Showing 87001 words to 90000 words out of 94205 words
Baffa Nawaz ya yi sannan ya koma ya zauna.
Banju ya kalli Baffa ya ce
203
HAUSACINEMA.COM
"Ba kai ka yarda da kanka ba?to inaso ne mu gwabza da karfin-karfi,ni aljani ne faɗa da aljani kuma ba
dadi" jan kafa baya Baffa ya yi ya ware hannunsa ya ce
"Bar ganin ka ƙereni a tsayi da girman jiki! a haka na daureka na kasheka a farko, ni mutum ne amma ba
irin wanda kake tunani ba na san kasan da haka" Baffa na fadi ya hau tada guguwa, ganin haka yasa
Banju wani juyi ya koma wani shirgegen Maciji blue mai matukar kauri da girma, wayyo karka so ka
ga yadda wasu daga cikin masu kallo aka watse daga ciki kuwa har da mom, dan tace wlh wannan kallo
ba da ita ba.
Kokarin sara Banju ya hau kai wa Baffa Baffa na b'acewa a cikin iska, yayinda masu kallo aka kara ja baya
ana darewa ana basu fili dan yau abun babba ne, an gwabza sosai tsakanin Baffa da Banju, da ya ga
tabbas ba fa zai samu galaba a kan Baffa ba nan ya yanki wajan jama'a yana shirin ya kai musu sara dan
kuwa ya tabbatar da Magaji zai kashesa! to dan haka a cikin wa innan dibbannin alumman gwara ya
shafe ko da rabi ne, nan ya yi kansu gadan-gadan ganin haka yasa Nawaz fizgar hannun Aziza suka sa
gudutare da mutane, ganin yadda Banju ya yi kan alumma yasa Baffa haɗa hayaki ya kwashe mutanen ya
zubar dasu gefe, jelarsa Banju yasa zai kwashi wasu kafin ya kwashe Baffa ya kuma kwashesu, ganin haka
yasa ya buɗe bakinsa zaiyi musu b'arin ambaliyar wuta cikin hanzari Baffa yayi wani tsalle ya tashi sama,
dan kuwa idan Banju yayi b'arin wutar nan za a mutu dayawa, kafin Banju yayi tuni Baffa ya haye saman
kansa tare da zaro wani wuƙa ya dab'awa Banju a tsakiyar kai, cak Banju ya tsaya, a hankali ya fara
sulalewa yana zama mutum har ya zama mutum gabadaya, yana gama zama mutum Baffa na zaune a
saman wuyarsa da karamin wukar da ya dab'a masa, tsalle Baffa ya yi ya sauka daga wuyar Banju ya
dirƙo akan kafafunsa ya juya baya ya maida hannunwansa ya rungume a bayansa.
Da kyar Banju ya ce
"Wuƙar Dafi!" Banju na faɗi wukar ta narke a cikin kan Banju ta b'ace bat, dan kuwa ba wuƙa bace kamar
sauran wuƙaƙe, Baffa ne ya haɗa da hannunsa dan zuwan wannan rana, sharabbbb!! Banju ya zube a
kasa, nan take ya kama da wuta har sai da yaci ya ƙone ƙurmuss!! Hamdala da Wani ihu da guɗa da
al'umma suka saka suna fadin
"Magaji! Magaji! Magaji!" suna daga hannu, wani hawaye ne ya tsiraro daga idon Baffa, da gudu Aziza ta
tashi ta zo ta rungume mahaifinta tasa kuka, shima Baffa tamkar an cire masa wuƙa a maƙoro haka
yakeji, Nawaz ne ya taso ya zo shima Baffa ha rungumesa, sannan ya karbi wuƙar ya damƙawa Aziza a
hannunta yace a mallamaka mata dan tare sukayi yaƙin, nan aka kara sa ihu ana kabbara kafin kace me
an daga baffa sama ana ambatar sunansa, sarki chubaɗo mai unguwan yankin kwana ori da kowa na
yanki kwana murna sukeyi harda hawayen farinciki, sauran yankuna kuwa ji sukeyi ina ma ace Magaji a
yankinsu yake, ko ba komai zasu samu karramawa da girmamawa da daukaka daga sauran manyan
yankuna, haka aka dinga miƙawa Baffa hannu ana jinjinawa jarumtarsa.
204
HAUSACINEMA.COM
Da kyar suka saffe sukayi sallar magriba, wasu yankuna wa inda basu da nisa sai sun koma yankinsu
wasu gobe zasu koma.
Ranar yankin kwana wasai, duk majalisa kuwa hiran Magaji Bawa ake yi da yaransa Azima da Aziza, Jauro
kuwa dan kunya da tsangwaman da ake masa yasa ya kasa fitowa.
Washe gari bayan manyan yankuna sun karrama Baffa nan suka gaya masa ai a yankuna yanzu babban
yanki shine yankin kwana, bayan an gama komai suka yi masu sallama, godiya sosai jama'ar kwana
sukayi ma wa inda suka samu damar halartan wannan gayyata ta fafatawa.
Bayan kwana uku da faruwar hakan komai ya zama daidai alhamdulillah Ma sha Allah.
Yanzu Baffa ya maida hankalinsa a wajan yiwa Almazeen magani, sai da Almazeen ya shafe sati curr kafin
ya farfaɗo ya dawo hayyacinsa, a wannan lokacin su mom sunyi sabo da mutanen kauyen kwana fiye da
tunanin mai tunani.
Washe garin ranar da al'mazeen ya farka nan sarki chubaɗo ya tara su yace yana da magana, bayan
kowa ya haɗu nan yake shaida bukatarsa na son sauƙa a kan kujerar mulkin yankin kwana, sannan ya
bayyana Baffa a matsayin wanda zai mulke yankin kwana, girgiza kai Baffa ya hau yi kafin yace a'a tuni
alumma sukace sunji sun gani, babu yadda Baffa ya iya dan kuwa bai so ba amma kowa ya nuna yana
son Baffa ya mulke yankin kwana, haka sarki chubaɗo yasa aka rubuta sakon gayyata inda yankuna suka
ce zasu zo, dan za ayi bikin da ba a taba yi ba na al'adun fulani.
Kamar yadda aka tanada haka kuwa ta kasance wajan karfe goma na safe aka fara bikin naɗa Baffa
sarautar kwana, inda manyan yankuna da ƙananun yankuna duk sun zo, anyi walima Baffa ya samu
alkairi ba ma iyakar shi daya ba harda jama'ar yankinsa, yankin kwana Allah ya ɗagata sama.
205
HAUSACINEMA.COM
Wajan irinsu biyu haka aka kammala taro lafiya, an yanka su shanaye dasu kaji da zabbi an sha kindirmo,
kai taro dai tayi saidai muce Allah ya taya Baffa Magaji Bawa Arɗo riƙoDa yamma Azima da Aziza suna
zaune a bukkarsu, hajja kuma suna bukkarta dasu mom,bayan Aziza ta gama koyawa Azima karatu ta
kalleta ta ce
"Aziza dama ina son na tambayeki" gyara zama Aziza tayi tace
"To inajin yar uwata" maganganun da Al'mazeen ya gaya mata a kunne ne take son Aziza ta fassara
mata, dan ta kwashe maganganun tsaf a cikin kanta, dan haka ta gayawa Aziza tace ta fassara mata,
dariya Aziza ta hau yi har tana riƙe ciki ta ce
"Inyee! Kin faɗa soyayya ne?" haɗa rai Azima tayi tace ban son wulakanci idan ba zaki gaya min ba sai
naje na tambayi mijinki Hamma Nawaz ko naje na tambayi mom"
"Allah ya baki hakuri maida wuƙar" nan ta fassara mata abunda kalmomin ke nufi, wani murmushi Azima
tayi tana rufe fuskarta da tafin hannunta, Aziza zatayi magana sukaji sallamarsu Nawaz sai da gabanta ya
faɗi, su dai basu fito ba sunajin maganarsu dai a tsakar gida, Almazeen ne ya ce
"Mom ya kamata mu koma gida, dan muje mu dubasu mu ga lafiyarsu, barin ma mu da muke da asibiti"
mom ta ce
"Nima na fara wannan tunani zuwa anjima zamuyi magana da Baban su Azizan" wani zaro ido Azima da
Aziza sukayi bama su kadai ba harda Hajja, dan tasan za a kwashesu a tafi dasu ne tunda yara da
mazajensu, kuka ta fara haɗiyewa, Almazeen ya kuma cewa
"Mom ina yaran naki suke? Ya kamata dai yau su zo su kai mu yawo mu ga gari" mom ta ce
"Hakane, Azima! Aziza!" a sanyaye suka amsa da na'am, barin ma Aziza damuwarta yafi bayyana ƙarara a
fuskarta, a tare suka fito suka duƙa, mom tace
"Ku dauko mayafi kuzo ku kai mazajenku yawon ganin gari" amsawa suka yi da to suka dau mayafin
dama dogon abaya ce iri daya a jikinsu, mayafinsa suka dauka suka rufa kansu da shi, a kofar gida suka
samu Almazeen da Nawaz sannan suka hau tafiya babu mai cewa qala, duk inda suka wuce sai an bisu da
kallon burgewa ganin yadda suke tafiya tamkar wasu taurari masu haska sararin samaniya.
Bayan sun kewaya dasu, Azima ta kalli Aziza tace
206
HAUSACINEMA.COM
"Ukhty muje rafin jimulo" a sanyaye Aziza ta amsa da to, dan tun lokacin da taji anyi maganar tafiya
jikinta yayi sanyi dan idan tace tana son komawa tayi babban karya, suna isa rafin wani iska mai dadi da
yake kaɗawa ga ruwa farin sol abun burgewa ga ganyaye kore shar kwance a wajan,
"Wowww!" Nawaz da Almazeen suka furta, Azima tana satar kallon Almazeen, hannunta ya kama suka
zagaya ta gefen rafin dan yana da bukatar suyi luv, dik da mugun kunyarsa takeji, suna barin wajan
Nawaz ya maida idonsa kan Aziza wacce duk ta taburce kamar ma kuka take son yi, dan ita har yanzu
bata taba ji Nawaz yace yana sonta ba, dan haka itama ba zata buɗe zuciyarta ba balle ta cutu, hannunta
ya kama tayi saurin daga ido ta kallesa, janta yayi ya haɗata da bishiya murya a can kasa ya ce
"What's the matter?" girgiza kai tayi sai kuma hawaye suka biyo baya, hannu yasa ya goge mata yace
"Ba ki so ki koma ne ko?" shuru tayi, wani murmushi yaƙen takaici ya yi yana sakinta ya juya baya ya ce
"Na faɗi daidai shiyasa kika ƙi cewa komai?, karki damu duk yadda kike so kiyi, bcox u are free now" ya
faɗa kamar a ɗan zafafe, rungumesa ta baya Aziza tayi tasa kukanta mai sauti, rintse ido ya yi ya ce
"Kamar dai na taba gaya miki bana son kuka ko? To sakeni!" sake riƙesa tayi, hannunta yaja suka isa
bakin ruwan ya zauna ya zira kafafunsa a ciki, itama zaman tayi kusa da shi ta kamo hannunsa ta kifa
kanta a kafadarsa, bata san lokacin da ta furta masa cewa
"Hamma Nawaz, ka taba ji kana sona? Ko kawai tausayina kakeji?" ajiyar zuciya ya sauke ya juyo ya
fuskanceta yace
"Idan har zaki iya karanta abunda yake cikin idona, sannan ki auna bugun zuciyata" ya fada yana ɗora
hannunta a saiti zuciyarsa dake bugawa da sauri
"Zaki iya ba wa kanki amsa, idan hakan bai samu ba, ki bari idan muka koma kd zaki tabbatar" daga haka
bai sake cewa da ita komai ba banda rungumeta da yayi.
Almazeen suna zagayawa baya da Azima ya rungumeta sosai a jikinsa, rufe fuskarta tayi da kirjinsa tana
murmushi tanajin wani bakon yanayi a tare da ita, sakinta Mazeen ya yi ya rungumeta ta baya ya ce
"Na gama haukacewa na susuce a kan son...." shuru yayi ganin tana ta wani aikin rufe fuska, bakinsa
yasa a saitin kunnenta yace
"Wai ni wannan kunyar na miye ne? tinda na farka ake guduna, ko dan sabida daren...." bai karasa ba ta
jiyo ta sauri ta rike bakinsa tana shigewa jikinsa, murmushi yayi yace to faɗamin
"Ana sona?" ɗago kai tayi tasa idonta a na shi ta ce
207
HAUSACINEMA.COM
"Idan ban furta hakan ba na zama butulu! wanda ya sadaukar da rayuwarsa domin tawa, miye ribata
idan ban so shi ba, ance tukaicin so kauna, sabida haka ina kaunarka Hamma Mazeen" wani runguma
Mazeen yayiwa Azima cike da so, kafin ya haɗe bakinsa da nata ya hau bata hot kiss, Azima tayi alkawari
ba zata taba juyawa Mazeen baya ba kamar yadda shi ma bai juya mata ba a lokacin da take abun gudu a
wajan mutane, shiyasa ko da yake romantic dinta bata yi yunkurin dakatar da shi ba, tsayuwa ce ta
gagaresu suka zube kasa, murzanta yake yi cikin salo da shaukin kauna, Azima ganin hankalinsa ya fara
gushewa ne ya sakata zare jikinta daga na shi,yayi saurin riƙota ta ce
"Don Allah Hamma, ka duba inda muke,kuma ma ai" sai kuma tayi shuru, saurin saita natsuwarsa
Almazeen ya yi, amma gaskiya ba zasu kara sati a garin nan ba zasu koma dan ya samu yaji dadin bai ji ba
a daren farko dan wuya kawai yaci.
Tashi yayi ya kama hannunta ya ɗagata tsaye, yace
"Muje gida" riƙesa tayi tace
"Kayi fushi ne?" ɗan murmushi yayi ya girgiza mata kai alaman a'a, wajan su Nawaz suka dawo har yanzu
suna zaune a bakin ruwa yana rungume da Aziza, Almazeen ya ce
"To romio and Juliet muje gida lokacin sallar magriba yayi" Nawaz yace
"Okay Laila da Majnun" dariya Almazeen yayi dan zuciyarsa fari sol.
Gida Suka tafi, bayan sallar isha'i mom ke gayawa su Nawaz yadda sukayi da Babansu Aziza kuma itama
tayi na'am da maganarsa na cewa a dan barsu Azima da Aziza tukunna, su zasu tafi gobe, Almazeen da
Nawaz kamar su kurma ihu, Nawaz da gajen hakuri yace
"Har na kwana nawa?"mom tace ungo nan naka
"Har na tsawon wata daya,ni kuma nace a barsu suyi wata biyu tunda alfarma suka nema,kuma ai
gaskiya ne tinda sun jima basu ne, yanzu kuma zama na dindindin zasuyi daku"
"Haba dan Allah mom, yanzu dake za a yanke wannan shawaran?" cewar mazeen,mom tace bana son
rashin kunya, maza ku tashi ku fara shiryawa, a zuciye Nawaz ya fice Almazeen ya bisa a baya.
208
HAUSACINEMA.COM
Washe gari asubanci sukayi, kaff jama'ar kwana aka fito yi musu sallama, Almazeen ne kawai yayi
sallama da Azima inda ya jima yana tsotsar bakinta, Nawaz kuwa ya ƙi kallon Aziza dan yace itama harda
haɗin bakinta dama ba son komawa take yi ba.
Baffa ya haɗawa su Mom kaya sha tara ta arziki yayinda suke zubawa juna godiya cikin mutunci da
mutuntawa, haka Baffa ya rungumi su Almazeen da Nawaz, sukayi musabaha da Malam Yunusa da Alhaji
Karami, su Inna wuro ma sunyi wa mom da Maman beenah abun arziki, mom tace
"Dan Allah wata rana ku kawo mana ziyara, da sunyi wata daya kuma mazajensu zasu zo su daukesu"
"In sha Allah" mota suka shiga aka dinga ɗaga musu hannu, da gudu Nawaz ya figi motar Aziza ta fito
itama da gudu tana daga masa hannu ya hangeta ta glass din mota amma sai ya kara gudun motar, cikin
rashin jin dadi tin daga Azima har Azizan suka juya jiki a sanyaye, a ranar haka suka wuni zuciyarsu babu
dadi amma suna zuba hira da wasa da dariya da Hajjarsu,yayinda Yawuro ta fara musu gyara tana
tsumasu dan tana so ace kafin nan da wata dayan nan sun sama zam-zam dasu, idan mazajensu suka
kusancesu basu ba kara tunanin wata mace.
Sabida gudun da suke yi yasa biyar na yamma suka fice daga jeji suka b'illa titi, yau ma sai da suka kara
kwana cikin garin yola kafin da washe gari suka kama hanyar kd, suna isa mom ta kira sultana tace mata
sun dawo, wani ihu da murna Sultana tayi a waya mom ta bata labarin abunda ya faru, bata gama ji ba
zumudi yasa ta katse wayar ta kalli Khalil dake danna waya tace
"Dear su mom sun dawo" da murna a fuskarsa yace
"Alhamdulillah"
"Dear tashi mu tafi ina son ganin Aziza"
"Oh Allah sultana ki bari su huta sai muje da daddare"
"O'o ni kawai ka tashi mu tafi yanzu sai ka dawo ka daukeni da daddaren" ta fada tana buga kafafunta a
kasa" hararanta yayi yace "ai saiki dauko mayafinki" kiss ta sauke masa akumatu tana godiya da gudu ta
hau sama dan dauka mayafinta ta sauko a mota ta samesa ya tada suka nufi gidansu.
Suna isa da gudu tayi cikin gidan tana fadin
"Oyoyo Mom! Oyoyo Anty Aziza!" mom dake zaune a parlour ta ce
"Sai dai ni Amma Aziza kam tana garinsu" turus sultana ta tsaya tace
209
HAUSACINEMA.COM
"Bangane tana garinsu ba mom? Sakinta Yaya yayi?"
"Taya zai saketa? Ba yanzu zasu dawo bane sai sun kwana biyu,mahaifinsu ne ya roƙi alfarma a barsu"
cikin rashin jin dadi Sultana ta zauna tace
"Wayyo wlh banji dadi ba mom, to ba komai Allah ya dawo dasu lafiya, inasu Yaya Nawaz da Yaya
Almazeen?"
"Muna isowa basu zauna ba asibiti suka wuce"
"Ayya Allah Sarki! Ohh wayyo Mom na bar Khalil a waje ashe" Mom tace
"Shi dai yaso zaman waje ai khalil ba baƙo bane"
"Wlh kuwa mom kyaleta iyayi take ji da shi waya na tsayayi" cewar khalil da yake shigowa ya duƙa ya
gaishe da mom ta amsa tana dariya,sultana tace
"Oh wato ma haka zaka ce ko? Ba komai ai"
"To dan Allah mom ki ji ni da 'ya fa, to me nace?" mom tace
"Ahh kai kam baka ce komai ba" khalil yayi dariya yana fadin
"Inasu Nawaz?"
"Sunje asibiti,ai muna isowa basu zauna ba"
"Ayya Allah Sarki, to bari na wuce mom"
"Ah to ita Sultanan fa?"
"Zan dawo na dauketa da daddare" khalil ya fada yana ficewa, sultana ta miƙe a dogon kujera tana fadin
"Ohh mom korata kikeyi?"
"To nan gidanki ne? Me zaki zauna ki min"
"To yau ma a nan zan kwana"
"ashe da rabon zaki kwana a wajan gate" mom ta fada tana hawa sama, sultana dakin Aziza ta shiga tana
tuno abubuwa da dama har bacci ya kwasheta, kamar yadda Khalil ya faɗa bayan isha'i yazo ya dauki
sultana, su Nawaz basu dawo ba sai wajan goma, sai da sukayi wanka kafin suka shiga wajan mom a
210
HAUSACINEMA.COM
lokacin tana waya a kawo mata 'yar