Showing 51001 words to 54000 words out of 94205 words
da tafiyar Nawaz abubuwa da yawa sun faru daga ciki kuwa harda fara azumi da aka yi,
sosai a wannan wata ta ramadan Aziza ta dage da addua Allah ya takaita mata wahalar neman yar
uwarta su samu su koma gida, dan ta ƙosa ta koma ta ga iyayenta,kullum da Hajja take kwana take tashi
a ranta har ma da Baffanta, ta maida lamuranta ga Allah.
Ta bangaren Azima kuwa ta kasa gane meke mata dadi, dama duk azumin duniya ita kam ba yinsa take yi
ba, to wannan din ma haka ta kasance dan ko daya bata yi ba, sosai kuma take sakawa su Hajjaju ido,
duk wani ƙullin da suke yiwa AL'MAZEEN.
Ana azumi lafiya da yardan Allah, tunda Nawaz ya bar nigeria ya kasa samun natsuwa, ga mafarkin Aziza
da ya gallazawa rayuwarsa wanda ya rasa ya zaiyi da wannan mafarki, ga shi ya kasa gayawa kowa,
wanda hakan har rama ya fara saka shi, wanda da an tambayesa zai ce azumi ne kuma ya haɗa masa da
ba a gida yake yi ba shiyasa.
Ana saura kwana uku sallah Sultana ta kai musu dinki wajan telarta inda ya cire musu zuƙa-zuƙan
dinkuna na gani na fada, laces kala biyu, atampa kala uku, sai shadda da material kala ɗaɗɗaya, da
gyalensu da takalminsu dasu sarƙa da ɗankunne, da komai da komai, hakika Mom ta yi kokari,Sultana
114
HAUSACINEMA.COM
kuwa ta yi bajinta wajan zabo musu kaya masu kyau, ita ma Azima anyi mata, amma sam basu gabanta
dan bata saka a ranta zata yi wani kwalliyar abu sallah ba.
Ana gobe sallah sai aikin suke yi dukkansu a kitchen har da Mom, Sultana ta ce
"Mom wlh zan yiwa Walid ba dadi, kinga yadda ya takura min wai yana son Aziza?" Mom ta yi murmushi
ta ce
"Kai yarinta, duka-duka nawa kike bare kuma Walid? to kuma aje ga maganar Aziza wacce take da 15,
Aziza ki maida hankalinki a kan karatunki kinji ko? In sha Allah bayan sallan nan zaki fara zuwa university
dinsu Sultana tunda Allah ya baki kwakwalwa karki biyewa shirmen Walid kar ma ki fara kulasa, idan
Khalil yaji ma ransa ne zai b'aci" Aziza a ranta ta ce
"Ina kuwa nake da lokacinsa,da yasan wacece ni ba zai so kara yin magana da mai irin sunana ba ma" a
fili kuma ta ce
"Ni Mom ina da burika da yawa bana da lokacin kulasa"
"Yawwa Azizata" cewar Mom suka ci gaba da aiki har karfe sha biyun dare kafin suka tattara suka
kwanta, da washe gari tunda sukayi sallar asuba basu koma bacci ba, abinci sukayi dukkansu har da
Mom, karfe takwas da rabi suka gama, Sultana ta ce
"Aziza kiyi wanka da sauri ki zo muje masallaci" Aziza ta amsa da to.
Wanka sukayi suka saka shaddarsu, sannan suka saka hijabansu mai alkebba da takalmansu, suka fito
har da Mom itama da ta dake cikin lace dinta,gabadayansu zasuje masallaci dan Mom tace abu daga
shekara sai shekara nan ma sai mai tsawon rai wanda Allah ya nufesa da gani.
Haka akayi idi lafiya, sai fatan Allah ya amshi ibadunmu na alkhairi ya yafe mana kurakurenmu amin.
115
HAUSACINEMA.COM
Bayan sun dawo gida, nan yan uwa da abokan arziki suka hau zuwa ana yiwa juna barka da sallah, masu
kawo abinci suna kawowa wa inda ake kai musu ana kai musu, Mom tana haɗawa tana bayarwa ana
miƙawa bayin Allah, dasu lemuka da purewater, da kuɗi haka Mom ta dinga rabo, Sultana kuwa tana
cikin yan uwanta ana shan su pics ana gaisawa an dade ba a hadu ba, Mom ce ta shigo babban parlour ta
kira sunan Sultana ta ce
"Sultana ina Aziza ne kam?"
"Wlh Mom tun da muka dawo inaji bayan mun gama hada abincin da za a fita da shi ban ƙara ganinta ba,
dan tun sadda baki suka fara shigowa ban ganta ba" Mom ta ce
"Kin san Aziza bata son mutane kamar ma kunyarsu takeji yanzu haka to ba mamaki tana daki"
"Wlh kam Mom kunyar mutane takeji,ko mu a gida Aziza bata gama sabo damu ba bare kuma yau ta ga
mutane ai ba zata fito ba,amma bari naje na fito da ita dan yau yawon sallah zamu je a ga yan uwa da
abokan arziki" Mom ta ce "dubota to, sai ku shirya ku fita nima zanje gidan Hajiya Hauwa(gidan sirkan
Sultana, Hajiya Hauwa ita ce Mamansu Khalil wanda zai auri Sultana) dan yau muma zamuje ziyara ne"
"To Mom" Sultana ta faɗa tana tashi da sauri ta yi dakin Aziza a lokacin ta gama kukanta tana tunanin
wan can sallar tana gida tare da Hajjanta da Baffanta, Sultana tana shigowa Aziza na fitowa daga toilet ta
wanke fuskarta, Sultana ta ce
"Ohh Allah Aziza, sabida kinji gidan a cike shine kika boya a daki? To maza ki shirya, zamuje yawon
sallah"
"A'a Anty Sultana bana son fita,bazan je ba"
"Wlh sai kinje, Mom ma fita zata yi,yau ranar zumunci ce, yau fa ranar farin ciki ne amma ke na ga kamar
ba baki farin ciki ko mun yi miki wani abu ne?"
Aziza ta girgiza kai,
"To idan har ba mu miki komai ba ki shirya yanzu ki canza kaya ki saka atampa,bari nima naje na canza
kaya" Aziza ta gya ɗa kai, Sultana ta fice.
116
HAUSACINEMA.COM
har Sultana ta shirya ta sha makeup ta kashe ɗauri ta yi pics ta turawa Khalil dinta, sannan ta fito dauke
da handbag dinta ta shiga dakin Aziza ta sameta ta canza kaya amma tana zaune tana riƙe da ɗankwali a
hannunta, Sultana ta ce
"Ba kiyi kwalliya ba?"
"A'a Anty Sultana ba zan yi ba"
"A yau sallan? Wlh baki isa ba" Sultana ta fada tana daukar powder ta hau gogawa Aziza a fuska, sannan
ta shafa mata red lipstick, duk da fuskarta taki bari ya fito sosai amma ta yi kyau, sannan Sultana ta
kashe mata ɗauri, Subhanallahi! Aziza ta yi kyau sosai, nan Sultana ta daukesu hoto, duk da Aziza bata
ɗago fuskarta sosai ba, sannan bata ɗaga idonta ba.
Bayan sun fito parlour suka sake yi da Mom, sannan suka fice a gidan, a mota Sultana ta turawa Nawaz
pics din tare da rubuta masa HAPPY SALLAH BRO NAWAZ.
Ko da Nawaz ya buɗe ya ga hotunan yan uwa da abokan arziki, Allah Sarki gida dadi,ya fada yana
murmushi a ransa, wani hoto ya bude ya ga Mom sai da ya sumbaci hoton, sannan ya sake buɗe wani ya
ga Sultana ta yi kyau sosai ya ce "nice sis" ya sake bude wani ya ga da Mom da Sultana ya yi murmushi
yana faɗin
"My world" wani hoton ya sake buɗewa ya ga Sultana da Aziza amma bai ganeta ba, sai da ya kara buɗe
wani ya ga tana dukar da kai kamar amarya kafin ya ganeta, sun sha lalle kuwa, wani hoton ya sake
buɗewa Aziza na zaune a mota bata ma san sultana ta dauketa ba, lumshe ido Nawaz ya yi yana karanto
adduar masifa dan Aziza ji yake yi ta zamo masa masifa, kansa ne ya hau sara masa sai da ya ɗan ji dai-
dai kafin ya fita dan yaje ya samu amininsa su ɗan fita suma.
117
HAUSACINEMA.COM
Kwana hudu su Sultana suna yawo,kullum kuma idan suka yi wanka sai Sultana ta musu hoto ta turawa
Nawaz, tun yana buɗewa har ya daina buɗewa,dan ganin hoton shike kara masa mafarkai a nasa ganin
kenan.
Ta bangaren Azima ko kaɗan bata yi wankan sallah ba bare shigar sallah, haka ranar sallar ta wuni tana
jin haushin kowa,kiris ya rage abincin sallar ma bata watsa masa dafi ba, dan haka kawai ta ga kowa na
murna da farinciki ita kuma tana ji kamar zuciyarta ya fashe da baƙin ciki da takaici, haka aka gama cin
sallah Azima bata yi shigar sallah ba illa kayan fulaninta da ta dinga yawo da shi har satin sallah.
Bayan komai ya daidaita haka rayuwa ta ci gaba da tafiya, bayan sallah da sati biyu Aziza ta fara zuwa
university din su Sultana, bata shiga hidimar kowa kasancewar tasan ita din ba mutum ba ce,haka zata je
ta dawo,idan kuma Sultana na da paper su kan je tare su dawo tare, tana nan tana tara kuɗinta har ma
da wa inda ta samu da sallah dan tace kwanan nan zata bar gidan.
"Innalillahi wa inna ilayhirrajiun! Dan Allah Jauro ka taimakawa ƴata kar mayyar nan ta kasheta!" ya faɗa
yana mai riƙe kafar Jauro, Jauro ya ce
"Wlh Malam Halliru na kasa yiwa 'yarka magani, wannan mayyar tana da taurin kai" Salti dan gidan Jauro
ya ce
118
HAUSACINEMA.COM
"Wlh Baffana baya da baiwa irinta Baffa Magaji, dama wajan Baffa Magaji kuka je da yanzu ta samu
sauki, amma ku fara zuwa kuyi kamun kafa da Sarki Chubaɗo"
"Wlh zanci ubanka Salti! Zaka fita mini ka bani waje ko sai na bazar da kai da sanda?" Salti ya miƙe yana
kunkuni yana fadin
"To dan na fadi gaskiya kuma Baffa" Salti na fita, Malam Halliru ya ce
"Hakika munyi kuskure, dole wajan Magaji zamu je neman taimako"
Wajan Sarki Chubaɗo Malam Halliru yaje yana kuka yana ba wa Sarki yankin fulanin kwana hakuri a kan
ya taimaka yasa baki ya yiwa Magaji Bawa magana ya taimaka ya duba masa 'yarsa, Sarki Chubaɗo cikin
tunzura ya ce
"Ayhoo!! Ashe ku kuna son yaranku, shi da ku ka kora masa nasa ya yi yaya kenan? har kwanan gobe
Jumala bata magana bata um bata um-um,nan ku ka daure Aziza kuna shirin kasheta! anyi haka ko ba a
yi ba?" cikin kukan nadama Malam Halliru ya ce
"Munyi kuskure ranka ya dade! Amma ba laifinmu bane Jauro ne ya zugamu ya sa mana tsoro da shakku,
dan Allah a taimaka mini" Sarki Chubaɗo ya ce
"Idan Jauro ya ce ku faɗa wuta zaku faɗa ne? idan har Magaji zai taimaka maka a nasa ra'ayin farillahi
hamdu! amma idan ya ƙi wlh daga nan fada babu wanda zai saka baki" Malam Halliru ya amsa da ya
yarda shi dai ayi masa izini yaje gidan Baffa, Sarki Chubado ya daga masa hannu alamun yaje godiya
sosai Malam Halliru ya yi ya tashi da gudu har yana tuntube, bayan Malam Halliru ya tashi Wazirin
kwana ya ce
"Ranka ya dade bana tunanin Magaji zai ƙi taimakawa Malam Halliru" Garkuwan Fulanin kwana ya ce
"Tabbas haka ne maganarka Waziri, Magaji Bawa Allah ya masa kyakkyawar zuciya,yana da tausayi da
hakuri, yanzu haka sai ka ga ya taimaka masa" Sarkin Fadar kwana ya ce
119
HAUSACINEMA.COM
"Ai Halin Magaji Bawa sak wannan Yarinya tasa Aziza, amma ka ga wannan shaiɗaniyar Azima hummm!"
Sarki Chubaɗo ya ce
"Barewa ba zata yi gudu ɗanta ya yi rarrafe ba, itama Azima Banju ke rayuwa a jikinta,ba zamu iya
tantace ya halayyarta yake ba har sai an rabata da Banju wanda yake rayuwa a jikinta,ko kun manta da
komai na jikinta yake rayuwa? Azima fa ba Azima ba ce BANJU ne, amma ni dai nasan Ɗawisu ba zatayi
k'yal-k'yal banza ba" Garkuwa ya ce
"Tabbas hakane, ranka ya dade, an fa ja watanni rabon da su Azima da Aziza a wannan yankin, wlh har
bana son haɗuwa da Magaji sabida tausayin da yake bani, ga shi dole mutum ya dinga tunanin yaran
suna lafiya ko akasin haka! Babban abunji ma ita ce Azima,mu nan da muke yankin jeji ne ya muka iya da
ita,bare kuma aje ga mutanen cikin birni da suke da yawa ɗin nan"
"In Allah ya yarda suna lafiya, Allah kuma shi zai ƙare bayinsa daga sharrin Banju, ina da kyakkyawar zato
wa yarinyar nan Aziza, zasu dawo In sha Allah, sannu-sannu baya hana zuwa sai dai a daɗe ba aje ba, duk
tsawon watanni ko shekaru su Azima da Aziza zasu dawo" cewar Wazirin kwana,Sarki Chubado ya ce
"Haka shima Magajin yake faɗi, zasu dawo In sha Allah,yanaji a jikinsa yaransa suna nan lafiya, kuma
zasu dawo garesa"
"To Allah ya dawo mana dasu lafiya,ni kam ma Azizan nake son haɗawa da ɗan wajena" cewar Garkuwa,
Waziri ya ce
"Kai yanzu Garkuwa a tunaninka ɗanka Garbiyo zai yarda ya auri Aziza ne? Ai kai ɗanka bai yi halinka ba
sam, tsoron bala'i garesa sai kace ba bafulatani ba" Sarki Chubaɗo ya yi dariya ya ce
"Wlh ko cewa akayi Azima da Aziza sun warke bana tunanin Garbiyo zai yarda ya auri Aziza" Garkuwa ya
yi murmushi ya ce
"Garbiyo kam ai sai a hankali amma idan ya samu Aziza rayuwarsa zata yi kyau dan na yaba da halin
yarinyar sosai wlh"
"Hakane kam, yanzu dai adduar shine Allah ya dawo dasu lafiya" aka amsa da amin.
120
HAUSACINEMA.COM
Baffa na zaune a bukka yana lazimi, Hajja kuwa ta samu zaman kofar bukka a kan tabarman kaba,idonta
kamar kullum a bakin kofar gida, sallah ce kawai yake tayar da Hajja sai kuma tsakar dare idan zata shiga
ta kwanta,duk da bacin sai dai sama-sama, ta ajiye idonta a bakin kofa tace ba zata gaji da jiran dawowar
yaranta ba, zasu dawo gareta tanajin hakan a jikinta In sha Allah.
Sallamar Malam Halliru ne ya fargar da Hajja, amma bata amsa ba, sai Baffa da ya fito yana amsawa,
Hajja ta jawo mayafinta tana gyara lullubinta, Baffa ya bada izinin shigowa, Malam Halliru ne da matarsa
da 'yarsa a hannunsa suna kuka, suka zube a gaban Baffa, shuru Baffa ya yi yana kallon Malam Halliru
kafin ya ɗora idonsa a kan 'yar dake hannun Malam Halliru,yana ganinta ya gano matsalar dake
damunta, shuru Baffa ya yi ba tare da ya yi magana ba, Malam Halliru cikin kuka yake fadin
"Dan Allah Magaji ka taimakeni, wlh ita kenan mini yarinyar,na jima kafin na samu haihuwa ga shi Mayya
tana shirin kashe mini ita ka taimakeni Magaji"
Shuru Baffa ya yi na wasu lokuta kafin ya ce
"Nima su kenan gareni, ɗaya ta gudu da kanta daya kuma kun kusa kasheta,inda daga karshe na koreta
da kaina!"
"Hakika munyi kuskure Magaji kayi hakuri" shuru Baffa ya yi bai yi magana ba,ganin haka yasa matar
Halliru zuwa ta kama kafar Hajja tana kuka, kallonta Hajja ta yi cikin sanyin muryarta ta ce
"Na san abunda kike ji a ranki a matsayina ta uwa na fahimci hakan, Baffan Biyu ka dubata dan Allah, su
ci albarkacin macizai" Hajja na gamafaɗi ta miƙe ta shiga bukka, Baffa kuma ya duƙa ya kama goshin
yarinyar ya matse, ya rintse ido, ya gane mayyar dake jikinta, tana ɗaya daga cikin wa inda suka gudu
ranar da ya haƙo kayansa, jin Magaji a kanta yasa ta hau kururuwa,Baffa ya ce
"Ai kin sake kawo kanki" cikin gurnani ta hau bai wa Baffa hakuri, Baffa ya ce
"Tun asalinki dama ke annoba ce, a wan can karan da ban ƙonaki ba dan na rufeki ne,yanzu kuma ƙonaki
zanyi, dan idan na barki ban san wa inda zakiyi kokarin kashewa ba" Baffa na faɗin haka ya rintse ido
tare da ɗora wa yarinyar wani farin dutse a kirji, ta sake ihu mai cike da amo, kafin ta koma tayi shuru
zuwa wani lokaci aka ji ta ɗiff! Malam Halliru ya ce
"Magaji ba dai 'yata ta mutu ba?"
" 'yarka bata mutu ba Malam Halliru amma ta samu lafiya In sha Allahu, ku tafi gida, ga wannan kuma
idan ta farka kuyi mata hayaki da shi" hawaye Malam Halliru ya goge ya ce
121
HAUSACINEMA.COM
"Tabbas mutane irinka basu da yawa a wannan duniyar namu Magaji, dan Allah ka yafe mini, wlh Jauro
ne, kayi hakuri dan Allah, Allah kuma ya dawo da Azima da Aziza lafiya" Baffa ya amsa da amin, Malam
Halliru da matarsa suka fita suna kan yiwa Baffa godiya, Baffa kuma bukkar Hajja ya shige ya sameta
zaune a bakin gadon karanta, ta yi shuru, zama ya yi kusa da ita ya ce
"Jumala?" hannu Hajja ta daga, ta ɗan yi shuru kaɗan kafin ta ce
"Karka damu Baffan Biyu,na rungumi kaddarata,amma ka san ita zuciya bata da ƙashi sai tsoka, duk
yawan watanni ko da an shekara ni kullum abu daya nake gani" tana gama fadi ta tashi ta fice, Baffa ya
ce
"Duk inda kuke Allah ya kareku, hakika idan har na kama Banju kisan da zan masa wannan karon ƙare ba
zai tona ba, dama irin wa innan hatsabiban aljanun basu gane rarrashi , nima zan nuna masa waye ni!"
Bayan wata biyar.
Abubuwa dayawa sun faru a wata biyar din nan, daga ciki kuwa har da 'yar gayu da Aziza ta zama turanci
a bakinta raɗau, ga shi shaƙuwa mai karfi ta shiga tsakaninta da Sultana,haka ma Mom bata nuna mata
bambanci tsakaninta da Sultana, lokuta da yawa Aziza ta sha yunkurin guduwa amma sai ta kasa hakan,
sakamakon yardan dasu