Showing 54001 words to 57000 words out of 94205 words
Mom suka yi da ita, ga shi ita ba zata iya gaya musu gaskiya a kan ƙaryar da ta
musu ba, ta rasa yadda zata yi, ga shi a wannan lokacin tana da bukatar ta canza wani gari ko Allah zai sa
a dace.
akwai ranar da suke hira da Sultana take gayawa Aziza zasu je zaria bikin ƙawar Sultana din, to yanzu
shirinta idan suka je bikin daga nan kawai ta gudu,idan har ta duba bata ga Azima a zarian ba, to zata
sake canza wani gari, dan yanzu alhamdulillah ko da Mom ba ta bata kudin aikinta ba, a kudin da take
122
HAUSACINEMA.COM
samun alkairi ya isheta yawatawa neman 'yar uwarta, bare kuma alkairin da su Mom suka mata yafi
abunda zasu bata sau dubu dari.
Ta bangaren Azima itama tana nan ta zama wata iri da ita, sai faɗi take yi ta shigo gidan da ya dameta
duk sadda ta shigo gidan taji kamar an ɗaureta, ga shi duk yadda ta ci burin hawa can sama part din
AL'MAZEEN abun ya ci tura, ala dole ta yi hakuri tana jiran dawowarsa,dan ta fara jin ƙishin-ƙishin a
bakinsu Maman Hanan cewa nan da wata shidda AL'MAZEEN zai dawo, dan haka Azima ta koma
tsumayin jiran dawowar Al'mazeen.
Yau saura kwana uku su tafi zaria, Aziza na zaune Sultana ta shigo da sallama da waya a kunnenta
hannunta dauke da kaya ta zuba a kan cinyar Aziza,kaya ne kala shidda kala uku iri daya, Aziza ta hau
ɗaga kayan tana mamaki, zama a gefen gadon Sultana ta yi, tana ci gaba da wayarta bisa alama kuma da
ƙawarta wanda za ayi aurenta suke waya, sai da ta gama wayar tsaf ta tabbatar mata cewa gobe da wuri
zasu fito kana suka yi sallama,sannan ta waigo wajan Aziza ta ce
"Azizi baby, ga anko ɗinmu fa"
"Ankonmu kuma?" Aziza ta faɗa tana cikin mamaki tana ɗaga kayan, Sultana ta ce
"E mana, zamu je bikine ba tare da kinyi anko ba? Wlh muna zuwa zaki zama kamar bare, shiyasa da na
tashi na cewa Bros Nawaz ya turo mana da kudi nayi mana mu biyu" shuru Aziza ta yi sai kuma ta sa
kuka, Sultana ta ce
"Miye haka kuma Aziza?" cikin kuka Aziza ta ce
123
HAUSACINEMA.COM
"Anty Sultana, anya dawainiyyar ba zaiyi yawa ba? aiki nake muku amma kun maidani tamƙar yar gida, ni
kuwa dame san saka muku? Sai dai na bi ku da addua ke da Mom,Allah ya saka muku da mafificin alkairi"
hannu Sultana tasa tana sharewa Aziza hawaye ta ce
"Ni da Mom kawai? Shi kuma Yaya ɗin fa! Yana yawan tambayarki wlh idan muna waya da shi, Aziza kin
riga da kin shiga ranmu ne wlh, muna jinki ne a jikinmu, shekaran jiya Mom ke faɗamin cewa ita tana
miki kallo ne tamkar ita ta haifeki,kuma tana tausaya miki na rashin iyaye da yan uwa da kika yi, tace ba
zata taba wulakantaki ba, dama wulakanci mu ba halinmu bane, duk wanda ya riƙe maraya tsakani da
Allah,Allah zai ba shi lada, In sha Allahu ko neman aurenki aka zo yi ba zamu taba cewa ke ba yar gidan
nan bane, Allah ne ya saka mana kaunarki a ranmu, sabida hankalinki da natsuwarki, wlh Aziza ina jinki
tamkar kanwata uwa daya uba daya, a rayuwata ina son na ganni da ƙanwa, amma ana haifata Allah ya
dauki ran mahaifinmu, har kwanan gobe Mom taki kara aure, Yaya shike mana komai da shike Allah ya
dafa masa, idan har Allah ya baka dama da dukiya amfaninka shine kai ma ka taimaki wa inda basu da
shi, dan haka ki daina sa damuwa a ranki ki saki jikinki nan gida ne, bari naje nayi waya da My Khalil"
share hawayen da ya sake zubo mata Aziza tayi ta ce
"Na gode sosai Anty Sultana, Allah ya shayar daku ruwan alkausara, Sultana ta amsa da amin tana fadin
"An fa fara maganar tsaida aurena,wlh ana maganar sai da naji zuciyata ta buga"
"Kai Anty Sulty waya gaya miki?"
"Nima ba gaya min akayi ba,dazu ne zan shiga dakin Mom naji suna magana da Hajiyar su Khalil, akan
cewa za a tsaida lokacin bikin"
"To shi da baya kasar ma?" Aziza ta faɗa tana ninke musu anko din, Sultana ta ce
"To nima dai naji Mom na cewa a bari sai Yaya ya dawo, kin san fa sun kusan dawowa gida gabaɗaya,
shima Khalil din ya kusan dawowa, wai ko kuma a tsaida ranar sai ya kasance lokacin da zasu dawo kar
bikin ya wuce saura wata biyu, na dai ji Mom na cewa wata takwas ko wata tara,kafin nan sun dawo
dukkansu kuma sun huta" Aziza ta gya ɗa kai tana fadin
"Allah ya tabbatar mana da alkairi"
"Amin ya Allah, da bikina fa ke ce zaki yi min babbar ƙawa wlh" Aziza na shirin magana wayar Sultana ya
dauki ruri tana dubawa ta ga Khalil ɗinta, da sauri ta miƙe tana fadin
"My love ya yi kira sai anjima" tana fadi ta fice da gudu, Aziza kuwa ware idanunta tayi tana jinginuwa da
bango sabon hawaye na sake zubo mata, komai yana shirin kwab'e mata, kawai mafita shine zatayi
addua Allah ya zaba mata abunda yafi mata alkairi,bata so sam Nawaz ya dawo ya sameta a gidan, dan
haka taja akwati ta haɗa kayanta tun daga yau, anko din kuma dakin guga ta yi dasu idan aka goge sai ta
miƙawa Sultana nata.
124
HAUSACINEMA.COM
Yau ce ta kama ranar da zasu tafi zaria, gaban Azizake dukan uku-uku tun farkawarta bata da
kuzari,ganin haka yasa Mom cewa Aziza meke damunki ne?
"Ba komai Mom"
"A'a Aziza karya ba halinki bane, karki fara meke damunki?" a sanyaye ta ce
"Kaina ke ciwo Mom"
"Subhanallahi! Idan ba zaki iya tafiyar ba ki bar shi ki huta abunki ita mai biki sai ta tafi" nan Sultana ta yi
tsalle ta dira da cewa wlh Aziza bata isa ba,kawai dai son mutane ne da bata yi, Mom ta ce
"A'a Sultana baki zo da gaskiya ba, yarinya tace miki bata da lafiya kice bata isa ba,kinga wuce ki tafi
kawai Allah ya kiyaye hanya" Sultana tace ita kuwa idan har Aziza ba zata je ba itama ta fasa, Aziza ta ce
"To ba kin riga da kin gaya mata yau kina hanya ba?"
"Sai na ce mata na fasa , kuma ai ba ina hanya nace mata ba muna hanya nace mata"
Aziza ta yi murmushi ta ce
"A'a ba za ayi haka ba Antyna ta kaina tashi mu tafi" Mom ta ce
"Ki biyewa Sultana ki kashe kanki"
"A'a mom ai nasha magani, ciwon kan zai sakeni"
"To Allah ya kiyaye hanya, a gaida su Hajiya Habiba, ai da ace zaku biya ta kano da na baku sako wa su
Hajiya Lawiza" haɗe rai Sultana ta yi ta ce
"Gaskiya Mom ba zamu kano ba, daga zaria sai kaduna In sha Allahu" ganin yadda Sultana ta haɗe rai
yasa Mom dariya ta ce
125
HAUSACINEMA.COM
"To shikenan Allah ya kare" ta faɗa tana rakosu har jikin mota, ta ce
"Ina dai ba zaku wuce kwana biyun ba ko?"
"In sha Allah Mom ba zamu wuce ba,ai ba zamu je mu zauna mu barki ke ɗaya ba" daga haka driver ya
jasu ,Mom tana ɗaga musu hannu.
Kasancewar tsakanin kaduna da zaria ba nisa nan da nan suka isa aka hau shagali dasu, haka sauran
ƙawayen amarya Sulaiha suka ja Aziza a jiki, amma matsalarsu daya da ita shine rufe fuskar da take yi, sai
da Sultana tace musu ai ko a gida ma haka take wuni fuska a rufe kasancewar tana da matsalar ido, daga
haka suka fara yi mata fatan sauki, sai yaba kyawunta sukeyi da dogon gashinta,ita dai Aziza nata
murmushi da godiya, dan duk tunaninta ya raja'a a ta hanyar da zata bi ta gudu, dan suna isowa zaria
bata yi kasa a guiwa ba ta duba amma bata ga Azima ba, yanzu garin da take hari taje shine garin da
Mom tace zata aiki Sultana idan har zasu je, wato KANO.
Ranar da suka zo anyi party da washe gari asabar aka ɗaura aure, bayan an daura aure da daddare akwai
dinner daga wajan dinner za a wuce da amarya gidan mijinta da washe gari kuma sai su koma kaduna, a
daren yau idan suka je dinner shine Aziza tasa a ranta zata gudu.
Sun sha makeup dinsu, suka cakare cikin net dinsu kalar sky blue sunyi kyau sosai,ita dai Aziza taƙi yarda
ayi mata makeup har amarya Sulaiha take fadi cikin wasa ai ita da kyau ɗinta ba sai an mata kwalliya ba
tunda bata so a barta.
Suna can babban hotel din da aka kama ana ci gaba da gudanar da abunda ya tara jama'a, Khalil ya kira
Sultana a waya kasancewar bata ji a ciki yasa ta fito waje tana wayar.
126
HAUSACINEMA.COM
Wasu maza ne su uku a wajan gate din hotel din suna cikin mota sai aikin busa hayaki suke yi, wani ne ya
daga ido daga cikinsu ya sauke a kan Sultana dake waya, sai da ya kara goge idanunsa kafin ya ce
"Kaii Ɗan Gidan Alhaji? Wa nake gani a can kamar kanwar Doctor Nawaz?" wanda aka kira da sunan Ɗan
Gidan Alhaji ya dago yana ƙarewa Sultana kallo ya ce
"Jar Uba! Ita ce wallahi! To me ya kawota zaria?" ɗayan ya ce
"Ko ma me ya kawota, lokaci ya yi da zamu rama abunda Yayanta ya mana a kanta" Dan Gidan Alhaji ya
ce
"To yanzu ya kuke ganin zamuyi?" dayan ya ce
"Ah mu kwamusheta kawai,muje mu huta da ita, ya ɗanɗani abunda mukaji sadda yasa aka kullemu a
kan wasu banzan talakawa!"
"Lallai Shaho ka kawo shawara, kuma dabadin Baban Ɗan Alhaji ba wlh da mun ƙare rayuwarmu a
kurkuku" Dan Gidan Alhaji ya ce
"Yanzu ku daina wannan maganar tunda ba mutane yanzu a kusa ku fita ku dauko mana ita" sai da suka
leka suka leka kafin suka fito daukar Sultana wanda hankalinta ya yi nisa sosai a wayar da take yi da
Khalil.
Aziza na zaune cikin kawaye da ta waiga ido bata ga Sultana ba ta tashi a hankali tana fadin
"Ki yafeni Anty Sultana zan tafi, ba zai yu ba rayu daku ba danni ba mutum bace,zanje neman yar uwata
dan mu koma duniyarmu!"
Da wannan tunani zuciyarta babu dadi kamar karta tafi dan an saba, ta fito saɗaf-saɗaf.
127
HAUSACINEMA.COM
Fitowar Aziza ya yi dai-dai da lokacin da su Shaho suka roɗa ma Sultana katako a bayan kai a kan idon
Aziza,ihu Aziza ta saka tana fadin
"Antyyyy Sultanaaaa!!!" ganin haka yasa Ɗan Gidan Alhaji Faɗin su haɗa da Aziza su kwamuso.
Dan haka suka bugawa Aziza katako a kai sau daya,jiri ne ya ɗibeta amma bata suma ba, ta hau kokawa
dasu dan ta kwace Sultana daga hannunsa, Shaho yasa katako ya dinga sauke mata shi a gefen kai har ta
suma kanta ya fashe yana zubar da jini, sannan suka daukesu suka saka a mota.
Basu zarce ko ina dasu ba sai wani gidan Ɗan Gidan Alhaji da Babansa ya gina masa, suna zuwa su Shaho
suka fito dasu Sultana da Aziza wanda suke sume, suka shige dasu, suna shiga dasu suka kwantar dasu a
parlour, D'an Gidan Alhaji ya ce a bari su farka, Shaho yace ba sai an jira sun farka ba dan babu lokaci, a
yayyafa musu ruwa kawai su farka, ga wannan yarinyar ba mamaki ita ma kanwarsa ce dan naji ta kiran
wannan da Anty, wai cakwai kenan gata kirjinta a cike yake,yaran dai za a shana fa" Dan Gidan Alhaji ya
yi murmushi yana lashe baki tare da binsu da kallo, Shaho ne ya kawo ruwa cikin bokati ya shekawa su
Sultana da Aziza tun daga kansu har kafarsu, a firgice Sultana ta farka ita ce ta fara dawowa hayyacinta
tana riƙe bayan wuyarta dake mata tsami, ware idanunta ta yi a kan Ɗan Gidan Alhaji, tayi saurin ja da
baya tana girgiza kai,tana juya idonta ta sauke shi a kan Aziza wacce bata riga da ta farka ba, a razane
Sultana ta hau jijjiga Aziza tana kuka tana kiran sunanta ganin yadda jini ke b'ulb'ula a kan Aziza, cikin
kuka Sultana ta ce
"Wlh idan Yayana ya sani dukkanku babu wanda zai tsira" D'an Gidan Alhaji ya ce
"Kafin nan Ubana ya min biza na bar kasar, kuma ko da zai sani sai mun miki mummunar tab'o,ko nace
sai munyi muku mummunar illa!" Ya fada yana sa hannu zai damki Sultana Aziza ta cafki hannunsa gam
tana daga kwance dan duk taji abunda yake fadi, cafka bana wasa ba Aziza ta yiwa hannun Ɗan Gidan
Alhaji, da mugun mamaki Sultana ke kallon Aziza wacce take kwance idonta rufe ga jini, cikin rawar
murya Sultana ta ce
128
HAUSACINEMA.COM
"A....ziii.....zaaa...! dan Allah ku kai min ƙanwata asibiti kar ta mutu, baku da imani!! Ku azzalumai ne!!"
Shaho ya yi kan Sultana yana zuwa zai kai mata mari Aziza tasa kafa ta tokaresa sai da ya yi sama kafin ya
bugu da bango ya faɗi kasa, da sauri Dan Gidan Alhaji ya ce
"Kai wannan yarinyar fa na ga alama tana ji da kanta, ga shi ta riƙe min hannuna kamar zata b'alla, ke
dan uwarki da Ubanki! Sakar min hannuna" ya fada yana jan hannunsa da karfi amma Aziza ta ƙi sakewa,
Sultana kuwa tana takure a jikin Aziza tana kokarin yadda zata tsaida jinin da ke fita akan Azizan.
"Shaho, yarinyar nan fa taƙi sakina!!" Shaho wanda ya sha ƙasa ya miƙe a fusace yana fadin
"Wannan yarinyar sai fa mun nuna mata cewa ni cikakken dan iska ne, ban taba kisan kai ba, amma inaji
zan fara a kanta, dan naga tana fama da tashen balaga, ko dazu bugu ɗaya nayi wa dayar ta suma amma
ita sai da na mata biyar! dan haka ba zata sakeka ta dadi ba,bari ka gani" Shaho ya faɗa yana jan wani
karfe a bayan windown labule, ganin haka yasa Sultana fasa ihu dan ta ga gadan-gadan ya nufi Aziza
dake kwance, a haukace Sultana ta hau faɗin
"Dan Allah Aziza ki sakesa, ba danni ba Dan Girman Allah, kinga munyi sallama da Mom lafiya-lafiya kar a
koma mata da gawawwakinmu, dan Allah Aziza ki sakesa! Ki sakesa nace!!" Sultana ta faɗa da karfi a
tsawance, sake masa hannu Aziza ta yi, tana sakinsa ji ya yi tamƙar kashin hannunsa ta tsatstsage,a
hankali tasa hannu a tsakiyar gashin kanta ta dafe,da kyar ta miƙe zaune sabida jirin dake dibarta dan ta
bugu sosai a kai,inda yake saurin musu illa kenan shine duka a kai, amma duk sauran jiki dan sun bugu
aikin banza ne.
Kanta a duƙe tana riƙe da kai da hannunta daya, dayan hannun ta yi musu nuni da yatsarta manuniya
cike da gargaɗi ta ce
"Duk wanda baya so Uwarsa! ta haifi wani, to kar ya kuskura ya sake ya taba mini Antyna, ku maidamu
inda kuka dauko mu!" dariya Shaho da ɗan Gidan Alhaji da ɗayan suka yi, ƊAN GIDAN ALHAJI ya ce
"Zamu maidaku bayan mun yaga muku rigar mutunci! Ke kuma mai bamu umarni kar mu tabata,
Yayanta ne yasa aka kullemu watanmu biyar a kurkuku da kyar mahaifina ya fiddomu, dabadin shi ba ma
da har yanzu bamu fito ba, ai kema bamu san kanwarsa ba ce! Mun daɗe muna neman hanyar fansa! Sai
ga shi ta kawo kanta har zaria, abun ya bada kala fa, dan haka ke ki fara zuba ido ki ga yadda zamu mata
kafin a gama da ita a zo kanki, Shaho ku banƙaremin ita!" kukan tashin hankali Sultana ta saka tana
129
HAUSACINEMA.COM
kokarin kama Aziza su Shaho suka fizgota suka bajeta a kan carpet ɗaya ya riƙe mata hannaye ɗaya ya
riƙe mata kafafu, kuka Sultana take yi tana ambatar sunan Allah da Yayanta da Mom da Aziza da Khalil,
Aziza sai yunkurin tashi take yi ta kasa, ganin Ɗan Gidan Alhaji ya fara sa hannu yana tattaro doguwar
rigar dake jikin Sultana yana yin sama da shi rintse ido Sultana ta yi, ta sadaƙar kawai,ganin haka yasa
Aziza ware gashin kanta tasa hannu ta b'alli daya tasa a bakin, wani gurnani ta saki tare da hucin Maciji,
jin hucin maciji yasa Sultana buɗe ido da sauri dan tasan irin wa innan abubuwan tunda tana yawan
kallonsu, saurin juyowa suma Ɗan Gidan Alhaji da muƙarrabansa sukayi suna kallon Aziza wacce take
tsaye gashi ya rufe mata fuska, kwashe gashin ta yi ta tattare ta maida shi baya ta ƙulle,bata da wani
mafita wanda ya wuce haka, idan