Showing 75001 words to 78000 words out of 94205 words

Chapter 26 - Azima-Da-Aziza-Macizai Ne Complete

20 Jul 2024

37843

Sady sun koma daki Sumy ke fadin




176
HAUSACINEMA.COM


"Duk lokacin da na kalli wancan jakar yarinya 'yar fulanin can ji nake kamar na kashe shegiya! har yanzu
ban manta da kaini kofar lahira da tayi ba" Sady tace

"Mu jawo shegiya yau mu ci ubanta a dakin nan kawai" Sumy ta ce

"Haka za ayi" fitowa sukayi nan suka hangi Azima da tray a hannunta tana hawa part din Al'mazeen,
Sady tace

"Kalli Matsiyaciya, mu jira ta dawo mu ja banza muci uwarta!" nan suka tsaya suna jiran saukowar
Azima.




Da sallama ta tura kofar parlorn a lokacin Al'mazeensuna waya da Nawaz, tana ajiyewa ta tashi ta juya
zata fita da sauri Al'mazeen ya ce

"Azima tsaya!"

Nawaz ya ce

"Azima? Azima kuma? Al'mazeen wace Azima?"

"Amm Nawaz ina zuwa zan kiraka" Al'mazeen na faɗi ya ajiye wayar, da kallo Nawaz ya bi wayarsa da shi
yana fadin

"Azima irin sunan yar uwar Aziza ce fa? anywhere mutane nawa ne masu suna iri daya" daga wannan
tunanin ya ajiye wan can a gefe.




"Azima pls ki tsaya ki saurareni! Fushin ya isa haka kiyi hakuri dan Allah! Har tsawon wani lokaci zaki
dauka kina fushi dani?"




ƙin magana tayi yace

"To shikenan idan ba zaki min magana ba, ga wayar ki karba,babban aminina Nawaz zaiyi aure shi da
kanwarsa yau saura kwana shidda bikin,ni kuma zan tafi nan da kwana uku kafin nan gobe zanyi kwana
biyu a asibiti dan akwai mutum bakwai da zan yiwa aiki, ki karbi wayar dan na dinga jin lafiyarki, sannan




177
HAUSACINEMA.COM


idan na dawo jibi ba lallai bane mu samu magana da juna ba, dan ba da wuri zan dawo gida ba, da washe
garin kuma da wuri zan kama hanyar kaduna" saurin karban wayar tayi tana fadin

"Nima zan bi ka bikin" tashi yayi yana fadin

"Ba zaki bini ɗin ba, ba fushi kikeyi dani ba ana neman sati uku baki min magana"

"To kayi hakuri na daina fushin amma zan bi ka"

"To naji, saiki shirya, mutanen gidan nan ma zasuje, idan kika je ma zaki ga wata mai kama dake"

"Mai kama dani kuma!? Ni babu wani mai kama dani a duniya! ni ni daya ce"

"To naji amma ki dai shirya da wuri,dan inaso ace karfe shidda da rabi mun bar gidan nan" murna ta
hauyi tana tsalle zataje yawo, watakila ma daga can ta samu kafar guduwa ta gudu ta huta da ala'ƙaƙai,
sai da safe ta masa zata fice ya dakatar da ita, yace

"Kina son makaranta?" tabe baki tayi ta girgiza kai, ƙura mata ido yayi yana hango gaskiyarta yace

"Kwanaki na tambayeki kin sauke al'kur'ni kika ce min a'a shima nace zaki ci gaba kince bakiso,ke baki
san ilmi shine mutum ba?"

Azima a ranta ta ce

"Humm! Wani karatu ni da ko sallah bane yi" amma a fili da shike tana murnan barin gidan ya sakata
fadin

"Idan muka dawo daga kaduna na yarda zanyi makarantar" ta faɗa tana murmushi"

"Kinyi alkawari?"

"E nayi" ta faɗa tana ficewa.




da murnanta ta hau saukowa tana zuwa dai-dai step din tsakiya taji an fisgota an shige daki da ita aka
wurgata ta fadi kasa, tana daga kai ta ga su Sumy da Sady ,hade rai Azima tayi tana shirin magana sady
tace

"Inyeee yar banza miye a hannunki? Kinje ya gama kwalularki sai ya baki me?" ta faɗa tana sa hannu ta
fizgi wayar daga hannun Azima, tashi tsaye Azima tayi, sumy tasa hannu ta yaye mata mayafi ta
jefar,Azima ta duƙar da kai,maganar Al'mazeen ne ya faɗo mata da yake cewa shi a rayuwarsa baya son
rigima, sannan yadda yasa doka su daina shiga tsabgar Azima haka itama Aziman yace ta daina shiga



178
HAUSACINEMA.COM


tsabgarsu idan kuma maganar aiki ne to yanzu ma shi zata dinga yimawa tinda dama shike biyan duk
ma'aikatan gidan, tunowa da haka ya sakata fadin

"Kunga bani shiga hidimarku tunda Hamma Mazeen bai son rigima,ku bani wayata!?" Azima ta faɗa tana
cije baki gami da miƙa hannu, Sady ce take ƙurewa dalleliyar wayar kallo tace

"Inyeee! waya mai tsada wa yar aiki! yar aikin ma ƙidahuma!? To wlh ba zan bayar ba fasawa zanyi sai
dai duk abunda zai faru ya faru" da sauri Azima tace

"Karki fara wannan kuskuren dan na....." maganarta ne ya tsaya cak sakamakon rutsa wayar da Sady tayi
da bango, saurin zuwa daukar wayar Azima tayi jikinta na b'ari alaman b'acin rai, tana daukar wayar ta
ga ya ragargaje, bata gama saita b'acin ranta ba taji an jawo wuyar rigarta, waigowa tayi ta ware blue
eye dinta a kan Sady, Sady na ganin ido a rine tayi saurin sakin wuyar Azima taja da baya,ihu Azima ta sa
ta haɗa hannuwanta biyu ta ɗagasu sama ta tayar da guguwa ya dauki Sady ta dinga bugata da bango,
ihu Sady keyi yayinda Azima ta wurga wani bakin abu a kofar shiga daki wanda duk ihu da kacaniyar da
za ayi a dakin babu mai ji, nan ta haɗa da sumy ta dinga cin uwarsu,kuka suke suna bata hakuri tare da
gaya mata basu san cewa ita ba mutum bace tayi hakuri, Azima da ta kara yin sama da Sady ta buga
mata kai a silin fuskar Sady duk jini ta ce

"Shin zaki iya maida min wayata ta koma yadda take? Na sha gaya muku karku tunzurani ku ga asalin
wacece ni amma kun kasa fahimta! An gaya muku ko wane yake mutum! Balle kuce zaku takasa son
ranku!" cikin kuka Sumy tace

"Dan Allah Anty Azima kiyi mana rai! Ni wlh yau din nan bana kwanan gidan nan,gobe da sassafe kuma
katsina nayi,wlh har ta auren Hamma Mazeen din ma nikam na yafe" Sady ma mai kwasar baƙar wuya
tace itama ta yafe, sakinsu Azima tayi suka zubo a kasa sharab kamar an watso kaya, suna faduwa suka
hau tattaren kayansu, a daren suka fice ba tare da kowa ya sani ba sai mai gadi da kuma driver da suka
ce masa ya kaisu gidan wata kawarsu, Azima sai da ta gargaɗesu da cewa wlh idan suka sake suka gaya
ma wani abunda ya faru sai ta maida Sady kunkuru ta maida Sumy gwaɗo, jin haka yasa sukace bakinsu
ƙanin kafarsu.

Bayan sun tafi Azima ta dau wayarta ta sa hannu ta shafe kayanta ta koma yadda take kamar ba abunda
ya same shi tayi hanyar dakinta ta kwanta tana murmushi tana kallon wayar wajan kusan sha biyu da
yan mintoci,bayan ta gama daddannawa ta ajiye ta lumshe ido alaman bacci yazo sai taji wayar na
ƙara,dubawa tayi tana hararan wayar, to waye kuma a wannan lokacin? Ta tambayi kanta, dagawa tayi
kamar yadda Al'mazeen ya nuna mata tasa a kunne, da masifa ta fara tarban wanda yake kan layi

"Dalla waye! A wannan lokacin! Baka iya hakura ka kira gobe ne! Ko baka san yau na karbi wayar bane?
Idan Hamma Mazeen ya sani ai sai ya kwace! Idan kuma ya kwace ko ma waye kai Allah ko a ina kake sai
na maidaka burgu!" dariyan Al'mazeen taji ta zare ido tace




179
HAUSACINEMA.COM


"Hamma Mazeen? Dama kai ne? Bakayi bacci ba? Ina dai ba wani abu kakeso ba?" ajiyar zuciya ya sauke
mai karfi ya ce

"Na kasa baccin ne shine nace bari na kiraki muyi hira"

"Oh to inajinka" hira suka hau yi ko wannensu ya saki baki,Al'mazeen yana son gayawa Azima yana sonta
amma sanin ba ko da wani lokaci take saiti ba zata iya tsince masa notinan kai ta damka masa a tafin
hannunsa, shiyasa ya yi shuru suka ci gaba da hira har wajan biyun dare, harbi suka ji ya fara tashi a
gidan, Al'mazeen yace

"Ƙaran miye haka? Subhanallahi! ba dai b'arayi ba! Azima karki fito!"

"A'a Hamma mazeen kai karka sauƙo"

"Azima nace miki karki......"

"Na ce maka ka tsaya ko!" ta faɗa a tsawance tana ajiye wayar ta fito, fitowarta ya yi dai-dai da balla
kofar parlor da sukayi suka shigo dik da kofar security door ne, suna shigowa da Azima suka fara karo
duk sun rufe fuska suna riƙe da bindigogi, Azima suka cafka suna tambayarta ina mai gidan tace baya
nan, ogansu ne ya bada umarni a shiga lungu da saƙo na gidan a fito da duk mutanen gidan har da
ma'aikata, nan kuwa aka hau fito da ma'aikata sannan aka sauko dasu Maman Hanan da Beenah da
Maman Beenah,Hanan da Hanif duk aka fiddo dasu,bindiga aka ɗorawa Maman Hanan a goshi ana
tambayarta ina Al'mazeen kafin Maman Hanan tayi magana Azima ta kuma faɗin baya nan da karfi babu
alamun tsoro a tattare da ita,Al'mazeen kuwa yana aikin dambe da kofar dakinsa wanda ya kasa
buɗewa, Maman Hanan jin bindiga yasata fadin

Ai part din Al'mazeen na saman nasu dan haka yana can sama, nan ogan b'arayin yace su hau su
duba,dama wa inda suka hau daga farko basu lura da dayar step din ba, wani ke fadin yau zasu cika
aljihunsu da kudi a wannan gidan, Azima tace

"Idan baka cika aljihunka da kudi ba,ni na maka alkawari zan cika maka cikinka da gubar dafin maciji!"




"Kai wannan yarinya bata da kunya! Waike bakinki baya shuru ne zan fasa kanki da bindiga fa!" cewar
wani daga cikin b'arayin, ogansu yace ku kyaleta mun san irinsu ai, bari mu karbi abunda ya kawo mu
daga nan mu rabata da baki har abada muyi mata fyaɗe muyi gaba, wani kallo Azima ta musu tana shirin
magana taga an fito da Al'mazeen ana jansa, ranta ne ya b'aci ganin yadda suke fizgar shi kamar kaza.

Gaban ogan aka kawosa ya dago ido yaga ahalin gidansa a zube a kasa an kewayesu da bindiga Azima
kuma ana riƙe da ita.




180
HAUSACINEMA.COM


"Dan Allah karku yiwa kowa komai plss" Al'mazeen ya faɗa hankalinsa a tashe




Wani dariyar mugunta ogansu ya sake ya ce

"Abunda ya kawo mu ba mai tsanani bane Kuɗaɗe kawai zaka bamu sannan mu yiwa wannan yarinyar
fyaɗe mu kama gabanmu" zare ido Al'mazeen ya yi jin sunce zasu yiwa Azima fyaɗe hakuri ya hau basu
amma da shike zuciyarsu ta riga da ta bushe da rashin imani sukace babu abunda ya damesu, Al'mazeen
yace

Su fadi kudin da zai fanshi Azima,nan suka masa wani zunzurutun kudi wanda idan ya basu ya kwashe
kudin acct dinsa kaff kai har ma da gidan da suke ciki a yanzu, zufa ce ta hau wankewa Al'mazeen jiki
yace musu baya da wa innan kuɗaɗen a gida, sannan kudinsa na acct bai kai wannan ba sukace karya
yake yi,idan babu kudin a gida to ya musu transfer (kai b'arawo da karfin hali yake wlh).




"Ko da yana da shi ba zai bayar ba!" Azima ta faɗa jikinta na rawa sabida bakinciki izuwa yanzu yaci ace
kaff ta sare b'ayin nan amma fitowar Al'mazeen ya dakatar mata da komai.




"Ai kuwa idan bai bayar ba lahira zatayi baƙo, ke kuma zamu yaga-yaga dake! idan kuma kinci musu ya
kuma fadin cewa ba shi da kudin da muka tambaya ya gani, dan ko biyar ba zamu rage ba" shuru
Al'mazeen ya yi zuwa can suka ce yana bata musu lokaci akwai gidan da zasuje

Almazeen yace

"Wlh kudina na acct bai kai haka ba,kuyi hakuri na baku kuɗin duka amma bai kai yadda kuke bukata ba"




"Amma lallai ka raina mana hankali, a wannan babban gidan naka zakace baka da kudin da muka
tambaya ashe kuwa baka son rayiwarka da ta wannan yarinyar!"




"Ku kashesa!" ogan b'arayin ya faɗa, daga Al'mazeen akayi aka saita masa bindiga ganin haka yasa da
sauri Azima ta rintse ido hannunta ya kama da wuta ta ciki, saurin saketa wanda suka riketa sukayi
sakamakon wani bala'in zafi a tafin hannunsu, rintse ido Al'mazeen yayi yana kalman shahada, ji yayi



181
HAUSACINEMA.COM


karan an saki kunnamar bindiga, kafin bullet din ya shigo jikinsa Azima ce ta fara shigewa jikinsa bullet
din ya shigeta a baya, saurin buɗe ido Mazeen ya yi ga Azima a jikinsa da Alama bullet din jikinta ya
shiga!

"Azimaaaaa!!" Mazeen ya faɗi hankalinsa tasheda sauri tasa hannu ta shafi fuskarsa nan ya kafe, sannan
ta juya ta watsawa su Maman Hanan wani baƙin hayaki nan suma suka kafe sannan ta juyo tana kwashe
gashin fuskarta ta nannaɗe ta waro blue eye dinta, dan idan bata ci ubansu ba hankalinta ba zai kwanta
ba,bakinciki zai iya sawa ma ta sari kanta ta mutu.




Su kuwa b'arayi tsayuwa kallon bala'i da ikon Allah suka yi, wani gurnani Azima tayita juya nan ta zama
macijiya.

Karyan iskanci nan suka saka ihu, ta ce

"Kamar yadda baku da imani haka nima ban da shi, nawa kam har ya fi naku! RUWA BIYU!AZIMA! AZIMA
BANJU MACIJIYA! NI MACIJIYA CE!" tana faɗi ta hau binsu da sara, sai da ta saresu kaff sannan ta naɗesu
kaff dinsu da jelarta ta sulale ta jasu suka bar gidan, b'acewa tayi ta kaisu jeji ta watsar dasu sannan ta
koma gidan, nan ta samu mai gadi a sume an harbesa a kafa shima,bata yi ta kansa ba ta koma ciki ta
samu har yanzu suna nan a daskare hannu tasa ta shafe jinin dake wajan tass sannan ta watsawa su
Maman Hanan wani bakin hayakin nan ta sakesu, Al'mazeen kuwa kara shigewa jikinsa tayi ta shafo
fuskarsa nan shima abun ya sakesa a firgici ya riƙo Azima wacce ke sulalewa a jikinsa yayi saurin haɗeta
da kirjinsa yana ambatar sunanta, dago kai yayi bai ga kowa ba yaga wayam

To meya samesa sai kace wanda komai na jikinsa ya tsaya na wucin gadi.

Su Maman Hanan kuwa masu fitsari a jiki da masu kashi duk sunyi, Hadiza kuwa cewa tayi wlh yau
gidansu zata tafi dan daren nan babu abunda ta gani sai bala'i ido da ido, Al'mazeen na daukar Azima
suka fito gabadaya nan ya iske mai gadi a kwance shima da harbi a kafa, kwashesu yayi duk ya kaisu
asibiti a lokacin da ya fito ana kiran sallan assalatu.




Bayan sun isa asibitinsa duk yan gidan aka hau basu taimakon gaggawa shi kuwa ya wuce cikin
emergency da Azima, shi da kansa ya hau mata aikin cire mata bullet din da ya shiga bayanta,duk
abunda yakeyi tanajinsa sarai har ya gama yi mata komai, allura ya dauko zai mata tayi saurin riƙe
hannunsa tana girgiza masa kai, da sauri ya hau kiran sunanta,murya can kasa tace

"Hamma karka a yi mini allura zai cutar dani, jikina bana allura bane karka mini dan Allah" hawaye
Al'mazeen ya goge yana gya ɗa kai alaman ba zai mata ba, duba agogo ya yi yaga bakwai dan haka ya
wuce masallaci dake cikin asibitin ya yi sallah sannan ya koma ya duba lafiyar kowa ya ga kowa lafiya



182
HAUSACINEMA.COM


harta mai gadi an cire masa bullet yana zaune, sai a lokacin yaji ya samu natsuwa ya kira jami'an tsaro ya
shaida musu duk abunda ya faru, bayan ya gama musu bayani ya tuno da ashe ya bar wayarsa a gida dan
da wayar asibiti ya kira jami'an tsaron kasancewar akwai wa inda ya sani a ciki, wayar wata nurse ya
karba ya saka lambar Nawaz ya hau kira, sai da ya masa kira uku kafin nawaz ya daga Al'mazeen ya ce

"Dude ni ne"

"Kai Dude jiya muna magana kace zaka kirani baka kirani ba ni kuwa nata kiranka baka daga ba,ina fata
dai komai lafiya?"

"E to da sauki dai" nan Al'mazeen ya ba wa Nawaz labarin abunda ya faru, hankali tashe Nawaz yace
gashi nan tahowa Kano, Al'mazeen ya ce

"Noo! Wlh karka zo don't worry we are safe now alhamdulillah! and Karka gayawa Mom am sure
hankalinta zai tashi but still zan taho jibin In sha Allah dan na saka jami'an tsaro a lamarin,pls karka
damu ina lafiya"

"Pls take care of urself" daga haka sukayi sallama.




Sai wajan karfe hudu kafin suka gama watsatstsakewa sannan suka ɗunguma sukayi gida har lokacin yan
sanda suna zagaye da gidan,nan maƙota aka hau yiwa su Al'mazeen jaje ana yin Allah ya kiyaye gaba,
nan police suka ba wa Al'mazeen rahoton sun san b'arayin sun jima suna aikata b'arna amma yanzu sun
nemesu sun rasa amma zasu ci gaba zurfafa bincike, godiya Mazeen ya musu sannan yace yana da
bukatar matakan tsaro a gidansa, nan D.P.O. ya shaida masa babu komai, sannan ya kamo Azima wacce
ke zaune a mota ya fito da ita suka shiga ciki, dakinta ya kaita ya kwantar da ita ya kalleta yace

"Meyasa kika tare min harbi?"

"Nima ban san meyasa nayi hakan ba, amma naji a jikina ba zan iya bari a harbeka ka mutu ba" shuru
Mazeen ya yi sannan ya tashi ya fita.




Sai dare tukunna su Maman Hanan da Maman beenah suka hau neman su Sumy da Sady, ko da aka kira
wayarsu cewa sukayi sun jima a katsina, nan aka basu labarin abunda ya faru Sady tace




Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login