Showing 9001 words to 12000 words out of 94205 words

Chapter 4 - Azima-Da-Aziza-Macizai Ne Complete

20 Jul 2024

37832

fuskarta a haka ba

"MACIJIYA AZIZA LAFIYA!" Azima ta fada cikin halin ko in kula.




"AZIMA ME YARON DA KIKA KASHE YA MIKI!?"




kyalkyalewa da dariya ta yi ta ce

"Sabida ya cancanci ya mutun ne, saboda ya ganoni, kuma yace sai ya faɗa kin ga kuwa dole na kashe sa
tunda...." dauketa da mari Aziza ta yi, tana dagowa ta sake kai mata wani marin, ran Azima ya tunbatsa
nan ta riƙiɗe ta koma macijiya,in da ita ma Aziza yau ta rikiɗe ta zama macijiya fara sol, nan dambe ya
kaceme.




Da washe gari asubanci yankin jimo suka yi, takwas na safe su na yankin kwana,a maƙabarta jikin ƙabarin
Jarman macizai, kuka sosai sarki Haruna yake yi shi da jama'ar yankinsa wa inda suka zo, an sha musu



21
HAUSACINEMA.COM


mutuwa amma farat ɗaya na Jarman macizai wanda yake jarumi a yankinsu ya gigita tunaninsu, haka
suka ƙarashi koke-kokensu suka gama dan ba dawowa zai yi ba, haka jamar'ar kwana suka taru ƙwansu
da ƙwarƙwatansu suka sake yiwa yankin jimo ta'aziyya tare da ban hakuri, daga fuskarsu kawai zaka kalla
ka gane su na cikin mugun damuwa da tashin hankali, babu yadda yankin jimo suka iya dole suka hakura
tunda dai Jarman Macizai ba dawowa zaiyi ba ya tafi kenan, sai dai fatan Allah ya yafe masa.




Bayan kwana biyu an gama ƙuri'u, inda aka samu sab'anin ra'ayi, jama'ar da suka fi rinjaye shine wa inda
suka ce aje yankin ja'i neman taimako kar aje yankin tudu a fara zuwa yankin ja'i, dan ba za a zauna da
matsala ba tare da an bukaci taimakon Allah da wa inda zasu shawo kan matsalar ba, shi dai Baffa shuru
ya yi bai ce kanzil ba, haka aka sa mai rubuta wasika ya rubuta aka yiwa yankin ja'i aike da shi.




Sarkin fulanin yankin ja'i na zaune Maga Isar da Sakon yankin ya zo ya zube a gabansa yana fadin

"Allah ya taimakeka! Hakika a yau nasara tamu ce" wazirin fulani ya ce

"Maga Isar da Sako meke tafe da kai ne?" murmushi Maga Isar da sako ya yi ya ce

"Hakika yau muke da nasara, sako ce ta isko mu daga yankin kwana! su na cikin bala'i shine suke bukatar
taimako daga yankinmu, yanzu haka ga takwabi sarkin kwana wato Chubaɗo ya aiko mana da shi alaman
sun sakar mana igiyar, munyi nasara su sun faɗi, wannan takwabi da Chubaɗo ya aiko mana da shi alama
ce na sun duƙawa wannan yanki tamu"




22
HAUSACINEMA.COM




Sarkin fulanin yankin ja'i ya ce

"Maga Isar da sako, zai fi kyautuwa da kayi mana bayani dalla-dalla, ko kuma ka buɗe wasikar da suka
aiko da shi ka karantawa dukkan wanda yake zaune a wannan fada dan jin meke tafe da sakon"




Ƙara russunawa Maga Isar da sako ya yi ya buɗe wasikar ya fara karantawa kamar haka.




" _ASSALAMU ALAIKUM, SAKO CE DAGA YANKIN KWANA IZUWA YANKIN JA'I, MUNA FATAN WANNAN
SAƘO TA ISA GAREKA SARKIN FULANIN JA'I WATO SARKI JAWO TARE DA MAI UNGUWAR YANKIN JA'I
WATO MAI UNGUWA SODANGI, A YAU MU YANKIN KWANA MUN WAYI GARI CIKIN RUƊU DA RUƊANIN
TASHIN HANKALI DA RASHIN ZAMAN LAFIYA, WA HAKA NE MUKA RUBUTO SAƘO DAN YA YI TATTAKI
ZUWA GA YANKIN JAMA'AR DA SUKE JA'I GABAƊAYA, AMADADIN NI SARKIN FULANIN YANKIN KWANA
CHUBAƊO DA MAI UNGUWAR YANKIN KWANA ORI, DA ARƊO DA TSOHON SARKIN FULANI MANDI, DA
MAGAJI BAWA DA DUK WANI WANDA YAKE YANKIN KWANA MUNA NEMAN TAIMAKONKU! MUN
GAMU DA IFTILA'IN MACIZAI WANDA SUKE KASHE MANA MUTANE! AN KASHE DUK WASU MASU KAMA
MACIZAI NA YANKINMU! MUN NEMI TAIMAKON YANKIN JIMO INDA SUKA TAIMAKA MUKA ROƘI
ALFARMA DA JARMAN MACIZAI YA KAWO MANA DAUKI WANDA SHI MA AKA KASHESA KWANA BIYU DA
YA WUCE, GA WANNAN TAKWABIN DA MUKA AIKO YANA NUNI NE DA MUN ZUBAR DA MAKAMAN
YAƘIN GABAR DAKE TSAKANINMU NA TSAWON LOKACI MUN DUƘAWA YANKINKU, MUN YARDA KUNYI
GALABA A KANMU! BA DAN KOMAI BA, SAI DAN MUNA NEMAN ALFARMA DA A TAIMAKA MANA DA
TAIMAKON INNU MACIJI MUN SAN SHI KA ƊAI NE KAWAI ZAI IYA, TUNDA HAR TA ALJANUN MACIZAI DA
MAYU DA ALJANU DUK YANA FAƊA DASU, DAN ALLAH SARKI JAWO DA MAI UNGUWA SODANGI A
TAIMAKA MANA, KANMU A ƘASA! A YAU MUN YARDA YANKINKU YANA SAMAN TAMU, SAƘO DAGA
YANKIN KWANA, SAI MUNJI DAGA GAREKU, MUN GODE_"




Wani murmushi sarkin fulanin ja'i ya yi yana mai kallon Maga Isar da Sako,yayinda jama'ar ja'i suka hau
murmushin nasara, dan sun jima suna neman cin galaba a kan yankin kwana amma sun kasa, hakan ya
samu asali ne da nasabar da Baffa yake da shi,amma wai yau sai ga shi su da kansu suke cewa sun zubar
da makaman yaƙinsu? Wannan ai nasara ce babba a garesu, wakilin yankin ja'i ya ce




23
HAUSACINEMA.COM


"Allah ya taimakeka! Ai mu nasara ce ta tako da kafarta tazo mana har gida, wai shanu daga sama
gasheshshe!"




Wazirin ja'i ya ce

"Ai ranka ya daɗe abunda muka jima muna nema ne, shine suka sakar mana shi yanzu,tun yaushe muke
neman nasara a kan yankin kwana amma mun kasa samu sabida Magaji Bawa" wazirin fulanin ja'i ya
karasa maganarsa yana murmushi, wakilin fulanin ja'i ya kuma cewa

"Ranka ya daɗe kar mu b'ata lokaci kawai mu amsa da cewa e mun amince da bukatarsu" girgiza kai
garkuwan fulanin ja'i ya hau yi ya ce

"Shekara da shekaru ake ɗibi ba daɗi tsakanin yankinmu da yankin kwana, rana daya tak su aiko mana
da sako su ce sun janye anya babu lauje cikin naɗi? A gaskiya ni ban yarda da yankin kwana ba, sai dai
wani shirin kawai suke yi ta yadda zasu shafemu!" garkuwan fulanin ja'i ya karasa maganarsa yana haɗa
rai sosai, sarki Jawo ya ce

"Bana tunanin haka! Idan ma kuma hakane karka manta muna da fidda kunyar gasa a yankin nan wato
INNU MACIJI wanda a halin yanzu shi suke bukatar taimakonsa,Innu Maciji dai duk faɗin yankuna sun
san shahararsa! Tunda shi ya lashe kambu na daya a gasar fidda gwajin macizai! Innu Maciji bai ci
sunansa a banza ba! Tunda har aljanun maciji da mayu yana yaƙi dasu kuma ya ci nasara, dan haka idan
muka tura Innu Maciji dan zuwa taimakawa yankin kwana kamar yadda suka bukata yaje ya dawo ya
kake tunanin martaban da yankin ja'i zai samu tare da karramawa daga sauran yankuna?"




Ajiyar zuciya Garkuwan fulanin ja'i ya sauke tare da kallon Sarki Jawo ya ce

"Ranka ya daɗe bana so mu manta da abu daya, a lokacin da aka raba kambu Magaji Bawa ya jima da
sauke duk wata gab'ob'in baiwa da yake da shi, na san idan har zaka manta da tarihin Magaji Bawa da
Tsohon sarkin ja'i ya baka ba zaka manta da sunansa da ya shahara a sauran yankuna ba, GWARZON
DAFIN MACIZAI!! ka tuna?" Garkuwan fulanin ja'i na furta wannan kalma sai da mutanen da suke wajan
suka firgita, Wakilin Fulanin Ja'i ya ce

"A gaskiya na so na yarda da maganarka Garkuwan ja'i! Me yasa Magaji ba zai yi wani abu a kai ba da
zasu dinga bukatar taimakon yankuna! A da shi Magaji a ina ne bai yi taimako ba, gaskiya maganarka
abun dubawa ce" Maga Isar da sako ya ce




24
HAUSACINEMA.COM


"Amma shekaru ashirin Magaji Bawa ya ce ya daina duk wani abu na yaƙe-yaƙe da yake yi, bayan ya
sauka ne shine aka naɗa Firi jarumin yankin kwana ko ba haka bane? Ni a tunanina da ace Magaji Bawa
zai iya wani abu a kai da ba za a zo neman taimakon Innu Maciji ba har su russunawa yankin nan"




"Amma dai kun san da cewa duk wata shahara da Innu Maciji zai yi ba zai taba kamo ko da tsilen
takalmin Magaji Bawa ba ko?"




Maga Isar da sako ya ce

"Ni dai bana tunanin haka gaskiya, da ace zai iya da ba zasu zo nan ba" Sarki Jawo ya ce "tabbas haka ne
maganarka Maga Isar da sako, yanzu abunda za ayi,aje a cewa mai unguwa Sodangi akwai magana ta
gaggawa, a biya a kira Innu Maciji, a rubutawa yankin kwana da cewa su tsumayemu zuwa gobe idan
muka gama shawara da tattaunawa zamu tura musu da sako idan ma mun amince ko akasin haka"
Sarkin fulanin Ja'i yana gama magana ya miƙe tsaye ya bar wajan.




YANKIN KWANA




Maga Isar da sakon yankin kwana ne ya gama karanta wasikar da yankin ja'i suka aiko musu da shi, sarki
chubaɗo ya ce

"Ba komai yau da gobe duk daya ne a wajan Allah, Allah ya nuna mana" mai Unguwa Ori ya ce

"Amma Allah ya kara maka yawan rai, anya yankin ja'i zasu yarda su taimakemu kuwa? Gani nake kamar
su na neman hanyar da zasu wofantar da bukatarmu ne, tunda mun sanar dasu yankin jimo sun rasa




25
HAUSACINEMA.COM


jarman macizai, da mun sani da bamu rubuta musu da cewa an kashe jarman macizai ba" Arɗo ya girgiza
kai ya ce

"Maganar duniya bata b'uya, gwanda dai da muka gaya musu gaskiya zai fi, balle kuma abu babba irin
haka ya faru ace manyan yankuna basu sani bane? Ai hakan ma ba mai yuwa ba ce, dan naji ance yankin
gangare da yankin jauro da yankin ulela da yankin nasare duk sunje yiwa yankin jimo ta'aziyyar jarman
macizai"




Sarki Chubaɗo ya ce

"Mu jira har zuwa goben muji sakamakon abinda zasu ce" Arɗo ya yi murmushin karfin hali ya ce

"Bana tunanin yankin ja'i zasu wofantar da bukatarmu! Abunda muka jima da sanina suna neman yankin
kwana ta duƙa musu, sai ga shi laluri tasa duk taurin kan da fulani ke da shi mun russuna musu da muka
ji uwar bari, dan muna da bukatar mu san waye ba mutum ba a yankin nan! WAYE MACIJI! a yankin nan!
Dole azo ayi gwaji dan a fidda zargin juna a zukata, gwanda a nuna mana inda matsalar take mu kuma
mu san ta inda zamu shawota"

Aka amsa da haka ne,nan dai suka gama tattaunawa suka ajiye maganar tasu akan su saurari yankin ja'i.

Bayan an watse a fadar Sarki Chubaɗo Arɗo da Baffa ne suke tafiya a hankali su na magana kasa-
kasa,Arɗo ya ce

"Magaji, fatan kana sa a ido sosai a kan su AZIMA DA AZIZA?"

"E Arɗo ina iyakar bakin kokarina wajan saka musu ido, ita Azima baka iya gane gabanta,gwanda Aziza,
gasu dai a tare aka haifesu amma halayyarsu ta sha bamban, a kwana biyun nan basu kula juna, Jumala
sai korafi take yi a kan nayi musu magana ko me ya haɗa su, amma ban dauki hakan da mahimmanci ba
sabida ba shi ya kamata na kula ba, kare rayukan yankin nan shine abu mafi mahimmanci" Arɗo ya gya
ɗa kai ya ce

"Tabbas hakane, ba mamaki sun ɗan yi faɗa ne tinda ana samun irin haka" Baffa yace

"Eh nima haka nake tunani Azima bata da dadi ko kadan, Arɗo barin wuce gida"

"To a gaida Jumala da Azima da Aziza"

"Zasu ji" Baffa ya fada tare da yiwa Arɗo sallama.




26
HAUSACINEMA.COM


Tun safe Aziza ke rafin jimulo tana wanke kayan Hajja da na Baffa, Azima kuwa dan Aziza na rafin jimulo
yasa ita bata je ba tana gida, abinci Hajja ta ɗora amma Azima ta hana abincin dahuwa, har la'asar tana
zaune a kan tabarma kaba tana saƙe wani igiyoyi, Hajja ta kalleta ta ce

"Wai ni kam Azima wannan saƙe-saƙen da kikeyi na miye ne? Tun safe kike zaune a wajan ba sallar
azahar bare la'asar ki tashi kiyi sallah" ba tare da ta dago ta kalli Hajja ba ta ce

"BANA SALLAH!"

Baki sake Hajja ta kalli Azima ta ce

"Kina fashin sallah ne?" kafin Azima ta bada amsa Aziza ta yi sallama da kaya a hannunta ta shige bukkan
Hajja ta ajjiyesu sannan ta fito ta duƙa ta ce

"Sannu da gida Hajja"

"Yawwa sannu Azizatuna, kin dawo?"

"E Hajja na dawo"

"Ayya Aziza maimakon idan kin wanke kayan ki dawo gida idan ya bushe anjima a kwaso shine kika
zauna har yamma a rafi ba tare da kin dawo gida ba? Ga shi haka kika fita ba ki ci komai ba" murmushi
Aziza ta yi a ranta ta ce

"Idan na so zan iya wanke kayan nan na busar da shi a lokaci guda sabida karfin dafin da nake da
shi,amma bana son hakan nafi son na samu ladar iyayena" a fili kuma ta ce

"Wlh ba komai Hajja bana jin yunwa ai"

"Allah ya miki albarka Aziza ke da yar uwarki, kinyi sallah ne?"

"Amin, E Hajja nayi sallolina a rafin jimulo ban bari lokaci ya shige ba" Hajja ta kalli Azima ta ce

"Azima kince baki sallah kina fashi ne?" da blus eyes dinta ta dago ta kalli Hajja ta ce

"Ni sallah ne kwata-kwata bana yinsa a rayuwata!" dam!dam!dam! Ƙirjin Hajja ya bada ta b'ata shuru
tana bin Azima da kallo, da kyar ta buɗe baki zata yi magana amma Azima bata jira hakan ta faru ba dan
kamar ƙiftawar ido ta tashi tare da tattare dogon igiyar da ta saƙa ta shige bukka, Aziza ganin yadda
hankalin Hajja ya tashi da maganar da Azima ta faɗa ya sakata faɗin

"Karya take yi Hajja, kin san halinta bata damuwa da maganar da zata faɗi zai yi maka dadi ko akasin
haka faɗi kawai take yi" sai a lokafin Hajja ta sauke ajiyar zuciya, Aziza ta ƙwaƙulo murmushi dan sallah
kam Azima baya yi, ta ce



27
HAUSACINEMA.COM


"Hajja ba a gama abinci ba?"

"Wollah Aziza ban san wani irin abinci yau nake dafawa ba, tin rana na ɗora kafin ayi azahar amma har
yanzu ta ƙi nuna" shuru Aziza ta yi tana kallon tukunyar kasan na wani sakanni kafin ta ce

"To Hajja je ki ciki ki huta yanzu zan karasa"

"A'a Aziza yanzu fa kika dawo daga...."

"Ohh dan Allah Hajja ki je ki huta" murmushi Hajja tayi tana shigewa bukka, Aziza ta buɗe abinci ta ga
rashin dahuwarsa yana da nasaba da sa hannu da Azima ta yi, rintse ido ta yi ta buɗe nan idonta ya
koma fari sosai ta zaro harshenta ta hura wani hayaki a cikin tukunyan, nan kalar abincin ya canza
alaman ya dahu, sannan ta rufe tana miƙewa tsaye ya yi dai-dai da shigowar Baffa da kuma fitowar Hajja
daga bukka, sannu da dawowa suka masa, Baffa ya amsa yana zama a inda Azima ta tashi, kallon baƙin
igiyar da Azima ta yi saƙa da shi ya gani guntun, dauka ya yi a fili ya ce

"Zaran saƙar dana? me yake yi a gidan nan? Wa ya kawo?"

"Zaran saƙar dana kuma?" Hajja ta faɗa tana kallon hannun Baffa da ya riƙe zaren yana kalla, Aziza ce ta
matso kusa daBaffa ta duƙa ta ce

"Baffa me zaran ya ƙunsa?" shuru Baffa ya yi na wasu lukota kafin ya ce

"Ba ƙaramin hatsari wannan zaren yake da shi ba, ana amfani da shi wajan yaƙi! Ko kuma a ɗaure
takwabi da shi, duk wanda aka sara ko aka yanka da takwabin da aka d'aure da shi to sunansa gawa!
Walau mutum ko aljan! " a firgice Aziza ta ce

"Kenan mutum mutuwa zai yi?"

"E Aziza, wa ya kawo zaran nan gidan nan? Sannan ta ya aka samo shi? Dan nasan ba a samunsa nan
kusa sai an je can cikin jejin lore, wanda wannan jeji tun kafuwarsa shekaru aru-arubabu wani ɗan adam
din da ya taba zuwa idan ba ni ba"Hajja ta ce

"Ai kuwa dai Azima ce na ganta da shi dan tun safe take zaune a inda ka tashin nan take saƙa shi,bayan
ta gama ta shige ciki, bata jima da shiga ba ka shigo" da sauri Baffa ya miƙe tsaye ya ce

"Azima! Azima! Azima!?" ya kwala kiran sunanta da karfi, Aziza ta ce

"Bari na kirata Baffa" cikin faɗa Baffa ya ce

"Nan da bukka ta ce bata jin kiran da na mata?" Hajja ta ce

"Ayye Baffan yan biyu ka bi a hankali mana, watakila bacci ne ya kwasheta Aziza kirawota"Baffa ya ce



28
HAUSACINEMA.COM


"Ke da kika ce ina shigowa bata jima da shiga ciki ba shine har bacci zai kwasheta?"

"Ai Azima bata da wuyan bacci" cewar Hajja, shi dai Baffa shuru ya yi tare da gyara tsayuwarsa ya maida
hannunsa baya yana jiran fitowar Azima.

Tana kwance a gadon kara, rabin jikinta macijiya sai juyi take yi kanta a hargitse, Aziza ta shigo da
sallama ko amsawa Azima bata yi ba, Aziza ta ce

"Ba ki jin Baffa na kiranki ne?"

"Mtswwwww! Na ji mana, tunda dai ni ba kurma ba ce! Je ki ce ba zan zo ba!" a fusace Aziza ta sa
hannnu ta janyo wuyar Azima ta ce

"Wallahi!

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login