Showing 42001 words to 45000 words out of 94205 words

Chapter 15 - Azima-Da-Aziza-Macizai Ne Complete

20 Jul 2024

37857

fuskarta a fili ya ce

"Wai meke damuna ne kam? Mtsww!" ya ɗan ja gajerar tsaki yana fita a dakin, gida ya koma dan kansa
ke masa ciwo sosai,magani ya sha cikin ikon Allah bacci ya kwashesa bai farka ba sai daya saura,yana
tashi ana kiran sallar azahar, bai tsaya bata lokaci ba ya yi alwala ya tafi masallaci bayan ya dawo babban
parlour ya wuce ya samu Mom da Sultana suna zaune suna hira, gaishe da Mom ya sake yi ta amsa
Sultana ta gaishesa ya amsa yana haɗe rai da fadin

"Keee me ya hanaki zuwa skull?"

"Brother yau bani da komai shiyasa ban je ba"

"Kin san dai bana son wasa da karatu ko?"

"E Brother bana wasa da karatu ko Mom?" ta fada a shagwabe tana kallon Mom,Mom ta yi murmushi ta
ce

"Ai kai ma kasan yadda Sultana ke son karatu,ya gajiyar hanyan da kuma jikin?"



91
HAUSACINEMA.COM


"Alhamdulillah Mom na warware"

"To Ma sha Allah haka ake so, dama mun gama shiryawa kai muke jira idan ka farka sai mu gaya maka
zamu je asibitin duba yarinyar"

"Okay Mom bari nayi wanka sai na kai ku,nima akwai marasa lafiyan da nake son dubawa, gobe kuma
zanje abuja akwai aikin da nake da shi"

"Kuma?" cewar Mom,ya ce

"E wlh Mom,ai idan har mun samu sauki sai dai idan mun dawo kasarmu gabadaya,tunda ko kaɗan
zuwan nan wan can guy din dan ya raina min wayo ba zuwa yakeyi ba,ya maqale a kasar wasu"
murmushi Mom tayi ta ce

"Ka kyalesa mana Nawaz,kasan fa ba jin dadin zama yakeyi dasu HajiyaLawiza da Hajiya Luba ba, kai
mutanan duniya sai Allah wlh,ace kuna zaune karkashin mutum kuna cin albarkacinsa kuna rayuwa da
dukiyarsa amma kun tsanesa kuna cin dunduniyarsa,kai Allah shi kyauta" Nawaz ya amsa da amin yana
fadin

"Ba ri na shirya nazo na kaiku nima na samu nayi aikin dake gabana a hospital din"

"To a fito lafiya" cewar Mom.




Mintuna sha biyar ya daukesa ya gama shirinsa ya shiga ya yiwa su Mom magana suka fito suka nufi
asibiti,ko da sukaje kwatanta musu room din ya yi shi bai shiga ba ya tafi dan akwai cs din da zai yi, su
Mom ne suka shiga suka zauna da ita,Sultana tasa hannu ta kwashe mata gashin fuskarta ta ce

"Woww! Allahu Akbar! Ma sha Allah!"

"Menene Sultana?"

"Wlh Mom kyakkyawa da ita, ki ga gashi, wayyo Allah na ni,wlh Mom kamar ba yar nigeria ba" Mom tayi
murmushi ta ce

"Baki rabuwa da shiririta Sultana ba bafulatana ba ce"

"Ai wlh Mom ko a fulanin ba kowa ke da kyau ba"



92
HAUSACINEMA.COM


"To anji ki rufe min baki, karki cika marar lafiya da surutu Yayanki ya shigo ya sameki kina zuba zaneki
zaiyi kema kin sani" zare ido ta yi tana riƙe bakinta dan tasan sarai zai zanetan sai dai idan bata cika masa
ciki ba dan akwai sa da saurin zuciya abu kaɗan ke tunzura shi ransa ya b'aci.




Su na zaune a asibitin sai wajan uku da rabi kafin Aziza ta fara farkawa, farkawartata yazo mata da
mugun mafarki Azima ta biyo Baffa da wani zabgegen takwabi tana shirin kashe Baffa bayan sun gama
dambatuwa In da Baffa karfinsa ya ƙare ya hau kwalawa Aziza kira ta kawo masa dauki Banju zai
kashesa! Ga Hajja a sume a kasa, wani ihu Aziza ta yi dai-dai da lokacin da Nawaz ya sako kafarsa dakin
ya zo dubasu ya iske ihunta tana fadin

"BAFFAAAANAAAAA!!! HAJJAAAAA!! KEEEEE!!! AZIMAAAAAA!! KARKI KASHE BAFFAAAA!!" sauri yin
kanta suka yi Nawaz ya tallabota kirjinsa ya kalli Sultana yace "maza je ki kirawo min wasu nurses ko Dr
duk wanda kika samu su zo yanzu" da gudu Sultana ta fice suka dawo da nurse mutum hudu, nan yace
su ba shi allurai, bayan sun miƙa masa ne tana ta faman buge-buge, Mom tana tsaye daga saman kanta
tana mata tofi, yana mata alluran ta koma ta yi lamo a kirjinsa tana kan ambatar sunan Baffanta da
Hajjanta, kamar da minti biyar abun ya lafa,Mom ta ce

"Nawaz ya dai?"

"Ba komai Mom,nan da 30mins zata farka zata dawo dai-dai In sha Allah" Mom ta ce

"Ka gani ko Nawaz? Gwara da Allah yasa baka barta ba ka taho da ita, Allah ya bata lafiya ya tashi
kafaɗunta" ya amsa da amin yana me leƙa fuskarta ya ga gashi ya rufe,kwantar da ita ya yi ya fice,
Sultana ta zauna kusa da ita tana kamo hannunta.




Kamar yadda Nawaz ya fada haka kuwa ya kasance 30mins ta farka, tana buɗe ido ta hau bin inda take
da kallo, ba dai har ta mutu bane yanzu haka tana lahira? Take tambayar kanta,kallon hannunta ta yi ta
ga wata budurwa zaune kusa da ita, ga wata dattijuwar mata zaune hannunta dauke da carbi tana lazimi,
budurwar kuma hannunta da waya tana dannawa,saurin janye hannunta Aziza ta yi ta matsa baya, tana
dafe kanta da kafarta da ta ga an daure mata shi,nan abunda ya faru ya dawo mata kai, Sultana ta ce

"Sannu kinji! Ya jikin naki?"

"Sultana kira yayanki mana" cewar Mom




93
HAUSACINEMA.COM


"To Mom" Sultana ta faɗa tana ficewa.




Tare suka dawo da shi, a lokacin Aziza na maqale can jikin gado tana wani irin kuka kanta a sunkuye tayi
mayafi da gashin kanta, jin magana yasata dagowa kaɗan ganin mutum na matsota ya sakata fashewa da
sabon kuka tana fadin

"Aradu karka matso kusa dani" a yadda take magana zaka san babu hausa a harshenta,banza da ita
Nawaz ya yi yasa hannu zai tabata ta saki ihu tana kiran sunan Baffa, haushi ne ya kama Nawaz ya daka
mata tsawa

"Keeeee!!! Bana son hauka!! Ki natsu!!" Mom tace

"Haba Nawaz!? Miye haka? Ka mata a hankali mana" wani tsoro ne ya kama Aziza,ganin haka yasa Mom
matsowa kusa da ita ta ce

"Ɗana ne! Ba zai cutar dake ba, wancan kanwarsa ce, shi kuma likita ne, ya bugeki ne bisa tsautsayi
sannan wannan asibitinsa ne yana kula dake,alhamdulillah kin farka, yanzu haka kina garin kaduna
ne,munji kina ambatar sunan Baffanki, da kinji sauki zamu maidaki gida kinji ko? Karkiji tsoronsa zai duba
ki ne uhum?" Mom ta faɗa tana bubbuga Aziza, dubata Nawaz ya yi ya fice cikin haushi.




Tun shigan Azima dakin munir da niyyar gyarawa ba a sake ganin mai kama da ita ba, har dare, kuma
cikin wani ikon Allah babu wanda ya nemeta,dan sun manta da ita,tunda sun san mai aikinsu ta gudu sun
manta sun dauki sabuwa, sai wajan karfe tara Munir ya dawo shi da Baby, bayan sun yi magana da Zuby
da Hajiya Baby ta wuce dakinta,Munir ma ya wuce nasa,yana shiga ya yi turuss yana ganin ikon Rabba,
Azima ta yi ɗaya-ɗaya a kan gado ta bararraje an samu gado mai laushi bana kara ba, sai kwasar baccinta



94
HAUSACINEMA.COM


take cikin salama hankali kwance, gashinta da ya sha wanki sai kyalli yake yi duk ya baje ya rufe mata
fuska, wani yawu muqut Munir ya hadiye yana fadin

"Kai daga ina wannan balarabiyan?" ya fada yana yin kanta ba tare da yayi dogon tunani ba shin aljana
ce ko mutum.




Hannu yasa jikinsa na rawa yana lashe baki yana kwashe gashin da ya rufe mata fuska cikin bacci Azima
ta ji mutum a kanta, bata gama tabbatarwa ba sai da taji saitin hannun mutum a wajan dukiyar
fulaninta, nan da nan ta farga da abunda ke wakana a kanta, idonta ne ya sauya,da tafin hannunta ta
tokari kirjin Munir kamar kiftawar ido da bismillah sai ga Munir ya yi sama ya bugu timm da kasa!! Saurin
tashi Azima ta yi,ta dauki mayafinta ta yi lullubi sannan ta yi kan Munir,tana zuwa ta shaƙosa da hannu
daya ta haɗasa da bango,nan idon Munir ya yi waje yana so ya yi ihu amma baya so kannansa suji su
rainasa, lallai yau ba shakka ya yi gamo da aljana a garin ɗan banzan son matan tsiya tun bai tsaya ya ga
wacece ba ya afka mata ga shi tana neman kashesa,lokuta da yawa Munir ya sha yiwa yaran aikinsu
fyaɗe,da anyi kara kuwa uwarsu zata zuba kuɗi ta karbo ɗanta tace an masa sharri.




Cikin zafin zuciya Azima ta kamo hannun Munir wanda ya taba mata kirji da shi, matse hannun tayi
jikake ƙashi na haɗewa yana bada ƙaƙassƙasssƙass!! Ihu Munir ya sake na azaba, Hajiya da Zuby dake
parlour suka ji ihun Munir da gudu sukayi dakinsa, a lokacin da ya yi ihu Azima ta sakesa ta koma gefe jin
kafar mutane da gudu, kafin su shigo Azima ta duƙa kasa a gaban Munir, Hajiya da Zuby suna shigowa
Munir ya yi saurin maida hannuwansa baya, Hajiya tace

"Munir ihun me kakeyi haka?"

"Ha...ji....ya...wa..ce..ce...wan...nan...yarinyar.." sai a lokacin suka maida kallonsu ga Azima da take duƙe
tana murmushin mugunta ta cikin mayafi, tsaki Zuby tayi tace




95
HAUSACINEMA.COM


"Mtswww Munir amma dai wlh kaji kunya,duk iya shegenka amma wannan yarinyar kake yiwa ihu?
Sabuwar mai aikin da hajiya ta dauka ne fa, wlh nikam har na manta da ita a gidan,ke dan uwarki miye
kikeyi a dakin nan tun rana har yanzu?" matse hannu Azima tayi tana cije baki, da kyar ta ce

"Da na shigo na manta abubuwan da Inna Lantana ta gaya mini nayi ne,kuma da nazo fita ban san ta
inda zan fita bane shiyasa na zauna, shi kuma da ya shigo ya ganni sai ya tsorata" Hajiya ta ce

"Ba dole ba!, fuska a rufe kina dukar da kai, banza kawai maza ki tashi ki gyara masa dakin yanzun nan
idan kin gama kije ki gyarawa Baby da Zuby nasu, sannan ni kuma kije ki wanke min toilet, ohh ina nufin
bayi ko kewaye ku ke cewa oho,dalla tashi!!" Hajiya ta faɗa da tsawa suna ficewa a dakin ita da Zuby,
Munir ya ce

"Kee dan ubanki! Dama ke mai aiki ce shine kika shaƙeni! Kin san waye ni kuwa?" waigowa Azima ta yi ta
ce

"Kamar yadda kaima baka san wacece ni ba! Ka kiyaye! Bana gargaɗi sai dai zartar da hukunci!" tana
gama fadi harta juya zata fita ya ɗan sake ihu yana maqale hannunsa, juyowa Azima ta yi ta dawo ta
cafke hannu yayinda ta sake matsewa ta ware hannun ya sake sakin kara, hannun nasa ya dawo dai-dai
ta ce

"Ban taba lalata abu na gyara ba! Sai dai idan aka gyara na b'ata!" tana gama fadi ta fice, wajan Lantana
a kitchen taje Lantana tana ganinta ta ce

"Ahh Azima tun rana ina kika shiga haka?" abunda ta gayawa su Hajiya shi ta kara nanatawa Lantana
daga nan ta hau tayata aiki suna girkin Azima taji tana bukatar watsa dafi a cikin abincin,amma
kasancewar tasan Lantana zata ci yasa ta hakura da watsa dafin,bata taba jin bata son kisa ba sai a kan
Lantana ko meyasa hakan oho,bayan sun gama kowa yaci abinci suka gyara kitchen har sun kwanta
Hajiya ta kwalawa Azima kira, cike da takaici da haushi Azima ta dauki mayafinta ta fice tayi dakin Hajiya,
ko sallama ba tayi ba ta shiga Hajiya na zaune a gefen gado,tana ganin shigowar Azima kamar an
bankota yasa Hajiya miƙewa da masifa

"Ke wace iriyar jahilace! Ƙidahuma bagidajiya! 'yar can cikin jeji kawai! ban gaya miki ki zo ki wanke mini
bayi ba?" Azima na shirin magana Munir na kwala mata kira, Hajiya tace

"Maza je kiji me yake da bukata ki gama masa ki zo ki wanke min toilet dina yau din nan, ai babu ke babu
bacci" fita Azima ta yi ta nufi dakin munir yana tsaye daga shi sai gajeran wando,kallonsa tayi ko gizau
bata yi ba balle taji dari-dari dan ta gansa a haka

"Keee!! Banza 'yar jeji, gyara min gadona"

"Kaiiii!! Banza shanu ɗan iska ban gyarawa!" ta juya zata fita Munir yasa hannu ya fizgota ya ɗaura mata
sannan ya tureta gado ya bita ya danne, wani gurnani Azima ta yi tare da rikiɗewa rabinta mutum



96
HAUSACINEMA.COM


rabinta macijiya! A haukace Munir ya tashi a saman kanta ya yi baya-baya ya faɗi a gado jikinsa na rawa,
gashinta ta kwashe blue eye dinta ya bayyana ya ƙare rinewa

"Ban ce maka ka kiyayeni ba! Baka san wacece ni ba ko!?"

Cikin shiɗewar numfashi sabida tsananin tsoro da firgici Munir ya ce

"Dama ke ba mutum ba ce!!?"

Murmushi Azima ta yi ta ce

" RUWA BIYU! Mutum Macijiya!"

"Dan Allah kiyi hakuri karki kasheni!"




"Duk wanda ya ga kwayar idon Azima baya sake ganin wani!" tana fadin haka ta koma macijiya ta saresa
a bayan wuya nan munir ya faɗi ya hau murkususu yana birgima har ya dai na! rai ya yi halinsa, sai da
Azima ta ga ya mutu kafin ta zama mutum ta fice a dakin taja ta rufe shi, ta koma dakin Hajiya da take ta
sababi, Azima ta ce Hajiya

"Ki ɗan jira a parlour na gama gyara miki dakin"

"Saura kuma karki gama da wuri ki ga yadda zanyi dake a cikin daren nan 'yar can cikin jeji kawai!" Hajiya
ta faɗi tana ficewa, Hajiya na fita Azima ta kulle kofa ta hau gadon Hajiya ba daɗewa bacci ya kwasheta,
Hajiya kuwa tana parlour tana jiran Azima ta gama gyara da fito yau ne gobe ne shuru,har bacci ya fara
kwasar Hajiya, ta farka taje ta tura kofar ta jita a gangame! Bugawa Hajiya ta hau yi amma a banza har ta
gaji, tana bugawa tana aunawa Azima zagi, dakin Zuby taje ta buɗe mata Zuby tace ita ba zata tashi ba ta
riga da ta kwanta,haka ma Baby ita kam har da yiwa Maman tsawa ta tayar da ita a bacci, haka Hajiya ta
dawo parlour ta kwanta a kujera nan ta kwana.




Azima bata farka ba sai bakwai na safe tana tashi ta wargaza dakin Hajiya ta kwashi kudin dake dakin
kafin ta buɗe dakin ta fito,nan ta ga Hajiya na bacci wani murmushi ta yi na gefen baki, dakin Lantana ta




97
HAUSACINEMA.COM


nufa taje ta sameta zaune tana karatun al'kur'ani mai girma, wani wawan jiri ne ya ɗibi Azima,Lantana
ganin haka yasata rufewa ta tashi da sauri ta kamo Azima tana tambayarta lafiya? Azima ta ce

"Lafiya lau! Ga wannan kudi ke da mai jiran ƙyauren gidan nan(gateman) ku bar gidan nan ku koma
garinku,ke yar wace gari ce?"

"Ni 'yar can cikin kauyen kano ne, amma meyasa zamu tafi?'' cikin tsawa Azima tace

"Bana son tambaya zaku tafin nan ne ko zaku shiga sahun wa inda za a binne?" jin haka yasa Lantana
karban kudi jikinta na rawa dan bata taba jin murya nai amo da firgici irin wannan ba harta kayanta tace
ta yafesu dama tsumokara ne, ta ce "ki yafeni Hajiya Azima idan na bata miki sai wata rana" bata jira
amsar Azima ba ta fice, takai wa Mai gadi yana tambayarta miye tace masa kawai ya yi ta kansa, sai da
Azima ta tabbatar da sun bar gidan kafin ta ja kofa ta koma, shiganta parlour ya yi dai-dai da farkawar
Hajiya, bata yi wata-wata ba tasa hannu ta fizgi Azima ta gaura mata mari dai-dai sadda Baby da Zuby
suke buɗo kofa dan lokacin haɗa musu tea ya yi, Zuby ce ta ce

"Hajiya me ya faru haka?" cikin kumfar baki Hajiya ta ce

"Wannan 'yar jeji ni zata bari na kwana a parlour?"

"A parlour kuma?" cewar Baby tana bin Azima da kallo da kanta babu dankwali sai gashinta da ya rufe
mata fuska

"Ke ba magana ake miki bane?" cewar Zuby tana hararan Azima dake tsare jikinta na tsuma, hannu Baby
tasa taja gashin Azima yana kwashe na fuskarta nan Azima ta ware kwayar idanunta a kan Baby,wani ihu
Baby ta saki tana ja da baya, Zuby tasa hannu zata juyo da Azima dan ta ga me Baby take yiwa ihu kafin
ta juyo da Azima, Azima ta juyo ta hura mata baƙin hayaki a fuskarta, kafin su farka tuni Azima ta yi juyi
ta zama rabi mutum rabi macijiya, fadin yadda su Hajiya suka shiga firgici ba zai misaltu ba, ihu suke yi
suna kiran Munir,dariya Azima ta kyalkyale da shi ta ce

"Ya riga ku mutuwa! Yanzu a cikinku wa zai bisa na biyu? Bari na kawo muku shi ku gan shi" Azima ta
faɗa tana shiga dakin ta naɗo munir da jelarta ta zo ta jefar da shi a gabansu a tsakiyar parlour, wani
kuka su zuby suka saka ita da baby hajiya kuwa jiki na kyarma ta takure jikinta gefe daya.




A tsawace Azima tace




98
HAUSACINEMA.COM


"NA CE A CIKINKU WA ZAI BISA NA BIYU!!?" cikin kuka da tashin hankali suka hau fadin tayi hakuri karta
kashesu basu so su mutu, Azima tace

"Akwai abu daya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login