Showing 57001 words to 60000 words out of 94205 words
har ta bari tana kallo aka yiwa Sultana fyaɗe ba zata yafewa kanta ba,
dole Sultana tasan asalin wacece ita a yau, tana tsaye jini na kan wanke mata fuska, dama idonta a rufe
yake,hannu tasa ta shafe kanta nan take aka nemi ciwo aka rasa, bama iyakar Ɗan gidan Alhaji da
mutanensa ba, harta Sultana ware ido ta yi kamar zasu faɗo kasa yayinda zuciyarta ya yi wani mugun
tsinkewa, Shaho ne ya yi karfin halin faɗin
"Waike wacece ke!?"
"MACIJIYA, AZIZA MACIJIYA!!" tana faɗi ta buɗe idonta nan take ta rikiɗe ta sama katuwar Macijiya fara
sol sai kyalli takeyi, ba shiri Su Shaho suka saki Sultana wanda ganin Aziza ta koma Macijiya ta saki ihu
tana sumewa.
neman hanyar guduwa su Shaho suka hau yi, Aziza ta naɗosu da jelarta, sannan ta koma rabin mutum
rabi macijiya, kafin ka ankara masu sakin zawo a wando da masu fitsari duk sunayi, cikin tashin hankali
da kiɗima da ɗimauta Shaho ya ce
"Dama ke ba Mutum ba ce?"
" RUWA BIYU" (taken Hajiya Azima kenan).
"Ku godewa Allah bana kisa,bana fata kuma ranar da zanyi kisa! Inaso ne na muku gargaɗi da kakkausar
murya, babu ruwanku da Hamma Nawaz shi da familynsa, sannan duk ranar da dayanku ya ƙara aikata
abu marar kyau zan maida shi kwaɗo, sannan idan har ku ka ba wa wani labarin abunda ku ka gani yau a
take zaku mutu, kuna jina!!?"
130
HAUSACINEMA.COM
"E wallahi Mamanmu mun ji ki,mu dai dan Allah kiyi hakuri!" suka haɗa baki wajan faɗi, watsar dasu
Aziza ta yi, sannan ta zama mutum, su kuwa da mugun gudu suka watse nafsi-nafsi kowa ya yi ta kansa.
Da sauri ta yi kan Sultana yayinda hawaye ya hau wanke mata fuska, zata tab'ata kuma sai ta fasa, zata
tashi sai koma ta kara komawa tasa hannu ta shafi inda aka buga mata katako a bayan wuya, sannan ta
mike zata tafi taji Sultana ta riko hannunta, ganin haka yasa Aziza hura mata wani farin hayaki, nan take
Sultana ta buɗe idonta, tana buɗe ido ta saukesu a kan Aziza, nan ta saki wani kuka tana fadin
"Dan Allah kice min film nake kalla,ko kuma duk abunda ya farun nan ki ce min mafarki ne ba gaskiya
bane" tana maganar ne a ruɗe tana juyi ta rasa inda zata sa kanta dan firgici ganin haka yasa Aziza ɗora
hannunta a goshin Sultana, lokaci daya ta samu natsuwa, hawaye ne ya zubowa Aziza ta ce
"The game is over Anty Sultana! da,fari naso nayi tafiyata ba tare da kun san wacece ni ba, amma ke
Allah ya nufa zaki sani, ba zan iya yarda na watsar da yardan da kuka mini ba,ko ba komai yanzu idan na
tafi zanyi farin ciki idan kika koma zaki gayawa Mom cewa ni ba mutum ba ce,bazan taba manta
alkairinku a tare dani ba, hakika Anty Sultana ni ba mutum ba ce MACIJIYA CE!!"
Girgiza kai Sultana ta hau yi tana fadin
"Gaskiyan Yaya ne da Mom wata rana sai na fara ganin abunda nake kalla a gaske, to ko dai na samu
tab'in hankali ne sabida dukan da aka min? Amma taya mutum zai ga maciji a zahirance irin haka?"
hannu Aziza tasa ta kamo fuskar Sultana ta ce
"Kalli cikin idona!" ɗagowa Sultana ta yi ta sauke idonta a cikin na Aziza nan ta ganshi sak idon mage mai
fari-fari
"Wannan shine dalilin da yasa bana buɗe fuska sabida idona! Ki yarda Anty Sultana ni ba mutum ba
ce,duk labarin da na baku a kaina karya nake yi, wannan shine asalin gaskiyata, ni macijiya ce,na zo
neman 'yar uwata ce ta biyuna, shine dalilin da yasa na shigo cikin gari, idan kinason jin labarinmu ba zan
boye miki komai ba, ki kasa kunne ki sha labari" Aziza ta fada tana gyara zama,ita dai Sultana banda rawa
da jikinta ke yi sai b'arin baki babu abunda takeyi tana yiwa Aziza kallon tsoro, nan Aziza ta dauko mata
labari tiryan-tiryan a natse take warwarewa Sultana zare da abawa, bata boye mata komai ba ta gaya
mata komai tsaff! Wani gauron ajiyar zuciya Sultana ta sauke ta ce
"Innalillahi wa inna ilaihirrajiun! Ai ko a fina-finan da nake kalla ban taba ji ko na gani ba, to meyasa baki
gaya mana gaskiya ba?"murmushi Aziza ta yi ta ce
131
HAUSACINEMA.COM
"Babu wanda zai zauna da macijiya, da ace a lokacin na gaya muku zaku koreni,idan kuma baku koreni
ba zaku dinga tsorona, na zauna shuru a gidanku ne dan na tara kudin da zan nemi yar uwata mu koma
al'karyarmu, dan Allah ki ba wa Mom hakuri idan kin koma, sannan ki nema mini yafiyarta idan na mata
abu a rashin sanina, haka ma dan Allah ki nema min yafiya a wajan Hamma Nawaz, sannan kema ki yafe
mini" Aziza na gama faɗi ta fashe da kuka ta tashi da sauri zata fita,sultana tace
"A yau kin ceci rayuwata, da ace ba dan ke ba, abunda nake yiwa gidan mijina tanadi da yanzu an karbe
shi, bani da sauran wani mutunci da kima, da na koma matatta ko da ina raya, a yadda naji labarinki ke
abun tausayi ce ba abun gudu ba daga ke har Baffanki da Hajjanki da kuma yar uwarki! Ai ke ba abun a
gujeki bane Aziza, dan ke din mai tausayi ce, idan har kin yarda dani kuma kin yarda munyi miki halacci
ba ki so ki saka mana da butulci to ki biyoni gobe mu koma kaduna,nayi miki alkawari zan tayaki neman
yar uwarki gari ya gari, idan har kin yarda dani fa amma" wani kuka ne ya sub'ucewa Aziza ta ce
"Anty Sulty?" rungumeta Sultana ta yi ba tare da tsoro ko fargaba ba,
"Dama akwai mutane irinku a duniya? Tabbasduk lalacewar mutanen duniya na Annabi basu ƙarewa"
cewar Aziza tana kuka, Sultana tana bubbuga bayanta ta ce
"Ni dai ki min alƙawari ba zaki gudu ba,kuma karki kara tunanin guduwa,Mom mutum ce mai zargin
kanta a koda wani lokaci zata dinga zargin kanta da bata miki riƙon tsakani da Allah bane shiyasa kika
gudu, dan Allah karki saka mata da haka"
"In sha Allah Anty Sulty babu inda zani" daga haka Sultana taja hannun Aziza suka fice a gidan ga dare ya
tsaga ana neman gaff kiran sallan assalatu, fitowa bakin titi sukayi, Sultana ta ce
"Muna waya da Khalil yan iska sun bugeni wayar ta faɗi, na san za a nemu kam kuma hankalinsu zai
tashi" Aziza ta ce
"Nima takalmina kafa daya ya fadi, yanzu ya za ayi kenan?"
"Kawai ki daukemu mu b'ace muje gida" zare ido Aziza ta yi ta ce
"A'a Anty Sulty,mu nemi wani hanyar dai" suna nan tsaye har aka kira assalatu, Aziza tace mu zauna a
nan mu jira har ayi sallar asuba nasan a lokacin motoci zasu fara wucewa sai mu wani wanda zai kai mu
gida, tunda bamu sallah ba da sauki ai"
"Yan iska mutanen banza! Da yanzu sai su mana fyaɗe muna period ko?"
"To suna tsoron Allah ne, ai basu tsoron Allah" zama Sultana ta yi a kasa tana fadin
"Ai shikenan" itama Azizan zama ta yi, nan kuwa aka yi asuba kafin motoci suka fara gilmawa da kaɗan-
kaɗan har suka tare mai taxi, Sultana ta gaya masa unguwar da zai kaisu ya daukesu.
132
HAUSACINEMA.COM
A gate din gidan mai taxi ya ajiyesu, suna fita suka samu harda yan sanda, mutane ana tsaye cirko-cirko
daga ciki kuwa harda amarya da ango, wanda jiya da aka tashi a wajan dinner amadadin ayi gida ai sai
hankali ya tashi, kuma ga wayar Sultana da suka samu a gate din da kafar takalmin Aziza guda daya,
shiyasa suna gani suka sa a ransu ai kawai an sace su Sultana ne, sai kuma ya haɗe da Khalil da yake ta
faman zabgawa wayar Sultana kira dan yaji lokacin da Aziza ta kwala mata kira sadda aka buga mata
katako a kai wayar ta fadi kasa,kuma yaji sadda suke cewa a dauko da Aziza, itama aka dinga buga mata
katako, sannan sun ga jini a wajan, jinin kan Aziza wanda ya fashe.
Hajiya Habiba mahaifiyar amarya Sulaiha ganinsu yasa ta ta tarosu da kuka tana tambayar lafiyarsu, nan
suka tabbatar mata da suna lafiya, aka tambayesu me ya faru,nan Sultana tace daukesu aka yi, yan
sanda suka tambayesu waye suka ce basu gane mutanen ba, dan sun rufe fuskarsu,
"Taya aka yi kukayi escaping daga hannunsu?" Sultana ta ce
"Ashe bamu zamu dauka ba, su da kansu suka sakemu, a bakin titi muka kwana kasancewar dare ya
tsaga, sai da akayi asuba muka samu mota ya kawo gida"
"Ina dai basu muku komai ba ko" cewar Hajiya Habiba
"E Ammi basu mana komai ba"
"Na godewa Allah, da me zan cewa Hajiya yara daga zuwa biki ni Habiba,tana can hankalinta tashe
wallahi, dan ma dai tana da karfin zuciya" nan aka shiga jajinta lamarin, aka ce su shiga su huta Sultana
tace sam ai yanzu kam gida zasuyi, anyi-anyi su bari sai anjima tace sam,ganin haka yasa Hajiya Habiba
cewa to jami'an tsaro su rakasu har kaduna har cikin gida, kayansu kawai aka fiddo musu aka sa a both,
Sultana ta rungumi Sulaiha ta ce
"Ƙawata kuyi hakuri fa jiya hankalinku ya tashi ga shi ko gidanki ba a kai ki ba"
"Haba Sultana ba dole ba"
"To shikenan ai muna lafiya, kiyi hakuri ba zan samu zuwa gidan ba amma na miki alkawari zan zo idan
an kwana biyu, a sha amarci lafiya" daga haka sukayi sallama wata ƙawar Sulaiha ta mikawa Sultana
133
HAUSACINEMA.COM
wayarta da kafa ɗayan takalmin Aziza,bayan mota suka shiga jami'an tsaro suka rakasu a baya, har
kaduna.
Suna isa da gudu Sultana ta shige gida,Mom tana tsaye a parlour ta kasa zama, Sultana na shigowa ta ce
"MOM!?" da sauri Mom ta juyo tace
"Sultana" rungumeta tayi, cikin hawaye Mom ke tambayar lafiyar Sultana, shigowa Aziza da yan sanda
sukayi, Mom na ganin Aziza ta yi saurin zuwa ta rungumeta tana tambayar lafiyarta,jikin Aziza ne ya kara
sanyi, da yanzu ta gudu wani tashin hankali zasu shiga? Da yanzu wannan abun bai faru ba da shikenan
ta b'ata rawarta da tsalle, hakika zamanta dasu akwai wani babban sirri da Ubangiji ya boye, shin yanzu
su gayawa Mom gaskiya ne ko yaya zasuyi?" Mom ce ta shafo fuskarta tace
"Kina lafiya 'yata?"
Aziza ta gya ɗa kai,nan yan sanda suka kara yiwa Mom bayani kafin Mom ta musu godiya suka fice,suna
fita Hajiya Habiba na kira,nan Mom ta shaida mata ta kwantar da hankalinta sun zo gida lafiya, dama
tsautsayi ai baya wuce lokacinsa Allah ya kiyaye na gaba kawai, daga haka suka yi sallama aka rabu
lafiya, Mom ta kallesu tace
"Bakuyi wanka ba ko?" suka gya ɗa kai
"Kuje kuyi wanka ku kwanta ku huta idan kuka tashi sai ku ci abinci, tunda yanzu ana neman shaɗayan
safe ne" suka amsa da to, Aziza a sanyaye ta shige dakinta, Sultana kuma ta haura sama, sai da ta yi
waya da Khalil dinta ta tabbatar masa tana lafiya dan hankalinsa ya tashi bai rintsa ba jiya, ta ba shi
labarin ai Aziza ce ta taimakesu, amma bata gaya masa komai a kai ba, dan tayi alkawari ko wa Mom ne
ba zata gaya ba har sai Aziza ta yarda, wanka ta yi sannan ta bi lafiyar gado dan bacci takeji sosai, haka
ma Aziza ita ma wankan ta yi ta kwanta zuciyarta a cin kushe, ga tunani fal a cikin ranta,ji take kamar
kanta zai fashe, ta ɗau minti talatin tana juyi kafin bacci ya kwasheta.
134
HAUSACINEMA.COM
Basu farka ba kuwa sai hudu na yamma,Mom ma bata tashesu ba, ta dai musu odern abinci, bayan sun
farka ruwa suka sake watsawa kafin suka ji sun watstsake, kasancewar suna fashin sallah dukkansu
shiyasa basu wani damu ba, Sultana ce ta fara fitowa ta shiga dakin Mom ta sameta suna waya da
Nawaz,sai da suka gama Mom tace
"Kin tashi? Kinyi sallah?"
"A'a Mom ina fashin sallah, Aziza ma haka"
"Yaushe kuka fara?"
"Ranar da muka isa zaria"
"Ok ya yi kyau,banda shan zaƙi dai da abu mai sanyi"
"To Mom"
"Kije ki ga idan Azizan ta farka,ku ci abinci"
"To Mom, amm Mom Khalil yace zai dawo a satin nan"
"Lafiya dai ko?"
"Nima ban sani ba, amma yace ya fasa cike sauran watannin" gya ɗa kai Mom tayi ta ce
"Nima maganar da muke yi kenan da Nawaz yace zasu dawo, jin abunda ya faru yace gwara kawai ayi
auren kwanan nan a kaiki hankalinsa da nawa ya kwanta nima kuma nayi na'am da abunda yace, dan
haka yace zasu dawo dukkansu shi da Son,idan suka dawo sun dawo kenan, nan da wata daya" shuru
Sultana tayi dan bata so haka ba, ba tare da tayi magana ba ta fice, kasa ta sauko bata ga Aziza a parlour
ba dan haka ta zuba musu abincin tayi dakin da sallama Aziza na zaune a bakin gado, tana sallaman Aziza
ta amsa tana shirin rufe fuska, Sultana tace
"Babu amfani ai tunda nasan komai, zo muci abinci" ta fada tana zama kan carpet, zamowa daga gadon
Aziza tayi ta kalli Sultana ta ga jikinta a sanyaye Aziza ta ce
"Anty Sultana yana ganki haka akwai matsala ne?"
"Babba ma kuwa Aziza, Khalil jin abunda ya faru yace zai dawo a cikin satin nan, Yaya kuma yace shima
zai dawo nan da wata daya dan ayi aurena hankalinsu ya kwanta shi da Mom,kuma Mom tace shi da
amininsa zasu dawo, dama yanzu dawowa mai gabadaya zasuyi" Aziza ta ce
"A'a bangane ba,ina da tambaya, shin Hamma Khalil ba shi bane abokin Hamma Nawaz ba wanda suke
kasa daya?" dariya Sultana tayi ta ce
135
HAUSACINEMA.COM
"Taya? Khalil fa shi yana paris ne, su Yaya Nawaz kuma suna america ne, sunan babban aminin Yaya ba
Khalil bane, ke yanzu duk zamana dake baki san my husband to be ba? sunan babban aminin Yaya
Nawaz AL'MAZEEN NE shi kuma ɗan Kano ne ba dan kaduna bane,gidansu ne Mom tace zata aikemu
nace bazan je ba.
Cikin girmamawa Hadiza ta amsa da to, sannan ta yi waje can wajan kofar baya na kitchen, ta samu
Azima zaune tana tsinke fulani tana wurgarwa, Hadiza ta ce
"Azima meke damunki?" ɗagowa tayi ta girgiza kai alaman ba komai
"To ki zo mu haura sama na nuna miki part din Oga Al'Mazeen zai dawo nan da sati biyu, Hajiya Lawiza
tace
Ki fara karkaɗe kura" zunbur Azima ta miƙetana fadin "muje"
saman suka haura step na hawan uku can ne part din Al'mazeen, kasancewar baya son hayaniyar gidan,
shiyasa idan yana gari ya dawo office yake hawa ya zauna a can shuru abunsa, harta ƙaramin kitchen
akwai a saman, shiyasa baya damuwa da a kawo masa abinci, dan baya so ma yana cin abincin gidan dan
bai yarda dasu ba, suna iya zuba masa abinda ba haka ba a cikin abinci.
Tunda suka fara taka step din bugun kirjin Azima ya tsananta, Hadiza ke gaba Azima na binta a baya, har
suka je bakin kofar parlourn Hadiza tasa key ta buɗe suka shiga, duk da mai dakin ya shekara baya nan
amma har yanzu da kamshin turarensa na tashi, sai kuma uban kura kasancewar idan baya nan babu mai
cewa a dinga bude dakin ana karkaɗewa, Hadiza ce ta kalli Azima ta ce
"Azima bari na tayaki dan kuran yayi yawa"
"A'a ki bar shi kawai Hadiza, ai aikina ne je ki kawai"
"Yanzu zaki iya wannan aikin ke daya?" shuru Azima ta yi bata ba wa Hadiza amsa ba,ganin haka yasa
Hadiza ajiyewa Azima su tsintsiya da mopa dasu omo da dai kayan aiki, har Hadiza zata fita Azima tace
"Dama kin tafi da wa innan kayayyakin naki dan ba amfani zanyi dasu ba" da mamaki Hadiza ta juyo ta ce
136
HAUSACINEMA.COM
"To idan ba kiyi shara da tsintsiya ba dame zakiyi?"
"Ban taba shara da tsintsiya ba" Azima ta faɗa tana zuwa wajan jikin hoton da ta hango, hannu tasa ta
goge hoton, nan take fuskar AL'MAZEEN ya bayyana, rasssrasssrasss!! ƙirjinta ya buga ta ja da baya tana
girgiza kai, Hadiza ta ce
"Karki tsorata, shine Al'mazeen ɗin, karki ga fuskarsa a haɗe mutum ne mai saukin kai, nan gidansa ne,
amma idan kika ga yadda yake rayuwa a cikinta sai kin tausaya masa" Hadiza ta fada tana matsowa kusa
da hoton tasa tsummar dake hannunta ta goge wani wanda suke su biyu ta ce
"Kinga wannan? Sunansa NAWAZ babban aminine ga AL'MAZEEN,idan har kika ga Al'Mazeen na fara'a to
yana tare da Nawaz, shi Nawaz a kaduna yake,kuma dukkansu likitoci ne, sabida tsananin shaƙuwa da
son da suke yiwa juna,bayan sun bude asibitinsu suka saka masa suna mai harufan sunayensu ALWAZ
HOSPITAL na Nawaz na shi na kaduna, shi kuma Al'Mazeen na shi na nan kano, yana da kyauta,baya da
kyashi, yana da taimakon duk wani na kasa da shi,duk yadda zan baki labarin Al'Mazeen yafi haka, amma
idaa ya dawo zaki