Showing 24001 words to 27000 words out of 94205 words
ruɗu ba sai da ta
yi gamo da gawar mutum takwas wanda Azima ta kashe, daga karshe Aziza ta koma tayi zaman yan bori.
YANKIN JA'I.
a lokacin da garkuwan fulanin yakin kwana suka isa yankin ja'i da gawar Innu Maciji hakika sun ga tashin
hankali, sun ga masifa da bala'i a wajan jama'ar yankin ja'i, ko kaɗan sarkin fulanin yankin ja'i wato Jawo
da kuma mai unguwa Sodangi da sauran duk wanda yake yankin ja'i basu tsaya sun saurari su Garkuwan
fulanin kwana ba, suna isa da gawar fadar sarki Jawo nan yankin ya ɗauka daga tafiyar Innu Maciji yau
yankin kwana sun kashesa, nan jama'ar yankin ja'i suka janyo wuƙaƙe da adduna da sanda kokara,suka yi
kan su garkuwan fulanin kwana tare da fadin su ma ba za a barsu a raye ba, Galadima da Liman suka ce
yadda suka tunzura gwanda kawai su gudu, garkuwan fulanin kwana ya ce bai kamata su gudu ba tare da
sun musu bayanin abunda ya faru ba" Galadiman fulanin kwana ya ce
"Baka da hankali ne garkuwa? Ka ga yadda suka haukace suna ihu ka ce mu tsaya musu bayani taya zasu
sauraremu? Ka zo kawai mu gudu dan ceton ranmu daga baya idan suka yi sanyi sai mu dawo! Amma
kaga yanzu suna abu kamar wa inda mahaukacin zaki ya cije su" Garkuwa ya ce
"A gaskiya ba zamu tafi ba tare da munyi musu bayani ba,tunda duk abunda ya faru mu muka ja wa
kanmu! Da ace mun bi shawaran Magaji da ba haka ba"
55
HAUSACINEMA.COM
"Amma dai garkuwa kasan rashin hakuri irin na yankin ja'i da haukarsu ko? Ka zo mu gudu idan ba haka
ba zasu iya kashe m...." maganar da Liman bai karasa ba kenan yaji saukar dutse a goshinsa,nan ya riƙe
goshin yana faɗin "Ya Rabbi!" kafin su Garkuwa su dago nan suka ji ihu, inda gaba daya ahalin yankin ja'i
mata da mazansu kowa ka gani da makami nan suka yo rututu suna shirin kai wa su Garkuwa
farmaki,nan suka hau musu ruwan manyan duwatsu kafin su isosu,ganin haka yasa Galadiman fulanin
kwana da Limamin fulanin kwana suka kwasa a guje dan tseratar da ransu, sauran mutum biyar na fada
mutum uku su ma suka arce da gudu aka bar Garkuwan fulanin kwana da mutum biyu na fada su uku
kenan, kafin Garkuwan fulani ya yi kokarin faɗin wani abu tuni, an rufesu da duka da sanda, yayinda
ƙanin Innu Maciji yasa adda ya sare daya daga cikin ɗan fada a wuya yana sare san nan ko minti daya bai
yi ba yace ga garinku, ganin haka yasa garkuwan fulanin kwana yace shi da dayan ɗan fada su gudu, da
kyar suka kwace suka hau dokinsu ba shiri suka sab'i hanya jikinsu jina-jina da jini, dan garkuwa ma kam
an saresa a hannu.
Har mutanen yankin ja'i zasu bi su garkuwa, Sarki Jawo ya ce su dawo ai sun b'allowa kansu yaƙin da
basu san wanda zai tare musu ba, za ayi wasika a tura musu su shirya tarban yaƙi,kuma suna da yaƙinin
zasuyi nasara ta hanyar shafe al'karyan kwana tunda Magaji Bawa ya yi murabus!.
YANKIN KWANA.
Haqiqa yau yankin kwana tana cikin ruɗu da ruɗani,yayinda suka jera gawawwaki har na mutum sha
ɗaya wanda saren maciji ne a jikinsu.
Yau da safe mutum biyu sun sha dafin maciji sun mutu, Innu maciji saran maciji ya mutu,yanzu kuma ga
gawawwakin mutum sha daya, tsananin tashin hankali yasa suka kasa yiwa gawawwakin jana'iza ga
magriba ya gabato, ganin haka yasa sarki Chubaɗo bada umarnin a musu sutura a binnesu kar su yi
kwanan keso, da kyar suka yi musu jana'iza suka binnesu, bayan sun fito daga maƙabarta sai ga isowarsu
Galadiman kwana shi da Liman a fujajan, da sauri mutanen yankin kwana suka tarbesu suna tambayarsu
me ya faru? Baffa ya kalli goshin Galadima dake zubar da jini an fasa masa goshi,Baffa ya ce
"Daga ganin goshin Galadima ba sai an tambaya ba! Mun taro yaƙi ko? Ina su Garkuwa!?"
Da washe gari asubanci Baffa ya yi ya bar yankin kwana dan bai ga ta zama ba, ko da Aziza ta farka ita ce
kawai ta tambayi ina Baffa yake nan Hajja ke gaya mata ya tafi jejin gangare dan samo wasu ganyen
magani, Aziza ta ce
"Allah ya dawo min da Baffana lafiya" Hajja ta amsa da amin.
56
HAUSACINEMA.COM
Ita kuwa Azima tunda ta fara bacci ba ita da farkawa ba sai gefen sallar la'asar, ko da ta farka Aziza na
shirin ɗora mata hannu a goshi ta yi saurin rike hannun Aziza ta ce
"Ba bukata Aziza, yau ina cikin farin ciki babu wanda zan kashe amma za a mutu dayawa gobe! A'a ba
wai ina nufin ta hannuna ba fa,dan naga kina min wani kallo! Wallahi babu wanda zan kashe! Amma
gobe akwai zubda jini a yankin kwana!" tana gama fadi ta tashi ta fito ta samu Hajja a tsakar gida, Hajja
ta ce
"Azima wannan baccin naki ya yi yawa, haba dan Allah mutum ya ta faman bacci ba sallah ba salati ko
kina fashin sallah ne?"
Yatsine fuska Azima ta yi kafin ta ce
"Ni fa Hajja wannan fashin sallan da kika fadi me ma yake da suna? Al'ada ko? To ni banayi! Kuma ban
taba yi ba! Sallah gabadayanta ne bana yi,kuma ma Hajja sadda Aziza ke zuwa islamiyyar Malam Saini ni
kin taba gani naje ne? Har Aziza ta yi sauko ni ban taba zuwa Islamiyyar Malam Saini ba,ko kuma kin taba
gani da watan ramadan ina azumi? Ki kyaleni da maganar wani abu wai shi sallah!" tana gama fadi ta
fice, Aziza na tsaye a bukka tana kallon Azima, bayan Azima ta fita Hajja ta kalli Aziza hankali tashe ta ce
"Aziza meke damun yar uwarki!?" murmushin tausayin Hajja Aziza ta yi ta matso kusa da Hajja ta kama
hannunta ta ce
"Kun kusa ku sani Hajja nan ba da jimawa ba, dan bazan iya jure ganin hawayenki na zuba a kanmu ba,
zan gaya miki gaskiya da zaran Baffa ya dawo ko da kuwa za a kashemu!"
Hajja ta bude baki za ta yi magana da sauri Aziza ta ce
"Dan Allah Hajja karki ce komai, Azima bata sallah bata salati bata Azumi duk wani aikin ibada bata yi,na
gaji da miki karya Hajja, bazan iya jure miki karya ba!" tana gama fadi ta fice da gudu da kuka.
Aka bar Hajja da kakkarwar jiki.
Da yamma sai ga wasika daga yankuna uku izuwa yankin kwana, zasu kawo musu farmaki gobe da safe,
hakika wannan sako ya hautsine hankalin jama'ar kwana inda mata da dama har ma da mazan wasu
suka fara kuka, sarki Chubaɗo da mai unguwa ori suka ce ga shi Magaji baya nan, kuma babu halin yi
masa saƙo har sai ya dawo, saukinta ma Garkuwa ya ɗan samu lafiya, kafin kace me Sarki Chubaɗo ya
bada umarnin ayi shela a yankin kwana gabadayanta za a kawo farmakin yaƙi gobe kuma yankuna
uku,dan haka kowa ya kasance cikin shiri amma bana tarban yaƙi ba.
57
HAUSACINEMA.COM
Hajja da Aziza sun kasa zaune sun kasa tsaye sabida tashin hankali sai jeka ka dawo suke yi a tsakar gida
amma Azima na zaune hankali kwance tana fizgar dogon gashinta, Aziza ce ta kallenta ta ga babu alamun
damuwa a tattare da ita,cikin haushi da tsanar Azima da ya fara ɗarsuwa a zuciyarta ta ce
"Wai ke Azima wace irin dabba ce ke ana maganar kawo farmakin yaƙi amma kina zaune kina tsifar kai?"
"Macijiya!" Azima ta faɗa ba tare da ta ɗago ta kalli Aziza ba, Hajja ta juyo a firgice ta ce
"Ma mai kika ce Azima! ?" tana shirin kara nanatawa Aziza tayi saurin faɗin
"Mahaukaciya kawai!"
"Ga ki kuwa babbar mahaukaciya!" Azima ta faɗa tana dagowa a fusace.
"Dan Allah fadan ya isa haka!" Hajja ta katsesu,
"Kuyi ta addua kawai Allah ya bamu mafita yafi wannan fadar naku" ko uhum basu kuma cewa ba.
Da washe gari kamar yadda sako ya iskesu haka kuwa ta kasance inda yankin ja'i da yankin jimo da
yankin tudu sukayi cincirindo sun zo yaƙar yankin kwana, amma abun mamaki babu wani daga yankin
kwana da ya dauki makami, abun ya basu mamaki, Arɗo shine wanda ya fito ya fara magana
kasancewarsa Babba, tsohon bafulatani mai dattako
"Mu ba zamuyi yaƙi daku ba, idan har kuna so duk ku sa takwabi ku kashemu! Har ga Allah munyi imani
wannan ita ce kaddararmu! Bamu kashe Innu Maciji ba, a ranar da aka kashe Innu muma munyi rashin
mutane a yankin nan har mutum sha huɗu, haka ma jarman macizai, sannan sarkin fulanin tudu bamu
aikata muku komai ba kawai neman fitina kukeyi,idan kuma yaronka da aka kashe a yankin nan ne laifi
ya aikata aka masa hukunci, na rantse da wanda ya busamin numfashi idan har aka samu ɗan wani
yankin kwana da laifi makamanciyar wanda ɗanka yazo yankin nan ya aikata wlh mun yarje muku ku fille
kansa ku kawo mana kamar yadda mukayi, ba a barin laifi a ɗoran kasa, dan ba a san mai zai kuma
aikatawa a gaba ba, mu sabida muna bin al'ada da ibada shiyasa yankinmu ta yi baƙin jini a wajan sauran
yankuna, idan har maganar da nayi baku gamsu ba kuna iya shafemu a doron kasa ko kwayi farin ciki"
Arɗo na gama fadi jama'ar kwana suka miƙa wuya,ganin haka yasa yankin jimo jikinsu yayi sanyi suka ce
ba zasuyi yaƙi da yankin kwana ba,nan take suka juya, yankin tudu da yankin ja'i kuwa sunce suna nan,
sai sun shafe yankin kwana.
Gudu Baffa ke yi a dokinsa dan haka yake ji a jikinsa mahaifarsa babu lafiya.
A kwana kuwa ganin yadda yankin ja'i suka fara zubar da yara da manya ta hanyar saresu da takwabi
yasa garkuwan fulanin kwana cewa Sarki Chubado da Ardo
58
HAUSACINEMA.COM
"Ranka ya dade, hakika ba zamu tsaya a shafemu ba tare da mun sa hannu ba dan bamu aikata laifi ba,
burin yankin ja'i shine su ga sun shafe yankin kwana, dan haka kowa ya dibo makamai mu gwabza tunda
haka suke so" mai Unguwa Ori ya ce
"Tabbas hakane" nan garkuwa ya bada umarnin a dauka takwabi a fara maidawa yanki biyu martani.
Duk wannan tarzoma da akeyi Azima na saman bishiya tana kallo tana dariya, Aziza ganin kisan da ake
yiwa mutanen yankinta ya yi yawa ne ya sa ta fadi a ranta "inaaa! Burin Baffa shine ya ga ya mutu ya bar
yankinsa lafiya, dan haka dole ne na dakatar da yaƙin nan ta ko wani hanya in ba haka ba, tabbas yau
babu sauro da zai rage a yankin nan" ta kalli Hajja dake tsaye tana kalman shahada dan yawancin
mutane sun sadakar da zasu rayu ta ce
"Hajja ina jin fitsari zanje gida na dawo" ta karasa fadi tare da juyawa,saurin kamo hannunta Hajja ta yi
ta ce
"Aziza bakki hankali ashe ban sani ba?kina ganin yadda ake zubar da jini tamƙar ana ɗibo ruwa a rafin
jimulo ne ake watsawa kice zaki koma gida kiyi fitsari? Idan kika bincika wasu a nan har da kashi sukayi a
jikinsu,dan haka Aziza yi fitsarinki kawai a jikinki, gwanda mu tsaya ta nan idan har Allah yasa aka gama
da sauran kafin a iso kanmu,idan kuma Allah yasa Baffanku ya dawo a kan lokaci to, dan shiyasa nace
miki mu tsaya a nan sabida ga hanyar da zai fito nan" Hajja ta faɗa tana kara riƙe hannun Aziza, girgiza
kai Hajja ta yi ta ce
"Hajja to ni kin riƙeni babu fa Azima a nan" da sauri Hajja ta ce
"Na shiga uku! Azimaaaa!?"
"Kwantar da hankalinki Hajja bari na je nayi fitsari sai na dubota mu dawo tare"
"To dan Allah Aziza ki kula,ki min alkawari zaki dawo lafiya?"
"Na miki alkawari Hajjata zan dawo lafiya" sai da Aziza ta faɗi haka kafin Hajja ta saketa,da gudu Aziza
tayi hanyar gida dan ta shirya ta dawo ta tare yaƙin.
Haka Baffa ya shigo yankinsa ya samu gagarumin yaƙi, amma da shike baya da lokacin tsayawagida ya
wuce kai tsaye ya haɗa maganin furen surfa, sannan yaje ya kirawo Hajja a inda ya ganta sadda ya shigo,
amma ita bata gansa ba, yake tambayarta ina Aziza da Azima? Hajja ta ce
"Aziza tace min zata zo gida ba mamaki tana kewaye cikinta ya tsure sabida wannan tashin
hankalin,Azima kuma ban ganta ba dan Aziza tace min idan zata dawo zata dubota su sameni a can"
Baffa ya ce
59
HAUSACINEMA.COM
"Boye a can,ni kuma zan boye a nan karki kuskura kiyi magana kinji ko?" Hajja tana shirin tambayar Baffa
me yake son yi ya ce
"Jumala karki tambayeni komai! Zaki ganewa idanunki!ke dai kiyi abunda na sakaki! Yaƙi kuma inada
yaƙini a kan garkuwa zai tarewa yankin kwana tunda yasa hannu kafin na gama wannan binciken da
zanyi, dan haka karki tambayi komai kawai je ki boye,kuma karki kuskure ki fito" Hajja ta amsa da to,
maganin da Baffa ya haɗa ya kewaye kofar shigowa gida da shi, sannan ya zuba wani ya koma ya
maqale, Azima dake kwance a jikin bishiya haka kawai taji kamar an tsikareta saurin saukowa tayi a
saman bishiyar idonta ya kara canza kala nan ta nufa hanyar gida ba tare da tasan dalilin hakan ba
wanda take ji kamar an saka mata kuran karfe ne yake janta.
Aziza ce ta fito daga kewaye idonta jajur alama ce na taci kuka, tana fitowa ta shige bukkarsu, Baffa dake
maqale ta zanar kofar waje ya hangi Azima na tahowa tana layi, tana zuwa zata shiga gidan da aka yi
wani sama da ita aka bugata da kasa, yayinda taji ko wani fata ta jikinta na mata zafi, ihu ta saka tana
rirriƙe jikinta, ta kafarta ta fara rikidewa, wani wawan zare ido Baffa ya yi,yayinda yayi sumar wucin gadi,
wannan shi ake kira tashin hankalin da ba a sa masa rana.
Aziza kuwa shiryawa tayi dan taimakawa yankinta ta zo fitowa kenan har ta sa kafa akayi sama da ita ma,
ihu ta saka ta fadi kasa wanwar, girgiza kai ta hau yi jin yadda jikinta ya amsa tana shirin rikidewa ta
koma macijiya,cikin dimauta take furta "furen surfa na macizai? Wa ya kawo ya zuba a kofar gida?
Innalillahi wa inna ilaihirrajiun! a'a a'a a'a!!"bata bari hakan ya faru ba ta shige bukka da gudu, Hajja
dake kallonta ta zaro ido waje,to meke faruwa da yarta ga Baffansu yace karta fito? Anya zata iya kuwa
ba zata fita ta je ta duba me ya samu Aziza ba? Hakuri dai ta yi amma hankalinta na kan Aziza, Aziza
kuwa tana shiga bukka ta hau kwalawa Inno Fandi kira yayinda fatar jikinta ya koma fari sol, daga
kugunta abunda yayi ƙasa ta koma macijiya, cikin matsanacin kuka Aziza ke kiran Inno Fandi har ta
bayyana, ta ce
"Na shiga ukuna Inno Fandi furen surfa na macizai wa ya zuba?"
Inno fandi ta ce
"Yanzu za a fara Aziza! Ba kowa bane ya haɗa maganin furen surfa illa Magaji, wanda a halin yanzu
Azima tana waje tana rikidewa,ke ma haka gaki nan, a yanzu BAFFANKU YA GANE CEWA AZIMA
MACIJIYA CE! kece kawai bai gani ba, dan haka ki gaya masa gaskiya dan a san yadda za ayi a yi maganin
abun"
"To wani irin maganin abun Inno Fandi? Karshe dai nasan kashemu Baffa zaiyi da hannunsa" Inno Fandi
ta ce
60
HAUSACINEMA.COM
"Bana da ikon gaya muku komai, idan har na gaya muku zan iya mutuwa, Magaji shine zai gaya muku,
yanzu dai me kike da bukata na miki?"
"Ina so naje na tsaida yaƙin da akeyi ne kafin na dawo ayi ta gida, ki taimaka min na fita a gidan nan"
Inno fandi ta ce
"An gama" sannan ta dauki Aziza suka b'ace dan zuwa tsaida yaƙi.
A waje kuwa fadin halin da Baffa yake ciki bata lokaci ne bayan ya farfaɗo daga suman da yayi, a hankali
yake tunkarar Azima dake birgima tana ihu jikinta na kan rikiɗewa, rasa abun yi Baffa yayi kawai yasa
kuka ya duƙa a gaban Azima, ganin haka yasa Azima b'acewa b'att! A wajan Baffa ya yi zaman yan bori.
A wajan gari kuwa sadda Inno Fandi ta fice da Aziza nan Aziza ta b'ace tana kwasar mutanen yankin ja'i
tana watsar dasu, mutum na tsaye sai dai yaji an dagasa an wurgasa, idan ta tashi kwasa kuwa sai ta
kwasa kusan mutane goma da jelarta ta watsar dasu, mutanen yankin tudu jin sun daina yaƙi da mutane
sun koma yi da aljanu ya sakasu fara arcewa suna fadin kaff! yankin kwana ba mutane bane, harkazalika
yankin ja'i da suka fara jin jiki su da kansu suka tsare, su Garkuwa gani kawai suka kafin kiftawar ido da
bismillah duk yawan rundunar da suka zo sun watse, hamdala suka fara yi suna godiya ga Allah, amma
tabbas an kashe musu mutane.
A hankali Aziza ta bayyana ta zama mutum tana ganin mutane kwance a cikin jini yara da manya mata da
maza, hawaye ta share gami da kama hanyar gida,tana cikin tafiya Inno Fandi ta kira sunanta
"AZIIIZAAA!" cak Aziza ta tsaya, sannan Inno Fandi ta ce
"Idan kinje gida ki tambayi Baffanku Magaji Bawa su waye BANJU DA BAHULA!" Inno Fandi tana