Showing 30001 words to 33000 words out of 94205 words
zaman lafiya da
kwanciyar hankali ya kare mana, ba mu sake yin kasa a guiwa ba muka sake zuwa wajan Banju basa
hakuri amma kamar mun sake zugasa ne muna tunzura shi, ba zan iya ƙayyace miki mutanen da Banju ya
66
HAUSACINEMA.COM
kashe ba Aziza, haka ya bi dangin Jumala mahaifiyarku ya kashesu ita daya kawai ta tsira, a lokacin Arɗo
ya dauketa ya kaita gidansa sannan ya daura mana aure da ita, a lokacin Baffa Mandi shi ne sarkin
fulanin kwana, haka shima iyayensa matansa yaransa da duk wani danginsa sai da Banju ya kashesu! a
lokacin ko yaro aka haifa yau Banju ya samu zai kashe, babu kalar farmakin da Banju bai kawo min, akwai
sadda yankin kwana ya koma zallar ƙura ne ke tashi tare da jinin mutanen da basuji ba basu gani ba,nan
nayi tattaki naje na samu Banju nace masa daukar Fansansa a kaina ne meyasa yake so ya shafe yankina,
ina nine na masa laifi to ya kasheni ya kyale jama'a amma nan yace min ko da ya kasheni ya min alkawari
babu wanda zai rage a raye a mutanen yankin kwana sai ya kashe kowa! ko da kuwa ɗan da yake ciki ne
sai ya kashesa! a lokacin nayi niyyar na miƙa wuyata ga Banju amma na fahimcesa kamar yadda ya faɗi
ba zai kyale kowa ba, nan jama'ar kwana aka hadu aka yi tattaunawa inda kowa ya kawo shawara a kan
na kashe Banju dan abun nasa yayi yawa,da fari naqi amincewa sai daga baya na amince, a lokacin da
zamu gwabza na fahimci ba zan iya kashe Banju kai tsaye ba,kamar yadda shima ba zai iya kasheni kai
tsaye ba, a lokacin ne na tafi jejin lore aka bani zare mafi hatsarin gaske, wato zaren saƙar dana, a wajan
yanki muka gwabza da Banju gaban dukkanmutanen yankin kwana, kin ga wannan takwabi da shi na
kashe Banju bayan na saƙa zaren saƙar dana na naɗe a jiki na sokesa da takwabin a ciki, nan ya fadi yana
aman jini amma jinin ba ja bane kore ne, kafin ya fadi kasa shine ya mana alkawarin cewa zai dawo
daukar fansa a kaina ta ko wace hanya dani da mutanen yankin nan, to kinji abunda ya shiga tsakanina
da Banju!"
Baffa na gama ba wa Aziza labari tasa kuka tana fadin
"Kenan yanzu Baffa Fansar da Banju yake dauka a kanmu ne? Innalillahi wa inna ilahirrajiun! Yanzu Baffa
kashemu zaka yi?" Baffa ya girgiza kai yana fadin
"A'a Aziza! Kin taba ganin Uban da ya kashe yaransa ne? Amma idan ta kama zan iya Kashe Azima dan
tsaida wannan bala'in,idan ba haka ba tabbas ba a fara mutuwa ba, ke rabaki da Bahula ba zai yi wuya
ba, amma ko da an rabaki da ita ke Banju ya maidaki Macijiya sabida bai samu yadda yake so a jikinki ba
sai ta jikin Azima, kuma ni bana da masaniyar makarin abunda Banju ya miki, amma akwai wani Babban
Malami mai suna Malam Shadi a can yankin ja'o zamu je wajansa dan ya mana bayani,ki kwantar da
hankalinki, amma kafin nan muna da bukatar tsaida Azima mu ɗaureta, ki daina kuka kinji? Tashi mu tafi
gida" Aziza ta miƙe tana share hawayenta suka nufi gida, a hanya kafin su karasa Baffa ya haɗu da Salti
ɗan gidan Jauro mai maganin kwana aljanu sun bugesa, da sauri Baffa ya yi kansa yana dubasa,girgiza kai
ya yi yana fadin
"Sai da nace kar wanda ya fito ai ga irinta nan, taurin kan Salti iri daya ne da na Ubansa Jauro" Baffa ya
faɗa yana daukar Salti, gida suka nufa suna isa Baffa bai yi nauyin baki ba ya gaya musu ai Banju ne a
jikin Azima, Bahula kuma tana jikin Aziza, sannan ko an raba Aziza da Bahula Banju ya maidata Macijiya,
wani kuka mai rikita zuciya Hajja ta kuma sakawa, yayinda Aziza ta faɗa jikinta suka hau yi tare, Baffa
Mandi ya ce
"Abun da za ayi yanzu shine, ya kamata muje wajan wannan Malamin wato Malam Shadi na can yankin
Ja'o mu je zuwa gobe kawai dan bamu ga ta zama ba, amma kafin nan dan Allah kar a fadawa jama'ar
67
HAUSACINEMA.COM
gari dan ba a san me hakan zai haifar ba har sai munje an dawo, mu da muka sani ya tsaya a iya mu
kawai" aka amsa da hakane, nan Arɗo ya ce
"Magaji? Ana ta wannan maganar ina Azima?"
"Azima?" Baffa ya nanata sannan ya kuma cewa
"Tun sadda ta b'ace ban ganta ba" Aziza dake kuka a jikin Hajja ta miƙe tana goge hawaye ta ce
"Baffa bari na dubota na gani tana ina" Baffa ya ce
"To dubota Aziza" rufe ido Aziza ta yi ta shafa hannun damanta da hannun hagunta,amma abun mamaki
bata ga Azima ba, saurin bude ido tayi tana fadin "taya hakan zai faru?"
"Menene Aziza?" Arɗo ya tambayeta
"Arɗo bana ganin komai,bana iya ganin Azima amma taya hakan zai kasance?"
"Ki sake dubawa Aziza" Baffa ya faɗa Aziza ta gya ɗa kai tana fadin to Baffa, ta sake rintae ido amma
wayam, sake buɗe ido ta yi ta ce
"Wlh bana ganinta, Baffa ya ce zan duba da kaina amma sai bayan munyi sallar magriba fatana dai daya
kar ace Azima taje ta yi wani ɗanyen aiki"
"In sha Allahu ma ba zata yi ba" cewar Baffa Mandi,kamar yadda Baffa ya faɗa bayan sallar magriba ya
hau duba inda Azima take amma abunda bincikensa ya nuna masa shine kwata-kwata Azima bata yankin
kwana ta fice gabadaya daga wannan sassanin, a firgice Baffa ke furta kalman "INNALILLAHI WA INNA
ILAIHIRRAJIUN! ALLAHUMMA AJIRNI FI MUSIBATIHI WA AKHLIFNI KAIRAN MINHA!" da gudu Hajja da
Aziza suka shigo suna tambayar Baffa menene? "Azima bata yankin nan kwata-kwata,bata wannan
al'ƙaryan! ta bar wannan sassanin, Banju ya ja min 'ya sun bar wannan yankin!" cewar Baffa hankalinsa a
matuƙar tashe, Aziza ta ɗora hannu a kai tana fadin
"Wlh Baffa ta sha fadin tana son shiga cikin inda yake da mutane da yawa ta tarwatsasu,kenan ina Azima
ta nufa!? Duk inda zata je dai ba alkhairi zata shuka ba,dan nasha gaya mata shiganta mutane ba alkairi
bane, yanzu miye abun yi Baffa?" girgiza kai Baffa ya yi ya ce
"Ban sani ba Aziza! Allah ya kaimu gobe asubanci zamuyi mu tafi yankin ja'o dan zuwa wajan Malam
Shadi" Aziza ta juya tana kallon Hajja wacce ta kasa tsayar da hawayen da ke zuba a idonta, a hankali
Aziza ta fice a bukkar tana sharan hawayen tausayin iyayenta, Aziza na fita Baffa ya matso kusa da Hajja
68
HAUSACINEMA.COM
dake hawaye tun tana kuka mai sauti har ta koma kukan baya fita sai ambaliyar hawaye, cikin sigar
rarrashi Baffa ya ce
"Jumala kiyi hakuri! Ki dage da addua muna kai wa Allah kukanmu! Dan Allah ki daina wannan kukan kar
ya jawo miki ciwo, kinji!?" dago jajayen idonta Hajja ta yi ta watsasu a cikin na Baffa wanda tun tahirin
aurensu bata taba kallon tsakiyar idonsa ba sai yau, muryarta a dashe ta ce
"Ciwo? Ciwo fa ka ce Baffan yan biyu? Wani irin ciwo ne ya fi na zuciya? Shin kasan ya nake ji a raina?"
"Ko ma ya kike ji ki yawaita nanata kalman Innalillahi wa inna ilahirrjiun! ya zaki dinga jin sassauci a
ranki, sannan....."
"Don Allah Baffan 'yan biyu!" Hajja ta kasa Baffa ba tare da ya idasa maganarsa ba, cikin zafafan hawaye
ta dago ta ce
"Ni dai kawai abunda nake bukata a wajanka shine ka dawo min da yarana! Ka dawomini da Azima da
Azizana, ni dai ban haifi macizai ba! mutane na haifa,idan wani abu ya samu Azima da Aziza hakika zan
iya mutuwa kawai ka dawo min da yarana!" ta tashi ta fice da gudu a bukkan, Aziza dake maqale a jikin
bukkan tana sauraronsu ta riƙe bakinta gam tana kuka itama da gudu ta fice a gida ta yi rafin jimulo, taje
ta ci kukanta har ta godewa Allah kafin ta dawo gida, bukkar Hajja ta shige ta sameta zaune ta zauna
kusa da ita ta ɗora kanta a kan cinyar Hajja ta ce
"Hajjana! Inaji a jikina kamar na kusan barinki! Ba wai ina gaya miki dan na tashi hankalinki bane, duk
duniya babu abunda na tsana kamar na ganki ke da Baffa cikin tashin hankali,abunda yasa nake gaya
miki Hajja dan na nemi yafiyarki ne! Hajja ki yafe min idan har nayi miki wani abu a zaman da muka yi
dake! Kowa da kalar kaddararsa amma mu wannan shi ne namu kaddara! Ba mu kasance cikin mutane
da zamu yi rayuwa dake ba Hajja,dan Allah ki yafeni! Ki yafemini!!" Aziza ta karasa da sakin kuka mai ban
tausayi da karya zuciya,tana sa kukan Hajja ta rungumeta tana bubbuga bayanta dan tama kasa magana
ko tace zatayi maganar ma muryarta ba zai fito ba dan ya dashe!" su na nan suna kuka har dare ya tsaga
kafin Baffa ya shigo ya musu umarni da suyi alwala suyi sallah, hakan kuwa ta kasance, Baffa ne yaja su
sallah suna gayawa Ubangiji, da haka har asuba ta yi basu rintsa ba.
Bayan Baffa ya dawo daga masallaci tare suka shigo da Ardo da Baffa Mandi, a lokacin Aziza da hajja
suna zaune sunyi jingum-jingum, Baffa ya ce
"Aziza ta shi mu tafi, Jumala ke kuma ki tafi gidan Arɗo" ko uhum Hajja bata ce ba tana riƙe da hannun
Aziza,fuskokinsu a kumbure,shima Baffa ɗaurewa kawai yake yi baya so ya kara karya musu guiwa amma
da zai samu dama da shima ya sha kukan nan ko zai samu mai rarrashinsa, da kyar Aziza ta zare
hannunta daga na Hajja ta fice da sauri jin wani kukan na shirin cewa a ba shi hanya, Hajja kuwa tuni ta
sake saka wani kuka tasa hannuwanta a fuska, saurin ficewa Baffa ya yi jin hawaye ya fara bin fuskarsa,
yana fita babu b'ata lokaci suka hau doki, da Baffa da Baffa Mandi da Arɗo sai Aziza, suna hawa doki
suka dauki hanyar yankin ja'o ba tare da bata lokaci ba.
69
HAUSACINEMA.COM
Tun bayan da Azima ta bar yankin kwana take aikin tafiya ba tare da ta gaji ba dan bata jin gajiya a
tattare da ita, hakika tana shan tafiya, dan kuwa ace mutum wanda yake ba aljani ba idan zai fita daga
yankin kwana zuwa cikin garin kafin ya iske titi a kan doki sai ya shafe sati biyu, shiyasa su haka suke ba a
shigo musu su ma kuma basu shiga gari dan nan ne rayuwarsu a kauyensu mai cike da abun burgewa da
albarkatun korayen shuke-shuke, a kwana daya Azima ta yi rabin tafiya abunka da ba tafiyar mutane ba.
Sai kusan gaff azahar su Baffa suka isa yankin ja'o ba tare da bata lokaci ba aka musu iso izuwa ganawa
da Malam Shadi, suna shiga bukkarsa Malam Shadi na haɗa ido da Aziza ya hau salati yana sanar da
Ubangiji nan gaban Baffa ya bada dammm! amma ya daure suka zauna ana gaisawa cikin mutunci da
mutuntawa, Malam Shadi ya kalli Baffa ya ce
"Ohh Allah Magaji Mazan fama kana raye? Yaushe rabonka da yankin nan? Inaji fa tun sadda wan can
muguwar mayyar ta sakamu a gaba kazo ka rabamu da ita ban sake ganinka ba sai dai kayi aike" Baffa ya
yi murmushin boye damuwa ya ce
"Wlhkuwa Malam Shadi,tun sadda na daina shige-shige naji komai ya fita a raina"
"Allahu Akbar" cewar Malam Shadi yana kallon Aziza da ta dukar da kai gabanta na faduwa, ya kalli Baffa
cike da al'ajabi ya ce
"Magaji Bawa ina ka samo MACIJIYA!?" juyawa Baffa ya yi ya kalli Aziza da ta rakube ta dukar da kai kasa
kamar ma kuka take yi,sannan ya maida kallonsa ga Malam ya ce
" 'yata ce Malam, na kawota ne wajanka dan ka duba min ita, Banju da na kashe yace zai dawo shine ya
dawo daukar Fansa a kan yarana, yanzu haka dayar ta bar yankin kwana kwata-kwata, ita kuma wannan
ka ganta nan, shine nace bari na kawosu wajanka dan a san ta yadda za a rabasu da su,bana so
gwagwarmayan da nayi ya shafe yarana"
"Shafa kuma ta nawa magaji? Ai shafa kam an gama shafansu tunda gasu nan a macizai" cewar Arɗo,
Malam Shadi ya gya ɗa kai yana fadin
"Ya Hayyu Ya Qayyum Ya Zuljalalu wal'ikram, hakika Banju mugun aljani ne, Banju mugu ne fiye da
tunanin me tunani, amma Magaji kai ma zaka iya yiwa yaranka magani ai"
Girgiza kai Baffa ya yi ya ce
"Zan iya sake kashe Banju, amma abunda nake tsoro shine Banju na rayuwa ne a cikin Azima yana tafiya
ne da kafafunta, yana aiki ne da hannuwanta,yana gani ne da idanunta,yana motsi ne da motsinta,
sannan a binciken da nayi Azima a sume take a jikin Banju, idan har na kashe Banju to tabbas Azima ma
ta tafi, na duba na ga ita Aziza rabata da Bahula ba wata damuwa ba ce, amma kuma tashin hankalin a
nan shine,ko Bahula ta bar jikin Aziza, Aziza ba zata samu lafiya ba dan Banju ya maidata Macijiya sabida
70
HAUSACINEMA.COM
bai samu yadda yake so a jikinta ba" jinjina kai Malam Shadi yayi bayan Baffa ya gama yi masa bayani,
Baffa ya kuma cewa
"Ina da bukatar taimako dan bana so na salwantar da rayuwar yarana! Jumala ba zata yafemini
ba,sannan nima bazan yafewa kaina ba Malam Shadi"
"Matso nan kusa dani Aziza karki ji tsoro" Malam Shadi ya fada yana kallon Aziza, a hankali ta taso ta
matso kusa da shi ta duka, wani magani ya ɗiba a kasko ya watsa mata a fuska,ihu Aziza ta saka tana
furta "Ya Allah! Ya Allah! Ya Allah! Baffana zafii!!" abun tausayi, hawaye ne ya cika a idon Baffa yana ji
kamar ya tashi ya fita amma ina ba hali, Malam Shadi yasa hannu ya damƙi goshin Aziza da karfi,
murkususu ta hauyi tana son kwacewa amma ta kasa,rintse idonsa ya yi yana gane-gane da hange-
hange, ya dau lokaci yana riƙe da goshin Aziza wacce ke murkususun azaba har sai da ta suma kafin
Malam Shadi ya saketa, Baffa ya yi saurin taro 'yarsa ta fada jikinsa,jikinsa na rawa hawaye na zuba a
idonsa ya d'ago ya kalli Malam Shadi yana fadin
"Malam me ya sameta?"
"Haba Magaji! Sai kace baka san yanayin aiki ba,ka kwantar da hankalinka zata farfado, amma gaskiya
akwai babbar matsala wanda ba zan iya ce muku komai a kai ba, akwai aikin da nake so nayi cikin dare
ina so na bincika na ga taya za a rabasu da mugun nan Banju, sannan Babban tashin hankalin shine 'yar
uwarta Banju ya jata sun bar al'ƙaryan nan,ina take? Ina za a ganta? Duk babu wanda ya sani" Arɗo da
Baffa Mandi suka sharo zufar tashin hankali, Malam Shadi ya ɗora da cewa
"Babban damuwar shine abunda Banju zai ja Azima ta aikata,amma zanyi bincike a kai yau In sha
Allah,ina dai a nan zaku kwana?" Baffa suka amsa da eh, sannan Malam Shadi ya kira wani almajirinsa
yace ya kawo masa tarbama wanda yake na kara ne, bayan an kawo ya ce a shinfiɗe Aziza a kai, bayan
Baffa ya kwantar da Aziza Malam Shadi ya kunna mata hayaki, sannan suka fita waje suka zauna suna
tattauna yadda zasu yi a kan lamarin.
Sarki Chubado ne da mai unguwan kwana ori suke tattaunawa a kan batun Azima da Aziza Macizai
ne,suna ta alhinin lamarin, su biyu suke magana a kan cewa suna tausayawa Baffa, a garin yaya sai ga
Salti ɗan gidan Jauro mai maganin yankin kwana yazo wucewa caraf a kunnensa, dan Salti ba dai gulma
ba,nan yaji duk wani tattaunawa da Sarki Chubado da Ori ke yi a kan lamarin har da tafiyar da su Baffa
suka yi yankin ja'o, da gudu Salti ya kwasa yana fadin zai je ya gayawa Baffansa dan yasan zai yi farin ciki
da wannan labarin da zai kai ma sa.
Sarki Chubaɗo cikin fushi ya kalli mutanen da suke wajan ya ce.
"Amma wallahi kun bani mamaki! Kuma kunji kunya! Yanzu akwai masifar da zata samu Magaji wanda
har zai sa ku juya masa baya? Idan har ku wa inda ku ka zo bayan shekara ashirin baku san
71
HAUSACINEMA.COM
gwagwarmayen da Magaji ya yi ba, to ku wa inda ku ka zo kafin bayan shekara ashirin zaku ce kun manta
da wannan halaccin ne? Dayawanku a nan wasunku basu da dangi kaff Banju ya kashesu! dabadin
Magaji ba babu ko da ƙwaro da zai rage a wannan yankin!!" Sarki Chubado ya karasa da tsawa idonsa
jajur dan ransa ya b'aci matuka
"A ce ina sarkin fulanin yankin kwana amma Jauro ya ja ku ba tare da sanina ba ku zo yiwa Magaji rashin
mutunci da dibar albarka! Jauro ne sarkinku!! Na ce Jauroo neee sarkinkuuu!!!?" shuru jama'a suka yi
masu zare ido da masu tsilli-tsilli da ido suna yi, Mai Unguwar yankin kwana bayan Sarkin fulanin kwana
Chubaɗo ya dasa ayar tasa shima ya karbe da cewa
"Jauro dai mai maganin yankin kwana ne kamar yadda ku ka sani, amma a da kun san waye GARKUWAN
YANKIN KWANA KAFIN A ƊORA GARKUWA NA YANZU!! TO GA SHI NAN SHINE DAI! MAGAJI BAWA!!
kafin