Showing 78001 words to 81000 words out of 94205 words

Chapter 27 - Azima-Da-Aziza-Macizai Ne Complete

20 Jul 2024

37853

183
HAUSACINEMA.COM


Ashe da rabon ba zamu ga masifa biyu ba,munga daya kun ga daya,maganar auren Almazeen kuwa sun
yafe Allah zai bamu wani kar muzo mu bamuci kudi ba mu mutu a banza saianjima anty suka kashe
wayarsu.

Bayan kwana biyu Azima ta warware sai shirin tafiya kaduna akeyi gobe, har yanzu kuma ba a samu
wani rahoto ba dangane da b'arayin, su Almazeen zasu tafi gobe shida Azima, su Hajiya Lawiza kuma sai
ana gobe daurin aure zasu je.

Da washe gari kamar yadda Mazeen ya cewa Azima ta shirya akan lokaci hakan ce kuwa ta kasance karfe
takwas suka kama hanyar kaduna, gaban Azima sai bugawa yakeyi.

Itama Aziza yau da bugun zuciya ta farka dan bata san da maganar aurenta da Nawaz ba duk wannan
hidima sai a daren jiya, tun tara suka tafi gidan gyaran jiki da lalle dan idan basuyi yau ba gobe Sultana
tace ba fita zatayi ba,kuma mom tace dole ayi walima a goben tunda jibi ne daurin aure jumma'a kenan.

Goma da rabi Al'mazeen suka iso, a lokacin gidan ya fara cika da mutane yan biki, yana shiga ciki ya yi
parking din motarsa bugun zuciyar Azima ya tsananta,kallonta ya yi ya ce

"Menene?" girgiza masa kai tayi alaman babu komai

"To fito" suna fitowa Nawaz shima na fitowa daga part dinsa zai shiga wajan mom ta kirasa ya hangi
amininsa, da sauri yazo suka rungumi juna ya kara yi masa jaje, bai ma lura da Azima dake maqale kanta
na mugun juyawa ba ga jiri ga zufa, har sun fara tafiya Al'mazeen ya waigo ya ce

"Azima?" da sauri Nawaz ya juyo ya kalleta tana sanye da black shadow a idonta, fuskar a bude amma
tayi rolling din veilmai rufe rabin fuska,ƙura mata ido Nawaz yayi, ya kalli Al'mazeen yace

"Who is she?"

"I will tell u later, now let's go inside, Azima muje ko?" jinjina kai tayi tana gaishe da Nawaz ya amsa ba
yabo ba fallasa suka shiga, suna shiga aka hau yiwa Nawaz tsiya ango ango aure ba shiri a lokaci guda
mun zata sai mun buga mata gangan gauro ashe yanzu kuwa wa Almazeenu zamu buga mawa, cewar
tsofaffi, su dai dariya sukayi suna hawa sama Azima na kan binsu a baya, dakin mom suka shiga da
sallama mom ta amsa tana yiwa Almazeen oyoyo gaisheta yayi ta amsa cikin kulawa tana fadin

"Ka ga ikon Allah ko? Abokinka zaiyi aure ,da ina shirin takura muku ashe Allah ya riga da yayi ikonsa,
yanzu ma kai zan takura ma wa, naso ace a tare zakuyi aure wlh!"




"Mom ba komai ai,komai lokaci ne nima ranata tana zuwa in sha Allah"




184
HAUSACINEMA.COM




"Amma dai ba da wannan Alishan ba ko?" Nawaz ya fada yana hararan Mazeen

"To wai ina ruwanka?mom ki masa magana"

"E kuma gaskiya ne ina ruwanka kai zaka zauna masa da ita ne" mom ta fada tana daga kai ta kalli Azima
dake tsaye a bakin kofa kanta a duke jikinta na rawa

"Wacece kuma?"

"Amm umm e mom tare muka zo da ita, inasu Sultana?"




"Ayya sannu da zuwa ɗiyata" Mom ta fada tana kurawa Azima ido ganin wani sirhitaccen kamanni da
takeyi da Aziza, duƙawa har kasa Azima tayi ta ce

"Ina kwana mom? Mun sameku lafiya?" hakan da tayi ba karamin dadi Almazeen yaji ba, Mom ji tayi
muryan ma irin na Aziza amma sai dai Aziza ta fita sanyin murya sosai,

"Alhamdulillah! Ga shi kin zo su Sultana sun tafi gidan lalle da gyaran jiki, amma zo na nuna miki dakin
sultana sai ki zauna ki jira su, ko kina so a kaiki gidan lallen kema a miki?"

"A'a ban taba yi ba ma a rayuwata, zan jira su ɗin kawai" mom tayi murmushi ta kama hannun Azima
caraf idonta ya sauka akan zoben hannun Azima iri daya sak da na Aziza,kuma Aziza tace sadda aka
haifesu kakansu Arɗo shi ya ba wa Hajjarsu ta saka mu shi a hannu, daurewa Mom tayi ta ce ya sunanki?

"AZIMA!"

"Ma sha Allah Azima suna mai dadi, Azima wa?"

"AZIMA BANJU!!" ba iyakar Mom ba harta Nawaz wanda yake kokonta sai da ya waigo a firgice, da kyar
Mom ta iya riƙe kanta tana murmushin yaƙe ta rungumo Azima ta kaita dakin sultana sannan ta koma
daki ta samu Almazeen na tambayar Nawaz meke damunsa, Mom Na shigowa Nawaz ya mike yana fadin

"Wlh ita ce mom, yar uwar Aziza ce, Allah Alhamdulillahi³!" Mom da Nawaz suke faɗi, Al'mazeen da
kansa ya shiga duhu yace

"Dan Allah Mom ku min bayani ku fiddani a duhu, dama Aziza tana da yar uwa ne?"mom tace




185
HAUSACINEMA.COM


"Dole zamu maka bayani amma kafin nan a ina kasan Azima ina ka sameta?" bai boye musu ba aiki
takeyi agidansa a cam ma ya sameta dan tun bayanan su Maman Hanan suka gaya masa an dauke
sabuwar mai aiki, har izuwa sadda ya dawo da shakuwar da ta shiga tsakaninsu.




"ALLAH KENAN MAI YIN YADDA YA SO, HAKURINKA BAYA FADI KASA BANZA! ALLAH YA TAKAITA MANA
WAHALA" cewar Mom tana jinjina kai, zama sukayi nan Mom ta hau warwarewa Al'mazeen komai bata
kara ba bata rage ba, Al'mazeen ya zare ido yace

"Kenan mom AZIMA DA AZIZA MACIZAI NE? SANNAN YAN BIYU NE? mom ta gya ɗa kai,

"Kenan Azima ba Azima bace Banju ne?" mom ta ƙara jinjina kai

"Innalillahi wa inna ilaihirrajiun!" mom ta kara da cewa

"Wannan shine dalilin da yasa auren Nawaz da Aziza ya tashi babu shiri dan yin jahadi ya taimaki Aziza"
jinjina kai Al'mazeen yayi ya ce

"Idan har Aminina zaiyi wannan aikin ladan ba tare da ya faɗa soyayya ba ina ga ni da na fara son Azima?
Sannan ta taimakeni da badin sanadinta ba da yanzu b'arayi sun kasheni!" nan ya bai wa mom labari
mom ta hau salati tana sanar da ubangiji, sannan ya kara da cewa

"Ta taimakeni! Ta ceci rayuwata yayinda ta saka nata a hatsari! mom ina son Azima! Ina so kuma jibi
nima a ɗaura min aure da ita amma karta sani, kamar yadda Banju shaiɗanin aljani ne zai iya kashemu
idan har yasan da hakan, sannan ya kamata a gayawa Aziza kar ta dawo gidan nan dan karsu haɗu da
Azima har sai bayan an daura aure" Mom tace

"Hakan ma wata shawara ce mai kyau,idan yaso aka daura auren da washe gari ranar sai mu shirya tafiya
yola,ko kuma da an daura kawai mu wuce tinda Aziza tace cikin daci suke, sai ku shirya mota mai ƙarƙo
da zai iya kaimu zamu tafi da Malam Yunusa da ƙanin mahaifinku da kuma Hajiya Lawiza ko kuma Hajiya
luba"

"E hakan ma yayi mom" cewar nawaz,na suka gama tsara abunda zasuyi.




An gama yiwa Aziza lalle tana zaune,ita kuwa Sultana ana wanke mata nata, gajiya da zaman Aziza tayi ta
ɗan jinginu tana lumshe ido, tana lumshe ido wa zata gani? Azima ta hanga wani ajiyar zuciya ta sauke
da jan numfashi ta buɗe ido tace




186
HAUSACINEMA.COM


" AZIMAA!?" sultana tace

"Azima kuma? Ina kika ganta?"

"Wlh na ganta Anty Sulty ina rintse ido na ganta,ina zuwa bari na sake dubawa" rintse ido tayi ta shafo
tafin hannunta nan ta hangi Azima kwance a gadon sultana, a hankali ta buɗe ido tace

"Azima a gida kuma a dakinki a gadonki?" sultana zatayi magana wayarta ya yi kara, tana dubawa ta ga
mom saurin dauka tayi tasa a kunne tayi sallama mom tace saurareni da kyau Sultana" nan mom tayiwa
sultana bayanin komai sannan tace

Idan sun gama su biya gidan kawarta Hajiya Biba su ajiye Aziza sannan su su dawo, yanzu sultana ki yiwa
Aziza bayanin komai yadda na miki,mom na gama fadi ta ajiye waya,sultana ido bude ta kai bakinta
saitin kunnen Aziza tayi mata bayani dalla-dalla,itama Azizan ido a waje ta kalli Sultana, sultana ta jinjina
mata kai.




Basu gama ba sai gaf magriba dan haka ko da suka tashi suka biya suka ajiye Aziza a gidan Hajiya Biba su
kuma suka wuce gida.

Ko da suka isa Sultana bata nunawa Azima komai ba tayi maraba da ita ta hau janta a jiki.

Nan sanarwan aure ya koma na mutum uku.

Da washe gari walima Mom ta ba wa Azima haɗaddiyar dogon riga wanda yasha stone, a jiya ne ma da
dare tasa aka nemo mata kasancewar ba ayi shiri da ita ba, bata tayi ta saka Azima ta karba ta mata
godiya, kasancewar a gidan za ayi walimar a tare kusa da juna Mom ta zaunar da sultana da Azima,itama
Aziza ana can anayin nata a gidan kawar mom, sadda aka fara wa'azi dodon kunnenta kamar zai
tarwatse ji take har fatarta ƙuna yakeyi dan da karfi Malama Rasheedat Hassan Usman ke fadin Allah
yace Annabi Yace.




Duk wanda yazo ya tambaya wannan itace amaryan Nawaz din sai mom tace a'a ta Al'mazeen ce, lokacin
dasu Maman Hanan suka iso kamar su mutu da bakin ciki dan tun a jiya labari ya iskesu nan suka dinga
tsinewa Almazeen da Azima, har suna cewa dama ya sane ya ƙi fada musu zaiyi aure.

Anyi walima lafiya aka watse lafiya.




187
HAUSACINEMA.COM


Da washe gari karfe sha ɗaya za a daura aure kasancewar su Nawaz zasu kama hanyar yola ne da an
daura aure.




Tun wayewar gari Azima ta kasa zama ta kasa tsayuwa ta rasa dalili, a gidan Hajiya Biba kuwa itama Aziza
ta matsu suyi ido huɗu da Azima.




Ma sha Allah sha ɗaya nayi dai-dai aka shaida daurin auren Khalil Alhaji Yaro da Amaryarsa Sultana Alhaji
Sardauna, sai kuma na NAWAZ ALHAJI SARDAUNA DA AMARYARSA AZIZA MAGAJI BAWA, SANNAN AKA
DAURA NA AL'MAZEEN ALHAJI SAHABI DA AMARYARSA AZIMA MAGAJI BAWA! ana daura aure Azima na
zaune a daki da su Sultana da kawayen sultana nan ta riƙe kirjinta ta hau tari, ana gama daura aure
Nawaz da Al'mazeen da wasu abokai sukayi gidan Hajiya Biba dan dauko Aziza, da lullubi aka fito da ita
kanta na juyawa kasancewar mahaɗi daya suke da Azima wacce take mayuwacin hali a gida su Sultana
sun rufo a kanta.

Da kyar Aziza ke fizgar numfashi ta gaida su Al'mazeen suka amsa ,hankalin Nawaz na kanta yana lura da
halin da take ciki.

Suna isowa gida guɗa ya hau tashi ana ga angwaye ga angwaye, Mom tace su hauro sama, Aziza ta taka
step jiri ya kwasheta zata fadi da sauri Nawaz ya tallabota nan jama'a aka sa ihu ana musu tafi, shi dai
matarsa kawai ya kama suka hau sama, hannun kofar Aziza ta murɗa fuskarta a murtuke, tana tura kofar
a lokacin Azima na duƙe sultana na bubbuga bayanta.

"AZIMA!" Aziza ta kira sunanta murya a daskare, wani wawan dagowa Azima tayi caraf idonta ya sauka
cikin na Aziza wacce Nawaz ke rike da kafaɗunta.




Murtuƙe fuska Banju ya yi ya ce

"Magaji! ba dawowa nayi ba"

"Na sani Banju! ba dawowa kayi ba,jarumar 'yata ce ta dawo da kai"

"Kaii Magaji! Kunceni! Idan ba haka ba yankin kwana ta koma toka! Dan kasan wanene Banju! Bana da
imani! Kasan karonmu da kai!" murmushi Baffa yayi yace

"Amma ni Magaji Bawa! ban gudu ba hakane Banju?" haɗe rai Banju yayi baffa ya ci gaba da fadin


188
HAUSACINEMA.COM


"A yanzu ko Magajiyata Aziza tsaf zan iya sakata kasheka! amma halin da ka sakani yasa nake son
kasheka da hannuna! ka fara ƙirga numfashinka daga yanzu zuwa gobe" dariya Banju ya yi yace

"Ashe kuwa idan zaka kasheni zaka haɗa da 'yarka, karka manta gangar jiki daya muke da ita" Baffa
shima murmushi ya yi ya ce

"Duk makahon da kaji yace ayi wasan jifa yasan ya taka dutse bare mai ido kuma kai ma kasan bakin
rijiya ba wajan wasan makaho bane, a wannan tafiyar kaine makahon inaji ka manta da cewa yanzu haka
Azima na da aure ko? mijinta shine zai fiddaka daga jikinta ni kuma na kawo karshenka ta yadda ba zaka
kuma dawowa ba,kisan farko da na kasheka ban so ba, amma a yanzu ne zan kau da ka" wani ihu Banju
ya yi yana son tsincewa, Baffa yace

"Aziza!" juyowa tayi ta kalli Baffa, Baffa ya mata alama da ido, ta gya ɗa masa kai sannan tayi gaban
Banju tana shirin sake kafar da shi, da karfi ya furta mata "BAHULAAAAA!!" a kunne yana son tada
Bahula dake jikin Aziza, wani ja da baya Aziza tayi ta dafe saitin zuciyarta da kanta, ganin haka yasa Baffa
jan Aziza da sauri ya watsa mata wani farin hoda nan Aziza ta sulale zata faɗi Nawaz bai yi kasa a guiwa
ba ya tare matarsa, da yatsa daya Baffa ya do ki goshin Banju, kamar anyi ruwa an dauke haka Banju ya
tsaya cak, Mom cikin tashin hankali ta kama hannun Aziza wacce take kwance a jikin Nawaz ta ce

"Dan Allah Baban Aziza kayi wani abu, Aziza ta sha wuya wlh! Duk wani masifa kanta yake afkawa dan
Allah tunda ga Azima a cire mata Banju ko Aziza ta huta, me yasa baka kashesa yanzu ba?" cikin kunya
Baffa yace sabida har yanzu yana jikin Azima, idan na kashe Banju a yanzu Azima ma ta tafi!" nan Mom
ta gane abunda Baffa ke nufi, ta kalli Hajja wacce ke tsaye a gefe tayi lullubi tana duƙe da kai, Mom ta ce

"Nawaz shiga da Aziza cikin gida, Maman Aziza? Dan Allah ki daina ɗaurewa kina wannan kunyar taki, ki
saki jiki ki rungumi yarki, an wuce wannan zamanin kunyar, yarki ce fa? Karki cutar da kanki kina son jin
dumin yarki amma ki ta rabewa, dan Allah bana son haka, ai gwara ki ja ta a jiki kafin na dauketa"
rasssss!! gaban Hajja ya faɗi jin mom tace zata dauke Aziza, amma bata iya furta ko da uhum bane tabi
bayan Nawaz da ya shige da Aziza, mom ta ce

"Baban Aziza zamu yi magana" Baffa ya ce

"To madalla bismillah" gefe suka koma suka kebe, mom ta ce

"A ba wa Almazeen matarsa yau suyi mu'amala ta aure dan a kawo karshen wannan masifan, karka ce
zaka biyewa kunya, wajan ceton rai babu zan can kunya, a nema masa inda za a kai masa matarsa, a
gobe ka kashe Banju,idan kuma hakan ba zai yu ba to a bamu su mu koma birni idan yaso komai ya
daidaita a can Banjun ya fita sai a kashesa a can birni sai mu tafi tare da ku, amma ya ka ce?"girgiza kai
Baffa ya yi cikin sauri ya ce

"Maganar a bar yankin nan a shiga gari akwai matsala, ba zan boye miki ba, Almazeenuzai fuskanci
kalubale wajan kusantar Azima, Banju ya wuce duk tunaninki , kuma bayan ya kusanceta zaiyi ciwo, ba



189
HAUSACINEMA.COM


lallai bane ku a cikin gari kuna da maganguna irin tamu ta gargajiya, ga misali a kan Aziza haka tayi ta
faman ciwo sai da ku ka zo kafin ta samu furen huriri ta warke, a nan aka fara yaƙin a nan kuma nake so
a ƙarasata,bana so a kai muku masifa kuna zaman lafiya, burin Banju kenan ya sake barin yankin nan,ni
kuwa ba zan bar haka ta faru ba ta yardan Allah, dazu bayan munyi sallar asuba maganar da Baffa Mandi
da Arɗo suka min kenan a ba wa Almazeenu Azima yau, akwai wani gida da Arɗo yasa aka zagaye a can
kusa da wajan gari, amma akwai tsirarakun fulani a wajan kawai dai gidan ne shi daya, yanzu haka zamu
tafi da shi Almazeenu din, kafin nan zan ba shi wasu magunguna da rubutu su sha shi da Nawazu din,
dan shi ma yana da bukatar haka tunda miji ne ga Aziza" Mom ta ce

"To ba damuwa hakan ma yayi Allah ya iya mana" Baffa ya amsa da amin, mom ta kira Nawaz da
Almazeen tace musu su bi Baffa, Malam Yunusa kuma da kanin mahaifinsu Nawaz Alhaji Karami suna
tare dasu sarki chubado da mai unguwa ori sai hira sukeyi ana shan damemmen fura da nono, gwanin
sha'awa.




Gidan suka je, duk da gidan kara ne amma yadda aka shirya gidan ya burge Almazeen, tarko Baffa ya
saka a ciki da waje ta yadda ko Banju ya fice a jikin Azima ba iya guduwa zaiyi ba.

Sannan Baffa ya ba wa su Almazeen da Nawaz wasu maganguna da rubutu yace su sha, ya basu na kariya
da na sha da na wanka da na gogawa dana murzawa dana ɗorawa duka babu wanda bai basu ba, daga
nan sukayi wani gida gaba kaɗan da na inda aka ba wa Almazeen, Baffa yace

"Nawazu, kai ma a nan zaka zauna ka riƙe Aziza, dan a lokacin da abun da ke jikinta zai fita zata iya shiga
wani hali, zata iya fita hayyacinta, idan kuma ta subuce zamu iya rasata na har abada dan babu abunda
Banju ba zai yi ba" Nawaz yace

"In sha Allah hakan ma ba zata faru ba Baffa, hakuri da gaskiya sune a sama, zamuyi nasara a kan Banju
bi'izinillahi ta'ala!" Baffa ya yi murmushi na jin dadin samun sirkai kamarsu Nawaz da Almazeen, haka shi
ma wannan gidan ma ya saka matakan tsaro.

Wunin ranar kuwa Baffa bai zauna ba shiri yayi sosai ya koma asalin Garkuwa Magaji Bawansa
kyakkyawa fari dogon bafulatani mai dogon hanci da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login