Showing 21001 words to 24000 words out of 94205 words

Chapter 8 - Azima-Da-Aziza-Macizai Ne Complete

20 Jul 2024

37830

tare da Hajja ta sake magana ba tasha, tana gama sha Aziza
zata yi magana taji ana shelan kiran sallar magriba, hakan ne yasa kawai ta rungume Hajja wacce taji
komai na kanta ya dauke, sun ɗau lokaci a haka kafin Aziza ta saki Hajja ta yi alwala ta gabatar da sallar
magriba ta jima tana addua kafin ta tashi ta canza kaya ta ɗauki abubuwan da zata dauka ta kara da wa
inda Inno Fandi ta bata ta fito ta fice a gidan kafin Baffa ya dawo, tana zuwa bayan zanar gidansu ta rufe
ido nan ta b'ace b'atttt!!.




Ko da Azima ta dawo gida ita ma shiri gwabzawa ta yi da Innu Maciji,dan ta lashi takwabin kashesa!.




Hajja kuwa bata tambayi inda Aziza take ba.




Tun tsawon dare Azima ta zama macijiya ta sulale a hankali ta fice a gidan, bata zarce ko ina ba sai
tsakanin shigowa yankin kwana da yankin ja'i.




49
HAUSACINEMA.COM


"Garkuwa suna can, ya ƙi tahowa wai sai ya musu bayani, da wuya yanzu idan su Garkuwa su na
numfashi" Liman ya karasa maganarsa yana zama sharaf a ƙasa yana fifita da hularsa irin na fulanin nan
wanda ake saƙa shi, cirko-cirko suka tsaya, yayinda Mai Unguwa Ori ya ce

"Mu ba mu kashe Innu Maciji da gangan ba,akasari ba bamu ne muka kashesa ba! Me yasa zasu kashe
mana garkuwa!?" cikin fusata wanda yake nuni da damuwa da ɗimauta Baffa ya ce

"Laifin su waye!? Na ce laifin su waye!? Ga irin abunda nake gaya muku amma kun kasa fahimta, ai
shikenan sai mu jira har ta Allah ta kasance damu! Ga bala'in kisan macizai! Ga bala'in yaƙi dame zamu ji
ne kam! Ya Rabbi gamu gareka! Babu yadda banyi daku karku aikawa da yankin ja'i wasika ba, yanzu mai
hakan ta haifar!? Da ace kun saurareni duk ba za a kai ga haka ba, amma mu da shike fulani Allah ya yi
mu da taurin kai bamu jin shawari, wlh da kun bi abunda zan shinfiɗa da mun magance matsalarmu da
ikon Allah sabida ina da imanin za a....."

"Ka rufe mana baki Magaji!!Ya isheka haka!!" Jauro ya katse Baffa, Jauro shine mai magani na yankin
kwana

"A kan me zamu bi abunda zaka gindaya!? Kana da halin da zaka taimakemu amma kayi hakan ne? Duk
wani yaƙin da zai kunno kai kasa a ranka har da sa hannnunka a ciki! Da ace ka taimaki yankinka har za a
yi aike a wani yanki mai suna yankin ja'i ne! Dan haka babu abunda zaka gayawa mutanen yankin nan!
Sai ka bar mu mutu! Idan an kashe Garkuwa da yan faɗa biyu sai mu ma mu jira mu ga mai zai yi
ajalinmu,Macizai ne ko kuma jama'ar ja'i!"




"Haba Jauro miye haka ne kake yi! Bai kamata ka faɗawa Magaji wannan maganar ba! Kwata-kwata ma
yanzu ba lokacin musayar yawu bane!" cewar Arɗo, Jauro ya ce

"A kan me ba zan faɗa masa ba! Karya nayi ne! Na ce karya nayi ne!!?" sarki Chubaɗo ya ce

"A gaskiya ban san me zance a wannan lamari ba, amma zan iya bin maganar Jauro! Magana ta domin
Allah wannan yanki ya kafu tun kakanni, wanda ya taimaka ya kara tsayawa ma wannan yanki kai ne
Magaji! Tun ban san da cewa zan zo na zama sarkin fulanin kwana ba, ni dai roƙonka zanyi da girman
Allah ka taimakemu Magaji! Muji da masifa ma daya ta ishemu ba sai an ɗaɗo mana da na yaƙi ba" Sarki
Chubaɗo ya faɗa yana haɗa hannunsa alaman roƙo,Baffa ya jinjina kai tare da faɗin

"Naji! Kuma na yarda! Abunda aka binne shekaru ashirin shine zanje haƙosa yau! Shin zaku iya fama da
masifu biyar!? E ko a'a? A da masifa daya ce, sannan ku ka kuma janyo mana wata da hannunku, yanzu
kuma kun bada dama aje a kara haƙo wata shin zaku iya tayani tareta? Nayi imani a yanzu yankin kwana
babu mai iya tayani yaƙi da aljanu babu shi!"




50
HAUSACINEMA.COM


" AZIZA! Baffa ya ji an raɗa masa a kunne, da sauri ya dago yana waige amma bai ga kowa ba, "Aziza
kuma?" Baffa ya tambayi kansa a zuciyarsa yana shirin faɗawa kogin tunani ya tsinkayo muryan Arɗo da
Baffa Mandi suna fadin

"Gaskiya ba zamu yarda a haƙo ba,ta bakinka Magaji babu wanda zan iya wannan yaƙin kawai a bar
maganar mu sake neman taimako ku kuma ka faɗa mana hanyar da zamu bi" Sarki Chubaɗo ya ce

"E hakane magaji, ka gaya mana wace hanya ce zamu bi?"




"Inaaaaa! Sam-samba zai yu ace Magaji bane zai bamu mafita sam ban lamunta ba! Ni fa wlh ina zargin
Magaji, duk yadda aka yi yaransa ne MACIZAI!" Jauro ya faɗa yana huci, saurin dagowa Baffa ya yi yana
kallon Jauro, dama ya jima da sanin jauro baya sonsa yana baƙin ciki da shi, ya jima yana masa ƙulli
amma kawai bai san yadda zai yi da Baffa bane, shuru Baffa ya yi yana kallon Jauro, yayinda Arɗo ya
katse Jauro da fadin

"Wai lafiyarka kuwa Jauro? Ko dai akwai wata a kasa ne tsakaninka da Magaji?"




"Miye haɗi na da shi?" Jauro ya faɗa yana yiwa Baffa kallon ƙasƙanci,

"Kawai dai gaskiya abunda na sani ne,meyasa ya ƙi aurar dasu yara duk sun gandare a yanki babu mai
rab'arsu, shekarunsu goma sha biyar oh Allah ni Jauro, yara na tafiya jiki na lankwasa ace mutane ne!
Taya hakan zata kasance!? Kullum fuskarsu a rufe sabida babu ido mai kyau, sannan duk taron da za ayi
na magani basu zuwa, dan Allah a cikinku nan ku gaya min suwaye suka yarda da yaran Magaji mutane
ne?" nan wa inda Jauro ya haɗa baki dasu suka amsa da basu yarda da Azima da Aziza ba, sannan Jauro
ya matso kusa da Baffa wanda ya koma tamƙar wanda aka dasa bishiya ya ce

"Zan fara sakawa yaranka ido fiye da yadda na saka musu a baya, idan har na gano cewa su ɗin ba
mutane bane na maka alkawari da hannuna zan kashesu a gabanka!!" rass!rass!rasss! Gaban Baffa ya
bada yana kallon Jauro, shi kuwa Jauro yana gama faɗi ya juya zai bar wajan ya tsinkayi muryar Baffa na
faɗin

"Allah ya baka sa'a,ni nan zan baka takwabin da zaka kashe yarana a gabana!" ko uhum Jauro bai ce ba
ya bar wajan, Baffa Mandi ya ce

"Wai miye haka ne kam?" murmushin takaici Baffa ya yi ya ce




51
HAUSACINEMA.COM


"Ba komai! Ni na jawowa kaina ai!" shi ma ya juya zai bar wajan sai gasu Garkuwa a muraran! Da sauri
aka tarbesu kowa yana furta kalman Innalillahi wa inna ilaihirrajiun! Da sauri aka sauko dasu daga dokin
yayinda Garkuwa ana sauko da shi yana sumewa, ba shiri aka ce a kai sa wajan Jauro ya duba sa.

A ranar yankin kwana babu wanda ya rintsa, Aziza kuwa ta yi neman Azima ta rasa hakika Aziza idan tace
akwai natsuwa da sauran hankali a tare da ita ta yi karya.

Da washe gari Aziza na idar da sallar asuba ta fice, jejin kwana ta nufa, tana zuwa ta kirawo Inno Fandi,
Inno Fandi na zuwa Aziza tasa kuka, girgiza kai Inno Fandi ta yi ta ce

"Aziza ba kuka bane mafita, abu mai mahimmanci shine a yanzu ki maido da natsuwarki, rashin
natsuwarki shi ya hanaki ganin Azima, zaki iya ganinta amma sai kin samu natsuwa, sannan zaki iya zuwa
dan ki gayawa Baffanku gaskiyar su waye ku, dan ba zaku ci gaba da boyewa ba Azima na kashe
mutane,idan ba haka ba a duban da nayi kowa na yankin nan ya kusan mutuwa! Abunda Magaji baya so
dole karshe shi zai aikata, wato haƙo baiwarsa da ya binne shekaru ashirin, sannan duk yaƙin da zata
kama da wuta kece garkuwar mahaifinki Aziza,ki koma gida Magaji ya ba ki asalin tahirin rayuwarsa na
abunda ya faru shekara ashirin amma har sai kin gaya masa gaskiyar su waye ku!" Inno Fandi na gama
faɗi ta b'ace, Aziza kuka takeyi kamar ranta zai fita,taya zata fara faɗawa Iyayenta su ba mutane bane
Macizai ne? Taya!? Ya Hajja da Baffa zasuji? Idan suka gano cewa duk kisan da akayin nan Azima ta yi
su?" kuka sosai ta yi ta godewa Allah fuskarta ya yi jajur idonta ya ƙara komawa fari sol, tashi tayi tana
ajiyar zuciya tare da tattaro natsuwartakamar yadda Inno Fandi ta gaya mata sai ta samu natsuwa kafin
ta iya sanin ina Azima in ba haka ba yau ma kisan da zatayi sai Allah ne yasan adadi, a hankali ta rintse
ido tana karanto adduar samun natsuwa ta hanyar tasbihi ga Ubangijin talikai, sai da taji zuciyarta ya
samu natsuwa ta sauke ajiyar zuciya sannan ta rintse ido nan ta ganota kwance a jejin hayi, da sauri ta
buɗe idon tana me daukar hanyar jejin hayi ba tare da bata lokaci ba gwanda taje suyi na yau.

Maga Isar da Sakon yankin kwana ne yake karantawa fada sakon yankin ja'i kamar haka

" _DAMA MUNYI MAMAKI ACE KUNA DA MUTUM A YANKINKU KAMAR MAGAJI BAWA AMMA ACE KUN
ZO YANKINMU NEMAN TAIMAKO DA INNU MACIJI! HAKIKA MUMA MUN ZAMA SHASHASHU DA MUKA
YARDA DA KUDIRINKU! BAYAN MUN SAN DA CEWA KU ƊIN ABOKAN GABANMU NE NA TUN TULI-TULI!
A KODAYAUSHE KU YANKIN KWANA KUNA SO KU DINGA NUNAWA KUN FI SAURAN YANKUNA! TO
MUNA SO KU SANI KU KARA SANI, LOKACI YA YI DA ZAMU MAIDA YANKIN KWANA BABBAR
MAƘABARTA! DAN KUWA MUNYI SAƘO YANKIN JIMO MUN ZUGASU NA JARMAN MACIZAI DA KU KA
KASHE! TUN KAFIN KUYI AIKE YANKIN TUDU MUN RIGAKU DAN BA ZAMU YARDA DA KASHE MANA INNU
MACIJI DA KU KA YI BA, MUN GAYAWA YANKIN TUDU KUN KASHE MANA INNU MACIJI SANNAN BA
MAMAKI KU MUSU AIKE A BAKU IRO MAGANIN MACIZAI TO MUN TOSHE WANNAN HANYAR DAN MUN
TONOWA SARKIN TUDU TSOHON RAUNIN DA YANKINKU SUKAYI MASA TA HANYAR KASHE MASA
GUDAN JININSA, DAN HAKA KU FARA SHIRYAWA TARBAN YAƘI NA YANKUNA GUDA UKU, YANKIN JA'I:
YANKIN JIMO: YANKIN TUDU: SAKO DAGA YANKIN FULANIN JA'I._"




52
HAUSACINEMA.COM


Maga Isar da sako yana gama karantawa aka hau kallon-kallo, Mai Unguwa Ori ya ce

"Yaƙi da yanki uku a kan yankin daya?"

"Kuma lokaci daya?" cewar Sarki Chubaɗo,Arɗo ya ce

"Mu dai mun san bamu aikata komai ba, mu sa a ranmu wannan wata jarabawa ce daga Allah, kuma
yana sane damu, shi zai kawo mana dauki, kar mu ce zamu yi wani shirin yaƙi, mu zubawa sarautar Allah
ido" kowa ya amsa da haka ne sannan kowa ya watse cike da alhini.




Azima na kwance a kan bishiya rabinta mutum rabinta macijiya, jelarta na lilo a ta saman rashen bishiya
fuskarta a haɗe har gefe da gefe ya yi jaa! Idonta kuwa ya kara rikiɗewa ya rine ya koma blue sosai harta
fari babu, Aziza tana zuwa jejin hayi jelar Azima ta fara hangowa, saurin karasowa ta yi ta ce

"Azimaa!?" jin muryar Aziza yasa Azima sulalowa tare da komawa mutum, a fusace tayo kan Aziza tana
isowa gabanta kafin ta yi mata magana Aziza ta yi saurin dafe goshin Azima nan take taji abu ya shige
mata kai sai da ta girgiza.

Ganin yadda Azima ta tsaya yasa Aziza faɗin

"Azima lokaci ya yi da zaki saduda! Ki dakata haka" murmushi Azima ta yi tana yiwa Aziza kallon baki da
hankali

"Ni kike cewa na saduda? To naji zan saduda, amma bayan na kashe Baffa!" ta faɗa tana cije baki, Aziza
ta ce

"Wai ke wace irin dabbace Azima?" murmushi Azima ta kuma yi ta ce

"MACIJIYA! ina kina tambaya ne wace irin dabba ce ni? To ni Macijiya ce kamar ke amma bambancin
shine ni muguwa ce ke akasin haka! Har yanzu ban huce da abunda kika min ba, ki bar ganin kinsa jikina
ya yi sanyi kin kafar min da dafina! Ba shi zai dakatar dani ba, na iya yau ne kawai, amma gobe zan haɗa
da kisan da banyi yau ba!" Aziza ta jinjina kai ta ce

"Kin sha fadamin idan na isa na dakatar dake! Ni kuma na sha fada miki cewa bazan bar hakan ta faru ba,
shine zan kara nanata miki, ba zan bar hakan ta faru ba! Dan haka muje gida, kafin Hajja ta titsiyemu da



53
HAUSACINEMA.COM


tambaya!" a hankali Azima ta juya tana dafe kirjinta dan abunda Aziza ta tura mata ya shigeta sosai, a
hankali suka jera suna tafiya dan Azima na da bukatar ta kwanta dan jikinta da ya mutu, sabida abunda
Aziza ta tura mata a hankali yake bin jikinta yana kashe mata shi, dan makarin dafi ta tura mata.



Da haka suka iso kofar gida Aziza ce ta fara shigewa da sallama ta samu Baffa da Hajja suna zaune yana
labarta mata wasikar yankin ja'i wanda kaff abunda Baffa ya faɗi a kunnen Azima, a tana rarrafawa da
kyar amma wani dadi ne ya mamaye zuciyarta nan ta hau murmushi tare da fadin

"Yankuna uku zasu yaƙe yankin kwana? Wayyooo Dadi!bari na ɗan daga kafa dan ganin yadda za a shafe
yankin kwana idan ya so na kashe Magaji Bawa daga baya!" ta faɗa gami da sallama ta shiga gidan, Hajja
ta ce

"Azima ina kika je ne? Ni anya jiya na ganki kuwa? Yana ganki haka kamar wacce bata da lafiya?"

"Kin ganni mana Hajja! Ko dai wannan bala'in ne yasa kanku ke da Baffa ya kama da wuta!? Sannan da
kika ganni haka ba wata matsala bace babba kaina ke ciwo, da nayi bacci na farka zan dawo dai-dai"
Azima ta fada tana kallon Baffa, da ido Baffa yake bin Azima yayinda take yi masa wani irin kallo, Hajja ta
ce

"Allah ya kyauta, jeki kwanta" Hajja ta shige bukka, Azima ta juya kenan zata shiga bukka idon Baffa na
kanta dan ya kasa kauda ido a kanta, wuyarta taji ya mata ƙaiƙaiyi tasa hannu ta sosa, tana sosawa sai ga
sab'ar maciji ya fadi carab a idon Baffa, wani wawan firgita Baffa ya yi,ya tashi jikinsa na rawa ya karasa
ya dauki sab'ar yana kalla,saurin girgiza kai ya yi yana fadin

"Innalillahi wa inna ilaihirrajiun!! Me hakan ke nufi?" jikin Baffa ya yi mugun sanyi dan ya tsorata ba
kadan ba, bukkarsa ya shige yana jeka ka dawo dauke da fatar a hannunsa, cikin rawar murya ya ce

"me ya kamata nayi? Dole na haɗa maganin ganowa idanuna, amma kafin na samu furen surfa sai naje
jejin gangare, kuma kafin na dawo sai na samu kwana biyu sabida dogon tafiya ne ban ci ta zama ba, In
sha Allahu zan tafi gobe" yana gami fadi ya fito ya shiga bukkar Hajja ya gaya mata gobe da safe zai tafi
jejin gangare Hajja ta ce

"Me zaka je yi?"

"Akwai maganin da nake son haɗawa ne, kuma furen da ganyen dole sai naje jejin gangare"

"To Baffa yan biyu Allah ya kaimu lafiya" Baffa ya amsa da amin ya fice, bai zarce ko ina ba sai wajan
Ardo bai boye masa komai ba kasancewarsa mahaifinsa ya gaya masa komai, sosai hankalin Arɗo ya
tashi ya kallesa ya ce




54
HAUSACINEMA.COM


"Magaji bana so ka gaya ma kowa wannan batun ka ji ko? Har sai ka tabbatar" Baffa ya gya ɗa kai cike da
damuwa, nan suka ci gaba da tattaunawa a kan lamarin.

Amma bata ga inda Azima ta yi ba, rafin jimulo ta je amma ba Azima bare mai kama da ita, hankali tashe
Aziza ta hau neman Azima amma bata ganta ba, jejin kwana ta nufa ta hau dubata amma bata ganta ba,
riƙe kai Aziza ta yi tare da furta "YA ALLAH! dabadin ace kisan kai haramun bane babu abun da zai hanani
ban kashe kanmu a yau ba kowa ya huta, wannan wani irin bala'i ne haka? Ya Allah ka yaye mana, Allah
ka bani mafita ka nuna min haske, Ya Allah ka nuna min hanya! Ya Allah ni dai bana da masaniya a kan
fansar da Azima take dauka, dan a iya sanina banga wanda ya mana laifin komai ba, Ya Allah idan ita
haka halinta yake Allah kai kasan yadda zakayi da ita, Allah ka taimake Baffana da Hajjata da jama'ar
mahaifata! Ya Allah ka karesu daga dukkan sharri!" Aziza ta karasa adduar hawaye masu zafi suna wanke
mata fuska tare da jinginuwa a jikin bishiya, wani nishi taji na tashi a bayanta da sauri ta buɗe idonta da
ta lumshe tana waige daga ina nishin ke fitowa, taji ashe ta bayan bishiyar ne,saurin leƙawa ta yi nan ta
iske wata budurwa kwance bakinta saijini ke bulluƙowa, cike da tashin hankali Aziza ta karasa ta ɗagota,
tana dudduba meyasa meta,goshinta ta kalla ta ga bakin maciji wanda yake sara ne na Azima, ihu Aziza
ta yi tana ajiye kan budurwar a kasa ta tashi da sauri tana ja da baya ta kuma sakin wani mahaukacin ihu
tana furta "AZIIIMAAAAAAA!!!?" da gudu ta bar wajen dan babu taimakon da zata iya yiwa budurwar
dan kuwa gubar ya shige mata jiki sosai dan harta idonta da tafin hannunta sun koma blue.

Duk inda Aziza take tunanin zata ga Azima amma da ta je sai dai ta iske gawa, hakiƙa fadin
yaddahankalinAziza ya tashi b'ata lokaci ne, ga shi ta rasa yadda zata yi, bata kara shiga

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login