Showing 90001 words to 93000 words out of 94205 words
aiki wacce zata dinga tayata aiki da zama dan ita daya ne, sai da ta
gama wayarta ta fuskancesu ta ce
"Sannunku da dawowa fatan komai lafiya?" Almazeen ne yace
"E mom komai lafiya alhamdulillah! Amma muna kewan matayenmu,bamu san halin da suke ciki ba ,su
ma basu san wanda muke ciki ba" mom tayi murmushi tace
"Haba dai ai wata biyu kamar kwana biyu ne a wajan ubangiji" sai a sannan Nawaz ya yi magana fuskarsa
a haɗe
"Mom wata biyu kuma? Ba wata daya naji kince ba? Baffa ma fa wata daya naji yace" mom tace
"E wata daya ne nice nace suyi wata biyu" tashi Nawaz yayi zai fice mom tace
"Akwai abinci a dinning"
"Bana jin yunwa" yana gama fadi ya fita, Almazeen shi ma tashi yayi mom tace
"Kana nan ne tukunna?"
"A'a mom zan tafi gobe naje na duba asibitina nima, ba zan dawo nan kusa ba sai an kwana biyu idan
zamuje kwaso matanmu" mom tace
"Ya kamata a haɗa musu lefe ayi shagalin biki, ya kasance kafin su dawo an tanada musu komai, da kuma
gida wajan zama, shin a gidanka na kano Azima zata zauna? Kasan fa yanzu ba kamar da bane, Aziman
yanzu ba jin dadin zama zatayi dasu Hajiya Lawiza da yaransu ba, Azima kuma matarka ce amanace a
hannunka a san abun yi gaskiya" komawa Almazeen yayi ya zauna yace
"Mom ko da a kano na zauna da Azima wlh su Maman Hanan zasuje su takura mata, inaga gidan dake
kasan unguwan nan zanje na taya naji, tunda babu abunda nake yi a kanon idan kuma ta asibitina ne ni
zan iya zuwa ina kwana biyu ina dawowa" mom tace
"Hanya zai aureka kenan, to ba matsala Allah ya zaba mana abunda yafi alkairi, ka ga shi abokin naka ba
shi da matsala a nan zasu zauna dani" Almzeen yace
"Ai hakan yafi mom shiyasa nima zan dawo cikin masu sona kawai" mom tayi murmushi, sun jima suna
tattaunawa har wajan sha biyu kafin ya yiwa mom sai da safe ya tafi, a kwance ya samu Nawaz ya ɗora
hannu a fuskarsa alaman tunani, zama shima ya yi, Nawaz yace
"An rabaka da matarka amma me ka zauna mom ke gaya maka? Ai wlh na fahimci mom idam na ci gaba
da zama zata iya cewa su yi wata shidda ma" da sauri Almazeen yace
211
HAUSACINEMA.COM
"Kamar kuwa ka sani cewa tayi sai sunyi shekara" wani zabura Nawaz ya yi yace
"She mene?"
"Shekara" Almazeen ya fada yana dariya, tsaki Nawaz ya yi, sai da mazeen ya gama dariyarsa kafin ya
basa labarin yadda sukayi da Mom, Allah yasa mu dace, Nawaz ya faɗi tare da shigewa daki ya kwanta,
amma kamar jiya ya kasa bacci dan kuwa sun bar wa juna abin tuni.
Ta bangarensu Azima da Aziza yadda mazajen nasu ke ji a kansu haka suma suke ji a kansu.
Da washe gari Almazeen na wanka dan zai tafi kano yau Nawaz na danna system, wayar Almazeen ne
yayi kara yayi kara yana dubawa yaga Alisha
"Mayya!" Nawaz ya fadi a fusace yana ci gaba da aikinsa,jin kiran wayar takeyi babu fa shi yasa ya jawo
wayar zai daga wata daraba ta faɗo masa, murmushi yayi tunowa da haukan kishin Alisha dan haka
Nawaz ya daga kafin Alisha tayi magana yace
"Wai ke baki san yayi aure bane?"
"What!?"
"Yes daidaine abunda kikaji na fadi, yanzu baya yayinki! Idan kuma baki yarda ba zan gwada miki kiji dan
ki tabbatar da abunda nake gaya miki sabida...." maganar Nawaz ne ya tsaya sakamakon fitowa da
Almazeen yayi, Nawaz yace
"Allah ya taimaki Majnun na Azima! wai ni kam ina Alisha ne Almazeen?" mazeen ya riƙe kai yace
"Wlh nikam na ma mance da ita"
"Kar dai kace min bata san kayi aure ba?"
"Wlh bata sani ba,har shakkar gaya mata nake dan ban san yadda zata dau lamarin ba" Nawaz yace
"To ai ga shi sai ka gaya mata" ya fada yana mikawa Almazeen waya, wani zare ido Almazeen yayi Nawaz
kuwa ko a jikinsa, ba yadda ya iya haka ya karbi wayar yana shirin yi mata bayani ta wankesa tass a kan
cewa ya ci amanarta kuma babu ita babu shi, tana gama gaya masa ta ajiye wayarta.
212
HAUSACINEMA.COM
"Me kenan kayi haka Nawaz?"
"Me kuwa nayi? Ita fa ta kira! Cika min kunne take,kuma ma ai taimakonka nayi" ya fada yana ci gaba da
aikinsa, Allah ya kyauta Almazeen ya fadi Nawaz ya amsa da amin, yana gama shirinsa ya shiga ya yiwa
mom sallama a lokacin an kawo mata wata mai aiki, Allah ya tsare ta masa ya amsa amin sannan ya
shiga motarsa sai kano.
Haka suka ci gaba da rayuwarsu amma hankalinsu yana kan matayensu wanda suma kullum acikin
tunanin mazajensu suke, ga shi babu netwrk babu waya bare a ji muryan juna ko hankali zai kwanta, a
daddafe akayi sati biyu, Almazeen yaji ina sam ya kasa hakuri ya tattaro yazo Kd yacewa mom zasu je
dauko matayensu Mom tace aa suyi hakuri dai a cike sati biyun, da kyar sukayi sati uku hakurin Nawaz ya
kare ya shirya tafiya ya cewa mom zaije kano, mom ta tambayesa lafiya kuwa yace mata lafiya lau kawai
zaije bikin wani abokinsu ne dama kuma yana da tiyatan da zaiyi a can, Allah ya kiyaye hanya a dawo
lafiya mom ta masa
Nawaz yana zuwa kano dama tare suka shirya tafiyarsu shida Mazeen nan suka dauki hanyar yola ba tare
da sanin mom ba.
Sai da suka kwana da washe gari suka yanki jejin kwana, kasancewar Nawaz ya ƙware a driving
musamman ta fannin gudu yasa wajan biyar suna cikin yankin kwana, tun shigowar motarsu yara suka
hau bi, a lokacin kuma Azima da Aziza suna kwance a bukka Hajja tana gidan Arɗo, Azima ta tsokani
Aziza, Aziza ta hau binta da gudu zata daketa kanta ko dankwali babu, a wannan gudun ne suka fito har
waje daidai a kan idon Nawaz da Almazeen, ga shi sun wani kara bulbul dasu sun ciko, wani daci Nawaz
ya hadiye yana wurgawa Aziza harara, ganin basu san da zuwan su bane yasa Nawaz danna horn da karfi
a firgice suka juyo, ko wacce idonta a cikin na mijinta ya sauka, gaban Aziza ne ya buga ganin hararan da
Nawaz ke binta da shi, ita kam shikenan ta shiga uku, ranar da zai tafi ba ayi rabuwar dadi ba, yau kuma
ya dawo za a fara rigima,tukunna ma me ya kawosu? Ai ba yau bane ranar da ya kamata ace sunzo
daukarsu, Azima ce tayi karfin halin murmushi duk da itama zata iya cewa ba yanzu bane ya kamata ace
sun dawo daukarsu ba, Nawaz ne ya hangi wani ɗan fullo rataye da sandarsa a wuyarsa yana tahowa ga
Aziza kai ba dankwali tsoro kuma yasa ta kasa gaba ta kasa baya, da sauri Nawaz ya fito a motar yazo ya
ja hannun Aziza suka wuce gida, ganin Nawaz ya fita yasa Azima shiga motar da sauri tana yiwa
Almazeen oyoyo.
213
HAUSACINEMA.COM
yana rungumeta ya saki ni'imartacciyar ajiyar zuciya
"I miss u!" yaji ta fadi, saurin sakinta yayi yace
"Wow! Aziza ta koya miki kenan!" gya ɗa kai tayi tana murmushi tace
"Yanzu nima inajin yaren sosai"
"To yayi kyau, ina Baffanmu da Hajjarmu?"
"Baffa yana fada,Hajja kuma taje gidan Arɗo, amma na tabbata yanzu labari yaje garesu kunzo yanzu
zaka ga hajja har ma da Baffan"
"To kafin su zo ,mu sha soyayya a mota tinda Nawaz ya ja Aziza ciki" ya fada yana shirin kama bakinta
tace
"Amma naga kamar da fushi ya jamin yar uwata,kuma wlh laifi nane, dan tana kwance na
tsokaneta"jinjina kai Almazeen yayi yace
"Nima naji haushin wannan tsalle-tsallen naku, kawai murna da farincikin ganinki ne ya danne fushina,
amma shi baya iya control ɗin fushinsa sam, dan Allah karki sake" a sanyaye Azima tace
"To kayi hakuri Hamma Mazeen"
"Ai ya wuce" ya faɗa yana shafota.
Suna shiga cikin gidan, bukkarsu ya wuce da ita, suna shiga ciki ya saki hannunta a masifance yace
"Ashe baki da hankali? Miye haka? Au ashe da bamu nan abunda kukayi kenan? Guje-guje? Wannan ai
kauyenci ne! Da Aurenmu a kanku amma kuke guje-guje ga karti na wucewa, ke da shike kece isassa kai
ba dankwali ko? Ya miki kyau ki shirya gobe zamu tafi" zaro ido Aziza tayi kwalla na cika a idonta kafin
tayi magana yace
"Okay wato baki son tafiya sabida can babu maza da guje-guje ko?" yana cikin faɗa da masifa ta
rungumesa ta ce
"Sorry!" tana fadi kuwa yayi shuru da fadan nasa, yayi missing dinta dan haka yasa hannu ya rungumeta
yace
"Karki sake, hakan da na gani ya taba min zuciya"
214
HAUSACINEMA.COM
"In sha Allah, kayi hakuri" zaiyi magana suka ji sallamarsu Hajja dasu Almazeen da Azima dasu inna wuro,
fitowa Nawaz da Aziza sukayi inna wuro tace
"Ohh Allah wato kai har ka wuce daki da ita? Wai wai wai kar ayi abun kunya bari Magaji yazo a baku
matayenku" Nawaz da Almazeen sukayi murmushi nan aka hau gaisawa, Hajja tana tambaya ya mom,
suka amsa da tana lafiya tama ce a gaishesu (kaji su Almazeen da Nawaz da karya mom da bata san
sunzo ba).
Bayan sun gama gaisawa da matan suka wuce wajan Baffa a fada, nan aka hau gaisawa suka shaidawa
Baffa sunzo daukar matansu ne zasu tafi gobe,Baffa Mandi da Ardo da sarkin yankin kwana mai murabus
chubado suka hau dariya, ardo yace a basu matansu kawai su tafi, nan suka ce su gobe suke son komawa
Baffa yace ba damuwa Allah ya kaimu.
Ko da suka zo hira Nawaz da Aziza basu yi wani dogon hira ba ya jaddada mata akan su shirya da wuri, su
Almazeen ne da Azima aka sha luv shima ya gaya mata su shirya da wuri.
Asubanci sukaku ma yi inda jama'a aka fito rakasu, hajja kam taki fitowa rakasu, Azima da Aziza kuka
kamar ransu zai fita,itama Hajja kukan takeyi, su Inna wuro ne suka yi musu nasiha akan su bi Allah da
Manzon Allah sannan su bi mazajensu,yi nayi bari na bari shine aure, da haka suka shiga mota ana daga
musu hannu nan Nawaz yaja motar da gudu suka hau tafiya, a hanya Almazeen ne ya rarrashi Azimansa,
Aziza kuwa da tayi kukanta da kanta ta bawa kanta hakuri tayi shuru.
Sai shidda suka fice a jeji, kamar yadda suka saba hotel suka kama, ko a daki Nawaz baccinsa yayi, Azizan
ma haka, Almazeen kuwa yaso kashe arnan sama Azima ta hau masa kuka dole ya kyaleta ya lallatsata
kawai ya barta, ko da mom sukayi waya da Nawaz da daddare a lokacin suna yola take ce masa ta kirasa
bai shiga ba yace mata ai sun shiga tiyata ne gobe ma suna nan dawowa, Allah ya dawo dasu lafiya mom
tace.
Da safe sai wajan takwas kafin suka sake kama hanya a wannan lokacin anyi canji Almazeen ne ke driving
Nawaz na zaune a gefe Azima da Aziza suna zaune a bayan mota, jifa-jifa suna ɗan taba hira.
Sai wajan hudu suka shigo garin gwamna, basu zarce ko ina ba sai gida, da sallama suka shiga a lokacin
mom na magana da sabuwar mai aikinta Lami taji sallamarsu Nawaz, amsawa tayi tana juyowa sai
ganinsu Azima da Aziza tayi, da mugun mamaki mom ke kallonsu kafin tace
"Dama dauko su Aziza kukaje yi ne?" Almazeen ya hau sosa kai, Nawaz yace
"E wlh mom, cewa akayi Aziza nata kuka tana so ta dawo ta ganni tayi kewarki,ko zakice ba haka
bane?"ya fada yana kallon Aziza wacce tayi narai-narai da ido tace
215
HAUSACINEMA.COM
"Wlh mom ba haka bane"
"Ohh nayi karya kenan?"
"Ni dai ban ce ba, amma wlh ni banyi kuka ba ko Azima?" Azima ta kunshe dariya tace
"Ni dai ban sani ba" mom tace kyalesu na san ba zaki ce ba, to sannunku da kokari ance ku bar yara suyi
wata kunje kun kwasosu ai shikenan, Azima Aziza ku hau sama dakin sultana na da, suka amsa da to
sannan suka hau sama, mom tace
"Maganar lefensu dama jibi ne za a kawo,shagalin bikin fa?"
"Mom dan Allah a bar wani maganar shagali" cewar Nawaz,mom tasan halinsa duk wa innan abubuwan
bai damesa ba, mom tace gobe kasa a kwashe kayan part dinka a kawo sabbi dan dama munyi wannan
maganar dasu Baffan Aziza da yan uwanta kafin mu dawo, na gaya musu mu yaran kawai mukeso, amma
dik da haka mahaifinsu ya bada garken shanu biyu na Azima da kuma Aziza yace dai ba dadi ace yara ba
a ga kayan da yan uwansu suka musu ba, bare kuma ace akwai uwa da uba, na karba ne dan ya fimu
gaskiya, dan haka Almazeen ya maganar gidan naka?"
"Eh mom an gama magana gobe ma za a iya zuwa ayi jere dan haka zamuyi other tare da Nawaz"
"Eh hakan ma yayi, ai da wasu daga yan uwansu sunzo sun ga inda yaransu zasu zauna, ko da yake ba
damuwa zasu zo wata rana" nan su mom suka gama tattaunawa, bayan sallar magriba Aziza ta cewa
mom zataje gidan anty sultana, mom tace je ki tambayi mijinki, dabadin tana son zuwa gidan Sultanan
ba da ta hakura, amma haka tayi jahadi taje part dinsa tace masa zataje gidan sultana, ga mamakinta
yace mata ta shirya ya kaita, da murna kuwa suka shirya harda Azima, a tare suka je yiwa mom cewa sun
tafi,mom tace
"Azima kin gayawa Almazeen cewa zakije?"
"A'a mom, to karki fita a gidan nan har sai kin gaya masa"
"Mom baya nan" Azima ta fada kamar zatayi kuka
A waya mom ta kira Almazeen ta gaya masa azima zasuje gidan sultana yace ba komai sai sun dawo, a
tare suka fito suka shiga mota dan Nawaz na mota,gidan sultana ya kaisu, da sallama suka shiga sultana
na saka turaren wuta ganin Aziza yasa ta saki ihu tana rungumeta cike da kewar juna, haka ma ta
rungume Azima,nan suka baje a parlour suna hira sultana ta kawo musu ruwa da lemo nan aka hau
labari, har sai da Nawaz yazo daukarsu karfe tara kamar karsu rabu, nan Nawaz suka gaisa da khalil
sannan ya cewa su Aziza su shiga su tafi gida.
216
HAUSACINEMA.COM
Kamar yadda suka tsara da washe gari aka zo aka canza kayan parlour da daki aka saka sabbi,mom ce ta
tambayesu ra'ayin kala, Aziza tace pick Azima tace purple, kai mom tayi kokari sai son barka Ma sha
Allah, a ranar da yamma ta kira kawayenta aka zo aka raka Azima gidanta da babu nisa sosai a nan kd
dan Mazeen yace ba zai kai Azima can kano ba, bayan an dawo daga rakiyar Azima mom da kanta ta
dauki Aziza ta kaita part din Nawaz,kamar yadda tayiwa Azima Nasiha haka ta yiwa Aziza, daga nan ta
tashi taje tayi kwanciyarta, mom na fita Aziza ta sulale kafin Nawaz yazo ta koma dakinta na da tare da
Lami suka kwana, haka Nawaz yayi neman duniya bai ga Aziza ba.
AL-MAZEEN kuwa yau yake ango dan dadin da baiji ba ranar yau ya shata a wajan Azima dan kuwa ta
shayar dashi ni'ima, bai sarara mata ba ko kaɗan ita kam ta miƙa wuya tabi dama kuma sun sha gyara, da
washe gari ma haka ta ga tattalin soyayya da kauna.
Aziza kuwa wasan boya suka fara da Nawaz a gidan, haka zai wuni bai ganta ba a kwana bai ganta ba, har
aka kwashe sati daya yana neman hanyar da zai damƙeta zata gane bata da wayo dan ya ga alama ta
rainasa.
Yana kwance waya ta shigo masa yana dubawa ya ga daga outside ne, dagawa yayi nan aka shaida masa
ana nemansu a america akwai wani course din da zasu sakeyi na shekara daya, wani tunani ne ya faɗo
masa nan yace ya amince zasu zo, Almazeen ya kira ya shaida masa halin da ake ciki, Almazeen ma
amincewa yayi, sannan Nawaz yaje ya samu mom da maganar sannan ya gaya mata zasu tafi da
matansu, mom tace babu damuwa sai suyi musu passport yaushe ne tafiyar! Nawaz yace nan da sati
daya amma ranar labara zasu tafi abuja a can za ayi musu komai, Allah ya kaimu mom tace.
Labari ne ya iske su Azima da Aziza zasu tafi america, wai! kirjin Aziza kamar zai faɗo kasa dan firgici,
Azima kam an zama yar hannu.
Sai ranar da zasu tafi abuja Nawaz ya sa Aziza a idonsa, suna hada ido kwafa ya mata, mom ta rakosu har
bakin mota tana musu adduar Allah ya tsare.
Awa biyu da rabi ya kaisu Abuja a ranar aka yiwa su Azima da Aziza komai kasancewar da kudi a kasa, da
washe gari kuma suka ɗaga kasar waje.
Sun isa lafiya inda sukayi waya da mom suka ce mata sun isa lafiya, gidan da suka sauka yanzu mai part
biyu ne dan haka Almazeen ya ja matarsa suka nufi part daya, Nawaz ma hannun Aziza yaja suka nufi
dayan, suna shiga bedroom ya tureta a gado ya bita ya danne yace
"Kin rainani ko? Yau zamu raba raini, ki tashi ki watsa ruwa yau zaki bani hakkina!" ido waje Aziza ke
kallon Nawaz shi kuwa ya ki yarda ma su haɗa ido.