Showing 15001 words to 18000 words out of 94205 words

Chapter 6 - Azima-Da-Aziza-Macizai Ne Complete

20 Jul 2024

37827

fara rikiɗewa tana komawa macijiya, nan ta zama wata shirgiɗeɗiyar macijiya
mai cike da abun tsoro, nan aka hau guɗa wanda yasa duk jejin lore ya dauka, kafin wannan katon
halittan ya ce a maidata gida lafiya, nan suka fizgi Aziza,wacce tunda suka fizgeta bata kara sanin ina
kanta yake ba, sanyin asuba ne ya farkar da ita,tana buɗe ido ta ganta a kofar gida, saurin tashi ta yi tana
karkaɗe jikinta, nan abunda ya faru a daren jiya ya hau dawo mata, lallai kam jejin lore ba jejin mutane




35
HAUSACINEMA.COM


bane, da kyar ta saita kanta jin yadda jikinta ke mata ciwo, da sanɗa ta shiga cikin gida, tana shiga Baffa
na fitowa daga kewaye ya yi alwala zai je masallaci, ya ce

"Aziza har kin farka? To shiga ki tada Hajjarku sannan ki tashi Azima su yi sallah"

"To Baffa" Aziza ta faɗa ta shiga ta tada Hajja sannan ta fito ta shige bukkarsu, ko da ta shiga bata gan
Azima ba, a ranta ta ce ko ina taje oho mata, kayanta ta ajiye sannan ta fito ta yi alwala ta yi sallah ta
jima tana addua sannan ta tashi.

Abu na gaba da zata yi shine daukar zaren saƙar dana taje ta kona shi, to amma abun tambayar a nan
shine a ina Azima ta ajiyesa? "zaki iya dubawa ki gani ta tafin hannunki ai an baki karfi a daren jiya a jejin
lore" wata zuciyar ta bata amsa da haka, da sauri ta buɗe tafin hannunta na dama tasa hannun hagunta
tana shafe tafin hannun daman tare da lumshe ido, nan ta ga ashe ma a cikin kayanta Azima ta ajiye
zaren saƙar danar, tasan tabbas Aziza sai ta binciko,kuma duk bincikenta ba zata duba kayanta ba tunda
ba zata yi tunanin zata saka a ciki ba, da sauri Aziza ta buɗe ido tana fadin "lallai Azima ke shaiɗaniya ce!
A cikin kayana kika ma ajiye?" da sauri ta wargaza kayanta ta dauki zaren wanda Azima ta saƙa shi ya yi
tsayi, lullubi ta yi ta boyesa a cikin mayafinta ta fito a hankali dan gari ya yi haske, har ta kai bakin kofa
zata fita ta ji Hajja na kwala mata kira da gudu ta fice dan bata son ta rasa wannan damar, jejin kwana
taje ta ajiye zaren bayan ta duba babu kowa a wajan, da ido ta kalli zaren yayinda idon nata ya koma
jajur kamar garwashin wuta,nan wani jar wuta ya fito daga idonta ya kama zaren,nan zaren ya kama da
wuta har yana wani irin ƙara passpasspass! Da sauri Aziza ta ja da baya, nan zaren ya ƙone ƙurmuss!
tokar Aziza tasa hannu ta shafe shi ya b'ace nan ta sauke ajiyar zuciya mai karfin gaske tare da fashewa
da kuka tana zubewa a kan guiwowinta tasa goshinta a kasa ta yi sujjadar shukur,ta yi tsammanin ta
kashe wannan bala'in bata san wanda yake shirin ci ba.

AZIMA.




tun fitarta a gida tana kwance a kan bishiya a macijiya tana jiran isowar Innu maciji, sai bayan da garin
Allah ya fara wayewa ta ga wasu yan matasan samari biyu sun zo sun tsaya a jikin bishiyar da take
kwance, dayan ya ce

"To ma ban da abun Mai Unguwa taya zamu iya kare Innu Maciji da za a wani turo mu dan mu tarbesa"

"Nima dai abun da na gani kenan" saurin zare ido Azima ta yi ta kallesu da kyau sannan ta yi murmushi

"Ohhho kenan yan fadar mai unguwa ne! Aiko su ya yi, shin na bar ma su bada labari ne? Idan kuma
suka tona min asiri fa?" nan ta haɗe rai tare da sulalowa daga bishiyar ta zama mutum, hannu ta miƙa
sama sai ga kwaryan nono, murmushi ta yi ta buɗe kwaryan wanda yake cike da nono kindirmo fari sol
abun sha'awa ta watsa dafi a ciki sannan ta gyara mayafinta tayi lullubi ta rufe fuskarta ta nufi inda suke,




36
HAUSACINEMA.COM


cikin karairaya ta musu sallama, su kuwa sun ga ƴar budurwa har rige-rigen amsawa suke yi,cikin
harshen fulatanci suke magana ta ce musu

"Ga fa nono, daga ina ku ke da sassafen nan haka ku ka zo ku ka zaune a tsakanin yanki?".




"Wlh mai unguwa ne ya aiko mu, kin san ai masifar da ake fama da shi a yankin nan na macizai, to yau
Innu Maciji zai zo wanda yake yankin ja'i shine mai unguwa ya aiko mu dan mu tarbesa,kin san kwanaki
da Jarman macizai ya zo gawarsa kawai muka gani, kai duk wannan macijin da yake kisan nan ko take
kisan nan ko humm idan Innu Maciji ya zo zan ce ya bani dama na kashesa da hannuna"cije baki Azima ta
yi ta ce "da gaske?"

"Aradun Allah kuwa! Sanda zan sha na dinga roɗewa macijin kai har sai ya koma ga Allah" damƙe hannu
Azima ta yi jin yadda ranta ya b'aci zuciyarta na tafasa amma ta daure tare ta k'wak'ulo murmushin
mugunta ta ce

"Ai kuwa nima ina da wasu sirrika a kan macizai, kafin na gaya muku ga wannan nonon ku sha" ta fada
tana tura musu kwaryan, dayan ya ce

"Allah sarki! Ashe kin san yau da yunwa muka tashi,ga shi kafin mu karya karin kumallo aka turomu
yanki" murmushi kawai Azima ta yi ba tare da ta sake magana ba, nan suka buɗe nonon nan suka hau
sha, sai da suka shanye tass har suna mata godiya, Azima ta kyalkyale da dariya tare da yaye mayafin
fuskarta nan blue eyes dinta ya bayyana, tare da rikiɗewa ta hau komawa macijiya, tsananin tsoro da
firgici yasa suka kasa motsi illa junansu da suka rungume gagam!, bayan Azima ta zama macijiya sannan
ta koma ta zama mutum ta matso kusa dasu ta duka ta ce

"NI CE AZIMA MACIJIYA! WACCE DUK KASHE-KASHEN DA AKE YI NI NA KE YI! NI! NI! NI CEEEE! SANNAN
KU TAKU TA KARE DAN DAGA NAN BABU WANDA ZAI MOTSA A CIKINKU, DAN KUN SHA GUBANA" tana
gama faɗi kuwa suka hau aman jini, su na riƙe wuyarsu tsananin azaba, jini na fita ta baki da hanci, suna
birgiman fitar rai Azima na ta sheƙa dariya, da haka har suka daina motsi, bayan sun mutu ta kwashesu
ta maida su gefe ta ajiye sannan ta ci gaba da tsumayin jiran isowar Innu Maciji, ba jimawa sai ga shi nan
kuwa ya yanko a kan dokinsa, daka gansa ka ga basamudan bafulatani mai ji da kansa, wuyarsa rataye da
maciji, Azima na ganinsa ta hau murmushi tare da gyara lullubinta ta zo ta tsaya a kan hanya, (ga Azima
ga Innu Maciji, ya zata kaya?).




37
HAUSACINEMA.COM


Kamar yadda ta yiwa jarman macizai haka ta yiwa Innu Maciji, shi ma kalar tambayar da jarman macizai
ya mata shi ya mata

"Mutum ko aljan?" murmushi ta yi tare da fadin

" RUWA BIYU!" sannan ta juyo gami da yaye mayafinta, Innu Maciji na ganin kwayar idonta nan ya sauƙo
da sauri tare da zare takwabinsa yana fadin

"Keeeee!" haɗe rai ta yi ta ce

"Ajali ya kiraka!"

Gyara tsayuwarsa ya yi ya ce

"Kina tunanin zan mutu a hannunki ne?"

"Ashe dai baka cika ba! Tunda har ba zaka iya bambance wacece ni ba, amma ina so ka sani ba zaka
shiga yankin nan ba,kamar yadda ba zaka koma yankinku ba" tana gama fadi ta yi kansa tare da komawa
macijiya,ganin haka yasa Innu Maciji saurin b'acewa dan ya ga da karfinta ta nufosa, Azima gani ta yi
Innu Maciji ya b'ace yasa ta koma mutum tana ta kalle-kalle,ji tayi an tokareta ta baya nan ta fadi kasa ta
bugu tukunna Innu Maciji ya bayyana yana dariya yana kallonta ya ce

"Ba mamaki baki da labarin waye Innu Maciji ko? Humm ni ne nan mai fada da aljanu da mayu, sabida
shaharata yasa sadda aka raba kambun girmamawa ni ne nan nayi na daya, dan haka sai na baki wahala!
Na galabaitar dake sannan na daukeki na kaiki wajan mutanen yankinku na nuna musu ke!" yana gama
fadin haka ya zaro wani dogon igiya ya naɗe Azima da shi, ya hau bugunta tare da watsa mata wani
ruwan magani wanda da ya watsa mata zata kurma ihu, fatar jikinta ya koma blue sabida karfin dafinta
ne ke raguwa, haka Innu ya ci gaba da ganawa Azima azaba wanda izuwa yanzu fadin halin da take ciki
b'ata lokaci ne, sai da ya ga bata iya motsin kirki sannan ya kyaleta yana shirin daukarta ya ɗorata a
dokinsa yaje ya nunawa jama'ar yankin kwana, har ya dauketa Azima ta buɗe ido a galabai ce, a ranta ta
ce

"Yanzu idan aka kaini Baffa da kansa na san zai kasheni! To ina kuma daukar fansata!? Inaaa ba zan bari
hakan ta faru ba! Ba zan bar yankin nan ba, ba tare da burina na son maida yankin kwana maƙabarta ba,
sannan ba zan bari na mutu ba tare da na shiga cikin gari ba" tana gama fadi ta yanki gashin kanta ta
haɗiye ta rintse ido ta mamayi Innu Maciji wanda ya sab'ata a wuya yana shirin ɗorata a kan doki, nan ta
zama macijiya tasa jelarta ta shaƙe wuyar Innu Maciji, shaƙa bana wasa ba, sannan tasa hannu ta
b'abb'alle guru da layoyin dake jikinsa ta zubar, sannan tasa ihu ta koma macijiya gaba dayarta ta hau
sarensa,duk yadda Innu Maciji ya so kwacewa ina hakan bai samu ba, Azima sai da ta ga Innu Macijiya ya
zube kasa babu rai a tattare da shi sannan ta sulale gefe ta koma mutum tana sauke ajiyar zuciya
idanunta jajur, kallon Innu Maciji take yi na wasu lokuta sannan ta ja samari biyun da ta kashe ta haɗa da
innu maciji sannan ta bar wajan.



38
HAUSACINEMA.COM


Bayan Aziza ta koma gida aikin gabanta ta ci gaba da yi, ko kaɗan bata tambayi ina Azima take ba,nan ta
yiwa Hajja shara da girki sannan ta hau ɗibar ruwa, sai da ta cika babbar randar kasarsu sannan Hajja ta
ce

"Ayye Aziza ba za ki huta ba?" murmushi ta yi ta ce

"Hajja hutuna shine naga Allah ya rabani dake lafiya" Hajja ta yi murmushi jin dadi tare da sa mata
albarka,nan suka zaune hira suka shantake sai zuwa anjima Hajja ta ce

"Wai ni ina Azima ne kam?"

"Wa ya san mata" cewar Aziza,

"Bata rafin jimulo ne?"

"Ni dai wlh Hajja har na gama jido ruwa ban ganta ba, da ace tana can dana ganta"

"Ikon Allah!" Hajja ta fada, Aziza ta ce

"Hajja miye amfanin damuwa a kan Azima ita da ba jaririya ba,duk inda taje zata dawo ai" Hajja ta ce

"Hakane" suka ci gaba da hirarsu, sai zuwa can Aziza ta ce

"Hajja wai ina Baffa? Tun fitarsa sallar asuba fa bai dawo ba ga shi yanzu ana neman lokacin azahar"
Hajja ta ce

"Oh! Kinga na mance ban gaya miki ba, ai suna can fadar sarkin fulani, Chubaɗo"




"Wani abun ake yi ne?" Aziza ta tambaya cikin rashin sani tana kallon Hajja, Hajja ta ce

"E lafiyar kenan, kin san ai an yiwa yankin ja'i aiken wasikar taimako, har Innu Maciji ma ya ce zai zo yau,
to jiran Baffan naku nake yi idan Innun ya iso zai zo ya gaya mana muje can fadar sarkin fulani"




Wani firgita Aziza ta yi ta miƙe tsaye ta ce

"Hajja yaushe aka yi aike yankin ja'i har Innu Maciji yace zai zo?" ita ma Hajjar miƙewa ta yi ta ce

"Aziza lafiya kuwa?"




39
HAUSACINEMA.COM


Kama hannunta Aziza ta yi ta ce

"Hajja tun yaushe ne Azima bata gida?" Hajja ta ce

"Ban sani ba Aziza, dan ni tun wayewar garin yau ban ga Azima da idona ba, ba shine nake tambayarki ko
kin ganta rafi ba"

"Innalillahi wa inna ilaihirrajiun!" Aziza ta faɗa tana jan mayafinta zata fita Hajja na tambayarta ina zata
je, har ta kai bakin kofar zanar gidansu bata kai ga fita ba suka yi mugun karo da Baffa wanda ya shigo a
fijajan hankalinsa a tafin hannunsa, da sauri Hajja da Aziza suka tare Baffa,ganin yanayin da Baffa yake
ciki yasa Aziza fara addua a ranta Allah yasa dai Azima ba Innu Maciji ta kashe ba,idan kuwa ta kashesa
tabbas ta b'allowa yankin kwana yaqi.

Da sauri Aziza ta ɗibawa Baffa ruwa ta kawo ta ba wa Hajja, Hajja ta karba ta ba wa Baffa wanda da kyar
ya yi kurbi daya wanda ya taho masa da kuka,ganin haka yasa ita ma Aziza ta fashe da kuka, Hajja na
ganin Aziza ta fashe da kuka ita ma tasa kuka,nan aka rasa mai rarrashin wani,da kyar cikin kuka Aziza ta
kama hannun Baffa tana faɗin

"Dan Allah Baffa ka gaya mana meke faruwa!"

" AZIZA? JUMALA! AN KASHE INNU MACIJI!! DA MASU TARBAN BAƘIN SHIGOWA YANKIN KWANA SU
BIYU!"

BAFFA na fadin haka Aziza ta sake hannunsa tare da yin zaman yan bori!

"Innalillahi wa inna ilaihirrajiun! mai Azima take son zama?" kasa motsin kirki Aziza ta yi illa komawa da
ta yi tana bin Baffa da Hajja da suke kuka da ido, sai zuwa can Hajja ta ce

"Ya aka yi da gawarhar an binne su ne?" Baffa ya girgiza kai ya ce

"Ba zamu iya hakan ba, ana ganin gawar ba shiri Arɗo da Chubaɗo da Ori suka ce garkuwan fulani da
Galadima da Liman da mutum biyar a fada su tafi yankin ja'i da gawan, yanzu Allah ne kadai yasan me zai
faru an kashewa yankin ja'i Innu Maciji, taya zasu fara fuskantarmu su fahimce mu? Innalillahi wa inna
ilaihirrajun!" nan suka ci gaba da jajinta lamarin inda a karshe Hajja da Baffa zasu fita Hajja ta ce

"Aziza zo muje"murya can kasa wanda take ji da kyar ma take maganar ta ce

"Hajja kuje zan zo"

"To amma kiyi lullubi kafin ki fito anani ko?" Aziza ta gya ɗa kai, kanta a sunkuye, Hajja da Baffa suka
fice,dan Aziza tana ji ba zata iya tafiya ba jin kamar kafafunta basu gangar jikinta.




40
HAUSACINEMA.COM


Bayan fitar su Hajja da Baffa kamar da rabin awa sai ga Azima ta shigo babu sallama kamar an wurgota
ko kallon Aziza ba ta yi ba, da ido Aziza ta bi Azima tana ji kamar ta haɗa musu guba su sha su mutu ko
duniya zata zauna lafiya.




Azima na shiga bukka ta hau dariya kasa-kasa gami da faɗin

"Innu Maciji na kashesa! Yau kuma MAGAJI BAWA zaka mutu! Sauran mutanen yankin nan za a kashesu
ne idan tarzoma ta tashi, dan nasan yankin ja'i ba zasu hakura ba, ta fada tana murmushi tare da zura
hannu dan ta dauko zaren sakar dana da ta saka a kayan Aziza amma ta ji wayam,ido buɗe take warware
kayan Aziza amma bata gani ba,kamar mahaukaciya haka Azima ta fito ta zo ta tsaya a kan Aziza

"Ke Aziza Magaji! Nayi ajiya a kayanki amma ban gani ba" dago kai Aziza ta yi ta kalli Azima sannan tasa
hannu ta share hawayenta ta miƙe a hankali cikin sanyin murya ta ce

"Me kika ajiye a kayana?"

"Mtswww! Bana son rainin hankali Aziza! Ki bamu abuna!?"

"Wani abunki?"

"Zaren sakar dana da na ajiye a kayanki" Aziza ta jinjina kai ta ce

"Owoohhh zaren dana? Na ƙonasa!!" wani zabura Azima ta yi tasa hannu ta shaqi wuyar Aziza ta ce

"Kin ƙona fa kika ce!? Ke meyasa baki son mu dauki fansa ne kam!? Me yasa ba zaki bari na rama mana
abunda aka mana ba! Kin ƙonasa!? Aziza ke mahaukaciyar wace al'karya ce? Na ce ke....." ture hannunta
Aziza ta yi daga wuyarta sannan ta kwalfa mata mari ta ce

"Kin kashe Innu Maciji da samarin fada mutum biyu! Akan me!"




Ɗagowa Azima ta yi ta wanke Aziza da mari ita ma, ta kuma shaƙe mata wuya

"Kin min asara! Shin kin san da cewa jejin lore sau daya tak suke ba wa mutum abu? Kuma dole da zaren
sakar dana zan iya kashe Baffa me yasa! Aziza na ce me yasa! To wlh kin jawowa kowa, yau kisan da
zanyi ban ga mai dakatar dani ba!" tana gama faɗi ta zama macijiya ta sulale ta fice, ganin haka yasa
Aziza ita ma ficewa da gudu.




41
HAUSACINEMA.COM




Bata motsa ba, har Azima ta gama hajijiyarta, ta girgije ta zama macijiya daga ƙasanta, ta ce

"Mu gwada mana Aziza, yau inaji da abunda ba ki ji" murmushi Aziza ta yi ta ce

"Dan kin saƙa zaren dana shine kike tunanin zaki iya dani? Kawai cewa nayi ki faɗa min wanda za ki
kashe da shi, idan ba haka ba na gwada ta wata hanyar" sosai Azima ta haɗe rai fuskarta ya fara komawa
blue ta ce

"Idan zakiyi kawai kiyi! Bana son magana a baki sai dai a aikace!" Azima na gama faɗi ta daga hannunta
ta huro wuta, Aziza na tsaye na kallonta, sai da Azima ta gama hura wutar ya yi jajur sannan ta yi wani
gurnani ta hurawa Aziza, Aziza na

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login