Showing 39001 words to 42000 words out of 94205 words

Chapter 14 - Azima-Da-Aziza-Macizai Ne Complete

20 Jul 2024

37838

84
HAUSACINEMA.COM


"Amm yi hakuri ba nufina na ɓata miki rai ba,naga yadda kika ta kalle-kalle ne kamar baki san kowa ba,
shine nake so na taimaka miki" ya karasa maganarsa yana murmushi, itama Azima murmushin ta yi ta ce

"To taimakona da me? ko nazo nace da kai inada bukatar taimako ne iyee!!? Na ce maka ina da bukatar
taimako ne?"

"Allah ya huci zuciyarki sarauniyar kyawawa, Kano gari ce mai girman gaske da faɗi kuma ke naga alama
kamar baƙuwa ce, dan haka ki yarda na taimaka miki naga ke mace ce,ki zo muje gidanmu" mutuwa da
mamaki Azima ta yi ko me ta tuna ta yi murmushi ta ce

"Na gode da taimako muje"

"Ina kayan ki?"

"Wala!"

Ta ba shi amsa hankalinta yana can wajan kalle-kalle, jakarsa da ledarsa ya dauka ya ce

"Muje" ya yi gaba ta bisa a baya, kekenapep ya tare musu suka shiga, wani farin ciki ne ke mamaye
zuciyar Azima sai magana yake mata amma ina hankalinta ya yi ƙololuwa wajan ganin girma da faɗi da
cikowa irin na NA DABO TUMBIN GIWA, ana cikin tafiya sai ji ta yi kekenapep din ya tsaya sai a lokacin ta
maido da dubanta ga wani ƙazamin gida wanda ko bukkarsu na yankin kwana ya fi sa kyawun gani, bata
damu ba, yayinda ya ce mata ta fito a keken, ba musu kuwa ta fito tana kallon mutanen da suke zaune a
kofar gidan masu caca da masu shan wiwi da sigari har ma da masu shan giya, jin yadda ta hadiyi hayakin
sigari da wiwi yasa ta hau tari kadan-kaɗan tana yamutse fuska, mai kekenapep ya biya sannan ya kalleta
ya ce

"Mu shiga ciki ko?" ya yi gaba ta bisa a baya mutane sai kallonsu suke yi har suka shiga,suna shigewa a
cikin wa inda suke zaune a kofar gidan wata mace tayi shigar riga da wando,duk da babu mai kayan
mutunci a cikinsu, tab'o dayar dake kusa da ita ta yi ta ce

"Kee Bariki Dadi, baki ga Hoge ya wuce da wata bafulatana ba?" wacce aka kira da sunan Bariki dadi tana
riƙe da sigari a hannunta tana zuga suna buga caca ta ce

"Hoge dai? Yaushe ya dawo?"

"Ba mamaki dawowarsa kenan dan na gansa da kayansa" miƙewa tayi da sauri ta ƙudundumo wani ashar
sannan ta yi cikin gidan da sauri wa inda suke zaune a tare suka hau zugata suna fadin "idan kinje kici
uwarta da ubanta! Bariki dadi! Baki da kyau baki da dadi!" suna fadi suna ihu,ita kuwa fuuuu tayi ciki,a
lokacin Hoge har ya buɗe a kulkin dakinsa ya kalli Azima ya ce




85
HAUSACINEMA.COM


"Shigo mana yar fullo" a hankali Azima ta sa kafa ta shiga, a wani jagalgalalliyar katifa ta zauna tana saƙa
abubuwa dayawa a ranta, tana zama sai ga Bariki dadi ta banko kofar kamar zata b'alla shi, Azima bata
dago ba illa Hoge dake fadin

"Wannan wani irin iskanci ne haka?"

"Ga ka nan kuwa babban dan iskaci baƙin munafuki! Ka hanani kula ko wani bunsuru, sannan ka dauko
wata banziya daga dawowarka ka huce da ita a gabana! To wallahi sai naci Uwarta! Ke kuma munafuka
zo nan! Sai wani rufe fuska kikeyi sai kace wata ta Allah kina sunkuyar da kai, to idan baki sani ba ki sani!
Kina sa kafarki a nan gidan dukkan wata mutuncinki ya zube kuma saina koya miki hankali!" murmushi
Azima ke yi a ranta ta ce

"Inason mutane irin haka! Wa inda basu shiga gonata ba ina kau dasu balle wa inda suka shiga" bata
gama maganar zucinta ba Bariki dadi ta shaƙo wuyarta, tashi tsaye Azima tayi,tana tunanin dame zata
kasheta! ta sareta ne ko ta watsa mata dafi? Hoge ne ya fizgi Bariki Dadi ya koɗa mata mari sannan ya
ingizata waje ya juyo yana ba wa Azima hakuri, bata ce masa ci kanka ba,illa da ya gama rawar bakinsa
ya fice wai zai kawo mata abinci, bai jima ba kuwa ya shigo da bakar leda ya ajiye mata, budewa Azima
ta yi nan tayi arba da kayan dadi murmushi tayi dan bata taba ganin kalar abincin ba, da sauri ta buɗe ta
hau ci tana lumshe ido tana gya ɗa kai, shi kuwa yana zaune a gefe yana kallon gashin kanta da ya rufe
mata fuska aransa ya ce

"Hummm! dama ana ganin irin wa innan matan a gaske? Dole na shana wlh,daga ganin wannan ɗanya
ce jaƙab, zatayi ruwa zata kai yadda ake so, idan tayi daga nan zata zama cikata!" sai sambatu yakeyi a
zuciyarsa yana hadiye yawu,Azima kuwa fess ta cinye abubuwan da ya kawo mata, ta kwankwaɗe
maltina har tana lashe baki, tana gamawa ta koma ta jinginu da banko tana sauke ajiyar zuciya ta lumshe
ido,jin saukar numfashi ta yi a wuyarta, saurin buɗe ido ta yi ta gansa ya matsota sosai, sai wani washe
baki yake yi, bata gama karantarsa ba taji yana fadin

"Meyasa kike rufe baiwar kyawun da Allah ya miki da wannan dogon gashin naki? Duk da ba a ganin
fuskarki da kyau amma da an ganki an ga kyakkyawa ajin karshe, dan Allah ki buɗe idanunki na
ganki,sannan ina so ki bani hadin kai nayi miki alkawari zan baki duk abunda kikeso zan miki komai" cije
baki Azima ta yi jin yadda wani baƙin ciki ya mamaye zuciyarta,daurewa ta yi tasa yatsarta babba
manuniya a kan goshinsa, ta ture kansa daga wajan saitin wuyarta sannan ta ce

"Kasan daga ina nake? Sannan ni fuskata kallo daya ake mata,idan har ka gani babu fuskar da zaka kara
kalla a rayuwarka"

"E na yarda ni dai ki bude fuskarki na gani, sannan zan baki abun dadi" ya fadi yana shirin kai hannunsa
kirjinta,da sauri Azima ta ja da baya tana fadin

"Owohh kenan kai ɗan iska ne! Zan koya maka hankali, ka taba ganin maciji?"




86
HAUSACINEMA.COM


"E amma a zahiri sau daya na taba gani kuma ƙarami ne ma,amma ina gani a fina-finai"

"To yau zaka ga Babban a zahiri ido da ido!" ta faɗi tana dariya yayinda ta kwashe gashinta ta maida su
baya,blue eye dinta ya bayyana, a gigice hoge ya ja da baya, yayinda ta hau rikiɗewa,tun kafin Azima ta
taba Hoge numfashinsa ya fara barazanar daukewa, yana ganin zureren Maciji har na sheƙi a gabansa
nan ya fadi sumamme, Azima ta sa baki ta saresa a gabansa, sannan ta koma mutum ta fice, ta zo fita
kenan suna karo da Bariki dadi,shaƙeta bariki dadi tayi,Azima tace

"Dama kafin na tafi ina nemanki!" tana gami fadi ta zaro harshenta ta watsa mata dafi sannan ta bar
gidan.




Kuka Hajja keyi yayinda Inna Wuro da Yawuro suke ta aikin bata hakuri suna rarrashinta,amma pinaa
Hajja kamar ba da ita ake yi ba, idonta ya kumba ya yi him sabida kuka fuskarta ya yi jaa! Baffa ne ya
duka a gabanta ya ce

"Jumala? Kiyi hakuri,In sha Allah idan anyi duniya DAN MANZON ALLAH S,A,W, Azima da Aziza zasu dawo
garemu In sha Allah,kuma yaranki zasu dawo mutane ko da kuwa zan rasa raina na miki alkawari!" ita dai
Hajja bata ce komai ba, tun daga wannan rana Hajja bata um bata um-um, idan ta zauna idonta na kan
bakin kofa,ta ajiye idanunta har izuwa ranar da yaranta zasu dawo gareta.




87
HAUSACINEMA.COM


Fitan Azima yawatawa ta ci gaba da yi,dama ita ba sallah take yi ba balle ya dameta, idan kuma wani mai
kararren kwana tsautsayi tasa ya shiga hidimarta ta kashesa ta yi gaba, yau kwananta uku da shigowa
garin kano bata damuwa da wajan kwana idan dare ya yi duk babbar bishiyar da ya mata zata zama
macijiya ta hau ta kwanta tayi bacci ko ta huta, yau ta fito tana cikin tafiya taji ƙaran mota ƙiiiiiii! da sauri
ta juyo ta ga wata matashiyar budurwa ce wacce zata kai shekara ashirin da biyar,fitowa tayi tana
zazzagawa Azima zagi, yayinda take binta da ƙaramin kallo

"Ban da hauka taya zaki rufe fuska ki dinga tafiya a kan titi! Sakarya kawai bagidajiya!!" cije baki Azima
tayi meyasa ake son ce mata bagidajiya? duk da bata san ma'anar kalman ba amma taji ta tsani kalman,
lankwabe murya ta yi ta ce

"Dan Allah ki taimaka mini, ni yar gudun hijira ce an kashe dukkan yan uwana a rigarmu ni daya ce kawai
na rage,ban san kowa ba ban san inda zanje ba, dan Allah ko aiki ne a gidanku ki nema mini zan dinga yi"
yatsine fuska ta yi tana fadin

"Kuma fa kamar naji Hajiya na neman mai aiki,to amma gaskiya sai dai na sakaki a cikin both dina dan ba
zaki shiga mini mota ba"

"Ina ne shi hakan bat din?"

"Banza jahila both nace, nan kenan zo ki shiga" ta fada tana mata nuni da both tana budewa,Azima ta
shige tana murmushi tare da fadin

"Matakin farko!" tana rufe murfin both din Azima ta koma Macijiya, shiga motar tayi ta ja tana tsaki.




A kwana ukun nan Aziza ta fito daga bakin titi ita ma,tana fitowa ta zube a kan titi tana sakin kuka tana
kiran sunan Hajjanta da Baffanta, Inno Fandi ce ta taimaka mata ta fiddota bakin titi sannan ita ta koma,
kuka sosai Aziza ta yi kafin ta tashi ta hau tafiya, tana ganin kamar ta shigo wani sabuwar duniya ne, bata
ma san a inda take tafiya ba, shi kuwa da sauri yake jan mota,yana driving yana duba tym, wayarsa ce ta
yi kara yana dubawa ya ga Friend 4 Life, dagawa ya yi, ya ɗan yi shuru tukunna kafin ya ce

"Hey Dude bazan maka karya ba,wlh bazan je na dubasa ba,guy din nan ya raina min hankali, jiya banyi
niyyar kwana a garin yola ba amma ya sakani kwana, yanzu haka ma nikam gani a hanya ko kwana zanyi
sai dai na kwana amma yau din nan sai na kasance a cikin garin Kd in sha Allahu!" yana magana a waya
ransa a b'ace sai ji ya yi, ya yi sama da mutum, wani mahaukacin burki yaja ya fito da gudu, yana isowa
gareta tana lumshe ido, duk da bai ga fuskarta da kyau ba gashi ya rufe amma daga ganinta a jeji ta fito,
kallon gabas ya yi,ya kalli kudu,ya kalli arewa,ya kalli yamma bai ga wani ɗan adam ba, shi a tunaninsa
sun fito kiwo ne yan uwanta suka tafi suka barta, to amma idan haka ne shi ya zaiyi da ita? Ga kanta ya



88
HAUSACINEMA.COM


fashe yana zubda jini, "No dogon tunani ba nawa bane i need to save her lyf first" ya faɗa yasa hannu
yana shirin daukarta, wani mummunar faduwar gaba ce ta riskesa inda yaji dukkan wata gab'a ta gangar
jikinsa ya sake, saurin kauda abun a ransa ya yi ya dauketa ya sakata a mota ganin bata motsa, yana
addua Allah yasa dai bata mutu ba.




Murmushi ya mata ta zo ta rungumesa tana yi masa sannu da hanya, ya amsa da "yawwa sannunki,ina
Mom kar dai har tayi bacci?"

"Kai anya kuwa, da muna zaune da ita a nan bata jima da tashi ta hau sama ba"

"Okay bari na dubata" ya faɗa yana maida dubansa ga tv'n ya ce

"Ke da kallon horror ko, sai kin fara ganinsu a gaske zaki sani" murmushi Sultana ta yi ta koma tana zama
shi kuwa ya hau sama,dakin Mom ya shiga da sallama tana zaune tana waya, zama ya yi kusa da kafarta
har sai da ta gama wayar ta ajiye kafin ta kallesa cikin kulawa ta ce

"Nawaz sai yanzu? Ya hanya an dawo lafiya?"

"E wlh Mom, Alhamdulillah! ina wuni? Ya gida? na sameku lafiya?"

"Alhamdulillahi Doctor, fatan dai lafiya ko? Ko dai gajiya ce dan fuskarka ta tuna,yanzu haka ma da
Amminka muka gama waya wai ta kiraka wayar bata shiga nace ba mamaki hanya ce ba netwrk"

"E hakane zan kirata gobe yanzu dare yayi zan shiga part dina,kunyi waya da Son dinki ne Mom?"

"E dazu ya kirani dan albarka"

"Mom muna cikin waya da shi dazu tsautsayi tasa na buge bafulatanan yarinyar mutane"

"Subhanallahi!" Mom ta faɗa tana zabura

"Kwantar da hankalinki Mom tana hospital dina" nan ya bata labarin yadda hatsarin ya kasance har
izuwa shawaran da ya yanke na tahowa da ita kaduna idan taji sauki sai a maidata gida, Mom ta sauke
ajiyar zuciya ta ce

"Shawaran da ka yanke mai kyau ne Nawaz, Allah ya bata lafiya, ma je mu dubata gobe idan Allah ya
kaimu ni da Sultana"

"Allah ya kaimu Mom" ya faɗa yana duba agogon hannunsa



89
HAUSACINEMA.COM


"Dare yayi Mom zanje na kwanta na huta akwai gajiya a tare dani"

"To Allah ya tashemu lafiya a huta gajiya,Allah ya yi albarka" Nawaz ya amsa da amin yana tashi ya fice a
dakin, yana saukowa ya kalli Sultana ya ce

"Idan baki kashe tv'n nan kinje ki kwanta ba Allah sai na zaneki" da sauri Sultana ta miƙe ta kashe tv'n
kasancewar tasan halin Yayan nata, sai da ya ga ta hau sama kafin ya fice ya nufi part dinsa, wanka ya yi
ya gabatar da salloli har da nafila ya jima yana addua kafin ya tashi ya koma gado ya kwanta,har ya
lumshe ido ya buɗe ya dauki wayarsa ya kira Amininsa suka hau ɗan taba hira inda yake ba shi labari ya
buge bafulatana, Allah ya kiyaye gaba ya masa,sannan ya ce

"Yaushe zaka dawo america?" Nawaz ya sauke ajiyar zuciya ya ce

"Nan da 2wks In sha Allahu,but idan nazo ina shekarar karshe zamuyi mu dawo gida gabadaya?,dan
gaskiya na gaji da zaman outside"

Daga can bangaren ya ce

"In sha Allahu, duk da ni bana son zaman nigeria gaskiya"

"To ya zaka yi dole ka dawo,duk lalacewa kasarka kasarka ne, sannan karka damu da abinda Momma
take maka, ka ci gaba da yi mata biyayya a matsayin uwa,wata rana zata gane In sha Allah" ajiyar zuciya
ya sauke, nan Nawaz ya gane damuwar dake damunsa dan haka ya kau da hiran ya jawo musu wata, sun
kai biyun dare kafin suka yiwa junansu sallama, yana ajiye wayar bai jima ba bacci ya kwashesa,yana
cikin bacci ya hau mafarkin yarinyar da ya buge da mota, suna cikin wani ƙasurgumin jeji sai faman ihun
take zabgawa tana fadin ya taimaketa ya taimaki rayuwarta, tana ihu tana gudu yana binta a baya, da
haka har suka je jikin wata babbar bishiya taja ta tsaya kanta a sunkuye tana sanye da kayan fulaninta,ta
ƙanƙame jikinta tana ihu, shi kuwa yana riƙe da fitila a hannunsa yana haskawa sabida tsananin duhun
jejin, yana shirin matsowa gareta ya ga mummunar tashin hankali dan kuwa gani ya yi ta koma wata
zabgegiyar macijiya fara sol sai ƙyalli take yi,tana ci gaba da ihun ya taimaketa.




A mugun gigice Nawaz ya farka yana fadin

"INNALILLAHI WA INNA ILAIHIRRAJIUN!!³" hannu ya miƙa ya kunna wutar dakin ya rike kansa da karfi
dan ji yakeyi kamar kan na shi zai faɗo kasa, gabadaya jikinsa ya jiƙe da gumi, yayinda ko wani kofar
gashi ta gangar jikinsa ya buɗe sun miƙe tsaye, jijiyoyin wuyansa duk sunyi waje, jikinsa sai b'ari yake yi
har yana jin wani zazzabi, da kyar ya jawo wayarsa ya duba tym ya ga karfe biyar, tashi yayi ya shiga
bathroom ya dauro alwala ya tada sallah, yana nan zaune yana addua har aka kira sallah, sai da yayi



90
HAUSACINEMA.COM


raka'atul fajir sannan ya miƙe da kyar ya fita zuwa masallacin da yake wajen gate ɗin gidansu, bayan an
idar da sallah ya shiga ya gaida Mom bai wani zauna ba yace mata kansa na ciwo zai sha magani ya
kwanta dan bai samu bacci daren jiya ba, Allah ya kara sauki Mom ta masa ya koma part dinsa ya
kwanta, ba jimawa bacci ya sake kwasansa amma still mafarkin daren jiya shine ya kara tayar da shi,
cikin kiɗima ya zauna a bakin gado yana tunani barkatai.

"To miye haɗina da wannan yarinyar? daga haɗuwa da ita jiya shikenan sai na kasa bacci? ni da ko
fuskarta ban gani da kyau ba gashin kanta ya rufe! sannan me hakan yake nufi nake ganinta a macijiya!?
ko dai ba mutum ba ce? kai inaa a'a ko dai wani abu ya sameta ne a asibitin?" sauri tashi ya yi ya dauki
jallabiyarsa yana kiran nurse's din da ya basu kula da ita,amma babu wacce ta daga a cikin su biyun, tym
ya duba ya ga 7:30 da sauri ya zare car'key dinsa ya fice ya bar gidan ya nufi asibitinsa mai suna ALWAZ
HOSPITAL KADUNA.




Yana isa ko parking bai gama ba ya shiga ciki da sauri,yana shiga reception ya samu nurses ɗin suna
bacci, a tsawance ya tayar dasu nan ya hau su da faɗa a kan basu san aikinsu ba, hakuri suka hau ba shi
amma bai tsaya ya sauraresu ba illa dakin da Aziza ke kwance,kamar yadda ya barta jiya haka ya sameta
tana bacci gashinta ya rufe mata fuska,yana ganin lafiyarta ya saki ajiyar zuciya wanda bai san dalilin
hakan ba bai ma san lokacin da ya saki ba, dubata ya sake yi ya ga zata iya farkawa ko da wani lokaci,
hannu yasa da niyyar kwashe gashin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login