Showing 12001 words to 15000 words out of 94205 words

Chapter 5 - Azima-Da-Aziza-Macizai Ne Complete

20 Jul 2024

37834

Wallahi! Wallahi! Kinji na rantse miki ko? To sai kinje, kuma dole ki ba wa Baffa amsar
tambayoyin da zai miki, za ki tashi ne ko sai na b'ace dake a dakin nan na wujijjigaki!?" Aziza ta karasa
maganar idonta da fatar jikinta suna canza kala, ganin haka yasa Azima miƙewa fuuuu ta fice, rufe ido
Aziza ta yi ta dawo dai-dai sannan ta bi bayan Azima, a tsaye ta sameta Baffa na tuhumarta inda ta samo
zaren sakar dana, cike da rashin tsoro da rashin kunya ta ce

"A inda ake samu na samo!"

"AZIMA!!!" Aziza ta faɗa a tsawance ta yi kanta dan ta kai mata mari, da sauri Hajja ta ja hannun Aziza
sannan ta fashe da kuka, murguɗa baki Azima ta yi ta fice a gidan ma gabadaya, Baffa kuwa suman tsaye
ya yi, Aziza kuma tana lallashin Hajja dake kuka.



Cikin kuka Hajja ta ce

"Wai ni meke shirin faruwa dani ne kam? Me yasa Azima ta zama haka? Kwata-kwata yanzu bata
shakkar gaya mana magana! Aziza dame ku ke so naji? Idan ba ki taimakawa yar uwarki ki gyara mata
halinta wa zai iya yin hakan?" Hajja ta ci gaba da kuka, Baffa kuma bukka ya shige ya zube a bakin gadon
kara jikinsa na rawa, hakika jejin lore ɗan adam baya shiganta ya fito lafiya, duk ɗan adam din da ya
shiga jejin lore to sunansa gawa! Shi ma sanadiyyar shigarsa jejin lore ya yanko zaren saƙar dana sadda
zasu gwabza da Banju ne, rass! rass! rass! gaban Baffa ya bada nan zufa ta shiga tsatstsafo masa ta ko
wace kusurwar gashi dake gangar jikinsa, a fili ya ce

"AZIMA BA MUTUM BA CE! TAYA ZAN GWADATA NA GANE HAKAN DAN NA WARKARWA ZUCIYATA
TANTAMA DA ZARGI!? INNALILLAHI WA INNA ILAIHIRRAJIUN! YA ALLAH KASA KAR ABUN DA NAKE
KWANA NAKE TASHI DA SHI YA ZAMA GASKIYA!" Baffa ya karasa maganarsa hannunsa a sama hawaye
na gangarowa.




29
HAUSACINEMA.COM


Da kyar Aziza ta ɗaga Hajja ta shigar da ita bukkarta tana lallashinta amma ina Hajja ta kasa tsaida
hawayenta, kasa juran kukan nata Aziza ta yi ta miƙe a hankali ta fita zuwa randar kasar dake tsakar
gidansu ta ɗibo ruwa a kwarya ta bude bakinta ta zuba abu a ciki sannan ta koma ta ba wa Hajja, ƙin
karba Hajja ta yi ta ci gaba da kuka, Aziza ta ce

"Dan Allah Hajja kiyi shuru ki daina kuka, kin ga gidan nan bamu da sauran ganyen magunguna balle na
haɗa miki ki sha idan kanki ya fara ciwo, zan yiwa Azima magana ga ruwan nan ki sha zuciyarki ta yi
sanyi" da kyar Hajja tasa hannu ta karbi ruwan ta sha, tana shan ruwa ko minti uku bata yi ba, ta zube a
jikin Aziza, hawaye ne masu zafi sosai suka zubowa Aziza a fuskarta a fili ta ce

"Kiyi hakuri Hajja ki yafe min ba zan iya ci gaba da kallon kukanki ba, baccinki shine mafi alkhairi, tun a
yau da ba ki san su waye mu ba kina irin wannan kukan ran da kika sani za ki hadiyi zuciya ne Hajja? Ina
ba zan bari hakan ta faru ba! Ba zan iya rasaki ke da Baffana ba! Zan ci gaba da boyewa tare da dakatar
da yar uwata, ko da kuwa zamu kashe juna" Aziza ta karasa maganarta tana sake rungume Hajja, ta sha
kuka sosai kafin ta gyarawa Hajja kwanciya ta fita.

sallama ta yi a bukkan Baffa, da sauri Baffa ya share hawayensa ya ce

"Shigo Aziza" cikin natsuwa ta shigo,zama ta yi kusa da kafarsa ta ce

"Baffa kuka kake yi?" girgiza kai Baffa ya yi ya ce

"A'a ba kuka nake yi ba Aziza" shuru Aziza ta ɗan yi kafin ta sauke ajiyar zuciya ta ce "Baffa

ina so na san meke ƙunshe da wannan zaren da Azima ta saƙa"

"Me kuma kike so ki sani bayan wanda na gaya miki Aziza? Hatsarin da ke cikin wannan zaren ba zai faɗu
a baki ba tsananin yawanta, da ace za a dauki kwaya ɗaya tak! A jefata a cikin rafin jimulo, ina mai
tabbatar miki duk wanda ya sha ruwan wannan rafi zai mutu!"dam! dam! dam! gaban Aziza ya bada nan
ta shiga saƙe-saƙe a ranta tare da tunane-tunane, shin wa Azima take son kashewa da wannan zaren?
"BAFFA" wata zuciyar ta bata amsa da sauri ta miƙe tsaye a firgice tana zare ido tare girgiza kai gami da
fadin



"A'a karya ne! Ba zai yu ba! Ba zan bari hakan ta faru ba!" ganin yadda ta ruɗe lokaci ɗaya ne yasa Baffa
tashi da sassarfa ya kamahannunta ya zaunar da ita ya ce

"Aziza natsu mana! Tsaya...kina ji? Menene? Gaya mini? Miye ba za ki bari ya faru ba?" kuka Aziza ta
fashe da shi mai tsanani tana kwanciya a jikin Baffa, sosaihankalin Baffa ya tashi yana tambayar Aziza
meke faruwa!.

Cikin kuka Aziza ke faɗin



30
HAUSACINEMA.COM


"Me yasa! Me yasa! Me yasa!" da kyar Baffa ya shawo kan Aziza ta yi shuru ta daina kuka, Baffa ya ce

"Aziza meke faruwa ki gaya min gaskiya karki boye min komai, ni mahaifinki ne" saita natsuwarta Aziza
ta yi ta ce

"Baffa, haihuwarmu ta yi muku rana?"

"Subhanallahi! Wannan wace irin magana ce kike faɗi Aziza?"

"Baffa kukan da Hajja ta yi a kan Azima dazu bazan sake bari hakan ta faru ba, ba zan sake bari ba!"
ajiyar zuciya Baffa ya sauke,ita kuwa Aziza ta yi hakane dan kawar da shakku a zuciyar Baffa, shuru na
ɗan wani lokaci ne ya ratsa wajan kafin Aziza ta ce



"Amm Baffa? Taya za a lalata zaren saƙar danar da yake hannu Azima?"

"Wannan ba shi bane abunda nake tunani Aziza, yadda aka yi Azima ta samu zaren nake tunani"

"Amm amma Baffa ta ce inda ake samu ta samu! Ya matsayin hatsarin jejin lore yake?"

"Azizafaɗin hatsarin jejin lore ba zai yu ba, dan yafi karfin ki fasalta shi da komai, taya har Azima zata
shiga wannan ƙasurgumin jejin ta fito tana yar adam? Wannan shine tambayar da nake yiwa zuciyata
amma na kasa samun amsa, ban san meke shirin faruwa da mahaifana ba"




"Baffa ka rabu da maganar Azima, kasan wani lokaci ba hankali gareta ba, yawwa kuma Baffa na mance
ne ban gaya maka ba, Azima kamar tana da aljanu! Dan cikin dare sai na dinga ji kamar tana ta buge-
buge da sambatu ita dayanta, Baffa na tabbata su ne suke saka ta rashin kunya,kuma ba mamaki karya
take yi ba ita taje jejin lore ba, sai dai idan aljanun ne suka je suka kawo mata, ka yarda dani Baffa
gaskiya nake gaya maka" Aziza ta karasa maganarta tana riƙo hannun Baffa, jinjina kai Baffa ya yi ya ce

"Kenan wani irin aljanu Azima ke da shi? Wanda har zasu iya kawo mata zaren saƙar dana? Me zata yi da
shi? Kuma har tasan yadda ake saƙata?" zare ido Aziza ta yi ta hau rawar murya tare da in'ina

"Amm....eh.....umm....ohh...Baff....Baffa ....kar...ka...da..mu...da...Azima...ni nan zanji da ita, zan mata
hayaƙin aljanu zata warke da yardan Allah na san ka yarda dani ko Baffa?" murmushi Baffa ya yi yana jin
kaunar Aziza a cikin ransa, hakika ba zai ce baya son Azima ba tunda ita ma ƴarsa ce, amma aka ce mai
kyautata maka shi ne wanda yake rayuwa a cikin zuciyarka,

"Na Yarda da ke Aziza, Allah ya miki albarka" murmushi Aziza ta yi ta miƙe tsaya tare da fadin "Amin
Baffana" fita ta zo yi a bukkan har ta duƙa sai kuma ta ɗagotare da juyowa ta ce




31
HAUSACINEMA.COM


"Amm Baffa? Baka faɗa mini abunda zai iya lalata zaren saƙar dana ba?"

"Aziza sanin wannan ba sauki garesa ba, har sai an koma jejin lore, jejin da mutane ba su shiga"




"To amma Baffa kai a garin yaya ka shiga ka fito?"




"Tsoron tarihi ne Aziza, kun dai sannin a matsayin mahaifinku! Amma har kwanan gobe baku da tarihin
mahaifinku, na sha miki alƙawari zan baki tahirin jarumtar mahaifinki! Abunda yasa bana son faɗi yanzu
sabida jarumtar bata jawo min komai ba sai babban kuskure"

Da sauri Aziza ta dawo ta zauna ta ce

"Baffa kamar ya? Dan Allah ka gaya min"




"A'a Aziza dama kin tashi kin tafi ne da ya fi miki alkairi, dan ba zaki ji komai ba a yanzu" ganin yadda
Baffa ya yi maganar yasa Aziza miƙewa a hankali ta fice, tana fita ta koma bukkansu tana tsaye tana ta
saƙa da warwara, a fili ta ce

"Kenan domin dakatar da Azima nima sai naje jejin lore? Idan kuwa hakane! yau din nan zanje domin
dakatar dake, amma kafin nan sai kin gaya min wanda kike hari da zaren sakar Azima!" Aziza ta faɗa tana
harɗe hannuwanta.

Zaune suke a fadar sarki Chubaɗo, da sauri Maga Isar da saƙon kwana ya zo ya zube a gaban sarki ya ce

"Ranka ya daɗe! Sako ce daga yankin ja'i" da sauri wa inda suke zaune a wajan suka mai do da kallonsu
kan Maga Isar da Sako, wazirin kwana ya ce

"Maga Isar da sako, buɗe ka karanto mana abunda yankin ja'i suka rubuta" jiki na rawa Maga Isar da
saƙo ya zo zai buɗe sakon sarki Chubaɗo ya dakatar da shi da cewa

"Dakata! Maga Isar da Saƙo, wannan saƙo ba na iyakar mu na nan kawai za a karanta ma wa ba, a'a
yanzu maza kuyi aike a tara mutane,kuje ku sanar da Mai unguwa Ori, ku kira Arɗo tare da Baffa Mandi,
da Magaji Bawa duk a hallara yanzu" Maga Isar da sako ya amsa da to, sannan ya mike da sauri dan isar
da saƙon sarki chubaɗo.

A cikin yan mintuna ƙalilan kowa ya hallara a fadar sarki Chubaɗo , kowa yana fargaban kar yankin ja'i
ace sun rubuta ba zasu taimake su ba.



32
HAUSACINEMA.COM


Bayan kowa ya bada hankalinsa sarki Chubaɗo ya ce

"Maga Isar da sako karanto mana abunda yankin ja'i suka rubuto" Maga Isar da sako ya amsa da to,
sannan ya buɗe wasikar yankin ja'i ya fara karantowa kowa naji.




" Wa'alaikumussalam,da fatan yankin kwana su na lafiya? Ya kuma fargaban iftila'in da ku ke ciki? Kashh!
Ayya! Allah Sarki! Wasikarku ta iso garemu na neman taimako! Tunda har yankinku ya duƙawa tamu
yankin,mun yarda zamu taimaka muku da Innu Maciji! Zai zo gobe, amma abun mamaki ace kuna da
mutum a yankinku kamar Magaji Bawa har sai kunzo yankinmu neman taimako? Koma miye
daukakarmu ce, tunda yankuna yanzu zasu shaida kun watsar da makamanku wa yankinmu, saƙo daga
yankin ja'i, mun karb'i ƙudirinku!_"

Maga Isar da sako yana gama karantawa Baffa ya miƙe cikin fushi ya ce

"Sadda muka tura wasika yankin jimo dan su taimaka mana da jarman macizai magana mai dadi suka
mana sannan suka jajanta mana suka amince da bukatarmu, amma yanzu wannan wasika na yankin ja'i
har da izgilanci a ciki" Arɗo ya mike shi ma ransa a b'ace ya ce

"Duk abunda aka gaya mana laifin waye Magaji? Na ce laifin waye!?"tsohon Sarkin fulanin kwana Baffa
Mandi ya ce

"Yanzu ba lokacin nuna fushi bane sabida halin da muke ciki, tunda sun amince zasu taimaka mana
shikena!" Garkuwan fulanin kwana ya ce

"Amma abunda Arɗo ya faɗa gaskiya ne, Magaji da ace ka yi wani abu a kai da yanzu wannan bala'in an
gama shi, me yasa ba zaka dawo yadda kake da ba? Idan ka manta da takenka sai a tuna maka....!"

"Ya isa haka Garkuwa!" Baffa ya dakatar da shi idonsa jajur, Ori ya ce

"Garkuwa yana da gaskiya Magaji, da ace kayi wani abu a kai da yanzu yankin ja'i basu gaya mana
magana ba" Wazirin kwana ya ce

"Tabbas hakane Magaji, da ace kayi wani abu a kai da har yaushe zamu duƙawa yankin ja'i balle su mana
izgili kamar mu muka ɗorawa kanmu masifar!" haka kowa yasa Baffa a gaba ana cewa duk abunda
yankin ja'i suka faɗi har da laifinsa, jikin Baffa ne ya hau rawa ya daka tsawa da faɗin

"NA CE YA ISAAAAA!!" ya juyo yana kallon mutanen da suke wajan ya ce

"Wai ku baku duba gagarumin bala'in da nake hangowa ne? Na koma na haƙo kayayyakina da na binne
tamkar haƙo maƙabarta ne wa yankin nan! Dan karku manta da aljanun da mayun da na rufe! Duk abuna




33
HAUSACINEMA.COM


ban cika kisa ba sai inta kama dolen- dole! Tunda na kashe Banju nayi sallama da kwanciyar hankali,
wanda a yau duk faɗin yankin kwana babu yaran da ake zargi kamar yarana AZIMA DA AZIZA! duk da ba
zan hanaku zarginsu ba, amma ko da sau daya ne zaku min uzuri! na rayu ne wa yankina inda nayi aikin
tuƙuru da jinina da lafiyata! naje na haƙo abunda na binne duk aljanu da mayun da na ɗaure tass zasu
kunce, me ku ke tunani zai faru da iyalin da nake da shi a halin yanzu?" Baffa ya faɗi yana fashewa da
kuka yana dukawa, jikinsu ne ya yi sanyi sosai, yayinda Arɗo ya dago Baffa yana rarrashinsa inda sarki
Chubaɗo da mai unguwa Ori suka hau ba shi hakuri tare da nadaman ganin laifinsa, Arɗo ya ce

"Kayi hakuri Magaji, yanzu abunda za ayi a rufe wannan maganar, Allah ya kaimu gobe Innu Maciji ya zo
ya warware mana wannan sarƙaƙiyar" Sarki Chubaɗo ya ce

"Kowa zai iya kama gabansa"

Da kaɗan-kaɗan aka fara watse wa, Arɗo da Baffa Mandi da Baffa ne suka fara tafiya, Baffa Mandi ya ce

"Amma na rasa me yasa Magaji kake yawan maganar Banju" Baffa ya ce

"Sabida ni kaɗai nake ganin abunda nake gani a gidana" yana gama faɗin haka bai jira amsarsu ba ya yi
gaba, Arɗo ya sauke ajiyar zuciya ya ce

"Mandi, akwai abunda yake damun Magaji" Baffa Mandi ya ce

"Nima haka nake gani, amma anya baya da nasaba da yaransa da ake yawo dasu ake zarginsu kuwa? A
gaskiya Magaji ya yiwa yankin kwana hidima bai kamata a dinga masa haka ba"

"Gaskiya kam hakane" tafiya sukeyi a hankali suna tattaunawa, Baffa kuma hanyar gida ya ɗauka.

Zaune ta sameta a rafin jimulo, ita ma zama ta yi kusa da ita ta ce

"Azima tambayarki na zo yi"

"Wai ni Aziza me yasa kika rainani ne? Ba nice gaba da ke ba?" murmushi Aziza ta yi ta ce

"Au haba dai da gaske? Rainin babu dadi ne? To haka iyayenmu suke ji a ransu idan kika musu, balle ni
da ba ki bani ko da kwana daya bane, kawai iskar duniya kika rigani shaƙa" Azima ta kyalkyale da dariya
ta ce

"Macijiya Aziza me ya kawo ki wajena?"

Kallonta Aziza ta yi ta ce

" ZAREN SAƘAR DANA! WA ZA KI KASHE DA SHI!?" sake kyalkyalewa da dariya Azima ta yi ta ce




34
HAUSACINEMA.COM


"Idan naki faɗi fa me zakiyi?"

"Sai na gwada ta wata hanyar!" Aziza ta faɗa tana mikewa tsaye, da sauri Azima ta mike ta ce

"Muje zuwa" tana gama faɗi ta hau ajijiya, Aziza na tsaye tana kallonta.

A wani ƙasurgumin jeji Aziza ta tsinci kanta, jeji mai cike da wani mugun duhu da abubuwan tsoro tare
da wasu mugayen halittu marasa kyawun gani da ban tsoro, haƙiƙa ganin wa innan abubuwa sun tsorata
Aziza, amma tunowa da maganar Inno Fandi da cewa kar ta tsorata yasa ta takure tare da tattaro
jarumta, ta hau tafiya, tare da furta kalman "makarin zaren saƙar dana!" wani sowa ne taji na tashi ta
tsakiyar kanta da wani irin mugun jijjiga nan wasu halittu suka yi sama da ita, saura qiris Aziza ta saki ihu
amma kuma ta daure tana karanto dukkan adduar da ya zo zuciyarta, nan halittu suka dauketa suka kara
yin sama da ita suka hau tafiya da ita a cikin duhu,amma duk wannan duhu ba shi ya hanata ganin
mugayen halittu marasa kyau da ban tsoro ba.

Wa inda suka dauketa basu ajiyeta a ko ina ba sai a gaban wani katon halitta wanda bata san dame zata
fasalta halittarsa ba sabida tsananin muni da girmarsa, ana ajiyeta muryar wannan katon abun ya ce

"Keeeee! Me ya kawoki jejin lore!!!" a yadda muryarsa take ɗan adam idan ya jita ya ci ace ya mutu
tsananin amo marar daɗi da kaifi, cikin dakiya Aziza ta ce

"Makarin zaren saƙar dana, shi nake so" shewa wannan halittar ya yi,sannan ya ce

"Ya matsayinki yake a halittu!?"




" NI MACIJIYA CE!" Aziza ta bada amsa, wannan halittar ya ce

"Ke ba iyakar macijiya ba ce, akwai wani sirri a tattare dake, dan haka ko ba mu baki makarin zaren saƙar
dana ba,kaifin gubar dake jikinki zai iya ƙonasa! Amma kasancewar sau daya tak! Muke bada alfarma
zamu baki taimako guda daya, zamu ƙara miki karfi, da kinje ki hurawa zaren wuta ta idon ki zai ƙone
ƙurmuss! Ga wannan" ya faɗa yana daukar wata kyakkyawar dutse mai cike da hasken gaske ya hura
mata shi ya shige ta goshinta, abun na shiga jikin Aziza sai da ta girgiza ta yi kamar zata faɗi amma ta yi
iyakar iyawarta bata faɗi ba,dama tana tsaye ne ita ba a sama ba ita ba a kasa ba, abun na shiga jikin
Aziza nan ta kalli fatar jikinta ta ga yana sab'ulewa har yana komawa wata fari-fari, kafin ta gama
dawowa hayyacinta tuni ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login