Showing 72001 words to 75000 words out of 94205 words

Chapter 25 - Azima-Da-Aziza-Macizai Ne Complete

20 Jul 2024

37840

balle yace zai kira alfarma su ba shi Azima yayi magana da
ita, shawaran da ya yanke shine idan ya tashi a office ya biya ya siya mata waya sai ya koya mata yadda
zata dinga amfani da shi.

Bai fara aiki da wuri ba sai wajan hudu ya fara duba marasa lafiya shiyasa yau bai tashi da wuri ba sai
wajan takwas da rabi, bayan ya tashi sai da ya biya ya siyawa Azima waya tukunna ya nufi gida.

A lokacin Azima na parlour hankalinta tashe tana ta aikin safa da marwa sabida ganin yau Al'mazeen bai
dawo da wuri ba, tana cikin wannan zullumi ya yi sallama ya shigo, wani ajiyar zuciya ta sauke wanda
bata san lokacin da ya fita ba, da sauri ta karasa gabansa tana tura baki ya ce

"Yi hakuri 'yar fullo"

"To yau ina ka tsaya kasa duk na damu! Nifa tinda nake a rayuwata ban taba damuwa da damuwar kowa
ba sai a kanka na rasa dalili! Ban taba sanin miye tunani ko damuwa ba sai a kanka, abunda na sani a
rayiwa shine daukar fansa!"




"Fansa kuma!? To kiyi hakuri yau aiki ne ya min yawa a office,nima wuni nayi ina tunaninki kuma babu ta
yadda zanyi magana dake shiyasa na siya miki waya da zan dawo, zancan kuma nuna damuwa a kaina ba
mamaki ni ɗin na musamman ne!" gaban Azima ne ya faɗi amma da shike tana zumudin waya yasa bata
bada hankalinta a kan fadin da ya yi cewa shi ɗin na musamman bane.

Wayar ya nuna mata amma yace ba zai bata ba har sai ya mata chajinsa, jakar hannunsa ta karba, ya yi
gaba tana binsa a baya idonta kyam a kansa,gani take kamar akwai wani mugun haske dake fita ta
ƙeyarsa tare da wani farin mutum na mata kwala

"MAGAJI BAWA!" ta faɗa tana shirin kaiwa keyar Al'mazeen duka, juyowar da yayi ne yasa tayi saurin
maida hannunta, ya ce

"Mene? Waye kuma Magaji Bawa?" haɗe rai Azima tayi ta ce.

"Tsohon abokin gabana ne"




170
HAUSACINEMA.COM


"Abokin gaba kuma?" Al'mazeen ya faɗa cike da mamaki.

"Karka fiye tambaya" ta fada tana wucewa gabansa ta rigasa hawa, duk abunda sukeyi a kan idonsu
Sumy:Sady:Maman Hanan:Maman Beenah:Hanan:Sumy tace

"Muje kasa ku ga yadda zan tsara wasan nayi cilli da shegiya wajen gate a daren nan" suka sauko a tare,
suna saukowa, Sumy ta ware murya tana kwalawa Azima kira sai kace gidan ke ci da wuta, a lokacin
Azima na tsaye a kan Al'mazeen dake jona mata wayarta a chaji, jin kira kuma Al'mazeen ya gane murya
ya ce

"Sumayya? Sun zo ne? To meyasa take kiran Azima haka?" Azima wacce zuciyarta ya tunbatsa jin yadda
ake kiran sunanta abun ya bata haushi, a tare suka sauko da Al'mazeen,ya kalli Sumy ya ce

"Sumy, Sady, yaushe ku ka zo? Sannan meya faru kike kiran Azima haka?"




"E mana,mun zo dazu, da muka zo na ba wa Azima kayana ta haura min da shi sama, na zo da sarƙata ta
gwal amma yanzu na duba ban gani ba, da na shiga dakin kuma na ga Azima a jikin kayana ta bude min
akwati har nake tambayarta me take yi sai ce min tayi babu komai nayi hakuri, ka dai ni ba saninta nayi
ba banda yau" Maman Beenah ta ce

"Anjima ana yi mana dauki ɗaɗdai, amma dai bamu taba zarginta ba, kasancewar mun yarda da ita"




"Haka ne kam, nima na nemi sarkata wanda ka siya min ɗin nan ban gani ba" cewar Hanan.

Al'mazeen a rayiwarsa ya tsani mai halin b'era dan haka ya ɗago ido yana kallon Azima wacce jikinta ke
rawa idonta sun ƙanƙace sun kara rinewa, harta hannunta ya fara sab'ulewa yana zama blue, cikin wani
irin murya Al'mazeen ya ce

"Azima da gaske ne? Kin dauka mata sarƙa?"




Wani ihu da gurnani Azima tayi tasa hannu ɗaya ta damƙi wuyar Sumy, nan Sumy ta hau jijjiga kai jin an
shaƙe mata magudanar numfashi, cikin daga murya Azima ta ce

"Faɗi gaskiya ko yanzu ki jiki a kabari! Kikace na sace miki sarƙa! Nayi miki kama da b'arauniya! Da ku ka
sakani daukar kayanku na dauka!?" duk maganar da Azima take yi tana rike da makogoron Sumy wacce
ke mutsil-mutsil idonta har ya fara zazzagowa, su Maman Hanan sai dambe sukeyi da hannun Azima a
kan ta saki wuyar Sumy amma sun kasa koda motsi ne da hannun Azima, harta Al'mazeen ya kasa


171
HAUSACINEMA.COM


b'anb'are Azima daga cikin Sumy, cikin in-ina da shaƙewa gami da fitar hayyaci Sumy murya irinta wa
inda suka sha azaba ko suke sha ta ce

"Wallahiii.....karya......na.....ke...yi...."




Sakin wuyarta Azima tayi tana huci,tana sakinta Sumy ta zube kasa a sume, cikin tashin hankali suka
ɗagota,Beenah wacce saukowarta kenan daga sama dan dama bata nan akayi wannan show din,
Mamanta tace

"Beenah! Hanzarta dauko ruwa a fridge" ganin Sumy a baje yasa beenah kwasa da gudu taje kitchen ta
dauko ruwa aka yayyafawa Sumy, da karfi ta fizgi numfashi, ganin ta saki ajiyar zuciya yasa Al'mazeen ya
fizgi Azima ya wanka mata mari, wani gurnani Azima tayi tasa hannu zata shaƙi wuyar Al'mazeen da
hannu biyu amma tamkar an daskarar mata da hannu ne ta kasa, cike da mugun zuciya da mugun jin
haushin kanta ta yi hanyar waje, ganin haka yasa Al'mazeen dafe kai yana ambatar sunanta amma kamar
ba da ita yake yi ba.

Gate ta nufa da niyyar barin gidan, dan ta ga Alkadarinta yana gaff da karyewa, kamata ya yi ace ta kashe
sumy dan ita duk wanda ya tabata hukuncinsa kisa ne! haka ma Hamma Mazeen da ya mareta, amma ta
kasa aiwatar da komai,to me hakan ke nufi? ai gwara ta bar gidan kafin abunda take rayuwa da shi
shekara shabiyar zuwa sha shidda a rabata da shi.




Al'mazeen ne ya biyota yana kiranta amma kamar ba da ita yakeyi ba dan ta zuciya, karamin kofar gate
tasa kafa tayi kwallo da shi,ga mamakin mai gadi sai ganin kofa ya yi a kasa da sauri ya tashi ya matsa ya
bata waje, tana sa kafarta a waje da niyyar fita kamar wanda wutar lantarki ta kama haka taji a jikinta, ji
tayi kamar an ja kafarta akayi sama da ita sannan aka wurgota cikin gidan, sai da ta yi sama tukunna ta
faɗa kan wani dutsekanta ya bugu, zare ido Al'mazeen ya yi yana fadin

"Azimaaaa!" da sauri ya yi kanta yasa hannu ya dagota, harta baƙin tabarau dinta sai da ya fadi, a lokacin
da Al'mazeen ya matso gareta ta rufe ido jin yadda wani mashahurin jiri dake kwasarta dan kanta ya
buge sosai, cikin tashin hankali Al'mazeen ke fadin

"Subhanallahi! Azima! Azima! Azima! Dan Allah kiyi hakuri ba da nufi bane,meya sameki?" jinta shuru ba
motsi yasa ya dauketa cak ya koma da ita ciki, yana shiga har yanzu ana tsaye a kan sumy wacce bata
gama farfaɗowa ta dawo hayyacinta ba.




172
HAUSACINEMA.COM


Ganinsa sukayi ya shigo da Azima a hannun sai kace baby yana shirin sa kai ya haura sama,cikin masifa
Maman Hanan ta ce

"Kai Al'mazeen! Wannan wani irin rashin hankali ne! Ya zaka dauko yar aiki haka a hannunka sai kace
matarka!? A gabanka fa ta shaƙe Sumayya tana shirin kasheta amma baka dakatar da ita ba, zata bar
gidan ka je ka dawo da ita, ga Sumayya nan dake bukatar taimako amma baka kalleta ba ka wani dauko
wannan ƙidahumar jejin matarka ce ko aurenta zakayi!bayan kasan kuma su Sumayya da Sadiyya sune
matan da zaka aura ko? ko dai akwai wani abu a tsakaninka da wannan daukar kaddaran ne?" (wai
Azima ce daukar kaddara)rai a haɗe Al'mazeen ya juyo ya ce

"To auranta zanyi! Ta fiye min su Sumayya da Sadiyya sau dubu! Ina sumayyan ce ta jagaleta? Ita ma
Azima ta suma,ku kai sumayyar sama bari na duba Azima tukunna,zan zo na duba Sumayyan daga baya"
yana gama fadi ya hau sama ya bar su shanye da baki.

A gadonsa ya kwantar da ita yana dubata, gefen kanta ya gani ya ɗan fashe, hannu yasa da niyyar yi
mata treatment ji ya yi ta riƙe hannunsa, kallonta ya yi ya ga har yanzu idonta a rintse yake, a hankali ta
miƙe ba tare da ta kallesa ba tasa kai zata fita yayi saurin shan gabanta,

"Azima yi hakuri! Ki fahimceni ba da nufi na mareki ba, laifinki ne inata miki magana ki saketa amma kin
ƙi ki

saurareni, taya zaki shaƙeta haka idan ta mutu me kike tunani zai faru? Ba ke kaɗai ba harta ni sai an
kulleni dan anyi kisan kai a gidana! da kin kasheta sunanki fa zai koma criminal ne, kuma ba zan so hakan
ta faru ba amma kiyi hakuri kinji? karki yi fushi" ya faɗa yana haɗe hannuwansa alamun roƙo,Azima
kuwa juya kanta tayi gefe har yanzu taki yarda ta buɗe, yana gama magiyarsa ta rab'a ta gefensa ta fice,
riƙe kai Al'mazeen ya yi yana jan ajiyar zuciya,box dinsa ya dauka ya fito yayi side din su Hanan, ya nufi
dakin baki wanda su Sumayya suke zama idan suka zo, da sallama ya shiga har zuwa yanzu suna tsaye a
kan Sumy, rai a haɗe fuskarsa ba annuri ya shiga, allurai ya yiwa Sumy sannan ya ɗora mata ruwa, nan
da nan bacci ya kwasheta, kwashe box dinsa ya yi zai fita Maman Beenah ta ce

"Al'mazeen? Amma ina fatan batun auren yarinyar nan kawai ka faɗa ne ba da gaske kakeyi ba?"

Cak Al'mazeen ya tsaya ya juyo ya ce

"Da gaske nakeyi! Zan aureta! taya zan auri Sumayya? daga zuwanta yau ta bi Azima da sharri! Laifi biyu
wanda na tsana a rayuwata! tayiwa Azima ƙarya da ƙazafin abunda bata yi ba,ƙazafin ma kuma na sata!"
yana gama fadi ya fice, aka barsu da zare idanu.




Part dinsa ya koma, yana tajin babu dadi na ganin Azima tayi fushi, shirin bacci ya yi ya kwanta dan yana
tashi sallar dare.



173
HAUSACINEMA.COM


Da washe gari kamar yadda Azima ta saba haka ta shigo ta kawo masa abinci amma bayan sallama ko
gaishesa taƙiyi, shi kuwa kallonta yakeyi yadda ta duƙar da kai fuska babu rahma ranta a haɗe, ganin har
zai fita bata yi masa magana ba ya saka shi fadin

"Ba ki huce bane? na fa baki hakuri, ba zaki min magana ba? to ga wayarki, kalli ki ga yadda zakiyi amfani
da shi" turo baki tayi tana fadin

"Bana so" sannan ta fice, Al'mazeen ya sosa kai ya ce

"Tab lallai abun babba ne, duk yadda jiya ta nuna murna da farincikinta akan wayar yanzu kuma tace
bata so?" haka yasa kai ya fice, a office sai tunaninta yakeyi, Azima kuwa wuni tayi fuskarta a murtuke
dan abunda ya dameta ya dameta, tunda tazo fita akayi sama-sama da ita sannan aka maidota gidan ta
rasa inda zata saka kanta.




Wasa-wasa Azima ta dauki zafi dan har aka kwashe sati daya bata magana da Al'mazeen tsakaninta da
shi sai dai ta kai masa abinci ta gyara masa daki,duk kulawar da take ba shi bata daina ba magana ce dai
bata masa, a sati dayan nan kuwa Al'mazeen ya yarda ya kamu da soyayyar Azima, kullum sai ya bata
hakuri amma taƙi ta sauraresa dan ita kadai tasan bakincikin da take ciki.

Ta bangaren su Aziza sun fara shirin bikin Sultana wanda zai gudana nan da sati biyu ciff, Aziza daurewa
kawai takeyi tana abubuwa, amma bata da wani kuzari da karfin dafi.

Ana saura sati daya biki duk hankalin sultana a tashe yake.




Al'mazeen ya shaidawa Nawaz a kan cewa idan ana saura kwana uku ɗaurin aure zai zo.

Ko da Sultana ta kara yiwa Khalil magana a kan tafiyarsu kano yace ta hakura kawai sun yi magana da
Al'mazeen yace zai gaya musu ita ba sai taje ba,sultana ji tayi kamar ta kurma ihu dan bakinciki.




Fitowa daga daki Aziza tayi zata hau sama da wani jiri ya ɗibeta zata fadi dai-dai lokacin da Nawaz ya
sawo kai parlorn amma kafin ya iso ya tarota tuni ta fadi kasa,sunanta ya ambata ya dagota yana jijjigata
a hankali yana kiran sunan Mom da sultana, da sauri suka sauko kasa suka samu Aziza kamar ta suma ne
yaya ne oho

"Nawaz me ya sameta!?" mom ta tambaya hankalinta tashe, Nawaz yace

"Wlh mom ban sani ba,ina shigowa ne na ganta tana faɗuwa!" Mom ta ce


174
HAUSACINEMA.COM


"A gaskiya Nawaz shawaran Malam Yunusa zamu bi, kawai ranar daurin auren sultana a haɗa a daura da
naka da Aziza! mu tausayawa yarinyar nan halin da take ciki! Sai daurewa takeyi tana hadiyar zafin ciwo,
a kananun shekarunta tayi ƙanƙanta da jurewa!" mom ta fada tana sakin kuka mai ban tausayi, Nawaz
wanda shima idonsa ya canza kala ya ce

"Duk yadda kikayi dai-dai ne mom"

"Ka dauketa ka kaita daki! Sultana ke kuma ki zauna da ita, bari naje na sanar da cewa auren biyu ne"
mom ta fada tana hawa sama, shi kuwa Nawaz ya dauki Aziza ya kwantar da ita a daki sannan ya fice
yana neman layin Al'mazeen dan ya shaida masa har da shima za a daurawa aure.

A cikin ƙanƙanin lokaci mom tayi sanarwan auren Nawaz da Aziza wanda mutane sun sha mamaki,
amma da shike ance ba a mamaki da ikon Allah sai kowa ya bi lamarin da fatan alkairi.




Sadda Nawaz ke gayawa Al'mazeen akan cewa zai auri Aziza ba karamin mamaki Al'mazeen ya yi ba, har
yaushe Nawaz ya fara soyayya da Aziza da har ta kaisu ga maganar aure nan da sati daya? Sannan Nawaz
baya son auren yarinya kamar yadda baya son auren babba sosai ,ya tabbata idan Nawaz ne zai iya cewa
Aziza tayi masa yarinta, haka dai ya share maganar yana fadin shima ga shi ya kamu da son Azima,yana
so ya ba wa Nawaz labarin Azima amma sai yaji kamar an riƙi bakinsa, dan haka ya share maganar
gabadaya yana tambayar Nawaz dame-dame zasu shirya da bikin tunda aure yazo a bazata, nan Nawaz
ke gaya masa babu wani abunda za ayi wanda ya wuce daurin aure daga shi shikenan, dan harta sultana
tace babu abinda zatayi da an daura aure kawai a kaita,babu yadda khalil baiyi da ita ba ko da walima ayi
nan ma tace ta yafe, ya fahimci rigima ce kawai take ji da shi amma da ta shigo hannunsa zai sauke mata
shi.

Da misalin karfe tara hamma mazeen ya kira Hadiza a waya yace ta kirawo masa Azima, Hadiza ta amsa
da to sannan taje kiran Azima wacce yanzu dakinta daban ita daya, a lokacin tana kwance a gado ta
zama macijiya, Hadiza kuwa tana zuwa ta sako kai ta tura kofa, wani burki tayi turuss! Ganin abunda ko a
mafarki bata taba gani ba, shirgiɗeɗen maciji blue sai sheƙi yakeyi, wani mahaukacin ihu Hadiza ta sake
tana zubewa a kasa sumammiya, da sauri Azima ta waigo nan tayi saurin komawa mutum ta yo kan
Hadiza.

Da gudu su Maman Hanan suka fito har da Al'mazeen wanda ya sauko daga part dinsa, dakin Azima suka
nufa inda suka ji ihu ya fito, suna shiga suka samu Hadiza a baje Azima na tsaye a kanta, suna shigowa ta
duƙar da kai kasa.




"Me kika mata!" cewar Maman Beenah hankali tashe, Sumy wacce ta jima da dawowa dai-dai ta ce




175
HAUSACINEMA.COM


"Ba mamaki itama an shaƙeta ne! Duk yadda akayi wannan yarinya ta taba zaman prison" Al'mazeen
cikin fushi ya kalli Sumy yace

"Ban ce duk wanda yake son kansa da zaman lafiya a gidan nan ba ya daina shiga hidimarta!!?" shuru
sukayi ya kalli Azima ya ce

"Me kika mata?"

"Ban mata komai ba,nima daga kewaye nake naji ihu na fito da sauri sai na ganta a sume,idan kuma
baku yarda ba idan ta farfaɗo ku tambayeta"Al'mazeen ya kalli Sady yace

"Kawo ruwa a yayyafa mata"

"Me?"

"Nace kawo ruwa a yayyafa mata!" ya faɗa a tsawance Sady ta fice tana yatsine fuska, ruwan ta kawo
aka yayyafawa Hadiza a firgice ta farka da karatun ayatul'kursiyyu a bakinta! Nan aka hau tambayarta
menene, cikin fitar hayyaci Hadiza ke fadin maciji! maciji!

"Maciji!!" Sumy Sady da Hanan da Beenah suka rungumi juna suna ihu,harta su Maman Hanan da
Maman Beenah bayan Al'mazeen suka koma jikinsu na kyarma suna tambayar Hadiza ina macijin,
yayinda Azima take kallonsu ɗaya bayan ɗaya ta cikin gashin kanta da ta sauko dashi ya rufe mata fuska,
Al'mazeen yace maciji dai a dakin nan?"

"E wlh nagani! Katon maciji! Ruwan ganye! Babba ya cike wannan gadon! Na ganshi a kan gadon nan!
Wlh na gani! Maciji! Babba maciji!" duk a ruɗe Hadiza ke magana,jin abunda take fadi yasa suka maida
maganar ta ta shirme ba mamaki tayi gamo ne,su sumy suka hau tsaki

"Hanan je ki kirawo Talatu ta zo ta kai Hadiza daki,kafin nan bari nayi mata alluran bacci" ya fada yana
ficewa, su ma su Maman Hanan duk ficewar sukayi.




Ba jimawa Al'mazeen ya sauko da allura a hannunsa ya zo ya yiwa Hadiza sannan ya ce Talatu ta kaita
daki ta kwantar da ita,bayan sun fita Al'mazeen ya kalli Azima wacce kanta ke duƙe yace

"Zan sha shayi, za a iya haɗawa a kawo min?" ya tambayeta yana mai ƙura mata ido, gya ɗa masa kai
kawai tayi sannan ya fice ita kuma ta nufi kitchen dan haɗa masa.




Bayan su Sumy da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login