Showing 6001 words to 9000 words out of 94205 words
yi kan Aziza, da sauri Aziza
ita ma ta sake zama macijiya suka haɗe aka hau dambe, da jelarta na maciji ta nannaɗe wuyar Azima ta
shaƙeta sosai, murkususu Azima ta hau yi tana son kwacewa daga hannun Aziza amma ta kasa, inda
karfinta ya fara karewa dan duk muguntarta bata kai Aziza karfin dafi ba.
Nan numfashinta ya fara yin sama inda a karshen jikinta ya sub'ale ta koma mutum sumammiya, ganin
haka yasa Aziza sakinta ta wullata kusa da rafin ita ma ta koma mutum sannan tasa hannu ta dibo ruwa
ta watsa mata a fuska, wani wawan ajiyar zuciya Azima ta sauke alaman ta sha wuya, da tari ta farka
tana yunkurin tashi ta ce
"Duk abun da zakiyi Aziza kema kin sani ba zaki iya kasheni ba!
Kafadarta Aziza ta kama hawaye cike a idonta ta ce
"Nima bana fatar kasheki! Har na bar duniya bana fata na kashe ko da tururuwa! Azima kisan ya yi yawa!
Azima me kikeson zama ne! Ga shi yau kin sani na aikata abunda bana son aikatawa wanda ban ma taba
aikatawa ba! meyasa Azima! Me yasa! Me yasa!" Aziza ta karasa tana sakin kuka mai cike da ruɗani.
Zufa Azima ta goge tana ture hannun Aziza daga kafadarta ta ce
"Kullum ba zan gaji da faɗin cewa da ni ce da karfin gubarki da na shafe jama'ar yankin nan an wuce
wajan! Duk wanda nake kashewa sun tab'oni ne! Bana mantuwa bana yafiya!"
A fusace Aziza ta sa hannu ta dago Azima tsaye tare da fadin
"Da anyi magana za ki ce ba ki mantuwa ba ki yafiya! Ni a iya sanina ban ga abun da aka miki ba kike
wannan kisar! Shin zaki iya gayamin laifi daya tak ƙwaƙƙwara wanda aka miki kike kisa? Mutum ko da ya
miki kallon bai miki ba shikenan ya cancanci kisa!? Kina fakewa da cewa dan kar a tona mana asiri da
cewa mu ba mutane bane macizai ne, a da ina yarda amma a kwana biyun nan na daina yarda dake! A
da kin san da cewa ke macijiya ce amma ba kya kisa kamar na kwanan nan me yasa Azima!? Me yasa!?"
14
HAUSACINEMA.COM
Idonta ne ya sake rikiɗewa zuwa blue sosai, fatar jikinta har na caccanza kala ta ce
"Fansa! Fansa! Fansa! Fansa nake ɗauka Aziza!"
"To fansar me Azima gaya min?"
"Abun da mutanen yankin nan suka min shekarun baya"
Da mugun mamaki Aziza take kallon Azima dan ba ta taba furta wannan kalman ba sai yau, ta ce
"Shekarun baya fa kika ce!? Duka-duka yaushe aka haifeki da zaki dinga lissafin shekarun baya?"
Murmushin mugunta Azima ta yi ta ce.
"Koma yaushe aka haifeni! Ba damuwarki ba ce! Amma ina so ki sani ki kara sani! Sai na kashe BAFFA!
sai na kashe ARƊO! sai na kashe TSOHON SARKIN FULANI KWANA! da kuma wanda suka sauka a
bayansa! sai na kashe MAI UNGUWA! kee sai na shafe dukkan mutanen yankin nan! Sannan na shiga
birni cikin inda yake da jama'a da yawa na tarwatsasu! Zan bar wannan alƙaryan!"
Gabanta Aziza ta tsaya ta ce
"NI KUMA AZIZA MAGAJI ARƊO! ZANYI YAƘI DAKE NA DAKATAR DAKE! ZAN TAIMAKI MUTANEN YANKIN
NAN KO DA KUWA ZASU GANE CEWA NI MACIJIYA CE SU KASHENI! ZAN TSAYA A GABAN BAFFA NA
KARESA BA KI ISA KIYI MASA KOMAI BA!".
Murmushi Azima tayi ta ce
"Idan kin isa ki dakatar dani Aziza! Na fi ki mugunta! Kin fini karfin dafi! Muje zuwa Allah ya ba wa mai
rabo sa'a!" Aziza ta yi murmushi ta ce
"Amin!" nan Azima da Aziza suka rabe ko wacce tayi hanyarta daban.
Hankali tashe Maga Isar da sakon sarkin fulanin yankin jimo ya faɗo fadar sarki Haruna ya ce
"Allah ya taimakeka! Mummunar labari! Mai cike da tashin hankali, hakika yau munyi asara! Munyi
babbar rashi!" daga nan kuma ya fashe da kuka! Nan hankalin jama'ar wajan ya tashi yayinda Sarki
Haruna ya miƙe tsaye ya ce
"Maga Isar da sako, me ya faru!?"
15
HAUSACINEMA.COM
"Haqiqa mun shiga ruɗu da ruɗani! Munyi sallama lafiya-lafiya da jarman macizai, amma yanzu haka
sako ne daga yankin kwana a kan cewa an kashe jarman macizai! Yanzu haka gasu can sun dawo da
kayansa da dokinsa! rigarsa duk jini!"ba iyakar sarkin fulanin jimo ba harta jama'ar da suke zaune a
wajan sai da suka miƙe tsaye.
Waziri ne ya yi karfin halin faɗin
"Ce dasu su karaso su mana cikakken bayani dan bamu fahimci maganarka ba Maga Isar da Sako!" da
sauri Maga Isar da Sako ya tashi yaje ya ce dasu su karaso, jiki a sanyaye babu kwari suka karaso suka
zube a gaban sarkin fulanin yankin jimo, daga kallon da ake musu yasa suka sha jinin jikinsu, da kyar
garkuwan fulanin yankin kwana ya ce
"Allah ya taimaki Sarki Haruna, da fari kafin muce komai zamu fara da ban hakuri da neman afuwa da
gafarar duk wani wanda yake wannan yanki a kan rashin jarman macizai! Haqiqa munji kunya! Mun
yarda munji kunya! Amma ba laifinmu bane, mai afkuwa ce ta afku, amadadin Sarkin fulanin yankin
kwana da Arɗo, da mai unguwar yankin kwana wato Ori, dani Garkuwan fulanin yankin kwana da Magaji
Bawa da duk jama'ar da suke yankin kwana muna mai neman yafiyarku a kan abunda ya faru na rashin
jarman Macizai! Haqiqa ya cika jarumi kuma ya amsa sunansa, ba zamu manta da halaccin wannan yanki
ba har izuwa karshen rayuwarmu! Mun gode da yunkurin taimakonmu! Haqiqa mu abun tausayi ne, kuyi
hakuri ku yafe mana! Bai kai ga aiwatar da aikinsa ba muka iske gawarsa da saran maciji, ba zamu iya
kawo muku tashin hankali goma da ashirin bane, shi yasa muka sallacesa muka binnesa muka yi masa
sutura, zaku iya zuwa ganinsa tare damu gobe idan Allah ya kaimu sai muje ku ga ƙabarinsa!" Garkuwan
fulani ya karasa maganar a sanyaye yana mai duƙar da kai.
Tabbas jama'ar yankin jimo sunji mutuwar jarman macizai har can kasar zuciyarsu yayinda suka ji tsanar
yankin kwana duk da hakika sun tausaya musu matuƙa, amma zafin mutuwar jarman macizai ya hanasu
ce uffan wasu Garkuwan fulanin yankin kwana, ba a wani musu tarba mai kyau ba dan kuwa su na cikin
ƙunci da jimanin mutuwar jarman macizai, inda suka sa da washe garida safe zasu yi asubanci su tafi
yankin kwana.
YANKIN KWANA.
Ko da su Aziza da Azima suka koma gida ba su shiga hidimar juna ba, harta abinci da Hajja ta haɗa musu
ga mamakinta sai gani ta yi sun raba kwano, sosai abun ya damu Hajja ta yi musu tambayar duniya me
ya hadasu, Aziza ce dai ta iya cewa babu komai fa Hajja, amma Azima kam ko kallon Hajja bata yi ba.
16
HAUSACINEMA.COM
Bayan anyi sallar isha'i dukkansu suka hallara a fadar mai unguwa, kowa da kalar shawarar da yake
badawa, shi dai Baffa duk sauraronsu yake yi ya gaza cewa kanzil, inda a karshe Arɗo ya ce
"Magaji in ce dai lafiya ko? Na ga kowa na ta magana amma kai baka ce komai ba" ajiyar zuciya Baffa ya
sauke ya ce
"Hankalina yana can wajansu Garkuwan fulani, ko ya Haruna zai dauki lamarin? Abun fa sai wanda ya
ɗaure" Ardo ya ce
"Tabbas haka ne Magaji, to ya zamu yi? Mu ma ba yin kanmu bane, Allah yasa su fahimce mu" aka amsa
da amin, tsohon sarkin fulani ya ce
"Yanzu abun duba a nan shine taya zamu shawo kan wannan matsalar? Abun kara yawa yake yi fa?
Jarman macizai da safe! Yaro dazu! Ba zamu zauna mu naɗe hannu a kirji mu zuba ido a shafe mu ba,
mai zai hana mu aika da kokon barar mu neman taimako yankin tudu?" wani zabura Baffa ya yi yana
girgiza kai ya ce
"A'a Baffa Mandi, kar mu kara wannan kuskuren! Munyi kuskure na farko an rasa jarman macizai, yanzu
kuma sai mu sake aikata wani ta hanyar yin aike yankin tudu! Mu nemi taimakon IRO MAGANIN
MACIZAI? Duk shawaran da za ayi a sauran yankuna amma banda yanki biyu, ban da yankin tudu ko
yankin ja'i, kar mu taro wani yaƙin ba tare da mun dakatar da wani ba, kun san tsananin gabar da ke
tsakanin yankin tudu da yankin ja'i da yankinmu, har kwanan gobe ana samun kisan kai a tsakanin yankin
nan da yankin ja'i, har kwanan gobe yankin tudu su na riƙe da abunda ya faru sun kasa mantawa kiris
suke jira su fasa abunda yake zuciyarsu, dan Allah ku fahimceni!"
Shuru wajan ya dauka kowa da abunda yake tunani,
Sai zuwa can anjima Mai Unguwa Ori ya ce
"To shikenan, za ayi ƙuri'a duk bangaren da ya fi rinjaye shi za a zaba, idan bangaren kar aje neman
taimako yankin tudu ko yankin ja'i sunfi yawa to ba za aje ba,idan kuma bangaren wa inda suka ce aje
sunfi yawa to za a je" shi dai Baffa shuru ne ya yi yana hango musu gagarumar balbalin gobarar yaƙin da
zai tashi amma sun kasa ganewa.
17
HAUSACINEMA.COM
Shuru Arɗo ya yi yana kallon Baffa na wasu lokuta kafin ya ce
"Shike nan Magaji, ba zan takura maka ba, amma ban yi tsammanin zaka tsorata da maganar Banju haka
ba"
"Ba tsorata nayi da maganar Banju ba a lokacin da ya faɗi, amma a halin yanzu ina cikin zullumi na
maganar Banju, dan idan baka manta ba ya ce zamu gani ko ba jima ko ba daɗe sannan kuma zai dawo
daukar fansa a kaina da mutanen yankin nan, abunda yake faruwa a halin yanzu abun a duba ne, sannan
bamu san wani martani sarkin fulanin yankin jimo zai maidowa mutanen da suka je ban hakuri garesu
ba, ba kowa bane zai lamunci hakan, munyi aiken neman taimako anzo dan a taimaka mana amma kuma
sai a mai da musu da kaya ace an kashesa! Innalillahi wa inna ilayhirrajiun!" Baffa ya faɗa fuskarsa dauke
da zallar damuwar da yake ciki, Arɗo yaja ajiyar zuciya ya ce
"Ko ma miye ne idan suka dawo ma ji, yanzu dai ka je amma ka tabbatar bayan sallan isha'i ka halacci
fadar mai unguwa"
"In sha Allahu zan zo" daga haka suka yi sallama, Baffa ba hanyar gida ya yi ba dan ba gidan zai koma ba
illa cewa da ya yi su Hajja da Aziza su koma gida, ina Azima bata zo ba? Aziza ta ce
"Eh Baffa bata zo ba" girgiza kai kawai ya yi ba tare da ya yi magana ba, Hajja da Aziza suka dauki hanyar
komawa gida, su na tafiya su na hira, Hajja ta ce
"Ohh Allah ni Jumala, ko me ya hana Azima zuwa? Ita kullum ta fi so ku ta zama a bakin zargi"
"Ai ko basu zauna a bakin zargi ba, ba lallai bane yaranki su kasance mutane ne!" da sauri Hajja da Aziza
suka juya su na kallon Mairo da Hadi wanda suka riƙe ƙugu sai kace zasu dake su, Hajja ta ce
"Mairo me kike nufi?"
"Oho miki kuma! Kin fi kowa sanin abunda nake nufi, yara ko ma dai nace iyayen yara! Ace kamar su
Azima da Aziza a wannan yankin gote-gote dasu amma babu aure! Sannan suna tafiya jiki na lankwasa!
Daga mai idon mage (wato Aziza kenan) sai mai ido ruwan ganye(Azima kenan) taya kuwa zasu zama
mutane, ga shegen kyau! Duk da lokacin da muka yi yan matanci dake duk yankin nan babu mai
kyawunki sannan babu jarumi sama da Magaji, ba wai hakan yana nufin zaku haifi yara masu kama da
mutanen wani duniya daban bane ehe! Ko ki so ko karki so Azima da Aziza dai ba mutane bane!"
18
HAUSACINEMA.COM
Idon Hajja ne ya kawo ruwa ta ma kasa magana, da kyar ta ce
"Mairo idan ke kike aurar wa sai ki zo ki aurar dasu, sannan kuma idan kina canza halitta ki zo ki canza
musu" caraf Hadi ta cab'e zancan da cewa
"Wa ye bai sani ba, ba mamaki duk wannan kisan da ake yi a yankin nan Azima da Aziza suke yi, kuma da
saninki ke kike daure musu....."
"YAAAA ISAAAAAAAA!!!" Aziza ta faɗa da kakkausar murya, ganin yadda fuskar Mahaifiyarta ya jiƙu da
ruwan hawaye, gaban mahaifiyarta ta tsaya yayinda idonta suka kara rinewa zuwa fari-fari ,yatsarta
manuniya ta ɗaga tana nuna Mairo da Hadi cikin gargaɗi ta ce
"Zan iya jure komai! Zan iya shanye komai! Amma kar na ga hawaye a idon MAHAIFIYATA SANYIN
IDANIYATA! ku fita tsabgarmu! Mu mutane ne, maganar da kika fada yanzu kuma Inna Hadi ki bar shi a
iya nan kawai kar yaje gaba!" Aziza na gama fadi ta kamo hannun Hajja suka bar su Mairo da Hadi jiki na
rawa, Hadi ta ce
"Mai....Mai...Mairoo....ban....gaya...miki....da...da..da cewa ba mutane...bane...wollah inaji ko rantsuwa
nayi ba zan yi kaffara ba...kalli ki ga lokaci daya yadda idonta ya canza...anya ma ni kuwa ba su bane....."
saurin dakatar da ita Mairo ta yi ta ce
"Hadi ki bar maganar nan a nan dan ban shiryawa mutuwa ba, zo mu tafi" Mairo ta fizgi hannun Hadi.
Sun ɗan yi tafiya Hajja ta tsaya, Aziza tasa hannu tana sharewa Hajja hawaye tare da fadin
"Kiyi hakuri Hajja, dan kuka mai ja wa uwa jifa ko Hajja!?" Aziza ta faɗa tana fashewa da kuka, Hajja ta ce
"A'a Aziza, har ga Allah ni har zuciyata ban taba zargin yarana ba, na san ni dai mutane na haifa"
"To me yasa kike kuka Hajja?"
19
HAUSACINEMA.COM
"Saboda dukkan uwa ta gari ba zata so a dinga sokin yaranta ba! Har raina nake jin zafi" Hajja ta fada
tana mai kamo hannun Aziza, wani tausayin mahaifiyarsu ne ya ɗarsu a zuciyar Aziza, duk yadda take
tausayawa kanta da yar uwarta tafi tausayin Hajja, ranar da zata gane cewa su din ba mutane bane
MACIZAI NE ranar da zata san duk kisan da ake yi Azima ke yi, shin ya dace ta ci gaba da boyewa Hajja
cewa su ba mutane bane? Ko dai ta fito ta gayawa Hajja da Baffa gaskiya? Kai amma kuwa gunduwa-
gunduwa za ayi dasu, sannan Azima ta ce ko da ta faɗi ba shi zai hanata cika burinta ba! Girgiza kai Aziza
ta yi ta sake rungume Hajja tana kuka, Hajja zata yi magana suka ji nishi na tashi ta gefensu wanda yake
ciyawa ne kore shar a wajan, saurin maida hankalinsu suka yi, Aziza ta ce
"Hajja kamar fa nishi nake ji?"
"E nima naji Aziza, kamar ta nan yake fitowa zo mu duba mu gani" suka yanki gefen ciyawar, wani yaro
suka gani kwance fuskarsa ta koma blue bakinsa sai fitar da farin kumfa yake yi tare da jini, salati Hajja ta
saka, da sauri Aziza ta dagosa tana kallonsa tare da jinjigasa, gefen wuyarsa ta kalla ta ga saran maciji,
wanda bata raba dayan biyun AZIMA ce, girgiza kai ta hau yi cikin tashin hankali, ta buɗe baki, Hajja ta ce
"Aziza me ya faru da shi?"
"Hajja maciji ne ya saresa, bari na gwada yi masa magani" kasancewar lokuta da dama Aziza na gwada
wa Hajja kamar tana magani wanda Hajja ke danganta hakan da nasaban Baffa, bata jira Hajja ta yi
magana ba ta hura iska a bakinta ta rufe ido gam na wasu daqiqu sannan ta buɗe, yayinda idon ya koma
fari sol, hannu tasa a bakinta ta dibo farin yawu ta gogawa yaron a wuyarsa dai-dai shatin saran, sannan
ta koma kallonsa, duk fuskarsa ta yi blue, tana saka masa ya hau gurnani yana murkususu sannan ya
koma ya yi ɗifff! Hajja ce ta daga hannunsa ta ga ya koma, da sauri ta janye Aziza ta ce
"Aziza zo mu bar nan wajan"
Kallon Hajja Aziza ta yi cikin damuwa ta ce
"Hajja taya zamu barsa bayan yana buqatar taimako,ki bari na taimaka masa Hajja kar ya mutu"
"Ai ya riga da ya mutu Aziza! Ki zo muje kar ace kece kika masa wani abun"
20
HAUSACINEMA.COM
Suman tsaye Aziza tayi tun sadda Hajja tace ai ya riga da ya mutu, kallon yaron kawai take yi, hannu
Hajja tasa ta ja Aziza da sauri suka bar wajan basu tsaya ko ina ba sai gida, suna shiga gida Aziza ta shige
bukkansu bata ga Azima ba, duk yadda akayi tana rafin jimulo, hannu tasa ta goge hawayenta tare da
daukar mayafinta, Hajja ta juyo zata bata ruwa ta ga ta fice a gidan da sauri Hajja ta bi bayanta tana
fadin
"Aziza! Ke Aziza!? Azi..." Hajja bata karasa ba sakamakon dakatar da ita da Aziza ta yi, ta rufe mata ido ta
hura mata iska, haka kawai Hajja ta tsinci kanta da komawa gida, Aziza kuma hanya ta yanka ta yi rafin
jimulo, a yadda take tafiya zaka gane cewa ba mutum ba ce, haqiqa yau Azima ta kai ta karshe! Me
wannan karamin yaron ya mata da zata kashesa!.
Tana isa rafin ta kwala kiran sunan Azima.
"AZIMAAAAA!" sulalowa Azima ta yi hannunta dauke da mangoro fuskarta wasai, ganin fuskar Aziza ya
sakata sakin baki dan bata taba ganin