Showing 81001 words to 84000 words out of 94205 words
halin girma da cikar zati da haiba.
Da daddare mom ita ce tayiwa Azima da Aziza komai,ita da Maman Beenah suka raka Azima da Aziza,
Almazeen wani irin kunya yakeji, hajja kuwa ta kasa fitowa a bukka tana zaune tana tasbihi ga Allah, tana
roƙon mai duka da ya fidda mata yaranta lafiya, hakika ita kam ta ga jarabta.
190
HAUSACINEMA.COM
Bayan an mikawa Almazeen Azima wacce take da ita da babu za a iya cewa duk daya, sannan aka wuce
aka kai wa Nawaz Aziza duk da shi ba wani abu bane zai wakana a tsakaninsu.
Ko da su Mom suka koma itama ba kwanciya tayi ba, alwala tayi ta zauna ta fuskanci gabas, Maman
Beenah kuwa gadon kara ta haye tayi kwanciyarta dan tace bacci takeji.
Baffa ma uban gayya bai ga ta zama ba balle ya rintsa dan kuwa a tsaye yake kyam.
AL-MAZEEEN DA BANJU AZIMA.
A bukka kuwa Almazeen zama ya yi ya kurawa Azima ido yana kallonta, shi bai ma san ta ina zai fara ba,
ya kwashi kusan mintuna talatin yana kallonta daga bisani ya tashi ya ɗauro alwala ya yi sallah raka'a
biyu, ya ciro wayarsa ya yi karatun alkur'ani mai girma ya daga hannunsa sama yana adduoi sannan ya
shafa ya miƙe a hankali ya fara rage kayan jikinsa, wani magani da Baffa ya basa yace ya shafa a jikinsa
idan zai taba Azima, maganin ya shafa a hannunsa da dukkkan jikinsa, yana tabata sai da ta
girgiza,kwantar da ita yayi, Banju dake jikinta yana kallon abunda ke faruwa ɗauresa kawai Baffa yayi,
wani gurnani ya fara nan ya hau buge-buge, Almazeen da iyakacin karfinsa ya fizgi kayan dake jikin
Azima, nan dambe ya kacame duk da banju yana daure amma ba shi ya hanasa kokarin yunkurin kashe
Almazeen ba shima Almazeen yaci albarkacin daure Banju da Baffa yayi amma duk da haka yanaji a
jikinsa, duk kalman da yazo bakin almazeen indai na salati ne yin shi yake yi
,Banju bai gama sarewa ba sai da ya ga Almazeen ya yiwa Azima kaff da kayan jikinta, yunkurin komawa
maciji Banju yayi amma kafin ya fara hakan tuni Almazeen ya karanto adduar saduwa ya fara kokarin
shiga jikin Azima, wani sarawa kansa yayi tare da wani wawan jiri dake shirin watsa shi waje daurewa
yayi ya riƙe kokaran gadon karan gam jikinsa na kyarma, nan Azima ta fara canzawa tana zama wata
halitta daban mai matukar ban tsoro da firgitarwa, kokarin zare jikinsa yayi dan dama bai shigeta sosai
ba, tunowa da maganar Baffa na cewa kar ya kuskura ya kyale Azima har sai ta yi attisha sau uku dan duk
hanyar da Banju zai bi dan ya ga ya hana Almazeen kusantar Azima zaiyi, daga karshe kuma zai kashesa
ya kuma guduwa, tunowa da haka yasa Almazeen ya dage da iyakacin karfinsa sakamakon b'ari da jikinsa
ke yi ya shige Azima gabadaya, wani ihuu Azima ta saka da karfi wanda sai da ya karaɗe gefe da kewayen
inda suke, ta shaƙo wuyan Almazeen wanda shi kadai yasan abunda yakeji kamar ana zare ransa haka
yakeji tsananin azaba dan harta fatarsa ji yakeyi kamar ana soya masa shi, sake damƙar kafaɗun
Almazeen Azima tayi ta dage ta saki wani attishawa mai karfin gaske dan kuwa an karya makarin Banju
tunda Almazeen ya afka cikinta, tana yin attishawa na ɗaya tayi na biyu, na ukun ne nan wani guɗa ya
hau tashi, tana attishawar Banju wanda ya yi tsalle ya fice ta baki da hancin Azima, ƙauuuuu! Azima taji
yayinda ta wani firgita tana jan wani numfashi da iskar duniya,da nauyin kaita hau ware ido da kyar jin
idon kamar an liƙe mata su, tana ji tamkar yau ne uwarta ta haifeta, tana gama buɗe ido mutum ta
191
HAUSACINEMA.COM
hanga a saman kanta, Almazeen wanda yake gaff da sumewa yana ganin ta bude ido a hankali ya sauke
bakinsa saitin kunnenta cikin mayuwacin hali da kyar ya furta
"Alhamdulillah! Wlcm back my dear wife, am so happy, u are back! i promise that i wouldn't let any
harm attack u, i will sacrifice my life to u, cox I luv u, am really luv u, i fell in luv with u Azima! pls don't
leave me alone" Almazeen na faɗi ya hau kokarin zare jikinsa daga na Azima, a lokacin Azima taji wani
mugun raɗaɗi ta kasanta hakan ne yasa taja wani numfashin mai cike da azaba, a tare suka suma.
Banju dake tsaye yana
kallon Almazeen wanda yake son kashesa dan ya lashi takwabin sai ya kashe Almazeen, amma inaaa ya
kasa kusantar almazeen balle ya kashesa kasancewar Almzeen mutum ne mai riƙo da ibada baya sanya.
NAWAZ DA AZIZA.
Sadda aka raka Aziza tsayuwa tayi a bakin bukkar taki karasowa, Nawaz na zaune yana danna wayarsa da
tun shigowarsu garin babu network ko ɗigo, ɗaga ido ya yi ya kalleta ya ga jikinta sai rawa yakeyi, da
alama tsorata tayi, a hankali ya tashi yaje gabanta bata ma sani ba tayi zurfi a tunani, ji tayi an kama
hannunta, a firgice ta dago idonta ya haɗe da na Nawaz, ganin duk ta taburce yasa Nawaz rausaya kai
yace
"Ya haka? Jaruma a waje, matsoraciya a gabana?" ya faɗa yana matsota sosai, ja da baya tayi tana shirin
ficewa yasa hannu ya jata ta shige jikinsa,
"Haba jaruma, karki bani kunya mana" mutsu-mutsu ta hau yi tana son kwace jikinta, yasa hannunsa
duka biyu ya kewayeta ta kasa kwacewa ya ce
"Ko za a watsar dani ne?" nan ma bata masa magana ba, ya ce
"Idan baki min magana ba, zan cinye bakinki" mamaki ne ya kama Aziza, oh dama haka Nawaz yake?
take tambayar kanta, bata gama yankewa ba sai da taji ya dauketa ya ajiyeta a saman gadon kara yana
shirin kwanciya a kanta tayi saurin miƙewa zunbur tana fadin
"Sorry Hamma" murmushi ya yi a boye, ya ce
"To matso kusa dani, kin san Baffa yace na rikeki da kyau dan haka matso" ya faɗa yana ware mata
hannu alaman ta shigo cikin jikinsa, ganin yadda ya sauya fuska ba alaman wasa yasa ta matso a hankali
192
HAUSACINEMA.COM
ta shige jikinsa ta kifa kanta a ƙirjinsa, yasa hannu ya rungumeta da kyau yana son fassara me zuciyarsa
takeji game da Aziza.
A lokacin da Almazeen suka fara dambatuwa da Banju, a lokacin Aziza na kwance a jikin Nawaz, lokaci
daya kamar an zabureta haka ta miƙe, cikin hanzari Nawaz ya fizgota ya maidata jikinsa ya matseta dan
ya tuno da maganar Baffa da yake cewa idan Aziza ta subuce za a iya rasata shiyasa ya kara matseta
sosai a jikinsa, ihu Aziza ta saka jin fatar jikinta na sabulewa, saurin ture Nawaz tayi ta koma gefe tana
ƙanƙame jikinta, fuskarta ne ta ji yana b'anb'arewa, hannu biyu tasa tana tare fuskarta tare da ihu, ganin
halin da take ciki yasa Nawaz saurin tashi zai zo gareta, nan yabga masifa, daga ƙugunta abunda ya yi
sama ta zama macijiya fara sol sai kyalli take yi, sak irin wanda yake gani a mafarkinsa, hannu ta miƙa
masa cikin azaba tana fadin
"Help me plss! ka taimakeni Hamma Nawaz!" ta faɗa siffarjikinta na ƙasa na haurawa zata zama
macijiyar gabadaya, da saurin Nawaz ya rintse ido yaje ya rungumeta ƙaƙam! Yana rungumarta ta tsaya a
haka, a lokacin da Banju zai fita a jikin Azima itama Aziza taci azaba dan nan suka hau gwada karfi da
Nawaz, hakika shima ya jikata, dan kuwa sadda abun zai fita gani ya yi wani farin abu shi ba dutse ba shi
ba tsuntsu ba ya fice ta goshin Aziza, yana fita numfashinta ya tsaya cak yayinda ta koma mutum, haka
Nawaz ya zauna riƙe da ita a jikinsa, gab'ob'insa na masa ciwo sosai, har asuba.
Sanyin asuba ne ya fara farkar da Almazeen wanda da kyar yake iya buɗe ido sabida nauyin da suka
masa, ya jima a haka kafin da layi ya tashi ya janyo kayansa ya saka, ya rufawa Azima jikinta, ya koma ya
kwanta a gefenta yana sauke huci mai zafi.
Baffa suna idar da sallar asuba Arɗo yace su je a duba yaran nan.
Mom aka kira dan da ita za aje Hajja ta ƙi fitowa ƙememe.
Suna zuwa gidan Hajja zata shiga da saurin Baffa ya dakatar da ita ya hanata shiga, yace tana shiga Banju
zai iya kasheta dan shi yanzu duk wanda ya samu zai kashe ne" Baffa ne ya fara shiga cike da yarda da
kansa sabida ya yi imani da Allah ya yi riƙo da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam,duk wanda ya yi
riƙo dasu baya da fargaba a kan kowa, yana shiga kuwa Banju dake neman hanyar guduwa a gidan tun
daren jiya ya kasa sabida Baffa ya ɗaure ko ina da ina, suna ido huɗu Baffa ya daga takwabi, Banju yace
"Magaji a gwabza idan ba tsoro! karka kasheni sai mun gwabza!" Baffa ya yi murmushi yace idan ka so
haka"
193
HAUSACINEMA.COM
"Zan so! amma ka ajiye takwabi" Baffa ya ce
"Ba daga yanzu zamu fara ba, kafin nan ga wannan" Baffa na faɗi ya wurgawa Banju wani igiya nan ya
daure Banju ya fito da shi, yana fitowa da shi ita kam mom bata iya daga ido ta kalli Banju ba, dan tace
mugun ji da mugun gani Allah ya rabamu dasu, Baffa na cewa zata iya shiga da sauri ta wuce shi kuma ya
wuce da Banju, mom na shiga ta samesu a yashe, Azima ta jijjiga sannan ta taba Almazeen wanda jikinsa
ke rawa alaman ciwo jikinsa zafi raɗauu kamar wuta, na Azima ma akwai zafi amma na Almazeen ya fi
nata, babu wani taimako da zata iya masa, amma zata iya taimakawa Azima, dan haka ta fito ta haɗa
ƙirare ta tafasa ruwan zafi, kafin ruwan ya gama sai ga jikan Ardo Sanda ya kawo wasu magunguna yace
Baffa yace idan su Hamma Almazeen da Azima zasuyi wanka a zubamusu shi a ruwan wankan suyi
wanka da shi, wannan kuma su sha, sannan a ba wa Hamma Mazeen wannan,wannan kuma a ba wa
Azima" mom ta karba tana masa sannunsa da aika.
Mom da kanta ta taimakawa Azima tanuna mata yadda zatayi wankan tsarki, sannan tayiwa mata wanka
haka,ita dai Azima wani iri take jin kanta, riƙota mom tayi suka shiga bukkar har yanzu Almazeen ya kasa
motsi koda da yatsarsa daya ne, taimakawa Almazeen mom tayo shima ya yi wanka ya yi sallah a zaune
ya sha magungunan da Baffa ya bada a ba shi daga nan ya hau bacci,itama Azima maganin ta sha ta hau
bacci, haka ma Aziza wanda aka aika aka ba wa Nawaz yasha ita ma ya bata ta sha duk suka buge suka
hau bacci.
Can wajan dandalin yanki Baffa yaje ya daure Banju, ko kaɗan Banju baida kyawun halitta gani, ga girma
katam da shi tamkar basamude ga baƙi fiye da misali, kai babu ta yadda za a sunfanta zubin halittan
Banju.
Bayan Baffa ya daure Banju yasa maga isar da sakon yankin kwana a kan ya rubuta wasika yayi aike
sauran yankuna ana gayyatar su izuwa kallon fafatawa a tsakaninaljani Banju da Baffa bisa umarnin
gayyatar sarkin yankin kwana wato sarki chubaɗo, kamar irinsu yankin ja'i da yankin tudu da yankin ja'o
da yankin gangare, da yankin shani, da dai sauran yankuna.
Sadda wasika ta iskesu sun sha mamaki, kai wannan ai babban fafatawa ne a tsakanin Magaji bawa da
Maciji Banju, wanda ya yi b'arna da ta'adi a yankin kwana, wanda ya kashe shahararrun masu kama
macizai irinsu jarman macizai dasu Innu maciji, da iro mai maganin macizai da dai sauransu, hakika duk
yankuna sun amince zasu zo ganin wannan fafatawar tsakanin mutum da aljan,duk da wannan ba sabon
abu bane a wajan Garkuwan Kwana Magaji Bawa Arɗo.
194
HAUSACINEMA.COM
Mom ce ta cewa Baffa dan Allah ya taimaka ya raba Aziza da Bahula ta koma asalin cikakkiyar mutun
ɗinta ta huta gaba daya, Baffa ya yi murmushi ya ce wannan ba wata matsala ba ce, suka je gidan har
zuwa yanzu suna bacci, goshin Aziza Baffa ya riƙe ya rintse ido, attishawa Aziza tayi sannan ta fara
hamma, wani farin abu ne ya fito ta bakinta, a hankali farin abun ya koma kamar farin hayaki haka, daga
nan abun ya zama mutum wanda ake mata kallon dishi-dishi, Baffa ne kawai yake iya ganinta dan kuwa
mom ba ganinta take yi ba, kallon Baffa Bahula tayi tana girgiza kai hawaye na zuba a idonta dan tasan
Baffa kashe mata Yayanta Banju zaiyi dan tasan ko a wasa Yayanta Banju ba zai haɗa karfinsa da kwatan
karfin da Magaji ke da shi ba,kawai dai a mugunta ne baya da lamba ta biyu, dukar da kai Baffa yayi,
daga haka Bahula ta b'ace, muryan mom Baffa yaji tana magana
"Baban Aziza? Yanzu shikenan sun warke babu wata matsala ko?"
"In sha Allahu, sun warke, amma wanda ba yanzu zaiji sauki ba wanda shi ba mu san a ya zai farka ba
shine Almazeenu, amma harta Azima zata farka lafiya lau,kuma idan ta farka za a gaya mata gaskiyar
abunda ya faru kar a boye mata duk da abun da suka faru zata iya gani duk da ta kasance a sumeamma
zata iya gani kamar mutum mai bacci yana mafarki sabida sun rayu a jiki daya da Banju,jikin ma kuma
nata ne, zata tuna komai kuma zata gane komai shiyasa za a gaya mata sabida rashim gaya mata zai iya
haifar mata da wani matsala, mom ta gya ɗa kai tana mai tausayawa Almazeen.
Basu suka farka ba sai lokacin sallar azahar, wani ɗauuuu!! Aziza taji a kunnenta da ta farka, zata fadi da
saurin Nawaz ya riƙeta, wanda shima yanzu baya jin komai ciwon jikin nasa ya tafi
"Kina lafiya?" Aziza ta gya ɗa kai tana gyara tsayuwarta, zuwa can ta ce
"Azima? yar uwata?" ta faɗa zata fice da sauri Nawaz ya rikota yace suyi sallah kafin su tafi, sallan kuwa
suka gabatar shi ya jasu sannan suka fita sukayi gidan da Almzeen da Azima suke, mom ma tana gidan
tana kula da Almazeen wanda a zaune ma ya ƙara gabatar da sallah, Azima kuwa tunda ta farka har tayi
sallah karo na farko a rayuwarta, bata furta ko da uffan bane kallo kawai take bin mutane da shi
abubuwa suna dawo mata kamar a mafarki haka take tariyowa, tana zaune a kan sallayar kaba su Nawaz
da Aziza suka shigo da sallama, Aziza tana ganin Azima a kan sallaya tasa kukan farinciki tana fadin
"Azima?" daidai lokacin su Inna wuro da su Yawuro har ma da Hajja dasu Baffa suka shigo, juyowa Azima
tayi tana binsu da kallo, ganin Aziza yasa ta ce
"Aziza?" wani kuka Aziza tasa ta ƙaraso da sauri suka rungume juna ƙaƙam
"Me ya faru Aziza?" Azima ta tambaya cikin sheshsheƙar kuka
" zan gaya miki"cewar Arɗo, nan ya hau yiwa Azima bayani dalla-dalla tun fara kisa da yaƙi da komai da
barin yankin kwana har izuwa yanzu, wani kwalalo idanu waje Azima tayi ta hau girgiza kai tana fadin
195
HAUSACINEMA.COM
"Ni....ni....ni....ban.....ban....ban...kashe....kowa....ba.....Baffa.......bana....da niyyar kasheka...Hajja ban
miki rashin kunya ba.....Aziza...banyi faɗa dake ba.....dan Allah kuyi hakuri..... Ban kashe kowa....ba..."
duk Azima ta bi ta ruɗe mom ta jata a jiki ta ringume tace
"Mun sani Azima,mun san cewa jinin Magaji da Jamila ba zata aikata hakan ba, kwantar da hankalinki, ba
ki kashe kowa ba,mugun nan azzalumin aljani Banju shine ya kashe" ɗago daga jikin mom tayi tana kan ci
gaba da kuka, duk da zafi da ciwo da ƙasanta ke mata ba shi ya hanata tashi da gudu ta shige jikin hajja
da kuka ba, itama Hajja kukan takeyi, dagowa tayi ta kalli Baffa ta hau girgiza kai da hannu tana fadin.
"Aziza?" Azima ta kira sunanta itamamurya a sarƙaƙe, Nawaz ne yace kawayen Sultana su fita, da sauri
kuwa suka fice,suna fita Al'mazeen ya sawa kofar key, wani kallo Azima ke bin Aziza da shi har ma dasu
Mom, Mom ce ta tunkari Azima tana shirin yi mata magana da sauri Aziza ta ce
"A'a Mom!" tsayawa cak mom tayi, Aziza ta mata ido a kan taja baya, Al'mazeen ne ya matso kusa da ita
ya ce
"Azima zan iya ce miki wani abu?" shuru Azima tayi kirjinta na bugawa,
"Azima Ina sonki! Kuma na au...." maganar da Al'mazeen bai karasa ba kenan Azima ta saki ihu tana
toshe kunne, matsowa kusa da ita Aziza tayi ta duƙa a gabanta tace
"Azima? Ohh ina nufin Banju! Ka sa kunne da kyau, yanzu haka yola zamu tafi, yau sai yankin kwana In
sha Allahu! zaku haɗe da Baffana! dama kasan karonku dashi ba dadi" wani dariya Azima ta hauyi marar
dadin sauti tace
"Ke a tunaninki zan yarda na koma ne?"
"To taya zaka iya guduwa? Albishirinka! Yanzu haka da aure a kan Azima!" wani zaro ido Banju ya yi yana
fadin
Sun ci amanarsa sai ya kashe miji waye mijin, Al'mazeen ya amsa da cewa
"Ni nemijin!" wani kururuwa Azima ta saka ta miƙe da karfinta da niyyar zama macijiya dan ta saresu da
sauri Aziza tasa hannu da wani farin haske ta tokari goshin Azima nan tayi ɗiff!.
"Na kafar da ita zamu iya tafiya" Aziza ta faɗa jiri take ji amma