Showing 18001 words to 21000 words out of 94205 words

Chapter 7 - Azima-Da-Aziza-Macizai Ne Complete

20 Jul 2024

37831

ganin yadda wutar ya nufota ta yi tsalle ta haɗa wani farin hayaki ta
maidawa Azima abunta nan ya sameta patttt! A ƙirji! Zubewa ƙasa ta yi tare da komawa mutum, a
hankali Aziza ta zo gabanta ta ɗurkusa tana shirin yi mata magana taji yankan wuƙa a kafadarta ya shige,
kafin ta farga Azima ta yi mata kafa ta nausheta a ciki nan ta faɗi kasa numfashinta nayin sama, Azima
kuma ta miƙe tana dariyar mugunta gami da cewa.




"Gaskiya bana da burin kasheki yar uwata, amma ya zama dole ko dan na kammala aikina a kan lokaci!
dan zaman wannan dajin ya isheni ina da bukatar shiga gari, to amma idan kina raye taya burina zai cika?
Ba ki san ta yadda akai na samu zaren saƙar dana ba taya kuwa zan gaya miki wanda zan kashe da shi!?
To ba zan faɗa ba! Yanzu kuma idan na kasheki bani da wata sauran damuwa a rayuwata ko abunda zai
dinga kawo min cikas da burina!"




Duk maganar da Azima ke yi Aziza na jinta yayinda hannunta daya tana riƙe da kafadarta da yake zubar
da jini dayan kuma yana kan cikinta da Azima ta yi mata naushi da kafarta, tsoronta daya shine Allah
yasa wuƙar da Azima ta yanketa da shi babu zaren saƙar dana a jiki, idan hakane yana nufin Azima zata yi
b'arna? Idan ta kasheta zata kashe sauran mutane sannan ta shiga cikin gari ta tarwatsasu? Inaaa! Hakan
ba zai yu ba, dole na dakatar dake ko ta wace hanya! To amma me zanyi yanzu? Aziza take tambayar
kanta mafita, Azima kuwa na tsaye ta juyawa Aziza baya tana ta zuba kamar indararo, wata zuciyar ta
cewa Aziza

"Kin manta ba zaku iya kashe juna ba? Amma ke zaki iya kashe Azima!Duba Taurarinku dake haɗe ke
kaɗai aka yarjema wa dan ki gani da mai zaki dakatar da Azima" a hankali Aziza ta miƙe ta kama bishiya
ta ɗan jinginu, ta lumshe ido, nan ta hau gane-gane, tabbas ba zasu iya kashe juna ba amma zata iya
karyawa Azima kwarin guiwa, sannan wukar da ta yanketa da shi babu zaren sakar dana a jiki, Aziza na



42
HAUSACINEMA.COM


ganin haka tasa hannu ta shafe inda Azima ta yanketa nan wajan ya koma kamar ba a taba saka ma shi
wuƙa ba, sannan a ranta ta ce

"Inno Fandi! Yau inaso ki bani abunda kika sha miƙa min ina ƙin karba,ko ta wace hanya ce ina so na
dakatar da Azima,ina so na san wa zata kashe da zaren saƙar dana dan na basa kariya,duk da zuciyata
tana zargin Baffa Azima take son kashewa! Amma ita baka iya tunanin abunda zatayi dan komai ma zata
iya yi! Inno Fandi yau ina so ki bani" Aziza a ranta take magana idonta a lumshe, wata farar tsohuwa ce
fara sosai tsohuwa tukuff ta bayyanawa Aziza tana murmushi ta ce

"Wani lokaci domin tsaida zubda jini! Muma sai mun wanke hannayenmu da jini! Magaji Bawa ya ajiye
baiwarsa yayinda ya binnesa, na zabi shiga jikinki dan taimaka miki ke da mahaifinki a lokacin da na
hango bala'in da zai faru a rayiwarku bayan an haifeku, Magaji ya yi tunanin binne baiwarsa zai ce
wannan yanki ta yi sanyi, amma kashe Banju shine babbar bala'i ma wannan al'karya dan yace zai dawo,
ba zaki iya jin komai a bakina ba Aziza dan alƙawarin da muka yiwa Magaji cewa daga bakinmu wani nasa
ba zai ji tahirinsa ba sai dai idan shine ya bayar, sabida alkhairin da Magaji ya mana ba zan manta da shi
ba, hakika Magaji Bawa jarumi ne, Aziza wannan abunda zakiyi ba ƙaramin yaƙi bane wanda ke daya ba
zaki iya yi ba,ni kuwa bazan iya tayaki ba, amma ga wannan ki ɗora shi a ɗamtsen hannunki zai taimaka
miki sosai,sannan karki taba rabuwa da shi dan wani sirhitaccen karfi ne, duk sadda kike bukatar
taimakona ki kirani zan zo!" tana shirin b'acewa da sauri Aziza ta ce

"Inno Fandi! Jejin lore! Ina so naje" zaro ido Inno Fandi ta yi ba tare da ta yiwa Aziza magana ba ta b'ace,
a hankali Aziza ta buɗe ido ta kalli Azima wacce har yanzu take tsaye take magana a kan zata kashe
Aziza.




Ɗora zaren da Inno Fandi ta bata ta yi a damtsen hannunta sannan ta juya baya ta rintse ido nan fatar
jikinta ya hau sab'ulewa alama ce na zata koma macijiya, nan ta zama wata katuwar macijiyafiye da
yadda take zama a da, fara sol sai kyalli take yi, Azima dake ta zuba tin dazu bata san abunda ke faruwa a
bayanta ba, sai bayan da ta gama maganarta na karshe da fadin

"Sai fa hakuri! Amma yau za ki mutu! Ni haka nake! Muguwa ce ni! Ban san sani ba! Ban san sabo
ba!"tana gama faɗi ta juyo dan cakawa Aziza wuka nan ta ga babu Aziza, ɗaga kan da zata yi ta hangi
kanta a can sama, Aziza ta zama katuwar macijiya mai cike da tsoro da firgici, da mugun tsoro Azima ta ja
da baya tana fadin

"Ya haka?" bata ankare ba ta ji anyi sama da ita an yi kasa da ita, kafin ta girgije ta ji an dauketa ana
zagaye iska da ita, sai da aka wujijjigata sosai sannan aka yi wulli da ita, faɗuwa ta yi ta bugu.




43
HAUSACINEMA.COM


Buɗe baki Aziza tayi a tana macijiyarta hau yiwa Azima ruwan macizai su na fita suna saren Azima, sai da
ta cikata da macizai sannan ta koma mutum tana tsaye tana kallon Azima wanda macizai ke sara, Azima
ta kasa tabuka komai, da taji jiki taji tabbas zata iya mutuwa ita kuwa ba zata yarda ta mutu ba tare da ta
dauki fansa ba yasa ta ce

"DAN ALLAH AZIZA! KI KWASHE MACIZANKI! ZAN GAYA MIKI WANDA ZAN KASHE!"jin haka yasa Aziza
ware hannu ta janyo macizan sannan ta b'acer dasu, tana janyesu Azima ta zube kasa a galabaice, Aziza
ta ce

"Gaya min! Wa za ki kashe da zaren saƙar dana?"

" BAFFA" Azima ta faɗa cikin muryan galabaita, saurin ja da baya Aziza ta yi ta ce

"Baffa?"




Da jan ido a tsawance Azima ta ɗago idonta ta watsasu a cikin na Aziza ta ce

"Eh Baffa zan kashe da zaren saƙar dana! Ban san wani irin kalar baiwa Baffa yake da shi ba, amma
abunda na sani shine duk wata hanyar guba da nabi dan son kashesa duk basu aiki! Tun ina gwada
kashesa a boye har na fara bayyanawa kika sani! Bincikena ya nuna min cewa zaren saƙar dana ne zai
kashe Baffa wanda da shine ya......." maganar da Azima bata karasa ba kenan Aziza ta wanketa da mari,
za ta kara Azima ta riƙe hannun Aziza ta ce

"Karki kuskura idan ba haka ba a yau din nan wannan al'karya zata koma toka, kodayaushe kina nuna
min karfin dafi da baiwar da kike da shi, ga taken kalmata ta karshe wanda kika sani Aziza, IDAN KIN ISA
KI DAKATAR DANI!"




miƙewa tsaye Aziza ta yi ta ce

"Na yarda da maganarki Inno! Domin tsaida zubda jini! Dole ne muma sai mun wanke hannuwanmu da
jini! Ke dodon mutan yankin nan ne da Baffa ko Azima? To ki sa a ranki ni nice dodonki, dakatar dake
kamar na yi na gama" dariya Azima ta kyalkyale da shi ta ce

"Muje zuwa, ai ba a buga komai a wasan ba! " ba tare da Aziza ta sake magana ba ta bar wajan, a hankali
Azima ta miƙe ta b'alli gashin kanta tsili ɗaya ta hura wani hayaki a jiki sannan ta haɗiye nan inda
macizan Aziza suka sareta wajan ya koma ya yi fess sannan ta dauki hanyar gida, Aziza kuwa ba gida ta yi




44
HAUSACINEMA.COM


ba, dan bata ga ta zaman gida ba,dole ne taje jejin lore dan lalata zaren sakar dana in ba haka ba kuwa
Baffa da sauran jama'a zasu mutu.




A tunzure ta zo shiga gidan, amma jin maganar da Baffa da Hajja ke yi ya sakata maqalewa a jikin zana
tana sauraronsu, Hajja ke faɗin

"Innu maciji kam ina da sa rai a kansa sosai, zai iya kawo mana karshen wannan matsalar da yardan
Allah, tunda yana gwagwarmaya da aljanu, a goben zai zo?"




"In sha Allahu! Haka suka ce zai zo a gobe, amma a gaskiya da a so samuna ne da bamu nemi taimakon
yankin ja'i ba sam wollah, karki so ki ga izgilancin da suka mana a cikin wasikarsu kafin su amince da
bukatar yankin nan"




Ajiyar zuciya Hajja ta sauke ta ce

"Koma miye tunda sun amince shikenan Allah ya shiga mana gaba! Idan kuma tsohon gaba ne yanzu
kuma ta kau ai, tunda yankin kwana ta duƙa musu" girgiza kai Baffa ya yi ya ce

"Jumala! Ba shi bane abunda nake hange! Idan wani abu ya samu Innu Maciji ko da ƙwarzani ne to fa!
Sabon yaƙin da ba ayi ba kwanakin baya shi za ayi yanzu! Duk inda ake neman rashin hakuri masu jiran
sammacin yaƙi idan aka samu yankin ja'i to an kai karshen magana, mutanen da jira suke a tab'osu ko
kaɗan ne su yiwa mutane cin mutunci, meyasa gabanmu dasu yafi tsanani? Ina sabida yankin kwana taƙi
daukar cin mutunci ne, amma al'ummar yankina sun kasa fahimtar abunda nake gaya musu, idonsu ya
rufe da neman mafitar wannan bala'i shiyasa duk shawaran da zan basu, ba su gani inda a karshe ma laifi
ne suke gani, suna ganin kamar zan iya wani abu a kai amma naki, duka so suke naje na haƙo kayana da
na binne wanda haƙo wannan kaya sabon bala'i ne da barazana wa rayuwar su Azima da Aziza har ma
dake! Balle kuma ace ni da ake neman fansa a kaina! Su tsaya su saurareni na gaya musu yadda za ayi
amma sam!" Baffa ya faɗa yana riƙe kansa dake sara masa, shuru Hajja ta yi ta ce

"Komai ya yi zafi maganinsa Allah Baffan yan biyu, mu dage da addua Allah na nan!"

"Haka ne Jumala, Allah ya shige mana gaba"




45
HAUSACINEMA.COM


"Amin" Hajja ta fada tana miƙewa da fadin

"Ko inasu Azima da Aziza suke? Kai wannan yara yanzu haka suna can rafin jimulo" Baffa dai bai kuma
cewa uffan ba.




Wani murmushi Azima ta yi da saurin komawa baya, ta ce

"Kai ashe dai ina da babbar mugun ƙulli! Gobe Innu Maciji zai zo, ayya Innu Macijiashe kwana ya kare!
Ajali ya yi kiranka gobe, wayyo dadi zan so na ci gaba da ganin tashin hankalin wannan yanki, hakika Innu
Maciji gobe asalin Macijiya Azima zata kasheka! Wayyo farin ciki! Zanyi tsumayen jiran zuwanka yankin
kwana!" ta faɗi tana dariya tare da gyara mayafinta, sannan ta shiga gidan da sallama wanda rabonta da
sallama harta manta,tana yin sallamar taji har wani ɗaci wuyarta ke mata, da mamaki Hajja ta amsa ita
da Baffa dake zaune, kusa da Baffa Azima ta zauna tana murmushi sai kuma ta koma tayi fuskar tausayi
tana kallon Baffa ta ce

"Baffa kayi hakuri da abunda nayi dazu ban san nayi ba, amma Aziza ta fahimtar dani, ka yafe min Baffa
ba zan sake ba, ban san lokacin da nake yi ba dan Allah Baffa " shuru Baffa ya yi yana kallon Azima a
ransa ya ce

"Kenan da gaskiyar Aziza, Azima aljanu gareta?" a fili kuma Baffa ya ce

"Shikenan ya wuce Azima,Allah ya miki albarka, amma ki gaya mini gaskiya ina kika samu zaren saƙar
dana?"




Turo baki ta yi ta ce

"Baffa ganinsa kawai nayi a hannuna! Yanzu kuma ya b'ace, ban gansa ba"




Baffa ya sauke ajiyar zuciya har yana hamdala, Azima ta miƙe taje ta rungume Hajja wacce rabon da ta
rab'eta ba zata iya tunawa ba ta ce

"Hajja ke ma kiyi hakuri" murmushi Hajja ta yi har kwalla na taruwa a idonta tana shafa fuskar Azima,
yatsine fuska Azima ta yi a ranta tana kallon Hajja ta ce

"Ni dai bana jin shaukin komai a tare daku, ko da ba zan ji a kan Baffa ba a matsayinki ta mahaifiyata ya
kamata ace naji shaukin uwa da 'yarta, amma bana ji saboda ni ba mutum ba ce! muguwar macijiya ce,




46
HAUSACINEMA.COM


shiyasa ma babu amfanin na dinga rab'anku, abunda nake so shine....." maganarta ce ya tsaya jin Hajja ta
jijjigata tana mata magana, dan tun dazu Hajja ke mata magana amma hankalinta ya yi nisa da tunani

"Na'am Hajja me kika ce?"

"Tunanin me kike yi Azima?"

" kawai Hajja babu komai mai kika ce?"

"Ina Aziza?" tsaki Azima ta yi a boye da tana shirin tace bata sani din ba, sai kuma ta tuno da abunda
take son yi ta ce

"Na barota a rafi, Hajja bari na tayaki aikin gida yau" tana gama faɗi ta hau gyara kara a murhu,Hajja har
can kasar zuciyarta take jin farin ciki, Baffa ya miƙe yana fadin

"Ba ri naje na gaida Inna Wuro (matar Arɗo) kwana biyu ma tace ba kuje kun gaisheta ba, wai dama
Aziza ce yar albarka yar dakinta, ke kam ma Azima ko meyasa jininku bai zo daya ba oho!"

"Ai ni babu wanda jinina ya zo daya da na shi!" Azima ta faɗa tana murmushin gefen baki mai ciki da
ma'anoni, Hajja ta ce

"Kinyi magana ne?"

"A'a Hajja ban ce komai ba, bari naje na ɗibo ruwa" ta faɗa tare da daukar tulu ta yi waje.




Tsaye take a wani jeji suna magana da Inno Fandi, Inno Fandi ta ce

"Aziza jejin lore ba kamar sauran jejin yankin kwana bane! Jeji ne da bai tara komai ba fa ce sai manyan
aljanu masu mugun sihiri, babu abunda babu a jejin lore,kina tunanin zaki iya zuwa?"




"Inno Fandi Azima ma taje ta dawo balle ni? Ba ma Azima ba, Baffa da yake mutum ma yaje" murmushin
manya Inno Fandi ta yi na yaro-yaro ne ta ce

"Aziza tabbas Baffanku mutum ne amma ba kamar kowa ba"




47
HAUSACINEMA.COM


"Eh ni dai Inno Fandi ko ma miye zanje"




"To shikenan Aziza, dokar tafiya jejin lore, ba a yinta da rana, sai dai ki bari da magriba ki tafi, sannan ki
tabbata kafin garin Allah ya waye kin baro jejin! Za ki ta gane-ganen abubuwa amma karki tsorata, dan
tsoronki barazana ce ga rayuwarki!"




"To amma Inno Fandi ina ga hakan ai babu amfani tunda ni ba mutum ba ce macijiya ce" sake murmushi
Inno Fandi ta yi ta ce

"Sanin kasancewarki ba mutum ba shiyasa nake gaya miki hakan, da ace mutum dan adam ne da ya
kama hanyar sunansa gawa! Tun kafin ma ya kai ga shiga" Aziza ta jinjina kai, nan Inno Fandi ta gama
gaya mata matakin da zata bi taje jejin ta dawo, godiya sosai Aziza ta mata daga nan Inno Fandi ta b'ace,
Aziza ta kamo hanyar gida, tana cikin tafiya har ta kusa isa gida ta haɗu da wasu yan matan yankinsu
wanda za a kamasu nan da sati daya wato amare kenan, wanda dukkansu babu wacce ta haura sama da
shekara shaɗaya, su hudu suka sha gaban Aziza, dayar mai suna Lantai ta ce

"Ke wacece Azima ce ko Aziza!?"Aziza ta ƙara gyara lullubinta tana rufe gefen idonta da gashinta da ya
sauko mata har kirji ta kara dukar da kanta kasa ta ce

"AZIZA" wata mai suna Huwe ta ce

"Yau kwayar idonki muke son gani, da asalin fuskarki!" gaban Aziza ne ya faɗi ta ɗan dago a hankali ta ga
rana ya faɗi ga shi dole taje gida ta yi shiri, dan haka ta ce

"Kun ga bana son kalen rigima da jan faɗa ku barni naje gida ni ba sa'arku ba ce!" dariya suka kwashe da
shi inda suka hau tureta tana ja da baya, har suna faɗin wai gandamemiya marasa farin jini sun ƙi aure,
babu mai sonsu! Gajiya Aziza ta yi inda ta daka musu tsawa sai da suka dare, hannu tasa ta kwashe
gashinta na gefen fuskarta farin eyes dinta na mage suka bayyana, da mugun gudu wannan ta yi
gabas,daya ta yi kudu,daya arewa,daya kuma ta yi yamma, Aziza ta ce

"Alhamdulillahi! Ni ku ka samu, da ace Azima ce sai dai a aurar da wasu amma ba ku ba" tana gama fadi
ta wuce da sauri tana sake rufe gefen fuskarta.




48
HAUSACINEMA.COM


"Assalamu alaikum" Aziza ta yi sallama Hajja dake kwashe kaya ta amsa ta ce

"Aziza sai yanzu? Tun dazu nake tambayar Azima tace min kina rafi, sawunta yau biyar tana ɗibo ruwa"




"AZIMAR!?" Aziza ta tambaya a mamakince, Hajja ta ce

"Eh wollah, yana ganki haka Aziza ba ki da lafiya ne?"

"E Hajja kaina ke ciwo sosai, shiyasa ma na zabi na zauna a rafin yau, ammm Hajja ga wannan ki sha"

"Inji waye?" Hajja ta tambayi Aziza

"Ba kowa nina haɗa miki sabida ciwon bayan da kike fama da shi"

"Ayye Aziza ai naji sauki tun wanda kika bani kwanakin can"

"E duk da haka ma ki sha wannan Hajja" ba

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login