Showing 1 words to 3000 words out of 92582 words

Chapter 1 - MATAR MUKHTAR COMPLT

SAKINA   

16 Aug 2024

7134

MATAR MUKHTAR

Written by:
Sakina Yazid
(Innar su Amal)

FIKRA WRITERS ASSOCIATION

BABI NA 1

01


A shekaru hudu da sukayi da aure basu taba samun wata matsala ba domin domin Safiyya macece mai hakuri da kau da kai, musamman a kan lamarin mutumin da take matukar so. Shi din ma kuma ba daga baya ba, duk wani hakki nasu ita da yaran yana saukewa harda kari sannan kuma shi din ma yana matukar kaunar matarsa.


Ma'aikacin gwamnati ne wanda a yanzu ya kai kimanin shekaru goma yana aiki, da yake kuma duniya ta canza sai ya hada da kawo kwamfutoci daga kasar Indiya yana sayarwa a nan Nigeria. Don haka babu laifi suna rayuwa cikin rufin asirin Allah tare da yaransu guda biyu, Usman wanda suke kira Nurain me shekaru uku sai kuma Khadija wadda suke kira Nana mai shekara daya da rabi.

................


Bayan ya gama karin kumallonsa ya shirya kamar yanda ya saba ya fita aiki, ya barsu ita da yaran a gida da yake babu mai zuwa makaranta. Nan da nan ta yiwa yaran wanka ta goya Nana yayinda ta mika Nurain wajen kanwarta Hamida wadda tazo musu hutu. Saida suka dauki kimanin awa daya da rabi suna bacci itada Nana sannan ta tashi ta shiga kicin.

Indai bai fita da abincin rana ba ya saba dawowa gidan bayan azahar yaci abincin sannan idan yana da wani abun sai ya sake fita, don haka da wuri ta tashi ta gama komai ta hada abincin rana.


A zaune suke a falo suna kallon tashar NTA Hausa yayinda suke cin abinci, ita tana ci a kwanonta inda Hamida take ci tana bawa Nurain; wayarta tayi kara daga kicin. Kafin tace wani abu Hamida ta mike ta dauko mata wayar daga kicin inda ta mantota.

Da sallama ta amsa wayar tayi kasake tana sauraro, ko da bata da lambar amma ta dauki murya; Mustafa ne abokin Abban Nurain wanda waje daya suke aiki.

Kafin su gaisa yace


'Kin gane ko Safiyya, wallahi abokina ya sami minor accident ne gamu nan ma a emergency na asibitin Nassarawa yanzu. Ya ma damuna yayi ne a kan lallai sai na kirawo ki na sanar dake amma kar ki wani daga hankalinki buguwa ya danyi sai kuma firgici gashi nan likita yana dubanshi.'


'Inna lillahi wa inna ilaihi rajiun, Subhanallah bari na taho yanzu.'


Magana Mustafan yake yana kokarin yace ta zauna zai kirawota in akwai bukatar tazo amma ko sauraronsa batayi ba ta jefa wayar kan kujera ba tare da ta katseba.

Ta mike ta dubi Hamida tana nuna mata Nana tace


'Rike min ita, babansu yayi accident yana asibiti zan je na gani.'


Kafin ta bata amsa ta wuce daki da sauri ta barsu a nan. Hijabi ta saka sannan ta dauki jakar hannunta, ta tsaya a tsakiyar dakin tana duba jakar, bata da ko sisi sai naira dari biyu wadda ya bata shekaranjiya da zai fita ta sa katin waya ta sayi data na whatsapp. Ta zaro dari biyun ta kalleta, ta danyi lissafi a kwakwalwarta ta tabbatar dari biyu zata kaita asibitin Nassarawa sannan ta mayar da ita cikin jakar.

Ta fito falon tayiwa Hamida sallama sannan ta fice.


Tana zuwa ta tarar da Mustafa a wajen da ake jiran ganin likita wanda ya sanar da ita an shige da Mukhtar din ciki, ta sami guri itama ta zauna. Tana ta addu'a Allah ya sa dai a hayyacinsa yake, tana son tayi waya gidansu ta sanar da Hajiyarsa amma ta daure taga an fito da shi tukunna don taga yanda jikin nasa yake.

Jimawa kadan aka leko aka kirawo Mustafan, cikin sauri ta bi bayansa suka wuce dakin likitan.

Yana kwance a kan gadon duba mara lafiya idonsa a rufe kamar mai bacci yayinda likitocin su biyu da ma'aikacin jinya daya suke tsaye a kansa.
Likitan ya dubi Mustafa yace

'Kaine kazo da shi ko?'

Ya jijjiga kai alamar e. Likitan yace


'A yanzu dai bamu sami wata babbar matsala ba sai dai kawai ya firgita kadan sannan kuma ya buge a hannunsa na dama. Yanzu haka an yi masa allurar da ka kawo gashi nan har ya sami bacci, za a tura shi a kan wannan gadon kuje da ma'aikata ayi masa x-ray a hannun sannan a nuna muku daki, sai zuwa gobe idan muka ga hoton hannun nasa kuma muka ga ya sami natsuwa za a sallameku.'


'To likita mun gode.'


Ya amsa yayinda ma'aikacin jinya ya hadasu da wani ma'aikacin wanda ya tura gadon da Mukhtar yake kwance a kai yana bacci har zuwa dakin hoto.

Gaba daya Mustafan ne ya biya kudin akayi komai, sai da aka basu daki sannan Safiyya ta kirawo kaninsa Saifullahi ta sanar da shi halin da suke ciki.


Tunda taga la'asar tayi ta kirawo Hamida ta sanar da ita ta rufe gidan ta kwashi yaran su tafi gidan Umma da safe sa yi waya.

Nan suka zauna da Saifullahi da daya kanin nashi Aminu har dare yayi; sau daya ya farka ya dan ci abinci kafin wani lokaci kuma ya sake komawa bacci.

Bayan sunyi Sallar isha'i a masallacin asibitin suka dawo dakin suka sameta, har yanzu dai baccin yakeyi. Saifullahi ya dubeta yace


'Anti Safiyya ki taso na mayar dake gida sai Aminu ya kwana da shi.'


Da sauri ta jijjiga kai


'Ai babu komai zan kwana, yaran duk sun tafi gidan Ummanmu.'


Ya kalleta ta jijjiga masa kai tana sake bashi tabbacin hakan za ayi babu wata damuwa.

Don haka suka wuce suka barta a nan inda ta tashi ta rufe musu kofa tunda Saifullahi da Aminu sun riga sun kawo musu duk wani abun bukata.


Cikin dare ta kasa bacci, shi kuwa yana ta bacci saboda allurai da magungunan da aka bashi.Nan ta tashi ta shiga bandaki ta yi alwala ta tada salla. Kafin ta kai raka'ar farko wayarsa da Mustafa ya bata wadda ta saka nasa a chaji ta dau ringing. Ta cigaba da sallar ta, kafin tayi raka'a biyu an kira ya kai sau biyar.

Tana sallamewa ta dau wayar ta duba.

Mahaifiyarsa ce Hajiya.

Nan da nan ta danna wayarta don ta kira hajiya sai akace bata da credit a wayar, ta san baya rasa credit a tashi wayar don haka ta dau wayarsa don ta kirata.

Tana dubawa taga an kulle wayar wanda dama ta san da haka, ta san da hoton yatsansa yake kullewa don haka ta tashi ta kama yatsan ta dangwala nan da nan kuwa wayar ta bude.

Take ta dannawa Hajiyan kira tana dagawa ta ce



'Safiyya ina kuka shiga na ke ta kiranku shiru, ya jikin nashi kuwa? Aminu yace min yana ta bacci, bai farka ba?'


Ta yi mata bayani halin da suke ciki da abinda likitoci suka ce. Sukai sallama ta ajiye tana ta fargabar halin da Mukhtar din yake ciki.

Ta mayar da wayar chaji ta idar da sallarta, ta kashe fitilar ta koma ta kwanta. Ta fi awa daya tana juyi bacci yaki daukarta har ta gaji ta tashi ta kunna fitilar. Ta dubashi ta tabbatar yana numfashi ta janyo kujera ta zauna ta zuba masa ido tana kirga numfashinsa tana fatan ya tashi lafiya domin dazu da ya farka baya son bude ido kuma baya son magana.

Ta riga ta san bata da data shi kuma kullum wayarsa da data don haka ta tashi ta dauko wayarsa ta kunna data ta jona da tata wayar ta hau yawo tsakanin Whatsapp da Facebook, haka ta dauki lokaci har kallo tayi a youtube wai ita ta sami data.


Ta gama ta kashe tata datar ta dauki tashi wayar zata kashe ta sai wani message ya shigo wayar ta Whatsapp, ta karanta layin farko da ya nuna ta saman wayar kamar haka


"missing your beautiful lips my love"


Taji kamar an buga mata guduma a tsakar ka nan da nan rufe ta duk da babu zafi ko daya a garin, ko tunani batayi ba ta bude WhatsApp dinshi domin ta karanta message din.


'Sucre' shine sunan da akayi saving lambar da shi, ta karanta sunan nan ya kai sau goma kafin ta cigaba. Ta fara yin kasa don taga ko da akwai wasu chats din masu kama da wannan, tana yi tana gumi kwakwalwarta a tsaye cak don ta kasa tunani. Har ta gaji da yin kasa bata samu wani sako daga mace mai kama da wannan ba don haka ta koma sama don ta karanta sakon Sucre.

Tayi ta yin sama tana kokarin ganin lokacin da ya fara musayar sakonni da Sucre amma ta kasa zuwa saboda yawan sakonni, don haka sai kawai ta fara biyo sakonni a hankali.


Da fari har tana tunanin aure yake nema ya boye mata amma hirarrakin ba suyi kama da na me neman aure ba, irin wadannan zantukan da hotunan sun fi kama da wadanda akeyi da karuwa.

Shi dai bai tura mata hotonsa ba amma ita ta turo masa hotunanta kalakala; wani da kayan bacci tana shan ice cream, wani daga ita sai towel da ruwa a jikinta alamar wanka, wani kuma ta yi kasa da wuyan rigar nonuwa a waje, wani video ma daga ita sai breziya da pant tana zaune a gefen gado tana ta faman lashes lebe kamar wata mayunwaciyar mayya. Hirarrakin kuma yawancinsu na batsa ne domin zata iya cewa har saduwa an yi a wadannan hirarrakin kuma wasu shi yake fara su balle tace ko yarinyar ce take masa kutse.

Idonta ya rufe saboda hawayen da suke fitowa tana ta faman gogewa, tana yin kasa kadan ta ga hotunansu shi da ita a bakin wani swimming pool ya rungumeta daga shi sai gajeran wando ita kuma da kayan swimming irin na breziya da pant din nan, ga wani kuma bakunansu a manne da na juna. Ta share hawaye ta ajiye hannun da ta rike wayar da shi a cinyarta yayinda ta dafe kirjinta da daya hannun, ta dago ta dubi fuskarshi. Har yanzu bacci yake hankalinsa a kwance, ta zura masa ido kawai tana bin fuskarsa da kallo. Ta kawar da kanta ta sake share hawaye


'Inna lillahi wa Inna ilaihi rajiun.'


Ta dubi wayar dake hannunta, ta tabe baki tare da ajiyar zuciya. Ba zata iya cigaba da karanta sakonnin ba saboda yanda zuciyarta take kuna idonta yana zubar da hawaye. Ta kashe datar sannan ta kashe wayar ma gaba daya sannan ta mike ta ajiye a kan durowar da take gefen gadon.

Ta koma kan daya kujerar da take daga gafe jikin bango ta zauna jagwaf kamar wadda aka tunkuda.


'Inna lillahi wa Inna ilaihi rajiun.'


Ta fada a karo na babu iyaka. Ta ja tissue wadda take ajiye a kan jakarta ta face majinar da ta cika mata hanci, ta goge hawayen da ke fuskarta sannan ta mayar da tissue din ta ajiye.

Ta daga idonta ta dubeshi tana cike da tsananin mamaki, tabbas da wani ya bata labarin wadannan sakonnin da ta gani a wayarsa cewa zatayi ana sone a kashe mata aure. Ko daya bai taba yin wani abu da zai saka mata zargi a zuciyarta ba shi yasa ma ta zata ita kadai ce a zuciyarsa. Da ace ma aure zai kara abun ba zai dameta sosai ba domin ta san shi din yana da damar auren mata hudu, amma sam wannan sakonnin basuyi kama da na neman aure ba.

Tabbas zina sukeyi da wannan yarinyar domin ko a cikin hirararrakin da ta gani sun kai a kirasu da zinar sannan kuma ga hotuna da suke nuna cewa a aikace ma an aikata zinar. Ga shi shi din mutum ne mai ilimin addini balle tace bai san hukuncin hakan ba, to me hakan yake nufi? Gashi dai ita kadai ce lamabar da taga ana wannan hirar da ita, duk ragowar hirarrakin wadanda suka shafeshi ne na aiki da kullum.

To kenan ba wai neman mata da yawa yakeyi ba wanna Sucre din ita kadai yake nema? Ko kuma dai itace wadda yake yayi yanzu? To yaushe Mukhtar ya zama haka?


'Inna lillahi wa Inna ilaihi rajiun.'


Ta fada a fili saboda tambayoyin da take bukatar amsarsu sun fara cika mata kai. Nan da nan zuciyarta ta karye, ta muttsuke ido tana fatan ya zama mafarki take amma ta gane idonta biyu.

Bata san tsahon lokacin da ta dauka a haka ba sai ji kawai tayi ana kiran assalatu, ta gyara zama ta kafa tagumi tana kallon fuskar Mukhtar. A hankali ya bude ido ya dan bi dakin da kallo har ya hangota a kan kujera, ya yi mata murmushi ya fara kokarin tashi zaune.

Ta mike tsaye cikin sanyin jiki ta karasa kusa dashi tana fatan Allah ya taushi zuciyarta kada ta yi abinda bai dace ba a halin da suke ciki.

Ta dafe shi tana fadin


'Ka tashi a hankali Habibi, likita yace kada kayi motsi da karfi har sai an tabbatar babu inda yake maka ciwo.'


Ya karasa zama ta saka masa filo a bayansa tana yi masa sannu. Ya gyara zama sosai yayinda ta janyo kujerar kusa da gadon ta zauna tana kokarin kaucewa hada ido dashi. Jim kadan ya kira sunanta


'Safee.'


Ta dago ta kalleshi ba tare da ta amsa ba


'Kuka kika yi ko?'


Ta goge kwallar da ta makale a idonta tana murmushi tace


'A'a don dai yanzu na tashi daga bacci ne.'


'Wani mai adaidaita-sahu ne ya shigo min garin na kauce masa na je na daki fitilar dake gefen titi. Ina jin dai babu wanda na juwa ciwo ko?'


Ta gyada kai tace


'Eh, kai kadai ne kuma muna fatan da sauki.'


'Alhamdulillah, babu ma inda yake min ciwo yanzu sai hannuna, ina jin kuma buguwa ce kawai.'


'Eh haka likitan yace da aka kawo masa x-ray din hannun.'


Ya zuro kafafunsa kasan gadon ya mike tsaye, nan da nan itama ta mike ta matso. Yayi murmushi ya mika hannu alamar ta bashi hannunta, tana saka masa hannun ya jata jikinsa yana dariya


'Ai zan iya tsayawa da kaina, kuka ya kare ko? Tunda mijin Safiyya bai mutu ba.'


Ta zame jikinta tana fadin


'Ka bari dai na kirawo likita ya dubaka.'


Ta kakalo murmushi tayi masa sannan ta wuce kiran likitan tana share kwalla.


Haka dai suka karasa jinyar tana ta yake tana daurewa, da ya daga wayarsa Sai gabanta ya fadi balle ma taga yana murmushi yana duban wayar. Sai taga kamar da Sucre suke zantukan banza. Sai bayan azahar sannan aka sake dubashi aka sallamesu.


Suka tattara suka koma gida.
MATAR MUKHTAR

Written by:
Sakina Yazid
(Innar su Amal)

FIKRA WRITERS ASSOCIATION

BABI NA BIYU

02


Tunda suka koma gida take ta daurewa amma zuciyarta ta kasa sakewa da shi, yake kawai take shi kuma yana harkokinsa kamar yanda ya saba. Idan ya ganta cikin damuwa sai ya zata ko don bashi da lafiya ne take cikin damuwa don haka yake ta kokarin nuna mata ya sami lafiya.

Bai san ta bude sakon Sucre ba don bai ma kula da sakon ba, bayan ya bude wayar dai tayi masa sako tana tambaya

'ni ka share ko?'

sai yayi mata bayanin ya yi hatsari a mota. Suka cigaba da hirarsu daga nan don haka bai ma san da wancan sakon da Safiyyan ta bude ba.


Kwanansu biyu da fitowa daga asibiti ya koma aiki.

Haka suka cigaba da rayuwa, shi bai ce mata komai ba ita kuma bata ce masa komai ba. Gaba daya ma tsoron ta tayar da zancen take musamman da ya cigaba da rayuwarsa kamar babu wata mace sai ita.

Bata taba jinsa yana waya da wata mace da sunan soyayyaba kuma bai taba nuna mata akwai wani abu da yake boyewa ba shi yasa ma bata damu da kulle wayar da yakeyi ba, yana bude wayar ne da yatsansa ko kuma ya zana pattern. Cikin kwana biyu ta faki idonsa ta haddace pattern din da yake bude wayar don haka da ta sami dama sai ta bude wayar ta duba sakonnin shi musamman da Sucre.

Suna nan suna cigaba da hirarrakinsu na batsa yayinda ita take cigaba da turo masa hotunta na rashin kunya a duk lokacin da ya bukata.


Duk wanda ya kalleta ya san tana cikin damuwa amma banda Abban Nurain, kallonta ne baya yi ko kuwa tsabar ko-in-kula ne oho. A haka har akai sati biyar da fitowarsa daga asibitin.



.....


Kamar kullum ta jera masa abincin safe a kan kafet wajen karfe takwas da rabi na safe. Yana shan shayi ita kuma tana zaune a gefensa tana kallon kasa tana kuma wasa da kafet da yatsunta.


'Safee.'


Ya kira sunanta.


Ta dago suka hada ido alamar amsa kiransa.


'Wai me yake damunki ne?'


'Babu komai, me ka gani?'


Ta bashi amsa tana murmushi.


'Kwana biyun nan baki da wani aiki sai tunani, jikinki ne kawai a nan zuciyar tana can tana wani wasiwasi na daban.'


Ta dan yi yake kadan


'Umm! Babu komai, yau da gobe dai kawai ka san jiki da jini'


'Yau da goben nan dai Allah ya sa ta lafiya ce, ko kuma na ce idan tayi wari ma ji.'


Ta dan yi dariya yayinda shi kuma ya sa yatsa ya lakace mata hanci yana dariya, ta tashi ta fara kwashe kwanukan da ya gama cin abinci. Tana yi tana jin zafinshi a ranta; wato don rainin hankali ma sai yau ya kula bata cikin walwala tunda shi yane tare da masoyiyarsa.


.......


Kamar yanda ya saba duk shekara yana zuwa taron karawo juna sani wanda ake yi duk shekara wato ICAN annual conference, wannan karon ma shirin tafiya taron yakeyi. An riga an basu kudin registration da kudin mota daga office don haka ya gama duk wani shiri na zuwa taron wanda za a yi a Abuja. Ta riga ta san da taron kuma ta san bai taba zuwa da ita ba, wanda akayi tana amaryane ma ta so yaje da ita kuma tun lokacin ya nuna mata ba zai iya ba saboda transport ga kudin kama hotel sannan kuma baya son ya dinga tafiya yana barinta ita kadai a hotel room wuni guda; haka dai ya tsarata ta hakura. Don haka wannan ma bata sa rai ba, tana kallo yayi registration a computer dinsa.

Ya riga ya sanar da ita gobe litinin zai tafi don haka tun da rana ta hada masa jakarsa kamar yanda ta saba idan zai yi tafiya, duk wani abun bukata ta hada masa a jaka. Hatta kayan da zai saka da safen ma da takalminsa duk ta ware tunda ya gaya mata karfe bakwai

08, January 2025
Nafisa

I cant download the book

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login