Showing 63001 words to 66000 words out of 94205 words
Allah karki koreni! Dan Allah karki ji tsorona!" girgiza mata kai Mom
ta yi ta ce
"Ko daya ba zanji ba, kamar yadda kike a da haka kike a yanzu, ai ba laifinku bane, a gaskiya Banju ba
karamin mugu azzalumi bane marar imani, Allah sai ya saka muku, Allah ya bayyana mana Azima lafiya,
Allah kuma ya kare bayinsa wanda Banju yake shirin tarwatsawa" suka amsa da amin,bayan sun gama
yan koke-kokensu da jajinta lamarin Mom ta miƙe ta fice zuciyarta cike da zullumi, abu sai kace a film,
bata fata ta ga Aziza a macijiya a labarin ma ya isa, Mom na fita Sultana da Aziza suka sauke ajiyar zuciya,
Sultana ta ce
"Alhamdulillahi! Mom ta rage mana aiki"
"Kamar ya?"
"Da taji mana, da yanzu muna nan muna wallahi tallahi dake" murmushi Aziza ta yi tace
"Duk da haka ku zuciyarku daban yake, mutane irinku kaɗan ne"
"Humm! Yanzu ke kuma kenan dolekafin ki koma mutum sai kunyi aure?"
"Ai babban damuwar yana jikin Azima, idan har ta warke nima na warke In sha Allah, amma da kamar
wuya a samu wanda zai auremu har ya taimaka mana mu dawo mutane kamar kowa"
"In sha Allahu, Allah zai kawosa,kuma zaki gani,muddun kunyi tawakkali Allah zai dubi hakurin da kukayi
na cinye wannan babban jarabawan, sannan ya saka muku ta yadda baku tunani"
"Haka ne kam" Aziza ta faɗa tana gyara zama, sun jima suna hira.
145
HAUSACINEMA.COM
Bayan kwana biyu komai ya dawo dai-dai, kamar yadda Khalil ya faɗa zai dawo cikin sati to hakan ne ta
kasance,dan kuwa shirye-shiryen dawowarsa akeyi,dan da ya dawo biki kawai za a sha, yace ayi biki a ba
shi matarsa.
Ranar lahadi da da daddare ya iso gari, bayan da ya huta maganar biki Hajiyarsa ta hau masa, yace tunda
yau ya dawo a bari nan da kwana hudu ko biyar sai aje dan a saka rana, duk da shima Nawaz ɗin yace
zasu dawo su ma kwanan nan, da haka suka ajiye maganar.
Washe gari da misali karfe goma na safe yasha wankansa yasa manyan kaya na mutunci ya shiga ya
gaida hajiyarsa, ta ce
"Khalil ina zuwa ne haka? Ko dai za a je ganin ɗiyata Sultana ne?"
"E wlh Mom, zanje dai gaishe da Mom ne"
"Ah ba wani nan kar ma ka wani fara fakewa da Mom Ah to ,a gaishe min da su Sultanan" tashi ya yi
yana dariya yace zasuji sannan ya fice.
Bai gayawa Sultana a kan cewa zai zo da safe ba, ya dai gaya mata ya shigo kaduna da daddare da
misalin takwas da rabi, ko da ya isa gidan kasancewar mai gadi ya san shi ya hau masa sannu da
dawowa, Khalil ya amsa yana dariya, da shike gidan ba baƙonsa bane, nan ya shige kansa tsaye yana
146
HAUSACINEMA.COM
buga sallama, Aziza ce kawai ta farka a lokacin ta gana mopping kenan, ta ga mutum,tana ganinsa ta
ganesa ta ce
"Lahh Hamma Khalil marabalale" ta fada tana hawa sama da gudu ya yi murmushi ya ce.
"Kanwarmu kenan" ya nemi waje ya zauna, da gudu Aziza ta shiga dakin Sultana ta haye gadon ta
janyeta, Sultana ta bude ido cikin haushi ta ce
"Dan Allah miye haka Aziza!?"
"Kai Anty Sultana kin san da cewa Hamma Khalil zai zo shine kike bacci har yanzu baki masa girki ba, ba
kiyi wanka ba haba dan Allah" ai Sultana tana jin an ambaci sunan Khalil yazo ta miƙe zunbur, ta ce
"Ke Aziza da gaske Khalil yazo?"
"Wlh yazo yana parlourn kasa" da sauri Sultana ta miƙe da kayan bacci ta ɗiro a gadon ta fita ta shiga
dakin Mom ta ce
"Mom wai Khalil yazo"
"E na sani"
"Shine Mom ni ban sani ba, bai fa gaya min zaizo ba, ga shi ban shirya masa komai ba, ban yi wanka ba"
Mom ta dauki mayafinta tana fadin
"Too idan kin gama mitan saiki haɗa masa komai ɗin sannan kiyi wanka" ta fice, fita itama Sultana ta yi,
ta samu Aziza na kwashe kaya a parlourn sama,ta ce
"Aziza yanzu ya zanyi?"
"Karki damu Antyna,yanzu kedai kawai kije ki cakare wanka, zan kula da saura"
"Thats my lil'sis" Sultana ta fada tana shiga daki da sauri, kasa Aziza ta sauko ta shiga kitchen, a cikin
mintuna qalilan ta jera tray ta haɗa abubuwa a kai na burgewa da ban sha'awa tazo ta ajiye a gaban
Khalil wanda yake duƙe a gaban Mom suna magana, sun jima suna magana da Mom kafin Mom ta tashi
ta koma sama, ba jimawa gimbiyar tasa ta sauko, nan aka hau hiran soyayya na yaushe gamo, sannan ta
kara gabatar masa da Aziza.
147
HAUSACINEMA.COM
Kamar yadda Khalil ya fada bayan sati daya da dawowarsa aka zo aka tsaida ranar aurensa da Sultana
wanda za ayi nan da wata daya da sati uku,wanda Nawaz shi da Khalil ɗinne suka yanke wannan
shawara.
Tunda aka saka wannan rana Khalil ya hana Sultana sakat, tayi-tayi ya bari suje kano amma ya ƙi, yace ta
bari ba yanzu ba,ita da basu shiri da yan kano din ma, bayan sunyi haka da shi ta gayawa Aziza, Aziza ke
tambayarta meyasa bata son kano, Sultana ta ce
"Ni da Hanan yadda kika san kamar wuta da auduga, sannan rashin kirki da mugunta irin na Maman
Hanan da Maman Beenah abun ba a magana karki so ki yadda suke yiwa Yaya Almazeen, kuma shine mai
kudin fa, gwara ma dai Beenah muna ɗan shiri amma banda Hanan, bana son halinsu ne sabida
muzgunawa Yaya Al'mazeen da sukeyi"
"Mutane kam ai sai addua, Allah ya kyauta kawai" Sultana ta amsa da amin.
Hadiza! Hadiza! Hadiza!.
Da gudu Hadiza ta fito ta zube a gaban Hajiya Lawiza Maman Hanan kenan, cikin yauki ta kalli Hadiza ta
ce
"Hadiza, maza ki kirawo Azima ki haura da ita can sama part din Al'mazeen ta fara gani da tattare ƙura,
suna nan dawowa nan da sati biyu"
148
HAUSACINEMA.COM
Damm! Gaban Azima ya buga tayi saurin ware blue eye dinta,ta maimaita
"Azizaa! Aziza dai!?" Maman Beenah ne ta kallesa ta ce
"Al'mazeen kasanta ne dama? Sannan sunanta ba Aziza bane, wannan sunanta Azima ne" girgiza kai
Al'mazeen ya hau yi yana ƙarewa Azima kallo,yatsar hannunta ya kalla yaga irin zoben da ya gani a
hannun Aziza dazu, sannan ace kuma ba Aziza bane? Ko dai ya yi gamo ne? da sauri ya haura sama, yana
shiga part dinsa ya ga sai kyalli yakeyi an gyara sosai bai tsaya karewa ɗakin kallo ba, wayarsa ya ɗaga zai
kira Nawaz sai kuma ya fasa ya kira layin mom,ringing uku mom ta daga suka gaisa yace mata ya isa
lafiya,mom tayi hamdala ta masa sannu da hanya ta kara da cewa
"Ya ka samu mutanen gidan,su Hajiya Lawiza da Hajiya Luba?da kuma yaran?"
"Lafiyar su lau"
"Ya naji muryarka haka Al'mazeen? Kamar kana cikin tashin hankali ko damuwa, ba dai daga dawowarka
suka fara cusa maka baƙin ciki ba?"
"A'a mom basu bane, amm nace ba mom? Aziza fa? Ya jikin nata?"
"Alhamdulillah da sauki, ko ba sauki musulmi ai ba zai ce babu ba sai dai yace alhamdulillah, Sultana tana
tare da ita dik da naji tace tana da paper 12 zataje skull ga abokin naka ma shima baida lafiya, bayan
tafiyarka da ya shigo idonsa a kumbure wai kansa ke ciwo"
"Subhanallahi! Allah ya basu lafiya, dama tunda na ga yanayinsa na san bai da lafiya dan ina kyautata
zaton jiya bai yi bacci ba dan a parlor na samesa zaune da asuba, amma da na tambayesa yace min ba
komai,zuwa 12 in sha Allah zan kirasa naji ya jikin nasa maybe yanzu yana bacci, bari na kira sultana naji
ya na Aziza yake" nan ya yiwa Mom sallama yana katse wayar, sultana ya kira a lokacin tana magana da
wata classmate ɗinta a waya,tana gaya mata ba zata samu zuwa skull ba, Brothern'ta da sistern'ta basu
da lafiya, suna cikin magana ta ga wayar Al'mazeen ya shigo dan haka sukayi sallama da kawarta ta daga
naAl'mazeen, sai da ta masa an isa lafiya kafin yace mata
"Ya jikin Aziza?" kuka ta sa tana kara masa wayar a saitin fuskar Aziza dake fidda huci tana gurnanin
zazzabi,bayan ta kara masa wayaryaji kafin ta maida wayar kunnenta tana ci gaba da kuka tana fadin
149
HAUSACINEMA.COM
"Bro ka ji ta ko? Yadda ka barta haka take sai ma abunda ya ƙaru"
"Subhanallahi! Allah ya bata lafiya kin bata wa innan maganin kuwa?"
"E bai jima ba da na bata,amma kamar bai yi aiki ba"
"Karki damu kinji zai mata a hankali kiyi ta yi mata addua, Allah ya bata lafiya!"daga haka ya katse
wayar,ya hau jeka ka dawo a daki yana saƙa da warware, "AZIMAA!?" ya faɗa yana rike kai
"To ko dai yar uwar Aziza ce? Tunda sunansu mai haɗi iri ɗaya ne? Amma kuma Nawaz yace an kashewa
Aziza kowa bata da kowa! To ba mamaki kamanni ne" daga haka ya miƙe ya shige toilet abunsa ya
watsar da tunanin jin yana shirin saka masa ciwon kai.
A kasa kuwa ba ƙaramin daru aka sha da Azima ba a kan abincin da za a kai wa Al'mazeen, ta dage ta
kafe tace wlh ba zai ci wannan abincin ba, Maman Hanan ta ce
"E lallai kam Azima, wato kin samu waje kinyi freesh shiyasa zaki fara murza iskanci son ranki ko! To wlh
ki bi a hankali" ba tare da Azima tayi magana ba ta karbi abinci a hannunsu Hadiza tayi wajan kitchen da
shi ta ajiye ta hau yiwa Al'mazeen sabo, girki takeyi duk da ba wai ta wani iya sosai bane, amma da taji
ance Al'mazeen zai dawo yasa kullum tana kitchen dasu Hadiza tana ganin yadda ake girkin barin ma
wanda aka ce mata Al'mazeen ɗin ya fi so.
Tana girki tana tunanin sunan da Al'mazeen ya kirata da shi,hakika hankalinta ya ɗan tashi
"Aziza! Aziza! Ina Al'mazeen ya san Aziza? Shi da baya ma kasar, to ba mamaki wajan kiran sunanta aka
samu kuskure zai ce Azima yace Aziza" share zancan tayi ta ci gaba da aikinta dan ta san wan can
sakaryan tana can jeji, sai bayan da ta kammala ta jera a tray ta dauka ta haura sama.
A hankali ta tura kofar ba tare da tayi sallama ba, Al'mazeen na zaune a parlour da system a gabansa da
alama aiki yake yi, yaji mutum ya shigo ba sallama, haɗe rai ya yi, ita kuwa Azima sallama baya daya
150
HAUSACINEMA.COM
daga cikin dabiunta, abunda Al'mazeen ya tsana kenan, dan shi mutum ne mai girmama addininsa fiye
da komai a rayuwarsa, Al'mazeen da na riƙo da addini fiye da tunanin mai tunani, murya can kasa yace
"Fita ki min sallama, karki sake ki min magana ba tare da kin min sallama ba" juyawan kuwa tayi ta fita ta
sake shigowa tare da fadin
"Salamu alaikum" tana tura bakin, bakintan kawai yake iya hangowa yadda take tura shi tana murguɗa
shi tunda fuskarta a rufe yake, abun dariya ya ba sa dan haka ya ɗan murmusa ba tare da ta gani ba,
abincin ta ajiye tare da fadin
"Kayi hakuri" bata ma san sadda tace masa ya yi hakurin ba, jinjina kai Al'mazeen ya yi,ya ce
"Kece Azima?" ta gya ɗa kai,
"Daga ina kike?" damm! gabanta ya buga, amma da shike zuciyarta a tsaye yake ƙyam tace
"Daga can cikin kauyen kano a wata rugar fulani"
Al'mazeen a ransa ya ce
"E tabbas to basu da alaƙa da Aziza"
"Ina abincin da aka dafa min?" murguɗa baki Azima tayi tace
"Na ajiye musu a bayan kitchen idan sun ga dama su dauka su ci ko su san yadda zasuyi da shi" tana
gama fadi ta mike fuuuu ta fice, girgiza kai Al'mazeen ya yi ya ci gaba da aikinsa, sai wajan sha daya da
rabi ya ja tray din da ta ajiye masa ya buɗe yana kan buɗewa sai ga ta ta shigo ta duƙa tunowa da dazu
ya koreta akan bata yi sallama ba sai ta kara ficewa da sauri ta shigo tana fadin
"Salamu alaikum! ai saika kirani nazo na zuba maka"
"Kina da waya ne?" girgiza kai Azima ta yi ta ce
"A'a bani da shi,amma idan kace AZIIIMAAAA!! Ai zanji na taho da sauri!" girgiza kai Al'mazeen ya yi
ya tashi zai shiga daki, da sauri ta ce
" HAMMA MAZEEN abincin fa?"
Cak Al'mazeen ya tsaya yana nanata sunan "Hamma Mazeen!" kirjinsa ne ke bugawa da sauri-sauri,
"Ina zuwa ki zuba kawai ki tafi" ya faɗa yana shigewa bedroom, Azima haushin kanta ne ya kamata, wai
meyasa take masa abu kamar wanda ake sakata ko ana bata umarni ne? Meyasa take jin faduwar gaba a
151
HAUSACINEMA.COM
kansa, meyasa take jin makarin gubarta yana tattare da shi? Amma kuma tana ji kamar ita da shi an jona
musu kuran karfe, saurin tashi tayi ta fice.
Sai 1 Nawaz ya farka ya ɗan ji kan nasa da sauki amma kan ya yi masa nauyi, wanka ya yi a nan daki ya yi
sallah, sannan ya lallaba a hankali ya shiga cikin gida, ba kowa a parlor dan haka ya fara haurawa sama,
sai kuma ya juyo yana kallon kofar dakin Aziza, saukowa ya yi ya nufi dakinta, a hankali ya tura da
sallama, mom da sultana ma ashe suna dakin, Aziza na jingine tana sallah a zaune a kan gado, saurin
karasowa kusa da mom ya yi ya ce
"Mom jikin nata ya yi tsanani ne haka shine baku tasheni munje asibiti ba?"
"Humm! Nawaz kai ma fa ba lafiyar gareka ba, ka ganta nan jiya bata rintsa ba"
"Bari ta idar da sallar sai a kaita asibiti"
"A'a Nawaz ba sai anje asibiti ba, babu amfani, zaku ƙara huda mata jiki ne kawai, yanzu sai kuce zaku
sossoka mata allura a ɗaura mata ruwa aja jini, wanda hakan kuma...!" sai Mom tayi shuru, a lokacin
Aziza ta sallame sallarta, Nawaz ya miƙe yana fadin
"Mom dan ta gaya miki bata son allura sai a biye mata dan lafiyar wa akeyi? Ina dan lafiyarta ne!" ya
faɗa cikin haɗa fuska, ya nufeta yana faɗi wa Sultana ta tashi taje ta cewa driver ya juya mota.
Aziza kuwa ganin ya nufota yasa ta kwalalo ido waje, dan kuwa jikinta yana fidda farin sab'ar maciji idan
ya gani fa? Saurin girgiza masa kai ta hau yi muryarta a shaƙe da baya fitowa sosai ta hau fadin ya
kyaleta kar yazo inda take, ko kaɗan bai tsaya ya saurareta ba yasa hannu ya yaye bargon jikinta ya kamo
hannunta,ji yayi kamar wani fata ya maqale masa a hannunsa, sake hannun nata ya yi yana kallon tafin
hannunsa, wani zare ido Nawaz ya yi sai kace idon zasu faɗo ƙasa,ganin sab'ar fatar maciji fari sol a
hannunsa, Aziza kuwa banda kakkarwa babu abinda jikinta ke yi,tana sake boye hannunta a cikin hijabin
dake jikinta tana jan bargo tana son rufe kafafunta, saurin fizgar bargon Nawaz yayi jikinsa na kyarma,
yasa hannu ya figi hijabinta ganin haka yasa mom cewa da sauri
152
HAUSACINEMA.COM
"Nawaz ka haukace ne!? baka da hankali ne!? mai kake shirin yi!?" ba tare da ya saurari mom ba ya ɗago
Aziza tsaye wacce jiri ke kwasarta, hannunta ya riko ya ware nan kuwa ya ga jikinta duk b'awu, a lokacin
kuma Aziza ta suma, dagota ya yi yana jijjigata cikin tashin hankali yana tambayarta wacece ita.
Cikin kuka Sultana tasa hannu ta kwace Aziza daga hannun Yayanta ta rungumeta ta ce
"Yaya ta suma fa? Dan Allah Mom kiyi wani abu a kai"
Nawaz yasa hannu zai kara jan Aziza daga jikin sultana, sultana tayi saurin juyawa da ita ta kwantar da
ita tana murza tafin hannunta tana kuka
"Zan fa karyaki Sultana ina wasa dake ne!!?"
"Wlh Yaya ko kasheni zakayi ba zan bari ka kasheta ba, dan Allah mom kiyi magana ki gaya masa
gaskiya,babu amfanin wannan boye-boyen"
"Nawaz ya isa haka! Aziza Macijiya ce!" Mom ta faɗa a tsawace,
Nawaz ne ya yi baya-baya yayi zaman yan bori sharab, mom ta karaso ta kama hannunsa.
kenan mafarkinsa akan yarinyar macijiya ce gaskiya ne? Kallon Mom ya yi da jan ido ya ce
"Mom da macijiya muke rayuwa kuma ke ma kin sani? Taya hankali zai dauka ace mutum maciji? Da ace
sultana ce ta faɗa ba abunda zai hanani ban kaita asibiti an duba min kwakwalwarta ba"
Ajiyar zuciya mom tayi tace
"Zaka iya tsayawa ka saurareni uhum? Nawaz magana nake maka" kifa kansa ya yi a kafadar Mom
hawaye suka hau gangaro masa wanda bai san dalili ba.