Showing 69001 words to 72000 words out of 94205 words
ba" Nawaz ya fada yana shagwabe fuska yana kallon Mom, mom ta ce
"E ai naga Al'mazeen din nace kai kaje ka dubata, idan kuma ba zaka dubata ba sai ka gaya min na cewa
Son yaje ya duba min ita" Nawaz ya miƙe yana fadin
162
HAUSACINEMA.COM
"Yaushe na isa, yi hakuri Mom luv ɗina, yanzu kuwa zan dubata, Sultana je ki dauko min box ɗina"
Sultana ta amsa da to ta fice da gudu, shi kuma ya yi hanyar dakin,yana zuwa ya tura kofar ya sameta
kwance ta zubar da gashinta a kan pillow, a ransa ya ce
"Wai idan wannan gashinta ne ma sha Allah" sai da ya yi gyaran murya kafin ya yi sallama, da sauri Aziza
ta mike tana jan hularta dan ta rufe kanta, tana saka hular wanda bai rufe mata gashi ba sauran ya
kwanta a kafaɗunta, ta dukar da kai jikinta na rawa, kallonta Nawaz ke yi yana yaba kyawunta a
zuciyarsa sai furta ma sha Allah yake yi, har Sultana ta shigo dakin tana masa magana amma bai ji ba, sai
da ta tabosa kafin ya juyo, dariya Sultana ta hau maqalewa tana miƙa masa box din, ganin haka ya dalla
mata harara ba shiri ta hadiye dariyarta, murya can ciki yace
"Me kike ji a jikinki?"
Murya na rawa Aziza ta ce
"Amm.....uhum......zazzabi ne sama-sama"
"Kinci abinci?"
"E naci"
"Tun yaushe?"
"Tun karfe biyu"
"Na rana?"
"E"
"Baki da hankali ne! Taya zaki zauna da yunwa bayan baki da lafiya! Ko baki san shima wani babban
ciwon bane! Sultana je ki kawo mata abinci yanzun nan taci a gabana, na duba na gani allura zan mata
ko magani zan bata" jin ya kira sunan allura yasa Aziza ta ɗago, nan hawaye suka b'alle kamar an buɗe
pampo, cikin fuskar tausayi ta ce
"Dan Allah Hamma Nawaz zan sha magani amma banda allura,bana son allura" ta hau masa magiya tana
kallonsa amma shi idonsa a kwayar idonta yake yana kalla bugun zuciyarsa yana kara tsananta, da kyar
ya dauke idonsa a kanta ya juya baya, sultana ce ta shigo da plate da abinci da ruwa ta mikawa Aziza
dake kuka wiwi, Nawaz ya ce
"Na fa tsani kuka, kici abincin nan idan baki son allura,bana son shirme, idan kuma baki ci ba alluran zan
miki" jin haka yasa Aziza fara ɗurawa cikinta abinci, sai da taci rabi ta kalli Sultana da tayi shuru kamar
bata wajen, ta ce
163
HAUSACINEMA.COM
"Anty sulty na koshi, Hamma Nawaz bani maganin" kallon Sultana yayi babu alamun wasa ya ce
"Karba plate ɗin ki fita da shi" karba sultana ta yi ta fita,sultana na fita ya hau jan ruwan allura ganin
haka yasa Aziza fashewa da kuka tana ba shi hakuri kar ya mata allura, bata so ko kaɗan karfe ya huɗa
jikinta kasancewar tana da jikin maciji hakan zai iya mata illa dan karfe ne zai huɗa jikinta,maciji kuma
baya son tab'o, ko kaɗan Nawaz bai damu da kukanta ba duk da yanaji har can kasar zuciyarsa, ya rasa
meyasa yake jin tausayin yarinyar, bai so ko kaɗan yana mafarkinta a mugun yanayi, bayan ya saita
alluran ya nufeta, da sauri Aziza ta miƙe ta diro a gadon ta hau ja da baya, ihu ta saka zata gudu yasa
hannu ya jata, Mom da Sultana da Almazeen da suke parlour suka jiyo ihun Aziza da sauri suka tashi suka
yo dakin da gudu, suna shigowa suka samu Aziza da Nawaz sai zagaye daki suke yi, Mom tace
"Miye haka me zan gani?" ganin Mom yasa Aziza rugawa da gudu ta buya bayan mom, tsaki Nawaz yayi
yasa hannu ya jata a bayan Mom yana fadin
"Mom ai kinga irinta, bana son hidiman yarinta wlh,allura fa zan mata amma kalli yadda ta sakani zagaye
daki sai kace wacce zan zare ranta!"
"Haba Nawaz! Miye haka sai kace ba likita ba, ka lallabata mana ka bita a hankali, Aziza ki tsaya kinji?
idan ya miki zakiji sauki, kinga yau kin wuni a daki ga jikinki da zafi, bana son ina ganinki a haka kinji?"
girgiza kai Aziza ke yi tana fadin
"Mom zai min illa!"
"To dan Allah fa kiji mom, wai zai mata illa, taya allura zai miki illa ana shirin nema miki lafiya" yana faɗi
ya haɗata da jikinsa ya matseta,a karfinta na nml mutane ta kasa kwace kanta, sadakarwa tayi, jin ya
matseta ya danna mata allura yasa ta ƙanƙameshi tana kara sa kuka, allura biyu ya mata kafin ya saketa
ya fita a dakin, Al'mazeen wanda ya ƙura mata ido yana kallonta ya fita ya bar su Mom da sultana suna
rarrashinta, cikin kuka ta ce
"Mom allura karfe ne,kuma jikina na maciji ne, zai min illa" a tare mom da sultana suka zaro ido,mom
tace "Aziza meyasa baki gaya mana da wuri ba? Subhanallah! Yanzu me zai faru?" girgiza kai Aziza tayi
jiri na dibarta ta zube a jikin mom abun tausayi, hawaye Mom ta goge tace
"Ya Allah, kasa abunda yake zuciyata wanda nake shirin haɗawa ya zama alkairi, Allah kasa ya zama
jahadi dani da iyalaina, ya zama silar shiganmu aljanna!"
"Me kike shirin yi Mom?"
164
HAUSACINEMA.COM
"Inaso na saka Yayanki Ya Auri Aziza!" jinjina kai Sultana tayi ta ce
"Mom nima na jima da fara wannan tunanin, dan babu wanda zai auresu yayi wannan jahadin idan ba
wani ikon Allah ba,mom ya kamata ki gayawa Yaya tun daga yanzu, sannan dan Allah mom a daga bikina
zuwa shekara mai zuwa" wani harara mom ta gallawa Sultana sannan tace
"To je ki gayawa Nawaz" shuru Sultana tayi dan ko giyar wake take sha ba zata gayawa Yayanta Nawaz a
daga bikin ba, yanzu sai ya daki banza.
Aziza zazzabi da kaɗan-kaɗan ya fara rufeta, ga shi abunda take so babu shi a cikin gari, furen huriri
shine zata jiƙa ko ta tauna ganyensa shi kadai ne zai dawo da ita hayyacinta,amma ina zata samu?" haka
ta dinga b'ari.
A daren yadda Aziza bata rintsa ba,haka ma Nawaz, wanda da ya rufe ido ita yake gani sadda take kuka
tana cewa kar ya mata allura, tausayinta ne ya rufe masa zuciya, tashi ya yi ya kalli Almazeen dake bacci,
parlor ya fito ya zauna ya riƙe kansa, ji yake kamar yasa kuka, ko yaje ya ganta ko zaiji sauki a ransa,
abunda ya shafe wata uku yanaji a ransa bayaso ya tabbata, baya so zuciyarsa ace ta kamu da son
wannan jaririyar yarinyar, sannan meyasa yake mafarkinta tun daga ranar da ta shigo rayuwarsa, meyasa
yake ganinta a siffar macijiya? Saurin tashi tsaye ya yi, tare da naushin iska, a fili yace
"Kamata ya yi ace na tsaneki, dan kin takurawa rayuwata da yawa! Tsawon dare bana bacci duk sabida
dake! Why! Why! Why Azizaaa!!" ya faɗa yana rike kansa da yakeji kamar zai rabe gida biyu, anan ya
zauna har asuba, bayan Almazeen ya farka ya shiga bathroom yayi alwala ya fito parlor nan ya ga Nawaz
yashe a parlor, kallonsa ya yi ba tare da ya yi magana ba yace
"Nawaz kayi alwala kazo muje sallah" Almazeen na fadi ya fice, shima Nawaz din alwala ya yi ya bi bayan
almazeen bayan sun dawo daga masallaci, Al'mazeen ya hau shiri, yana shiri yana tambayar meke
damun Nawaz, Nawaz yace masa ba komai, bai takura ba ya kammala shirinsa, takwas ya shiga ya yiwa
165
HAUSACINEMA.COM
mom sallama, mom tace dan Allah kafin ya wuce ya shiga ya duba Aziza ya bata magani dan jiya bata
rintsa ba jikin ya yi tsanani,da to Al'mazeen ya amsa.
Aziza kwance sai b'ari takeyi jikinta mugun zafi, hannunta Almazeen ya kama ya ga wani zobe a
hannunta a ƙaramin yatsarta na karshe, bai damu ba, ya gama dubata ya ajiye mata magunguna sannan
yamusu sallama ya tafi.
Har wajen mota Nawaz ya raka amininsa tare fadin sai sunyi waya Allah ya tsare, sai da Al'mazeen suka
fice kafin Nawaz ya shiga ya gaida mom idonsa a kumbure shima dan baiyi bacci ba ga kansa dake
ciwo,cikin kulawa mom ta ce
"Nawaz lafiya kuwa?"
"Mom kaina ke ciwo jiya banyi bacci ba"
"Subhanallah! Sannu Allah ya baka lafiya, ka sha magani ka kwanta"
"To Mom" ya faɗa yana tashi, yana so ya tambayeta Aziza amma yakasa,dan haka ya koma part dinsa ya
sha magani ya kwanta.
Bayan ya fice wayar Mom ya dauki ruri, tana dubawa ta ga malamin da tasa ya mata istihara a kan
Nawaz da Aziza, da sauri ta daga suka gaisa cikin girmamawa,nan ya shaida mata akwai alkairi mai girma
da yardan Allah tsakanin Nawaz da Aziza, shi gwargwadon abunda ya gani kenan, godiya sosai mom ta
masa nan ta kara jin karfin guiwa.
Dakin Aziza taje ta samu jikin nata ya kara tsanani, sultana idonta ya zazzago tsananin tashin hankali,
Sultana tace
"Mom a gayawa Yaya ko akwai maganin da zai bata, kar ta mutu"
"Sultana shima baya da lafiya idonsa a kumbure da kyar yake budewa shiyasa ban gaya masa na Azizan
ba,mu bari nasa ya sauka tukunna" Sultana ta ce
"Mom,anya kaddaran Yaya ba a haɗe yake da na Aziza ba kuwa?" shuru Mom tayi, sai zuwa can tace
"Allah ka bayyana mana Azima cikin sauki Ya Allah, Allah ka jinkirtawa wannan baiwa taka Aziza,duk da
tana karama da kananun shekaru amma tana da hakuri da tawakkali da juriya" hawaye Sultana ta goge
166
HAUSACINEMA.COM
ta fice a dakin, khalil ta kira a waya tana kuka tana roƙonsa a kan a daga bikin nan kar ayi nan da wata
daya, dalili ya fara tambayarta amma ta kasa gaya masa,inda a karshe ya katse wayarsa dan ya kasa gane
me Sultana take nufi ko dai ta daina sonsa ne?.
Yau fa Azima murna tun daga baka har kunne, Al'mazeen na hanya, bayan su Hadiza sun gama shirya
masa abinci ita kuma ta gyara masa part dinsa tas, ta zo shiga cikin kitchen ta hangi Maman Hanan akan
abincin Al'mazeen tana barbaɗa masa magani, girgiza kai Azima tayi, ta bar wajan ba tare da maman
hanan ta ganta ba,amma tayi alkawari ba zata bari al'mazeen yaci abincin nan ba.
Goma da rabi motar Al'mazeen ta yi parking a harabar parker motoci, ya jima a motar yana sauke ajiyar
zuciya kafin ya fito, nan ma aikatan gidan suka hau masa sannu da dawowa tare da gaya masa sunyi
kewarsa, cikin parlour ya wuce nan Maman Hanan da Maman Beenah suka hau murna suna masa oyoyo,
a hankali ya russuna ya basu girmansu ya gaishesu sannan ya fara haurawa samansa, Maman Hanan ta
ce
"Fuskar mutum kamar fura a dame kullum, Hadiza! Zo ku kai masa abincinsa sama"
"Ba zai ci wannan abincin ba, wani zan dafa masa!" saurin juyowa Maman Hanan da Maman Beenah
sukayi suna kallon Azima da kanta ke duƙe da lullubi, cak Al'mazeen da zai hau sama yaja ya tsaya jin
kamar ya san mai irin muryar, Maman Hanan ta ce
"Sabida me ba zai ci ba?"
"Sabida bana da bukatar yaci, a bai wa wasu su ci,ko a ajiyewa su Hanif su ci idan sun dawo!" a daqile
Azima ke magana, da sauri Al'mazeen ya dawo da baya,nan kuwa ya ganta sanye da bakin abaya itama
fuska a lullube, yatsar hannunta ya kalla ya ce
"AZIZAAAA!?" a mamakin ce.
"To yanzu miye mafita? Wani sharrin satan zamuyi mata?" cewar Maman Hanan, Maman Beenah ta ce
"Yanzu ke Maman Hanan idan kikace ta sace miki abu za ace dan ta murɗewa Hanan hannu ne,
Al'mazeen ba zai yarda ba, tunda su Sady suna hanya mu jira isowarsa kafin mu yanke shawara" Hanan
dake kuka ta ɗago tana kallon hannunta da shati ya fito raɗa-raɗa ta share hawaye tana fadin
"Wlh sai na koya mata hankali, zata gane shayi ruwa ne,ita har ta isa! Wacece ita! Waye ubanta! Tana
'yar aiki!"
"Bar ta ubanta zamu ci dan naga abun nata ya fara wuce gona da iri" Beenah ta ce
167
HAUSACINEMA.COM
"Hummm! Ku ga sadda tazo gidan nan ba ruwanta, amma daga dawowar Al'mazeen sai wani falli take ji
da shi, ga shi kullum tana part ɗinsa da yana nan da baya nan, anya kuwa babu wani abunda yake
gudana a tsakaninsu?"
"Ai dama ba banza ba! kinga dai yadda Al'mazeen ke shakkarmu..."
"A'a fa Maman Hanan ba dai shakkarmu ba,yana dai kyalemu kasancewarsa mai biyayya yana shanye
duk baƙinciki da takaicin da muke ƙunsa masa" Maman Beenah ta katsewa Maman Hanan hanzari ta
hanyar faɗin haka.
"To ai ga shi yanzu wannan 'yar banzar mai aikin tana shirin hanamu rawar gaban hantsi 'yan kuɗaɗen da
muke karba a wajansa wannan shegiya 'yar banzan tayi ƙyam-ƙyam" Maman beenah zata kuma yin
magana suka jiyo sallamarsu Sumy da Sady da karfi sai kace zasu tada gidan, kafin su Maman Hanan su
sauko Azima ce ta fara sauƙowa ta fito part din Al'mazeen hannunta dauke da kaskon turaren wuta da
alama saka masa tayi, wani kallo Sumy da Sady suka bi Azima da shi har ta gama saukowa tayi hanyar
waje ta kofar baya ba tare da tasan Allah ya yi wasu halittu a wajan ba, Sumy ta ce
"Tooo! Ina aka samu balarabiya ko ba india?" yatsine fuska Sady tayi ta ce
"Oho" saukowarsu Maman Hanan ne ya katsewa su Sumy maganar da sukeyi, nan aka hau musu sannu
da zuwa, sai amsawa sukeyi a gadarance,Sumy ce mai gajan hakuri ta ce
"Anty (maman Hanan kenan) wacece wata 'yar dogowar yarinya fara ,tasa riga da wando da wani baƙin
glass sai kace ba india?" Maman Hanan tayi tsaki tana bin Sumy da Sady da kallo ta ce
"Yoo ai ita ce wacce muke gaya muku Azima"
"Kan Uba! To ma uwarwa ta yiwa wannan shigan a gida tana mai aiki uban wa ya bata wannan damar!?"
cewar Sumy, Hanan ta share hawayen da suka gaza tsayuwa dan ji take kamar hannunta zai fita ta ce
"Ba dai yanzu ku ka iso ba? To tunda Al'mazeen ya dawo take ji da iskanci iri da kala"
"son Al'mazeen din take yi ne?" cewar Sady tana tabe baki, Beenah tace
168
HAUSACINEMA.COM
"Kar dai har kin fara kishinsa?"
"Wa? Ni? Allah ya kyauta! Al'mazeen baya raina sam, dan haduwa ya hadu amma ni zan auresa ne dan
kudinsa kamar yadda ku ka ce Anty,zamu auresa ne sabida kuɗinsa da mun kwasheshi sai ya sakemu"
"Kai kuyi magana a hankali a ƙasa fa muke, kuma wannan shegiyar tana nan, to ma yanzu kin san me ya
faru?" cewar Maman Hanan, nan ta basu labarin tsiyar da Azima ke yi a gidan, ta kara da murɗewa
Hanan Hannu da Aziman tayi da safe sadda Al'mazeen zaije aiki, har Hanan na nuna musu hannunta da
ya kumbura, haɗa baki Sumy da Sady sukayi suna fadin zasu ci Uban Azima, suna kan meeting din yadda
zasu korata a satin nan sai gata ta shigo tana shirin sake wucewa kamar dazu Sumy da ta hangeta tun
farkon buɗe kofa ta ce
"Keee ƙidahumar jeji jikar shanuka! Zo nan" wani birki Azima taci ta tsaya cak ba tare da ta dawo ba,
Sady ta ce
"Dake ake ballagaza!" cije baki Azima tayi idonta na sake rinewa, rintse ido tayi ta hadiye takaicinta
sannan ta dawo da baya ta tako tazo gabansu ta tsaya, Sumy ta ce
"Keee! Cire wannan bakin glass din idon naki!"
"Ke a wa fa!? idan naki cirewa wata uwar zakiyi!?" Azima ta faɗa tana tinkaro Sumy, ja da baya sumy
tayi, ganin haka yasa Maman Beenah faɗin
"Kee Azima! ba kya ganin baki ne? Ki dau kayansu ki haura musu da shi sama a wannan dakin da Hadiza
ta gyara dazun nan"
"Su ɗin kutare ne? ko basu da hannun dauka ne? idan sun ga dama su da kayan nasu su kwana a nan"
Azima na gama faɗi ta juya tana taku jikinta na langwasa harta taka step daya ta juyo ta kalli Sumy ta ce
"Kee kuma! karki kuma kuskuren fadin cewa na cire wannan madubin, dan kuwa kallo daya ake yiwa
idanuna! idan kika kallesa baki kara kallon komai a rayuwarki!" Azima na fadi ta hau sama fuuuu! Aka
bar su Maman Hanan a daskare.
"Ahaf kun gani da idonku ko?" cewar Maman Beenah, Sumy ta ce
169
HAUSACINEMA.COM
"Na san yadda zanyi da shegiya bari Al'mazeen din ya dawo" ta fadi tana hawa sama, Beenah ta kira su
Hadiza suka dauki kayan su Sumy suka haura musu da shi tunda Hajiya Azima Banju tace bata hawa da
shi.
Yau kasancewar ya wuni a office yana tunanin Azima yasa bai yi wani aikin komai ba, ga shi yana son
magana da ita kuma ba hali tunda ba waya ne a hannunta ba,kuma tin daga ranar da ya dawo ya fahimci
babu jituwa a tsakaninta da mutanen gidan