Showing 27001 words to 30000 words out of 94205 words
faɗin
haka bata kuma cewa komai ba, da gudu Aziza ta yi hanyar gida,ko da ta isa har yanzu Baffa na zube a
kofar gida ya kasa tashi, da sauri Aziza ta dagasa tana kiran sunansa "Baffa! Baffa! Baffa!" a tsorace dan
tayi zaton Azima ta yi masa wani abun ne dan zata aika, da kyar Aziza ta kama Baffa ta zo shiga gidan ta
ga har yanzu da sauran furen surfa a kofar gidan, ga shi babu abunda zata iya yiwa furen surfan, abu
daya zata iya yi shine ta nemi taimakon Inno Fandi, tun kafin ta kirata ma ta bayyana ta kwashe sauran
na bakin kofar kafin Aziza ta ja Baffa suka shiga gida, suna shigowa Hajja wacce har yanzu tana maqale ta
kasa fitowa bisa da cewa Baffan yan biyu bai ce ta fito ba shiyasa ta ci gaba da maqalewa, ganin Aziza ta
shigo da Baffa a hannu yasa Hajja fitowa a kiɗime tana fadin "Subhnallahi! Aziza me ya faru da
Baffanku?"
Aziza bata tsaya ba wa Hajjaamsa ba illa randar kasa da ta nufa ta dibo ruwa mai sanyi ta watsawa Baffa
nan ya sauke ajiyar zuciya yana ji kamar numfashinsa zai dauke, ruwan Aziza ta ba shi da kyar ya karba
ya sha sannan ya dafe kansa, sannu suke jera masa ba tsayawa, sai zuwa can Hajja ta ce
"Wai ni kam Aziza kamar dazu na ga shigarki bukka,amma tayaya kika fita a gidan ban gani ba? Ko
b'acewa kika yi?" Hajja ta tambayi Aziza ne kawai amma ga mamakinta sai ji ta yi Aziza ta ce "e Hajja
b'acewa nayi, sabida bazan iya bi ta bakin kofa ba, Baffa ya zuba furen surfa!" zaro ido Hajja tayi bama
61
HAUSACINEMA.COM
Hajja ba harta Baffa da bai gama dawowa dai-dai ba ya ɗaga kai yana kallon Aziza wacce ta miƙe tsaye
tana ja da baya tana girgiza kai tare da hawaye mai ban tausayi tana fadin
"Gwanda ayita ta kare, yau zaku san wani irin yara ku ka haifa, Hajja Baffa kuyi hakuri hakika baku haifi
mutane ba, Baffa na san da hannunka zaka kashemu bayan kasan mu ɗin su waye! Na san ka gama gane
Azima nice kawai baka gane ba,bazan iya munafurtanka ba Baffa!" da sauri Hajja ta miƙe tana fadin
"Me kika faɗi ne haka Aziza!"
"KARKI MATSO INDA NAKE!!" Aziza ta fada da karfi, Hajja ta ce
"Sabida me Aziza? Nifa mahaifiyarki ce!" tana fada tana kara tunkaro Aziza dake matsawa baya, rintse
ido Aziza ta yi ta buɗe ta haɗe rai cikin daga murya ta ce
" SABIDA NI MACIJIYA CE! AZIMA DA AZIZA MACIZAI NE!" Aziza ta faɗi tare da komawa Macijiya! Wani
mahaukacin kara Hajja ta saka tare da yin baya-baya ta faɗi timmm! A kasa, ganin haka yasa Aziza
komawa mutum ta yi kan Hajja tana jijjigata tare da ambatar sunanta,amma ina Hajja bata motsi
numfashi ya tsaya cak, cikin kuka Aziza ta ce
"Hajja ba dai hadiye zuciya kikayi ba!? Na shiga ukuna Baffa!!" Aziza ta fada tare da juyowa wajan Baffa
nan ta ga ashe shima ya suma! Randar ruwan kasar gabadaya Aziza ta dauka ta juye a kan iyayenta, da
kyar suka saki ajiyar zuciya, suna dawowa Aziza ta ce
"Baffa waye su BANJU DA BAHULA!!!?" wani zabura Baffa ya yi yana kallon Aziza, da sauri ya miƙe tsaye
ya ce
"Dole kafin nasan abunda ke yawo a jikinku saina haƙo abunda bana son haƙowa, Aziza na fahimci ke ba
kamar Azima ba ce, da ace ke kamar Azima ce yadda muka suma da kin kashemu! Na sha zargin Azima
na son kasheni amma naki ba wa shaidan damar da zai saka min waswasi a zuciyata a kan 'yar da na
haifa ta cikina! Dan haka zan gaya miki waye Banju da Bahula da abunda ya shiga tsakanina dasu, amma
kafin nan zo muje jejin firi"
Saurin riƙe hannun Aziza Hajja tayi idonta jajur ta ce
"Ya isa haka Baffan yan biyu! Ka sha saka rayuwarka a hatsari ga shi yanzu ta shafi yarana!" Hajja ta
fashe da wani matsinacin kuka tana zuba guiwowinta a kasa, da sauri Aziza ta kama hannunta, ko kaɗan
Hajja bata ji tsoron Aziza ba, cikin kuka ta ce
62
HAUSACINEMA.COM
"Macizai! Macizai! Macizai! Ni Jamila na haifi Macizai! Inaaa ba zai yu ba ni kawai a dawo min da
yarana!" Hajja ta kuma sa kuka bai tab'a zuciyar mai sauraro, rungumeta Aziza ta yi cikin tausayawa
domin kuwa Hajja abun tausayi ce ita da Baffa, fita Baffa ya yi yaje ya kirawo Arɗo da Yawuro, da Inna
Wuro, da kuma tsohon sarkin kwana wato Baffa Mandi, bai boye musu komai ba ya gaya musu komai,
hakika hantar cikinsu ya kaɗa fiye da tsammani, Arɗo ya ce
"Lallai kuwa idan har Banju ne ya dawo daukar Fansa! Kisa bai ma yi komai ba kenan! Ashe kuwa idan ba
a dakatar da Banju ba idan har shine sunanmu toka" Baffa ya ce
"Bazan bari hakan ta faru ba, yanzu daga nan jejin firi zamuje nida Aziza, zanje na haƙo kayana dan nasan
taya zan taimaki yankina da kuma yarana" Baffa Mandi ya ce
"Magaji!? Hakowa fa kace? Aljanu da mayu ayi yaya dasu?" Arɗo yace
"Buhun bala'in Banju gwanda haƙo aljanu da mayun da Magaji ya kulle, dan ba karamin babban shaidani
bane Banju! Ko ka manta b'arnan da Banju ya yi kafin Magaji ya kashesa?"
"Taya kuwa zan manta Arɗo? Bayan dukka ahalina Banju ne ya kashesu!"
Baffa wanda ke goge gumi ya ce
"Aziza tana tare dani, dan haka yanzu a gayawa su sarki Chubaɗo halin da ake ciki, sannan a cewa yara
da manya kar wanda ya fito ko da kofar gida ne, domin kasan aljanun da aka ɗaure duk wanda ya samu
damar guduwa zai fito ne da haushi da b'acin rai na dauresa da akayi na tsawon shekaru, dan haka duk
wa inda suka samu zasu bugesu ne, Yawuro, Inna Wuro ku kula da Jumala, Aziza muje" Aziza ta amsa da
to Baffa a sanyaye abun tausayi, zasu fita Hajja ta kuma sa kuka tana salati dan ita kadai tasan abunda
yake damunta, su Yawuro da Inna Wuro suna dannarta, yayinda Arɗo yace bari yaje wajan Chubaɗo su
zanta a kan lamarin.
B'acewar Azima jejin hayi ta nufa tana kan ihu fatar jikinta na mata zafi sosai,zubewa tayi a kasa tare da
furta "KARYANKA! NACE KAYI KARYA MAGAJI! FANSA NE DAI SAI NA DAUKA! AMMA NA RASA MEYASA
KAKE GALABA A KAINA TUN TSAWON SHEKARA ASHRIN! YANZU MA SO KAKEYI KA SAKE KASHENI! INA
HAKAN BA ZAI YU BA, DOLE NA MAKA MUGUN TABO! TA HANYAR CI GABA DA RAYUWA A GANGAR
JIKIN 'YARKA AZIMAAA!!"
Wannan murya na gama fitowa ta b'alli gashin kanta tasa a baki nan taji sauƙin raɗaɗin, sannan ba tare
da bata lokaci ko dogon tunani ba Azima ta dauki hanyar barin Al'karyan yankin kwana dan ta shiga cikin
gari ta cika burinta na tarwatsa jama'a da hanasu kwanciyar hankali.
63
HAUSACINEMA.COM
Baffa da Aziza suna isa jejin firi ba bata lokaci Baffa ya fara haƙo abunda ya binne, yana gaff da gama
cirowa ya kalli Aziza ya ce
"Kin shirya?" Aziza ta gya ɗa kai gami da cewa "e Baffa a shirya nake"
"Fara" Baffa ya faɗa,yayinda Aziza ta daga hannu sama ta fara haɗa wani baƙin guguwa mai cike da rami
dan tare mayu da aljanu ya kasance ko da zasu gudu kaɗan ne, da karfi Baffa ya fizgi wani abu kamar irin
akwatin karfe na tun tsawon wasu shekaru, yana fizgowa take wani mahaukacin guɗa ya tashi, wanda ba
iyakar jejin firi ba dukkan jeji sai da ya amsa tare da dukkan mutanen yankin kwana babu wanda bai ji
wannan gudar ba, Aziza na tsaye sai haɗa zufa takeyi yayinda take riƙe da wannan baƙin guguwar wanda
ta riƙe aljanu da mayu, ganin halin da take ciki da sauri Baffa ya buɗe akwatin wanda da ka gani kasan ya
daɗe ya dauki guru da layarsa ya maida (Allahu Akbar Baffa an tuno baya) duk wani abu da Baffa ke
amfani da shi sai da ya dauka,na ɗaurawa ya ɗaura na sakawa ya saka, na mannawa ya manna, ya fiddo
wani tulu mai murfi, yana fiddowa ya sake kama wasu aljanu da mayun ya rufe yayinda wasu suka gudu,
Aziza na sakewa ta zube sumammiya, Baffa bai damu da sumar da tayi ba dan na hucin gadi ne, ta ma yi
namajin kokari, dan ko shi iyakar abunda zaiyi kenan,kuma dabadin ita ba da yana haƙo abun nan ba tare
da an rikesu ba bala'in da zata kunno yankin kwana sai Allah.
Baffa na ciro kayansa ya haɗa wasu taurari guda biyu wanda suke kamar dutse mulmulen laka, sunan
Azima da Aziza ya rubuta a kai, nan wani haske ya bayyana, na Azima ya fara gani, nan ya hangi Banju a
gangar jikinta, Azima a sume take, wasu hawaye masu zafi ne suka wanke wa Baffa fuska, sannan ya
duba taurarin jikin Aziza, nan ya ga Bahula ce ke rayuwa a jikinta, sannan ita an maidata Macijiya ba
wani ke rayuwa a jikinta kamar Azima ba, cikin ruɗu da tashin hankali Baffa ya watsawa Aziza wani farin
kasa nan take ta sauke ajiyar zuciya ta farka, ya ce
"Aziza muje gida" girgiza kai Aziza ta yi ta ce
"Baffa ba zan je gida ba har sai ka gaya min waye Banju da Bahula" Baffa ya ce
"Yanzu kuwa zan gaya miki Aziza, yau zan baki labari"
Tabb cakwakiya! Shin ya zata kaya ne? Idan Baffa ya ba wa Aziza labari taya za a rabasu da wannan
bala'in? Ga shi Azima ta bar yankin kwana ta do shi hanyar shiga gari,Dukkan wasu manya tambayoyi
yana sauran shafuka da suka rage a gaba, naira darinki ya isheki! Idan kuma kika jira cmplt dari uku.
Karku bari ayi babu ku.
Gyara zama Aziza ta yi ta naɗe kafarta sannan ta ce
"Ina sauraronka Baffana!" miƙewa tsaye Baffa ya yi ya juya baya gami da maida hannunwansa baya ya yi
tsayuwar da jaruman maza ke yi wanda suka yarda da kansu ya koma ainahin asalin MAGAJI BAWANSA
sannan ya ce
64
HAUSACINEMA.COM
"Aziza! a da an yi wani mutum jarumi! sadauki! jajircacce! tsayayye! marar tsoro da fargaba!, da tare
dukkan wani faɗa! kin san ana cewa ba a faɗa da aljani ko? to wannan mutumin yana yi! wanda a yanzu
shike tsaye a gabanki! Wanda wannan mutumin mahaifi ne gareki da kuma 'yar uwarki Azima, kamar
yadda kika sani Ardo mahaifina ne wato kakanku! Inna wuro mahaifiyata ce! wasu daga mutanen
yankuna suna fadin cewa nayo gadon Arɗo a lokacin yana saurayi, amma kin san me Arɗo ya ce?" Aziza
da ta ƙurawa Baffanta ido tana yi masa kallo kamar bata taba ganinsa ba dan gani ta yi gabadaya ya
canza mata ya tashi daga Baffanta da ta sani ya koma wani mutum daban ta girgiza kai alamun a'a, Baffa
ya ɗora da cewa
"Arɗo cewa ya yi ni daya ne tak a wannan yankin dama sauran yankuna babu na biyuna! domin kuwa
baiwata daga Allah ne, tun ina yaro nake mu'alama da aljanu sannan nake taimako! a taimakon da
nakeyi ba iyakar mutane ba har ma da aljanun,a lokacin na shiga yankuna da dama dan kai wa wasu
dauki! Yankin kwana ta shahara ta yi suna ta sanadina, tun a lokacin nake cin karo da abokan gaba da
maƙiya wa inda basu sona sabida farin jinin da nayi a wajan yan mata a lokacin babu wani kyakkyawan
jarumi ka ma na, shiyasa na kara yin baƙin jini, mahaifiyarku kamar yadda ku ka sani 'ya ce ga Ƙanwar
Arɗo wanda suke uwa daya uba daya, Jumala yarinya ce mai kunya da natsuwa da hankali da sanin ya
kamata, tun ranar da naje gidan Inna Kab'o na ganta naji na kamu da sonta amma ban san taya zan
bayyana mata ba, Jumala ta ta so ne a babban gida wanda suke da tarin iyalai masu yawa, wanda a
yanzu Jumala ita daya ce tal ta rage a danginta duk Banju ya kashesu!"
Kasa hakuri Aziza ta yi ta ce
"Baffa miye dalilin Banju na kashe mutane? Sannan naji Baffa Mandi ma ya ce shi ya kashe masa
ahalinsa! Sannan wanene shi Bahula din?"
"Bahula mace ce ba namiji bane Aziza! Saurin me kikayi Aziza? Zaki san komai a yau! duk wani jeji babu
wanda bana shigansa da ikon Allah sannan na fito lafiya ba tare da wani abu ya sameni ba, domin nayi
imani da Allah da ANNABI MANZON ALLAH S,A,W, nayi karatuna a wajan wani Babban malami a nan
yankin kwana mai suna MALAM SHAINI wanda shima ahalin yanzu baya raye Banju ya kashesa! shi da
iyalansa!"
"Kenan Baffa yawancin mutane Banju ya kashesu?"
Juyowa Baffa ya yi ya kalli Aziza sannan ya yi wani murmushi ya ce
"Kisan da Banju ya yi ba zai kirgu ba, dan zan iya ce miki a cikin kashi dari na mutanen yankin kwana
Banju ya kashe kashi arba'in! Banju mugu ne, na kasance ina shiga jeji dan nemo ganyayyaki na haɗa
magani, akwai wani jeji mai sunan jejin 'Bingel, hakika har kwanan gobe ban kara shiga jejin 'bingel ba"
"Kenan Baffa akwai jeji mai suna jejin 'bingel?"
Baffa ya gyaɗa kai
65
HAUSACINEMA.COM
"E Aziza, akwai a wannan jejin ne na tafka babban kuskuren da ban taba yi ba a rayuwata, ko kuma nace
ya haɗu min har da tsautsayi! dan a wannan jejin ne tsautsayi ta haɗani da Banju, a da ban san wani abu
mai suna tsoro ba a rayuwata! Banju shine mutum na farko da ya fara shuka min tsoro a zuciyata, ba dan
komai ba sai dan ikirarin da ya yi a kaina da mutanen yankina a sadda zan kashesa! ba dan komai na
tsorata da Banju ba illa ta'adi da b'arnan da ya yi a yankin nan"
"Ranar wata laraba ba zan taba mantawa ba naje jejin 'bingel dan nemo wani ganyen magani da zan
haɗawa Inna Kab'o mahaifiya ga Jumala Hajjarku ciwon kafa ya sakata a gaba, a lokacin kuma an gano
cewa ina son Jumala ita ma kuma tana sona har an fara maganar haɗamu aure, na shiga jejin 'bingel har
na tsinƙe ganyayyakina zan fita, da shike duk inda zanje ina tare da addana kin san fulani da takwabinsu
suke yawo ni kuwa harda kifiya nake yawo, kifiyata kuma tana da guba a jiki, sabida shige-shigen da nake
yi na saka rayuwata a hatsari dole na dinga tafiya da kariya duk da nasan ni Allah shike kareni, kifiyata ba
mutum ba duk wani abu da zan harba da shi sai ya mutu walau na harbi aljanu ko mayu ko wani dabba
ko ma me da kika sani, na juyo zan bar jejin bingel ban ankara ba na hangi wani zureren jelar maciji mai
cike da ban tsoro, dama kafin nan a kwanaki muna samun koke-koke daga maƙotan yankuna a kan saren
maciji wanda nike zuwa dubawa,saren macijin kuma ya fita daban da saren macizan da na sani, to ganin
wannan macijin ke da zuwa ban tsaya dogon tunani ba sabida na ɗan firgita na ciro kifiyata har uku na
saita macijin na harba, kin san wane harba?" da sauri Aziza ta girgiza kai
" BAHULA wanda ƘANWA take a wajan Banju, wanda yake haukan sonta yake ji da ita, ban taba sanin
suna rayuwa a wannan jejin ba, sannan ban san da cewa aljanun macizai bane,ni dai na ga Babban maciji
kuma na harba, ina harbinta nan naga abunda ban taba gani ba, wato nan ta rikiɗe ta zama mutum
kifiyar da ma harbeta da shi daya a kirji daya a juya daya a baya, kafin na farga da abunda na aikata nan
naji ihun Banju yana furta "BAHULAAAAA!!" wanda sai da jejin bingel ya girgiza, a lokacin da Banju ya zo
ga Kanwarsa Bahula ina tsaye ina kallon Ikon Allah, yayinda lokaci daya naji jikina na rawa, ko a lokacin
da Bahula zata mutu sai da ta cewa Banju Dan Allah ya gyara halinsa na mugunta bata so a sake koransa
a wannan jejin kamar yadda ya buwayi asalin garin da suke a jejin aka koresu ta hanyar yi musu turaren
barkono dan tun asalin Banju mugu ne fiye da misali, a lokacin da na ga haka na matso kusa ina bai wa
Bahula hakuri, murmushi ta min bakinta na fitar da baƙin jini ta ce min ba komai tasan ba da gangan nayi
ba, sannan ta roƙi alfarma a kan cewa na bar ɗan uwanta Banju yayi rayuwarsa a jejin bingel, sun taso
tare kamar yadda aka haifesu tare dan su ma yan biyu ne, a hannun Banju Bahula ta cika, Bahula tana
mutuwa Banju ya hau kuka ina basa hakuri dan babu taimakon da zan iya yiwa Bahula dan guba ya
shigeta,hakika nima nayi kukan kuskuren da na aikata, nan na dinga ba wa Banju hakuri, amma abunda
ya ce min shine, shi BAYA MANTUWA,KUMA BAYA YAFIYA a lokacin Banju ya yi yunkurin kasheni amma
ya kasa, yayinda ni kuma na gudu,ina zuwa gida banyi nauyin baki wajan faɗawa mutane abunda ya faru
ba,tabbas a lokacin mutanen kwana sun tsorata matuka,inda aka yi cincirindo aka je aka ba wa Banju
hakuri amma ya nuna sam ba zai hakura ba, bayan kwana biyu da faruwan haka nan yankin kwana ta
koma mace-mace na hanyar kisan maciji ko kuma kisan gilla ta sanadin wani gurb'ataccen guba wanda
Banju ne ke yi, a kwana biyu Banju ya kashe mutane sama da dari a yankin kwana, nan fa