau, saide tahangeta daga nesa-nesa awajan Yaya Captain.

Ajiye bindigar tayi anan taga wata farar takarda da rubutu ajiki takardar tana bude ba'a ninke taba.
Zama tayi awajan tadauka tafara karantawa, tun lokacin da idonta yakai inda taga yasa RUQAYYA gabanta yafara faduwa.
Cikin sauri tafara karanta abinda ya rubuta "RUQAYYA kiyi haquri,antura ni yaqi zan maye gurbin Captain shu'aib,kiyi min Addu'ah,idan Allah yasa nadawo shikkenan, idan ban dawo ba kici gaba dayimin Addu'ah,naso ace nabarki har sai nadawo zuwa lokacin idan Addu'ah ta takar6u may be kinfara sona,to amma bazan iyaba...,inason koda sau daya ne nima na kasance da matata naji abinda sauran maza masu aure sukeji,ayau zan kar6i haqqina a wajanki,nadade inashan magungunan da likita yabani saboda matsalar rashin haihuwa ta, idan Allah yasa kafin nadawo kinsamu ciki idan namiji kika haifa asaka masa sunan ASHRAF,idan mace kika haifa asaka mata sunanki, saboda keda Ashraf kune mutum biyu danake so duk duniya sama da kowa bayan Momy na, kiyafemin..."

Yana kawowa nan rubutun yaqare,zuwa wannan lokacin da Mawahib take karanta wannan takardar, tuni takarda ta jiqe da hawaye.


Dama magungunan dataga yanasha na matsalar sane?
takardar ta cukwikwiye tarufe idonta da'ita tana wani irin kuka mecin rai,sosai take kuka kamar anyi mata albishir da mutuwa.
Mamy da taji shiru Mawahib batazo tayi breakfast ba tafuto zuwa dakin cikin damuwa,Hajiya kilishi data futo daga kitchen taga Mamy tana sauri zata wuce tace"maryam lafiya kuwa?"

Mamy ta kalleta"Yaya Mawahib ce naji shiru bata futo ba,har zan fita aiki banga tazo tayi breakfast ba,shine zan duba"


Cikin damuwa itama tace"muje,yarinyar nanfa saimun tashi tsaye akanta"

Suna zuwa dakin suka sameta tana rusa kuka,idanunta sunyi jajir,cikin sauri suka qarasa Hajiya kilishi ta zauna abakin gadon ita Kuma Mamy ta tsugunna taja Mawahib jikinta tana bubbuga bayanta alamun lallashi, cikin rawar murya kamar zata fashe da kuka itama Mamyn tace"kiyi haquri mana,Mawahib Addu'ah zaki masa ai"

Cikin kuka ta nunawa Mamy takardar tace"Mamy wasiyya ya barmin fa....,yanzu Ina shara nagani,dama yasan tafiya zaiyi yabarni bazai dawo ba meyasa bazai tafi dani ba?"
ta qarasa maganar idonta yana tsiyayar da hawaye.
Hawaye yazubo daga idon Mamy takasa cemata komai tadaiyi kokarin rungume ta ajikinta.
Hajiya kilishi ta dauki takardar ta karanta lokaci daya itama tafara kuka,tasaka gefen zaninta tana share hawayen,cikin kuka tace"kimasa Addu'ah Mawahib...."

daga haka takasa cewa komai tafuto daga dakin tana ruskar kuka.
Mamy da Mawahib kuwa sun dade adakin babu mai lallashin wani,sannan Mamy tasamu qwarin gwiwar goge hawayen ta takamo Mawahib din suka futo daga dakin.

Tundaga wannan ranar saiya kasance abincin ma tadaina ci,saide ruwan shayi,idan ta zauna ba zatayi magana ba saide tayi shiru tana tunani,har Mamy tafara tsoro kar cutar damuwa ta kamata.

Da daddare Mamy tahanata zuwa dakin Captain Aryan tadawo da'ita dakinta suna kwana tare,acikin kwanakin dasuke itada Mamy kullum basa bacci sai sun gabatar da nafila cikin dare sunyi addu'o'i sannan Mamy ta kwanta, Mawahib kuwa idonta biyu ras bata jin bacci,shiru take tana tuna irin rayuwar dasuke a Abuja itada Yaya Captain.
Har akira sallar asuba idonta biyu,gari yawaye amma ko gyangyadi batayi, Mamy data lura bata Iya bacci hakan yasa take yimata allurar bacci,shine zata dade tana bacci har asamu qwaqwalwar ta tahuta.

Hakan yasa washegari Mamy taje part din Hajiya kilishi,ta tarar har Alqali ma yana nan, bata 6oye musu komai ba akan matsalar Mawahib tafada musu komai,anan Alqali yace zaisa ayi mata rubutu ko Allahu zaisa tadawo hayyacinta takuma fauwalawa Allah komai, sannan yace Mamy ta matsa mata akan Addu'ah dakuma karatun qur'ani.

Mamy taji dadin maganganun Alqali,koba komai itama Hajiya kilishi asamu tadawo nata hayyacin, tunda daga ita har Mawahib din ansara gwara gwara a cikinsu.


Kwana biyu dayin wannan maganar Mamy tana zaune afalo itada Abba da Mawahib suna ganin labarai, Mawahib da Alqur'ani a hannunta tana karantawa,kwata kwata hankalinta baya kan abinda su Mamy suke gani,tana Sanye cikin hijab, Abba da Mamy kuma suna ganin Labaran, saide kowa yayi shiru da alama suma kawai kallon sukeyi gudun karsuyi tunani.

Ashraf da Hajiya kilishi da Alqali suka shigo falon,Mamy tayi musu sannu da zuwa, Mawahib ta Kalle su tace"ina kwananku?"

Alqali ya amsa mata cikin murmushi, zama sukai Alqali ya kalli Abba yabashi wata gora cikeda ruwan Addu'ah na rubutu yace"isah wannan na Ruqayya ne,ta dinga sha safe da yamma"

Cikin girmamawa Abba ya kar6a yace"to Yaya insha Allahu za'a bata,ai jikin nata naga da sauqi ma, tunda gatanan tadena zaman daki da'ita muke zama afalo saboda kada ta yawaita tunani..."

Kafin Alqali yayi magana gidan talavision din dasuke watso labari suka sako photunan wasu sojoji guda uku,cikon na hudun kuwa Yaya Captain ne,Mawahib da idonta yakai kan Sojojin nan tana ganin fuskar Yaya Captain ta ajiye qur'anin hannunta tazubawa tv ido gabanta yana faduwa,gaba daya suma su Alqali sai suka maida hankalin su kan labaran, inda me bada labarin yake cewa"rundunar Sojojin Nigeria wadda aka tura yaqi domin qwato dubban mutanan da yan ta'adda sukai garkuwa dasu sun samu nasara akan yan ta'addan inda suka qwato dukkan mutanan, sannan suka kashe mafi yawan yan ta'adda bisa jagorancin Captain Aryan I. Alqali,kada mutane su manta ba qaramin yaqi bane wannan, musanman dajin da wannan Yan ta'adda suke ciki,shide wannan daji ya kasance mafi munin daji acikin dajujjukan damuke dasu afadin qasar nan,tsawon wata uku kenan da'aka tura Captain Shu'aibu tareda rundunar sojin Nigeria,inda Allah yayi qarar kwanan sa a wannan daji, daga baya gwamnatin Nigeria tabada umarnin atura wasu Sojojin inda hukumar Sojan qasan Nigaria tatura mutane hudu,daga cikinsu akwai Captain Aryan I. Alqali, wanda muke samun labarin mutuwar sa yanzu haka daga majiya mai qarfi inda yasamu harbi agefen zuciyarsa, har yanzu de hukumar Sojojin Nigeria takafa ta tsare wajan ganin......"

Dif idanun Mawahib ya rufe tadena ganin komai sai duhu,ahankali Hajiya kilishi ta lumshe idonta tafara qoqarin maida qwallar dazata zubo mata,bataso kokadan tayi kuka,wani abu mai tauri yazo ya tsaya mata a maqoshi tana so taja numfashi amma takasa, saide har lokacin tahana kanta zubar da hawaye ko daya.

Ashraf yasaka hannu yagoge hawayen idonsa kansa aqasa ya gagara dagowa bare ya kalli fuskar dan'uwan nasa da'ake nunawa.

Alqali yatashi tsaye ya goge gumin fuskarsa ya kalli Abba da idanunsa sukai jajir yace"isah muje musamu khaleed saimu wuce Abujan"

Cikin sauri Abba yagyada kansa amma yakasa cewa komai saboda yana bude bakinsa kuka zai Iya qwace masa.

Shiru falon yayi bakajin motsin kowa sai kukan Mamy data kasa riqe kukanta ta sunkuya ta dora kanta akan hannun kujera tana kuka kamar ranta zai fita.

Hajiya kilishi data lura Mawahib bata motsi cikin sauri tatashi tafara kiran Sunanta tace"Mawahib!"

Taji shiru, tasaka hannunta duka biyu tafara jijjigata cikin rawar murya wadda take gab da fashewa da kuka tace"Mawahib!!"

tagado ta kalli Alqali da Abba dasuke shirin fita tace"Alhaji kuzo ku duba kar itama mu rasata"






(So Sad 😭)

(matan sojoji Allah yakare muku mazajenku,🤲🏻,Wanda suka rasa mazajensu ubangiji Allah yabasu haqurin rashin su,🤲🏻😭)




Mawahib littafin kudi ne,duk me buqata naira 500 ne kacal ta wannan account din
0164549488
Amina muhammad
GTbank

Kokuma katin MTN ta wannan number 08033300034

idona nahana bacci nacinye lokaci na narubutashi,bazanja Allah ya'isa ba,amma muddin kika karanta baki biyani haqqina ba nabarki keda mahaliccinki faqad👌🏻





Amnah El Yaqoub✍🏻
[7/18, 5:57 AM] AMINA KABIR CAPS: *Page 78*




Abba ne yasunkuya ya tatta6a fuskarta yana kiran sunanta "Ruqayya! Ruqayya bude idonki"

Shirun da yaji ne yasa yata6a qirjinta yaji bugun Zuciyarta yana nan, sannan yace"suma tayi"

Ya kalli Mamy ko zata bata wani taimakon yaga Mamy sai faman kuka take ko kallon Mawahib dinma batayi ba.
Ya kalli Ashraf yace"bamu ruwa Ashraf"

Tashi yayi fuskarsa tana tsiyayar da hawaye yaje fridge yadauko gorar ruwa guda daya yabawa Abba, yakar6a tareda budewa yazuba a hannunsa sannan ya shafa mata dan kadan a fuskarta, amma bata farfado ba.
Hajiya kilishi tace"mutafi asbiti kawai"

Mama Sadiya da Alhaji khaleed ne suka shigo falon, Mama Sadiya sai kuka take tana salati.

Gaba daya itada Mamy sai suka sa duka mutanan falon kuka,amma abun mamaki Hajiya kilishi har yanzu batayi kuka ba,idonta de yana cike tab da qwalla, kuma tana magana kanajin muryarta tana rawa alamun tana dab da fashewa da kuka.

Abba ya kalli Ashraf yace"karomin wani ruwan"

Ashraf yasake bude gorar zai zuba masa ruwan, wayarsa ta dauki qara alamun kira yashigo, cikin sauri yaduba wayar,gabansa ne yayi wata mummunar faduwa a fili yace"Aryan...."

Cikin sauri Mamy tadago kanta ta kalleshi,Mama Sadiya datake goge idonta ta dankwalin kanta itama ta dakata duk suka zuba masa ido,Alqali ya kalli Ashraf daya qame a tsaye yakasa daukar wayar, yatashi yakar6i wayar, yana fadin"ina tunanin mutuwar zasu fada mana"

Yadauki wayar yazauna a kujera sannan yasaka wayar a speaker yace"Assalamu Alaikum"

Daga can 6angaren cikin muryar nan tasa me aji yace"Ash...."

Cikin sauri Alqali yatashi tsaye yace"Aryan...Aryan kana jina? kaine kake magana ko kunnuwana ne?"

Murmushi yayi yace"nine Daddy...."

Lokaci daya fuskar jama'ar falon ta washe,Hajiya kilishi tasaki wata irin ajiyar zuciya,sai alokacin wani irin hawaye yazubo mata.
Mamy tafara goge hawayen idonta tana murmushi,kowa ya matsu abashi wayar, kafin Alqali yayi magana Alhaji khaleed yace"Aryan yanzu mukaji labarin mutuwar ka,kaganmu nan hankalin kowa yatashi iyayenka sai kuka suke"

Cikin mamaki yace"Uncle mutuwa kuma? rumors ne kawai,babu wanda yarasu acikin mu,basu gama tantance labari bane suke yad'ashi"

Alhaji Isah yace"Alhamdulillah Alhamdulillah, Allah abun godiya.... Yanzu kana Ina? yaushe zaka taho? kokuma de mu muzo gaba dayanmu muganka ko hankalin mu zai sake kwanciya?"

Captain Aryan yayi murmushi yace"Uncle yau zan taho gida komin dare insha Allah,yanzu haka muna Abuja shiyasa nasamu damar kiranku,munfuto wajan network"

Abba yace"to Alhamdulillah,ubangiji Allah yakawo ku lafiya Aryan,Allah yatsare ku"

Ya amsa masa da "Amin" sannan yace"Ashraf...."

Alqali yayi sauri yabawa Ashraf wayar,Ashraf dayake goge hawayen idonsa na farinciki ya kar6i wayar yace"Aryan"

Captain yayi dan qaramin murmushi jin Ashraf din kuka yake,danya kwantar masa da hankali yace"Whare is my wife...?"

Ashraf ya goge hawayen idonsa sannan ya kalli Mawahib dahar lokacin take kwance bata farfadoba,yasake goge hawayen idonsa danya kwantar masa da hankali yace" She's sleeping..."

Ajiyar zuciya Captain yasauke me nauyi sannan yace"kakula min da'ita kafin nazo itada Momy, saina qaraso"

Ashraf yace"to Aryan"

Gaba daya falon sai bakin kowa yabude, falo yadauki surutu,Hajiya kilishi tasake goge idonta ta kalli Mamy tace"Maryam tunda kinji labarin dannaki yana raye zoki duba tawa yarinyar"

Dariya suka saki gaba dayansu,ta taso takarbi gorar ruwan da Ashraf yakawo tabude bakin robar ta kwara mata,cikin sauri Mawahib tasaki wani irin numfashi tareda jan numfashi,Mamy ta kamota ta rungume ta ajikinta,ahankali tafara bude idonta harta budeshi ras,tana ganin mutanan falon ta tuno abinda yafaru,cikin d'acin zuciya tasaki wani irin kuka tace"Mamy da gaske yaya Captain yatafi yabarni?,meyasa saida yabari nafara sonsa zai tafi yabarni? meyasa mutuwa bata daukemu tareba,? Mamy nima mutuwa zanyi..."

Cikin lallashi Mamy tace" Mawahib Captain yana nan,bai mutu ba,yana nan da ransa yanzu muka gama waya dashi"

Hawayen idonta ta goge tace"Mamy dan karna mutu shiyasa kika fadi haka ko? da idona nagani ance yamutu"

Ashraf yayi sauri yakira Aryan,bugu daya yadauka yace"Aryan ga Mawahib tana so taji muryarka"

Yafadi haka tareda bawa Mamy wayar,daga can 6angaren Captain Aryan da beyi tunanin a speaker aka saka wayar ba, cikin sigar soyaiya yace"Baby bakya kewata ko...?"

tanajin haka ta kalli wayar da sauri,sannan ta kalli Mamy,cikin sauri ta 6oye fuskarta ajikin Mamy, Mamy tayi murmushi tabawa Ashraf wayarsa, Ashraf yafice daga falon da wayar a kunnansa.

Alqali yayi murmushi ya kalli Mawahib yace"shikkenan kuka yaqare ko Mawahib?"

Cikin sauri ta juya bayanta anan taga duka iyayen nasu maza da kowa da kowa na gidan duk suna falon,cikin sauri tacire jikinta daga na Mamy tatafi dakinta da gudu cikeda kunya(🙈)

kan gadonta tafada tasaki wani irin murmushin farinciki,fillo taja ta rungume a qirjinta tana sakin murmushi ita kadai, cikin sauri tatashi tafada toilet tayi wanka wanda ta dade batayi irinsa ba, sannan ta dauro alwala tazo tafara gabatar da sallar nafila tana sake yiwa Allah godia daya dawo mata da mijinta gida lafiya.


mutane suna jin labarin nasarar su Captain aka fara sallama a gidan ana yiwa mutanan gidan barka.
Su Daddy kuwa suna idar da sallah suka wuce wajan limamai suna sake yimusu godia akan irin taimakon dasuka basu na Addu'ah.

Ashraf kuwa gida yawuce yadauko Nabiha suka dawo gida.
tun yamma Mamy da Mama Sadiya suka shiga kitchen tare suka fara gabatar da abincin da za'a tar6i Captain Aryan,Nabiha kuwa tana wajan Mawahib sai tsiya take mata.

Zuwa magrib su Mamy suka gama komai, Hajiya kilishi tace"sukai komai da komai part dinta ahadu acan gaba daya aci abincin"

can suka kai abincin tareda taimakon Mawahib da Nabiha, Mawahib gaba daya hankalin ta ya karkata kan bakin get,gani take kamar bazai dawo ba,bayan sungama

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login