Showing 60001 words to 63000 words out of 94205 words

Chapter 21 - Azima-Da-Aziza-Macizai Ne Complete

20 Jul 2024

37849

tabbatarwa kanki" Hadiza na gama fadi ta juya ta fice.




Girgiza kai Azima ta hau yi, Banju dake jikin Azima yaji a jikinsa tabbas idan bai bar gidan nan ba,
AL'MAZEEN shine makarinsa na farko a karo na biyu, to amma taya zai bar gidan? dan ya sha yunkurin
haka amma zaiji kafafunsa tamkar an dauresa ne.




Baya-Baya Azima ta yi ta koma jikin kofa ta bude blue eye dinta ta zaro dogon harshenta tana busar da
wani tururi shi ba fari ba, shi ba baƙi ba, shi ba blue ba, tana hura wanna iskan hayakin nan take parlour
da dakin da toilet din da kitchen din suka zama sabbi dal, harshenta ta maida sannan ta saka key a kofar
ta shige bedroom ta zama macijiya ta hau gado ta kwanta dan bacci take ji, a macijiyar tayi kwanciyarta
ta hau bacci.




137
HAUSACINEMA.COM




"To yanzu Aziza a ganinki taya zamu je kano? Khalil ya hana, Mom kuma ta biye masa,kuma kinga yanzu
ne nake da freedom bayan aure kuma sai abunda Allah ya yi, ga shi yanzu bikin saura wata daya da sati
biyu, bai ma cika da sati biyun ba, wlh na rasa yanda zanyi" ajiyar zuciya Aziza ta sauke ta ce

"Anty Sulty, abubuwa suna shirin cakuɗe mana,ni a ganina ya kamata mu maida hankali a guda daya"

"To wanne kenan Aziza?"

"Bikinki! Kinga kamata yayi ace mu maida hankali a kan shirye-shirye,idan yaso bayan anyi auren a lokaci
hankalu zai kwanta,idan ya so sai mu dubi gaba"

"Tabb lallai Aziza na tabbatar har yanzu da ƙuruciya na yawo a kanki, taya Khalil zai bar ni da aurena
muje yawon gari ya gari neman Azima? A yanzu ma da ba ayi auren ba ya na ƙare? Gaskiya wannan
shawara taki bata yi ba, ni wlh wannan biki da an bar sa idan na cika shekara ashirin sai ayi! tinda yanzu
ina sha tara" ta faɗa da fuskar haushi, waro ido Aziza ta yi ta ce

"Cab Anty Sulty shekara ashirin fa kika ce? to wlh da a rugarmu na yankin kwana ne ace kamarki bata yi
aure ba wollah ko zanar kofar gidanku bakki iya fita sabida gori da habaici da bakar magana, kin ganmu
nida Azima, shekararmu sha biyar amma yadda kika san kamar mun shekara dari ne bamuyi aure ba, dan
a al'adan rugar yankin kwana yarinya tana da shekara goma za a fara yi mata wankan kindirmo, tana
shiga sha daya za a aurar da ita"

" a shekara sha dayan!?" Sultana ta faɗa tana zaro ido

Aziza ta ce

"Wlh da gaske Anty Sulty"

"Tabdijam, lallai kam, ai mu kam nan ke baki isa aure ba, amma da shike zamani ya canza ana iya miki,
amma karatu ne yafi dacewa dake, ina son zuwa kauyenku"




"Tab to mu dai a can kinga bamu san wani abu karatun boko ba amma akwai manyan malaman
Muhammadiyya,kasancewar muna can cikin jeji ne amma bamu da wannan duhun kan na jeji muna da
ilmin addini sosai, amma In sha Allah idan na koma zan wayarwa da mutane mahaifata kai ta hanyar
karantar dasu ilmi daga cikin wanda na samu daidai gwargwado, tabbas na yarda ilmi ginshiƙi ne na
rayuwa,ilminka baya cika kuma sai ka haɗa duka biyu a kanka, farko sai ka ajiye ilmin da zai ceceka ranar
lahira, sannan ka kara da na bokon wanda shima ta sanadinsa zaka iya shiga aljanna, Allah ya bamu ilmi




138
HAUSACINEMA.COM


mai albarka, rugarmu kuma In sha Allah idan Hamma Khalil ya bar ki zakije, amma fa karkije ki ƙi
dawowa"




"Amin ya Allah Aziza, hahaha taya zan ƙi dawowa?"




"Idan kikaji dadin rugarmu mana"

"Humm ke dai, ai kya bari naje na ganewa idanuna ko?" Aziza ta yi murmushi ta ce

"Ai shiyasa ban baki labarin ni'imar dake yankin sassaninmu ba" Sultana ta yi dariya ta ce

"To naji, kar dai ki shashantar da

maganata"




"To abunyi shine kawai ki ƙara tuntubarsa" Sultana ta jinjina kai tana fadin

"Ok zanyi hakan In sha Allah,ina zuwa" ta faɗa tana ficewa a dakin.




Kamar yadda Aziza ta cewa Sultana ta kara tuntubar Khalil da maganar ya bar su suje kano hakan kuwa
akayi, ganin ta takura yasa yace ta bari to idan su Nawaz suka dawo aka karasa saita komai sai taje tayi
kwana biyu idan ana biki saura sati daya, tasan halinsa baya canza magana dan haka ta amsa da to,
amma a zuciyarta ta yi lissafin garin da zasuje ya kai shidda, tace ai ba ayi auren ba, balle idan ta tafi tana
tafiya akan wutar jahannama (Allah ya kiyashemu amin).




139
HAUSACINEMA.COM




Tunda aka shiga saura sati su Nawaz su dawo, Mom dasu Sultana da Aziza wacce faduwar gabanta ya
tsananta a kwana biyun nan wanda ta rasa dalili hakan, suke shirye-shiryen dawowarsu Nawaz da
Al'mazeen, da aka shiga satin karshe murna a wajan Mom da sultana abun sai wanda ya gani, Aziza ta
kasa gane ita wani hali take ciki, shin murna take yi ne ko akasin haka, ta bangaren Azima ma kullum
tana sama part din Al'mazeen zata shiga ta gyara ta zama macijiya ta kwanta tayi baccinta.




MA SHA ALLAH.




A jiya ne su Nawaz shi da Amininsa Al'mazeen suka samu damar sauka a kasarsu nigeria, sun sauka ne a
airport din abuja, Al'mazeen ya kalli amininsa ya ce

"Dude mu wuce kd kawai"

"No wlh sai na huta, mu wuce hotel kawai mu watsa ruwa mu huta idan yaso gobe da safe tunda driver
ya zo 10 ma muna kd in sha Allah, ka ga kaima idan ka so zaka huta kafin ka wuce kano,ko ya kace?"

"As u wish" Al'mazeen ya faɗa yana shiga mota.




140
HAUSACINEMA.COM


A waya Nawaz yake gayawa Mom cewa sun sauka lafiya sai gobe da safe zasu shigo Kd, sannu da gajiyar
hanya mom ta musu,sannan ta ce Allah ya kaimu goben lafiya,bayan ta katse take gayawa Sultana sun
iso amma Nawaz yace sai gobe zasu shigo, itama dai Allah ya kaimun ta yi,ko da Sultana ta gayawa Aziza
sai gobe su Ya Nawaz zasu shigo kd amma sun dawo nigeria suna abuja,itama Allah ya kaimun tace
jikinta duk a sanyaye,ta bangaren hajjaju Azima,itama da taji kishin-kishin watakila sai gobe ko jibi
Al'mazeen zai shigo kano amma ya dawo nigeria ko kaɗan bata ji dadin hakan ba, amma tace tayi
hakurin jiransa na watanni masu tsayi dan dai kwana biyu babu damuwa.




Washe gari tunda sukayi sallar asuba basu koma bacci ba, suka share cikin gidan tass suka goge, Aziza ta
ce

"Anty Sulty kije ki k'ara gyara part din Hamma Nawaz, ni zan tsaya a kitchen" Sultana ta amsa da to
sannan ta fice ta bar Aziza ta hau aikin haɗa su abinci,ko da Mom ta shigo kitchen Aziza ta ce

"Haba Mom kina damu a raye me zaki zo yi a kitchen, dan Allah kije ki kwanta ki huta" murmushi Mom
ta yi ta kalli Aziza ta ce

"Hakika mahaifiyarki tayi farin haihuwa da ta haifeki, na yaba da hankali da natsuwarki, Allah ya miki
albarka ƴata" Aziza ta dukar ta kai tana juya white eye dinta ta ce

"Amin Mom ɗinmu" fita Mom tayi tana wasu tunani a ranta, hakika da ace Aziza mutum ce babu abunda
zai hana bata yiwa Nawaz kwadayin aurenta ba, duk da Nawaz Allah ya yisa da rainakon mace, yanzu zai
iya cewa Aziza tayi masa yarinya,ita kuwa zata so Allah ya bata sirka kamar Aziza wacce zata maye mata
gurbin Sultana idan tayi aure, ga shi dai Aziza ta shiga ranta sosai, duk da ita bata taba ganinta a macijiya
ba, bata ma fatan ganinta a macijiyan, amma taya zata fahimtar da Nawaz har ya aureta? Dan Nawaz
murɗaɗɗan mutum ne, zama tayi a bakin gado tana sauke ajiyar zuciya mai karfi,ta jima tana tunane-
tunane sannan ta hau adduar neman zabin Allah wa ɗanta da kuma Aziza wacce bata so ta rabu da ita.




Karfe tara da rabi suka kammala komai suka jera a dinning, sannan suka sakawa gidan turaren wuta ya
dauki kamshi, Sultana tace




141
HAUSACINEMA.COM


"Aziza je ki dau wanka nima bari na tafi"

"To Antyna a huta gajiya" Sultana ta hau sama, aziza kuma ta shiga dakinta, toilet ta wuce dan tana da
bukatar wankan nan sai kamshin abinci take yi,bayan ta fito ta dan murza mai kaɗan a fatarta wanda
yake sheƙi, wani doguwar abaya ta saka, ta shafawa kanta mai,ta daure gashin, bata sa hula ba,illa lullubi
da ta yi ta rufe fuskarta wanda ta jima bata rufe ba Mom ta hanata rufewa tace tayi rayuwarta ta daina
takurawa kanta tunda sun san gaskiya, amma da shike yau Nawaz zai dawo harda bako yasa tayi lullubin.




Tana nan zaune a dakinta har wajan goma da minti asharin, ihun Sultana ta jiyo tana fadin

"Oyoyooo my 2 Brother's!!" wani wawan faduwar gaba ne ya dira a zuciyar Aziza jikinta ya dauki rawa,
tana ji ana oyoyo tare da fadin ya hanya, muryan Sultana ta jiyo tana kwala mata kira, a hankali ta miƙe
ta gyara mayafinta ta fito jikinta na rawa, a lokacin Nawaz da Al'mazeen suna rungume da Mom, Sultana
na tsaye a gefensu tana dariya bakinta yaki rufuwa dan murna, bayan sun saki mom take kara musu ya
hanya suna amsa da lafiya alhamdulillah, nan Mom ta rufesu da addua na nasarar da suka samo,zama
sukayi a kujeran cikin parlourn, Sultana ma ta zauna kusa da Yayanta, tana kara gaishesa ya amsa yana
tsokanarta amarya-amarya, rufe fuska tayi da tafin hannunta jin Al'mazeen shima ya hau tsokanarta,
ganin yadda suke murna da nishaɗi yasa hawaye zubowa a idon Aziza tana kallonsu tana murmushi dan
sun burgeta, a hankali ta juya zata koma daki idon Sultana ya sauka a kanta, ta ce

"Aziza kina jina tun dazu nake kiranki Yaya sun dawo amma kika min shuru?" tun sadda Sultana ta kira
sunan Aziza hankalin Nawaz ya koma kanta yana kare mata kallo kirjinsa na bugawa, tunda ya bar nigeria
mafarkin yarinyar nan ya hanasa kiba, Al'mazeen ya kalleta shima yaji gabansa ya fadi, Mom tace

"Karaso mana ɗiyata" a hankali Aziza ta fara taka kafarta wanda take jinsa tamkar baya jikinta dan
kafafun sun mata nauyi, ta karaso ta duka tana gaishesu kanta a duƙe fuskarta kuma a lullube, amsawa
Al'mazeen ya yi sabanin Nawaz da yake ji kamar zuciyarsa zata tsaga kirjinsa ta fito waje, bayan ta
gaishesu ta mike ta kawo musu abun sha, suka ce ba zasu ci abincin yanzu ba, zasuje su kwanta su ɗan yi
bacci zuwa azahar,sai sun farka kafin su ci abinci, a tashi lafiya Mom ta musu suka miƙe a tare, har sun
kai kofa Mom ta ce

"Al'mazeen amma ba yau zaka tafi kano ba ko?"

"E Mom sai Allah ya kaimu gobe"

"To Allah ya kaimu lafiya"

"Amin" ya amsa a sanyaye yana bin bayan Nawaz wanda shi bai tsaya ba.




142
HAUSACINEMA.COM




Kwanciya sukayi ba jimawa kuwa bacci ya suresu, karfe daya da rabi suka farka suka yi sallah, Nawaz ne
ya fara tashi yana fadin

"Yunwa nakeji yanzu kam, ka zo muje muci abinci"

"Okay muje" Al'mazeen ya faɗi shima yana tashi, wayar Al'mazeen ne ya dauki ruri Nawaz na ganin mai
kiran ya yi tsaki yana fita.




A hankali take tafiya Mom ta bata sako ta kai wa driver zai kai wa Hajiya Hauwa, kanta a sunkuye ga shi
ta yi lullubi ga tunani,tana tafiya tana tunani, shi kuwa Nawaz hankalinsa na cikin waya yana dannawa,
dai-dai wajan kofar shigowa babban parlour sukayi karo nan kafarta daya ya zame yana shirin wucewa
ƙananan step guda uku na shigan parlourn ɗin, ganin haka yasa cikin saurin Nawaz yasa hannu ya
fizgota, mayafinta ya faɗi kasa, gashinta da bata yi masa daurin kirki ba ya koma baya yana lilo, tsoro
yasa ta waro idonta gabadaya waje, caraf sukayi 4 eye da Nawaz, wani mahaukacin bugawa kirjin Nawaz
ya yi ganin white eye ɗin Aziza, saurin saketa ya yi ta faɗi ta bugu da duwawu, taji zafi dan haka tace

"Washhh Allah na!" Al'mazeen dake waya ya ga Nawaz ya saki yarinyar mutane a kasa ta bugu dan ya ga
sadda sukayi karon zata faɗi ya riƙeta amadadin ya tsaidata da kafarta sai kuma ya saketa?.




"What's wrong with u dude?" Al'mazeen ya faɗa yana shirin sa hannu ya dago Aziza,kafin Al'mazeen ya
ɗagata,tuni Nawaz yasa hannu ya sake fizgota ya tsaidata da kafafunta, ya duka ya dauki mayafita ya sa
mata a kai, murya a daqile yace mata bar nan, da sauri kuwa Aziza ta bar wajan, Al'mazeen ya kallesa ya
girgiza kai ya wuce ya bar sa tsaye, jikin Nawaz ne ya dau rawa yana kara tariyo yadda ya ga idon Aziza,
me hakan ke nufi? Ya tsaya yana tambayar kansa.




143
HAUSACINEMA.COM


"To meyasa kika ce ba zaki je ba? Ni wlh na zata Hamma Khalil shine Abokin Hamma Nawaz" cewar
Aziza,Sultana ta ce

"A'a kinga hoton Khalil" Sultana ta faɗa tana nunawa Aziza hoton Khalil a wayarta, Aziza ta yi murmushi
ta ce

"Ma sha Allah,kun dace sosai, Allah ya kaimu musha shagali"

"Amin-Amin"

"To ke yanzu Anty Sulty miye abun damuwa dan za a saka bikinki?"

"Ke Aziza baki da hankali ko? Ke kin san takura irin na Khalil kuwa? Wlh idan ya dawo ba zai bari na dinga
motsawa ko nan da can ba,kuma duk abunda ya faɗi Mom zata hau kai ta zauna, taya zamu fara tafiye-
tafiye wajan neman Azima? Sannan ma duk ba wannan ba, wannan babban lamari bai kamata ace zamu
iya mu biyu ba, Mom tana da fahimta ni a ganina tun a ba kowa mu gaya mata gaskiya, dan kar a zo wata
rana ta sani kuma abun ya kwab'e mana" jikin Aziza ne ya dauki rawa ta kalli Sultana ta ce

"Anty Sulty Mom zata koreni!" ture abincin gabansu gefe Sultana ta yi ta kamo hannun Aziza ta ce

"Taya Mom zata koreki Aziza? Babu amfanin boye mata abunda zata sani duk daren daɗewa kamar
yadda nima na sani a yanzu, dan haka gwara mu gaya mata a san abun yi tun a yanzu, ga shi ana
maganar tsaida bikina kwanan nan, tsammaninki yanzu Khalil zai dawo a cikin sati, su Yaya Nawaz zasu
dawo nan da wata daya,ina mai tabbatar miki za a iya aurar dani nan da wata biyu, dan haka gwara muyi
da gaske, yanzu ki tashi muje mu samu Mom mu gaya mata gaskiya, dan hausawa na cewa da zafi-zafi
ake dukan karfe"

"Wani gaskiya zaku gaya min?" suka ji magana daga bayansu, ba iyakar Aziza ba, har ta Sultana sai da ta
kwalalo ido waje, Mom ta ce

"tambayarku nake yi, sai zazzare idanu kukeyi ku min magana mana, dan wannan idon naku baku da
gaskiya" Sultana ta kalli Aziza wacce take girgiza mata kai alaman kar ta faɗa, Sultana ta hau in-ina tama
kasa magana,idan ta kalli Mom, Mom zata ce ta gaya mata me suke boyewa,idan ta kalli Aziza zata
girgiza mata kai kar ta faɗi, dan haka Sultana ta kasa magana banda in-inar da takeyi dan an sakata a
tsakiya, ganin ta ruɗe har zufa take yi, ga Aziza da ka kalleta kaga tashin hankali a fuskarta ganin haka
yasa Mom kamo hannun Sultana ta ce

"A iya sanina ban yi miki tarbiyyar k'arya ba,ba halinki bane, sannan baki boye min abu, duk da ban san
Aziza sosai ba amma zan iya tsayawa na bugi kirji na faɗi halin Aziza, dan haka karku fara min karya daga
yau, karku boyemin komai, tun dawowarku nake ganin damuwa a fuskarku, ku gaya min meke faruwa"
kuka Aziza ta fashe da shi tana duƙawa ta rufe fuskarta da tafin hannunta, Sultana tace




144
HAUSACINEMA.COM


"Aziza ki kwantar da hankalinki, Mom zan gaya miki" Sultana ta zaunar da Mom tace

"Ban san taya zaki fara daukar maganar ba, watakila da ace ni daya ce zakice nayi gamo da aljanu"
Sultana bata fara cewa Mom Aziza macijiya bace,tun daga tushen labarin ta dauko mata tana bata
tiryan-tiryan har ta kawo mata shi karshe ta dasa aya, wani ware ido Mom tayi tana bin Aziza dakallo
wacce ta haɗa kai da guiwa tana kuka, hakika hankalin Mom ya tashi, Sultana kuwa ta gaya mata ta ga
Aziza a macijiya kuma ita ce ma ta taimaketa daga hannun su dan gidan Alhaji wanda da badin Aziza ba
da sunyi mata fyaɗe, jikin Mom banda kyarma babu abunda yakeyi, ta jima tana karanto kalman

"Innalillahi wa inna ilaihirrajiun!" kafin ta fara jin tana samun natsuwa, sai da ta ware tukunna ta yi kan
Aziza ta duka duk da zuciyarta na dukan tara-tara ta kama Aziza ta rungumeta tana rarrashinta, cikin
kuka Aziza tace

"Mom dan Allah karki tsaneni! Dan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login